TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 10

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 10

Hawaye bai daina zuba daga idanun Baban Sasa ba yayin da ya ke duban Saifullahi, cikin dashassheyiyar murya ya furta+ “Saifullahi har ka iya buɗar baki ka furta saki ga Amatullah? Ashe za ka iya sakin Amatullah?” “Kukan nan na ka shi ke ɗaga mana hankali Baba, dan Allah ka sawa zuciyar ka salama ɗan yau ba a biye masa, sai ya kara ma ka ciwo” Cewar Baba Zubairu cikin rarrashi.4 “Ni kuwa na ke iya masa! Kai waye nan! Hafiz! Hafiz! ya ka nan!” Baba Anas ne ya shiga kwallawa Hafiz Kira, in da ya shigo da saurin sa dama nan soro yayi laɓe ya na jin komai.2 “Je ka kira min uwar yaron nan!” Ya fada ya na mai nuna Saifullahi da ɗan yatsa. Gaban Saifullahi ne yayi mummunar faɗuwa ganin Hafiz ya fita da sauri, cikin sanyin murya ya ce4 “Dan Allah Baba….” “Dakata! Ba na so na sake jin ka tanka a nan idan har ba ni na ba ka izini ba!” Jin haka Saifullahi ya sunkyar da kai. Amatullah kuwa burin ta a sallame ta shiga gida ta mike kafa ko ta sami saukin zugin da ciwon da ya ke mata. Jim kaɗan sai ga Hajiya ta shigo da da sallamar ta. Gani yanda aka taru daki, fuskar Baban Sasa fal da hawaye, kuma ciki har da Saifullahi da Amatullah ta sha jinin jikin ta. Bai bari ta iya gaisar da Baban Anas na mai duban Saifullahi ya ce2 “Zan ma ka tambaya ɗaya, kuma ka bani amsa cikakkiya, saki nawa ka yiwa yarinyar nan?” Daf gaban Hajiya ya yanke ya fadi, ta na mai dafe kirji ta furta “Saki?” Saifullahi na mai sin da kai ya ce “Saki daya na mata Ba…..!”5 “Wallahi saki uku ya min……!”2 Amatullah ta yi saurin katse shi. Kallan ta ya ke kallon da ta kasa gane manufar shi. Kai ta kawar gefe cikin halin ko in kula. “Ina ga zai fi a bar shi a sakin ɗaya tun da shi yaro ɗaya ya ce yayi, kuma shi ne gaba da ita”8 Baba Mahmuda ya ara ya yafa ba tare da ya san dalilin da ta sa Baba Anas ya ke tambaya ne. Baba Anas na mai gyaran murya ya ce “Toh sai fa ku shaida, bisa ga alkawarin da na dauka, ni Anas na saki mata ta…….!”2 “Inna lillaahi wa inna ilaihi ilaihi rajiun!” Duka dakin su ka hau salati, wanda haka bai hana shi karasawa ba sai da ya dire da “Saki daya kamar yanda Saifullahi ya ce ya saki Amatullah saki daya!”3 “Inna lillaahi wa inna ilaihi rajiun” Amatullah ce ke na ta salatin akan abu biyu, na farko sakin Hajiya, na biyu kuwa Jin Baba Anas ya yarda saki ɗaya Saifullahi ya mata ba uku ba.2 Kukan Hajiya ne ya garwaye ɗaki, in da idanun Saifullahi su ka kada su ka yi jajur. “Haba mana Anas! Ya za ka biyewa ɗan yau ka yi wannan danyen aika aika! Ya mu na so mu toshe wani ramin za ka bude wani?!!!!” Cewar Baba Zubairu cikin faɗa faɗa. Baba Salihu mahaifin Amatullah kuwa cewa yayi “Assha! Assha! Assha! Malam Anas ba ka kyauta ba! Saki kuma? Ana zaune shekara da shekaru? Yanzu yaran nan za su sa ka furta saki hakan nan bakatatatan!” “Ban yi dana sani ba! Wallahi da ya amsa ukun ya mata a yau sai na sau tashi uwar saki uku!”2 Cewar Baba Anas in da maganar ta shi ta soki Hajiya da har lokacin kuka ta ke, da Saifullahi wanda zuciyar shi ke masa Kuna. Baba Sasa wanda kiris ya rage ya hadiyi zuciya dan takaici ya ce STORY CONTINUES BELOW “Anas ashe har yanzu akwai sauran ka a rayuwa! Ka dubi tsabar ido na! A gaba na ka furtawa mai dakin ka kalmar saki?”2 Cike da ladabi Baba Anas ya sunkyar da kai ba tare da ya tankaba. “Toh ina mai ba ka umarni ka mayar da ita ɗakin ta yanzun nan!” Baba Anas na mai dukar da kai, har ran sa ba haka ya so ba ya ce “Na mayar da ita Baba, na mayar da ita, Allah ya huci zuciyar ka” Cikin dakiya da umarni Baban Sasa ya dubi Saifullahi ya ce “Kai ma tun da saki daya ka mata, ina so ka mayar da ita a take kuma ……”4 Kukan da Amatullah ta saki ne ya dakatar da Baban Sasa, cikin kunar zuciya jin za a mayar da ita gidan Saifullahi ta ce “Ka duba girman Allah Baban Sasa na tuba, ka yafe min, tun da na ke ban taba ma ka musu ba, wallahi babu aure tsakani na da ya Saifullahi, wallahi saki uku ya min…..”4 Nan ta mayar da kallan ta zuwa ga Baban ta, ba ta gushe ba ta cigaba da fad’in “Baba ko ba uku ya min ba, ai aure ya haramta tsakanin mu! Ai ba a zaman aure da zargi! Wallahi cewa yayi ba ɗan shi ba ne,! Ya kira ni mazinaciya! Na rantse da Allan da ya halicce ni ban taba kusantar zina ba bare na kai ga aikatawa! Tun ina budurwa ballanta sanda igiyar aure ke kaina! Da ku mayar da ni gidan Saifullahi gwara kun kai ni kushewata….!”9 Cike da mamakin kiyayyar da ta ke masa Saifullahi ke kallon ta. Shi kuwa Baban Sasa mamakin yau Amatullah ce ke masa musu haka ya ke yi. In da nauyi da taikaicin Saifullahi ya kara mamaye Baba Anas. Mahaifin Amatullah ne ya runtse idanu ya ce “Yi shiru Amatullah, babu wanda zai kai ki kushewar ki, auren Saifullahi ne daga yau kin gama shi da izinin Allah, na san Baba zai mi ki adalci”9 Baban Sasa wanda kalaman Baba Salihu na karshe ne su ka ɗaure shi da jijiyoyin sa, duk da kuwa ya ga baƙin Baba Salihu, cikin danne bacin rai ya ce7 “Tashi ki shiga ciki, zuwa gobe za mu yanke hukunci” Da kyar ta ita tashi, in da ta karbi Emjay daga hannun Baba Mahmuda ta shige ciki ta na takawa da kyar. Hajiya ma Baban Sasa ne ya sallame ta, ta na kukan takaici ta shige gida. Ɗakin kaf idan aka dauke Baba Anas babu wanda bai ga bakin Baba Salihu mahaifin Amatullah ba, ba dan komai ba sai dan furucin da ya yi yana mai kare Amatullah, a na su ya nuna san diyar shi karara bai yi kara ba. Baban Sasa wanda ya fi kowa jin zafin Baba Salihu ne ya ce8 “Toh kai Saifullahi ka dai ji abin da yarinya ta ce, ka kuma ji hukuncin da uban ta ya yanke, ba ka kyauta min ba, duk yanda na so na haɗa wannan zumuncin, a yau an ruguza shi, dan haka sai ka sa a ran ka aure tsakanin ka da Amatullah ya kare…..”9 Wani irin yanayi mai kama da tashin hankali da bakin ciki na babu gaira babu dalili ne ya lullube shi, a da yayi zaton rabuwa da Amatullah zai zama tamkar an ɗauke masa dutse mai nauyi daga kan kirjin sa, ga mamakin sa sai gashi ya ji sabanin haka4 “Baban Sasa a duba ……”2 “Ka yiwa mutane shiru!” Baba Zubairu ya dakatar da shi. Baban Sasa bai gushe ba ya cigaba da faɗin “Bayan wannan danyan aikin da ka aikata ga yar uwar ka jinin ka, ka sani wasi wasi shin za ka iya ruke gidan ka kuwa? Wannan auren na ka da za a yi nan da wata biyu shin ba wani zanin za ka kwance mana a kasuwa ba?” Cikin kaduwa bai san sanda ya furta “Na yi kuskure Baban Sasa, a gafarce ni kar ka hana ni auren nan!” “Aure babu mai hana ka, mu ɗin ba kanana mutane ba ne ko sakarkaru kamar ka! Duk abin da ya faru har da laifin mu, da mu ka yi sake mu ka bari ka bar gaban mu, ka tafi can uwa duniya ka ci karen ka ba babbaka, da ka na gaban mu duk abubun nan da su ka faru da ba su faru ba! Wancan dakuna biyu na kusa da bangaran mahaifiyar ka, in da ta ke kiwon kaji nan na ke so ka gyara ka saka matar ta ka ciki”10 STORY CONTINUES BELOW “Allahumma ajirni fi masibati!” Cewar Saifullahi ya na mai goge zufa. Ya kara da “Afuwa Baban Sasa, wallahi wancan gidan kiris ya rage a gama gyarawa…..” “Ba dai gida na ba ne? Na karɓe kaya na! Haka wanda tsohuwar mata ke ciki a da, kudin da ka kashe wajan gyara ka lissafa min zan biya ka in ya so ka gyara dakunan da shi. Yanda iyayen ka ke zaune cikin gidan nan haka kai ma za ka zauna da mu!”8 Baban Sasa ya karasa maganar cikin jaddadawa. Shi kuwa tunanin yanda za a yi mace kamar Ayush yar gayu diyar masu kudi ya iya zama gidan nan na su babban damuwarsa. Wani Sabon zufa ne ya sake karyo masa, bai san sanda ya ya ja rigar sa ya shiga gogewa da shi ba. Babu wanda ya kula shi, a haka suka watse taro zuciyar kowa babu daɗi. *** Cikin wani irin yanayi Amatullah ta shiga ɗakin mahaifiyarta wanda Hafiz ya gama feshe musu mummunar labarin sakin Amatullah. Tafiyar ta Goggo Mairo ke kallo cike da tsusayawa, so take ta rungume ƴarta ta lallashe ta amma kawaicin da aka tayar da ita ana ma ƴan fari ya sa ba za ta iya hakan ba.2 Siddiƙa ce ta tashi ta amshi Emjay a hannun yayarta, kallon yaron take cike da ƙauna da soyayya. “idanunki kenan? Shi kenan son miji da boko su rufe miki ido, ko yawon Arba’in ki gagara yi” Goggo ta ɓige da faɗa ba tare da nuna ta san wani abin ya faru ba. Murmushi Amatullah ta yi don ta daɗe da sanin salon soyayyar Goggo gareta kenan yi mata faɗa da basar da ita. “Goggo yanzu ai komi ya zo ƙarshe, zan zauna nan babu mai hana mini zuwa ganinki” tace cikin danne kukan da ke neman zuwa mata. Sai da idon ta ya sauka akan Goggo sannan ta ji ɗacin sakin da aka mata. Tsawon zaman ta a gidansu babu ƴa macen da ta taɓa yin aure ta fito a dalilin saki, sai gashi ta zama farau a gidan.2 “Assalamu Alaikum! Ina Amatullah ɗin take” Hajiya Zainab matar Baba Hamza da yaran gidan ke kira da Mama ce ta shigo cike da tashin hankali. Rungume Amatullah ta yi tsam cike da hawaye ta ce “Bamu kyauta miki ba Amatullah, wallahi bamu kyauta ba, muna mata muka shashantar da ke a lokacin da kika fi buƙatar mu, kaico!” tace tana share hawaye da gefen zanenta. “Yanzu Babansu ke faɗa min, sakin bai min zafi ba kamar ɗinkinta da aka ce sai da aka sabonta Mairo ki duba ko sabo ya mutum ke yi balle a ce sai an kankare wajen kafin nan fa” tace tana magana cikin tausayawa da jinkai ga Amatullah. Zama su ka yi nan Amatullah kamar wacce aka buɗe ma baki ta shiga faɗin abubuwan da ta fuskanta na cin kashi a gidan Saifullah daga lokacin da ya ce ta je a cire cikin. “Kin ga ni ba, barewa zai yi gudu ne ɗansa yai rarrafe, ai duk abin da ya fito daga tsatson Sadiya zai aikata fin haka don an samu ma Baba Anas na ɗan sirka su da halin kwarai” Mama ta faɗi cikin takaici. Duk wanda ke gidan ya san yar tsamar da ke tsakanin Hajiya da Mama. Tare a ka yi aurensu kasancewar mazajensu sa’annin juna ne, Mama yar gidan matawallen Zazzau ce ta wancan lokacin saboda haka garanta da jerenta ya sha bambam da na Hajiya, ba’a shafe shekara ba hajiya ta siyar da nata tas, ta sa irin na mama hatta kala ɗaya, bayan sun haifi yaya uku Matawalle ya biya ma Baba Hamza da Mama aikin haji su ka je su ka dawo, tun kafin su dawo Hajiya ta sa yaranta su koma kiranta Hajiya ba innarmu da suke cewa ba.4 Kasancewar Mama ta iya faɗin gaskiya ya sa mafi yawan matan gidan ke tare da Hajiya a ƙulla sharri a kwance a alkhairi. Shekara na zagayowa Hajiya ta siyar da gidan gadon ta ta biya kujerar haji itama ta dawo liƙe da haƙorinta biyu a Saman dasashi. Bayan auren Baba Salihu da Goggo Mairo da irin ladabin da take ma surukanta da kula da su da ya sanya su ka so ta fiye da saura, duk matan gidan sun tsane ta in ka cire tsirarunsu kamar su Mama. Ita kuma mama ba ta girkin gaba ɗaya, bata wani shiga taron facaloli hakan ya san ba kasafai ake ganin ta cikinsu ba. Ita ce kaɗai sasanta ke kewaye a gefe, duk da ta aurar da duk yaranta mata hakan bai sa ta nema a cikin gida ba.2 “Kinga Sasarmu za ki koma, duk mai son ganinki ya biyo ki, sabon jego za mu fara” tace tana mai ɗaukan Emjay ta fice don ta san Amatullah na da bukatar ganawa da iyayenta. Sosai Goggo Mairo ta ji sanyi a ranta, don tun da Hafiz ya faɗi mata take tunanin yanda za ta yi, duk da a lokacin ta sadakar za ta zaƙe ta kula da ƴarta. Bayan shigowar Baba Salihu ya iske su jigum jigum kamar ma su makoki ne Goggo kefaɗi masa yanda su ka yi da Mama. “Ke ba za ki iya kula da ƴar ki bane Maryam” ya tambaya yana mai tsare ta da ido.2 Sunkuyar da kai tayi tace “Ka dai san zuciyar Hajiya Zainab mai kyau ce, ina laifi ta fitar da ni tsaka mai wuya. Yar fari ce fa Babansu” ta ƙarasa tana rausayar da kai gefe. “ƴar fari ko? Sannu mai ƴar fari, al’adar da ta sa kika kasa gane ukubar da ƴar ki ke ciki, ba damuwa kije Amatullah, amma ko kallon banza ta miki ki dawo kina da ɗakin uba, Nima zan maida hankali mu koma ginina, na gaji da wannan koma bayan gidan gandun nan” yace yana jan tsaki.8 Tare duk su ka ci abinci kafin saddika ta raka ta sashin Mama, inda su ka iske ta ware mata ɗaki ɗaya, ta sa ma ɗakin rushi kamshi na tashi daga ɗakin, ga makewayi maƙale da ɗakin. “InshaAllah gobe mai hidimar ki za ta iso daga gidanmu tun da ba zan iya wahalar ɗaura ruwa” mama tace cike da ƙauna. Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Amatullah, jin kaunar mama na ratsa take, nan ta tabbatar lallai ko me ɗan Adam ke yi yana da dalili. Ta san dai Mama bata nan aka yi rikicin auren su amma da ta dawo ko sau ɗaya bata taka gidansu ba. Kenan da ta ɗauki zafi da ta sha kunya. *** Jumma’a na zuwa Baba Anas da kanshi ya tuƙa ta zuwa zana test ɗin da za su yi, ta matsu ta ga Mimi ko don ta gode mata, lokacin da mahaifinta ke faɗa mata ƙoƙarin da Mimi ta yi ba ƙaramin jinjinawa soyayyarta da amanarta ta yi ba.2 “Sai a ce Ahlil Kitaab ba masoya bane” ta faɗi a ranta, duk da ta san ba za ka saki ɗan uwanka musulmi ka riƙe su ba amma tabbas annabi ya zauna da su cikin zama na amana da jin ƙai, tana mamakin musulmi mai taƙamar koyi da karantarwar Manzon tsira SAW amma ya zama mai rashin kyautata mu’amala da wainda ba musulmi ba.2 Tara da minti ashirin su ka isa Faculty of pharmaceutical sciences inda za su yi test ɗin da ƙarfe goma.“Nagode Baba Allah ya ƙara girma da ɗaukaka” tace cikin jin nauyi da farin ciki. “zan jira ki kammala sai mu wuce inshaAllah, Allah ya bada sa’a” yace mata yayin da take ficewa da ga motar. Tun bayan hargitsin sakin ta wani girmansa da ƙaunarsa ya ƙaru a zuciyar ta. Tabbas Baba Anas ya kasance cikin mutane ƙalilan masu ƙin nasu su so gaskiya, sannan ya kasance mutum mai riƙo da igiyar zumunta, har abada ba za ta daina gode ma Allah da ya yi Baba Anas ya kasance kaka ga gudan jinin ta. Rungume Mimi ta yi tsam da su ka haɗu har wasu yan ajin na masu tsiyan kwana ɗaya kawai da ba su haɗu ba. Dariya kawai su ka yi amma ita Mimi kanta ta hango soyayya da kaunar ta mai matsanancin yawa a idanun Amatullah. Hannun ta taja su ka zauna a kujera, “Na gode Mimi, Ubangiji Allah ya baki Alkhairin duniya da lahira” Amatullah ta faɗi cikin nuna alamun ƙarancin kalaman da za su bayyana godiyarta. Amma tun ranar ta ke ma Mimi addu’ar jinkai da samun rabon imani. “Common Maman Emjay, what are friends for” ta faɗi mata cike da ƙauna. A takaice Amatullah ta faɗi mata halin da ake ciki wanda hakan ba ƙaramin faranta ran Mimi yayi ba. Daga nan su ka duƙufa bitar karatu, har zuwa shigowar malamin. Ba za su ce ya musu sauƙi amma kam sun ji dadin sa sosai, don Allah ya basu sa’ar amsa duka don haka sun fito suna gode ma Allah. “Abuja zan je mid semester tare da Dee. In na ce in je Yola yanzu wahala zan yi” Mimi ta ce mata sa’ilin da su ke sallama. “Allah ya kaiku lafiya, ki masa godiya don Allah” tace cikin sanyin jiki. “Ki sani fa maman Emjay, babu wanda zai so ki sama da ke kan ki, sannan babu wanda zai wahala in kika yi sakaci da kanki sama da ke kanki. Duniya wani na tayaka son ka ne, sannan waninka iyaka ya yi imagining pains ɗin da kake ciki amma kai ke da wahala. Use this break wisely, breakups should not crash us, they are meant to make us stronger” Mimi ta ce mata tana riƙe da hannunta. Tare su ka fito Facultyn, har zuwa inda Baba Anas ya ke jiranta, nan Mimi ta gaida shi cike da ladabi suka yi sallama su ka wuce. Abuja zan je mid semester tare da Dee. In na ce in je Yola yanzu wahala zan yi” Maganar da ke ta shawagi cikin zuciyar ta kenan.2 ‘Shin bayan dangantakar jini akwai dangantakar zuci tsakanin Dee da Mimi ne? Kamar dai akwai, toh idan ma akwai ni tawa a wa? Ko ba komai ai addini ya riga yayi tazara a tsakanin mu.. .. ‘ Da wannan muhawarar cikin ran ta su ka isa gida. Godiya ta yiwa Baba Anas sannan ta shiga ta gaida Baban Sasa wanda har lokacin ya na da burin komawar ta gidan Saifullahi. Gwaggo kuwa gaisuwa ke haɗa ta da Amatullah, da ta gaishe ta ɓangaran uwar jinyarta ta ke wucewa.13 Ba ƙaramin kula da gyara ta ke samu wajan Mama ba, duk ta na ji a jikin ta dan kuwa in dai wajen gyara ne Mama ba ta tausaya mata. Yau ɗin ma gaishe da Gwaggo ta yi in da ta aje mata Emjay kafin ta wuce wajen Mama. Ferfesun naman rago mai romo da kunun gyada Mama ta ajiye mata, Sai da ta tabbatar ta ci da shanye roman tas sannan ta ce maza ta shirya ta zo ta zauna ruwa mai dan zafi da ta tanadar mata domin a samu ɗinkin ya fara haɗe kan sa. Saifullahi a na shi bangaran tun bayan da Amatullah bar gidan sa gaba ɗaya gidan ya daina masa daɗi, wani sa’in ma kukan Emjay har gizo ya ke masa a kunne.6 Tsananin yanda ya ke kewar su ya sanya ya ke Allah Allah ranar auren sa da Ayush ya zo, kila idan ya ga masoyiyar ta shi kusa da shi ya manta da batun Amatullah. Toh amma sharaɗin da Baban Sasa ya yanke ba ƙaramin damuwa ya ƙara masa ba, kullum da tunanin yanda zai bulluwa lamarin ya ke kwana ya ke tashi har dai ya yanke hukuncin tunkarar Ayush da maganar a yi ta takare ko zai sami sauki cikin ran sa. Sati biyu kenan da yanke ɗanyen hukuncin dole ya ajiye ta a gidan wanda yayi daidai da saura sati shida ɗaurin auren su. Shiryawa yayi asubar fari ya nufi hanyar Kano. Kallo ɗaya za a gano tsananin damuwar da ya ke ciki, duk yanda ya so ya ɓullo ma Ayush da zancen ya kasa ga bikin sai matsowa yake yi. Kamar ko yaushe tarbo ya samu cike da maƙulashe, Ayush ta cika shi da kwalliyan ta mai rikita shi, ga ƙamshin da ke fita daga jikinta na ƙara narkashi duk da ba su yi tasirin cire masa firgicin da ke ransa ba.Hira su ke jefi – jefi yana mai kara bayyana mata sirrin zuciyar sa da kuma tarin burikan da yake da na rayuwar auren su. Sai da ya gama samun ta, ya tabbatar da ta gama natsuwa da Kalamansa haɗe da yarda da dacen da tayi na samun sa a matsayin miji sannan ya ce “Aisha….” Har cikin ranta ta ji muryar ta shi musammam yanda ya kira ainihin sunan ta, kallon shi ta ke ba tare da ta amsa ba, ganin haka ya cigaba da faɗin “Ban san yanda zan mi ki bayani ki gane ba, amma zan yi iyakar kokari na, kuma kin san dai ba zan taɓa cutar da ke ba ko?” Ayush da gaban ta ya fara faɗuwa ta ɗan gyara zama sannan ta ce “Ina Jin ka, Baban Sasa ya ce ba za ka aure ni ba ne?” Kai ya girgiza ya na mai mamakin yanda ta kama sunan Baban Sasa haka, ya ce4 “Ya sallam! Ko kusa! Me zai sa ki yi tunanin haka?” Cikin yatsine ta ce “Toh ai yanda na ga ka na ba da labarin kakan na ka ne ai komai mai ma zai iya faruwa, bare kuma ka ce shi ya aura maka matar ka” “Auren ya mutu…..” “Sorry?” Ayush ta faɗa domin son Jin ya sake maimaitawa, dan gudun kar dai kunen ta ke zagi. Shi kuwa Saifullahi ya girgiza kai sannan ya kara da STORY CONTINUES BELOW “Na sake ta” “Ka sake ta fa ka ce? Saboda me ya sa? Kar dai saboda auren mu ne?” Cewar ta, ta na mai fatan hakan ne, shi kuwa Saifullahi nan ya sami hujjar da zai fake, ya tsinci kan sa ya na faɗin “Na so jurewa na haɗa ku ba don komai ba, sai dan biyayyan iyaye, Allah na gani yanda na ke kaunar ki ban ji zan iya adalci tsakanin ku ba, saboda haka sai na sauwake mata” Wani irin daɗi da annushuwa ne ya mamaye Aysuh duk da kuwa ta so ta ɓoye shi, amma hakan ya gagara. Ta na mai danna fara’a ta ce4 “Ayya Honey pie ai da ka barta, ko dan gujewar fushin su Baban Sasa”2 Ta tabuwa Saifullahi in da ya ke masa kaikayi, ya na mai share zufa ya ce “San ki da na ke ya sa idanuna rufewa Ayush, yanzu haka ina kan fuskantar fushin na su, saboda na saki yarinyar nan yanzu sun ce a lalle sai dai mu zauna cikin family house din mu……” “Allah ya sauwake na zauna gidan gandu in yamutse se kace dambu!”10 Ayush ta katse shi cikin tsawa, ta kara da “Ka san me ka ke faɗa kuwa Saif? Kamar ni? Ni Ayush ka ce na zauna family house din ku? Dama hakan nan zaman family house masifa ne bare kuma a ce ka saki cousin ɗin ka saboda ni? Na zauna a kuntata min kenan? Wallahi ba ka isa ba! Ko dai ka aje ni gidan da ka ce ka gyara min, wanda shi ma din ka san is not up to my standard, ko kuwa a fasa auren nan!”2 Ta kare maganar cike da tsiwa. Jikin Saifullahi yayi sanyi hankali tashe jin Aysuh na batun fasa aure “Ayush kar ki min haka, ki rufa min asiri ba zan iya rayuwa babu ke ba, ba kuma zan iya bijirewa maganar iyaye na ba, ki tuna fa kasa jure soyayyar ki ya sanya na saki Amatullah, su kuma dan su kuntata min ya sa suka bijiro da wannan hukunci…..” “Malam ni ina ruwa na! Ba zan zauna family hause ba!” Ayush ta kara jadadda masa. Juyin duniya da rarrashi babu wanda Saifullahi be yi ba, Amma ta ki. Ranar haka su ka rabu kowa babu dadi.2 **** Tun bayan tafiyar Saifullahi ta shiga tsaka mai wuya, gashi ba ta san jama’ar gidan su san halin da ta ke ciki dan tabbas su ka sani aure tsakanin ta da Saifullahi ba mai yiyuwa ba ne. Da zaman gidan ya ishe ta mayafi ta saka in da ta neme izini gurin mahaifiyar ta, ta figi motar ta kirar honda, ba ta zame ko ina ba sai gidan su kawar ta Sameera da ke hotoro GRA. Ba ta boyewa Sameera ko mai ba dan kuwa abokin kuka ba a boye masa mutuwa. Jiki sanyaye Sameera ta ce “Ayush kin san duk wannan abin na su ba dan komai ba ne sai dan su hana auren nan na ku, kuma gashi kin sa burin su zai cika!” Ayush na share kwalla ta ce “Ya ki ko so na yi Sameera? Kin fa san muddin aka ji wannan maganar a gida ba za su bari a yi auren nan ba!” “Idan har ki ka tsaya tsayin daka walllahi dole su hakura, Saifullahi na san ki fa Ayush! Maza da idan su ka ce an aura mu su cousin shikenan tsakanin ku, Amma shi ya rike alkawari har ya saki matar shi saboda ke? Ai ke ma kin san dole akwai consequences ai, bai kamata ki juya masa baya ba Ayush”2 Cewar Sameera. Shiru Ayush ta yi cikin nazari kafin ta ce “Yanzu haka zan zauna na haihu gidan gandu?” Sameera na girgiza kai ta ce “Kash wa ya ce mi ki zuwa za ki yi ki haihu? Ai idan kin ga kin haihu da Saifullahi to kun tashi daga gidan nan Ayush, inaaaa ko ni ba zan yarda ki haihu ba, emergency contraceptives pills za ki sha, within 72 hours za ki sha idan wani abu ya faru tsakanin ku you know, amma ya fi aiki idan ki ka sha immediately after sex, shi ne zai lalata kwaiyoyin sinadarin haihuwa da su ka shiga cikin, ya hana su developing zuwa kwayoyin halitta”2 STORY CONTINUES BELOW Cikin farin ciki Ayush ta ce “Dadi na da ke Sameera sanin duniya wallahi! Ai shikenan zan bi shawarar ki, zan faɗa ma sa na hakura zan yi zaman shekara ɗaya family house din na su, Amma fa ki samo min pills din nan, kin ga dai sati shida ya rage” “Kar ki ji komai mata a gidan Saifullahi, kuma wallahi kar ki saurara mu su in dai ki ka shiga family house ɗin nan, yanda su ka mi ki rama, musammam wannan tsohuwar matar ta shi da ya ke kira bagidajiya!”4 Su ka yi shewa su ka tafa. Nan Sameera ta cigaba da kimtsa mata yanda za ta yi gidan auren ta. Ita kuwa Ayush ta na mai maraba da gangar shaidan ɗin da Sameera ke buga mata. Daren ranar ta shaidawa Saifullahi amincewar ta na zama gidan su. Duk da yayi mamakin yanda ta canza ra’ayi cikin kankanin lokaci amma ya kasa tambayar ta dalili. Soyayyar su suka cigaba cikin jin dadi. **** Da yardar Allah da kuma taimakon kula da Amatullah ke samu wajan Mama jikin ta yayi kyau sosai. Har aka gama mid semester break ba ta iya daga waya ta kira Mimi ba sai dai Mimi ta kira ta, wai a nata kar ta kira Mimi ta na tare da Dee Yusuf. Duk yanda ta so ta yaki zuciyar ta akan wani abu mai kama da kishi da ke taso mata duk sanda tunanin dangantar da ke tsakanin Dee da Mimi ya zo mata.2 Fatan ta dai Allah ya sa ba abin da take tunani ba ne, saboda tazarar da ke tsakanin ta da Dee Yusuf bai hana ta kishin sa ba. Amatullah ba ta sami damar komawa makaranta ba satin da aka koma saboda yanda Mama ta dage lalle sai ta zauna a gida ta murmure, dan haka Mimi ce ke mata attendance da assignment har satin nan ya kare.2 Dangane da Saifullahi kuwa ta yi kokarin cire shi daga zuciyar ta duk da dai hakan ya ci tura saboda Emjay. Zaman taka tsantsan take yi a gidan gudun kar Allah ya hada ta da shi, ko yara sun bi da Emjayi ta bangaran Hajiya sai ta koro su, haka kuma ba ta fasa yaɗawa Amatullah da Gwaggo habaici ba musammam da ta ga auren Saifullahi ya taho gangaganga, komai na tafiya yanda ta ke so. Mimi kuma tun ranar da auren Amatullah ya mutu sanadiyar Dee Yusuf ta ke addabar shi da maganar Amatullah. Tun ya na share ta har ya mata alkawarin ta same shi office ɗin sa bayan ta gama lecture zai fada mata abin da ta ke son ji. Ana gama lecture din ta yiwa Amatullah waya, in da take shaida mata suna da test gobe in za ta iya ta samu ta shigo. Bayan sun gama waya ta wuce department din su Dee. Cikin office din na sa ta tarar da shi, sanye ya ke cikin farin yadi dinkin jamfa ya masa kyau na kwaran gaske. Ganin Mimi ta shigo sanye cikin hijabi da ya tsaya mata iya gwiwa ya na murmushi ya ce “Zama da madaukin kanwa, so Amatullah ce ta koya mi ki sa hijabi haka Mimi?” Ita ma din murmushi ta ke in da ta zauna kujerar da ke kallan ta sa tare da faɗin “Ban son sharri fa Dee, dama tun kafin na san Amatullah din ta ka na ke ɗan sa hijabi na” “Amatullah dina? Kin ba ni ita ne?” Cewar Dee ya na mai sosa kyeya “Do you still love her? Do you have feelings for her?” Kai ya girgiza, ya bata amsa “It doesn’t matter how I feel about her Mimi, she can never be mine…..” “But y? Ba dai saboda ta yi aure ba ne? Ai ya sake ta! I’m sure dan ta taɓa aure ba zai zama dalilin da za ka guje ta ba” Cewar Mimi cikin nuna rashin fahimtar Dee Yusuf. Kallon ta ya ke kafin daga bisa ya ce “Mimi ba za ki gane ba” “Try me” “Owk, iyayen ta ba za su taɓa bani auren ta ba, ba sa san tsatson da na fito daga ciki” “But Dee ai ya wuce, da ne, y not try your luck again? I mean everything has changed…” “Nope, not everything Mimi, expecially my background Mimi….wanda bai so ka da kwana ba ba zai so ka da wuni ba” STORY CONTINUES BELOW Shiru ne ya biyu baya, kafin daga bisani Mimi ta ce “Idan ita kuma ta na son ka fa?” Kafaɗa Dee ya daga ya sauke, sannan ya ce “I love her too, babu yanda zan yi Mimi”2 Cike da farin ciki ta ce “Akwai yanda za ka yi, ka ga yanzu ta na idda ne ko me suke kiran waiting period ɗinsu, last time da ta ke min bayani ta ce min until then ba za ta iya kula kowa ba, so you have enough time, ka shirya yanda za ka sace zuciyar ta da na iyayen ta, Amatullah ta sha wahala a rayuwar ta na aure, in ba haka ba you will end up with me, you know I love you right?”4 Dariya mai fitar da sauti ya ke yi jin furucin Mimi na karshe, ya daɗe da sanin Mimi ta na son shi, amma hukuncin addinin christain na hana auren cousin ne yayi tazara a tsakanin su, har ita da kan ta ta yi wa kanta gata ta yi watsi da wannan lamarin, abin mamaki sai gashi yau ita ce ke kokarin daidai ta shi da Amatullah. Cike da fara’a ya ce “Allah ya baki miji wanda ba zai ga laifin ki ba Mama na, yanda ki ka ce din shi zan yi, I don’t want to end up with beautiful Mimi, ba zan iya faɗa da samari ba” “Kaii Dee!” Dukan su dariya su ke cike da jin dadi su ka cigaba da hira. *** Kwanci tashi asarar mai rai, duk wani shirye shirye da ke gaban Saifullahi ya yi kokarin saukewa, ya gyara in da Baban Sasa ya umurce shi da tarewa, wanda hakan sai da ya kai shi ga cin bashin banki don ya gyara ginin da zata ji dadin zama. Ranar da za a kai lefe ya kama ranar asabar, Amatullah ta yi rashin sa’a ta na gida, ta so fita ta bar mu su gidan amma Gwaggo ta hana. Guɗa da habaici babu wanda Amatullah ba ta ji ba daga dangin Hajiya. Gwaggo da Amatullah na zaune a falo sai gashi an fara shigo da akwatuna ana ajewa gaban ta, da ta tambaya daga ina, kanwar Hajiya ta ce2 “Abin arziki Hajiya ta ce a kawo ki gani, kayan lefan Saifullahi ne, Allah yayi” Ta karasa maganar ta ba mai rangwaɗa guɗa. Kallon Amatullah Gwaggo ta shiga yi, wanda idanun ta sun ɗan ciko da kwalla tsabagen takaicin zaman da Gwaggo ta sa ta yi a gidan. Daki ta tashi ta shige ta tarar da Emjay na shan baccin sa, ita ma ɗin kusa da shi ta kwanta, hannun ta bisa jikin sa yayinda ta shiga karanto adduoin samun kwanciyar hankali. Gwaggo kuwa biye mu su ta yi, aka bude kaya da ita, ta na mai sanya albarka ba tare da ta kula da habaicin da ake yada mu su ba, dan kuwa ta san kawo kayan bagaran ta ma da biyu aka yi. ***** Ana saura sati ɗaya biki, yana shirin tarewa a Kano saboda bukukuwan da za su yi mahaifin sa ya kira shi. “Ango ka sha miya, amma na ga ka manta da wajibi kana ta ɓarin kudi a wanda ke shirin zama wajibi” yace cikin sakin fuska. Zai iya rantsewa tun bayan sakin Amatullah bai ga fuskar mahaifinsa a sake ba, sai ranar. Kallon sa yake cikin rashin sani.2 “Yarinyar nan Amatullah ka manta tana cikin idda ne, ko ka manta har yanzu cinta da shan ta yana wuyanka, bana ko zancen Babana don kace ba naka bane, amma kam yanzu ka ciro kuɗi ka bani na abincin Amatullah, kuma bana son harkan ƙaranta” mahaifinsa ya faɗi cikin dakewa. Gaba ɗaya kan Saifullah ya kwance, ita da ake maganar akanta tun daren nan bai sake ɗaura ido akanta ba, ba zai iya tantance tana gidan ko bata ba, ya san ya kan shiga ɗakin iyayenta ya gaida su amma ko Emjay bai sake kuskuren gani ba. Aljihunsa babu komi sai kudin da ya je ya canzo bandir ɗin yan hamsin hamsin, kallon mahaifin sa yayi yana mai sunkiyar da kai ya ce “Baba da za a min haƙuri na gama wannan hidiman zan bada” yace cikin muryar neman ɗauki. “A’a fa Saifullah, ba zamu yi haka da kai ba, duk wata dubu hamsin zaka bata har ta gama idda, yanzu dai bani nan in ga” yace yana miƙa hannu.4 Gaba ɗaya kudin Aljihunsa dubu hamsin da biyar ne, su kaɗai su ka rage masa gaban sa da bayansa. STORY CONTINUES BELOW “Baba…” “A’a fa engineer, miƙo kawai ga kuɗi nan ina hange a aljihunka”2 Cikin sanyin jiki Saifullah ya ciro sabbin kuɗin da ya yi niyyar zuwa yayi liƙi da su, ji yake kamar ya ɗaura hannu a kai ya dinga kuka don gaba ɗaya Baba Anas ya shiryi tona masa asiri. “Madalla, Allah sa a watse taro lafiya” Baba Anas ya fadi tare da jingina sosai a kujerar da yake zaune, zuciyarsa ƙal da farin ciki. Ya san ya katse masa da Hajiyarsa wani yanki na jin daɗi, sarai ɗazu ya ke jin tana faɗi cikin fariya Saifullah ya je ya canzo kuɗi, da yanda za ayi liƙi kada dangin Ayush su raina su. Dariya Baba Anas yayi, yana jin ko a haka ya barsu ya rage wani sashi na takaicin su da yake ji.2 A ranar Baba Anas ya damkawa Amatullah kudin, in da ta ce dan Allah ya taya ta neman izinin Gwaggo ta koma makaranta tun da exam za su fara, yanayin taro na biki ba zai bari ta sami nutsuwan karatu ba. Hakan kuwa aka yi, da sa bakin Baba Anas ta hade dan kayan ta da na Emjay cikin farin ciki ta yiwa Mimi magana. Gidan dalibai da Mimi ke zaune ta koma, dake gida ne irin na dalibai ‘ya’yan manya, gidan yayi kyau ba laifi. Nan Mimi ta bata ɗaki ɗaya, ta na murna lalle Dee zai yi alfahari da ita.4 *** Washe gari yan danki su ka iso, motocin ɗaukan kaya biyu su ka zo da shi cike da kaya, duk da iyayenta sun rage yawan kayan a dalilin faɗin Saifu na zamanta gidan Jamoh. Ta kofar kuyanbana su ka shigo tare da tahowa kamar za su fita gari su ka shigo ta ƙofar kona. “Kai cikin kuttu za ta zauna dama” faɗin ƙanwar mahaifin Ayush da ta san kan zaria sosai. Yanayin da ta faɗi cike da takaici ne da jin alamun kaskanci ga zuriar su.2 Shiru matan wajen su ka yi suna mai kallon yanayin anguwar, gidajen gandu ne mafi akasari sai sabbin gine-gine ɗaiɗaiku. Gaba ɗaya bakunan su kamar an ɗinke duk da dama ba wai zuga su ka yi ba, kannen mahaifinta ne guda uku tare da yar mahaifiyarta da kannen mahaifiyarta biyu. Hajiya Haske kuwa da ta san ƙanin mijinta mai kuɗi da gadon kuɗi ya so Ayush amma na nace ma Saifullah bata san lokacin da ta ja tsaki ba sa’ilin da motar ta tsaya a kofar gidan Jamoh. Gini ne na da amma da gani ya sha gyara, tambari alamun gidan sarauta liƙe a ƙofar gidan nasu. Kallon makotan gidan su ka yi sai su ka ga sabbin gine-gine masu kalar zamani uku ne kuma duk ba a kammala ba. “Marhabin sannunku da zuwa” Habiba matar Baba Mahmuda ta faɗi tana mai musu iso.. Turkewa su ka yi a ƙofar gida ba tare da alamun niyyar shiga ba, sai da ta sake faɗin “Hajiya bismillahnku ai sasan su na da ga ciki ne” tace kamar zata musu sujjada saboda ladabi ganin kallo ɗaya ta musu ta gane sun tsumu da Naira. “Anty wai har dankin a family house za ayi” hajiya haske da ta kasa hakuri ta ɗaga waya ta kira yayarta ce ta faɗi cikin tsananin ɓacin rai. Hakuri ta ba ta daga can ɓangaren tana mai nanata ai ƴar su ce ta ja musu wannan kaskancin. Hakan ya sanya su ka shiga ciki ba tare da ba da umurnin a sauke komi ba na kayan. “Don Allah muna son a mana iso wajen babba a gidan nan” faɗin Hajiya Jamila kanwar mahaifin Ayush. Kallon ta Habiba ta yi sannan ta aika a faɗi ma Baban Sasa kafin su isa, cikin ikon Allah Baba zubairu da Baba Anas na nan a wajen sai su ka ce a faɗi masu su shigo. Ƙatuwar dardumarsa mai cike da ƙamshi aka shimfiɗa musu, ko da su ka shigo sun iske ɗakin bai rasa komi na nagarta ba sai kuɗi amma su ka tsunga kamar masu kyamar ɗakin. Sun gaida Baban Sasa babu yabo balle fallasa a nan ne Hajiya Jamila tace “Sunana Hajiya Jamila, ina aure da aiki a birnin California, ni ƙanwar mahaifin Ayush ce, mun zo jere ne Baba amma Sam ba mu ga muhallin da za a sa kayan da mu ka zo da ita ba, balle har mu ce zamu ajiye ɗiyarmu a ciki” tace tana mai yatsina fuska, saura su ka amsa da Aikam dai.8 STORY CONTINUES BELOW  Baba Anas har zai magantu sai Baban Sasa ya hana masa, kallonsu yake yana raya a ransa har za su nuna ma bazazzage jin kai, bazazzagen ma Bamalle. Murmushi yayi yace “MaashaAllah! Allah ya ma rayuwa Allah, ai Muhalli nagarta da soyayya ke samar da ita ba kuɗi ko Nasaba ba. Ga ɗakuna can da mijin Ayush zai iya affording, if she really love him, she will be ever happy to live in it” turancin da ya ƙarasa maganarsa da ita ya sanyaya masu guiwa, saboda turanci ne irin na sarauniyar Ingila, duk a tunaninsu bai taɓa zuwa aji ba dole jin California ya San ba ƙaramar yarinya za a kawo ahlinsa ba. Jiki a sanyaye Hajiya haske ta ce10 “Baba ba mun raina bane, ganin kayan daidai wancan ginin da Saifullah ya nuna ne, garanta kaɗai ma ya isa ya ɗauke duka ɗakunan komi ashirin da huɗu ne” Tace cikin sanyin murya da fariya. Dariya Baban Sasa yayi ya ce “Ana iya siyarwa a ba amarya ta ja jari, tunda dai kun ga irin gidan da ta shigo” bai sake faɗin komi ba su ma suka ɗan ƙara zama na yan mintuna su ka miƙe. Daidai gwargwado Saif ya zuba kayan zamani sasan, ɗakuna biyu ne da kitchen da store da bayuka a kowane ɗaki. Nan dai suka shirya kayan da suka iya shiga ciki, sosai waje yayi kyau amma sun ji takaici da kayansu da dama basu samu waje ba. Motar ta da suka zo mata da ita su ka ajiye a wajen adana motoci duk da dai ba an tanadar da wajen don haka bane amma ahlin gidan anan su ke ajiyewa. Ko da suka shiga sashin su Hajiya, sakin maganganu kawai su ka dinga yi, matan gida aka samu chapter badawa.2 *** Bukukuwa sosai na gani na faɗa aka yi a ɓangaren su Ayush. Ango da Amarya sun yi kyau sosai, yan mujallu sun hallara sun ɗauki hotuna a duk wani event da aka yi. Faɗin farin cikin da ma’auratan su ka shiga ba zai misaltu ba. Ranar Lahadi da ƙarfe tara da rabi na safe aka ɗaura auren Saifullah da Aisha, ɗumbin masu kudin Nijeriya da kasashen da ake maƙotaka duk sun halarta. Bayan ɗaurin Aure aka ɗauko zuga zuwa gidan Amarya. Tafiyar Awa uku ya kawo su gidan Jamoh tun daga ƙofar gidan mahaifin Ayush, nan ma yan uwanta da kawayenta su ka shiga yaɓa magana. Duk kokarin Ahlin gidan Jamoh bai birge su ba, suna miƙa ta suka nemi hanyar tafiya, faɗi suke “Allah ya baki ladan zaman talauci, gida a ƙuntace, ina aka samu wajen zama a wajen nan balle ki miƙa ƙafa” haka suka dinga faɗi har su ka fuce su ka barta cikin ƙunci. Kamar yanda su ka tsara da Saifu ana jibi biki cewa kwana bakwai na amarcin su a hotel za su yi Don ba za su iya da takuran gidan gandu ba. Ana idar da isha’i su ka fice daga gidan, ba su tsaya ko ina ba sai cikin GRA inda ya kama musu ɗaki.2 Sosai su ka mori darensu, don duk wani salo Ayush ta yi kwas a kai kuma ta ba shi. Hakan bai sa ya gamsu ba, asali ma tuna masa yayi da kwanakin sa da Amatullah, kenan da gaske suturta jiki na ƙara taimaka wajen bambance zuma da suga ko kuma dai dan sun dan saba dan wasanni tun kafin su kai ga auren.Duk wannan tunanin bai hana masa yi mata alkawura ba tare da bata duk wani yanci da take so a rayuwarsu. “Kaga ita Ayush matar so ce ita Amatullah sai ka rike ta don samun cikon natsuwa da kamala” ya tuna hirar abokin sa bayan an sanya ranar sa da Ayush. Tabbas ga shi ya zahir, duk da ita ɗin ma shine farkon ta, amma tazarar da ke tsakanin Amatullah da Ayush mai faɗi ce. Ayush kuma neman yanda za ta sami damar hadiyar kwayoyin da Sameera ta siyo mata ta ke yi, bata shirya bacci ba sai da ta haɗiyi kwayoyin don gudun ɗaukan ciki, a tsarin ta ba ta ga za ta iya ɗaukan ciki kafin shekara uku bayan aurensu ba, bare yanzu da take zaune gidan gandu. A haka dai suka kwashi kwana bakwai ɗinsu sannan su ka koma gida, babu wanda ya ce da shi kanzil kamar yadda babu wanda ya ma sallama kafin ya tafi. *** Babu abin da ya fara ɗaga hankalin Ayush bayan dawowarsu sama da tashin ta da yayi ƙarfe bakwai ta je ta gaida iyayensa. Kallonsa ta yi sheƙeƙe tace “Honey pie, ba zan yi bacci ba Fisabilillah, wani irin in je in gaida mutan gida, ni fa bana son fara abin da ba, zan ɗore ba, ha’an” tace tana harararsa kamar ta yi kuka. “A’a fa babe, kinga duk wannan na ɗan lokaci ne kafin mu tafi gidan mu, sai mun so zuwa za su ganmu, ki yi haƙuri daga kin dawo shike nan” yace yana rungumar ta. STORY CONTINUES BELOW “Ɗakin Hajiyarka kawai zan shiga, wancan tsohon ma bana auren da shi don shi bakin cikin kasancewarmu tare yake” tace tana mai faɗin iya gasikyar ta, shi kuma ya dinga wangale baki yana tunanin wasan jika da kaka ta ke da Baban Sasa. “Shike nan mu je kin ji” yace yana mai miƙo mata gyale ta yafa akan kayan jikinta wainda su ke ƙanana masu bayyana sura.2 “Au ba zan iya fita haka ba, ni dai Allah zaka haramta min zuwa gaisuwan nan, what is wrong with my dressing for goodness sake” tace cikin tsiwa. “A’a muje, ba komi, naga amarya ce ai” “Amarya baka ci sadakinka bane” tace tana watsa masa harara. Tunawa da garar da ya kwasa da yanda ya san kowace rijiya da yanda take amsar guga. “Babe oooo muje muyi mu dawo kiji” ya ce yana miƙewa, haka suke tsallake mutane tana gaida su a tsaitsaye har ta isa ɗakin hajiya. Kujera ta samu ta zauna, sannan ta gaida Hajiya tana mai ƙare ma ɗakin kallo tana tsine ma soyayya a zuciyar ta, ‘in ban da soyayya wai nan ne za a kira ɗakin uwar mijina’ tace cikin ranta. “Ai na sha bacci za ku yi, hayaniyar biki ai sai da hutu” hajiya ta faɗi cikin murmushi, kallon Ayush take tana ƙara gode ma Allah da ta bata surukar da tafi ta kowa. “A’a ai muna neman Albarka ne” tace a yatsine. “Allah ya muku albarka” Hajiya ta caɓe cikin sauri. “Aameen” Ayush ta faɗi cikin miƙewa. Shi ma a mike su ka fice duk yanda Hajiya taso ta ɗan keɓe da shi. Haka rayuwar su ke tafiya kullum safe zata gaida Hajiya ta koma ɗakinta, abinci kuwa in bata soya dankali ba zata girka musu taliya ko farar shinkafa da wake su ci da mai da yaji.2 Tun yana ganin hakan a matsayin amarci ne har dai ya lura da gaba ɗaya cikin sa baya samun lafiyayyen abinci kamar da.6 *** Zaman Ayush a gidan bai tsinana ma kowa komi ba ciki har da hajiya, don cin abin hannun Ayush wahala ne, daban ta sa ƙannen sa Najaatu da Aisha su dinga zuwa suna mata gyaran gida da wanke wanke, hakan bai sa ta musu ihsani ba.2 Tun ranar da su ka dawo gidan ta ke raba idanu domin ganin Amatullah ko dan Saifullahi, amma babu su babu alamar su, har ta gaji ta tambayi Najaatu, in da take shaida mata ai tun satin biki ta ji Gwaggo ta ce ta koma makaranta saboda jarabawa. Hakan sam bai mata dadi ba, amma ta ce ba komai ta na nan tana jiran ta.4 Shigar da take musu a cikin gida kuwa babu ruwanta da wa zai gani, kwatakwata ɗan kwali bai dame ta ba haka za ta dinga tsallake matan gidan da sannu in zata shiga ɗakin hajiya. Abu ɗaya ne bata wasa da shi watau maganin ta, ko da wasa ba ta yarda ta yi tsallake ba don ba ta ga wajen haihuwa a gidan ba. Yau ma kamar kullum sanye take da doguwar riga mara hannu, tayi sabon kitso da lallai wanda ya kwanta a kan farar fatanta. Tuwo yace mata yana jin ci kuma ita har ga Allah ba ta iya ba, Najaatu take son kira ta tayata ta shiga wajensu tana tsallake su Hajiya da sauran matan gidan suna hidimar su, ganin ba sa wajen sai ta wuce soro in da ta ga su Baba Anas, Baba Idiris, Baba Zubairu da Baban Sasa zaune bisa tabarma. “Sannun ku”4 Abin da ta furta kenan, kafin ta gifta su ta leka waje. “Wacece wannan kuma” Baban Sasa yace bayan sun amsa mata sannu da tace. “inaga baƙuwa matar saif tayi” Baba Idris yace yana mai basarwa.6 Dawowar da ta yi tare da Najaatu ya basu damar gane ta. Cikin jinjina kai Baba Idiris ya ce “Wannan fa Aisha ce matar Saifullahi” Baban Sasa na mai kame baki ya ce “Wai matar Saifullahi ce ta zo ta tsallake mu da wannan shiga haka?”2 “Toh ai in dai wannan yarinyar ce kaɗan ku ka gani, wani shigar idan ta yi sai dai a kau da kai tsabagen munin shigar”2 Cewar Baba Zubairu cikin al’ajabi, ya kara da “tashin hankalina yanzu shi ne Kar Allah ya sa yaran gidan nan su dauki dabi’a irin na ta”5 “Ah ah, ‘ya’yan mu masu tarbiya ne, Allah ya tsare mu da ganin dabi’a irin wannan a zuri’ar mu, ina Anas surukar ka ce, ina fatan za ka yiwa tufka hanci!” Cewar Baban Sasa cikin jaddadawa. Kai Baba Anas ya gyada kawai, ya san dai in har hawan jini ya kama shi toh ko shakka babu Saifullahi shi ne sila. Baban Sasa be gushe ba ya kara da4 “Ai ni daga ganin dangin yarinyar nan na san Saifullahi ya saki rashe ya kama ganye, mu ka bashi diyar mu diyar mutunci ya watsa mana kasa a Ido, ai ga irin ta nan, ga irin wacce ya je ya kwaso” Ya karasa maganar ya na fitar da kwalla. Takaici ne ya dada rufe Baba Anas, in da ya tashi ya shige ciki.2 Ganin yanda ya shigo a fusace ya sa Hajiya bin bayan shi. Cikin ɗaki ya kwance mata kwandan takaicin da ya kwaso, ya kuma umarce ta da ta je ta yiwa surukar ta magana, ba sa shigar mutanen banza a gida, idan ba haka ba shi da kan sa zai mata magana kuma ba zai mata ta dadi ba. Ya na magana ya fice fuu, jiki sanyaye Hajiya ta nufi bangaran Ayush. A falo ta tadda ta, kwance bisa kujera. Ganin Hajiya bai sa ta tashi zaune ba, daga kwance ta ke duban ta, ta ce “Hajiya lafiya mu ke ko?” Cikin kame kame ta ce “Eh kwarai yar nan, lafiya lau, dama na zo ne da yar wata magana” Jin haka ta tashi zaune, ta ce “Bisimillah zauna mana Hajiya, na mi ki laifi ne?” Hajiya ma ta zauna, ta na mai girgiza kai ta ce “Ah ah ko kadan, dama yar shawara ce”2 “Uhum?” Cewar Aysuh ta na mata irin kallon nan na hadarin kaji, Hajiya ba ta kula ba ta cigaba da faɗin “Kinga a matsayi na uwar mijin ki, na ke son jan hankalinki akan shigar da kike yi, tabbas babu haramci a ciki saboda a gidan mijinki kika yi, amma ki sani fitowa a haka ya saɓa ma addini da al’ada. Don Allah ki ɗan dinga yafa mayafi kinji, Allah ya muku albarka ” ta fadi cikin sakin fuska. Takaici da bakin ciki ya sanya Ayush kasa cewa komai har Hajiya ta mata sallama ba tare da ta amsa ba ta fice, ta na fita ta kora Najaatu cikin zage-zage ta sa ma ƙofar sashinta makulli. Saifullah da ya shiga Abuja ya dawo gaf da magariba, yunwa ce sosai yake ji ga gajiya yana zuwa ya iske gidan a garkame. Komawa ɗakin hajiya yayi ya tambaye su ko Ayush ta fita ne nan Najaatu ta fadi masa abin da ya faru. “Amma Hajiya ya za ki biyewa Baba fisabilillahi ku ɓatawa yarinyar nan haka daga tarewar ta! Haba Hajiya!”2 Kafin Hajiya ta kai ga bashi amsa ya tashi cikin sassarfa ya isa ga ƙofar tasu, magiya yake da ban hakuri akan ta buɗe masa ita kuma faɗi take “Ba zaman kulle na zo yi ba, babu wani ɗan bura uba da zai sa nayi kulle” hakuri dai Saifullah yake bata inda mutane ke tsallake su tare da ganin halin da ya ke ciki.2 Yana kan bada hakurin ne Amatullah ta wuce shi tana mai waya, ga Emjay yayi ɓulɓul da shi rike a hannun ta. Shagala yayi yana mai mamakin dama a sashin Baba Hamza suke? Dama gidan nan take ko zuwa tayi? Idan idanunsa bai masa ƙarya ba kyau tayi ba ko kaɗan ba, surarta ya ƙara fitowa tayi shar da ita.8 “Haba Don Allah ki buɗe ki ji hukuncin da zan yanke Amatullah… ” ya ce hankalin sa na ga Amatullah da ta ɓace ma ganin sa. Babu shiri Ayush ta buɗe haɗe da jawo shi cikin ɗakin da rufewa. Jawo shi ciki da aka yi ne ya ankarar da shi abin da ya faɗi. Nan ya sanya dariya cikin borin kunya haɗe da faɗin+ “Haba Babe, kawai ki zauna kina sa mutane na min gani gani” yace mai rungumarta. “Wallahi ka sake ambaton sunan nan a gidan nan wallahi a bakin aurenmu” tace cikin ƙara haɗe rai.9 “ki gafarce ni Babe, wallahi sai da na faɗi ma Hajiya ina ruwansu da ke, ina ce dai ni kike aure” yace yana mai ƙara manne ta da jikin sa.2 “Ba kowa ya ja wannan abin ba na tabbata sai tsohon nan da ya kamata a ce ya rasu tuni amma ya tsaya cin zamanin wasu” tace cikin takaici, duniya babu wanda take tsana cikin birgewa dama da Baban Sasa. Tun farkon labarinsa da ta fara ji a duniya na yanda ya ke kawo mata cikas ne a rayuwa, ta san kuma ta ganshi da ta je kiran Najaatu.4 “Barni da shi zan same shi, inshaAllah nan da ƙanƙanin lokaci za mu bar musu zariar gaba ɗaya” yace duk da ya ji haushin kalamanta ga Baban Sasa amma sulhun da ya ke so daga ita yafi komi.6 “Allah ya amince Honeypie, zan kira Anty Rukayya akan issue din allocation na estate ɗin don mu samu” tace cikin farin ciki. Satin da ya gabata su ka ji labarin gidajen da ake rarrabawa ma’aikata gwamnatin tarayya don a rage masu matsalar samun gida a Abuja. *** Amatullah kuwa hutun karshen zango ta dawo, sun yi jarrabawa cikin sauki da fatan samun nasara. Ko da ta dawo Sasan Mama su ka sauka, cikin murna ta tarbe su, nan ta cika musu ciki da abinci. Emjay da yake wata shida a duniya yayi ɓulɓul da shi, fuskar sa sak na Saifullah haske kawai zai nuna masa. Mama wasa ta shiga yi da shi tana hurga shi sama tana caɓewa. “Ya karatun Amatullah, dafatan megidan nan nawa baya hana ki” Mama tace tana mai cigaba da wasa da Emjay. “Alhamdulillah! Ai mama Baaba tana mana kokari” Amatullah ta ce tana mai nufin yar aikin da mama ta haɗa ta da ita, duk da ba kwana take da su a samarun ba amma ko da za ayi takwas ta isa gidan. Sai yamma can ta fito don zuwa gaida Baban Sasa. Ta fito kenan za ta wuce ta ci karo da Saifullah yana buga ƙofa cikin magiya. Dariya sosai tayi a ranta, tana ganin yanda ya bi ta da kallo, maƙe dariyarta tayi har sai da ta tabbatar da ta ɓace ma ganin sa. Nan ta zauna a kan dakali, ta dinga tuntsira dariya. “Emjay ka ga abin da na gani kuwa, ka taya ni dariya mana” tace ma Emjay shi ma kamar ya ji abin da ta faɗi nan ya shiga wangale baki yana dariya shima. Sai da su ka yi mai isarsu sannan ta tashi ta nufi wajen Baban Sasa.2 Sosai yayi farin cikin ganinta duk da in ya tuna cewa ba ta gidan Saifullah sai ya ji babu daɗi a ransa. “Oh jikan yara wannan ƙiba haka se ka karya min mata” yace yana mai amsar Emjay. “Aikuwa Baba gashi se muni yake, ai kwalelenka matanmu ba sa sonka” Baba Zubairu ya ce, su baba Anas ya taya shi. Ita dai Amatullah banda murmushi babu abin da take yi, son iyayenta na ratsa, ita a halin yanzu ba ta da lokacin jin haushin kowa, lokacin da take ɓatawa wajen son kanta da neman cigabanta ma ya mata kaɗan. ” Amatullah!!!” Baban Sasa yace wanda ya dawo da hankalin su wajen shi. “Ki dubi yaron nan ki tausaya masa ki koma ɗakin ki Amatullah, Don Allah ba don ni ba” yace cikin sigar roko. Jin zancen tayi kamar saukar aradu amma ta ɗaure ta ce. “Wallahi Baban Sasa saki uku ya min, da tuni na koma” tace tana mai danne hawayen da ke neman fitowa. “Shi fa yace saki ɗaya ne, kaddara ukun ya miki a take zamanin Annabi SAW, da khalifancin ABUBAKAR RA zuwa Farkon Umar RA duk saki uku a lokaci ɗaya ana kirga shi a matsayin ɗaya ne, dalili yasa Umar RA ya maida shi uku, maluma na ganin ana iya ɗaukan hukuncin farko” yace yana mai ƙara narkar da fuska. STORY CONTINUES BELOW “A’a fa Baba, zance mafi inganci Shine a yi amfani da hukuncin sayyidina Umar RA. Annabi da kansa ya ce ALAIKUM BI SUNNATIE WA SUNNATU KHULAFA’UR RASHIDUN ka ga hadisi ne ingantacce da ya wajabta amfani da hukuncin su a fage na addini” Baba Anas ya tare shi, hakan ya saukar ma Amatullah natsuwa. “Kuma Babanmu wallahi yaron nan bai yi hankali ba, ka daina damuwa da lamarinsa, lusari ne ba ko ƙarami ba” Baba Anas ya ƙara faɗi ganin baban Sasa bai gamsu da shi ba. “Shine dalilin da ya sa nake son komensu, ka ga za ta gyara shi, da wuya amma da nasara a gaba” Baban Sasa yace a maraice.8 “Zata koma Baba, ka bar komi a hannuna inshaAllah” Baba Hamza yayi karaf ya faɗi yana mai musu signal da ido. A nan gaɓan Saifullah da Ayush su ka shigo wanda Ayush ta tabbatar da ta in gizo shi da su zo yayi magana da Baban Sasa akan a fita rayuwarsu. Babu bambanci a shigarta ta ɗazu su ka shigo da Sallama. Kallo ɗaya su ka yi ma juna ita da Amatullah su ka shaidi juna. Ta san dai za ta nuna ma Amatullah fari da tsawo amma diri da tsananin kyau ko kaɗan ba za ta kamo Amatullah ba. Sanye take da atamfarta riga da skirt da hijabinta da ya shiga da kayanta amma sheƙi da Amatullah ke yi ya ɗan rikitata don natural glow ne da ta fara koyon sirrinsa daga mimi.5 Ɗaukan Emjay tayi ta fice tana ma iyayen sallama su kuma suna masu bin ta da Albarka, kafin duk su gimtse fuska. “Baban Sasa Ƙaran Hajiya na kawo” yace yana mai yamutsa fuska ganin yanda iyayensa su ka yi fuskar shanu.3 “Toh me hajiyar tayi?” ya ce yana ƙara haɗe rai. “Ta fita idon iyali na, ko a musulunci an yarda ai mace ta yi shiga irin shigar da mijinta ke so, Baba ni ke auren Ayush ba kowa ba, haka nake son ganinta don haka ka ja masu kunne” yace yana mai kumburewa.2 “Tohhh Madalla da tabbatacce mara kishi, shi ne ka…” Baban Sasa bai ƙarasa ba saboda sarƙewa da maganar ta yi amma bai fasa nuna Saifullah da Yatsa ba, nan take ya faɗi a wajen sumamme.9 Ruwa suka ɗauko su ka watsa masa amma ko motsi bai yi ba, duba shi su ka yi nan su ka ga maɗiga na bugawa, ɗaga idon da Baba Anas yayi ya ga su saif tsaye a firgice ya ce “Saifullah Allah…” bai karasa ba dalilin rufe bakin sa da baba Zubairu ya yi. “Fice mana da gani Saifullah” Baba Idris ya faɗi cikin tsawa nan su ka fice sum sum shi da Ayush, ita tana addu’a Allah ya sa Baban Sasa ya margaya a huta shi kuma tsoro da Dana sani ne ke cike da kirjinsa.4 *** Asibitin Koyarwa ta Shika su ka nufa da shi, addu’a su ke kada ya rasa ranshi. Sashin gaggawa da hatsari su ka yi da shi inda take aka mika shi sashin masu fama da ciwon ƙoda bayan an duba an gano jininsa ne ya hau da kuma kodarsa guda ɗaya ta lalace, dole a cire ta in ba haka ba ciwon zai iya taba dayar kodan. A asibitin su ka kwana don likitoci a kansa su ka kwana, kafin su ka samu ya farfado amma nan aka nemi jini saboda saboda za a shiga da shi aiki. “Sai dai a siya duk mu nan da muke nan babu mai kalar jininsa, Salihu ne da mahmuda su ke da shi amma duk mu positive gare mu” Baba Zubairu ya ce ma likitan cikin damuwa. “Yaa salam, samun jini 0 negative yanzu aiki ne, amma kuje bankin jini ko za a dace” yace yana komawa wajen tawagarsa da ke duba Baban Sasa. Baba Anas na sauri don zuwa ya bincika ko zai samu ya bangaje mutum. A tare su ka ba juna hakuri nan su ka shaidi juna. “Baba ina kwana, da fatan lafiya na ganka a asibiti da safen nan” Yace fuska a sake. “Kai dai bari ɗan nan, Baba ne ake bukatar jini 0- ne, shine zan duba ko za a samu, ina ne ma blood bank ɗin” yace cikin ruɗu.2 “Subhanallah, Nima ai 0- din ne muje baba a yi min gwaji in lafiya lau sai a ɗibi nawa, Nima na zo wajen supervisor na ne” yace yana mai kamo hannun Baba Anas ganin yanda duk ya rude.2 STORY CONTINUES BELOW An ci sa’a jinin Dee lafiya lau ya ke, haka kuma ya na da ishasshe dan har leda uku aka samu daga wajen shi. Godiya mara adadi Baba Zubairu da Baba Anas su ka ta yi masa, da shi aka zauna har aka shiga da Baban Sasa aiki. Awanni aka dauka ana yiwa Baban Sasa aiki, har Allah ya ba su iko su kammala masa aikin aka fito da shi rai a hannun Allah. Yanayin da aka fito da shi ba su Baba Anas ba, shi kan shi Dee sai da ya sha jinin jikin sa, dan kuwa hatta su likitocin da su ka masa aiki ba su da tabbacin ko zai tashi.5 Daki na musammam aka kwantar da shi, Baba Zubairu ne mai dauriyar kai kawo, shi kuwa Baba Anas tun ganin yanda aka fito da Baban Sasa bakin shi toshe da abin bada taimakon numfashi ya ke fidda kwalla. Sai da aka kwantar da Baban Sasa, Dee Yusuf ya mu su sallama tare da alkawarin zai dawo jiki sanyaye ya tafi.2 Ranar daga Baba Zubairu har Baba Anas babu wanda ya runtsa, haka ma Baba Salihu tuni ya ɗauko hanya, in da Baba Muhamuda shi ma ya karaso tare da Baba Hamza da Baba Idiris. Har dare yayi Baban Sasa bai farfado ba nan aka shiga muhawarar wanda zai kwana da shi, dan kowannan su gani ya ke idan har ya tafi kafin ya isa gida za a kira a ce Baban Sasa ya cika. Daga karshe su ka yanke hukuncin barin Baba Idris, su kuma sauran su ka kama hanyar gida. Isar su kofar gida nan su ka taradda Saifullahi zaune, abin duniya ne ya isheshi tun bayar faduwar Baban Sasa wanda ya ke gani kamar shi ne sila, gashi kunya da tsoro ya sa kasa tunkarar asibitin. Ganin su ya tashi da saura ya na faɗin4 “Sannun ku da zuwa Baba, ya jikin Baban Sasa?” Babu mahalukin da ya amsa masa, Baba Anas kuwa ko kallon in da ya ke be yi ba, su ka shige gida su ka bar shi nan tsaye.4 “Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun! Ba zan iya jure fushin iyaye ba! Allah ya tashi kafadar tsohon nan ko Allah ya sa ku yafe min” Cewar Saifullahi yayinda ya koma in da yake zaune da ya zauna zuciyarsa cike da da na sanin biyewa Aysuh da yayi.2 Cikin gida kuwa, idan aka ɗauke Ayush kowa cikin zulumi ya ke musammam Amatullah wacce ta wuni ta na kiran wayar Baba Anas domin jin yaya jikin Baban Sasa. Gidan tsit kamar gidan makoki, jin motsin shigowar su ya sanya kowa fito ana tambayar “lafiya? Ya Baban Sasa ya ji da jiki?” “Babu sarki sai Allah, ku yi addua idan na tafiya ne Allah ya ba shi saukin tafiya, ya sa ya cika da imani, idan kuma mai tashi ne Allah ya saukaka masa ciwo, dan kuwa dai Baba na cikin wani hali!”2 Cewar Baba Zubairu wanda har lokacin shi ne ke da karfin halin magana. Abin ku da mata nan gida ya kaure da salati har da masu kuka. Sai da Baba Anas ya tsawatar mu su sannan kowa ya shiga hayyacin sa. Ayush da ke jiyo komai daga bangaranta ran ta ne yayi fari tas, Alhamdulillah tsoho zai mutu ta bar zaman gidan gandu, ta na mai adduar Allah ya sa ya tafi kenan.2 Jiki sanyaye Amatullah ta koma ɗakin in da ta dauro alwala ta shiga nafilfilu domin nemawa Baban Sasa sauki, ko da kuwa na tafiya ne. Dan kowa ya fidda rai Baban Sasa bai taba jinya da ta kai wannan tsanani ba.2 Ranar kowa kwanan zulumi yayi, cikin daren Mahaifin Amatullah Baba Salihu shi ma ya iso. Hatta Ayush da ke farin cikin rashin lafiyar Baba Sasa ba ta ji dadin daren nan ba, dan kuwa Saifullahi juya mata baya yayi a karan farko tun da ya auro ta.2 Da asubar fari su Baba Anas har Baba Salihu su ka dunguma asibiti, Nan ma su ka tadda Baban Sasa bai farfado ba, haka aka sake wani wunin zulumi da fargaba. Da la’asar Dee Yusuf ya koma duba Baban Sasa, Nan ya tadda duka baffanin Amatullah. Bayan ya gaishe su, su Baba Muhamuda, Baba Hamza, Baba Idris su ka amsa da kyar cike da kyama. Baba Anas ne ya ce1 “Ya ka nan zo zauna kusa da ni ɗana, abin da ka mana Allah ya ma ka, wannan yaron da ku ke gani shi yayi mana abinda duk cikin mu idan ban da Salihu da Muhamuda babu wanda zai iya ko da kuwa muna da niyya, wannan da kuke gani shi ya ba da jini har leda uku, wanda aka karawa Baba, duk da kuwa ya san kyamar shi da mu ke yi ……..” “Yanzu jinin arne aka sanyawa Baba? Haba mana shi ya sa gashi har yanzu bai motsaba ba shi ba raye ba shi ba a mace ba! Kwa bari a ɗura masa jinin mushe fisabilillahi!”6 Cewar Baba Hamza ya na mai kumfar baki. Shi kuwa Dee idan har maganar ta ba shi haushi sam bai nuna a fuska ba, dan kuwa ya san za a yi hakan. ” Baba ina ga babu ruwan bambancin addini a wajen ceton rai, nayi imani da littafi mai tsarki babu haka a cikin addinin ku, saboda Ubangijina na bashi, ina fatan Allah ya bashi lafiya”5 Dee ya faɗi cikin sanyin murya, kalaman sa be sanya sun ji sanyi a zukatansu ban na bakin ciki da takaicin jinin Arne ke gudana a jikin mahaifin su. “Sannan Baba in ma a blood bank a ka siyo, ana bambance jinin musulmi da Christian ne, sai naga aka yi rashin sa’a kila na mara addini kwata kwata zaku siya”8 Dee ya sake faɗi ganin yanda suke gimtse fuska, ya tashi tare da faɗin “Na bar ku lafiya, ubangiji ya tashe shi lafiya” Ya juya ya tafi abin shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *