TAWA TA SAMENI CHAPTER 19 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Allah ya saka ma telolin shagon yaya sulaiman da alkhairi ganin yanda na fito cikin dinkin da ke jikina material ne blue mai filawoyi fari da bakake ga stones suna kyalli nasa sarka da yan kunne fashion blue jaka ta da takalmi karamin gyalena fari ina cikin fesa turare ne wayata ta soma ringin na duba yaynmu ne na dauka kin shirya ne? tambayar da ya soma yi min kenan,na shirya na ce cikin sanyaya murya ya dan ja numfashi to fito WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
waje na ga kwaliyarki kafin in wuce kinsan fa ni zanje can ne mu tafi tare da mimi nace to amma raina nace ina ruwana in ma da mamanta zaku,ya kashe wayar na dubi agogo takwas da rabi na dare nace anya mama zata barni na tafi kuwa mami ta shigo dakin itama cikin less fari tayi kyau nace zakije ne?tace zanje kinsan nasir zanbi nace yawwa har naji dadi tace su Bilki da Sa’a da kyar ne zuwansu amma suna dai can gidan amarya nace
har an kaita ne?mami tace an kaita mana daga can zaa dauketa nace mami mamanmu na falo ne?ina son fita bana son ta ganni zata iya cewa na koma dare yayi tace aa bata nan shigowata na ganta da tire tayi sashin Alhj nace yauwa dama yaynmu ne yake kirana nayi kyau
mami banji kin yaba ba mami tace kinfa hadu wilh nace nagode,bari naje daga can fa zan wuce sai mun hadu don nima Nasir yace yana hanya sai yazo nan ya daukeni sannan yaje ya dau _ sauran kawayen Amarya,muka fito a tare tana fadin gara nayi damadama da abuna kada inje wata ta kwace min an ganni yar yarinya mukayi dariya muka tafa kowa ya kama gabanshi,nayi waje ita kuma
WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
tayi dakinsu jiran Nasir dinta,na dubi motar da ita kadai ce a harabar gidanmu ban san motar ba na dan tsaya nesa da motar ina ta dube dube to ina yayanmu yayi ne? din din naji hon daga motar gun motar na nufa ba dama
kaga na ciki ya sauke glass din motar sai da jikina yayi yarrr yanda na ganshi yayi masifar kyau kyanshi ya kara fito tamkar shi yayi kanshi ya bude min mazaunin gaba,shigo kawai yace min sannan na shiga wow wani kamshi da sanyi baa magana motar sabuwa ce dal, bai min magana ba muka fita munyi tfy sosai ba tare da yayi min magana ba sai wakar WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG mutuniyarshi wato celine dion ke tashi a cikin motar,can wayata ta soma ringin a jaka na ciro ta mama ce,gabana ya fadi na dauka mama tace
cikin tsawa ina kika fita yanzu?wurin dinner fa zamu
tafi.wa kika tambaya nace don Allah mama kiyi hakuri
tace karfe nawa zaku dawo?wllh ban sani ba,to ki kula da kanki ki tsare mutuncinki kinji ko?nace to mama in Allah ya yarda zan kiyaye,tace to don gsky da ina dakin ba zaki fita ba,tara saura sai yaushe za’’a fara bare a gama nace kiyi hkr zamu dawo da wuri,ya juyo ya dubeni bayan na gama wayar sannan ya dauke ido yamai da kan titi sannu a hankali ya tsaya a gefen titi ya kuma dubana kinyi kyau sosai nayi murmuahi nagode,ya zuba min ido
ni kuma na kasa dubanahi sai dai wani farin ciki da nake jin shi yaja wani dogon numfashi sannan yace
Imman!…ya ja sunan tare da kama hannuna wani irin
yanayi mai wuyar fassara na shiga ban taba jina cikin irin wannan yanayin ba ya dan murza min yatsuna sannan ya
tsare ni da ido tare da fadin baki amsa min ba na kira
sunanki iman nace umm….ya cigaba dan Allah iman ko
bana nan kada ki tsaya harkar samari ki taimakeni ki
cigaba da karatunki kinji?ki barni na zaba miki miji dai dai da ra’ayinki wanda kike so shima yake mutuwar sonki kinji little sister di ta,wani haushi ya kamani na zunburo baki a raina nace dama nasan ba wani sona yake ba Amira tace min ta ga kamar yana sona ne,ya kai yatsansa kan lebe na ya dan buga kadan sannan ya ce kina da wanda kike so ko?nace a’a_ cikin kulewa da shagwaba kamar zan yi kuka Www.bankinhausanovels.com.ng yace to menene na jin haushi umm?na kara turo baki gami da girgiza kai. kafaduna ya dafa,ina kyafta ido sai ga hawaye,kawai ji nayi ya jawo ni ya rungume wai yana lallashina,sorry my sister bar kuka,kan uba jina cikin kirjinshi sai na manta duniyar da nake, kai SO! ba dama ne,duk da na san bai kamata na biye mashi mu hada jiki ba amma sai na kasa janye nawa jikin,cikin taushin murya yace kince min,zakiyi krtn ko?ban motsa ba ya cigaba na san kina
kokari da hazaka ki gyara paper ki wannan shekaran kinji ko?karki damu da maganar aure yanzu barshi nan da shekara biyar nan gaba,ya dago ni daga jikinshi yasa hannunshi ya rike fuskata yana duban idona hawaye na zuba, idonshi cikin nawa yake kallona,kin min alkawari zaki yi krt ba sauraron samari?na rintse idona dan ba zan jure kallonshi ba sonshi sai ya kasheni a raina nace ni ba wani krt da zanyi tunda kai kayi naka auran ko menene
matsalarshi da karatuna?me zai karu cikin krt oho?kamar yasan tunanin da na keyi sai naji ya ce karki yi tunanin ina ruwana cikin harkar krtn ki akwai dalili kin gane bance komai ba ya sakar min fuska sannan ya bani hankici gashi share hawahenki na karba shi kuma ya anshi jakata yace nasan ba za’a rasa yan kayan shafe shafe cikin jakar ba ko?ya dubeni ko babu?nace akwai yace ni kike wa magana kina yanga?daidai lokacin ya cire sinkin hotunan jiya menene wannan?bai jira amsa ta ba ya cigaba da kallon hotunan yana cewa kai mun yi kyau amma duka nawa ne ni dai kallonshi nake kawai na gyara fuskata sosai shi kuma ya bude wani aljihu yasa hotunan sannan ya dauko wayarshi yana fadin bari na kunna wayar nan na san za‘ayi ta nemana a jita a rufe shi yasa nabi wayoyin na rufe, ni sai mamakinshi nake yi WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
kamar ba shi ba, ya dubeni zaiyi magana wayarshi ta
soma ringin ya dauka hello Nas yayane?ina juyo muryar Nasir na fadin Maska kai wane irin dan iskan mutum ne kana duba agogon ka kuwa?kasan ynxu tara da rabi kai fa kace tara daidai ba African tym shine ynxu dan iya shege daga dauko mota sai muji ka shiru kama kashe wayoyi,to ka samemu a wajen dinner domin har Amarya tana gun,yayanmu yace ni ake jira kenan yace eh mana kai kadai muke jira Amarya bata shiga gurin ba gata nan a mota sai ka iso ku shiga tare,gani nan yace Sannan ya
kashe ya ja mota muka tafi,ya dubeni kece mutum ta
farko da ta soma shiga motar nan, naso Mimi ta soma
shiga sai gashi kin mata shigar sauri kin shige mata
mota sannan hotonki shine na farkon zama ajiya cikin
aljihun motar kinsan ko a kannena kina da babban
matsayin da kannena basu taka ba, nayi murmushi
sannan nace nagode,muka isa gurin ya ajiye motar ya
fito yana neman Nasir a waya can ya sameshi Nas na
iso kuna daidai ina ne,yace gamu na bayanka kai baka
ganmu ba,ya dubeni to fito Hajiya,na fito daidai sanda Anty mimi ta fito daga motar Nasir muka dubi juna ni da ita, shadda galila tasa dark green shima yaynmu ita yasa ankon kenan sukayi tayi kyau na fitar hankali ta sa sarka kirar dubai ga ashoben da aka sa mata a kanta ya dauru gashi har kan kafada duk sai naji na raina kaina,ganin ta daure fuska kuma tayi fushi hatta Nasir na kula yayi mamakin ganinmu tare,shi kam gogan ko a jikinshi ya isa gurinta madam kin jirani ko?sorry zo muje ana jiranmu
ya kama hannunta muka bisu ni da Nasir sauran abokan ango sun taryi Amarya da Ango,wuri yayi wuri kowanne teburi mutum hudu mata biyu maza biyu,Amarya da Ango su biyu ne a gunsu mu kuma mu uku ne ni sai Mami sai Nasir,can an soma ciye ciye sai ga Adams bansan ta inda ya fito ba sai ganinshi nayi ya dubeni, yar kyakkyawa ina kika shiga ne yau duk banganki ba?kafin nayi magana ya juyo gun Nasir Assalamu alaikum abokina ai min afuwa ‘yar kyakkyawa ta tsone min ido bana ganin kowa sai ita yace to ai shi kenan tunda ka WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
ganta ynxu sai mu gaisa waalaikassalam,mu kayi dariya sannan ya zauna bakici komai ba yar gidana ya miko min cinyar kaza saitin bakina ci wannan mana na kauda kaina sannan nace a’a Adam bana cin komai juice zansha,yace
sha mana ko na danji sanyi kinga Nasir yasa yar gidanshi a gaba sai ciyar da ita yake ba ruwanshi dake,Mami tayi dariya tace to tunda ynxu kaxo ai sai ka bata yace to ba gashi taki ci ba na fa dade ina kallonki naga shigowarki tare da Maska da Amarya na dubi gun yayanmu ga mamakina duk hankalinshi na gurin mu ya cika yayi fam tamkar ya fashe Adams ma ya dubeshi yace yar gidana kin ga yanda Maska ke faman hararata?nace to ya maka kashedi kaki ji ba?Adam kana son bata ma kanka lokaci
ne kawai yardar yayanmu shine tawa,Adams ya dubi
Nasir yace Nasir yi mana sharia,Nasir yace ina jinku,naga yar kyakkyawa ina so ina ruwan yaynsu,Nasir ya nuna mami yace baga yar gidana ba da muka shirya
kanmu dole ya barmu,Adams yace to shi ne ta kasa
ganewa tabbas in kin yarda na san halin Maska in har
yace yes baya yarda yace no kin gane?so in har da
gaske kike sona zan aureki kuma zakiji dadi sosai yanda nake jinki a raina, ko! na dubeshi,yace ba sai
kin sha wahala wajen zuwa gurin malami ba zaki mallakeni son ranki,Allah sai yanda kikayi dani na rantse miki,na soma dariya shima yana dariya mami suna ta hirar su suma WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
yace a makaranta wane matsayi kike son ki taka?
Masters ko Degree ko Professor kikeson zama? zan barki da karfina da Aljihuna burina dai ki aureni ki haifamani yara masu kama da ke har da wannan dan dimple din naki, ya kai hannu zai taba min kumatu na goce ina dariya,sai yaynmu na gani akaina sai huci yake yace tashi a kaiki gida sha daya yayi ,nace yaynmu ka bari a tashi mana mama tasan wannan kuma zan kula da kaina……,ya katse ni tashi ko na mareki,tsoro ya kamani na soma kyarma adams yace Maska ya zaka ruda tane haba….shima ya katse shi please Malam yi min shiru kajiko,na nuna Mami ga Mami ma nan yace nina kawota?wanda ya kawo ta shi zai maidata na mike ya dafo min baya har gurin motoci,shiga nan ki jirani tunda ke bakya jin magana,kin je kin saki baki kina faman yima Adams dariya zanyi purnish dinki,ya rufe motar da
karfi ya tafi.haka na zauna shiru can da na gaji ga wuri yayi shiru sai sautin kidan can gurin dinner kawai sai na kira wayar mami nace wai yayanmu fa?tace gashi can wurin Amaryar shi suna zaune suna hira nace to na kashe wayar duk haushi ya isheni nace wato shi yana can yana hira da matarshi ni kuma ya hana ni neman miji ba wani jiranshi da zanyi tfy ta zanyi abuna wato ga mai gadi! na soma kici kicin bude kofa abin haushi sai na kasa hala kulleni da key ne in ba haka ba na jijjiga murfin ko motsi baiyi ba na kari masifa ta nakoma na zauna na hada kai da cinya na matse nayi shiru,har
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG