TAWA TA SAMENI CHAPTER 20 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 20 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI


          WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

ya katse ni tashi ko na mareki,tsoro ya kamani na soma kyarma adams yace Maska ya zaka ruda tane haba….shima ya katse shi please Malam yi min shiru kajiko,na nuna Mami ga Mami ma nan yace nina kawota?wanda ya kawo ta shi zai maidata na mike ya dafo min baya har gurin motoci,shiga nan ki jirani tunda ke bakya jin magana,kin je kin saki baki kina faman yima Adams dariya zanyi purnish dinki,ya rufe motar da
karfi ya tafi.haka na zauna shiru can da na gaji ga wuri yayi shiru sai sautin kidan can gurin dinner kawai sai na kira wayar mami nace wai yayanmu fa?tace gashi can wurin Amaryar shi suna zaune suna hira nace to na kashe wayar duk haushi ya isheni nace wato shi yana can yana hira da matarshi ni kuma ya hana ni neman miji ba wani jiranshi da zanyi tfy ta zanyi abuna wato ga mai gadi! na soma kici kicin bude kofa abin haushi sai na kasa hala kulleni da key ne in ba haka ba na jijjiga murfin ko motsi baiyi ba na kari masifa ta nakoma na zauna na hada kai da cinya na matse nayi shiru,har

MiSalin sha biyu da rabi ni lokacin ma barci ya soma dauka,ta ban ankara ba naji an bude motar an shigo dan ma baccin nawa a dar dar na keyinshi kun sanni da shegen tsoro sai na kware baki zan tsala ihu sai naji an rufe min baki gami da cewa shishit!,ya kunna wutar

motar duk da naga yaynmu ne har ynxu jikina bai daina bari ba kin cika tsoro Iman saidai kin fi burgeni in kina cikin tsoro idanuwanki su kan birgeni ya kai yatsansa saman idona na lumshe ido jikina yana wani irin tsuma saboda yanda yake sosa min saman idona ya janye yatsansa sannan ya daure fuska ya dubeni yauwa dazu me Adams ya ce miki WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
kike dariya?nace ba komai yace karya kike yi zan gaya maki abinda ba ki sani ba shi kike so ba kuma ba zaki aure shi ba,kafin ya rufe baki wayata ta soma ringin shi ya rigani daukan wayar yana duban sunan sai yaga ashe mama ce sai ya bani na karba gabana yana faduwa,Iman yayi maki kyau kinji ko,nace dan Allah mama ki yi hakuri yanxu zamu dawo yanzun nan fa aka tashi tace bana ga mami ta shigo ba ynxu nace to ai ni yaynmu ne yace tunda shi ya kawo ni zai maidoni ya min magana a hankali yace kice mata kuma na tsaya sallama da mutane ne,tace to kiyi sauri sha biyu ta wuce banda ma bana dakin kika fita da babu inda zaki ta kashe wayar,na dube shi yayanmu ka kaini gida ni mama ke jira dan na san itace da girki zata sashen Alhj shi yasa yayi wata yar dariya to bari mu tafi kar Alhj na yayi ta jiran
mamanki gashi kuma na tsare ki anan yana magana da
wata fassara ne na kula sai na kauda kaina gefe,ya tada mota yace yauma gidanku zan kwana ance wai sai gobe zanje gidana suna son yi mata budan kai gsky sun bani haushi menene kuma budan kai?nace nima ban sani baa raina nace me ya dameni da zaka dameni dube shi kawai, wayarshi ta soma ringin daidai sanda muka tsaya a harabar gidanmu zan bude na fita naji ya jawoni ba tare da ya min magana ba ya dauki wayar na ji yace Alhj Iman gata nan na kawo ta kome Alhj yace mashi sai yace to ynzu zata shigo,ki shiga Alhj na jiran matarshi nima zan shiga daki ne na kira tawa a waya dan kece kika hana na maidata gida sai dai Nasir ne ya kaita,cikin
mamaki nace ni?da yaushe nace?yace au baki ma san
san da kikace ba ko?to shi kenan sai da safe ya bude
min na fita ina dubanshi koda yaushe na ce kar ya kai
matarshi oho?yazo ya min sharri kawai.
Washegari budar kai da safe nice nayi musu abincin
breakfast musa dryva ya kai musu gidan Nasir,da rana
ana tafiya gidan Amarya ni kam ban fara ba don nasan magana zai zama kai na gurin Amarya ko ince tamkar naje neman fada,da daddare muna zaune a dakin Amira ni da mami,nan mami ta sameni gidansu Amirar mami na bamu lbr tsaruwar gidan,nace dama_ shi yaynmu ai dan gayu ne sannan ya saba da rayuwar turawa kinga kuma dole ne ya tsara gida na yan gayu,mami tace gashi kuma da kudin ba,Amira ta dubi mami dama akwai zancen da zamuyi dake,nan ta kwashe maganar son yaynmu da halin da nake ciki ta gaya ma mami,mami ta cigaba da mamaki dama WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG yaynmu kike so Iman?gabana na faduwa hawaye na zubo min wllh mami kinji halin da nake ciki kenan,tayi shiru dan lokacin sannan tace to sai dai muyi
ta addu’a amma Haj Yaya da Haj Laure basu da kyau inma kin shiga gidan ba zasu bari ki samu kwanciyar
hankali ba sannan shi kanshi yaynmu a irin ra’ayinshi
baya son karamar yarinya yafi son babba nace na sani Amira ta ce ni kam sai naga kamr sonta yake yi nace ke ba wani so jiya kinji yadda yake min zancen matar shi dan haushi ni ko kula shi banyi ba. Mun tsaida shawara akan cewa zamu tsananta addu’a kawai Amira ta rakomu har gida dan zata karbi littafinta a hannuna dai dai dakin yayanmu abokanshi ne sun sha kwalliya sai kamshi sukeyi mami ta dubeni yau za’a kai angonki gidan amarya na dubi wajen sannan nace to ni ina ruwana ,dai dai nan Adams ya fito shima sanye da waganbari blue ammy sky yace Iman na juyo ina duban shi amma gurin na tsaya,yazo yau duk bangankiba yar gidana ina kika shiga ne?ina nan banje ko ina ba na fada,
su mami suka gaisheshi yace mami ko?mami tace eh
yace kefa?ya nuna Amira mami tace Amira yace nice
name,suna ta surutunsu ni ko hankalina na can gurin
ganin ango ya fito sai ko gashi yasha kwalliya da wani farin yadi mai shara shara fari tas komai fari yasa har glass ban taba ganin yasa glass ba sai yau yayi kyau har ya gaji,takaici da kishi ne ya kamani raina ya sosu sosai na zuba mishi ido duban shi kawai nakeyi ba mamaki ganin karshe ne nake mishi dan yanzu ba gidan mu daya ba bani zan dinga dafa mishi abincin ba ba zan dinga dafa mishi lipton da daddare ba ba zai aikeni ba bare na mishi gyaran daki sai dai anty mimi bayan kwana kadan kuma su tafi England shi kenan nayi rashin yayanmu,nayi,WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
zurfi cikin tunani ban san su mami na min magana ba sai da suka dafani nayi ajiyar zuciya na dubesu yayane? Adams yace don Allah ki daina irin wannan tunanin wai ma tunanin me kikeyi?ban ma saurareshi ba na juya ina duban yaynmu ya shiga gaban motar Nasir,Nasir ya iso gunmu Adams zo muje mu kai angon can tun kafin ya kai kanshi,sai masifa yake mana wai in ba zamu je ba ya tafi abunshi,hankalina ya kuma tashi na juya nayi gida na barsu a nan mami da Amira suka shigo, kuka riris suka sameni ina yi dukkansu sun tausaya min tare da bani hakuri sunce na ringa danne kishina a gaban mutane dan
kar suni,cikin kuka nace ba zan iya ba dan wani
zazzafan so nake mishi ga mugun kishin shi dana ke
fama dashi ku taba kirjina kuji ji nake kamar zai bude
dan azaba kun san Allah Amira ko mimi bata kaini son
yaynmu ba,sai dai tabi bayana,sun zubo min ido suna
mamakina daga baya suka koma bani baki gami da
kwantar min da hankali suka ce nayi shiru kar mama
taji nayi tsaki sannan nace ynxu bana shakkar kowa ya sani yanda nakeji ni kadai na sani nan dai suka dan
lallasheni suka tafi.. So masifa ne yanda naga rana haka naga dare sai bayan nayi sallar Asuba sannan barci ya daukeni nannauyan barci mai cike da mafarkai kala-kala mama ta tasheni WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
karfe bakwai tayi lokacin da ciwon kirji mai karfi na tashi hankalin mama ya tashi sosai ta yiwa Alhj waya yana dakinshi sai gashi yazo,yace shirya ku je Rimi Clinic zan sameku ina yin wanka mama tace kodai a siyo mata magani a chemist?Alhj yace a’a ku daije in ciwonta ne fa kinsan da kirji yake farawa sannan ta suma ku dai tashi kafin suman yazo,ko wanka banyi ba muka tafi bayan mun ga likita ne sai ya bani gado raina baiso ba amma dole na kwanta an min allurai na samu bacci ya daukeni da sauri ba ni na farka ba sai wurin Azahar mama ta rike min hannu tana min sannu,na yunkura na tashi har yanxu Saitin zuciyata bai daina zugi ba,da taimakon mama na samu naje bayi bayan na dawo ne na samu likita ya shigo zai dubani daidai lokacin yaynmu ya shigo shima
suka gaisa da mama ya tambayeta jikina tacemashi da
sauki,sannan ta fita likitan yace na kwanta sannan yace ya nake jin saitin zuciyata?nace da sauki sosai saidai yana min zugi har ynzu na dubi yayanmu da ya kafa min ido na kauda kai dan ni ko ganin shi bana sonyi,Doctor ya juyo gurin yayanmu yace yallabai tun safe nake neman ka a waya ban sameka ba ko da dai kana Amarci don Allah kayi hakuri na taso ka ko?yaynmu yace no ba komai matsalar ntwk ne shi yasa baki sameni ba,ya cigaba da cewa sanda kika yi min waya ina kan hanyar zuwa nan don Alhj mu ya sanar dani da na kirashi, likitan yace ciwonta yana barazanar dawowa da karfinsa abinda ya haifar mata ada ciwon ta sa wani abu a ranta sosai ta matsa ma kanta da tunaninshi gabanta yana mugun
faduwa inta ganshi,ya batun da kai wancan lokacin?
kasan fa sai da lallashi sannan zaku san matsalar ta,kusan kuma maganinta sannan muma namu aikin yayi kyau,yayanmu ya dubeni sannan yace kamar yanda na sanar da kai na san matsalarta fiye da kowa a gidanmu ita dai ta cika zafafa abu ne,bata son bin komai a hankali shine matsalarta,yaja kujera ya zauna kusa da gadon Iman!ya kira sunana na dubeshi har ynxu mamakin maganarshi nakeyi yasan matsalata?ke nan ya san ina sonshi?dan ni dai a sanina bani da wata matsala da ta wuce WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG wannan.Anty yagana na shigowa Adams da mami
da Amira suka shigo ya rusuna ya gaida mama taja Anty yagana suka fita,Adams ya dubeni ke yar gidana ya haka ta faru?nayi murmuahi sannna nace ikon Allah kenan Adams ba abin mamaki bane ko da mutuwa aka ce nayi,ya tsare ni da ido kar ki ja mon yar gidana karki min fatan mutuwarki dan ban san halin da zan shiga baa raina naji zan iya auran Adams gsky ba zan tabbatar ma da yaynmu zancenshi ba shi kuma maye ne yake in har zai zauna da mutum sai ya san halin da yake ciki,Adams ya dawo dani daga tunanina kinyi shiru yar gidana ko jikin ne?a’a kadan kadan kirjina ke min ciwo su mami suka min sannu yaynmu ne yayi sallama ya shigo ganin
Adams ya bashi mamaki sai naga ya dauke fuska a
daure,hannu yaba Adams suka gaisa sannan yace dama naso daga nan gidan Nasir zan sameka muje ku gaisa da Amarya sannan mukai ku airport,ina su john suke?sun fita da Nasir nima ynxu naje sallama da yar gidana shine na samu su mami sukayi min bayanin tana nan sai mukazo amma fa ina ganin ba zamu tafi tare da su john ba,because of what?yaynmu yayi saurin tare shi da tambaya,Adams yace kana son sani ne?to saboda sister dinka yaynmu yace yana da kyau ka san su ma ta lagos zasu tafi dan haka muje mu sallamesu,Adams ya dubeni zan dawo yar gidana kinji ko?gira na daga shiko yaynmu harara ya sakar min ya wuce abinshi,mun jima dasu mami sannan mukayi sallama,sukan su yaynmu suna fita sai gidan Nasir inda rigima ta sarke tsakanin yaynmu da

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *