TAWA TA SAMENI CHAPTER 36 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 36 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

yace gimbiya ina gajiya nace kunzo lfy,yace lafiya,ina

mmn Sagir?nace tana Sallah mama ta fito suka gaisa

da har nace ni ba ranar zan koma ba mama ta bude

min wuta dole na bisu, Yaya Kabir yasa an gyara gidan

an share shi,na zauna a falona ya shigo kusa dani ya

zauna nayi kamar ban ganshi ba yace Iman kin canja

min sosai yanzu ba kya kula dani kamar da shiru na

mishi ya jawoni jikinshi tashi muje dakina mu kwanta

nace kayi hakuri ba zan iya kuma kwana dakinka ba,

yace kina hauka ne ko? nace ba hauka yace ya zaki ce

ba zaki kwana dakina ba alhalin ina mijinki? nace

yaynmu ina ganin girmanka kar kasa na gaya maka

magana, yace gara ma ki gaya min dan shiru shirunki

ya soma cutar dani ya cigaba ina matukar bukatarki ba

zan iya jurewa ba, na soma kuka ina fadin dama nasan

jikina kake so hakika iyayenmu sunyi kuskure da suka

zata kaine zaka rikeni amana ashe ba haka Www.bankinhausanovels.com.ng

Ya tare ni wayace miki ban sonki? fadin son da nake

miki kauyanci ne kin gani in za kiyi magana ki daina

kawo maganar so….da kana sona da ba kaini an cire

min ciki ba ina son abina kila ma shi ne kadai kwaina a

duniya tunda baka sona shi yasa baka son hada zuria

dani,yace ba zaki gane bane shi yasa amma ynxu na

yarda komai kika ce ki min afuwa nayi kuskure,shiru

nayi mishi gami da shigewa bedroom. Ku ziyarci blog dinmu  Har azumi ya riskemu bamu jituwa da shi, yayi

naki,karshe ma ya shareni,ina komai,girki da sauran

aikace aikace, girkin ma nawa nakeyi tana na ta, kowa

ran girkinta ta sama mijinta,duk da yaynmu yana

kokarin ganin kar Mimi ta gane sai da ta gane,don haka

take ta shigewa yaynmu gami dayi min kallon

banza,yaynmu yayi siyayya irin na neman lada su

gero,suga, madara ya aika kowanne gida,wato gidan mu

da gidansu Anty Mimi kai harda babana,haka har sallah

ta gabato ya mana siyayar kayan sallah ya sai ma yan

uwa da abokan arziki sannan ashe ya biya musu

ummara shi da Anty Mimi,ko ita ma bai gaya ma ta ba

sai da abin ya gabato, murna ta dinga yi tana

waya Www.bankinhausanovels.com.ng

tana gayawa kawayenta da sauran danginsu,ni ko sai

nayi kamar banji taba dama ranar nice da girki,yana

shan ruwa a falona ni kuma na idar da sallah ya dubeni

kiyi hakuri ba zamu je umra dake ba sai wata shekarar

in Allah ya kaimu,bace Allah ya sanya alkhairi na

tashi,da za su tafi yace komai na dangane da abincin

sallah yaya Kabir zai kawo sannan ya bani kudi nace to

ka san dai da sallah zani gida da gidan babana har

gidan kawu malam ya dubeni ban ce ki fita ko inaba,

haushi ya kamani, dama ina ciki gashi sai yayi ta jan

Anty Mimi suna wani soyayya a gabana dan naji haushi

ni ko sai na tashi na basu guri,na dubeshi gsky zanje

yawon sallah tun da nazo gidan nan ban taba fita ba

sai sanadin ciwo kusan shekara sai ka ce matar kulle

yace tun da ba matar kulle bace ki Je ai zan ji
Ibr na kara fusata nace ba fa siyana kayi ba hasalima ba gori Www.bankinhausanovels.com.ng

ba ganina kayi kawai an kawo maka shi yasa kake

wulakantani,yace Zauna ki gaya min me na miki?

kuskure daya na san na miki kuma na baki hakuri ni

nan da kika ganni kece mace ta farko bayan uwata da

na taba ba hakuri kuma kin ki ki hakura dadin abin ba

ke kadai gareni ba,abinda kike rowa ki jika ki sha ga

tsinuwar malaiku da kin bari ma cikin da kike fushi

kanshi da yanxu kin maida wani,raina ya kuma baci na

shige bedroom ina kuka.Tunda suka tafi kullum sai yayi

man waya wata rana in dauki wata rana na ki dauka,

dama dady wajen Haj Yaya suka kaishi,ko shekara bai

yi ba watan shi tara amma yana tfy.Da sallah ina zaune

gida dan ma yan yawon sallah sunxo min sosai Jamila

muna tare da ita tana tayani aikin sallah,shima
yaya Kabir yazo da Zee dinshi,babana ya aiko min da kudi Www.bankinhausanovels.com.ng

da kaji har da zannuwa ni da Anty Mimi har da Yaynmu

ranr baba uwa tazo da yaranta biu sun min wuni, Mami

da Amira rana daya suka zo min,mun sha hira har

dare,ita bikinta bayan sallah da Gidadonta,Sallah ta

wuce da kwana goma sha daya yaynmu suka dawo ko

waya bai min ba ranar ina daki ina karanta littattafan

da na ba Amira ta siyo min,na fito zani babban kicin ne

Sai naga mutane baje a falo,na tsaya ina mamaki

araina nace lallai yaynmu,ya dubeni yace kin tashi?ko

ba barci kike ba,ko tanka mishi banyi ba.Da daddare ya

shigo ya kawomin tsaraba na ce ya barshi na gode

bana so ga mamakina bai tsaya roko na ba yace to shi

kenan ya dauka ya fita.Satinsu daya suka soma shirin
Www.bankinhausanovels.com.ng
komawa nace tab ai ko wannan karon za’ayita,
tunda

Anty Mimi ta gama makaranta to ita ma sai dai ta

zauna amma barina jira ya kare dan wulakanci sai da

ana saura kwana biu su tafi sannan ya sameni a

bedroom yace ke jibi zamu koma don haka sai ki

rubuta abinda babu,na mike nace to ai nima na gaji da

zaman gidan sai ka maidani ga iyayena ko ka nema

min makaranta sai da ya harareni sama da kasa

sannan yace makaranta ki daina tunanin ta kin gama

karatunki ki tind na baki dama tun ba yau ba na

lallasheki amma kika ce ke aure,dama na ce kiyi kuka

da kanki dan haka ai aure kika zaba shi zakiyi,nace to

haka ake aure?yace tambayi kanki ya juya ya fita na

fada kan gado sai kuka.Shima dakinshi ya nufa yaya

zaiyi da yarinyar nan?shi dai yana sonta tsananin

bukatarta ne ya ke hana shi zama kusa da ita yayi lallashin ya bi ta fada a banza to wai shi yaya
zZalyi

ne,ranar da zasu tafi ko kofata ban bude ba ina jin

yaynmu yayi ta dukan kofar amma _ naki budewa a raina Www.bankinhausanovels.com.ng

kuma na kuduri aniyr in dai ya tafi to zan shiga

makaranta abuna sai dai in ya dawo ya sakeni,Alhj yayi

mashi waya lokacin suna tare da mama yace yayi sauri

yaje fita zaiyi kasuwa yaynmu yace ku tafi inaga sai

gobe tafiyar nan,sai gobe! Alhj ya bukata yacigaba

dama vakuyi bookin jirgi bane?yace nayi bookin din sa

Alh matsala ce a gidan nake son warwareta kafin na

wuce Alhj yace kai da waye?ni da Iman ba ma wata

babbar matsala_ bace,Alhj yace Iman?to menene?

yaynmu yace ka bari ba wata matsala bace mai girma

alhj yace to tunda ka dage kan cewa ba wata matsala

bace to baka da gsky yaynmu yace ina dai zuwa suna

aje waya mama ta dubi Alhj tace me yake faruwa dasu iman din?Alhj yace shirmen abdulrahman ne jiranshi na

tsaya yi muyi sallama don jiya bamu hadu ba ynxu na

mishi waya yana cewa warware wata matsala yake son

yayi tsakaninshi da Iman nace wace matsala ce yaki

fada shine nace bashi da gsky,mama tace kar kace

haka tukunna ina zuwa ta fita sai dakinta,layin yaynmu

ta kira tana tambayarsa abinda yake faruwa yace mata
Www.bankinhausanovels.com.ng
ba komi dama yana sonyi sallama dani ne kuma na

kulke kofa naki na bude,mama tace yayi tfyrshi yace ba

dama na tafi ba tare da nayi mata sallama ba,mama ta

samuAllhj ku saukeni gidan Iman din dan nayi waya da

yaynsu ynxu bansan me ake ciki ba.sai naji waya tana

ringin na tashi na dauka sunan mamana na gani na

dauka nace mama,tace bude min kofa,Jikina ya soma

rawa gabana na gaduwa nace to ina bude kofa mama

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *