TAWA TA SAMENI CHAPTER 22 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Na idar da sallar magriba ina zaune a takure duk
tausayin mahaifina ya cika ni Alhj ya shigo da sallamarsa ba sosai yake shiga dakin matanshi ba sai in bukatar hakan ta taso ya karaso gurina yaya dai Iman? Ify dai ko? nace lfy klau ka dawo Ify ya kasuwa?Amalhmdl Iman kuma Ify lau muka dawo ina Habiban fa?nace tana cikin dakinta,ya nufi dakin mama yana fadin Habiba sarkin hidima hala wani aikin takeyi,sun jima sannan suka fito naga fuskar mama murtuk babu alamar dariya ta zauna kan kujera shima ya zauna kan daya kujerar dake kusa
dani yana fdin ban sanki da fushi ba ba halinki bane
ruko,kuma ba kya gaba,uhm kuskure mutumin nan yayi ya kuma gane har kasuwa ya sameni shi da wani
Ibrahim ban san wanda ya nuna musu ni ba sai dai
ganinsu nayi nace miki har kuka yayi gabana yanzu kiyi hakuri ki zo muje suna falona ku gaisa,mama ta ce cikin fushi Alhj Mukhtar na taba yi maka musu?yace a’a tace to tin da kaji nace ba zani ba itama ni na haifeta ba zata ba to,ko kukan jini yakeyi ba zamu ba,yanzu ne ya san damu?ba zan iya ba wllh in kuma ya matsa min sai na
maka shi kotu da sauri na dubi mama kalmar ta
bani mamaki sam ban taba tunanin mama tana fushi haka ba
hawaye ya soma zarya a kumatuna sam ba zan so haka
ba Alhj da shima mamaki ya hana shi magana sai ya
mike ya fita falon shi ya sami babana da yaya Ibrahim
hakuri ya basu gami da ce masu su je su sami kawu
malam can kuwa suka tafi kawu malam ya jima yana
yima babana nasiha sannan ya ce je gobe ya dawo suje unguwar Rimi Www.bankinhausanovels.com.ng
Misalin karfe biYu saura kwata 1:45,zaune nake kan
sallayar da nayi sallah na jima ina adduoina game da
matsalolina, mama dake kan kujera ta dubeni Iman ynxu
ya zaki hada lesson da comp school din na ce nifa
mama ynxu duk basu dameni ba krt ma ya fita daga
raina mama ta kafa min ido sannan tace to me zakiyi in baki krt ba?nayi shiru ta saka salati ku jimun yarinya
aure kike so ke nan ko?nan ma banyi magana ba tace
shi kenan kudina sun huta sai ki fito da mijin ko,na dubi mama nace bafa dan haka dan haka bane dan….sai kuma nayi shiru,yi min magana dan menene? nace dama Www.bankinhausanovels.com.ng
wani abokin yaynmu da yake can England yake sona
yace kuma a can zamu zauna can zanyi karatuna mama tace Alhj yayi min maganar shi yA koma zakiyi krt ai dai
sai da sakamako mai kyau ko?nace to wane ma lesson
zan shiga,mama tace ga wata nan ramat road ki shiga
tunda an kusa fara jarabawar ina gama salamat tsohuwar
makarantarku zaki zana jarabawar a can,nace yauwa
dama yafi,…Alhj ne yayi sallama mama tace Ify Alhj?na Www.bankinhausanovels.com.ng
ganka da rana yace Ify lau ya dubeni nayi mishi sannu da
zuwa yace kuzo Habiba ke da Iman ku sameni a dakina
gabana ya fadi mama tace in fa baban Iman ne ba zani
ba yace ina dai jiranku,falon cike yake da mutane Alhj ne
a kujerar bakn kofa 2 sitter sai kawu malam can gefe na
gane yaya Ibrahim da kuma babana sai wasu mutane
uku da ban sansu ba nan da nan mama ta dunke fuska
kusa da Alhj ta zauna nima na zauna kasa gefen
mama,sai baba yace uwata zo nan kusa dani mana ,na
dubi mama sai naga bata kalleni ba dan haka sai na nufi
babana kasa na zauna ya jawo ni kaina ya dora kan
gwiwowinshi naji wani irin muguwar soyayya irin ta da da
mahaifi na ratsani kawu malam ne ya soma magana
Habiba ga uban Amina ya zo bada hakuri akan irin
kuskuren da ya aikata a can baya,mama tace ai bai min
komai ba,babana yayi karfin hali yace haba Habiba nasan
nayi maki kuskure dan Allah ki yafe ni nasan baki da
ruko habiba,mama tace ai ni Idris dan ka sakeni ba laifi
kayi ba tunda halas ne sannan Allah ya bani wani mijin
wanda yafi ka komai nima sakamakon hakurina kenan,na
dubi mama banji dadin maganar data fada ba babana
akafi?na kuma gyara kwanciyata a jikin shi ni ina sonshi Www.bankinhausanovels.com.ng
nace a raina,kawu malam yace yanzu dai yace ki yafe
mashi babna yace yauwa nidai kimin aikin gafara mama
tayi shiru sauran mutanen sukayi tasa baki mama tace
meyasa sanda ya zalunceni ba wanda ya bada baki sai
yanzu da ya milla da kanshi zaizo ya wani ce wai na
yafe mishi,kai Idris kai ne mutumin da banyi tunanin yi
maka afuwa ba,ta soma hawaye kai ne ka aure ni tun
baka da komai kai ne ka fara sanina ya mace kai na fara
haifa ma ‘ya amma daga karshe ka ce na tafi da yata kai
kafi son ‘ya’ya maza daga tsatson fati ka manta?dan
haka ynxu ma Sai kaje gurinta
Tunda muke da kai ko ince tunda muka rabu da kai ka
taba kawo daidai da pant aba Iman,Alhj yace kiyi hakuri Habiba ya wuce kice kin yafe masa,mama tana
kuka Alhj da sauran mutane ma suna bata hakuri kawu malam ya soma mata fada to tunda duk nan ba mu isa ba shi kenan karki yafe ko Allah ana mishi laifi yana kuma yafewa bare ke,ganin ran kawu ya soma baci sai tace shi kenan ya wuce ya shiga godiya yace Alhj Mukhtar kaima na gode da irin rikon da kaima uwata Allah ya saka da alheri ya dubeni uwata ynxu wacce makaranta aka gama?ko shirin aure akeyi?na boye fuskata a gwiwarshi,Alhj yace sun kammala sec bara to paper din tata batayi kyau bane shine zata
gyara sannan asan abinyi, babana yace to batun miji fa? Alhj ya ce eh akwai wani Adamu abokin Abdulrahim tare suke sana’ar tasu can a England shi nake zaton take so,amma sai mun gama bincike mutumin Ghana ne ina da abokin kasuwanci a can binciken ba zai bamu wahala ba tunda Abdulrahim yace min game da halayen Adamu babu matsala karatun ma yace a can zatayi shi ne nace ya nemi iso gurinta,babana ya dubeni uwata Www.bankinhausanovels.com.ng
kina sonshi?na kada kai alamar eh sannan na boye
fuska ina kuka dan na san ba shi nake so ba,babana
yace Alhj kaga wani sakarci?wai kuma kuka take
yi,mama dama tuni ta tafi nima na tashi zan tafi
babana yace uwata wai yaushe zaki zo mana kwana
biyu ne?na ce sai na tamabayi mama Alhj yace ko
zuwa jibi ne ai na kawota dan Habiba sai da lallashi
yanzu, babana yace ba komai kasan fushin irin na mai
hakuri bai iya ba har na fita babana ni yake kallo
bakinshi yaki rufuwa. Goman dare ina kwance kan gadon na murna duk ta
cika ni don munyi settling da babana wayata ta soma
ruri na duba Adams ne na danyi tsaki sannan na dauka yace yar gidana ya garin?nace yana hannunku yan England to haka ne ni dai na kira ne inji batunmu na runtse ido raina a jagule nace Adam na yarda zan
aureka da karfi yace da gaske kikeyi?nace kwaraI
kuwa,ashe kina sona Maska yace min ba kya sona karo
na farko kenan da Maska yayi min karya,na numfasa
sannan nace zancen so ai ya kare ko ina sonka ko
bana sonka tun da dai nace zan aureka ai shi kenan
sannan kayi hakuri Adams ina son barci ne shima sai
naji muryarshi tayi sanyi ya bar murnar yace to sai da safe na kiraki kinji?to na gode na tsaya ya kashe wayar Www.bankinhausanovels.com.ng
sannan na ajiye,daren nayi kuka sosai ba kukan komai
nayi ba sai na rasa abin sona shi kenan Adams ne
rabona zan auri Adams dan in nuna ma yaynmu cewa
tunanin shi ba gasky bane tunda baya sona ne da dai
yana sona ne da sai na tabbatar mishi da cewa nima
ina sonshi.Washe gari ina zaune akan kujera karama a nan kOfar dakinmu sauran mutanen gida kowa yana yan harkokinsa safa da pant dinsu jamila nake wankewa Sa’a da Bilki suna lido a kofar dakin su mami haj shuwa ce da girki dan haka tana ta kaiwa da komawa,lami mai aiki kuma tana wanke wanke anty mimi ta shigo tayi sallama ban san mai yasa ba duk sanda zanga anty
mimi sai gabana ya fadi ita kuma a nata bangaren haka
ne abin yake muna hada ido sai ta daure fuska gami da jan tsaki sannan ta kauda kai,su Bilki da Sa’‘a suka rugo suka rungumeta suna mata sannu da zuwa ta durkusa tana gaida haj shuwa sai ga yaynmu shima yayi sallama daidai sanda na gama shanya pant din ina wanke nawa pantys din,tun shigowarshi idon
Shi na kaina ni kuma duk da son ganinshi da nakeyi sai naki dubanshi dan ga matarshi kusa da inda nake zaune ya tsaya suna gaisawa da haj shuwa anty mimi kuma ta shiga dakin su mami dan gaida haj kulu,ba kya gaisuwa?ban dubeshi ba nace ina yini?yace ba zan amsa ba tun da ko kallo ban isheki ba bai san duk
haushin su nake ji ba shi da matar shi ba,menene
wannan kike wankewa a gaban mutane?sai naji kunya
duk ta kamani,anty mimi ta fito daga dakknsu mami
zata wuce sai yaynmu yace mimi baki gaida maman
sagir ba ranta bai so ba haka ta shiga dakinmu data
fito yace ta gaida ni na kwanta asibiti tayi jim can tace
ya jiki?tayi gaba nima sai nace da sauki shima ya shiga ya gaida mama ya fito lokacin su bilki sunbi anty mimi
dakin haj yaya sai haj shuwa a kicin ya dan duka saitin Www.bankinhausanovels.com.ng
kunnena baa wanke irin wadannan abin a waje SaI
atoilet kin ji ko?ya wuce na bishi da kallon mamaki na rasa mai yasa yanzu duk ya canza min baya jin nauyin yi min wasu maganganun daidai zai shiga dakin
hajyarshi sai ya juyo muna hada ido sai ya kashe min
ido daya ya shige dakin na kasa ci gabada wankin dan
duk ya saukar min da kasala kamshinshi kawai nake
shaka raina yayi fari tas na tattara na koma toilet dana gama kan gadona na haye na dau wayata na kunna dan kasheta nayi saboda ban san Adams na kirana duk sai inji na tsaneshi,text ya shigo min na bude sai naga show message i love you forever na duba. Yauma kamar kullum zai kai kusan sati biyu kullum sai an min wannan short msg na rasa waye?amma ina ganin Adams ne sai ya wani boye no naja tsaki ya karata nidai ba zan nuna mishi nasan yana yi ba ina yan fadace fadace na sai call ya shigo na duba sai naga yaynmu ne da sauri na dauka hello ki samenj dakin Kabir,hijabi na saka na fito falo mama yaynmu na kirana zai aikeni,to tace min Na fita zaune kan kujera na sameshi da remote a hannu
gani na fada ina Dubanshi sai naga ya daure fuska dan haka sai nima na shiga taitayina cikin dakewa da
miskilanci na shi yace zauna,na zauna ya dubeni da
farko ina maki murnar daidaitawa da mahaifinki da
fatan ki zama mai mishi biyayya ya cigaba da cewa naji batun Adam’s da kuma na gyara papers dinki kin zabga
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG