TAWA TA SAMENI CHAPTER 30 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 30 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

zansa Mama ta samo miki mai tayaki aiki kin gane ko?nace eh bama sai ka nemo mai aiki ba ni zanyi,yace shi kenan yanzu Babanki ya cika mana Store da kayan abinci gami da kayan cefane sai ki duba babban kicin duk abinda babu sai ki rubuta Kabir zai kawo nace to ya mike ya fita na bishi da kallo a raina nace dama nasan mai aiki zan zama a gidan nan.

Yayanmu zaune a gaban Haj Yaya san da yazo ya
sameta tana ta sunturi a daki abin duniya ya taru ya
mata yawa, in da ta san danta zai auri matsiyaciyar
yarinyar nan da bata kashe kudinta a banza ba gashi
kuma abinda ya faru tana kishi da uwarta sannan yarta ta aure ma ta danta kuma wanda ta fi so; bazata yiwu ba ta ta tada masifa Alhj yace zai saketa in har ta sa dan nata ya saki Iman,ita kam ba zata iya hada zuriya da Habiba, ta dube shi wacce shawara ka yanke a kan yarinyar nan?gabanshi ya fadi yace to Haj ni ya zanyi haka Allah ya kaddara…..ta dubeshi haka ka ce?yace to ya zanyi ne Haj kina jin fa abinda Alhj yace ki

Www.bankinhausanovels.com.ng
kwantar da hankalinki bana son ace ta kaina kun rabu tace to naji amma sai ka min alkawari ba zaka kula yarinyar nan ba dan gsky ba zan so hada zuri’a da Habiba ba,yayi shiru na dan lokaci can yace to Haj shikenan? tace in har ka min haka shi kenan kar ka yarda ka saurareta dama kayi ta mata wulakanci in sun gaji suje su dakkota yace to duk zanyi tace to yawwa Allah yayi maka albarka,ya fito yana nazarin yanda zalyi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shida daidai na yamma na gama dafa abinci gidan sai
kamshi yake na zuba ma Baba mai gadi da direba na fita na mika musu,ina fitowa wanka akayi kiran sallah sai dana yi isha’i sannan nayi kwalliya, paper less nasa yellow nayi kyau sosai na fito yana zaune a falona nace sannu da zuwa yace yauwa kin kaima Mimi abincinta ne?a’a ban kai mataba na dauka sai ka shigo amma bari na kai mata yace kawo nan in bana nan kika gama ki kai mata nace to na kawo mishi ya dibar mata komai ya fitaynace kai auran mijin wata ko matsala, ya dawo zO muci ai naci yace shi kenan daya gama ya fita sai misalin tara ya min waya na dauka yace na dafa mishi lipton zai zo ya dauka na dafa mishi mai kayan kamshi da tafarnuwa kadan a falo na ajiye mishi na shige dakina na kwanta. Haka naci gaba da zama tamkar yar aiki kullum da safe inyi gyaran dakina da falona in gyara babban falo na
hada Break fast na gyara kicin ban dai taba gyara mishi daki ba ban ma taba sanin yanda dakin yake ba,inyi abinci da safe da rana da yamma wataran ma har Anty mimi tace bashi take so ba yaynmu yace in sake mata wanda takeso, duk aikin da nakeyi bai taba damuna ba tunda na riga na saba saidai bai kai wannan ba kuma nasan lada nake samu batun kulani da yaynmu balyi ba ko a jikina tunda dama ni tsoro nakeji.Ina da kwana shida su Anty Yagana suka zo suka kawo min akwatuna har na gurin Adams, yaynmu dai bai min akwati ba sadakima babana ne ya bada.
shina na ashirin da hudu Anty Mimi ta tashi da nakuda
cikin dare misalin karfe biyu Yayanmu ya kwankwasa
min kofa na bude cikin tsoro yace nazo muje Asibiti
Mimi batada Ify da sauri muka tafi ya uzzura min da na fito mu tafi gyale kawai na rufa a kan kayan Www.bankinhausanovels.com.ng barcina riga da wando shi ya kaita cikin motar sannan na shiga na riketa sai fizge fizge takeyi tana kuka takasako salatimuna isa aka shiga da ita dakin haihuwa,jim kadan suka ce ta kusa mu kawo kayan haihuwa inji likita, yaynmu ya koma gida ya dakko abubuwan da likitan yace mishi,sai shida na safe ta haihu,san da suka zo mana albishir yaynmu yana masallaci sai ni suka ce min an samu namiji murna na dinga yi na kosa yaynmu ya dawo sai da ya dawo sun zanta da likitan na tare shi da murnata nace yaynmu Anty ta haifi Baby boy da murmushi yace alhmdll ina take?nace tana ciki ina kallon likitan ni ya kura ma ido nurse suka fito da yaron ni na soma daukanshi kyakkyawa yana kama da yaynmu sai dai farin mamanshi ya dauko,yaynmu ya daukeshi yana mishi addu’a likitan ya matso yana taya yaynmu murna ya dubeni kema sai ki kokari kiyi aure ko kin samu naki babyn,duk da murnar da yaynmu yake sai daya gimtse fuska gami da cewa naje na zauna na
koma kan benci na zauna can aka fito da Anty Mimi
zuwa dakin hutu,can ya dawo ya sameni zaune fuskarsa a daure yace min na tashi ya kaini gida yaje
yayi waya su Haj zasu zo, dama dan bai zo da
wayoyinshi bane muna mota yace shi ne na fito da
kayan barci dan wulakanci ba ko hijabi naxo ina ta
dariya a gaban doc,nayi shiru to me zance? shine fa ya uzzura min na fito na fito don tsoron masifarshi ne ko zani ban tsaya rubawa ba yace ina miki magana kinyi min shiru ko?na rasa me zance masa sai nace to kayi hakuri. Tunda aka yi haihuwar nan ban zauna ba dama ranar aka sallame su kullum gidan cike yake da yan zuwa barka girki nayi masu sau uku sau hudu, ga
habaicin su Anty Mariya da sauran kawayen mai jego gyaran gida har dakin mai jego sani sukeyi ina jin tsoron su ba zan ce bazanyi ba, ana sauran kwana biu suna ranar na sha wuya bugun fulawa suka Www.bankinhausanovels.com.ng jingine na cincin da doughnut kuma yan uwanta ba su sa hannu ba daga ni sai Mami sai ko matar Isma’il abokin yaynmu sune suka tayani,ga aikin gida da kyar nayi sallar isha’i na shiga bayi na gasa jikina na fito na kwanta na manta ban daf mishi lipton din nashi ba barci mai nauyi ya daukeni cikin barci naji ana tashina ni uwar yan tsoro na tashi zanyi ihu ya toshe min baki da tafin hannunahi yace ke sarkin tsoro ni ne ganin yaynmu nayi ajiyar zuclya
yace ina lipton dina?gabana ya fadi nace na manta ne yace to na tuna maki ya juya yayi waje haka na tashi na dafa mishi jikina na ciwo. washegari ya dawo da yamma ina falo ina gyarawa ya shiga dakin maijego ya shiga suna bedroom suna ta tsuga lbr tana basu Ibr yaynmu baya kula ni tun da nazo gidan bai taba kwana akina ba sai dai aiki kamar jaka ai bari a gama suna har kashin baby ita zata wanke, shi yana falo yana jinsu ga Anty Hadiza tana sallah a falon ba dama ta yanke tace su daina, tana tayi kawaye da Anty Mariya suna zugata, can yayi sallama ya shiga sai suka yi shiru suka daina maganar yaba ta kayan dake hannunshi ya juya dama kayan fitar suna ne yayi mana kala shida shida yayi mana, dakina ya wuce na aje tsintsiyar na shiga kicin dina na kawo mishi abinci gami da mishi sannu da zuwa na koma ga aikina na barshi nan yana cin abinci yana kallon TV. Ranar suna ko tun asuba na tashi na shiga kicin,dama yaynmu yace zaizo da abokanshi da safe suyi walima anan kafin mutane su soma taruwa dama nayi redin sinasir da mai na sai farar shinkafa da Www.bankinhausanovels.com.ng miyar anta sannan na dafa masu ruwan lipton mai kayan kamshi cikin katon fulas nasa ,farfesun kan sa sai peape mit na naman rago, bakwai da rabi na gama aikina, da yake a babban kicin nayi aikin.Nasuna kuwa ta ba kawayenta ne suyo daga can suzo dashi,ina shafe shafe bayan na fito daga wanka yaynmu yayo mani waya wai gasu nan zuwa,shadda galila yar gaske cikin kayan Adams take ta sha aiki kalar pink ni kaina na san na hadu, na zuba gwala gwalai na wuya da hannu har da kafa na baza turare sai kamshi nake zan fito yaynmu ya shigo sai mukayi karo dif yayi yana dubana shima yayi kyau cikin lallausan blue din yadin shi cikin murya kasa kasa idonshi a kaina yace kin gama?girata na daga alamar eh yace to sai ki kawo mana ya juya,darduma katuwa na fito da ita na nufi gurinsu,suna da yawa cikin ladabi na gaishe su sannan nace bari na sa maku wannan a kasa zaifi ko?na fada ina duban yaynmu fuskarshi ba a sake ba yace to bayan na shiga gidane na koma kicin ina fito da kayan abinci sai da na gama fito da kulolin sannan na kawo plate plate da cokula da kuma kofuna na kawo drinks da sugar da madara ko mai dai dai na shan tea kusa da yayanmu na tsuguna dan na sanshi yafi son komai a mishi na zuba mishi tea sannan na sa mishi sinasir da miya na dau karamin plate na sa mishi
farfesu na tura gabanshi,Isma’il yace duk kai kadai?
Nasir yace ka san yan kwallo da mugun ci shi dai balyi magana ba na jawo wani plate din yayi min wani kallo kasa kasa sannan yace a hankali bar nan,na tashi zan Www.bankinhausanovels.com.ng
wuce Nasir yace au mu da kanmu zamusa?Maska mufa
baki ne?yaynmu ya dauki kofin tea ya soma sha yana
fadin to kar ku zuba da kanku tun da cikin wani zaku
zuba ya dubeni da sauri na wuce,Ismail yace Maska
kana takurawa yarinyar nan dubanta kawai kayi amma da sauri ta bar gurin yace to ni bani son raini kuma ka
sani Nasir yace ta raini ai ta kare tunda yanzu taga
girman naka ko yaya yake Maska yace ba tonan asiri
ba ni bata ga kalar girmana ba suka sadariya Bello
yace kayi kokari kana da mace kamar wannan ai sal godiya haka suka yi ta hira.
Gidan dankam da mutane muna falo ni da Mami tace
kai Iman kinyi kyau sosai wannan dinkin ya amshe ki
nace me? tayi dariya sannan tace shi kenan tunda baki
gane ba nifa ba abin da nake a gidan nan sai aiki kumani bai dameni ba, Mami ta gyara zama ta
ce kina
nufin kallonki yaynmu ke yi? nace kallon ma ban isa ba
Mami tace lalai ynxu ke kin sa mishi ido?nace cab ji
Mami da wata magana ni ban ma san dadin abin ba
bare nace zan kai kaina ai ko na san komai ba zan
mishi ba ina mace Mami ta tashi ta jawo jakata ta ciro Www.bankinhausanovels.com.ng
wata yar kwalba ga wannan ki biya dubu uku,na
menene?tace ke ce zaki bani lbr kinga amfanin Sa Sal
zaki kwanta sannan ki shafa kadan dan dis zaki saa
tafin hannunki ki shafa yana da_tsananin kamshi?nace Www.bankinhausanovels.com.ng
yayi dubu uku Mami tace aikin shi yafi dubu goma zaki
fahimata in dai yaynmu ya shaki kamshin,na ce ai ba
tareqasa muke kwana ba tace ke dai kamar ba mace ba ke
ba zaki yi sanadin da zaki gifta ta gabanshi ba?nace to
ai bani da kudi Mami tace sai fa kin sai wannan turaren
yar arab take kawo mana har ma da wasu sai

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *