TAWA TA SAMENI CHAPTER 14 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 14 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 




MUN TSAYA 

na dubi kayan jikinshi kampala green nima haka sai naji tamkar na koma na cire ya dube ni zo muje na saukeki nace ka barshi yace duk da nayi latti sai na kaiki,dole na shiga muna shirin fita yayanmu ya shigo shi da wasu abokanshi cikin kayan training duk da kaninshi ne sai da gabana ya fadi yako tsira mana ido sai ya tsaida motar ya dubeni yace kin mani shara?na dubeshi yayi wani kicin kicin nace a’’a yace to fita ki min bai saurari amsata ba yayi gaba na dubi yaya Kabir nace to kaji fa abinda yace,yaya Kabir yace don Allah ki rabu dashi bari mu tafi nace wai ba haka a tsakaninmu haushi ya kama yaya Kabir yace toko dai yana sonki ne?nace kaji ka da wata
magana kaima kasan ko mata sun kare yayanmu ba zai soni ba yace saboda me kikace haka?nace ni nasan bani da kyau kuma gani baka yayi murmushi sannan yace ganinki kenan kina abubuwa masu fizgar hankali so ni dai yanzun ki yarda na fito sai a hada da nasu Mami,haushi yasa na bude motar na fito shima yayanmu na

ZAMU TASHI 

sameshi ya cika dam ina shiga ya dube ni duban wulakanci yace me kika tsaya yi a gunshi?nace ba komai ya nuna ni yace look ba zaki min yawo da hankali ba bani son na kara ganin kin shiga motar Kabir kina jina?ya daka min tsawa nace to,ya fita na shiga gyaran daki ina mamakin wannan ikon Allah..
Ina cikin goge TV ya shigo yana waya ya zauna kan
kujera yanda naji yana amsa wayar ne yasa naji duk
bakin ciki ya kamani ko bai fada ba nasan da Mimi yake magana har yana cewa karki damu nima kin manne cikin raina kuma ki saurareni in anjima da sauri na shiga bedroom dinshi har lokacin wayar yakeyi ranar da takaici na yini wata zuciyar tace min kina kishin banza kina wahala bai san ma kinayi ba


Kwana biyu ni dasu yaya Abubkr da duk wani mai son
ganina in dai saurayi ne sai dai a waya ranar juma’a ina zaune da yamma tsautsayin jin takaici ne yasa nace da mama bari in shiga gun Amira ina isa daidai dakin yayanmu shi kuma yana fitowa tare da Www.bankinhausanovels.com.ng abokinshi sun kai su bakwai daya ne naji yana cewa ango ango to Maska wata nawa aka sa yayanmu ne naji ya amsa da cewa sati biyu suka sa da sauri na juyo cikin sa’a muka hada ido shima sai naga yayi wani iri tamkar bai so naji zancan ba wani abu mai nauyi naji ya tokare min wuyana
kirjina kuma ya hau zugi da kyar nake janyo numfashina kokari nayi naci gaba da tfy amma bana ganin gabana sosai jirin da naji ya soma dibana shi yasa na juyo na koma gida ikon Allah nema ya kaini kofar dakinmu a nan na zube ban kuma sanin in da kaina yake ba na dai farfado na gani a gadon asibiti Mama tana zaune a kan kujera tana rike da hannu na wanda aka sa min karin ruwa ta min sannu na amsa da kyar a hankali na soma tuno abubuwan da suka faru shi kenan yayanmu ya zama na Anty Mimi ko shakka babu yana mutuwar sonta,na tuno wata rana ina shara a dakin yaynmu har na gama zan fita yace nazo nan na juya na koma nace gani yace baki sa turaren daki ba nace na mance ne,na shiga
bedroom din shi idona ya sauka akan wani kyakyawan
frame kamar kaida in dai zan shiga uwardakin yayanmu to ba abinda nake fara kallo sai wannan frame din yana da kyau ga daukar hankali gashi saitin kofa da ka shigo
shi zaka fara gani,na manta batun turaren daki na tsaya duban frame rubutun jiki yan kanana shi yasa ban taba karantawa ba amma lokacin sai na hangi rubutun saman kamar hausa akayi nayi mamaki frame mai kyau da shegiyar tsada irin wannan amma da hausa na ce kai yau sai na dauko shi na karanta duk da wane yare ne na duba dakin ko naga abinda zan taka don yayi sama sosai ba wani abu mai tsawo sai tebur karami kuma na glass
ne na jawo shi a hankali na taka daya ke nima ina da
tsawo na dauko,tabbas da hausa akayi rubutun a saman an rubuta: Www.bankinhausanovels.com.ng
Zinariyata Zuciyata ta jima tana begenta daga lokacin da idanuna suka fara ganinta,na tsunduma a sonta duk karancin shekarunta duk sanda na dubi idanunta sanyi kasala sha’awa suna gajiyar dani bare in naji kamshinta,a lokacin da nayi nisa da ganinta sai barci ya kaurace ma idanuna sai tunaninta bana jin dadin wani girki sai nata Allah ka azurtani da aurenta domin na samu ni’imarta har ka azurtani da ‘ya’ya masu albarka daga gareta (A)amin.
jikina yayi sanyi sai dai abin daya bani mamaki shine
yanda (A)a cikin (A)tamkar irin na zoben da yayanmu ya bani a cikin kayan tsaraba nace kai kilan ma ba (A)guda biyu ba ne wani tambarin ne na wani camfanin acan England din,na dubi fulawoyin dake jikin frame din da tsuntsaye masu ban sha’awa ina cikin juya shi ina cewa nasan Mimi yake nufi,shine Mami tace min baya sonta ashe ma ya jima yana sonta gashi yace tun tana karama,ina cikin tunani naji yayanmu daga falo yace baki ga turaran bane?nan jikina ya soma rawa ina kokarin
maida wa ne tsautsayi yasa na goce,frame din ya fado sai kan tebur din glass ji kake tats,jikina ya hau bari na soma tsuma tamkar mazari,na dauki frame din baiyi komai ba teburin ne ya fashe naga an daga labule da sauri na dubi kofar yayanmu ne tsaye nayi duba zuwa ga fuskarshi ya wani daure fuska me ya kai ki gurin frame kina ganin sirrina ko?hawaye ya soma zarya a kan
kumatuna nace a’a zan goge ne yayi kura ya daka mani
tsawa yi min shiru kuma sai kin biya dukkan abinda kika
fasa min,na durkusa kan gwiwoyina na soma cewa don
Allah kayi hakuri yace ai zaneki zanyi yanzun nan
muryata tana rawa nace please yayanmu ya dubeni cikin
wani yanayi mai wuyar fahimta sannan yace gyara min
wurin ki wuce,ban san kan kwalba nasa gwiwata ba sai da
na gama gyra dakin sannan naji zafi na duba.kamshin
turaren da naji shi ya dawo dani cikin hayyacina ko ba’a
fada ba nasan yayanmu ne ya shigo Asibitin nan ban
gama tunani ba ya kwankwasa kofa ya shigo dama fuska
ta kofa take kallo don haka yana shigo dani muka soma
hada ido sai naga tamkar an kara mashi wani kyau….
Na lumshe ido sai naji wasu hawaye sun zubo min ina
jinshi suna gaisawa da mama ya tambayeta jikina tace
da sauki ban ma san har na kwana ba sai da naji yace
tun jiya bata tashi ba?mama tace dazun nan ta farka ina
mata magana banji ta amsa ba nayi mata sannu ta amsa Www.bankinhausanovels.com.ng
bata kuma magana ba sai hawaye da ke zuba daga
idonta shiru yayi na dan lokaci sannan yace bari inga
likitan mama tace yanzun nan babanku ya tafi gurinshi
tun jiya ma yace ciwon zuciya ne yake son kamata ni na
rasa mai yarinyar nan ta nema ta rasa da har ta sa
kanta cikin tunani,muryar yayanmu naji cikin sanyin shin
nan yace ai maman Sagir cututtuka sunyi yawa ba sai
mutum yana wani tunani ba Allah dai ya sauwake ya
juya zai fita sai gaa
Alhj ya turo kofa yayanmu ya matsa Alhj ya shigo yana
ma mama bayani sun tabbatar da zuciyata na son ta
harbu sannan yace su tuhumeni ko akwai wanda takeso
ne ko abinda ya shafi haka yayanmu yace Alhj bari nima
na ganshi likitan sukace to lokacin Alhj yasa an tashe ni
zaune ni kaina nasan na rame sosai cikin kwana daya
yayanmu ya dubeni yace sorry Iman na dubeshi yaune na
fara jin ya kirani da Iman na daga kai alamar
amsawa,yace maman Sagir me taci?mama tace bata ci
komi ba yanzu ne dai zan hada mata to amma tace sai
tayi sallah tukunna,ya dubeni zaki iya yin sallar ne?nace
eh tare da taimakon mama nayi alwala muna fitowa daga
bayi yayanmu yayi mana sallama yace da daddare zai
dawo haka na cigaba da jinya har tsawon kwana uku
kullum yan dubiya suna zuwa,Amira da Mami nan suke
yini haka yayanmu da yaya Kabir nan sau uku suke zuwa
sai dai duk lokacin da yayanmu yaga yaya Kabir
haushinshi yake ji, gudun fadan alhj yasa kishiyoyin
mama suka zo sau daya kuma basu kawo mana abinci
sai dai anty Yagana da maman su Amira kayan ciye ciye
kam yayanmu ya kashe kudi har Anty Mimi ya kawo ta
gaisheni nasan dai dole tazo ba don son ranta ba,niko
ban ma ji wani dadin zuwanta ba don ma kadan ya rage Www.bankinhausanovels.com.ng
ciwona ya dawo musamman ma da naga sun sa anko
yellow kampala sun man kyau sai dai kishi da ya sani
gaba,ban san yanda akayi su yaya Abubkr sukaji ba sai
dai ganinsu nayi yaya Ibrahim ne yake ce min babana
yana nan zuwa,yace a gaisheni naji dadi har ina
tambayarshi yaushe zaizo?yace kilan yau ko gobe nace
kilan a sallame ni yau ai a ranar aka sallameni kafin sati
na dan girgije,yan skull dinmu na comp ma sun zo duba
ni randa na cika kwana goma ranar na koma zuwa
makaranta lokacin saura kwana hudu bikin yayanmu su
Mimi duk sun damu da bikin sai rawar kai suke yi har
Mami na cewa da ban warke ba bikin ba zai mata dadi
ba sannan suna son kudi gun yayanmu nice ma zan
amsar musu nace ke Mami ki rabu dani ba wani kudin da
zan tambaya a raina nace in baku san dan dole zan
zauna a garin nan ayi biki ina nan ba da ba dan mama ba
zata yarda ba da naje tudun wada gidan kawuna sai
angama sai na dawo da dare yayanmu ya aiko nazo lokacin
ina zaune a falo ni da mama tana nuna min memo data
buga da sunansu  Jamila da Sagir sai agogon bango
suma guda dari wai in bashi ince ni na buga na dauki
guda daya ina dubawa hotunansu ne sunyi kyau sosai na
hadiye wani abu da yazo min wuya na dubi mama nace
sunyi kyau amma kin sha kudi tace yaya za’’ayi ai yana
da mutunci sosai Abdulrahim na ce umm waya baki
hoton su?tace gun Kabir na amsa na rike hawayen idona
lokacin da naga sunana a matsayin wacce ta buga katin Www.bankinhausanovels.com.ng
nace wani abu ne jamila ta shigo anty Iman kizo inji
yayanmu na danyi tsaki nace kice kaina na min ciwo ba
zan iya zuwa ba a raina nace ba zanzo ba tunda ka
kama matarka a hannu kasata aikin,Mama ta dubeni kije
mana Iman kije mishi da agogunan nace banjin dadi ne
mama tace daure na mike na ciccibe kwalin agogunan na
ce bari na kai wannan sai na kuma zuwa na dauki dayan
da kyar nakai dakin nayi sallama na shiga yana zaune da
kaya a gabanshi fuskarshi babu walwala ya dago kai ya
dube ni yaya kai din na dan lumshe ido sannna nace da
sauki na kula tun da nayi rashin Ify sam baya son yimin
tsawa ko fada ya dubi kwalin dake gabana yace menene
wannan?Yaya gudummuwata kenan a ba jamai’a. Ina
zuwa na koma na dauko dayan kwalin na samehi yana
duba wa ya dubeni yace amma sunyi kyau mun gode,na
danyi yake nace um ya turo min kayan gabanshi yace ga
naki kayan bikin harda ankon,nace ai Baba yayi mana
ankon,yace duk da haka ki dauka ina son ki kaima telanki
da yake maki dinki don ya iya sosai nace yaya Sulaiman
ne ya ma samu aiki yanzu bai cika zaman shagon ba sai

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *