TAWA TA SAMENI CHAPTER 15 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 15 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

fuskarshi babu walwala ya dago kai ya
dube ni yaya kai din na dan lumshe ido sannna nace da
sauki na kula tun da nayi rashin Ify sam baya son yimin
tsawa ko fada ya dubi kwalin dake gabana yace menene
wannan?Yaya gudummuwata kenan a ba jamai’a. Ina
zuwa na koma na dauko dayan kwalin na samehi yana
duba wa ya dubeni yace amma sunyi kyau mun gode,na
danyi yake nace um ya turo min kayan gabanshi yace ga
naki kayan bikin harda ankon,nace ai Baba yayi mana
ankon,yace duk da haka ki dauka ina son ki kaima telanki
da yake maki dinki don ya iya sosai nace yaya Sulaiman
ne ya ma samu aiki yanzu bai cika zaman shagon ba sai

ZAMU TASHI 

dai yaranshi,yace to kikai inda za’ayi maki mai
kyau,takalman ki jakunkuna sai yau za‘’a kawo anjima kadan gidan Nasir na manta su nace na gode ya kuma duban hannuna ke bakiyi lallen bane?nace eh yace kiyi gobe zanzo na kaiki saloon mamaki ya kamani nace ko dai yana zaton da Amaryar yake magana ne?ni da ban taba shiga motar shi ba,na boye mamakina nace ai bana sa relaxer kitso nakeyi yace to kiyi kitson kinji ni?nace to.kaya ne kala shida less biyu super biyu sai materia] daya sai shadda,shaddar din kakkiya ce ta sha aiki riga da zani sitayal din ya hadu ga shaddar mai

tsada,turare kala uku masu kyau da mayukan shafawa sai sarka da yan Www.bankinhausanovels.com.ng kunne,Mama ta dubeni tace oh ni Habiba wannan
hidima tayi yawa, shida ke cikin biki kayan nan Iman
ba’a karbe su duka ba bani wayata gata can a chargy,na dauko mata shi ta kira tana mishi korafin
yawan kayan bansan me ya ce mata ba naga tayi murmushi tace ai kanwarka ce kowane ai ta maka kabiyata kenan?can kuma tace to shi kenan an gode Allah yasa ayi wannan biki lfy ya kuma bada zaman lfy.Washe gari na shirya sai tudun wada na kai dinkunan a can nayo kitsona da lallen filawa mai ratsin ja,gidansu Amira na biya tace min
zakije Arabian day din ne yau?nace Mami tay min
magana amma da kyar in zani kinsan bana shiri da Amaryar, Amira tace indai ba zakije ba nima ba zani ba dama domin ke zani nace to bari in zani zan maki waya ba karfe hudu bane?na duba lokaci a wayata karfe biyu da minti arbain nace bari na shiga gida dama dinki nakai tudun wada,Amira ta dubeni tace name kuma ba kinyi anko ba?nace jiya yayanmu yace ga nawa ankon dana duba sai naga ba anko bane ya dai minne kala shida harda takalma yau da safe ya bani takalman kala uku,Amira tace gsky jininku ya hadu,sanda baki da lafiyannan kar ki ga yanda ya damu ba dan munsan yanayin rayuwar shi kenan yin alkhairi ba damin zargi ko sonki yake na kai mata duka nace me zukekiyar mace kamar Mimi me zaiyi dani?Amira tace Iman kina da kyau amma sihirtacce ne sai na kusa dake komai sonki ko kuma yasan kyau zai gane kiga Mimi mai mata kallon gane muni zai ga muninta don tana da goshi da kuma….na katse ta mu bar zancan nima ai in an kura min ido za’a ga muni nawa,Amira tace Allah baza’a gani ba sannan ne ma za’a ga kyaun ki nace um bari na shiga gida. A gurin Arabian day kowa yayi kyau Amarya cikin jallabiya baka da dan hijabi tana zaune a gun da aka
tanadar mata muka shigo nima sanye nake cikin
Jallabiya mai hawa biyu baka da ja hijabina da takalmina Www.bankinhausanovels.com.ng
jajaye ne, Hijabin dan karami iya wuya su mami da Anty Mariya da kawayenansu sai kai kawo suke ni kam guri guda na kame mai kyamarar sai daukata yake tamkar nice Amarya,ga masu Hotuna,Amira tace kai Iman kin tafi da imanin masu hoton nan sai ke suke dauka kafi ninyi magana Bilkisu tazo tace kai bafa wannan bace Amaryar ba kun ganta tayi maku kama da Amare?nan suka juya suna daukar ko ina haka taro ya tashi Ify ba tashin hankali,washe gari sister day da safe yayanmu ya aiko nazo dakinshi na same shi ya dubeni me kike yanzu?nace ba komai yace to abokaina ne na england yau zasu iso ina sonki shirya masu abinci kaloli masu dadi don gidan Nasir zan saukesu kamar nawa ake bukata?ko muje kasuwar tare in yaso sai ki duba abubuwan da zakiyi amfani dasu gaba daya a wajen
girkin?nace to bari na sanar da mama yace shima bari yayi wanka,cikin riga da wando na material ruwan madara da filawoyi jajaye dan hijabina dan karami sai takalmi sai abinda ya kamata na siya da kulolin girkin da zan masu har da na sha ina tsaye jikin motarshi ya fito daki sai da ya shiga su Sa’a da Bikisu da Maryam kanwar anty Mimi dukkansu ni suka tsura ma ido na shige mukayi gaba,ba wani hira muka yi ba ya dai sa wakar tashi dakusan duk kullum sai naji ta a dakinshi tun ina jin haushin wakar har yanzu nima ina sonta kuma nama sai album din wakokin mata celine dion ina wakokin don sanyin muryarta,wayata ta soma kidan kuch kuch hota hai na kai hannu zan dauka sai naga yayanmu
ya dafa wayar ya dauka ya duba sunan Amira ya gani sai ya mika min nayi ajiyar zuciya sannan na amsa
hello,Amira yaya dai?tace kina ina ne?nace muna hanyar kasuwa ne menene?tace na sha kina gida ne na shigo,nace bana gida in na dawo zan shigo gidan muyi aikin abincin baki tace to sai kin dawo.
Sayayya mai yawa mukayi komai nace biyu sai yace na
dau uku,gidansu Amira ya saukeni ta fito muka kwashe kayan,mun shirya abinci kala kala dana sha a sababbin kulolin da muka siya muka shirya muna gamawa muka yi wanka na shiga kenan don nasa kaya yayanmu ya kira ni nazo yace kun gama?nace eh yace to ga musa dryva nan ya kaiki gidan Nasir ni kuma zamuje mu dibo su sauran minti biyar su shigo KD daga Lagos nace to,banyi wani shafe shafe ba nasa atamfa charas babba riga da siket ne dinkin shot play sai karamin gyale muka jera abincin
nace Amira tazo muje tace aah ba ruwana da wannan
yayan naku zai iya kado ni,nayi dariya nace shi
kenan,nayi kusan minti talatin da zuwa sannan suka iso Www.bankinhausanovels.com.ng
cikin harshen turanci suke magana nima na gaishesu
cikin yaren nasara,Nasir yace ko inyiwa Mami waya ne tazo ta taya yarinyar ne?ya harareshi yace ban ce ba nikuma bayan sun zauna na gabatar masu da kayan ciye ciye da shaye shaye na gida dana company,wani shima bakin fata ne duk sanda na dubeshi sai mun hada ido dashi haushinsa ya kamani can kuma wani daga cikinsu yace Maska wannan itace Amaryar?yace a’a ita kanwata ce sai yace to zaka bani kanwarka?don tana da kalar asalin yan Nigeria yayanmu ya daure yace baya son wannan maganar bakin fatar dake kallona yace Maska ni zaka ba wannan mai kyaun din,don bana neman wata
kasani,yayanmu bai kuma magana ba ya dubi Nasir
yace bari na kaita gida na dawo,ya dubeni tashi muje na dube su nayi musu sallama, a mota yace in zaki fita ki daina shafe shafen nan na dubeshi nace ban shafa komi ba sai hoda,yace duk inda kikaje sai ance mun ana sonki ni kuma krt nake son kiyi ni dai nayi shiru yace kin tuna alkawarin da kikayi min ko?nace eh yace to kar ki yarda ki yi wasa da cika alkawari kin jini?nace e. A kurarren lokaci muka isa gun Sisters day Angoma bai zoba na tambayi Mami tace min yayi ma Amarya waya yana tare Www.bankinhausanovels.com.ng
da baki muka zauna,nanma ba laifi bikin yayi kyau ranar ne akayi sa lalle banje ba, washe gari lunching
hamdala hotel za’ayi sanye nake cikin dogayen riga na shiga dakin yaynmu dan amsa kiranshi yace zauna na zauna a kasan carpet ya dubeni yace yau wane kayan zakisa,nace anko zamu sa yace to kar kisashi kisa sky blue din less din nan,na gama kanki ba tare da wani tunani ba na zame dan kwalin kaina kananan kitso ne 2step mai zigzag,yace to rufe ki shirya sosai ya dubi dakinshi yace ga kayana nan dukkan abinda kike so ki dauka na baki ki dauka nayi shiru na sunkuyar da kaina ya taso ya tsugunna gabana Aminatu ya kira ni a hankali cikin sanyin nan nashi na dube shi nidai da zance frame din nan nake so amma sai nayi shiru ya kuma kiran sunana na dube shi yace kina son Fridge?nace aaTV fa?nace a’a,Radio fa?nace a’a yace to me kike so?na dubi hotonshi yana sanye da farin JC mai ratsin ja yayi tsalle zai kama kwallo ina balain son hoton ya dube ni shi kike so?na kada kai alamar eh bayan shi fa?nace ba
komai ya mike ya ciro min hoton ya hado da wani shima mai kyau cikin jan JC kan kujera ya zauna sannan ya kama hannuna gabana ya fadi naji wani yarr a jikina ya rike yatsuna da zoben nan yake jiki wanda ya kawo min tsaraba kar ki rabu da wannan zoben komin wuya kinji? kasa magana nayi,yace wannan lallan ya min kyau waya miki?kafin na bashi amsa sai akayi sallama gami da shigowa gaba daya tsoro ya kamani da na juya naga Anty Mimi itama tsoron ne da mamaki a kan fuskarta na dubi yayanmu shi ko namijin duniya ko a jikinshi ya saki hannuna yace Mimi Ify na ganki yanzu?ta juya da gudu
tana kuka yace me aka mata oho,yayi tambaya ya ba
kansa amsa na mike da hotuna sai nayi gidan su Amira
ban koma cikin gida ba ita ko Anty Mimi dakin Haj Yaya ta nufa da kukanta da komai,ta sanar da WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG hajiyan komai haj yaya ta cika tamkar zata fashe ta dubi mimi tace kince yana rike da hannunta?Mimi tace sai kallon juna suke yi,haj yay tace lallai ma yaron nan jiya fa haka su Bilkisu suka ce min sun ga ya shiga mota da ita banyi maganin abun ba bari in kirashi,ta soma daddana waya tana fadin kannanshi bai taba sasu a motarshi ba sai wannan bakar mummunar yarinyar,ta soma magana kazo yanzun nan ta kashe wayar taci gaba da fadin sun
asirceshi shima kamar babanshi na shiga uku ni Murja tsakanina da Habiba Allah ya isa ban yafe mata
ba,yayanmu yayi sallama ya shiga dakin tana zaune kan kujera sai cika takeyi ya ballama Mimi harara sannan ya shiga ya zauna,duban wulakanci ta mishi sannnan tace yanzu kai saboda Allah me ke tsakaninka da yarinyar nan Iman yar karama da ita shine ta ke juyaka ta shanye ka nan gaba ma kila kace aurenta ma zakayi ko? ya sunkuyar da kai kasa bai amsa mata ba tace jiya ina kukaje?yace Haj waya kawo maki wadannan kananan surutan ne?nifa mutunci ne tsakanina da yarinyar nan tana hidima dani sosai don Allah haj ki daina jin zancan mutane yarinyar nan ita da uwarta suna da kirki kum….ta
katse shi an baka kaci a cikin abinci ba dole kace haka
ba na gaya ma ka koyaya ni zan mummunan saba maka ta nuna Mimi wannan ita menene laifinta?da zaka sasu a kasuwa sai kowa ya riga zabar Mimi kuma zanyi maganin agola a gidan nan wayarta tayi kara ta dauka ta duba ka dai ji na gaya maka ga babanku nan ma ya dawo shi ne yake kira bari naje,ta dube shi sai ka bata hakuri ai,tana fita ya galla ma Mimi harara san

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *