TAWA TA SAMENI CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

min kwatancen gidan su Anty Mimi sai tace min me zan je inyi?nace yayanmu ne ya aikeni,suka rakani suda Amira don na hau mashin tayi ma mai mashin din kwatancen inda zai saukeni muka tafi yanda Mami tayi mani kwatance haka nabi bayan na sauka a mashin nan da nana sai gani a gidansu anty mimi na shiga kannanta na samu suna wasa a harabar gidan sune
suka yi min jagora har ciki nan na sami Haj Laura da
wata kawarta suna hira na gaishesu da farko bata
ganeni ba sai da na gaya mata daga inda nake sannan
ta murtuke fuska tace zauna nan na zauna.Ta daga
murya ta kwala ma Mimi kira kan Mimi ta fito sai
wannan kawar tata take tambayarta wannan yar gidan wacece?maman tace yar gidan kishiyar hajiya ce yar’uwata itama ta yatsuna baki tace ai har ta haifi yar da takai girman haka?ko ba amaryasu ba?tace itama mana amma ai wannan agola ce sai shegen kankanba kan ta kuma cewa wani abu sai ga Anty Mimi ta fito tace gani Mumy, Hajiya ta dube ta sannan ta nuna mata ni tace ga mai nemanki nan muna hada ido gabana ya fadi tace meye kike nemana?nace yayanmu ne ya aikoni tace yace me?na isa gunta nace gashi


ZAMU TASHI 
yace na baki ta dubi kayan tace duk gidan ba zai aiko

kowa ba sai ke ko?shegu mayun asiri ni dai nayi shiru
na kasa magana,Haj laure dake zaune can gefe tace to ko bata kayan ta maida mashi mana,tace tabdi ai shi momy daban yake in har na bari aka maida kayan nan ai sai nayi dana sani,ta fincike daga hannuna tace ai zamu hadu ni dashi,a raina nace kamar zata iya mashi wani abu,ina jinsu sai faman masifa suke nace ai Sai kuyi a raina,ina fitowa daga gidan na soma raba ido ko zan ga mai mashin amma ban gani ba na soma tafiya sai naji ihu ban juya ba naci gaba da tafy mai motar yaja ya

tsaya ya fito ya biyoni yace ke yan mata ina magana,na juyo cikin dardar don ban taba tsayawa da wani ba nace Ify?ya ce kalau in har ba zaki damu ba ina son sanin sunanki nace don Allah mallam kayi hakuri,nacigaba da tfy ganin yana ta bina gashi ban sami mashin ba ko wane yazo sai ka ganshi da mutum akai nace sunana Amira yace to ina ne gidanku nan dai nayi mashi kwatancen gidansu Amira muka rabu dashi Ify,da kyar na samu mai Www.bankinhausanovels.com.ng mashin na isa gida in da na bar su yaya nan na samesu na dan rusuna nace na kaimata yana sanarshi(wato danna waya)ba tare da ya dubeni ba yace ki shiga daki ki dauki wata leda ke ma kije kiyi amfani dashi nace to nagode kwarai,bai amsa ba na mika mashi kudin hanuna nace ga canjin kai kawai ya girgiza mani na nufi dakinshi,irin ledar da ya aike ni da ita ce akan kujera don haka nasa hannu na dauka na nufi cikin gida ni da mama muka duba less ne me shegen kyau kala biyu sai wani yadi mai santsi shima kala biyu takalmi da jakka kala biyu mama tace kin gode,nace mama ki bani da na kamu dana su Jamila sai na kaima yaya Sulaiman a tudun wada tace sai dai gobe nace mata dama ai. A ranar yaya Abubkr yazo da daddare kofar gida ya tsaya ya aiko Kamal wai nazo,na fita muka gaisa muka shiga hirar duniya can ya ce kanwata yau nazo da alamurra masu girma nace tO yace zancen na zama ne na isa kofar dakin yayanmu ganin baya nan sai na dauko kujerun shi na robana aje mana a kofar dakin yaya kabir muka zauna ya dubeni yace Iman nace na’am yace ya kamata ace tuntuni kinsan inda nasa gaba,nace kamar yaya kenan?yace yau dai na gaji ina son in fadi maki cewar ina sonki kuma da aure ba da
wasa ba,nayi shiru don banyi wani mamaki ba don na
kula da hakan shima yaya Ibrahim kwana hudu kenan
da yazo min da irin wannan maganar,yace sister naji
kin yi shiru,nace to me zance?gasky yaya ni bazan
boye maka ba karatu zanyi har sai naga karshen
biro,ya tsura min ido sannan yace in har zaki yarda ki aureni to ni kuma na miki alkawarin zan jira ki,na dan bata fuska nace gsky kar katsaya jirana don ni sai nan da shekara ashirin zanyi kai kuma kila a lokacin kace na tsufa ko ni naga tsufanka,yace inda so ai tsufa ba matsala bane nayi shiru ina tunani shi ma fa haka mukayi dashi (wato yaya Ibrahim)sam wai jirana zaiyi,yaya abubkr yaci gaba da matsa min nace yaya mubar maganar nan in lokaci yayi sai ayi na Www.bankinhausanovels.com.ng sako mashi wani zancen muna cikin hira yayanmu ya dawo a motarshi na raya a raina cewa daga gidansu Mimi yake sai kawai naji banji dadi ba kuma wancan abin dake samani nauyin kirji ya taso,sau daya ya dubi inda muke ya shige dakinshi sai naji ma duk hirar ta gunsheni nace da yaya Abubkr zan shiga gida yayanmu ya dawo kuma fada yake mana ya dubeni yayi shiru sannan yace har yanzu bakida waya a hannunki ko?nace eh amma mama tace ina gama secondary zata sai mani ya juya gefenshi ya dauko wata leda yace min gashi wannan ni na sai maki ba Baba bane bare mama tace ki maida,nace to bari sai na fara fadi mata in ta yarda sai na amsa yace dole sai na amsa ko ya kwana gidan nan,dole na amsa yana tfy na dauki kujerun yayannu na nufi kofar dakinshi cikin sanda na ajiye zan tafi naji yace wanene a nan?nace nice yace me kike nema?nayi shiru sai gashi yazo bakin kofa fuskarshi a murtuke yake magana wayace ki daukar min kujera? nayi tsuru tsuru yace wannan shine na farko kuma inason ya zama na karshe kar ki yarda ki kuma daukar min kujera ko ni sa’anki ne?nace a’a na durkusa nace yi hakuri bai min magana ba ya wuce daki ni kaina dari dari nake bansan yanda zanyi da waya ba. Washe gari nayi kuru da safe na nuna mata tace ke bakya jin magana ko?nace miki sai kin kammala karatunki sannan zaki ci gaba sai na sai maki waya amma kinje kinsa Abubakr ya sai maki ko?to shi kenan,na soma hawaye ina cewa wllh mama bani na sashi ba tace ki maida mishi in yazo nace to har tara na safe ban daina kukan wannan magana ba ni ba wai wayar da Mama tace kar inyi amfani da ita bane ya dameni a’a sai dai ganin da tayi tamkar na roka,tafe nake ina share kwalla zanje gun mamansu Amira in amso ma mama kanunfari zata yi ma su sagir kulin kamu yaya Kabir naci karo dashi zai shigo gidan yace Iman me ya sameki? na cigaba da kuka yana ta magana nayi shiru,yace nasan su hajiyarmu ne ko?nan nayi magana nace basu bane ni da mamanmu Www.bankinhausanovels.com.ng ne,yace duk yanda akayi kece kika tabo ta nace wani ne ya saya mani waya shine take ganin kamar na rokeshi ne,yace to ta kwace wayar ne? nace nifa ba kwace wayar ne ya bani haushi ba,yace na fahimceki kafin ya kara wata maganar sai ga yayanmu sun nufo cikin gidan shi da Anty Mimi shima ya ja birki yana ce ma yaya Kabir brother me ya sameta?kabir ya soma yi mashi bayanin cewa bafa wani abu bane wai yayanta ya bata waya shine maman Sagir tace wai ta rokeshi ne,ya dan dubeni sannan ya dubi yaya Kabir yace to yanzun ta kawo karanta ne? yaya Kabir yace no na dai tambayeta ne shine take min
bayani,ya dubeni yace wannan marar kunya da ya
zauna mani a kujera shine yayanki?daka mani tsawa
yayi nace shine yace good gara da ta kwace wannaki
bashi da kunya bai iya gaida mutane ba sai aikin kallon mutane don haka in ya kuma zuwa kice mishi ya tsaya daga bakin gate sannan ki san kin maida mishi wayar nan,a fusace ya yi cikin gida daga ni har yaya Kabir da kallo muka bishi Kabir yace ki tafi inda aka aikeki,na tafi ina mamakin wannan karfin hali wai (barawo da sallam) Ashe yana shiga gida dakinmu ya shiga dama shima duk safiya yakan shiga falonmu ya gaida mama tamkar yanda yake gaida mama tamkar yanda yake gaida sauran matan babansa,bayan sun gaisa ne sai yake ce mata maman Sagir mai ya sami yarinyar dakin nan na ganta tana kuka? Sai mama tayi mishi bayani ta kara da cewa nasan ba zata rokeshi ba na dai mata haka ne don kar ta kuma karbar wani abu gunsa,yace hakan na da kyau ta maida mashi zan sai mata waya bansan bata da waya ba kuma sanda na dawo ban san tana nan ba,mama tace ka barshi kawai yayansu nima zan sai mata nafi son sai sun kammala krt don yan satittuka ne suka rage masu su soma jarabawa yace haka ne in ta gama ko ba na nan zan aiko mata da waya,mama tayi godiya sannan ta kara da cewa ga kuma dawainiyar kayan da ka sai mata jiya an gode,na dawo na samu zai fita daga dakinmu na dan dube shi harara ya Www.bankinhausanovels.com.ng watsa mani nayi sauri na dukar da kai,na shige daki.
Sam ya manta da cewa tare da Mimi suke sai da ya
shiga dakin Haj yaya sannan ya ganta zaune tana cika tana batsewa ya zauna a kan kafet din dakin
kasancewar mahaifiyarshi tana kan kujera ya gaisheta ta amsa a ciki ciki sannan tace kai wai ba zakaji magana ba ko?ya dubeta yace haj me ya faru?tace ai kafi kowa sanin abinda ya faru don tsabar iskanci ku taho da mimi amma ku taho amma sai ka bar ta anan tana ta faman jiranka kuma kasan makaranta zata je tace tun tara take da lectures yanxu goma da rabi a ina kasa gaba?kafin yayi magana mimi tayi saurin cewa wurin fa bakar yarinyar nan ya tsaya wai sun ganta tana kuka suka firgice shida Kabir sai tambayarta sukeyi ban…….tsawa ya daka mata ke shiga hankalinki
ni sa’anki ne?uban wa yace da zaki makaranta ki biyo
ta nan?me zan miki?karki sa ma_bakinki kwado zaki
sha mamaki duk sanda ana min magana kika tsoma
baki ya nuna kofa da hannunsa yace see your way,fita a nan ta mike jiki na rawa mama ki daina min fada a gabanta kin manta ita ce matar da kika zaba mani na aura?zata raina ni ne hajiya in kina min haka a gabanta har tana sa baki dan raini,wllh taci albarkacinki ne da sai na mata dukan tsiya,ya cigaba da cewa bata san cewa ni saboda ke ni zan aure ta ba ba wai don tayi mani ba?haj yaya tace tsaya tsaya ba na son cin fuska ka manta ni da uwarta nono daya muka sha? bayan haka ma mimi bata da makusa ubanta balarabe ne ka kuma sani inma ilimi ne akan nema take gashi tana sonka sosai amma kai sai faman goce goce kake yi shi yasa na canza shawara kafin ka tafi sai an sa ranar aurenku,ya dubi haj yace ki dai yi hakiri na dawo don kar aje ana dagawa tace sam ban yarda ba yace to shi kenan ta juya zancen dake cewa wacece take kuka kuka tsaya kai da Kabiru?yace waccan yarinyar da nake aike ce,nan ta hau bala’i da masifa tace dama in banyi da gaske ba sai Habiba ta shanye min yara yanda ta shanye babanku kallonka kawai nake yi wannan mummunar yarinyar yanzun itace abincinka gyaran dakinka,aike yanzu itace tunda haka kafi so ai sai kayi sauran ka ka soma kai shawara gun Habiba haka tayi

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *