TAWA TA SAMENI CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                       Www.bankinhausanovels.com.ng 



MUN TSAYA 

yayan nasu da ke waje ina tsoron ranar da zai dawo,ta dube ni don mi kika ce haka?nace don ina jin yanda suke Ibr shi wai ya cika masifa ga duka sannan
nasha jin yanda suke bada lbr irin son da yake ma hajiya yaya,sunce yana son mamarsa kamar ransa don bai hada ta da kowa ba yanda mami take bada Ibr sai kinyi mamaki sosai abin kamar ba gaske ba to kuwa ai kinsan dole ne ya kuma ki duk abunda taki gami da tsanar shi tunda sunce komi tace mashi yayi,don haka ina jin ance yau zai dawo zan hada ya nawa yanawa na kama gabana na koma can gidan kawu na malam,Amira ta dinga man dariya wai na cika shegen tsoro nace wai ke dariya ma nabaki?lallai Amira, tana dariya tace dole ne nai maki Www.bankinhausanovels.com.ng
dariya ma naga dai komai son uwar shi sai kin mata abu sannan zata sanar dashi sannan in baki sani ba su maza yawancinsu basu da daukar zance na tsegumi haka wannan sai mata sai ko sakaran namiji ina jin wannan bazai maki haka ba don shi dan boko ne nayi shiru ina

ZAMU TASHI 

nazarin maganarta can nace wannan gasky ne to Allah yasa dai kar ya kulani,Amira tace amin,mun kaure munata zuba lbr sai kawai ganin yaya Ahmed mukayi nace a’a yayanmu ustazi ba sallama ne?yace ku dai bakujin sallamar to mama tace a tashi ayi sallah dama masallaci zani,yasa kai ya yi waje na mike nace bari na wuce gida kawai,Amira tace ai baki isa ba sai kinyi sallah kinci abinci sannan zaki bar gidan nan,na kwace daga riko da tai min nayi waje ina dariya nace yaushe rabon da ki shigo gidanmu,ta biyo tana kira na gudu gashi nayi sa’a mamansu tana daki tana sallah a

gidanmu ma mamanmu sallah na sameta tanayinima sai na shige dakinmu naga jamila tana barci na tashe ta muka yi alwala muna idar da sallah nima na kishingide. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ranar lahdi da daddare sai gasu yaya abubakr sunzo
nan muka sha fira, yanxu anty faty ta gama mallake
babana sai abinda tace gashi har ynxu Allah bai basu
haifuwa ba sai karyar bari,na tausaya ma mahaifina
kuma na yi alkawarin sa shi a addua insha Allahu zan
kuma roki mama ta barni inje na gaida kakata in munyi hutu mun jima dasu sannan sukayi sallama damu suka tafi
muna shirye shiryen soma jarabawa zango na ukku
don shiga SS2 aka yaye mu a islamiya inda mukayi
walima a gidansu Amira duk gidanmu ni kadai nayi
sauka mami kuma sai shekara mai zuwa don tayi wasa
da karatun mama da maman su Amira harda Anty
yagana duk sun mana bige bigen abubuwa irin su
kalanda da robobi,hankici da sauransu,da zamuyi rabon katin walimar har su yaya Abubkr sai dana bawa Amira nayi mata kwatancen taje takai masu kuma sunxo mani da kyautututukan su inda suka bani waya a kwalinta wai inji babana na amsa cikin fargaba na kai dakin kwananmu na boye shima yaya Sulaiman yazo kuma shine ya dinko mana kayan da muka sa ranar walima nashi gudummuwar kenan wata shadda ce galila mai kyau da hijabai. Sai da komai ya natsa sannan na dauko wayar dasu yaya suka bani na kai ma mama na mika mata leda ta amsa gami da Www.bankinhausanovels.com.ng tambayar menene a ciki?nace su yaya Abubkr ne suka kawo wai inji babana na fada mata cikin tsoro,ta saki ledar daga tsaye tace ke kuma ki ka amsa to ko menene ma a ciki zan maida musu ni,haka kuwa akayi ta kira yaya Abubkr a waya ta bashi gami da yi mishi gargadin karta kuma ganin wani sako daga babana da sunan wai nawa ne tun daga nan suma su yaya Abubkr din ta daina sakar masu fuska.mun shiga SS2 cikin sa’a da nasara ranar wata jumaa mun tashi daga makaranata na tsaya ina amsar sakon wani littafi da zan amsar ma Amira gun wata yar ajinmu Hauwa aminu don yanxu in tana karantawa nakan zauna ta bani lbr ko ta karanta mani na amsa na isa gurin da Musa yake tsayawa wato direbanmu ban sameshi ba na tsaya nayi sororo can na hango wata yar ajinsu mami don yanxu ba aji daya muke dasu ba ni ina A su suna C na isa gunta sai na tambayeta ko taga su Sa’a?don mami bata zo ba tace
mani sun tafi abinsu nayi shiru na kuma ce mata motar tazo?tace ba bus din gidanku ba?na daga kai tace to sun dade da tfy,sai da nayi nisa a tfy kasa sannan wani tunani yaxo mani na tsaida mashin na hau sai da muka zo har kofar gate din mu sannan nace bari na shiga na amso maka kudinka ina shiga harabar gidanmu naga matasan layinmu sun cika a kofar dakin yaya Kabir har da wadanda ban taba ganinsu a layinmu ba,nace a raina ko yaya Kabir ya dawo ne?don ynxu yana bautar kasa ce a Bayelsa na shiga gida na sanar da mama abinda ya faru tace to a nawa ya kawoki?nace 40,ta bani 50na kai mashi a hanyar dawowa cikin gida ne nayi karo da Anty Www.bankinhausanovels.com.ng Hadiza dasu Anty Mariya suna dauke da manyan tururuka da kuloli a kai,Bilkisu kuma tana dauke da plates da cokula ga wani kwando mai dauke da kayan shaye shaye na dube su na kauce a hanya,amma duk da haka sai da anty Mariya ta daka min tsawa ke akuya ban hanya,na matsa musu suka wuce,na shiga ina mamakin wane bako ne yaxo ake mashi hidima haka?bayan naci abinci nayi wanka nayi sallah na shirya cikin riga da siket yan kanti ina zaune a tsakar daki ina yin note sai ga mami da gudu ta shigo
tana kwala min kira iman! iman!!na tashi da sauri ina
fadin gani nan nace menene?don duk na tsorata sai
tace min ki tayamu mura yayanmu ne ya dawo ya
bamu waya nayi ajiyar zuciya na dungure mata kai nace har kinsa duk na tsorata na amshi wayar kirar nokia yar karama mai murfi gsky ta burgeni sosai nayi mata murna tace su dasu Sa’a iri daya ya sai masu don dama ya sai ma su anty Mariya tun tuni,nace kunji dadin ku wllh tace muje ku gaisa mana ko zai baki kema na dube ta cikin sauri nace ki rufa mani asiri ai ni ynxu ba zan taba yarda ya ganni ba bare da hankalin kaina naje inda yake ta soma dariya gami da fadin kin fiye tsoro me zaiyi maki?daga ganinki sai ya hau dukanki sai kace mahaukaci?tacigaba da dariya na ture littafin
gabana na dube ta nace don Allah ki sanar dani wani
abu game da yayanmu mana, Tace Abdulrahim
sunanshi na gasky wato Abdulrahim mukhtar maska a
yanda naji ana cewa tun yana dan karamin shi sam
baida yawan fara’a ga miskilanci don zai iya kwana bai damu da yayi ma wani magana ba in ana son aga
fara’arshi to a bashi kwallo sannan kwallonshi ta samo asali ne tun yana makarantar primary inda yayi ta cin gasar da aka sha hada su da wasu Www.bankinhausanovels.com.ng makarantun,haka yacigaba har secondary,bayan kammala yaso a barshi yaci gaba da kwallonshi amma sai babanmu ya kiya sam dole yaje ABU zaria inda ya karanci politics har ya samu degree bayan ya gama sai ya shawo kan babanmu da kyar yayi wasanni da dama a nan gida nigeria kafin ya fita england inda wani coach yayi mishi hanya, Na dakatar da ita nace ke ni ban tambayeki Ibr kwallo ba,kunce yana dukanku ko?mami tace Allah yana duka sosai ma,amma sai ka mashi ba daidaiba,na dubeta nace kamar yaya ba daidaiba?tace baya son ya saka
abu kaki ko kai shirme,bai son kazanta kuma in ka
ganshi yana son ka gaisheshi amma baison yawan
gaisuwa ,kana ce mashi ina kwana is ok,yana da cin
abinci kinsan yan kwallo gashi da tsafta yana son
kamshi ke gadai abubuwa nan,in har kin kiyaye komai
babu abinda zai faru tsakaninku ko ynxu ki tashi muje ki gaishe shi mana,nace a’a mami ma gaisa wata rana nace to ynxu ya dawo kenan?tace aah bai dawo ba kenan,zai koma wannan zuwan ma in gaya maki haj yaya ce ta matsa yazo don su gana da yar gidan haj laure,anty mimi nace ita zai aura kenan?mami tace kuma abinda baki sani ba yana matukar bin maganar iyayenshi don ko wuta suka ce ya shiga zai iya shiga musamman haj yaya bai hada ta da kowa ba yana matukar jin maganarta,na dube ta cikin tsoro nace kinji ko?tana ce mishi ya koreni zai koreni ko dai ma in tafine?mami sai dariya take yi min,Kamal ne ya shigo ya sanar da mami mamansu na kiranta.Bayan Www.bankinhausanovels.com.ng kwana biyu ya raba tsaraba har su jamila da sagir ya basu,mama ma ta samu less da shadda da takalmi sagir din ma harda Jc shi da kamal,su mami english wax ya kawo masu ni dai banje ba kuma bai sani dani ba don ban yarda ya gani ba,ran da ya yi kwana ukku da dawowa mama ta amshi girki da rana ina tayata aikin burabisko mami ta same mu a kicin tace yaya yace a kai mishi abinci,nace yana cin birabisko ne?tace oho nace to inbazaki laifi ba kije ki ce mishi burabosko ne don kar ayi mishi laifi,tayi musrmushi sannan ta fita,anty yagana tayi sallama ta shigo na fito daga kicin na amsa,sannan na gaisheta gami da tambayarta saudat tace tana gida sannan ta wuce ciki tana ce min maman naki na ciki? nace eh,mami ta dawo tace yace akai ma abokanshi shi kuma a dafa mashi indomie amma ke zaki dafa ko?
tace eh nace to don kar inyi kuskure mami tayi dariya tace kai ke kam kin cika tsoro,sababin kuloli mama ta bani na zuba masu birabisko da miyar kaji yaji curry sai kamshi yake,na dauka na tafi nayi sallama a kofar dakinshi aka amsa mani cikin faduwar gaba na shiga nace sannunku mutum uku suka amsa kaina a kasa ban kalli kowa ba nace a ina zan ajiye?cikin dauriya nake magana gabana sai faduwa yake wani daga cikinsu yace maska tana magana,da sauri na dan dubi wanda aka kira maska yana ta faman danne danne waya tamkar ba dashi ake magana Www.bankinhausanovels.com.ng ba,dayan yace ke ajiye kan wancan table din,na dubi table din sai naga akai yayanmu ya dora kafarshi na dubi mai maganar nace ai yasa kafa a kai yayi murmuahi sannan yace ajiye ko ina kinsan halin yayan naku sai hakuri na ajiye gabansa don mami tace dama su ne zasu ci na juya zan tafi sai naji murya mai sanyi amma cikin fada akace ke haka ake bada abinci a gidanku ko?na juyo da sauri ga mamakina yana danne danne wayarshi kamar

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *