TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 1

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 1

Kashim Ibrahim library (KIL) babban ɗakin karatu ne cikin Jami’ar Ahmadu Bello da ke birnin Zariya. Kamar kullum yauma ɗakin karatun cike ya ke fal da ɗalibai maza da mata kasancewar lokacin jarabawar zango na farko na shekarar (first semester) ya matso. Ɓangaren da ta san ya fi kowanne rashin hayaniya ta samu ta raɓe. Sanye ta ke cikin shuɗin hijab dogo har kasa. Sam ba ta damu da ta shafa ko hoda ba bare a kai ga jambaki, irin bakaken matan nan ne da su ka amsa sunan “black beauty”. Duk yadda ta so ta mayar da hankali ta gane karatun da ke gaban ta, hakan ya gagara ba dan komai ba sai dan zaman da wani ya yi kusa da ita. Zuwan ta be fi da awa daya ba sai gashi shi ma ya zo, kuma ya rasa in da zai zauna sai kusa da ita duk girman library din, mitar da ta ke yi cikin ran ta kenan tana mai jan tsaki ɗaya na bi ma ɗaya. Tana cikin wannan halin ne ta ji kamar an gogi kafar ta wanda hakan ya sa ta saurin janye kafar da sauri, a fusace cike da alamar tambaya ta kai kallan ta gare shi. Tsintar idanun ta cikin na sa ya tabbatar mata da ya na sane ya sanya kafarsa ta gogi na shi, ko shakka babu irin ‘yan iskan mazan nan ne ma su yiwa mata goge, da be sami dama ba shi ne ya ke bin ta da kafa. Kallan da ta ke masa ne ya sanya shi janye tashi kafar da sauri tare da faɗin “Sorry Mama na! …”4 Maimakon ta ji sanyi cikin ran ta, sai ma daɗa tunzurata da yayi, wato yana nufin bai ma san kafar sa na gogan na ta ba ne, ko tsabagen shaiɗana ne da zai wani kira ta da “Mama na” tunda ya sami kafar tsohuwarsa ai dole ya goga. Take ta ji karatun ma ya fita daga ran ta, cikin zafin nama ta haɗa ya nata ya nata, har ta na bugewa da tebur tsabagen ɓacin rai ko gaban ta ba ta gani da sosai. Fuuu ta fice a fusace. Kai tsaye Queen Amina Hall ta nufa inda nan ya kasance hostel ɗin da take. Da ke bayan isha’i ne, ɗalibai samari da yan mata wanda su ka sha karatu da wanda ba ma su sha ba duk sun taru mararrabar hostel sai cafta ake. Sam ba ta kula da su ba, bare ta damu da sheƙe ayar wasu daga cikinsu ke yi na rungume rungume da shafe-shafe da ta ke jin labarin wasu kan yi, kan ta a kasa ta ke gifta su, zuciyarta na mata tuƙuƙi don gaba ɗaya niyyarta ta shanye handout biyu na course din da za su yi jarrabawa ta gaba. Daf da za ta shiga hostel din ta ji an tab’o kafadar ta, tsayawa ta yi cak kafin ta jiyo a hankali saboda jin da ta yi hannun namiji ne mai taɓo ta, wa za ta gani? Wannan mutumin nan ne dai ya biyo ta, har ya iya daga hannun sa ya taba ta cikin mutane……ji ka ke tas!!! Hannu ta sa ta dauke shi da marin da sai ya ga wuta a idon sa ba tayi tunani kafin aiwatarwa ba don gaba ɗaya ji ta yi banda cin mutuncin matatantaka da yayi har da musulunci da hijabin da ke jikinta ya ci wa mutunci. Gaba ɗaya hankalin jama’ar wajen ya dawo kansu, hasken lantarkin da ke ci a wajen kamar an ƙara masa haske don ya sadar da abin da ta aikata ga bawan Allahn nan. Jikin kowa yayi sanyin ganin wanda ke tsaye gaban ta hannun sa bisa kunci, bai yi zaton haka daga gareta ba hakan ya sanya marin zuwa masa a matsayin ba zata kamar yadda ya zo masu a hakan. Sanannan saurayi ne cikin Jami’ar wanda hatta wanda su ka shigo Jami’ar a wannan shekarar sun san da zamansa saboda shuhura. Ga mamakin kowa har ita mai marin wacce ta yi mutuwar tsaye ba tare da ta yi Dana sanin marin da ta yi ba, don tsayuwar da tayi jira ta ke kome ma zai faru ya faru don kwatakwata babu nadama ko karaya a tare da ita, sai gani kawai ta yi ya mika mata abu, ko da ta ware ido da kyau ta dubi abin da ya ke miko mata sam bata gaskata ba, a hankali ta mayar da kallan ta ga fuskar shi wanda ke dauke da murmushin da ya sanya kwarjini da kyawun fuskarsa bayyana, cikin nuna halin ko in kula da marin da ya sha ya furta “Ga shi, wayar ki ne da ki ka manta…” Hannun ta na rawa ta karɓa ba tare da saurari cigaban abin da yake shirin faɗi ba. Ta na karba ya juya, cike da takama da ko in kula ya ke tafiya yayinda ta bi bayan sa da kallo, shin wannan waye shi? “Ya Allahu ka rufa min asiri ni Amatullah…” Cewarta, a hankali ta juya ita ma cikin sauri ta na harhaɗa kafafu, daliban da ke gurin nan su ke ta cece ku ce akan abin da ya faru gaban su, daga masu ba ta kyauta ba, sai masu da su ne sai sun tattaka ta, sai masu Allah shi Kara7 ” Toh ai shi Dee Yusuf ya ɗauka kowacce mace ce ta rako mata, wallahi ta burge ni da ta kwashe shi da mari” ta ji wasu na faɗi daga bayanta. “Dee Yusuf!” ta so ta sake faɗi amma ina, zancen zucin da ta ke ya sa ta dena ji yadda ya kamata, kwakwalwarta ta dena sawwara mata daidai har ta isa ɗakin kwananta da ke gini na takwas ɗaki na goma sha biyu (block 8 room 12). *** Littafanta kawai ta ajiye saman gadonta, buta ta ɗauka ta fice ba tare da ta ce da Ahalin ɗakin uffan ba, kama ruwa ta je tayi sannan ta yi alwala, ɗakin ta koma ta gabatar da wutiri, sai a lokacin ta samu ɗan natsuwa, duk da haka ba ta motsa daga saman dardumarta ba, sam bata lura da kallon da kawarta ke mata ba. “Amatullah! Amatullah!! Amatullah!!!” sai a kira na uku ta ji ko dan ƙawar ta ɗaga muryarta ne ba ta sani ba. “Zulaikha sai ki firgita mai rai wallahi, ji tsawar da kika min” ta karasa tana mai jan gajeruwar tsaki, mamaki a karo na biyu ya sake kama Zulaikha saboda ta tsaki na ɗaya daga cikin ɗabi’un da Amatullah ta tsana. Tashi tayi ta ninke dardumarta, sannan ta haye gadonta da ke saman na zulaikha ba tare da ta ce da ita da ke jiran bayani komi ba. Ɗauko takardunta tayi don ta cigaba da dubawa amma ina babu abin da ke shiga, ga shi jarrabawar da za su yi gobe na physics department ne da duk wani mai karanta abin da ya jibinci kimiyya da ke aji ɗaya a jamiar yake yinsa, sannan adadin wainda ke maimaita jarrabawar kan fi rabin adadin masu rubutawa a karo na farko, saboda haka dukkan su ke tsorace da darasin. “Zulaikha na sadaƙar kawai zan sake physics dinnan” tace cikin karyewar zuciya. “Allahumma Ajirna” Zulaikha tace iya karfinta. “Kin shigo kafin lokacin da kika ɗibar ma kanki, kin shigo a firgice kin yi gamo ne?” Zulaikha tace tana shafa hannunta cikin sigar lallashi. “Marin wani Yusuf Dee yake ko wa nayi fa anan gaban Amina” tace iya gaskiyarta, yayin da Zulaikha ke hango kwantacciyar firgici a idon ƙawarta. Ba Ta dena shafa hannunta ba, ba ta ce komi ba kuma, so take ta tuna in da ta san sunan Yusuf Dee din, kamar wacce a ka raɗawa ta tuna. “Wai Dee Yusuf kika mara? Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, me ya kai ki Amatullah?” ta haɗa duka ta faɗa mata ba tare da ta jira amsar cewa shi ɗin ta mara ko wani ba. Hawayen da ta ga Amatullah na fitarwa ya kara tsinka mata zuciya. Zikiri take a hankali duk wanda ya zo bakinta, yayin da Zulaikha ta haura saman gadon tana lallashinta. “Kinga ba wani abin damuwa bane, Shine Sec Gen na SRC (Student Representative Council) Watau shugabanin ɗalibai masu wakiltar sauran ɗalibai, kuma shine in charge of student affairs department. Wasu sun ce bafullatani ne wasu sun ce babur amma kin tuna Halima ta statistics kin san yar Margi ce, toh ita na ji tana faɗin ɗan garin su, kin san yadda ake rububinsa hakan ya sanya masa girman kai, kuma Kinga kudin SRC na ɗiban su, amma ina jin kamar faculty of medicine yake na ji dai ana fadin first class guy ne, yana dai da yan kora ni shi ne kawai tsoro na amma banda haka bana jin komi” Zulaikha ta ƙarasa cikin tabbatar da abin da ta ke fadi. Kallon ta Amatullah take cike da mamaki, ta san ajinsu ɗaya, kawarta ce, tare su ke komi a ina ta san duk waɗannan bayanan da ita ba ta taɓa sani ba, ƙarshenta ma za ta iya rantsewa ba ta taɓa ganin wani halitta irin ta wanda ake kira da Dee Yusuf ɗin ba. Allah ya yi dare gari ya waye, jarabawar dai da ta fi firgita Amatullah yau za ta rubuta shi a matsayin jarrabawarta ta farko a jami’a wato ta kimiya Physics 131 (PHY131/ZAKS 131). Course ne da kowani dalibin aji daya da ke karanta wani abu da ya jiɓinci ɓangaren kimiya ke jin tsoro, balle kuma ita da ke ɓangaren Phamarcy, ba don komai ba sai don course ne da ake masa laƙani da “chain prerequisite for pharmaceutical chemistry (Pharm chem)” . Idan ɗalibi ya fadi shi ba zai taɓa yin na gaba da shi ba sai ya gyara wanda ya faɗi haka na nufin tabbatacciyar sake shekara (spill over) ce mai zaman kanta tun ana aji daya.5 Amma duk da tsoron faɗuwa sai gashi gaba ɗaya hankalin Amatullah ba ya kan Course din, ita babban tashin hankalinta bai wuce marin Dee Yusuf da ta yi ba gaba ɗaya shi ya hana ta karatu a daren jiya ga kuma wani ciwon kai da ya saka ta gaba. Zulaikha ta ce Faculty of medicine ya ke, kuma SEC GEN na SRC hakan ya sa hankalin ta ya dan kwanta ba don komai ba sai don ta na kyautata zaton ba lalle ta kara haɗuwa da shi ba, domin kowa in dai yanda ta faɗa daidai ne ya kamata a ce yanzu Shika ya ke ba nan Samaru ba, duk tunaninta shaf ta manta akwai wasu fannoni a facultyn da su ɗin gaba ɗaya rayuwar su a samaru ne. Haka dai ta lallaɓa ta shiga jarabawar, da ya ke ta safiya ce, karfe 8:30 zuwa 11:30, ko karyawa ba ta samu ta yi ba, yadda ta saba shigar nan na ta cikin hijabi har kasa yau ma hakan ta yi, ba ta zame ko ina ba sai ɗakin jarabawa da ake kira FSLT.2 Dan wuyar jarabawar, ba ita ta fito ba sai da lokacin kare jarabawar ta yi, aka karɓe tana mai takaicin rashin kammala wasu lissafin. Da sanya tafukan kafar ta waje da sarawar da kan ta yayi lokaci daya ne, sanadiyyar rana mai zafi da ke shirin ƙwallewa. Daga jikin ta har garin babu abin da ke mata dadi, don haka kai tsaye ɗakin kwanan dalibai ta nufa ba tare da ta tsaya magana da kowa ba, balle masu mayar da magana kan jarabawar in ban da fargaba da ɓacin rai babu abin da za su kara mata. Da rokan Allah ya mata katangar karfe da haɗuwa da Dee Yusuf ta ke tafe, zuciyar ta na dukan uku uku. Har ta wuce ta gaban Ribadu hall, ta dau hanyar da zai sada ta da Amina Hall, Sai kuma ta sake shawarar biyawa ta cikin social center ta siya abinci domin kuwa ba karamin yunwa ta ke ji ba, kuma yanda ta ke jin kan ta ba za ta iya tabuka komai ba, gashi idan akwai abin da Amatullah ba ta wasa da shi ya na bayan cikin ta. Social center babban matattaran dalibai ne a cikin jami’ar, wanda ke dauke da shaguna iri-iri, wanda ya hada da business center ne, wajan aski, shagon dinki, shagon dinki, wajan kallan dalibai(Cinema), shagon kwalama da makulashe da dai sauran su. Ba ta da takamamman wajan siyan abinci saboda ba ta fiya siya ba dafawa ta ke, dan haka nan ta fara rarraba ido domin neman restaurant daidai kudin ta. Ko da ta bi gaban wani restaurant da ake kira “Frizllers” wanda kaf social center nan ne matattara cin abincin dalibai ma su ji da kan su, tuni gaban ta ya shiga faduwa. Da sauri har ta na tuntube ta wuce restaurant din, dan kuwa yauma kamar kullum cike ya ke da samari da yan mata. Wani wajen siyar da abinci dan gaba da Frizllers din ta tsaya ta siya shinkafa da miya da salad. Hankalinta na kan wayar ta dake fama ringing ta fito daga restaurant din, wayar ta daga ta kara kunnan ta yayinda da ta shiga amsawa. Daidai gaban Frizllers Kamar ance daga kanki, nan su ka yi ido hudu da shi, Sanye cikin kanan kaya, jar riga da bakin wando, tare da ‘yan mata uku sun saka shi tsakiya. Hannun shi na hagu rataye a kugun daya daga cikin su. Idanu ya kafa mata ba ko gizo tuni bugun zuciyar ta ya karu tsabagen firgici, duk yadda ta so ta dake ta kasa hannun ta sai ya ɗau rawa. Ba shiri ta katse wayar da take, ita kan ta ba ta san sanda ta juya ba, restaurant din da ta sayi abincin ta nufa ta na mai jera addu’oi yayinda kanta ke sarawa fiye da da.4 Shigar ta restaurant din kujera ta ja ta zauna. Ganin yadda ta zauna hannun ta rike da kan ta ya sa daya daga cikin yaran wajan ta zo ta ce da ita “Lafiya kuwa?” Ba ta kai ga amsawa ba ta ji an ce ” Ina fa lafiya ta ga katon saurayin da ta mara a tsakiyar mutane…..toh laifi na ne dai har yau ban sani ba fa Mama na…. ” ya karasa yana maida akalar maganar ga Amatullah.2 Baki bude yarinyar ke kallan Amatullah cike da mamakin furucin Dee Yusuf wanda ta ke da yakinin zolaya ce dai irin tashi, ganin yadda Amatullah ta yi tsuru-tsuru da idanu, yayinda tsoro ya ƙara bayyana fuskarta domin kuwa ba ta san ya biyo ta ba. Yanayin da ta gan Amatullah ne ya sanya yarinyar mayar da kallan ta ga Dee Yusuf, wanda kallo daya za ka ma sa ka tabbatar da jin daɗin yanayin da ya jefa Amatullah ciki, domin kuwa murmushi ne kunshe a fuskar shi. Ganin abin ya fi karfin ta sai ta yi gaba abinta ta bar Amatullah da Dee Yusuf da ya sa ta gaba ba tare da ta ƙara ce da su kanzil ba. *** Wasa ta ke da ledar abincin da ke hannun ta, neman hanyar guduwa take don ba ta ƙi ta buɗe idanu ta ganta a kan gadonta ba. Gyaran murya yayi wanda hakan ya sanya ta daga ido ta kalle shi. Ta tsinci kanta ta na mai nazartar fuskar shi a karo na farko, Fari ne amma ba irin sosai din nan ba, ya na da dogan hanci har baka, yawan suman kan shi da wanda ya zagaye fuskar shi ne zai tabbatar ma ka da wadatar sumar da ke tattare da halittar shi. “Kyakkywar fuskar da na mara kenan” Furucin Amatullah a zuci kenan, kamar ya sani ya ce2 STORY CONTINUES BELOW “Ke na ke sauraro? Me na yi da na cancanci mari? Ki fada min Mamana” Kamar an aje dutse “uhum” ba ta iya furtawa ba balle ta bashi amsa, sun kai kusan minti biyar a haka, ita dai ta sunkuyar da kai ta na wasa da ledar hannunta, shi kuma ya tsare ta ido. Tun da ya ke a rayuwar shi be taba ganin yarinyar da ta tsaya ma sa a rai ba kamar wannan da ke zaune gaban shi, ga ta dai da ka gan ta ka ga mai karancin shekaru, amma yanda ta iya duban tsabar idanun shi ta sharara masa mari babu gaira babu dalili shi ne babban abin da ya tsaya ma sa a ran shi. Wai shi Dee Yusuf mace ta mara a cikin Samaru, ba ma jama’ar wajen ba shi kan shi ya na jinjina abin, dan ma in da Allah ya taimake shi ba tare da abokan sa ya ke ba, su ma labari su ka ji daga baya da ya kade har ganyen sa, yanzun ma neman yarinyar da ta mari Dee Yusuf su ke ido rufe.3 Wayar shi da ta fara kara ne ya katse masa tunanin da ya ke. Ganin wanda ke kiran sa ne ya sanya shi sake duban Amatullah tare da fad’in “Wannan uzuri ne babba, amma za mu sake haduwa, lalle na cancanci a min bayanin dalilin da ya sa aka mare ni Mamanaaaa” ya ce yana mai jan kalmar karshe. Da wannan ya juya ya fita yayinda ya shiga amsa wayar ta shi. Sai bayan fitar shi da kusan minti biyar ta iya sakin ajiyar azuciya, a sannan ta lura da irin kallan da jama’ar wajan ke mata, idanun kusan kowa na wajen kanta ya ke. Da saurin ta mike tsaye, ta na mai fatan Allah Kar ya sake hada ta da wannan bawa na shi. Allah kuwa ya amshi addua’ar ta har ta kai hostel babu shi babu alamar shi.7 Shigar ta daki ta yi sa’a babu kowa ciki, daga wacce ta tafi karatu sai wacce ke jarabawa. Bisa gado ta kwanta, gaba daya abuncin ma ya fita kan ta, Dee Yusuf da furunci sa ke mata yawo, tsoro na shigarta a hankali, duk iya tunaninta ta kasa gano mutum ɗaya a dangin ta da zai tsaya mata in zancen zai kai ga hukuma. Tunawa da artabun da aka sha kafin Baban Sasa ya amince da karatunta kaɗai ya sanya ta cikin tashin hankali. Daɗin ƙarawa rikicin nata ba da mace ƴar uwarta ba da namiji, tilawar da ta haddace shine “babu ke babu ɗa namiji, mijinki saifullahi na dawowa daga Rasha zan ɗaura aure ku” karatu ne da duk ta je gaida baban Sasa sai ya biya mata, yanzu kuma sai a ce gata an kore ta daga jamia saboda ta yi faɗa da namiji. “Me ya kai ni fitan karatun dare” tace hawaye na zubo mata sannu a hankali, hakan ya sa yin kuka ma’ishi sannan ta fara tuna asalinta don gaba ɗaya ta sadakar koranta za ayi 2 *** 28th September 1989 Gidan Jamoh babban gida ne a unguwar Amaru cikin birnin Zaria. Gida ne ginin ƙasa wanda ke da sassa daban daban. Sun kasance cikin kason zage-zagi da aka fi sani da mallawa, wainda tarihi ya nuna suna cikin jinsin Zazzagawa uku da ke da gadon sarautan ƙasar Zazzau watau Mallawa, Katsinawa da Barebari. Babba da yaro da ga tsatson gidan Jamoh na da kwale bibbiyu a duka gefen fuskarsu kamar kowane Bamalle. Sanyin iskar damuna ke kaɗawa ƙarfe tara na safiyar Alhamis na ashirin da takwas ga watan Satumba shekara alif ɗari tara da tamanin da tara, Hakan bai hana tsoho Jamoh zama akan kujerarsa ta azara da yake shan hantsi duk safiyar duniya yana mai sauraren radiyo a ƙasar bishiyar da ya yalwata Inuwa a tsakiyar gidan. “Baban Sasa! Baban Sasa!!” yaro ɗan kimanin shekaru takwas ya sheƙo da gudu yana faɗi. “Ja’iri! Sai kace ni ubanka ne, karar min da sunan za ka yi” tsohon ya faɗi cikin sigar wasa. Dariya Yaron yayi yana mai zama akan cinyarsa. “Innarmu ce tace in zo in faɗi maka Goggo Mairo ta sauka an samu yarinya” yace cikin murna yana yi yana wasa da gemun tsohon nan. “Madallah ka ce mun yi mata, dena ja min gemu salon ta ce kai take so ba ni ba” ya karasa yana mai ɗaga Yaron sama ba za ka ce yana da karfin ɗaukan Yaron nan ba in ka kalli furfuran da ya rufe masa fuska. Sashin ɗansa ƙarami a maza ya je don ganin abin da aka haifa, saboda ya san ƙaidar sa ce duk aka haihu da an kimtsa shine mutum na farko da yake fara gani, Hakan aka yi a haihuwa talatin da uku da yaransa maza su ka masa ciki kuwa har na yau. Addu’a yayi mata haɗe da huɗuba tare da raɗa mata suna kamar yadda yake yi a saura, in yayi ba ya faɗi ma kowa sai babban Ɗansa Zubairu. Alhaji Jamoh Bamalle ne Usul, sannan shine cikakken ma’anar maraya, don yana da shekara ɗaya da rabi mahaifiyarsa ta rasu, bai cika shekaru biyu ba Allah ya ma mahaifinsa rasuwa. Ya taso cikin gararanba a tsakar gidan babban gidansu, cikin ikon Allah lokacin da aka zo aka bukaci masarauta su ba da sunayen wainda za su je karatun boko wani kawunsa da ke aiki a fada ya bada sunansa. Hakan ya sanya yayi karatu har ya kammala makarantar Barewa College wanda a lokacin sunansa Kaduna college kafin daga baya ya zama Govt college Zaria kafin daga baya ya koma Barewa college. Tun bayan da ya kammala da shahadar grade II ya samu koyarwa a firamare bai sake komawa aji ba, da albashin sa ya auri matansa uku, da albashin sa ya raini yayansa goma sha shida inda ciki biyar ne mata saura duk maza ne, da Albashin sa ya mallaki filin nan har ya gine in da ya zama musu babban gida a yanzu a nan yaran sa duka goma sha ɗaya ke zaune da iyalinsu. Hajiya Sahura itace uwar gida, yaranta takwas, Zubairu shine babba, sai Idris, sai Hamza, sai Hadiza, Madina, Bilkisu, Yusuf sai autanta Salihu. Hajiya Talatu ce mata ta biyu a gidan ita yaranta shida duka maza, Anas, Dahiru, Yunusa, shuaibu, Mahmuda sai ƙaraminsu Muhammadu. Amarya da yaran ke kira da Goggo Kadarko tun da ta haifi yan biyu Hasana da Husaina Allah ya mata cikawa, haka hajiya Talatu ta haɗa da nata yaran ta rike. Daga Salihu sai yan biyu a tsarin shekarun yaran gidan Hakan ya sanya su ka taso su uku kamar yan uku, yana da shekara goma sha biyar su yan biyu na da sha uku aka tashi auren yan biyu, yayi kuka kamar ransa zai fita saboda shaƙuwa da ke tsakanin su, tun bayan aurensu ya maida hankali a karatun bokonsa don yana ganin shi kaɗai ne zai ɗebe masa kewa. Yayi karatu har matakin digiri a Fannin sadarwa sannan ya samu aiki da radiyo Nijeriya Kaduna kafin yayi aure. Aurensa na cikin auren da aka yi shelarsa a jihar Kaduna saboda duk maabota sauraron radiyo sun san Salihu Jamoh da shirye shiryensa masu ƙayatarwa musamman shirin jakar magori. *** Aurensa da mairo ya samar da karin arziki ta wajen sa don bayan auren ya samu ƙarin girma a wajen aiki, sannan gidan an samu yalwan arziki sannan ita kanta kullum cikin yi ma mutane ihsani take da kaɗan din da ta mallaka. Hakan ya sanya surukan son mairo fiye da sauran matan yayan. Tun ana ƙirga watannin auren har aka fara ƙirga shekaru Mairo ko ɓatan wata ba ta yi ba, nan matan yan uwa Salihu su ka sa mata karan tsana, amma duk sanda su ka jefeta da sharri sai ta maida musu da Alkhairi. Yayin da Allah ya azurta ta da cikin sai su ka fara zunɗenta suna fadin ƙaba ke damunta. Hakan bai sa ta canza musu ba ko ta neme su da sharri kullum dai Alkhairi, babu inda ta ke jin sanyi sai wajen matar Anas mai suna Hama, ita ce ta tsaya mata har ta sauka lafiya sannan ta aika ɗanta Saifullahi ya je ya isar ma kakansa Jamoh albishir ɗin haihuwa. *** Ranar suna aka sanar da sunan jaririya a Amatullah, an yanka rago an ci abinci a wadace an sha kowa yana cikin farin ciki. Rayuwar Amatullah ta kasance cikin gata, haihuwarta ta buɗe ma iyayenta samu yaya don duk bayan shekara biyu sai Goggo mairo ta haihu. Amatullah na da shekara uku ta fara bin yayyinta na gidan zuwa makarantar Allo, tun ba ta fahimta har ta fara ɗaukan karatu. Ko da ta kai shekaru shida aka sanya ta a makarantar islamiyyah kamar sauran yayyinta, gaba ɗaya rayuwarta sai ta zama daga sallan asuba za ta je Allo, ana tashin su karfe bakwai da kwata, nan za su dawo su karya sannan su tafi makarantar boko, su taso karfe ɗaya su ci abincin rana su huta ƙarfe hudu su tafi islamiyyah sai kuma shida, bayan sallan isha’i kuma su yi karatu da dare in da yayyinsu ke musu bitar karatun islamiyyah da Allo. Amatullah hazikace mai saurin fahimtar karatu sannan ba ta da mantuwa Hakan ya sanya da wuya a yi jarrabawa ba ta zo na ɗaya zuwa na uku ba. Da wannan kokarin ta kammala firamare ta shiga sakandire na boko da islamiyyah. Tana da shekara goma sha hudu aka aurar da sa’oi’inta da ke gidan bayan sun kammala hadda izu arba’in, da kyar Baba Jamoh ya amince da cigaban karatun Amatullah Shima bisa Yarjejeniyar ba ta da miji sai Saifullahi a cewar sa tun kafin ta kama nonon uwarta ya ma Saifullahi alkawarin auren Amatullah.5 *** Da taimakon fitar Saifullahi karatu ƙasar waje ya sanya Amatullah kammala karatun sakandire, samun kyakkyawar sakamako ya sanya mahaifinta rokon Baba Jamoh akan barinta zuwa jami’a, da kyar ya amince bisa sharaɗin ko bayan ba shi aka aura Amatullah ga wanin Saifullahi bai yafe ba. Wannan alkawarin Salihu Jamoh yayi shi a gaban dukkan yayyinsa da ita kanta Amatullah da mahaifiyarta. “Ni dai in karanta pharmacy shi ne damuwata, ko wa Baban Sasa ya so ya aura min” tace a ranta tana murnar amincewar kakanta tsoho mai ran ƙarfe mai ikon akan Ahlinsa. Bisa wannan Alkawari ta fara karatun Pharmaceutical science a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, nisa da rashin son zarya ya sanya mahaifinta tura ta hostel cike da yaƙinin za ta kama kanta kuma za ta zo da sakamako mai nagarta. Zazzaɓin da ta ji yana shirin kamata ne ya sanya tunawa da abincin da ta siyo, jiki a sanyaye ta zauna bisa gadon Zulaikha ta ci ta sha ruwa sannan ta haɗiyi paracetamol. A nan gadon bacci yayi awon gaba da ita tana mai karanta Suratul ma’idah a hankali. Bacin tayi kamar jaririya don ba ta san lokaci ya wuce har haka ba sai da Zulaikha ta shigo da hayaniyar ta, Hakan ya zama silar tashinta a bacci a nan ne ta gano ƙarfe huɗu har da rabi babu sallan azahar balle la’asar. “Yanzu na ga mutuminki, taɓ Amatullah sai yanzu na ga ƙoƙarinki wannan gabjejen saurayin kika mara? Wallahi yanzu na ganshi ya raka budurwarsa chapel, shi kuwa banda ɓatan basira duk yan mata musulmai ya rasa abin so sai arniya, kuma yanda yake kyakkyawar nan wallahi na san matanmu na sonshi ko da yake saboda ya dinga taɓa su ne, kin ga rikon da ya mata” haka ta ke faɗi babu wani waƙafi, zuru Amatullah tayi mata da ido, babu abin da take hangowa sai irin rikon da ta ga yayi ma yarinyar ɗazu da kuma tsareta da ido da yayi. “ALLAHUMMAK FINIHIM BIMA SHI’ITA” tace a hankali tana mai saukowa daga kan gado. “Waye abokin gaban da kike karanto ma addu’a ne Amatullah?” Zulaikha ta tambaya cikin mamaki. “Mutumin da kika hango mana, in ya nemi ɗaukan fansa ta wani fannin ya kike so inyi?” nan take Zulaikha ta shiga tunani kwatankwacin na Amatullah, da yake yanda take da surutu haka take da ruɗu ya sanya ta rungume ƙawarta gam cikin hawaye, Amatullah bata hana ta ba, kwarin guiwa ta samu ganin ko ba wanda ya tsaya mata ga Zulaikha nan kamar ita ɗin ta isa ta hana abin da zai iya faruwa ne. “Zauna ki ji abin da na tuna” ta ce tana jan hannun Amatullah. Sun zauna a gefen gado Amatullah dai ba abin da ta ke iya taɓukawa sai sauraro. “Kinga wallahi gara da kika mare shi, karkari in mu ka ga ya takura ki mu ce rungumar ki yayi dalilin marin kenan, Kinga halinsa ne taɓa mace babu wanda zai musa. Amma kafin nan ina da Niƙabi kin sani kawai ki koma niqabite abin ki” tace cikin tabbatar da iya gaskiyarta ta faɗi, murmushi Amatullah tayi kana tace. “Ai in mu ya zame mana oppressor, mu kuma muna da wanda ke bashi aron numfashi, ina addu’ar nan da ake ma shugaba mai danniya da zalunci? Yana nan cikin hisnul Muslim kin tuna? Toh da shi kawai za mu haɗa shi, aka yi ma miji da lakcara ma balle wani sec gen” Amatullah ta faɗi duk da a cikin zuciyar ta gaba ɗaya tsoro ne amma ɗauriya irin tata ya sanya ba za a taɓa gane ainihin abin da ke damunta ba. Da wannan ƙarfin gwuiwa ta tashi tayo alwala tana mai tuna lokacin da mijin goggonta Husaina ya sa ta gaba da duka, ba za ta taɓa manta lokacin da mahaifiyarta ke karanto ma ta addu’ar ba, tace in ta rike wannan ko kallon banza bai isa ya mata ba matukar ita ɗin ma ba cutar da shi take ba, Allah cikin ikonsa shi ke nan kuma zance duka ya bi tarihi. Sannan ita din ma farko shigowarta ABU, suna ganiyar rajista, wani ya dinga kwala su, sai ya shanya su a rana ba tare da ya sa musu hannu a takardar da su ke so ya sa ba. Haka zai ajiye su har yamma in ya fito sai yace “This is why An Abusite is naturally ahead” ya sa kansa yayi gaba. Da yayi masu na kwana uku kawai a na huɗu tana zama ta karanto addu’ar, kamar wanda aka hankaɗo ya fito ya kalle su ɗaya bayan ɗaya, sai ya yafito ta da hannu ya sanya mata hannu ta yi gaba abin ta. Tun daga ranar ta ƙara imani da Addu’a sannan ta sa a ranta ba ta da wani wayau ko dabara sama da addu’a. Da haka ta yo Alwala kana ta gabatar da sallan azahar da la’asar, Zulaikha da ke cikin yanayi na hutu kuma ta ɗaura musu abinci. *** A haka lokaci ya dinga shuɗewa, Amatullah ba ta gaji da addu’a akan Dee Yusuf ba, haka ta ke karanta hasbunallahu wa ni’imal wakeel 450 kawai da niyyar Allah ya makantar da Dee Yusuf akan ganinta. Yaa Mujibu kuwa ya amsa, haka ta ke fita jarrabawa ta dawo ta je tutorials ta dawo ba tare da sun sake karo ba, a hankali ta ke samun natsuwa, tare da imanin ba zai sake ganinta ba balle ya bi ta da wani sharri. Sun kammala jarrabawa cikin ikon Allah ya rage saura General courses da ake yi bayan sati ɗaya ko biyu da kammala jarrabawar makaranta gaba ɗaya. Da murna ta koma gida inda ta ga innarta abin ƙaunarta da kannenta da saura ahlin gidansu. Dawowarta ta iske Baban Sasa cikin hali na jinya, binciken da likitoci su ka yi ne ya tsoratar da iyalin saboda jin yadda aka lissafo musu abin da cutar ke bukata. Likitoci sun tabbatar da ƙodarsa ɗaya ta mace ɗayar kuma saura kiris. Zafin ciwo bai hana shi magana da ɗaukan hukunci akan iyalinsa ba, tun dawowar Amatullah yake faɗin a kira Saifullahi ya dawo ya cika alkawarin da ya ɗauka shekaru goma sha tara da su ka wuce. “Baba kar ka damu, kanan tare da mu nan da shekaru goma ko fiye, ciwo ba mutuwa bane in dai za a dinga dialysis din da su ka rubuta, sannan ka dage da magunguna insha Allah zaka samu sauki” Amatullah ke faɗin haka bayan ya gama tuna mata alkawari yayi ma Saifullahi tun ba sa mata nono a baki ba. Da haka lokacin jarrabawar ya matso ta kwashi jiki ta koma makaranta, ranar da su ka yi Gens 103, sun fito suna maganar mamakin da aka basu, Littafin (novel) din da su ka fi ji ma tsoro gaba ɗaya tambaya ɗaya ne ya fito a ciki. Tafe su ke za su shiga kasuwar Samaru Hakan ya sanya bin hanyar gate din da yake kusa da kasuwar watau North gate. Suna Tafe suna hirarsu daidai ofishin SRS taji ana faɗin “Salamun Alaikum Mamanaaaa” iya kaɗuwa ta kaɗu, ta fara raba idanu, sai gashi gabansu sanye cikin bakin yadi baki ɗinki jamfa. Abin ku da farar fata ba karamin kyau da kwarjini yayi ba. Ƙoƙarin tsayawa yayi gaban Amatullah, wacce ala’mun tsoro ya bayyana a fuskarta, ɗaya daga cikin abokan tafiyarta ce ta amsa ma sa da “wa’alaikum salam” Ya na mai murmushi gare su ya furta “Sannun ku, ko za ku iya bani aron ƙawar nan ta ku? Ina bin ta bashi ne”5 STORY CONTINUES BELOW Murmushi su ka mayar ma sa, dan kuwa in dai farin jini da kwarjini gurin ‘yan mata ne Allah ya bashi, bare kuma daliban aji ɗaya, a ce kamar Dee Yusuf ne ke kula su har ya na neman izinin su, duk da dai ba su ɗin ya ke so yayi magana da ba. Ita kuwa Zulaikha idanun ta kan Amatullah, wacce ta ke ma ta magiya ta ido, na dan Allah kada ta tafi ta bar ta, itama din cikin ba da hakuri Zulaikha ta furta “Amatullah bari mu dan ba ku wuri….’ Irin wannan kallon na ya za ki min haka? Amatullah ke yiwa Zulaikha, amma ina tana ji tana gani haka su ka yi gaba, sai ga ta daga ita sai shi. “Amatullah!!! ” Dee Yusuf ne ya maimata sunan a hankali wanda hakan ya sanya ta dawo da kallon ta gare shi. Takaicin bashin da ta ji ya ce ya na bin ta ne ya sa gaba ɗaya ta ji tsoran shi da take ji ya gushe. Ta na mai galla ma sa harara cike da tsiwa ta ce3 “Bashi kuma? Malam yaushe na ci bashin ka? Ka ga fa ka takura min! Ka ishe ni!! Wai me ka ke so da ni ne fisabilillahi!!! Wannan masifa har ina!!!!”2 Tun daga kwakwalwar shi har zuwa yatsun kafar shi haka muryar Amatullah ta shige shi, shigar ma ta bazata, yau ne karo na farko da ta buɗi baki ta ma sa magana. Ita a nata tsiwa da rashin kunya ta ke ma sa ko ta samu ya rabu da ita, nan kuwa ba ta san hakan ba karamin daure shi ta yi ba. “Shin wannan wata irin yarinya ce haka ta ke rikita tunani na…..?” Furincin da ya ke cikin ran sa kenan yayinda ya sanya hannayen sa biyu cikin aljihun wandon shi. “Malam da kai na ke magana fa, bashin me na ci gun ka?” “Ba Malam ba, sunana Dee Yusuf…..” “Ba sunan ka na tambaya ba, bashin me na ci ma ka?” Yadda ta mayar ma sa da tsiwa ne ya sanya bai san sanda ya dara ba, kana ya ce “Bashin marin da ki ka min” ya ƙarasa yana mai dariya ciki-ciki.2 Jin batun mari sai kuma jikin ta yayi sanyi, ta dan rage murya tare da fad’in “Hakuri ka ke so na ba ka? Allah ya ba ka hakuri, dan Allah ka fita harka ta” “Naaaah! ba zai yiyu ba Mama naah, da ace ba da hakuri kadai ya na magani da ba a kirkiri doka da oda ba, da yan sanda da koto ma ba su da amfani, da an toye hakkin dan adam da yawa, kin shiga hakkina kuma lalle sai kin biya”4 Cewar Dee Yusuf ya na mai gyara tsayuwa. Gaban Amatullah ba karamin faduwa yayi ba jin batun na shi. A hankali ta furta “Yanzu me ka ke so? Ta ya zan biya hakkin na ka?Yan sanda za ka kira min ko kuwa kotun za ka kai ni saboda na mare ka?” Idanun shi na mata dariyar kyeta, cikin zolaya ya ya furta ” Wanne ne zabin ki Maama naah?” Daga ido ta yi ta ga su Zulaikha sun yi mata nisa kwarai, cike da zafin barin ta da Dee Yusuf da Zulaikha ta yi duk da ta fi kowa sanin abin da ya haɗa su, da irin tsoronsa da ta ke ji, ta yi kwafa tana mai sake kai kallon ta ga gabas da yamma, kudu da arewa, ta ga babu wanda ke kallan su bare a san wainar da su ke toyawa. Bai ankara ba sai gani yayi ta dan matso gaban shi, idanun ta rufe ta furta ” Ka rufa min asiri ka rama marin da na ma ka…….” Fuskar ta ya bi da kallo, tun daga gashin giran ta mai cika, zuwa murfin idanun ta da ke dauke da zara zaran gashin idanu, ba wani dogan hanci gare ta ba, Amma bakin nan mai tsiwa dan tsut ya ke kamar na yar tsana, gashi irin wannan kalar ne da ake kira pink lips, dan kyan fatar ta har sheki ta ke ga alamun zanen ta na mallawa da ya fito a gefen fuskarta yana mai ƙara ƙawata fuskar nata, asalin black beauty ita ce Amatullah…..kyau kenan tuni ya shagala da kallon ta, ya na tunanin shin idan har ta na da wannan kyawun fuskar, Allah kadai ya san baiwar da ta ke rufewa kullum cikin hijabi, dan kuwa yanzun ma sanye ta ke cikin farin hijabi. Abun da dai ya tabbatar shi ne irin matan nan ce wanda ba su cika kiba ba. Jin shiru ya sanya ta bude idanun na ta, nan su ka hada ido, karfin idanun sa da yanda ya ke kallan ta ya sanya ta jan baya da sauri…. Kama shi da ta yi ya na kallon ta ya sanya shi gyaran murya, sannan ya ce “Shin ki na tunanin zan iya daga hannu akan ɗiya mace? Tur Allah ya tsare ni! Kai zafin wannan batu naki ai ma yafi marin da ki ka min Mama nah!!” har yanzu be dai na kallan ta ba. Ji ta yi kamar ta kurma ihu dan kuwa ta gaji da shi, ta gaji da tsayuwa da shi, ta gaji da magana da shi. A fusace ta idanun ta cike da kwalla ta furta ” Ni ba Maman ka ba ce ba!!!! Please don Allah ka rufa min asiri ka rabu da ni, rayuwa ta da ta sauran dalibai ba daya ba ne, wallahi Mahaifina ya ji wannan labarin na kaɗe har hanji na, don Allah…”5 “Shhhh” Ya katseta ta hanyar dora hannun sa bisa leban sa. Ya ƙara da ” Ki yi hakuri, tun da ki ka mare ni Allah ya gani ba zan iya hakura hakan nan ba, Abu mafi sauki shi ne ki zama kawata… ” Baya ta ja da sauri ta na mai faɗin “Auzubillahi minal shaidanir rajeem!!!!!!”2 Shi ma ɗin baya ya ja, yana mai kallon gefan shi hagu da dama tare da faɗin “Waiyazubillah!!!! Yaushe shaidan ya zo nan? Da fatan dai ba ni ne shaidanin na ki ba ko Mama nah?” Yayi maganar ne cikin zolaya, har sai da ita kan ta ta dan ji kunya. Shiru ta yi na wasu mintuna kafin ta furta “Babu wata alaƙa ta ƙawance ko abota tsakanin mace da namiji, ina mai sake ba ka hakuri bisa marin ka da na yi, dan Allah ka fita harka ta….” Ta na gama fad’in haka ta juya ta tafi ba tare da ta jira amsar da zai bata ba. Bin ta yayi da kallo fuskar shi cike da murmushi, bai daina kallonta ba har sai da ta kure masa. Nan ya sha alwashin kulla dangantaka tsakanin shi da Amatullah, ko ta na so ko ba ta so, ya daukarwa kan sa alkawari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *