TAWA TA SAMENI CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

nayi zurfi a tunani bansan har mama ta dawo ba sai dai naji tace
haba iman har yanzu kina kan yankan albasar nan baki tashi ba?nayi firgigit na juyo tace ai kina tunanin menene haka?bata saba mana da karya ba don haka na sanar da ita tunanin da nake na kara da cewa mama ina matukar jin dadin zama dake kuma ina alfaharin kasancewarki uwa a gareni tayi murmushi tace sai ki dinga koyi da hakan kuma kiyi watsi da duk wani kuskure da kika ga nayi sai da na zuba albasa a cikin man sannan nace wlh
mama ni ban taba ganin wani kuskurenki ba tace kar ki kuma cewa haka babu mutumin da baya kuskure dan
adam ai ajizi ne nace to,sai da muka gama cin abinci
sannan na nufi dakin su mami don in gaisheta ina son
inje amma ina tsoron haj kulu mahaifiyarta yanxu ma
ganin ta shiga wanka shine dalilin da yasa xan je duk da dai bayin a dakin yake amma nasan ta shiga wanka ne a bakin kamal inda na tambayeshi ta na nan yace man ta shiga wanka na samu mami zaune a falonsu tana cin kifi nace yan jinya an samu Ify kenan tace kar kice man komi komi tunda baki zo gaisheni ba nace wlh ina son in

ZAMU TASHI 

Zo gaisheki ina jin tsoro ynxu ma kamal na tambaya yace mani mominku ta shiga wanka,um kina jin tsoro ne?nace baki yarda bane tace na yarda nace Amira ta na gaisheki tace tana amsawa tace ai naji sauki kwarai don naci dan waken mama sosai kafin inyi magana sai muka ji maganar haj kulu fuskarta a daure ta nuna ni tace wannan yarinyar baki da zuciya in banda rashin zuciya har yaushe zamuce ki bar shigo mana daki amma kin Www.bankinhausanovels.com.ng
kasa to yi nan ta nuna min hanyar waje.ta cigaba da


cewa marar zuciya anyi halin uwa mami tace kai mama don Allah ta kaima mami duka a gadon baya yi min shiru yar iska duk ba kece kika jawota ba in
na kuma ganinta anan sai naci ubanki ni dai nayi waje cike da takaicin zagin da nasha. washegari monday ga aladar gidanmu duk mai girki itace zata tashi tunda asuba dafa ruwan tea ko wane daki suna zuwa su dibi nasu a cikin flask su kai daki suje su hada, yau haj kulu ce da aiki don haka sai da na bari ta
fita sannan naje diba bansan cewa madara ta kare ta kicinba sai da nazo hadawa da sauri na nufi daki na iske mama tana sa ma jamila safa nace mama babu madara ko kadan ta dubeni tace kash jiya…. amma ga
dari biyar can kan mirror dauki ki siyo yanda zata isa in yaso kafin ya wuce sai in sanar dashi nace to na dau kudin na fita,a tsakar gida na iske mami sanye da
uniform hannunta rike da safa tace har kun gama
karyawa?nace aah ya jiki tace da sauki yau dai zanje
makaranta nace da kyau kam ki leka ta dubeni ynxu ina zaki?nace shagon sani ta aje safar akan window din dakinsu tace muje in rakaki nace kardai a nemeki tace kedai muje,dashi ke shagon ba nisa nan da nan muka dawo shigowar mu kenan haj kulu ta fito daga daki ganinmu tare da mami ya yi matukar bata mata rai ta hau mami da zagi gami da daukar alkawarin dukan mami,haj yaya uwargida sarautar mata itace ta fito daga dakinta tace ke kulu kina bani mamaki ga yar iskar da zaki jibga nan ta nunoni sai ki hau yarki da zagi kinsan fa ita da uwarta in mutum ya sarkafe masu baya ji baya gani sai Allah da malaman gari indai zakiyi mata addua to kawai kiyi mata,niko Www.bankinhausanovels.com.ng uwar tsoro jin ance zaa bige ni sai nayi daki da gudu ko mama ban bari taji xancen ba don bata son tashin hankali kuma Allah ya taimaka ta kunna rediyo inda tasa kaset na kr2n Alkurani kira ar sudes,a gurguje muka karya don kar muyi latti muna cikin sallama da mama kamal ya shigo wai kuyi sauri ko muwuce inji anty mariya mama ta miko mani naira hamsin tace gashi sa jikka nace barta mama gafa ta jiya nan ban kasheba sagir yace meyasa mu ba’a bamu kudin mama tace ku ai ga kwandonku nan cike da kayan abinci
amma in kun girma zan dinga baku kuma,jamila tace kai sagir mama tace babu kyau a ba kananan yara kudi yace wai haka mama? Mama tace e mana nace kai muje kar ayi ta jiranmu mama sai mun dawo tace to..
haka rayuwa ta cigaba da kasancewa kuma kusan ko
yaushe inada abunyi ban cika zaman banxa ba in bani
makaranta to ina kicin in ranar girkin mama ne don haka nima babu girkin da ban iyaba na gargajiya ko na zamani haka nan kuma na kan gyara dakin mama da namu da falo sannan na kware gun wankin bayi nasa turaren wuta shiyasa dakinmu kullum yana cikin kamshi da sanyayar iska mai dadi na kan zauna nida yan kannena in koya masu kr2 Alkurani da sauran littatafai haka ina taimaka masu da homework dinsu shiyasa mun fita daban a gidanmu komi namu tsaf tsaf,a ranar wata Sunday lokacin muna hutun islamiya, hadda ma don muna kusa da fara
azumin watan ramadan da safe misalin karfe goma da
rabi na gama duk wani yan gyare gyare nace da mama bari na shiga gidansu amira dama nan ne gurin zuwana tace to ki gaida maman faruq nace to,na samu Amira tana faman krtun littafin hausa a falonsu ko sallama ta bata ji ba sai da na zabga mata uban duka sannan na fizge littafin na duba sunan shi naga Allura cikin ruwa,nace kedai kullum kina cikin krtu maman su ta fito na gaisheta
tace mani yasu mama nace tama ce a gaisheki tace ina amsawa na dube ta nace mama wai baki hana Amira krtun nan ne?maman su Amira tace nayi nayi taki bari yanxu ma boyewa take don tasan in na gani yaga shi nakenace in tana son tayi karance Www.bankinhausanovels.com.ng karancenta ta bari sai ta kai ss sannan ta kijiba sai tayi tayi basmaman tayi shiru cikin bacin rai na harari Amira nace kinji dadi mama ta bata rai saboda ke?mama tace ai ke kina da hankali ba kamar ita ba ta shige daki Amira ta dubeni tace kinji dadi kin hada ni da mama nace no Amira in iyayenmu sunce mu bar abu muyi kokarin bari don gsky zan gaya maki da ki kijin mgnr iyayenki gara ki bar duniya a guna kenan tace to naji taja hannuna tace zo muje dakina
nace ke dai Amira baki son fadin gsky muna shiga na
zauna bakin gadon nace mata don Allah Amira kiyi kokari ki bar krtn nan tun da mama ta baki damar yin krtn in kinje ss.Amira tace nayi kokarin na bari na kasa ne,nace ni ko kingani nan ko me mama tace na bari ko da zan rasa raina ne ba zan bari don bani da tamkarta nai shiru ina tunani hawaye ya zubo min na dubi Amira nace don dai iyayenku duka biyun suna nan raye ko ince a tare shi yasa baki san zaman agolanci ba cikin hawaye ban san sanda nace………
sunana na gsky shine Amina kuma naci sunan kakata ce mahaifiyar babana ,babana da mamana yan asalin wudil ne a wani kauye da ake kira indabo a jihar
kano,babana gidansu sun gaji sarauta don babanshi ne dagacin kauyen,yanxu haka itako mama yar malamai ce don babanta shine limamin garin sunan mahaifina idris kuma
shine da na hudu a gurin mahaifinsu yana da yayye yaya samaila sai yaya musa sai babana idi kamar yadda suke kiranshi sannan sai kannanshi biyu bala da sani su shidda ne a dakinsu matan dagaci biyu ne uwargida Amina mahaifiyarsu babana kenan wadda naci sunanta sai abokiyar zamanta basira wacce aka bashi sadaqarta ita kuma yayanta ukku Auwal,salisu sai hindu,suna matukar zaman lafy ba wani bambanci wannan shiyasa yayansu hadin kai da son junansu gashi suna ma mahaifinsu dagaci umar biyayya kuma dukkansu gidan liman suke daukar krt mama ko a lokacin tana kaduna gidan yayanta mai suna mal bashir ya dauko ta ne tunda mahaifiyarsu ta rasu shi babban malami ne a tudun wada daga yawan almajiranci Allah ya zaunar dashi a inda yayi
auren shi da baba uwa itama dai yar can din ce da yaje ya auro ta,yana almajiranci a wani zuwa da yayi gida shine ya tafi da wasu almajirai a cikinsu harda idi babana kenan domin yayi sauka tuni,zai dora ne su ko su mama su hudu ne a wurin liman kawu bashiru shine babba sai kawu Aminu sai kawu kabiru Www.bankinhausanovels.com.ng sai mama ita kadai ce mace tana da shekara tara mahaifiyarsu Allah yayi mata rasuwa kasancewar ita kadai liman ke aure sai kawu bashir ya dauko mama dama baba uwa bata taba haihuwa ba ko ince har ynxu Allah bai bata haihuwa ba sai ko ta rike mama,shi ko liman isuhu aka bashi sadagar mata guda biyu da taimakon baba uwa mama mai suna
habiba ta samu shiga firamare shi ko baba yana nan
yana hadda gidan sai Allah ya hada shi da makocinsu
Alh adamu a dalilin dan gwanjo ne a kasuwar bacci yasa baba yana rubutu yana kai masa daga nan yace ,,,,,,,   yayi sanaa irin ta gwanjo alh adamu shima dai dan kano ne
ana ce mashi adamu garko duk girinsu daya sai dai shi a garko yake bayan ya nemi izinin malaminsa wato kawu bashir kawu yace tunda kayi sauka hadda kakeyi ba bu komai ko da rana za ka iya haddar ka Allah ya bada saa wannan sanaar itace hanyar arzikin mahaifina tun yana kasawa a bakin titin kasuwar bacci in an kwance dila a bashi ya kasa har ya koma kwance dilar shima kafin shekara ukku har ya sayi rumfa kuma yana sayan diloli a wannan lokacin ne Allah ya ba baba uwa ciki ta haifi da namiji kuma mama a lokacin ta kammala primary shiko babana duk da ba a gidan yake ba yanzu yana zuwa da daddare haddar shi ya sanar da malam kamar yadda suke kiranshi kawu shi dai habiba yake so mutumcin da
baba yake dashi a idon malam shi yasa har ya amince
koda kauye suka ji wannan zance sunyi murna don akwai zumunci mai karfi tsakanin gidan dagaci da gidan liman,kauye aka koma akayi biki sannan su mama da baba suka dawo shekara biyu da aurensu baba yayi kudi sosai da gwanjo tuni ya gina gidanshi a unguwar sanusi ga motocin hawa da na haya da ya sai ma mama sannan ya tallafi yan uwa na kauye Www.bankinhausanovels.com.ng hakika yana da halin kanawa na asali don akwai taimakon na kusa dashi haka ya debo yayan yan uwa sa daga kauye ya sasu a makaranta dan yana da haushin rashin bokon da baiyi ba danma cudanya da mutane yasa ya fara jin dan turancin sa na yan kasuwa matsalar baba da mama daya shine rashin
haihuwa har wannan lokacin mama ta fishi damuwa shi ko ko a jikinshi yace Allah baya barci a gefen mama ita ma tana taimakawa yan uwanta dama tuni daga dagaci har liman sun keta hazo sannan angyra gidansu tsohuwa Amina(kakata) sun kaita ita da abokiyar zamanta harda yayyan babana,su mama dai kowa a kauyen ya gama zuwa a cikin iyaye da yayye sannan suma suka je ita da babana.kowa yaje sai ya roka masu Allah ya basu haihuwa har cikin dangi sun fara korafi gami da nuna masa ya kara aure ita ko tsohuwa Amina macece mai nagarta da ibada da yarda da kaddara don haka itace mai tsawatarwa sauran yan uwanta da kannen alh idi
(wato babana)takan mika lamarinta ga Allah don haka kullum ma tana yi masu addu,ar Allah ya basu yaya na gari masu albarka,shekaru goma da aurensu

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *