TAWA TA SAMENI CHAPTER 11 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 11 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

nace don son Annabi(SAW) kiyi hakuri ta bankade ni tayi waje sauran kishiyoyinta suka take mata baya,Alhj ya bisu da kallo sannan yace Allah sarki to Allah ya sa ku gane,ya dubi yayanmu yace kaima kayi hakurin dai zan baka cikin sanyin murya yace Alhj kaimin izinin na koma
england jibi,yace na maka amma yaushe zaka dawo?kar kaje ka kuma zama yace nan da wata shida ne yace to Allah ya kaimu ya fita na bishi da kallo.
Karya ne gane halin da fuskarshi take ciki wato laifinmu yake gani ko na uwarshi,ban taba ganinshi cikin dogayen kaya ba tunda yazo sai yau boyel ne baki amma kanshi ba hula Alhaji ya dubeni yace Allah yayi maki albarka Iman kiyi koyi da halin mahaifiyarki kinji?na daga kai ya cigaba da cewa muddin kikayi halin uwarki to kin dace,sannan mijin da zaki aura ma yadace,su Abdulrahim da Kabir duk yayyanki ne duk abinda suka saki kiyi,sannan in sun maki kyauta ki amsa kice kin gode

ZAMU TASHI 

nace to Alhj na gode,na mike na fita dakinmu na wuce
kai tsaye kan gado na fada raina a cunkushe na rasa meke daga min hankali son da Kabir yace yana min ko
matakin da Haj Yay tace zata dauka a kaina ne?wata zuciyar tace duk ba wannan bane tafiyan yayanku ce wannan amsar da zuciya ta bani itace sanadiyar tashina zaune saboda tashin hankali da naji ni a ciki na mike ina safa da marwa nace a fili ban so akayi wannan rikicin ba ba zanji dadi ba muddin yayanmu ya tafi kai zanje na bashi hakuri inya tafi na mutu,da sauri na dauki hijabina na fita falo nan nayi turus ganin mama a falon tace ina Www.bankinhausanovels.com.ng
kuma zaki?karon farko da na soma yi mata karya nace gidansu Amira tace me xakiyi?nace takalmina da gyalena zan dauko tace ko bari zata aiko maki ko ki aika Jamila karki fita ko ina ynxu zo nan kiji,na isa gunta na zauna tace kin dai ga abinda ya faru ko?nace eh tace to ina son kiyi taka tsan tsan da kowa a gidan nan

banda yawan shigewa duk wanda ya saki aiki to kiyi masa kamar yadda kikaji Alhaji yace maki,nace to ta kuma duba na tace yanaga kinyi wani sukuku dake?nace bani son tashin hankali ne mama shiyasa tace kar ki damu aikin shedan ne kuma ki cigaba da addua sannan daga ynxu zan na tashin ki duk dare in na tashi yin nafila sannan zaki dinga yin azumin litinin da alhamis,sai mu dinga tare in Www.bankinhausanovels.com.ng
kuma an gama bikin nan zanje wurin kawunki na samo
mana addu’o’i na tsari mu dukufa,Allah ya ja mana
gaba,sauran maganganun da mama takeyi duk banji su ba ina ta tunanin yanda zan ga yayanmu don nasan nice na jawo wannan tashin hankalin gaisuwar da naji mama ta na amsawa shine yasa na juyo Mami ce ta dubeni tace ya dai?na mike muka shiga dakinmu kan gado muka zube na dube ta nace ya dai tace ina gidan walima muna shirya guri sai ga Sa’a wai ana fada da mamanku da su Haj Laure har sunce sai sun zane ku?nayi tsaki nace kanfa kaya ne kin gansu nan jikina yayanmu ya bani ashe irin na Anty mimi ne shi kenan sai tashin hankali gashi yanzu ma yace zai koma jibi,Mami tace ai dama bayan biki da kwana biyu yace zai koma nace to ai gashi ba’a gama bikin ba ni gani nake ma duk laifina ne hawaye suka zubo mani akan kumatu Mami ta tsaya kallona baki bude shi ne harda kuka?kuma ma ina wani laifinki anan?
nace nasa kayan tace to baya baki don kisa bane?shi
yayanmu in zai ma mutum kyauta ba ruwanshi da wani nuna bambanci nace rakani na_ bashi hakuri,Mami tace tab ai sai dai kije ke kadai yayanmu ba ya son ai ta faman bashi hakuri musamman in yana cikin tashin hankali gara makin zauna,ke menene naki na damuwa? kina ganin zaki iya hana shi ya tafi ne?nace bani na ja komai ba,tace sannunki da kai ta mike zo muje gidan walima nace ni kaina ma ciwo yake bazan sami zuwa ba ta tafi na koma na kwanta na cigaba da kuka rurus,saidai da za’a tsira ni ko da bindigane ba zan ce ga abinda nake ma kuka ba sai da nayi ya ishe ni sannan ciwon kai ya yomin sallama kafin wayewar gari nayi rigif ko sallar Www.bankinhausanovels.com.ng
asuba kasa yi nayi sai wurin bakwai na safe yinin ranar nan haka nayi shi, misalin karfe uku Alhj ya shirya da Yaya Abdulrahim yace Habiba danku zai wuce fa,kan Mama tayi magana shima Yayan namu ya shigo ban san lokacin da na mike ba ya zauna a kan kujera yana gaida mama bayan ta amsa sannan ta ce ikon Allah tafiyar ta tashi ne Abdulrahim?na dauka gobe ne?yace eh gobe ne zanje lagos ne na kwana shida na safe jirginmu zai tashi yanzu ma jirgin karfe biyar zanbi zuwa lagos din yana magana niko bakinshi nake kallo da sauraron muryarshi mai dadi tamkar ba namiji ba ne yake magana ba Mama da Alhj suka shiga dakinta ya bisu da kallo sannan ya juyo ya dubeni na dukar da kai gabana sai faduwa yakeyi,ga mamakina naji yace Amina nayi sauri na dago kai baki bude ina dubanashi shima ya kafa min idanu na sunkuyar da kai don ba zan iya cigaba da kallon kwayar idonshi ba sai ina ganin wani abu yana fitowa daga idon shi,yana shigowa nawa,murya kasa kasa yace zan tafi kiyi mani addua kaina a kasa nace adawo lIfy Allah ya
bada sa’a,a lebanshi naga ya amsa,Alhj ne ya fara fitowa yana cewa Abdul walarka nace Mamata baka?yace no Maman Sagir kar ki damu ba sai kin bani komai ba Mama ta fito da dambun nama dayawa tace to ka tafi da dambun naman nan Iman tayishi shekaran jiya ya dubeni sannan yace to zan amshi wannan sai naji wani sanyi a raina suka fita nima na daga labulen dakinmu ina kallo ga yan biki nan sai a dawo lIfy suke mashi harda su Haj Yaya dasu mama aka fita harabar gidan wajen ajiye motoci nima na fito ina daga can baya ina kallonsa har aka shigar mashi da jakunkunan shi cikin boot din motarshi yaya Kabir ne zai jashi,ga wasu abokanshi suma zasu shiga wata motar ya fito daga dakinshi har ya sauya kayansa da jc jajaye masu ratsin fari dogon wando da riga mai dogon hannu sai takalmin kwallo Anty
Mimi ma ta fito sai kuka takeyi haushinta ya kamani a
ganina nice yafi dacewa inyi kuka ba ita ba ko mai yasa oho zai shiga mota kenan ya hango ni sai naga ya tsaya yana kallona har Anty Mimi ma ta juyo Www.bankinhausanovels.com.ng taga wa yake kallo?sai taga ni yake kallo sai naga ta kawar da kai niko sai na kwantar da kaina a jikin bango sannan na daga mashi hannu alamr bye bye sai ya shige mota suka tafi Tun daga wannan rana ban kuma wani sukuni ko walwala ba har mamakin kaina nakeyi kullum cikin damuwa bana wani cin abincin kirki gashi kowa ya gane halin da nake ciki a gida da makaranta sai dai kowa ya tambayeni sai nace bani da Ify ne.Azumi da nafilflii kullum cikinsu nake ranar da yayanmu yayi kwana biyar da tafy Mama taga
abin ya isheta bani magana sosai koda yaushe a kwance ga jarabawa ta matso amma bana wani krt sati da lahdi suka zo suka wuce amma banje islamiya ba wato (sanawiyya),Ranar monday mama tace kar naje makaranta na shirya muje Asibiti nace Ify ta kalau tace na dai shirya muje kawai rimi clinic mukaje mama tayi ma likita bayanin yanda nakeyi,likita ta barshi dani bayan fitar mama sai likita ya dubeni yace sanar dani yadda kikeji sai nace kasala nikeji sai kirjina da ke min nauyi kuma bani son yawan surutu yadan gwaggwadani sannan yace kina yawan tunani ko?nace eh yace to tunanin me kikeyi?nace ba komai yace karya ne da na rasa ta cewa sai na ce jarabawa ce nake tunani ba dan ya yarda ba yace to shi kenan ki daina yawan tunani kisa Allah a gaba ya rubuta mana magunguna muka tafi,haka nayi ta
shan magunguna amma tamkar ana zugani Mama ta
koma na gargajiya ni dai nawa shane a haka Www.bankinhausanovels.com.ng jarabawa ta same ni mukayi ta nidai ban sa rai da zanci ba ranar da muka gama ne a nata murna masu hoto nayi niko sai kallon mutane nake,Mami ta dafa ni tace ga wata yar ajinku can tana nemanki nace ina take?ta nuna min ita ashe Hauwa’u Aminu ce nan tamin korafin rashin sanin gidanmu ita kuma ta bani no wayarta ni kuma nace mata in na fara anfani da tawa sai taga tawa lambar,sai da zamu bar harabar makarantar ne sannan naji duk kewar makarantar ta ka mani.Abdulrahim zaune a kan kujera a
cikin falon Hotel din da yayi masauki, ko nace nan ne
dama club dinsu suka kama mashi tun farko,kanshi yana jingine a bayan kujera, tebur ne dan karami cike da kayan ciye ciye da shaye shaye amma sam ya kasa cin komai tunanin yakeyi wayarshi tayi kara ya juyo ya dube ta kamar kar ya dauka sai kuma ya dauka Mimi ce ta kirashi bai san dalili ba sai yaji wani kunci a ranshi amma sai ya daure ya dauka,tace yayanmu kana Ify? yace Ify kalau,yake dinfa?tace ina nan Ify dama naga tunda ka tafi baka kira ba ne,yau kwana shida kenan?yace ban sami dama bane,tace to ina jiran kiranka,yace to kawai ya kashe wayar juyawa yayi ya dubi abincinshi kusan
minti arbain kenan da kawo abincin amma ya kasaci ya kai hannu ya bude plate din abincin da yafi so yayi order amma sam sai yaji kamshin abincin ma baya mishi dadi kokadan a fili yayi magana yace yarinyar nan ta bata ni da kalolin abincinta masu dadi,yayi shiru yana tunani tun zuwan shi kasar nan bai wani ci abinci ba daga ruwan lipton sai dambun naman nan,kwankwasa kofar akayi ya bada izinin a shigo ne abokinshi ne shima dan kwallo ne amma shi bature ne ya dubi Abdulrahim sannan yace cikin turanci Maska naga baka shirya ba ne,wannan karon baka so dawowa ba ne tunda ka dawo sam baka da kuzari,me yasa?Abdulrahim ya mike yana fadin tunanin gida nakeyi ya shige dakin barcinsa shima ya shiryo cikin JC na training suka fita.A daran daya cika kwana bakwai da zuwa yana zaune a harabar Hotel din
haske ne ya kewaye gurin kamar rana gabanshi Www.bankinhausanovels.com.ng
gwangwanin coke ne da dan karamin plate cike da
dambun nama sannan ya kai hannu ya dauki wayarshi ya soma sana’ar wato danne danne wayarshi can yayi tsaki ya kashe wayar ya mike,da ya kamata ya nufi gurin abokanshi ne tunda ba dare ne yayi sosai ba kuma yasan zasu Sa ran Zuwansa, amma sam Sai yaji ba zai iya ba saboda wani abu da ya taba zuciyasa sama ya nufa dakinshi ya zauna a bakin gado sannan ya aje tarkaccen hannunsa a kasa wayarshi ya rike sannan ya soma sarrafata cikin kwarewa, Babanshi ya kira bayan ya dauka sai yace Alhj ina yini?bayan sun gaisa sai yake cema Alhj dama ya kira ne dan ya amshi lambar wayan Maman sagir domin yana da lambar kowa a gidan itace bai da ita,Alhj yace gata nan ma Habibar ku gaisa,bayan sun gaisa ne sannan ya bukaci lambarta ba tare da wani tunani ba ta bashi,ya jima yana tunanin dalilin karbar no
kafin daga karshe ya gane sai dai wani tunaninshi abin zai zamar mashi abin kunya da nunawa cikin
abokai,muddin suka san halin da yake ciki,nan a dalilin
wata kankanuwar yarinya wacce da yayi auren wuri
tabbas zai haifi kamarta.Kwance yake akan gadonshi
amma sai sautin daddadar muryar yarinyar yake dawo

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG A KODA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *