TAWA TA SAMENI CHAPTER 12 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 12 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

bayan sun gaisa sai yake cema Alhj dama ya kira ne dan ya amshi lambar wayan Maman sagir domin yana da lambar kowa a gidan itace bai da ita,Alhj yace gata nan ma Habibar ku gaisa,bayan sun gaisa ne sannan ya bukaci lambarta ba tare da wani tunani ba ta bashi,ya jima yana tunanin dalilin karbar no
kafin daga karshe ya gane sai dai wani tunaninshi abin zai zamar mashi abin kunya da nunawa cikin
abokai,muddin suka san halin da yake ciki,nan a dalilin
wata kankanuwar yarinya wacce da yayi auren wuri
tabbas zai haifi kamarta.Kwance yake akan gadonshi
amma sai sautin daddadar muryar yarinyar yake dawo

ZAMU TASHI 

mashi ya tuno ranar da bashi da Ify duk gidan ba wanda ya kula dashi tamkar ita muryarta ya tuna sannu yayanmu za ai maka wani abu ne?ya sake tuno yanda ya kara tsorata ta ranar da ta daukan mashi kujera tabbas in tana cikin tsoro tana matukar burgeshi yayi magana a fili inda yace nayi missing din ganin tsoranki. (Lallai Iman kinga takanki, mudai daganan sai muce! Allah yakyauta) Ya cigaba da juyi a kan gado ba komai ke dawainiya dashi ba sai begen yarinyar da yake gani abin kunya ne ace ya sota ya tuna da mimi yarinya mai kyau jinin larabawa sai dai shi baya jinta a ranshi yanda yake jin wannan yar mitsilar yarinyar zai auri Mimi ne kawai don


bin umarnin mahaifiyarshi kuma ya san duk inda suka
shiga ba zai ji kunyar nunata ba a matsayin matarshi
shekarunta ashirin da biyar shi kanshi shekara biyar ya bata bugu da kari gashi ta soma zurfi a Www.bankinhausanovels.com.ng karatunta,amma in yace wannan yarinyar zai aura shima yasan rigima zai jawo,yanda mahaifiyarshi ta tsane su wata zuciyar ta ce mashi ga yaran nan da rashin kunya tana jin kace kana sonta to raini ya shiga tsakaninku gara ma Mimi hadaku akayi kuma kasan ta mutu kanka don haka baza ta maka wani rawar kai ba,”A dawo Ify Allah ya bada sa’a” ya
kuma tuno muryata da yaji na karshe sannan lokacin da ta rakube a jikin bango tana mashi bye bye ya dawo mishi tausayinta yaji lokacin kuma jikinshi na bashi kamar itama tana jin yanda yake ji a ranta,zaune ya mike yana magana shi kadai tamkar wanda ya tabu yana fadin Amina kiyi hakuri bani da sha’awar auran mata biyu ki bari in runtsa ya kuma fadawa kan gado.Niko yanzu na zama kurma bana magana sosai ban kuma cika son magana ba sai dai maganar su Amira ce ke damuna da suka ce wai ina ciki mayen soyayya na dai ki sanar dasu wanda nake so,inko har zancensu gsky ne to na debo da zafi don ko in har yanda zuciyata ke mani game da yayanmu so ne to ko shakka babu gara na rufa ma kaina asiri nayi shiru da bakina don nasan ko yaji ubana zaici
don nasan ni ba ajinshi bacesme kamar Anty Mimi?
kammala karatuna shi ya ba samari damar damuna Www.bankinhausanovels.com.ng
tamakar anbi su an gaya musu musamman ma yaya
Kabir shine yasani wannan ya sani wancan,su yaya ma suna zuwa,ban manta wata rana yaya Kabir ya aiko Sagir dinmu ya kirani na fito na sameshi a daki kan kujera na zauna fuskata na kallon wani katon hoton yayanmu sanye yake da JC kore da fari irin na yan wasan Nigeria hannunshi a kan kirjinshi daga gani lokacin suna taken Nigeria ne aka dauke shi,muka gaisa da yaya Kabir ya soma yi min zancen soyayya niko hankalina ba ya tare dashi, yayanmu kawai nake kallo da kyaun da Allah yayi mashi ba abinda ya birgeni irin shedar sallah daya fito mishi a saman goshinshi yayi baki tamkar ya diga ina cikin wannan tunanin ne naji yaya Kabir na min magana da karfi nayi ajiyar zuciya sannan na dube shi nace ka gama?zan shiga gida yace na tambayeki baki bani amsa
ba nace ni ban wani jika ba na mike nayi waje yana
kirana na fito kirana naji anyi daga bakin gate ko ban juya ba nasan yaya Abubakr ne dogon tsaki naja sannan naje ina zuwa na hau shi da masifa shima kallona naga ya tsaya yi,ina cewa nace ni ba aure zanyi ba amma kun dameni don Allah ku rabu dani ko dole ne?na juyo abina wani abin haushi ina shiga falonmu sai ga yaya Suleiman zaune suna hira da Mama…(hhhhhhhhha.yarinya taki tasameki.)
dakin kwananmu na wuce nayi kwanciyata naki fitowa banfi minti goma ba mama ta shigo ta dubeni tace Sulaiman ya dade yana jiranki wai me kika tsaya yi wurin Kabir din?nace ya aike nine bayan na dawo kuma sai na gamu da da yaya Abubkr na cigaba da cewa gsky ni dai mama ki samu su yaya Abubkr kiyi musu magana nifa ba aure zanyi ba su rabu dani Www.bankinhausanovels.com.ng mana,mama tace aike ma yan uwanki ne kuma nasan in ki sanar dasu zasu kyaleki sannan suna ganin girmana sosai bazan iya tunkararsu da wannan zancen ba, nace haka fa shekaran jiya yaya Ibrahim yazo wai har yana takama zaije ya samu babana kuma ko ina so ko bani so shi zai bashi ni mama tace to bisimilla ai ga kinan taci gaba da cewa don haka ma ni koda auren ne cikinsu gara Abubakr din nace ni dai dukkansu har yaya Sulaiman din hakuri zaiyi dani dan
bana son auren zumuncin nan mama ta fita tana cewa dai gashi can ku gaisa,na dauki hijabina na fito falo fuskata a daure muka gaisa yace to Iman gani dai na kuma dawowa duk da kin sanar dani krt zakiyi shine na yanke shawara ki yarda a daura mana aure ni kuma zan yarje maki kiyi krt har kiga karshen biro nace mu bar zancen nan, ina Nana?yace Nana tana nan jiya aka sa ranarta goron ne ma na kawo ma Mama nace lallai Nana yanxu itama auren zatayi?yace shine mutuncin duk wata ya mace nace to Allah yasa alkhair ni zan shiga na kwanta ka gaida min da su baba uwa kace da Nana inna jiran zuwanta, yace amsata fa? ko zaki yi min waya don Mama tace kin soma amfani da wayarki nace jiya na soma sai dai ni bata dameni ba don haka ko lambar ban rike ba in Nana tazo taje maka da lambar yace ai bazaki min ko flashn bane tunda kinsan tawa nace to na maka
na shige daki ina jinshi yana fadin barakiya? Sannu a hankali zuciya da gangar jiki suka tsananta da
so kauna da kuma begen wanda bazasu samu ba sannan ni naki yarda da cewa sonshi nake ban yarda da nayi nutso a kogin sayayya ba sai da na samu kaina da rashin barci,sannan na kama karatun littatafai na soyayya,kallace kallace da basu dameni ba yanzun nakan zauna nayi duk saurayin da aka nuno sai naga bai kai yayanmu komai ba ni fa gani nake ba wani namiji wanda ya amsa sunan namiji in ba yayanmu ba,yauma kwance nake akan gado yar karamar Rediyon da nike yin karatu ce na manna a kunnena kaset na wakar fim din kugiya na sa wakar na ratsani Idona a lumshe sai nakejin kamar nice nakeyin wakar, duka naji an dada min da sauri na
tashi ganin Amira da Mami shine yasa nayi ajiyar Www.bankinhausanovels.com.ng zuciya nace kin dau alhakina Amira ta cire wayar kunnena sai ta dauke Radion ta sa a kunnenta dajin wakar sai naga ta cire da sauri tace Mami ji wannan kaset din Mami tasa taji sai naga sun dubi juna sukayi dariya nace wai menene?suka zauna suna cewa zancenmu gasky ne nace kamar yaya zancenku gsky ne?Amira ta dauke fuska tace Iman mun gamsu nace me na muku?Mami tace akwai abinda yake damunki amma kin kasa sanar damu,Amira ta amshe damu ne da munhau gaya maki nayi shiru ina tunanin me zan ce masu can dai nace Amira,Mami kunsan yayyena Abubkr,Ibrahim da Sulaiman?suka ce sosai ma kuwa nace dukansu sunce suna sona ni kuma bani son ko daya sannan yaya Kabir shima yace wai sona yake na mike tsaye don girmama maganar da zanyi na cigaba da cewa ni kuma zuciyata da gangar jikina sun nutse a son wanda bai san inayi ba kuma koda ya sani ba zai soni ba don yana da wacce ta fini kyau da ilimi da kuma shekaru,hawaye suka soma zubo min na juyo da sauri na rike kafadun Mami da karfi ina cewa ku bani shawara kawayena ku taimaka min da maganin da zan daina sonshi don kukan ku da zaku san ko wanene da kunce lallai zuciyata tayi wauta,suka kamani suka zaunar dani tsakiyarsu suka yi shiru dakin ya yi tsit daga ajiyar zuciata da nakeyi sai karan fanka
can Amira tace a ina yake?kuma yaya sunanshi?nace
kuyi hakuri wata rana zan gaya muku don ba anan yake ba Mami tace dakin gaya mana ai da mun san yanda zamu bullowa abin nace no ko zan mutu bazan taba tunkarar wani da namiji da sunansa ba yanzu ku bani shawara yaya zanyi na daina tunaninshi suka yi shiru can Mami tace rokon Allah zakiyi muma zamu taya ki nace sai dai mukara don kullum yi nake amma ba sauki sai dai abinda ya karu nan dai suka lallashe ni gami da bani shawarwari. Haka naci gaba da Www.bankinhausanovels.com.ng rayuwa cikin kunci,wata safiya misalin karfe takwas Mama tana dakin Alhaji ta kai masa abin kari ni kuma ina ta faman gyaran dakinmu na gama na
koma dakin Mama ina cikin aiki naji wayar Mama tana
ringin na dauka sai ga lambobin rakwacam na dauka
nace Assalamu alaikum sai naji ance Wa’alaikummussalam,jin muryar da ta amsa nan da nan na gane yayanmu ne farin ciki da na ji baya misaltuwa ina wannan tunanin ne naji yace Naman Sagir ina yini? nace ba ita bace ni ce Mama tana dakin Alhaji yace ok! nace ina kwana?yace lafiya amma mu nan rana ce kuna Ify?nace Ify lau yace to kice da Maman Sagir ina gaisheta dama don mu gaisa ne na kira kafin nace to har ya kashe ranar nayi walwala har yamma don jin muryar abin sona. Www.bankinhausanovels.com.ng Lokacin da zai tfy nan ko ince da zaya koma ina cikin
wannan tunani sai naji yace kin gama?dama na gama sai nace e yace to gashi na isa na dan rage tsawo yace wannan ya turo mani akwati naki ne sannan daya kuma zaki kaima Mimi nata nace to nagode Allah ya kara daukaka duk da bai amsa ba nasan yaji dadin

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *