TAWA TA SAMENI CHAPTER 6 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 6 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

kuma a dafa mashi indomie amma ke zaki dafa ko?
tace eh nace to don kar inyi kuskure mami tayi dariya tace kai ke kam kin cika tsoro,sababin kuloli mama ta bani na zuba masu birabisko da miyar kaji yaji curry sai kamshi yake,na dauka na tafi nayi sallama a kofar dakinshi aka amsa mani cikin faduwar gaba na shiga nace sannunku mutum uku suka amsa kaina a kasa ban kalli kowa ba nace a ina zan ajiye?cikin dauriya nake magana gabana sai faduwa yake wani daga cikinsu yace maska tana magana,da sauri na dan dubi wanda aka kira maska yana ta faman danne danne waya tamkar ba dashi ake magana Www.bankinhausanovels.com.ng ba,dayan yace ke ajiye kan wancan table din,na dubi table din sai naga akai yayanmu ya dora kafarshi na dubi mai maganar nace ai yasa kafa a kai yayi murmuahi sannan yace ajiye ko ina kinsan halin yayan naku sai hakuri na ajiye gabansa don mami tace dama su ne zasu ci na juya zan tafi sai naji murya mai sanyi amma cikin fada akace ke haka ake bada abinci a gidanku ko?na juyo da sauri ga mamakina yana danne danne wayarshi kamar

ZAMU TASHI 

yanda na sameshi,sai a lokacin ne ma na dan kalli fuskarshi, kykkyawa ne na ban mamaki don duk gidan
yafisu kyau sak kamarshi daya da _ hajiya yaya,tsawa naji in ba zaki zuba musu ba dauki ki tafi,da sauri na duka jikina na kyarma na zuba musu nan dakin ya bude da kamshin miyar kajin na mika wa kowa sannan na mike dayan yace dan bamu ruwa nace to zan fita dayan kuma yace ga fridge nan na nufi gun fridge ina tunanin yanda zan bude dan ban taba ganin irinshi ba cikin sa’a ina dafa shi sai naji na latsa wani abu sai koya bude kayan shaye shaye ne kala kala na rasa wanda zan dauko musu sai na dauko musu ruwaa babban gora na dauko five alive na aje masu da na duba saman fridge din sai naga kofuna irin na wajen na dauko tiran kofunan gaba daya na aje a gabansu,ina kokarin

mikewa ne mami tayi sallama suka amsa har da yayanmu ta shigo dauke da kula da plate da cokali na fita na dan tsaya a kofar dakin ina jiran mami Www.bankinhausanovels.com.ng 
labarin abinda yayanmu yayi mani sai na jiyo itama
tana shan nata fadan,muryar yayanmu ne yana ce mata yar iska haka ake dafa abinci?indomie ne din ba za ki iya dafawa ba?ina cewa ganin kin danfi su mariya abin kirki ashe kema useless ce,sam ban ga wani amfani ba gun mace matsawar bata iya abinci ba,ko aure kukayi irin abinda da zakuyi kenan ko?sai naji muryar wani acikin abokan yaya yana cewa to kayi hakuri mana maska,ai yara ne sai naji muryar yayanmu din yana cewa No…….  Nasir kar ka goyi bayan wadannan yaran sam basu iya
komai na mata basu iya girki ba basu iya gyaran daki
ba,sam basu iya komai na mata ba yan iska sai dare
yayi ka gasu suna surutu da samari sannan ace masu
yara?yaci gaba da cewa bari kiji ba za’’a yi asarar
wannan abincin ba maza ki dauka kije ki cinye shi ina
nan shigowa har dakinku inci ubanki in baki cinye shi
ba ina nan yanda kuka sanni ban canza ba fita useless kawai,nan mami ta same ni a kofar daki duk na kara firgicewa na dubi mami wadda ke zubda hawaye nace mami yanzu ya zakiyi da wannan uwar taliyar don Allah?tace zo muje sai da muka isa gun lungun shiga cikin gida sannan ta dubeni tace don Allah iman Ci wannan abincin kiji nasa hannu na dandana daidai kam yayi sai dai da ta dam kara wasu abu zai danfi wannan dadi,nace yayi mana tace to kinji shiyasa ni sam bana son ya sani wani aiki ga tozartani a gaban abokanshi nace to ki kai ma masu wanke wanke su tafi dashi gida mana tace wai in kaiwa su lami masu aiki?nace eh tace baki san yayanmuba kenan kar kiyi fata irin haka ta hada ku kuma duk matar da ta aureshi ta shiga uku,nace anty mimi zatayi fama muka wuce cikin gida bansan yanda mami ta kare ba,sai washegari a school take ce min zubar da rabi tayi ya sameta tana cin rabin.Washe gari gab da magriba na dawo daga Www.bankinhausanovels.com.ng islamiya da shike ina zuwa sanawiyya na shigo gida,zaune a kofar dakin yayanmu samari ne su hudu sai shi yayanmu yana tsaye yana daddana waya,nadan yi mamakin yanda baya gajiya da danne danne waya
ban taba ganinshi ba waya ba kuma ko da yaushe cikin
danna ta yake tun daga nesa nake kallonshi sanye
yake da dogon wando da riga daga nesa nake kallonshi sanye yake da dogon wando da riga mai gajeran hannu masu ruwan bula da ratsin fari an rubuta adidas jikinsu,gsky yafi yan gidanmu kyau,maza da mata dogo ne yana da dan fadi ga kwarjini gashin kanshi nannade ina tsammanin yana sanya mai ne akan ko kuma haka gashin nashi yake?oho ban san dalili ba duk sanda na ganshi sai gabana yayi wani mugun faduwa bana raba daya biyu don ina jin tsoronshi ne,na iso daf dasu kanshi a duke yana danna waya amma sai naji yace ke in kin shiga kice Sa’a ko Bilki su kawo mana butoci,to bama magana dasu Sa’a ko ince basa min magana kuma ban ga mami ba sai naje dakinmu na dauko butoci guda biyu na kai masu shi baya gun ina zaton bayinshi na daki zaiyi sagir na tura sagir ya kwaso mana butocin,wata rana asabar zan tafi islamoya don yanzu bana jiran kowa a yan gidanmu dan ba lokaci daya muke karatu dasu ba sai dai na biya wa Amira mu tafi,sanye nake da hijab har kasa nasa safa da nikab yayanmu na gani yana kulle dakinshi sanye yake da gajeren wando da yar rigar nike kafarshi da safa da takalmi but na kwallo da alama zai motsa jiki ne,nazo zan wuce ya dan dubeni ina jin yana son ya gane kowacece kamar na gaishe shi sai kuma na fasa ina zaton bai gane ni ba,na gota shi kadan sai ya juyo yace ke gabana ya fadi dama cikin faduwar gaba nike,na dawo kaina a kasa nace gani baiyi magana ba ya gama rufe dakin ya matso gab da ni sannan yasa hannu ya dage nikab din idona ya firfito don tsoro yace ooh na dauka mami ce,ya cigaba da magana fuskarshi Www.bankinhausanovels.com.ng 
a daure ke na lura sam baki gaida mutane ko? na dan
saci kallonshi fuskata yake kallo na kali kasa sannan
nace ina kwana?yace wuce bani so sai da na roka
kenan dubeta ,a raina nace masifaffe kar ka amsa din
na tafi abina. Zama da Amira yasa yau da gobe nima na soma karanta littafi kuma sai da na tambayi mama tace amma na dinga karanta masu kyau kuma masu amfani sannan in har zan karanta to ya zama bani da aiki ko na makaranta ko na gida shi yasa ma nafi yin karatun da daddare kasancewar bana fita ko ina ko samari sunzo kirana mama bata matsa mani ba don tace in kr2 nake son nayi to na tsayar da hankalina gun karatun.Yau monday muna hutun easter bani da wani aiki duk na gama kwance nake bisa gadona ina karanta wani littafi mai suna auren kisan wuta ina jin dadin Ibr banji sallamar mami ba sai dai naji an fisgw littafin daga hannuna cikin sauri na tashi tana dariya tace kai iman,ke dai kina krt nan baki jin komi,nace lbr ya hadu,tace hala na soyayya ne?nace eh tace ai na sani nace kin san me?ai ku ne kuke soyayya ni kin ganni da saurayi ne?naci gaba da cewa wallahi ni banma yarda akwai wata soyayya da kuke cewa ba,mami ta soma dariya tace lallai yarinya da sauranki ke da kike karanta littatafai ai ke zaki ba wani Ibr yadda ake soyayya,nace suma duk jinsu nake sai kiji an ce wai tana tuna shi tana mafarkinshi,don Allah da gaske ne?mami tace aa karya ne randa baku iya nutso a cikin soyayya ba zan yi Www.bankinhausanovels.com.ng magana ta katse ni da cewa ke ni ba wannan ya kawo ni ba an sa ranar su a anty Mariya wannan Alhajin kin ganeshi?nace mai katon cikin nan?tace eh shi ita kuma Hadiza wannan Sanusin mai jar motar nan,nace na ganeshi wanda ya taba cewa na kirata,don ya bata kudi ta bani shine ake cewa kar na kuma
gaishe da saurayinta,don mu duk wanda ya dafe mana
ya dafe mana kenan mami tayi dariya tace to shi. Yaya Abubakr yana zuwa gidanmu haka yaya ibrahim
dukkansu suna min hidima sannan yaya Sulaiman
shima yana zuwa sai dukkansu sun daina shiga wurin
mama Sai dai su gaishe ta waya,wani abin mamaki
kuma yaya Abubakar shi kadai yake zuwa haka ma
yaya Ibrahim din duk babu wanda ya taba min maganar soyayya ina ganin take takensu kuma bana jin zan iya amince ma dayansu. Yaya Kabir ya gama bautar kasarshi ya dawo gida,to shi dama muna shiri dashi rannan na fita da safe zani shagon mal Sani dan sayan sabulu naga yaya Kabir yana tahowa daga bakin kasuwa na jira ya iso nace kai kam ka cika yawo daga ina? Na duba wani abokin bab can da bashi da Ify nace ko Alhaji isa naji mami tana maganar zuwa duboshi yace yea shi ne,muka jero muna tfy har gida na tsaya daidai kofar dakinshi zai bani kwanukan dana kawo mishi abinci da daddare ya fito dasu kenan yayanmu shima ya fito daga dakinshi
cikin sauri na gaisheshi sau daya wato ina kwana yace
lafiya dama shi gaisuwarshi bata wuce haka in ma ka
kara to ba zai amsa ba na amshi na wuce sai naji
yayanmu na cewa kice mami tazo tayi mani shara kan
nayi magana sai yaya Kabir ya riga ni yace ai yaya
Abdulrahim dama wannan din kasa da kafi ganin daidai
dan ta kware yace to gashi in kin gama ki rufe mani
dakin kiba brother key din,nasa hannu biyu na karba
gami da cewa a dawo lfy bai amsa ba yayi gaba,na dubi yaya Kabir nace don Allah shi yayanmu baya amsa gaisuwa ne?Kabir yace yayanmu kenan ai shi daban ne duk yanda kika so ki san halinshi ba zaki iya ba mutum ne mai ban alajabi na wuce ina dariya,na sanar da mama aikin da yayanmu ya sani tace to na bar wankan naje na gyara mishi dakin zatayi ma su jamila in na dawo sai nayi nima nace to na shiga dakin yayanmu sai yau na yima dakin kallon tsaf,leather sit ne kujerun shi bakake ne masu girma setinau sai kayan wuta kafet da labulaye jajaye dakin sai kamshi yak nan na soma da bedroom din katuwar katifa irin wadda ba asa ta a gado din nan ce sai hanga na kayan sakawa a saman hangar akwatuna ne saiti biyu na dubi hangar rataye da kaya jibge a kan katifar ma duk kaya ne dai dai ko ina Www.bankinhausanovels.com.ng kwashe masu datti nayi a cikin wani dogon kwando irin na zuba kayan na gyara uwar daki tsaf sannan na koma falo shima nayi mishi aiki sosai na goge electronics din
komai yayi tsaf sannan na dauko turaren daki na feshe ko ina na kulle dakin,na kaima kabir,wanan shine silar fara sani aikinshi na zama mai gyara mishi

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *