TAWA TA SAMENI CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

               Www.bankinhausanovels.com.ng 



MUN TSAYA 

nace mama wanene yake ma baba sharri?tace aa mugun abu ai ba sai kasan me maka zaka roki Allah ba,nace to insha Allahu zan dinga yi mishi,da dare sai ga dan aiken baba,yaya Ibrahim ne baba ya aiko wai muzo ni da mama babban falo babu neman ba’asi ya dauki hannu a gaban mutane ya mari mama ga yan aiki ga yayyena ga ni ga anty faty bayan marin ya cigaba da fada wai karya kuma jin an taba mishi mata inko ta kuma marinta ta mari aurenta mama tana rike da kumatu sai nan tace cewa tayi maka na mareta?yace to yau kuke me yasa tun da kuke tare bata ce kin mare ta ba sai yau kuma tace tana son in rama mata shi yasa mama tace shi kenan ni Allah ya rama mani ta shige daki,duk da karancin shekaru na sai da nayi mamakin baba wai ya rama wa anty mari? na juya

ZAMU TASHI 

na dubi anty sai naga tana wani ciccika tana batsewa wai an rama mata, na bi mama daki na iske tana kuka na dafa ta nima na soma kuka ina cewa mama kiyi hakuri Allah ya saka maki. Anyi haka da kwana biyu na dawo daga kitso in da yaya Abubakar ya kaini tudun wada na mari yaya Abubakr din da wasa don ya dameni da tsokana tun a mota wai tsohuwa mai dan koko Allah kashe ki musha gumba,nayi banza dashi sai da ya tsaida mota sannan na dan kai mashi marin wasa kadan na bude motar nayi cikin gida da gudu,yace ni kika mara?sai


na rama shima ya fito yana dariya ya biyoni yana kirana nayi falo da gudu ina cewa so kake in tsaya ka rama ban kula ba na bude labulen falon na fada sai kawai naji na bige mutum lokaci guda kuma naji anyi Www.bankinhausanovels.com.ng jifa dani ashe nayi karo da anty faty ne shine ta jefar dani kuma ta biyoni da duka takeyi yaya da har ya juya da yaga na shige falo sai kuma yaji kukana nan da nan ya dawo ya iske anty nata faman dukana cikin zafin rai yake ma anty magana yace don Allah me yarinyar nan ta yi maki kike dukanta haka?yanzun nan fa muka shigo?ta juyo kanshi da zagi da gori,jin hayaniga shi yasa mama ta fito ta dubeni ta dubi yaya sannan tace Abubakr ba zaku daina daukar min magana ba ko?yaya yace wllh mama bamuyi
mata komi ba niko sai faman kuka nake ita ko anty faty Sai zage zagenta takeyi jin mama bata kula ta ba sai kawai ta shaki kwalar rigar mama tana cewa yau din nan na tsara zaki bar gidan nan duk nacinki miji ya wulakanta ki amma don bakin naci kin dage kin ki tafiya ko,ta cigaba da cewa to yau din nan za’a kama hanta ki koma wurin mai dattin hula,yaya ya fincike hannunta a wuyan Mama Sannan ya daura mata mari yace marar mutunci yar dangin jaraba rigima dai ta ki karewa har yamma sai da tayi ma babana aike har kasuwa wai yazo nan da nan sai gashi lokacin ma kowa ya kama gabanshi yaya Abubkr bai ma nan ni kuma ina daki mama tana koya mani karatu sai ganin baba mukayi ya shigo ko sallama babu ya jawo ni a gaban mama ya hau duka da
wayar wuta ina ta ihu gami da neman taimaki amma ina mama ko kallo ban isheta ba sai da ya gaji sannan ya barni don kanshi,sannan ya dubi mam yace ke kuma in tambayrki?mama ta dubeshi ba tare da tayi Www.bankinhausanovels.com.ng magana ba yace dake muka hada muka sayi gidan nan?mama tayi shiru yace ba dake nake magana ba mama tace ai ina jinka yace to ina son daga yau na sakeki saki daya sannan na barki minti goma ki barmin gidana….. Duk da nike karama ina jin ya ambaci saki sai na kara yanka ihu itako mama duk da dauriya da tayi don kar tayi kuka ace gabana sai da kukana ya sata hawaye koda mama ta gama kimtsa kayan ta ta fito falo zata tafi na biyo ta da gudu ina kuka babana yana zaune yana cin abinci da bai tanka ba sai da anty tayi mashi wata magana sai yace da mama ki tafi da yarki in kinji shawarata don ni yanxu nafi son yaya maza daga tsatson faty ga mamakina sai naji mama tace to Allah ya baku sannan na gode da shawara amma ko mun tafi da iman ai kanan nan a matsayin ubanta ko?maimakon yayi magana sai kawai ya kalli anty faty komi tace mashi oho sai ya juyo ya kalli mama yace kuje dai sai yanda hali yayi idan nine ubanta to na aiko maki amma fa gunki zata ci gaba da zama ba ba tare da mam tayi magana ba ta jani ko takalmi babu mukayi waje,wannan fita da mukayi itace fita ta karshe daga gidan babana mahaifi
kuma har yau ban kuma zuwa ba ban kuma ganin
babana ba ko anty fati ba. Muka koma gidan kawuna
marikin mamana daki guda kato bayan sati biyu babana ya aiko ma mama da dukkan kayanta haka mama ta cigaba da zaman iddarta har ta gama, itace tayi mani komi na shiga SS1 a makarantarmu wato salma,ina jin dadin zama da baba uwa wato matar kawuna suna da yaya biyar yaya suleiman shine babba sai yaya nura,anty rukayya ke binshi sannan sai nana itace sa’ata Sai karamin su mai sunan kakanmu liman ake kiranshi don sunan liman din yaci wato isuhu,nana maimuna gwarzo take itama jsl,yaya suleiman tela ne kuma yana zuwa poly ko da yake san da muke a  saura yan kwanaki ya gama shi ko yaya ustaz ne don yanzu haka ya na koyarwa a wata islamiya nan kusa da gidansu,sannan shima zuwa_ tashi_ wato sanawiyya a unguwar ma’azu,anty rukayya kuma tana aure ne a badarawa yaya suleiman yana debe mani kewar su yaya Www.bankinhausanovels.com.ng
Abubakar don shima yana tsokanata kasancewar mu
abokan wasa ne ya kance mani matar ni kuma ince
mashi ya mani tsufa bana sonshi yaya nura baida faraa shiya sa nima ban cika kulashi ba,wata rana ina zaune daki sai mama ta shigo lokacin kuma gab da babbar sallah ne mama tace iman shirya muje kasuwa nace to dama na riga nayi wanka sai kawai na dauki hijabina mai less a kasanshi nasa takalmina nace mama na shirya muka nufi kasuwa,bayan mama ta gama mana yan saye sayenmu nida nana sai tace muje
wajen yan zinari zata sai wani nace to muka je shagon shi makare da gwala gwalai kala kala da fara’arshi ya tari mama,naji yana cewa haj Habiba sai yau kikazo kasuwa?mama tace wllh ko Alh mukhtar maska inafa son nazo amma ban samu lokaci bane sai yau ya turo mana kujera yace mu zauna ya nunani yace wannan yarki ce ko?mama tace aa yace ke yarta ce ko yan mata?nayi murmushi yace ga murmushin nan irin naki ke ya sunanki?nace sunana iman yace suna mai dadi,sannan ya juya gun mama yace kin sami sakona a gun yagana? don tazo shekaranjiya ta kawo wasu karyayyun yan kunne,mama tace bamu hadu ba gsky mun dai rabu akan zata zo nan din yace sakona bai isa ba kenan?mama tace eh sai ya dubeta ya ce zaki samu ganina zuwa yaushe?sai nazo gidan naku,mama tace lafiya dai ko?yace sai alheri mama tace to ko yaushe kaxo zaka sameni sai dai da safe ina zuwa islamiya yace ba matsala zan shigo tudun wadan yanzu me kike so?mama tace ina son in saima Iman dubai ne kasan da na daukar mata a cikin kayan da ka kawo mana wancan sati ukkun da suka wuce to sai na ga kuma sun mata girma sai naba yagana tace kace mata sai bayan sallah shine nace bari nazo gunka ko zan samu wani,yace ba zaa rasa ba in kuma kinga ba wanda yayi miki to ki sai mata saudiyya mama ta zabar kirar dubai na wajen dubu tamanin har da abin hannu guda biyu yace gasky kina ji da wannan yar taki mama tace kai maska don na sai mata yan kunne?yana dariya yace sai nazo zan amshi kudin mam tace a’ah ga dubu hamsin nan bansan zan sami masu tsada haka ba mukayi sallama ya bani dubu daya yan hamsin Www.bankinhausanovels.com.ng hamsin a cikin kudin nayi godiya muka tafi,bani manta ana jajibir sallah Alh mukhtar maska yazo gun mama ni dai na dawo daga kitson sallah nida Nana na iske bako a dakin yaya suleiman da zai tafi mama ta shigo tace naje na gaida shi don yana ta faman magana in na shigo nazo mu gaisa,na zauna a kasa dashi na gaishe shi yace kin dawo muga kitson na nuna mishi yace iyye yayi kyau sosai yasa hannu a cikin aljihun shi ya dauko kudi sababbi yan naira ashirin bandir daya yace ga goron sallah don kilan ba zaki ganni ba naki karba nace ka barshi muna musu mama ta shigo jin musun da mu ke ne tace sunyi yawa ne alhaji ka rage yaki dole na amsa nayi godiya.Amira wacce tayi shiru tun da na soma magana kamar ruwa ya cita sai da nayi shiru sannan tace gsky iman ke yar gata ce to amma sai nan gaba zaki sani in Allah ya kawo karshen muguwar matar babanki,nace Allah yasa,Amira ta gyara zama sannan tace anty faty matar babanki ta haihu?nace kai har yanzu Allah bai basu ba tace to ina yayyenki Abubakar da Ibrahim kuma?yanzu basa zuwa nan?nayi murmushi nace kin cika tambaya Amira zaki yi kyau da yar aikin da nake ra’ayi wato yar jarida Amira ta basar da abunda
nace tace baki amsa mani ba nace basu san nan gidan ba don kwanaki baba uwa tace masu mama tayi aure,sai kuma ta kuma cewa to ina yayansu mami abdul wa ma kika ce mani?nace abdulrahim sunanshi mami tace yana england shi dan wasan kwallo ne nima ban sanshi ba amma ya sha masu aike nima na gani,shi kuma kabir aikinsa shi dai amira tace haba nasan shi mana ba shine yake karatu a kano ba,tace ai shi naga ba ruwanshi don naga yana maki wasa nace gsky shi kam ba ruwan shi ko zai zo hutune ya
kanzo da yar tsaraba su sweet biskit da yan kayan lashe lashe ya ba kannenshi tonima yanda ya basu haka yake bani don haka nima nake sonshi a raina ganin shi nake kamar yaya abubakar duk da bai tsokanata irin na yaya abubakar din amma kinga
yayan nasu da ke waje ina tsoron ranar da zai dawo,ta dube ni don mi kika ce haka?nace don ina jin yanda suke Ibr shi wai ya cika masifa ga duka sannan
nasha jin yanda suke bada lbr irin son da yake ma hajiya yaya,sunce yana son mamarsa kamar ransa don bai hada ta da kowa ba yanda mami take bada Ibr sai kinyi mamaki sosai abin kamar ba gaske ba to kuwa ai kinsan dole ne ya kuma ki duk abunda taki gami da tsanar shi tunda sunce komi tace mashi yayi,don haka ina jin ance yau zai dawo zan hada ya nawa yanawa na kama gabana na koma can gidan kawu na malam,Amira ta dinga man dariya wai na cika shegen tsoro nace wai ke dariya ma nabaki?lallai Amira, tana dariya tace dole ne nai maki Www.bankinhausanovels.com.ng
dariya ma naga dai komai son uwar shi sai kin mata abu sannan zata sanar dashi sannan in baki sani ba su maza yawancinsu basu da daukar zance na tsegumi haka wannan sai mata sai ko sakaran namiji ina jin wannan bazai maki haka ba don shi dan boko ne nayi shiru ina

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *