TAWA TA SAMENI CHAPTER 10 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Mami tace nawa yayanmu ya baki?nace ban kirga ba nan ta shiga zayyane masu wai wannan wace irin yarinyace,Anty Hadiza tace ai wannan daga ita har uwarta annoba ce,Anty Mimi ta cigaba da cewa kunga jiya a gabana ya bata waya irin tawa ce sak koda ganin kwalin sannan yau
zamu taho nan ta zo ta rabe ya dauko mu tare kunji
biyu,cikon na uku kuma sai gashi ya raba mana kudi
kilan ma daidai ya raba tamkar wasu kishiyoy,nan suka taru a kaina wannan ya kai mani bugu kowa dai na fadin albarkacin bakinshi, Mami ta iso daidai lokacin da wasu kawayen Anty Mimi suke cewa asiri tayi mishi daga gani,in ba haka ba me zaiyi da wannan mummunar yarinyar gara ma ki dauki mataki tun da wuri akan abin, Mami tazo tana cewa Anty Mariya kuzo anguna sunzo fa ana ta nemanku,kan suyi magana Anty Mimi tace Mami muga jakar wannan jakar,sai sannan Mami ta ganni ina kuka tace Iman menene?Bilki tace ba’a sani ba
ZAMU TASHI
ke dai ki bada jaka a kace Mami tace bazan bayar ba nace Mami bata ta mika mata sai da suka kirga kudi daidai da nata dubu ashirin da biyu ne dama ban kirga ba,saura sukace kar ki bata ko sisi Mami tace wllh sai naga ya wa yayanmu in har kika dauki kudin nan,Anty Mimi ta watso kudin da jakar a jikina sannan tace ki jira abinda zai biyo baya ta wuce sauran suka bi
Www.bankinhausanovels.com.ng bayanta aka bar daga ni sai Mami inata kuka,Mami ta kwashe tana tambayata abinda ke faruwa na zayyane mata komai itama na kula ta danyi mamakin kudin da ya bani tace Iman yayanmu yana ji dake fa nace Nami ku kula da wani abu daya yayanmu nice nake mashi aiki,shiyasa yake mani alheri amma wai
suna zargin wai yana sona ne ni nasan ko mata sun kare yayanmu ba zai taba cewa yan sona ba ke Www.bankinhausanovels.com.ng kinsani balle yana da kamar Anty Mimi,Mami tace ai itama anty Mimin ba wani kyau ne da ita ba uban gashi ne kamar jirgi ya daso tasha kuma a tsaye take ba wani diri kirji kamar na bera ba wasu nonuwan kirki nace to shi dai tayi mashi Mami tace ke zo muje ba wani yi mashin da tayi kawai saboda mamansu zai aure ta. TAWA TA SAMENLhaka na fada ranar daurin auren anty mariya ba wani abu yasa na fada ba sai ganin munsa less iri daya da Anty Mimi wato wanda yayanmu ya bani nasa daya daga ciki me ruwan lemun tsami takalmi da jaka iri daya itama ni take kallo ta zauna kofar dakin yayanmu a fararen kujerunshi ranta yayi matuka gun baci naga ta yi cikin gida ni kuma sai na nufi gidan su Amira,dama dazun ta aiko Faruq wai ta dawo dama jiya ne ta tafi unguwar dosa gun kanwar mamansu da suka dawo kwanan nan shine taje kwana,ta fito wanka na sameta nan nake zayyane mata abin dake faruwa ta Www.bankinhausanovels.com.ng
dinga mamakin karfin halin irin na nasu Aunty Mimi dan yayanmu ya min kyauta ta kara da cewa komai ya Sai maki ba zai biyaki ba irin dawainiyar da kike mishi ba nace suna zargin fa wai sona yake yi,Amira tace haba dai nasan ma ba zai fara ba domin kin……na katse Amira nace ni ba ajinshi bane nasan da haka kuma ko mata sun kare ba zai so ni ba Amira tace ba nufi na kenan ba ina nufin matsalar dake tsakanin mahaifiyarki da tasa ai yasan da wannan matsalar ba zaima ce yana sonki ba.Nace ato su sai hauka suke yanzun nan na hadu da anty Mimin shine ta ganni da kayan nan har jakar to tayi cikin gida ban san me zai faru ba,dama bikin nan sai yan tsegungumi sukeyi dangin Haj Yaya naci gaba da cewa kinsan abin da ya faru ne da babansu Mami ya tambayi Haj Yaya game da kayan da za’a siya don yayanmu ya riga ya sai masu sai yace to suyi mashi
list din kudin sukayi mashi hauka to hauka mana wai fa miliyan daya da rabi suka rubuta shiko ya kira mama tayi mashi lissafin kayan dakin har da na jere dana kicin duk ta sanar dashi naji ya bata kudi sukaje ita da Anty Yagana suka sawo mashi komi don Mama cewa tayi sai da tayi ciko suka kawo ya dinga sa Www.bankinhausanovels.com.ng mata albarka itama ta bashi nata gudummuwar na zannuwan gado to wannan abin shi yayi matukar tada hankalinsu Haj Yaya da har sunce sam kayan nan bai masu ba shine baban yace yayi in baiyi masu ba to su sai nasu da kudinsu kafin Amira tayi magana sai ga Jamila kanwata da kukanta wai ana fada da Mama nace mama da wa tace Mama da mutane yan biki nace yau mun shiga uku ko takalma bansa ba na nufi gida Amira ta biyoni,tun a harabar gidan nake jin hayaniya yaya Kabir na gani ya fito daga cikin gidan ranshi a bace da ganina ya nufoni
yace kar ki shiga zo nan,na soma kuka ina cewa ni dai
na shiga uku ya ja min hannu zo muje karki shiga,nace
ina kuka yaya Kabir barni naje naga Mama yace
Mamanki tana dakin Alhajinmu zo muje ya jani dakinshi ya zaunar dani kan kujera sannan ya tsugunna gabana yace kiyi shiru zan tambayeki ne,nayi shiru ina share hawayena yace yaya Abdulrahim yace yana sonki? nace aah yayi ajiyar zuciya sannan yace alhmdll yayi shiru zuwa can yace a gaskiya Iman na dade ina sonki shiyasa ma har yau na kasa kula duk wata ya mace da sunan so
na mike tsaye na ce Kabir tun ina ganinka da gashi karka yarda na kuma jin wannan zancen kana ganin balain da muke shiga kullum a gidan nan sannan zakace wai kana sona ni dai ba ruwana,ya zaro mani ido gami da tasowa kamar zai bugeni yace sai kin soni kuma ni da ruwana ba abinda ya dameni da _ fadan iyayenmu,na mike zan fita yace kar ki yarda ki fita su Haj Laure zasu dake ki muddin kika shiga,jin maganar duka ni uwar yan tsoro na dawo na zauna na sanyaya muryata nace sun doki Mama ne?yace suna hauka ne?ita ko kulasu ma batayi
ba shine yar Alhajinmu da tazo daga maska tace ta
shiga dakin Alhajin tasa na mashi waya yanzun nan yana zuwa shiyasa nace kar kije,na cigaba da kukana yaya Kabir yana lallashina har nayi shiru ya dinga shigar dakan shi a guna yana ce min in na yarda yasan Alhajinsu zai tsaya man kuma zai nemi canjin gun aiki mu bar kaduna haka ya yi ta cusa min raayi har na soma yarda,sai dai ina tunanin mama ba zata amince ba na dai yanke shawarar zan ci gaba da addua. wayar yaya kabir Www.bankinhausanovels.com.ng
tayi kara yace in dauka don nafi kusa da wayar,na dauka sai naga sunan yayanmu sai na mika masa yace ya baki dauka ba?nace yayanmu ne ban san mai yake ce mashi ba na dai ji yace gata nan sai na kuma jin yace dakina sai gabana ya fadi,sai naji yace to gata nan zuwa,ya dubeni yace alhaji yazo yana dakinshi an ce kije.nace yayanmu na gurin ne?yace shi ne yayi min waya wai Jamila tace nine na tare ki ina kike yanxu sai shine nace gaki nan ki tafi ko na raka kine?nayi saurin cewa a’a don kar agan mu tare,cikin dar dar na shiga gidan yan biki sai ni suke kallo gashi ko takalmi babu a kafata na shiga ciki nayi sallama a kofar falon Alhaji na shiga Alhaji na
kan wata kujera irin ta karfen nan ne dama nan ne gun zamanshi sai Mama akan kujerar gefen damanshi dayan gefen Haj Yayace sai Haj Shuwa kusa da ita Haj Kulu na dakin sai yaya ta maska(wato yayar Alhj)yayanmu na kan kafet kusa da kafar Alhaji nima na shiga na samu guri kusa da Mamana na zauna a kan kafet. Alhj na gaisar sannan yayi gyaran murya yace to gara ki Murja(haj yaya)menene sanadin wannan fadan?na tambayeki dazu kince sai an kira Iman gata tazo sai ki fada muji ynxu,ta soma magana cikin sababi ni dai Alhj kawai kayi mani tsakani da Habiba da kuma ‘ya’yana in kai ta gama da kai to ni da ‘ya’yana li’ilafi,,tashanye min yara basa cin girkin kowa sai na ‘yarta sannan yanzu shi wannan miskilin dana gani kamar zai zama namiji amma ba haka bane ya tashi sai kashe mata kudi yakeyi harda yi mata anko da matar da zai aura me hakan yake nufi? na dai san rokonshi sukayi don haka ayi mana iyaka dasu ba ‘ya’yanta ba nawa,tun da ta soma bata tsaya ba kuma ba a katse ta ba,jin tayi shiru sai na dago kai na dubi kowa kowa dai ita yake kallo sannan na dubi yayanmu wanda kanshi yake kasa Alhj yace to naji naki ke kuma Habiba ya abin yake?Mama ta soma magana cikin sanyin murya lafuzza masu kyau tace ni dai Alhaji a gefena ba
wani matsala yarinyar nan dai itace matsalar, da zaka amince min da sai na dauketa na maidata wajen
kawunta don inda bata nan gidan da baza ta ga ma
‘ya’yan Haj Yaya ba bare su sata aiki sannan muddin
tana nan gidan ba zan hanata aiki ma kowa ba har Hajiya Yaya inda zata sata,amma kiyi hakuri Yaya zan maido maki da dukkan abinda Abdulrahim ya sai ma Iman sannan kuma sai kiyi mashi magana ya daina sata aiki a zauna Ify,na dubi Mama hankalinta a kwance tayi maganar sabanin Haj Yaya wadda ke cika tana batsewa. Dakin yayi shiru sai can
Alhj ya soma magana yace Murja! Haj Yaya tace na’am da karfi tana karkada kafa yace ina son kisan cewa ‘ya’yan nan nawa ne kuma wancan ma tawa ce don ni da kaina na daukota ko uwarta bata san zan kawo ta ba sai dai ta ganmu Allah yasan wannan don haka ba zaki raba min kan ‘ya’ya ba kinyi kadan,Habiba yarinya ce a kanki Www.bankinhausanovels.com.ng
amma tafiki hankali da tunani saboda haka kar ki yarda ki amshi duk wani abu da yayi mata kuma aiki duk wanda yayi niyyar sata kar ya fasa don haka na gama wannan maganar sannan ki gargadi laure ta kiyayeni da wasa naji ta taba Habiba ko Iman sai nasa an daureta gara ma ta tabaki zaifi mata sauki,Haj Maska tace yayi daidai hakan,Murja in ka girma to kasan ka girma don haka sai ta soma kuka tana cewa dama namiji ba dan goyo bane nan na dauki kudina na baka ko basu ne silar arzikin naka
ba?daban haka ai da har yanxu kana a fakirin ka dole ka min sakamako da mun wulakanci ta nuna ni tace ke
kuma zakiga hukuncin da zan yanke a kanki muddin kika kuma ko kallon min ‘ya’yane na durkusa da sauri(don har ta mike)nace don son Annabi(SAW) kiyi hakuri ta bankade ni tayi waje sauran kishiyoyinta suka take mata baya,Alhj ya bisu da kallo sannan yace Allah sarki to Allah ya sa ku gane,ya dubi yayanmu yace kaima kayi hakurin dai zan baka cikin sanyin murya yace Alhj kaimin izinin na koma
england jibi,yace na maka amma yaushe zaka dawo?kar kaje ka kuma zama yace nan da wata shida ne yace to Allah ya kaimu ya fita na bishi da kallo.
Karya ne gane halin da fuskarshi take ciki wato laifinmu yake gani ko na uwarshi,ban taba ganinshi cikin dogayen kaya ba tunda yazo sai yau boyel ne baki amma kanshi ba hula Alhaji ya dubeni yace Allah yayi maki albarka Iman kiyi koyi da halin mahaifiyarki kinji?na daga kai ya cigaba da cewa muddin kikayi halin uwarki to kin dace,sannan mijin da zaki aura ma yadace,su Abdulrahim da Kabir duk yayyanki ne duk abinda suka saki kiyi,sannan in sun maki kyauta ki amsa kice kin gode
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE