TAWA TA SAMENI CHAPTER 1 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 1 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Na mike a hankali ina ninke sallaya ban kai ga ajiyewa ba naji ana sallama,na juya cikin don san in dauki muryar mai sallamar har kin shigo kenan?nace bayan na amsa sallamar ta shigo sanye da kayan makarantar islamiya masu launin farare kar,riga da wando da hijabi. Tace kina kallona ba zaki yi sauri ba sai munyi latti ko?nace ko munyi latti ai yau akwai layi na nufi daki dama nayi wanka sai kawai na dauki kayan makarantana dake goge kan gado nasa,Amira tace su mama basa nanne?nace eh basa nan gashi har jamila ta tafi a lokacin islamiya yayi amma basu dawo ba,na rungume takarduna da Alkurani na na fito falo muka fita na mika ma amira ta rike min


littattafaina don zan kulle kofar,natura key din Www.bankinhausanovels.com.ng inda muke sawa in mama zata unguwa ni kuma ban dawo daga makaranta ba sai ta aje min a gun in kuma zan fita tace in aje mata.Amira ta dube ni ta dubi dakin su mami tace yau su mami ba zasu bane?nace da kyar ne don yau ko makarantar boko bataje ba bata jin dadi in mun dawo kin gaida ita.isarmu islamiya kenan muka tarar da an tare yan latti ana yi masu bulala,Amira ta soma dariya don ta
sanni da tsoron bulala na dafe kirji ina fadin yau na shiga ukku zamu sha bulala ni iman,Amira tace don Allah mu karasa ba kece kika jamanaba?nace Amira ina jin tsoro ta ja hanuna na bita muna isa gun muka tadda harda Ahmed yayan Amira don shine Amir dinmu yace don Allah ku zo inyimuku ku wuce don yan kwanakin nan kun kware gurin yin lattiiNace don Allah yaya Ahmed kayi hakuri yace wilh sai nayi maku kun fi sauran ne?da zan kyaleku ya ci gaba da cewa kuna bata mani lokaci in har kuka bari kowa ya gama shiga sai na zane ku tas,wani kusa dashi yace to kai Ahmed ka bar su su wuce mana,yace Allah Aliyu bazasu shiga ba sai na dakesu wanda yaya Ahmed ya kira da Aliyu yace to bari ni in dake su to,yy Ahmed yace sai dae kai na dake kaa
madadinsu,in ko ba haka ba sai dai suzo ni in dakesu da kaina,Amira na da zuciya don haka sai taje ta mika
hannun shi ko bai bugi hannunba ya zuzzuba mata a
jiki,ganin haka ya sani na kuma rudewa ina faman
magiya don ni kowa ya sanni da shegen tsoro sannan
bani son abinda zai taba mani lfyata don haka ma
dawuya ka ga nayi laifi nakan yi kokari ganin nabi dukkan dokar da aka shimfida a gida ko a Www.bankinhausanovels.com.ng makaranta.Amira ganin zan bata mana lokaci taje gaban yy Ahmed tace ka bige ni a madadinta shiko da gayya ya ringa tsala mata har sai da Aliyun nan suka ce ya isa mana Ahmed niko hawaye na somayi na kama Amira muka wuce ina fadin me yasa kika je ya buge ki?ta soma share mani hawaye muka wuce ajinmu,Shidda na yamma daidai muka tashi dama mu yan aji biyar Ajinmu a sama yake,don haka titin kan layinmu naji an kwala mani kira cikin fada na juyo sai naga anty mariya gabana yayi faduwa don na san ganin ta ba alkhairi bane hakan ce ta kasance domin kuwa tana isowa gun mu sai ta hauni da zagi wai na taho makaranta ban jira su kamal ba don naga ba kannena bane shiyasa ta cigaba da zagina gami
dayi mani gorin gida wai shegiya agola yar kara nazo zan fare,Amira tace mani don Allah iman zo muwuce taja hannuna cikin fushi tayi maganar,anty mariya ta koma kanta tace ke kar kiyi mani rashin kunya don zanci ubanki a nan,Amira tace ba dai ubana ba kuma har kika yarda kika buge ni zakiyi da kin sani,cikin rawar jiki na rufe ma amira baki muna cikin wannan hali sai ga anty hadiza da bilkisu da saade dukkansu sai zaginmu suke yi,Sa’a har da dungurina,nan amira ta kai mata duka nayi saurin rike amira don kar suyi mana taron dangi su bugi banza don nasan kadan suke jira anty mariya tace waike amira nan da dukan Sa’’a zakiyi?amira tace yo da sai in barta ta duke mu,don kunga bata ramawa ne,iman din shi yasa ku ka raina ta, taci gaba da cewa,ai Sa’ar ba girman Iman din tayi ba,bilki tace to ta koma gidan ubanta mana in kuma bata dashi bane mu sani,naja hannun Amira muka wuce Amira ta cigaba da lallashina Www.bankinhausanovels.com.ng
sannan tace min,don Allah Iman in tambayeki mana?na share hawayen fuskata da gefen hijabina nace ina jinki tace babanki ya rasu ne ko yana nan? In ya na nan ina yake?na dan yi shiru sannan nace Amira baba na yana nan bai rasu ba wasu hawayen suka kuma zubo mani ban damu da in goge ba na cigaba da cewa yana tudun wada ta nan kaduna,Amira ta ce to ki koma mana don zaifi maki kwanciyar hankali komin talaucin ubanka ya fi zaman agolanci y not ki koma can?nace uhhm Amira mubar zancen nan wata rana zan sanar dake dalili mai karfi da ya hanani in bar gidan nan sannan kisan mahaifina ki kuma daina zargin ko kwadayi ne ya zaunar
dani a nan,Amira tayi sauri ta rike ni gami da tsaidani
wuri guda tace wilh ni ba nufi na kenan ba naga
wulakancin da su Sa’a ke maki yayi yawa ne shi
yasa,nayi mirmushin karfin hali nace no a
Amira karki damu na fahimceki sannan muka wuce gidan su Amira,kamar minti goma na dauka gidan su Amira sannan ta rakoni kofar gidansu tace min a cikin satin nan ba zata shiga gidanmu ba,ina shiga naga su Anty mariya sun rigani dawowa kuma sun fadi karya da gasky sai faman fada suke su da iyayensu suna ganina ai dawa Allah ya hada su ba dani ba suka hauni da masifa,Haj Kulu mahaifiyar mami harda aibantani gami dayi min gori
sannan tace zata ga Amiran don ubanta sai ta gaya mata dalilin da yasa ta zagi su anty mariya don ba sa‘anin yinta bane,ni dai sum sum na wuce daki
Mama na gani a falo ta zuba tagumi da alama taji duk abinda suke cewa (kishiyoyin nata)ta dubeni fuskanta cike da tausayina tace Iman menene dalilin da yasa kika tsokani mutanan nan bayan kinsan halinsu Sarai nace mama wilh ban san me nayi masu ba na dai ga anty mariya sun zo da su Sa’a suna ta Www.bankinhausanovels.com.ng faman zagina wai ko na taho makaranta ban jira su Kamal ba ko mene oho mama tace to naji suna cewa kuna ta zaginsu keda Amira nace Allah mama ni sam ban ma yi magana ba Amira dai ce kinsan ta da zuciya shine fa ta tanka masu amma sam bata zagesu ba,mama tace to don Allah ki daina kulasu sam musamman a kan titi in ma sun zo maki da irin wannan ki dinaga basu hakuri kiyi wucewarki kinji
ko?nace to mama muka mike don yin sallar magariba.
Misalin sha biyu da rabi muka taso daga harda yau ma
yan dakinmu ne kadai ni da jamila da sagir muka je,dama sauran yan gidan zuwa islamiya bai damesu bane bare ma hadda,gara ma mami takan je to amma tun Friday bata jin dadi,muka tadda mama a kicin tana girki na shige kicin din bayan na ba jamila Alkurani na da hijab ta wuce daki nayi ma mama sannu gami da amsar albasar da take yankawa,nace yau me kike dafa mana ne,tace dan wake nayi in kin gama yanka albasar ga mai can sai ki
soya shi bari in dauko kular baban ku nasa mishi,don
yace zaya aiko a dauka nace dan waken za’’a kai mashi kasuwa mama?tace nima haka na ce mashi sai yace yasan komi na dafa ba zaiyi shakkar kaishi cikin jama,a ba,nayi murmushin jin dadin an yabi mamana ai kin iya girki ne mama,ta fita tana dariya ina jin dadin yanda mama take sakar mani fuska duk da kasancewa ta yar fari a gunta sannan mama uwa ce mai wahalar samu takan ki nata don duniya ta soshi bata fada da zagin yayanta sai dai nasiha gami da lallashi.bani manta lokacin da nake karama mama ta kan zaunar dani ta nuna mani girman Allah gami da cusa mani tsoronshi tana nuna mani abinda zanyi da tsira daga azabarshi a wancan zamanin ta kance kar na zagi kowa ko an zage ni kar na rama sannan kar na yarda sallah ta ringa wuceni don haka ma tun ina karama nasan sunnoni da farillai gami da mustahaban sallah da alwala sannan bani zagi in ma wani yayi Www.bankinhausanovels.com.ng naji sai na gudu ince kar na sami zunubi saboda jin da nayi shiyasa ban iya zagi ba,sannan mama ta na da hakuri na ban mamaki zata iya zama da kowa ga ladabi don ban taba ganin tana musu da maigidanta ba komai yace tana yi sannan ga tsafta komi namu daban yake duk inda muka shiga ni da kannena
mukan zama abin sha’awa gashi mama ta iya girki sosai na zamani da na gargajiya shi yasa maigidanta ya kanyi alfahari da ita baya shayin kawo baki ko shi akai mashi kasuwa haka nan duk da cewar basu shiri da abokan zamanta suma suna farin ciki da ranar girkinta don sunci mai dadi sannan yayansu kanyi rigima a duk lokacin da suka zo cin abincin kai ko ruwan tea ta dafa daban yake don zaka iya shanshi ba sai kasa madara ba.nayi zurfi a tunani bansan har mama ta dawo ba sai dai naji tace
haba iman har yanzu kina kan yankan albasar nan baki tashi ba?nayi firgigit na juyo tace ai kina tunanin menene haka?bata saba mana da karya ba don haka na sanar da ita tunanin da nake na kara da cewa mama ina matukar jin dadin zama dake kuma ina alfaharin kasancewarki uwa a gareni tayi murmushi tace sai ki dinga koyi da hakan kuma kiyi watsi da duk wani kuskure da kika ga nayi sai da na zuba albasa a cikin man sannan nace wlh
mama ni ban taba ganin wani kuskurenki ba tace kar ki kuma cewa haka babu mutumin da baya kuskure dan
adam ai ajizi ne nace to,sai da muka gama cin abinci
sannan na nufi dakin su mami don in gaisheta ina son
inje amma ina tsoron haj kulu mahaifiyarta yanxu ma
ganin ta shiga wanka shine dalilin da yasa xan je duk da dai bayin a dakin yake amma nasan ta shiga wanka ne a bakin kamal inda na tambayeshi ta na nan yace man ta shiga wanka na samu mami zaune a falonsu tana cin kifi nace yan jinya an samu Ify kenan tace kar kice man komi komi tunda baki zo gaisheni ba nace wlh ina son in

 WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *