TAWA TA SAMENI CHAPTER 3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

matsalar baba da mama daya shine rashin
haihuwa har wannan lokacin mama ta fishi damuwa shi ko ko a jikinshi yace Allah baya barci a gefen mama ita ma tana taimakawa yan uwanta dama tuni daga dagaci har liman sun keta hazo sannan angyra gidansu tsohuwa Amina(kakata) sun kaita ita da abokiyar zamanta harda yayyan babana,su mama dai kowa a kauyen ya gama zuwa a cikin iyaye da yayye sannan suma suka je ita da babana.kowa yaje sai ya roka masu Allah ya basu haihuwa har cikin dangi sun fara korafi gami da nuna masa ya kara aure ita ko tsohuwa Amina macece mai nagarta da ibada da yarda da kaddara don haka itace mai tsawatarwa sauran yan uwanta da kannen alh idi
(wato babana)takan mika lamarinta ga Allah don haka kullum ma tana yi masu addu,ar Allah ya basu yaya na gari masu albarka,shekaru goma da aurensu


ZAMU TASHI 

Mamana da babana sun dawo ummara ta dawo da jinya mai tsanani bayan jin jiki da jinyar asibiti sakamako ya fito cewa tana da ciki fadar farin ciki ma bata baki ne,anan da kanshi baba yake mata rubutu take sha….. Wata tara da ‘yan kwanaki ta haifo ni sankaceciyar kowa ya zo barka sai ya yaba girma da gashina sai dai ni bakace tamkar mahaifina tun ina yar jaririyata har yau ban canzaba, dangin babana na dauko domin gaba dayan yan uwanmu Www.bankinhausanovels.com.ng dangin baba kamar mu daya muna da dan kyau daidai namu sai anan na dubi Amira nace kin dai ganni har yau ban canza ba na cigaba da cewa dangi sun
kwararo daga kauye da birni anan naci sunan tsohuwa Amina, kanwar mama kuma makociyarta itace ta ba da shawarar a kirani da iman,na taso cikin gata da tsantsar so gun iyayena da yan aikinmu da yayyena wadanda babanmu yake riko,shekara takwas na halarci makaranta nursery mai suna salmat intl dake kasuwar santara market makarantar yayan masu kudi ce don haka krt ba wasa duk lokacin hutu babana ya kansa a kaini kauye
don yace asali mafari wannan yasa na saba da

kakata
Amina da yan uwana ‘ya’yan baba lami mata sa’anina
Hassana da Ussaina muna wasa dasu kuma sune suke
kaini ganin dangi a sauran kauyukan,ina matukar son
kauye musamman yanayin damina tayi min a garin
domin muna zuwa gona kakata tana ji dani don haka
nima ina sonta suma dangi kowa na sona kawunnaina da liman suma ina zuwa in yi masu kwana biyu yau ina nan gobe ina can gata dai gani nan cikin sai in hutu ya kare zamu dawo wani sain da kuka nake dawowa a hado mani tsarabar kauye mai yawa dangin uwa da na uba sannan mu dawo tare da su yaya Ibrahim da yaya Abubakar, yaya Abubakar dan baba lami ne shiko yaya Ibrahim dan Baba Auwal ne(wato dan kishiyar kakata)tun kan a haifeni suke gidanmu kuma suna makarantar gumi college SS2 don haka tare muke zuwa hutu kauye dasu,kuma muna Www.bankinhausanovels.com.ng
kama dasu don duk wanda ya ganmu yasan yan uwa ne saboda kokarina a kai ta turani gaba a makaranta
sannan kusan kowanne malami ya sanni don haka ina da shekaru goma sha daya na kammala primary din tare da kyaututuka masu yawa muna zaman jiran fitowar sunayenmu ne,na fuskanci matsala ta soma kunnowa gidanmu in da mama ta tada hankalinta ni ban san dalili ba amma nasan nasha ganinta tana kuka in nace mama menene?sai tace idonta ke ciwo kuma koda yaushe zanga anty yagana kawar mama tana zuwa gidan su shiga daki da mama suna yan shawarwari,ni bansani ba wai ashe baba ne zaiyi aure da wata banufiya mai suna fati kuma ance ma mama bata da mutunci shine hankalin mama ya tashi tace da baba gsky ya canza mata sai baba yace karyar mutane ce kawai ya dinga lallashi gami da ban baki sannan ya kara mata jari har na naira dubu
dari takwas dama tuni ya sai mata motocin bus guda
biyu da babura ana mata haya dasu,anty yagana
makociyarmu ce yar asalin maiduguri ce amma zama ya kawo yayarta da mijin yar in da suke zaune kurmin mashi yayarta ce ta aurar da ita ga wanda take so Alh shu’aibu ma’aikaci ne a water board, tana da yara ukku kusan tare aka haifemu da yarta ta fari mai suna saudatu,suna amintaka da mama sosai haka ni da sa’adatu makarantarmu daya,bayan haifuwarmu ne anty yagana ta kara haifuwar yara biyu Nurfa da abida, Mama ko shiru tun daga kaina,anty yagana itace ta ba mama shawarar su hada jari su soma harkar yan kunnen gwal da jallabiya da zannuwan gado suna bada sako ta hannun wani abokin Alh Shuabu ne mai suna Alh Www.bankinhausanovels.com.ng Mukhtar Maska Dan zinare ne a kasuwar sheikh Abubakar gumi yana da shagunan jallabiya da gwala gwalai,shine yake kawo masu kaya in ya fita dubai harka ta amsu don da an kawo xaka ga matan manya suna zuwa suna dubawa suna saya don haka mama ta cire hankalinta daga batun auren baba,bayan auren amarya Fatima ta tare a dakinta da farko ta kwantar da kai amma ganin yadda mama ke facaka da kudi yanda baba ke ji dani sai hankalinta ya tashi ta shiga tsiro fitintunu iri iri yau tace kaza gobe tace kaza tasa su yaya Ibrahim da yaya Abubaar a
gaba,a nan mama ta taka mata birki tace kar ta sake ta takura masu suma gidan ubansu ne in tana jin masifar tata ta yi da wanda ya ajiye ta bada yara ba,wannan rigima har gun baba jin bata sami gsky ba shi ne tayi yaji sai da tayi wata sannan ta dawo,dawowarta shine ya zama sanadin juya mana baya duk yanda baba yayi sam baya sauraron mama da farko ban gane ba saida sunanmu ya fito munci makarantar mu salmat da mama ta sanar da baba sai yace kar mu dameshi ya gaji da biyan kudin makaranta,ni ba wani kokari ba shi maimuna gwarzo zai maida ni na ringa kuka ina rokonshi sai ce min yayi inyi hakuri shi ya gaji,haka na cigaba da zuwa islamiya da hadda boko kam ina ganin saudat tuni har ta shiga SS1 niko ina gida ,anty yagana tace da mama ta biya mani da ita tana da kudi tace ai ta mashi magana yace bai yarda ba,wata rana na dawo daga hadda da rana jugum na samu mama tayi a dole na zauna kusa da ita na dafa ta nace wai mama baki da lafy ne?tace kaina ke min ciwo iman,na tashi na nufi gun da muke aje magunguna na dakko mata panadol na dibo ruwa a kofi na kawo mata ta amsa tasha sannan tace kije dakin yayan ki duk wanda kika gani cikinsu kice yazo zan aikeshi wajen kawunku malam nace nima zanje mama tace to amma sai kinci abinci ko?nace e nayi sashen su yaya da gudu,a kofar dakinsu na tsaya nayi sallama yaya Abubakar shine ya amsa nace in shigo?yace in dai tsohuwa ce kar na ganta anan(haka su kan tsokane ni wai tsohuwa)na shiga nace kaine dai tsoho bani ba yace me yasa zaki sa mana tsufa daki don Allah kije waje nace naki din aje wajen baka girmeni ba ma zaka ce min Www.bankinhausanovels.com.ng
tsohuwa,ya kwashe da dariya yace waneni zai girmanki kece fa kika haifi su kawu da mama da baba anan gidan haushi ya kamani na hau tsaki irin na shagwaba ina son inyi kuka nace sai na gaya ma mama na juya zan fita ya jawo ni zo mana yar kanwata tawan zo mana kiji mama ta aiko ki guna ne?nace eh tace kazo zata aikemu gidan kawu malam ya mike ya dungureni shine baki fadi mani tun dazu ba?ya rike min hannu muka tafi dakin mama ban san me tace mashi ba na dai ga ta bashi kudi sanna tace in tafi falo inci abinci kafin ta gama bashi sakon,na
kunna tv na kamo cartoon ntwk ina kallo ina cin abinci sai naga anty Faty ta fito ni ban ma ganta ba sai gani nayi an kashe tv din na dube ta nace aunty ina kallon tom and jerry ne,tace na kashe ko zaki kunna ne?niko ban san gatse ba sai nace eh cikin masifa tace to zo ki kunna har ga Allah ni ban san gatse tai min ba sai kawai na tashi na kunna tv din remote din na hannunta kafin na
juyo sai saukar mari naji dau na yanke da ihu sai ga
mama da gudu ita da yaya Abubakar dama shi akwai shi da zuciya yace faty me tayi maki,anty faty tace in dole sai kasan abin da tayi min to ka nemi sani daga gareta dube ka dan kauye don kazo ka waye shine zaka kawo mana raini ko?yace naji ni dan kauye ne ke baa ma san asalin naku kauyan ba,don ba muga yanuwanki ba waya sani ma ko daga sama kika fado banza yar iska haka zaki kare a neman asiri,sai tayi kanshi da zagi harda duka nan da nan ya sharara mata mari gami da ture ta mama da tuntuni take tsaye tace kai Abubakar wuce kawai kabar aiken sai anjima,ta nuna ni ke kuma yi daki na mike sannan na jiyo mama tana cewa kin gani ko faty wannan shine abinda na jima ina sanar dake ki daina shige ma yarannan kinki ji to kinga irin…….kan mama ta
karasa sai ta katse mata hanzari da masifa ke Www.bankinhausanovels.com.ng munafuka bake kika sasu ba?to albishirinki yau dinnan zaki san matsayi na,,,,,, badai Abubakar ya mareni ba? zaku gane baku da wayo yau,nayi shiru a daki ina kuka mama tace to ina jiranki da alkhairi anty Faty tace ni kuma da sharri nake jiranki yau da nai nasarar raba alkhairi da tunanin wata ya mace haka zan rabaku da gidan nan mama tace to ai Allah ya fiki kuma ba ya barci kuma yana tare da masu hakuri ta cigaba da cewa ke ko nasan baki san haka ba tunda kin yi nisa ba zaki taba jin kira ba to sai
muce Allah ya shiga tsakaninmu da ke in kuma mai
shiryuwa ce Allah ya shiryaki,ta shigo ta sameni inata faman kuka ta zauna kusa dani
ta jawo ni jikinta tace iman wace adduar kike min,nace ina rokon Allah yasa ki daina samun matsala da baba,mama tace ki hada da babanki shima ki dinga yi mishi ki roki Allah ya kareshi sannan ya raba shi da
dukkan sharri da ake mashi,nace mama wanene yake ma baba sharri?tace aa mugun abu ai ba sai kasan me maka zaka roki Allah ba,nace to insha Allahu zan dinga yi mishi,da dare sai ga dan aiken baba,yaya Ibrahim ne baba ya aiko wai muzo ni da mama babban falo babu neman ba’asi ya dauki hannu a gaban mutane ya mari mama ga yan aiki ga yayyena ga ni ga anty faty bayan marin ya cigaba da fada wai karya kuma jin an taba mishi mata inko ta kuma marinta ta mari aurenta mama tana rike da kumatu sai nan tace cewa tayi maka na mareta?yace to yau kuke me yasa tun da kuke tare bata ce kin mare ta ba sai yau kuma tace tana son in rama mata shi yasa mama tace shi kenan ni Allah ya rama mani ta shige daki,duk da karancin shekaru na sai da nayi mamakin baba wai ya rama wa anty mari? na juya

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *