TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 11

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 12

Buɗe baki yayi don ya mayar mata da martani, Amma ya kasa cewa komai dan takaici, kallon ta ya ke in da har lokacin ta dage tsakanin ta da Allah neman maganin ta take. A fusace ta sake waigo shi ta ce “Wai dan Allah Saif menene haka?” Can ta sake wani tunani, cikin sigar kissa da tausasa murya ta ce “Saif wani kwallin magani na ke nima, dan Allah ba ka gan shi ba?” Hankali kwance ya na mai ɓoye ɓacin ransa ya amsa da “Wani cikin ɗan karamin kwali haka? An rubuta post pill kamar?” Ras gaban ta ya faɗi, ta na mai fatan Allah ya sa bai karanta kwalin maganin ba ya san maganin menene ta ce “Exactly, shi ne, maganin ciwon mara na ne” Sai da ya tashi ya zo gaban ta ya tsaya sannan ya ce “Eyaaaa Ina ga wani daban na gani ba wanda ki ke magana ba” Ta na mai hadiyar yawo dan jika makoshin ta tsabagen tashin hankali ta ce “Ba ni wanda ka gani din…..” “Ni na ce mi ki na ga wani abu?” Idanun ta na mai kawo ruwa ta ce “Saifullahi don’t play smart with me! Na san ka gani wallahi! Dan Allah ka bani!” Kallon ta yayi tun daga sama har kasa, sannan ya ce “Ni da na ke bagidaje how can I play smart? Kar ki matsa min dalla malama! Ina da abin yi! Shirin dawowar uwar gida na dakinta na ke yi!”8 Ya faɗa ya na mai kokarin wuce ta ya na mita, wani kukan kura ta saka ta na mai cinkwalar rigar shi ta ce “Burauban nan kayyasa! Kai ka isa! Na ce Saifullahi ka isa ka dawo min da wannan bakar yarinyar bagida…..”2 “Ke Aisha!” Ya daka mata tsawa, cikin gurnani da daga murya ya ce “Wallahi na rantse da Allah ki ka sake ki ka zagi Amatullah sai na tattaka ki nan! Ta fiki daraja! Ta fiki ɗa’a! Ta fiki tarbiya! Ta fi min ke komai a rayuwa! Shasha wacce ba ta san ciwon kan ta ba!”11 Ya na gama faɗin haka bai damu da kukan da Ayush ta saka ba, ko zagin da ta rufe shi da shi, ya fizge hannun ta daga cikin rigar sa, nan ƙasa ya zubar da ita ya fito ya barta ta na kuka ta na surfa masa zagi. Bakin hanyar fita yayi kacibus da Hajiya ta na shirin shiga wajen na sa, cike da damuwa Hajiya ta ke duban sa, ta furta “Saifullahi gidan na ka lafiya kuwa? Duka gidan nan fa ihu da kukan matarka ake ji sai ka ce ana zaman bariki?”2 Saifullahi na mai girgiza ka ya ce “Hajiya menene bambamcin yarinyar nan da ƴan bariki? Ina ƴan bariki ne ke shan maganin hana daukar ciki gudun kar su yo cikin shege? Idan dai haka shi ne wayewa Allah wadar da wayewa irin na Aisha!”6 Hajiya na mai dafe kirji ta ce “Me ka ke faɗa ɗan nan!” Nan ya bawa Hajiya labarin maganin da ya tsinta ɗakinsa, ya kare da “Ko tausayi na ba ta ji ta na gani na rasa ɗana, ashe ita kuma ta na nan ta na min bita da kulle dukan kabarin kishiya! Hajiya tun rasuwar Emjay Allah ya jarrabe ni da kewar yaron nan! Ba ni da buri da ya wuce na sake ganin jini na Hajiya!”2 Kai Hajiya ta ke jinjinawa kawai, Saifullahi bai gushe ba ya kara da “Saboda haka na yanke hukuncin dawo da Amatullah, Hajiya Amatullah ita ce cikon farin cikina! Hajiya ba zan iya rayuwa idan babu Amatullah ba, Hajiya Amatullah kaɗai za ta iya sharen kuka na, Hajiya ku taimaka min!”4 STORY CONTINUES BELOW “Amatullah fa ka ce Saifullahi?” Hajiya ta fada a sanyaye, Saifullahi na mai jinjina kai ya furta “Amatullah Hajiya” Cikin sauri kar Hajiya ta ga kwallan da ke idanun sa yayi sauri ya wuce ta ya fice. Jim Hajiya ta tsaya ta na mai jinjina maganar dawo da Amatullah, tabbas ta san Saifullahi bai yi sa’ar mace ba, dan kuwa Ayush sam ba macen arziki ba ce, ga kuɗin ga wayewar amma babu hali bare a moru da ita, ita sai da so samu ne da Saifullahi ya duba ya nemi wata diyar masu hannu da shuni, ko da kuwa nan cikin Zaria ne ba sai ya kai Kano ba, tunda diyar Kanawan ba ta zo da halin kirki ba.12 Da wannan tunanin ta ja jikin ta ta koma na ta bangaran kafin Aysuh ta fito ta Bata rabon ta. Daren ranan duka gidan kwana aka yi ana gulmar Saifullahi da matar shi, dan kuwa zagi da ihun ta babu wanda bai ji ba. Ita kuwa Amatullah fama ta ke da period da ya yi mata bazata tsabagen tashin hankalin da ta shiga na rashin Emjay. Washagari duk yanda Ayush ta hargitsa gidan domin neman maganin nan, sama ko kasa ba ta gani ba. Hauka ne kawai ba ta yi ba. Gashi tun daren jiya ta ke neman wayar Jamila amma ta kasa samu, sai da yamma dabara ta zo mata, ta kira gidan su ta ce da Mahaifiyar ta dan Allah ta tura ko da driver ne gidan Jamila ta na so ta yi magana da ita amma ta kasa samin ta. Mahaifiyar ta ta tambaya lafiya? Ya ta ji muryar ta haka. Ta na mai tabbatar mata lafiya lau kawai dama da sakon da za ta tura mata ne amma ta ji ta shiru. Da wannan ta amince ta tura driver gidan Jamila amma ya tarar ba ta nan. Hakan ya sa Ayush kara tsanan Saifullahi, ta kuma sha alwashin ba za ta kara bari ya kusance ta ba matukar ba maganin nan ta samu ba. *** Sati biyu da rasuwar Emjay Amatullah ta koma makaranta, duk abin da take babu wani walwala dan kuwa har lokacin ba ta daina kukan rasuwar ɗan na ta ba. Cikin dare ta sha kukan ta kenan yanda ta saba kafin ta yi bacci ta ji wayan ta na kara. Da kamar ba za ta ɗaga ba daga bisani ta sake shawara ta daga. Gaban ta ne ya fadi jin muryar da ya bakunci kunnen ta ya na mai faɗin “Assalamu Alaikum” Ta na mai gyara kwanciya, murya dashe ta amsa da “Waalaikumus salam” “God kar dai har yanzu kuka ki ke yi? Um Mama nah?”2 Yanayin muryar tashi da kuma yanda ya ke mata maganar ne cike da rarrashi ya sa ta kasa amsa masa ta na mai runtse idanu. Babban farin cikin ta tun bayan rasuwar Emjay shi ne labarin musuluntar shi da ta ji Baba Anas Yana yiwa Baba Salihu bayan dawowar shi satin da ya wuce.2 “Amatullah…..” Ya sake kiran sunan ta. Amatullah ta masa da “Um” Ya furta “Ki yi hakuri Mama na….” Shiru ne ya ƙara biyo baya, dan kuwa wani nauyi da kunyar Dee ta ke ji na babu gyara babu dalili. Dee kuwa da ya san ba amsa masa za ta yi ba ya kara da “Dee ne sorry I called you this late,I couldn’t help it, you keep crossing my mind. Amatullah I’ve been trying to stay away from you kasancewar sai kin gama idda” Cikin zuciyar ta fadi take ‘na kusa gama Idda Dee, na yi period har sau biyu bayan mutuwar aure na, na ƙarshe nake jira’ Azahiri kuma shiru ta yi masa, sai murmushi kawai ta ke tamkar ya na ganin ta “amma abin na neman rikita tunani na, ba na so na rasa ki a karo na biyu duk da dai ban sani ba ko kina da wanda ki ke so already…….”2 Ji ta yi kamar ta na jiyo bugun zuciyar ta tsabagen yanda gaban ta ke faduwa, idanun ta runtse yayinda murmushi ya bayyana a fuskar ta Jin Dee ya ce STORY CONTINUES BELOW ” Idan ma akwai, I will still fight for sai in da karfina ya kare, please let me know idan kin gama idda sai na zo mu yi magana idan kin amince sai na tunkari tsoho mai ran karfe da sojoji na, I love you Amatullah, I still do. Allah ya tashe mu lafiya”2 Ya kashe wayar. Wani irin daɗi ne ya ringa ziyarta zuciyar Amatullah yayin da maganar Dee ke mata shawagi cikin kwakwalwar ta2 “I love you Amatullah, I still do” Tun bayan rasuwar Emjay Amatullah ba ta sami baccin kirki ba sai a daren ranar. Ta yi bacci mai nishadi, cikin dare ta tashi ta yi nafilan dare ta yiwa Emjay addua tare da neman taimakon ubangiji akan maganar Dee.2 **** Kamar yanda Amatullah ta tashi cikin walwala, haka Aysuh, dan kuwa ta samu Jamila ta turo mata maganin nan fargaban kar Saifullahi ya mata bazata irin daren rannan ya kau, dan tun ranar ba ta kara yarda sun hada shimfida ba. Gogan na ta kuwa tun da garin Allah ya waye ya je kofar gida ya zauna, ya kasa ya tsare ya na jiran fitowar Amatullah ko ya ganta ya sami sanyi cikin ran sa. Ile kuwa sai gata ta fito cikin shigar nan nata da ta saba. Ganin ta ya tashi da sauri ya na faɗin “Amatullah an fito?” Fuskarta babu yabo ba fallasa ta amsa da “Eh, ina kwana ya Saifullahi?” Ya na murmushi jin dadin yanda ta amsa masa ya karasa gaban ta, tare da faɗin “Lafiya lau, kin tashi lafiya? Ya karin hakurin na mu?” “Alhamdulillah” Ta amsa a takaice. Saifullahi be gushe ba ya ce “Amatullah ina so ki san na yi matukar bakin cikin rashin ɗan mu, Amma babu komai Allah da ya karbi Emjay zai ba mu wani in Sha Allah”5 Daga idanu ta yi ta kalle shi jin kalaman shi na karshe, ganin yanda ta ke kallan sa ya gyara tsayuwa ya ce “Wato Amatullah ina so ki yi hakuri ki mance rayuwar da mu ka yi a da, ki sani cewa na yi nadamar duk kurakurai na, haka kuma na yafe na ki kurakuren, ina fatan za ki yafe nawa, ya kamata mu sasanta mu gyara zumuncin mu, abin da ya wuce ya wuce…..” Fuskarta ɗauke da murmushi irin na ya ke ta ce “Ya Saifullahi na makara, bari na tafi makaranta dan Allah” “Oh maganar tawa ba ta da muhimmanci Amatullah?” Kai ta girgiza tare da faɗin ” Ko kusa ba haka na ke nufi ba” Amsar na ta ya bashi damar faɗin “Na sani Amatullah, na san ki na so na, kamar yanda ni ma na ke son ki, duk abin da ya faru tsakanin mu sharrin shedan ne”2 Nan zaton Amatullah ya tabbata, na Saifullahi ya ɗan fara samun matsala sanadiyar rikicin matar shi, dan shi ne kadai bayanin yanayin da ya ke ciki. Sai a sannan ta lura da lalacewar da yayi, yayi baki ya rame. Ta na mai kallan agogan hannun ta ta ce2 “Ya Saifullahi na makara, bari na tafi” “Toh ko na sauke ki ne……?” “Toh tantabara uban Alkawari! Idan ka gama yamadidin ka zo ina jiran ka!”2 Cewar Ayush, wacce ta leko ko mayafi babu bare hijab sanye cikin kananan kaya riga da siket. Hannun ta rike da kugu. Kallo ɗaya Amatullah ta yi mata cikin ran ta tace ‘eh lallai wayayye sai wayayyiya’4 A zahira kuma kallon Saifullahi ta yi, wanda kunya da takaicin Ayush ya lullube shi kamar kasa ta tsage ya shige, ta ce “Ah ah ba dumuwa, zan tafi kawai, na gode” Ta juya ta yi tafiyar ta, ta na jiyo Ayush na faɗin “To ko za ka bi ta ne? Ina ga kai ka ce bagidajiya ce amma ji yanda ka ke makalkale ta kamar bunsuru!”2 STORY CONTINUES BELOW A fusace ya nufota ya na fad’in “Ni ne bunsurun Aisha? Me ya sa ba ki da mutunci ne ke” Ayush ta shige ciki da sauri Saifullahi ya bita ya na faɗa tamakar mahaukaci. Jama’ar gidan har sun saba da ya wuce sai a bishi da zunde da baki, su Baban Sasa kuwa suna sane su ka masa kunne uwar shegu, babu mai shiga lamarin sa tun ranar da yayiwa baban Sasa dibar albarka har ta kai shi ga kwanciyar abisibiti.2 *** Hutun mid semester ta dawo bayan sun shafe sati tara suna karatu,ganin zarya daga amaru ba zai fishe ta ba ya sa ta koma wajen mimi suke zaune a ɗakin ta, sosai ta ke jin sassauci na damuwar rasuwar Emjay, da taimakon Mimi, da addu’a har ma iyayenta ta samu ta ɗan ribaci damuwar. Zaune take tana taya Mama gyaran Alayyaho yaro ya shigo ya sanar mata da saƙon Baban Sasa. Ba ta kawo komi ba ta isa gareshi amma ganin Saifullah, Baba Anas, Baba Salihu da Baba Zubairu zaune ya sa ta ɗan sha jinin jikinta. Gaida su tayi sannan ta samu waje ta zauna cikin zulumin kiran da ake mata. “Amatullah!” Baban Sasa ya kira ta ya na mai kallon ta. “Na’am” Tace cikin sanyin murya. “Mijinki ya zo ya same mu nan ya ce ya maida aurenku, kamar yadda musulunci ta bashi damar maida aurenku. Ki yi hakuri, ki rungume ƙaddararki ki cigaba da biyayya. Ubangiji Allah ya miki albarka ya dubi gabanki da bayanki” Baban Sasa ya ce yana mai yin fuska irin na tausayi da rokon alfarma ta amshi bukatarsu.4 Shiru ya biyo bayan wajen, murmushin da ke fuskar Amatullah ya sanya ma Baban Sasa saukin raɗaɗin da yake ji na ganin kamar bai kyauta mata ba, don shi burinsa ɗaya ya buɗe ido ya ga Amatullah da Ɗan Yusuf a matsayin ma’aurata, ɗazu kamar ya taya ma Dee da ya kawo masa ziyara amma baya son abin da zai sa a gaba ya kalli Amatullah da wannan duban, hakan ya sa ko da wasa bai taɓa yi ma Dee yusuf maganar ta ba shi ma bai masa ba. Bayan fitar Dee ne Saifullah ya shigo masa a fujajan ya sanar masa ya maida auren Amatullah, tunda yana da yaƙini ba ta fara jini ba, yanzu kila ta fara tun da ba shayarwa take ba. Bai amsa masa ba sai da ya tara iyayensa sannan ya aika a kira Amatullah. “Yanzu sai ku natsu ku fahimci juna tare da tsaida ranar tariya” Baban Sasa ya ƙara ganin tayi shiru tana murmushi.1 “Baban Sasa ai na fita idda tun sati uku zuwa huɗu da suka wuce” tace tana sunkuyar da kai haɗe yin murmushi mai sauti. Ajiyar zuciya Baba Salihu da Baba Anas su ka yi a tare. “Ƙarya ta ke wallahi Baba, ai mace bata al’ada in tana shayarwa kuma bai isa a ce tayi tsarki uku bayan rasuwan Emjay ba” Saifullah ya ce a rikice. “Na rantse da Allah” tace cikin ƙara gaskata kanta. “Baba a kira Mama ita ce shaida, tun Emjay na da wata shida na fara, kuma ban taɓa tsallake wata ba” tace tana mai neman agajin Allah don gaba ɗaya bata yi tunanin zai ƙaryata.2 “Kwantar da hankalinki Amatullah, rabu da shi da guntun jahilcin da ke ɗan tafiya da shi” Baba Anas yace yana mai jan tsaki a ƙarshe. “Ke haka ake yi ba sanarwa, ai sai ki faɗi gudun faɗawa halaka” Baban Sasa ya ce yana mai jin wani iri a zuciyarsa, ba zai ce yana cikin farin ciki gaba ɗaya amma tabbas ya dawo daga rakiyar auren Saifullah da Amatullah.4 “Yanzu ai shike nan, tun da kin gama idda ke ce ke da damar zaɓa ma kanki miji, muna masu baki shawara da ko ji tsoron Allah yayin zaɓenki. Allah ya tabbatar da Alkhairi” Baba Anas ya sake faɗi, nan saura duk suka mara masa baya. Mutuwar zaune Saifullah yayi, ya rasa ina zai tsoma kansa, kallon su yake kamar mai neman ɗauki. Gaba ɗaya rayuwa ta tsaya masa chak. Ta ina zai fara, ya san ba yanda za a yi Amatullah ta saurare shi, kamar ba wata hanyar da zai sa a mata dole. Hakan ya sanya bai ko san sanda Amatullah ta fice daga ɗakin ba, dawowa yayi daga duniyar tunani ya iske babu Amatullah ba mahaifinta a ɗakin.2 Ba ƙaramin natsuwa ta samu ba ganin babu wanda ya tursasa ta akan amince ma Saifullah, da farin ciki ta baro ɗakin, ba ta yi tafiya mai nisa ba Mahaifinta ya tsaida ita, shi kanshi yayi farin ciki da ganin farin ciki kwance akan fuskar ƴar sa. “kiji tsoron Allah Amatullah, in kin tabbatar da saki uku ya miki ki sani babu sauran halaccin zama tsakaninku har sai kin yi wani auren, amma in dai shi ke da gaskiya kiji tsoron Allah, kada ki haramta masa abin da Allah ya halalta masa, babu mai miki dole” yace mata suna masu jerawa zuwa sashin su. “Wallahi Babanmu sau uku yana furta cewa ya sake ni” tace cikin shagwaɓa. “toh shi kenan. Allah yayi albarka” yace yana murmusa mata. “Aameen Yaa Rabbi” *** Tun kusan sati biyu da ya wuce ya kamata Ayush ta ga period din ta, Amma shiru ta ke ji, abu tun ba ya damun ta har ya fara ba ta tsoro. Babu shiri ta kira Jamila ta shaida mata halin da ta ke ciki, ta kare da “Wallahi idan har cikin Saifu na ɗauka sai na zubar!”2 “Dole ki zubar Ayush, ko ni ba zan ba ki shawarar haihuwa wannan gidan en kauyen ba!” Cewar Jamila cikin jaddadawa. Kana ta kara da “Kin san Allah tun wuri ki nemi pregnancy test strip, da kin ga positive ki kira ni, kuma kar ki bari kowa ya sani, in da hali ma ki fita ki samo da kan ki” Aysuh ta tashi cikin sauri kamar wacce aka tsikara, ta ce da Jamila “Yanzu ma kuwa” Ta kashe wayar. Cikin kankanin lokaci ta samu ta shirya, ta yi ficewar ta ba tare da ta faɗawa kowa ba. Sai da ta taka da kafar ta har zuwa titi sannan ta samu chemist ɗin da ta siya. Da kyar ta iya dawowa gida tsabagen gajiya. Sai kuma da ta dawo tsoro da fargaban result din ya sanya ta kasa yi nan ta ke, ta yanke hukuncin bari sai da safe ta na tashi daga bacci dama ya fi ba da sakamako mai kyau. Daren ya mata tsawo sosai, a kan kunnuwarta aka yi kiran sallah farko, cikin sauri ta shiga bahaya ta yi fitsari tare da tsoma tsinken gwajin. Ganin yanda layuka biyu ke ƙara fitowa raɗa raɗa ya sanya ta firgita, Sam ta manta cewa sun yi da Jamila akan kada wanda ya sani. “Wayyo! Saifullah ka cuce ni, Allah ya I’d shege tsinanne” ta ce iya ƙarfinta tana sakin robar fitsarin a ƙasa. A firgice ya tashi ya nufota yana tambayar lafiya, ransa duk a jagule saboda tabbacin ahlin gidan sun gama jiyo ta. Idanunsa suka fara sauka a tsinken gwajin sakamakon ya fito raɗoraɗo a kai, bai san lokacin da ya sa hannu ya ɗago ta tare da haɗa ta da jikinsa ba, dukansa take ta ko ina tana zagi don gaba ɗaya cikin da ta tsinci kanta da shi ya fi kibiya zafi a ƙahon zuciyarta.Ban kyauta ba na sani Babe, kin dai san ke nake so, ki yi shiru ki faɗa min abin da kike so ayi, yanzu kina ihu cikin dare kowa zai san ciki gare ki kuma ba za mu iya ɗaukan ko wani mataki ba” yace mata cikin raɗa, sai a lokacin ta tuna zancen ta da Jamila, take ta haɗiye duk wani kuka da kururuwa da ya ke zuwa mata. 2 “Ba wai bana son haihuwa da kai bane honey pie, Kai ma ka san son da nake maka ya sa na bar kuɗi da jin daɗin rayuwa don na kasance tare da kai” tace ganin ya bata goyon baya, ita kanta ta san wasu abubuwan da take masa ne ya sanya ya ke mata abin da ya ke mata, itama ba yin kanta bane, shi ya kulle ta a akurki. 2 “Na sani babe, amma ai baki taɓa natsuwa kin min bayani ba, na taɓa hana ki abin da kike so ne?” ya sake fadi bayan ya janyeta daga bahaya zuwa cikin ɗakin ta su ka zauna a kan gadonta. 3 “Tell me what you want babe, your wish is always my command your highness” yace mata yana kallon cikin idon ta. Nan ya mata kwarjini sosai ta kasa cewa komi, shiru tayi ta sunkuyar da kai amma tunawa da tayi dama na zuwa ne sau ɗaya in ta wuce dole sai mutum ya jira wata. 2 “A cire cikin nan don Allah, mu jira har mu koma gidan mu, ka ga a gidan nan wace tarbiyya zamu ba yaya, ko mun yi a ɗaka da ya shiga cikin gida za a wargaza masa” ta faɗi a hankali. Kiris ya ƙunduma mata Ashar, amma ya danne saboda in ya biye mata da faɗa shi ke da asara in ta zubar. 2 “Haka ne kuma fa, kinga ban taɓa tunanin nan ba, yanzu dai ki bari sai mu kai ayi flushing din sa out, this week will be a very busy week Amma I promise you ba za a wuce next week ba zai bi ma kwararar” yace yana rungumarta, ji yake kamar ƙaya yake runguma a jikinsa, tunanin dole ya nemo yanda zai shawo kan Amatullah yake don tabbas itace macen rufin asiri macen arziki. 6 Lallashinta ya dinga yi yana mata alkawura na ƙarya da in da kan aurensu ne toh tabbas za su zama na gaskiya ne. Kiran sallah na biyu ya tayar da shi daga gareta, alwala yayi ya gabatar da raka’atanil Fajr sannan ya wuce masallaci. Daga yanayin kallon da ya ga iyayensa na masa ya san tabbas sun ji muryar Ayush, addu’a yayi Allah ya sa Hakan ya sa su tausaya masa su maida masa da auren Amatullah. 2 *** Sati ɗayan da ya wuce babu abin da yake sai fafutukar son Magana da Amatullah, kasancewar ta koma makaranta ya sanya abin ya masa wahala. A tunaninsa hostel take, sai ya kwashi jiki ya je gaban Amina hall ko Ribadu hall ya zauna yana ƙirga masu shiga da fita hostel ɗin. 4 Ganin hakan bai cika masa burinsa ba ya koma zaman faculty of pharmaceutical sciences. Nan ma haka yake ƙarasa shawagin sa ba tare da ya ganta ba, sau biyu yana hango ta a aji suna ɗaukan darasi nan zai hakince ya jira amma kamar wacce ke rufe ido ba ya sanin lokacin da suke ficewa. Asali duk zuwan shi Mimi ce ke ganinsa sai ta fitar da su ta wata ƙofar ba wanda ya ke jira ba. “Ai nan gani nan bari malam” takance a ranta a duk lokacin da ta hango shi. 7 Ya kan kira Amatullah amma in zai kira sau ɗari ba ta ko ɗagawa, haka saƙonni daban daban na ban hakuri, soyayya da alkawari duk sai dai ta karanta ta share. Yau ma kamar yanda ya saba ya shigo sashin na su, ya iske suna karatu, nan ya nemi izinin malamin akan yana son ganin matarsa. Amatullah bata an kare da shi ba sai ganin da tayi yana nuna ta da yatsa. STORY CONTINUES BELOW Nan malamin ya kalle ta ya ce ” Oya Go and meet your husband” ji tayi duk wani bakin ciki ya taru ya tsaya mata a maƙoshi, niyyarta ta ƙaryata saninsa amma tunawa da tayi kallon matar aure ake mata har lokacin ya sanya ta mike jiki a sanyaye. 2 Tana fita ta tsaya a kansa ba tare da tace kanzil ba, “Don Allah muje ki bani minti ɗaya kacal, don Allah ba don ni ba” yace kamar zai mata kuka. Da har za ta juya sai kuma wata zuciyar tace da ita ta bishi. Sun Kai daidai matakalar benen da za ta saukar da su ƙasa su ka ci karo da Dee ya hawo kenan. “Cutie ina zuwa ne haka, Prof ya fita ne” yace yana mai tsare ta da idanu yana mai isar da wani irin saƙo mai narka zuciya. Murmushi ta yi tare da raɓewa gefe, ita ba ta sauka ba ita ba ya juya ba.2 Waigawa yayi ya ga Saifullah ya tsaya yana huci kamar kumurci. Dawo da kallonsa yayi gareta ya na mai murmushin da ke rikitata ya ce “okay Mamana” yace yana mai sunkuya mata kamar mai ladabi haɗe da nuna mata hanya ta wuce. Sai da ta zo daidai saitinsa sannan ya ce “I love you” cikin amon da hatta Saifullah da yaji sai da tsigar jikinsa ya tashi saboda sanyin da amon ya fitar. 4 Tsaki ya ja yayi gaba, Amatullah kuwa da yake jin kanta kamar wacce ke yawo a gajimare da kyar ta iya kai kanta ƙasan bene inda Saifullah ke tsaye. “Kar dai ki ce iskancin da kike kenan a makaranta kina zubar da mutuncin hijabi” yace a hasale 2 “ka ga ai wainda ba sa son ganin iskancin ba su biyo ni ba, lafiya kake nema na” Tace cikin tsiwar da ita kanta bata san tana da shi ba. Kallon ta yake cike da mamaki, don shi a iya zaman da su ka yi na shekara biyu a matsayin mata da miji zai rantse ko Yatsa aka sanya mata a baki furzarwa za ta yi ba za ta ciza ba. 4 “Ki dubi girman Allah ki amincewa son da nake miki, Amatullah wallahi duk lalacewana ba kamar tubabbe ba wanda ba tabbas a musuluncin sa, wallahi Amatullah warin Arnanci yake dana wuce shi” yace yana mai rage murya zuwa na mai roƙo. 4 “Allah” tace a mamakance. “Wallahi kinji na rantse miki” yace yana yar dariya, itama taya shi dariyar ta yi kana ta ce. 2 “ni kuwa sai nake ganin kamar warin nan ya fi komi tafiyar da tunani na, amma dai ka bani lokaci zan yi istikhara akan aurenmu. Kuma ka ga jarrabawar mu na kusanto mu, zuwa dai ƙarshen semester dinnan sai mu tsayar da magana. Bari na koma aji kar na rasa da yawa” Juyawa tayi tana kai aya. Farin ciki sosai ya shiga yi, don gaba ɗaya ya hango nasara ne a cikin haka. Tayi dan tafiya kaɗan ya ɗan ɗaga murya ya ce “Don Allah a dinga ɗagan waya” Kai kawai ta ɗaga ta wuce abin ta. Addu’a ta ke ta sake ganin Dee don tun da ya kirata din nan ba ta sake ji daga gare shi ba, ya kan aiko mata da kyaututtuka da gaisuwa daga Mimi amma bai kira ta ba balle ya nemi ganin ta. Addu’ar ta bata amsu ba don bata ganshi ba, aji ta wuce ta iske malamin ya fita, Mimi kuwa kallon tuhuma take ta mata, sai ta bata dariya. “Kin san tun last week yake zarya” Mimi tace tana yamutsa fuska. Dariya Amatullah tayi ta ce “Wallahi ba ki da kirki, baban babyn naki” “A’a fa shi da kanshi ya ce ba na shi bane, atoh!” nan din ma dariya Amatullah ta yi sosai, ita kuwa mimi cunkus tayi kamar za ta fashe. 2 “Wai har period nawa ake a gama waiting period din ne” Ta tambayi Amatullah cikin tuhuma, dariya tayi ta ce. STORY CONTINUES BELOW “Wani waiting period kuma, ba ki ga sai samari nake yi ba, ai yanzu yanda kika san iska haka nake free” tace tana mai shagala hannu ta wuyan Mimi. Ita kuma ba ta ce komi ba sai wayar da ta kara a kunne. “Kasan Allah Dee ta gama, ka tsaya kana kallon har kwaɗo ya maka ƙafa” 2 ta ce tana katse wayar, ba ta ce ma Amatullah komi ba, ta haɗe littafanta ta saka a jaka, ta fice daga ajin a nufin ta yi fushi. Cikin sauri ta bi ta, tana mata magiya. “Ai na ga baki da kirki ne, and I wanted telling you something, shike nan kowa ya riƙe sirrin sa” tace tana fisge hannun ta da ta kamo. “Nooo Mimi, wallahi ba haka bane, kiyi hakuri, kin san dai a kan Dee na san soyayya, kuma so ɗaya shi na ba, Haba ƙanwata” tace tana mai rungumarta. 2 Dariya Mimi tayi kana ta ce “Laa ilaha illah Allah Muhammad Rasulullah, tabbas babu addinin gaskiya sama da musulunci, na yi imani da Allah ɗaya ne kuma Annabi Isah Annabin Allah ne ba ɗansa ba” 10 Kuka Amatullah ta saki, kuka sosai take tana rungumar Mimi. 2 “Muje Mimi kiyi wanka, Mimi kin musulunta, Mimi yanzu duk wani zunubi da kika aikata an yafe miki, Mimi littafinki sabo ne dal babu datti ko ɗaya a ciki” Amatullah tace kamar mai sumbatu, abin da bata taɓa tunani ba, bata taɓa taya ma Mimi musulunci ba tana dai ƙokari wajen haska mata ni’ima da ke tattare da musulunci. 2 “Wai tun yaushe kika niyyata” tace mata yayin da su ke tafiya. “Tun bayan musuluntar Dee, sosai yake bani littafai na musulunci ina ganin babu addini da ya daraja mutum sai musulunci, it’s a religion full of humanity. A musulunci fa na ga in kana son ka ci nasara sai ka sa wani yayi nasara, a musulunci na ga yanda ake bayani akan duk abin da ya shafi rayuwa, daidai da yanda za a zauna a toilet. Maman Emjay sai in na yi comparing da halin musulmi sai naga gaba ɗaya ya sha bambam da abin da ke littafansu. 2 Dan zaman da muka yi da ke, naga yanda kike da tsantsan amana, idanunki basu taɓa rufewa akan abin da zaki samu ba balle ki hillace mutane ki samu, naga abubuwa da dama kina kamanta yanda aka siffanta manzo SAW ne, sai na yarda da cewa, lallai musulunci ba halin musulmai kaɗai za a duba ba, a karanta a Santa sai a kamanta. 2 Dee ya taɓa ce min in duniya sun haɗu suna aikata abu, ba zai taɓa canza haram ya zama halal ba, abubuwa dai da dama mai cike da jinkai na gani a musulunci” Tun da ta fara Amatullah ta ke kallonta, zuciyar ta fal da farin ciki, godiya take ma Allah har su ka isa. 2 *** Ayush ta gama amincewa da kalaman Saifullah, hakan ya sanya gaba ɗaya ba ta tuna ta nemi Jamila ba har sai da ta ga an yi satin da ya ce aiki zai masa yawa, an yi na biyu ana sati na uku sannan hankalin ta ya tashi. “Saif ni kam wai me muke ciki ne” tace bayan ta tsaya jiran sa har ƙarfe sha biyun dare da ya kan shigo mata gida. “ki duba ki ga fa yanzu nake dawowa, na gaji aiki ne sai godiya wallahi, amma ki shirya jibi inshaAllah sai mu je” yace yana wuce ta zuwa ɗaki. Bata musa masa ba ta amince. Haka su ke rayuwar su, ba a sake jin su ba amma kuma ba wai suna cikin jin daɗi bane. Ko da ta ga an ƙara kwana huɗu sai ta kira jamila, ba ta ɓoye mata komi ba ta faɗa mata. 2 “Amma ban san ke ɗin wata bi can bace sai yau wallahi. Aka ce miki zai amince ne, kuma kin san ƙarin sati huɗun nan ƙarin wata ɗaya kenan. Gobe zan aiko miki da maganin nan” tace a hasale. 2 “nagode Jamila you are indeed a savior” tace cikin farin ciki. 2 Washe gari ko da aka yi azahar an Kira ta saƙonta da aka sa a filin parking ya iso zaria, cikin murna ta figi motar ta taje ta amso. Sai da ta karanta takardar maganin sannan ta haɗiye guda biyu ta je ta kwanta. STORY CONTINUES BELOW Tun tana tsumaye ta ji shiru ba ta ga komi na fita daga jikinta ba. Haka ta yini kwance tana jira, da ta gaji da jira kuma ta fara dubawa nan ma shiru ba komi. Ganin har an kwana an tashi cikin bai motsa ba ya sanya ta ɓalle kwayoyi huɗu ta jefa a baki bayan ta gama cin kalaci. 2 “in aka yi azahar baka fita ba don uban ka sauran huɗun zan haɗiye” tace tana ajiyewa kusa da ita. 4 Bacci ne yayi awon gaba da ita, cikin bacci ta fara jin murɗawan ciki kaɗan kaɗan, ta ɗauka duk wasan yara ne sai da taga gaba ɗaya ta kasa motsin kirki, ga jini ya ɓalle mata ga bayanta ya riƙe sosai. 2 Da kyar ta ɗago wayarta ta kira saif yana ɗaga wa tace “zan mutu Saif zan mutu” “Hello! Hello!!” yake faɗi amma ina bakin nata ya ɗauke gaba ɗaya. Hakan ya sa shi zuwa gidan cikin sauri, ko da ya ido a sume ya ganta cikin jini, ɗaukan ta yayi ya fice ba tare da nemi ɗaukin kowa ba. Asibiti mai zaman kanta nan kusa da su ya kaita, babu ɓata lokacin aka fara dubata. Addu’a sosai yake yi da fatan Allah ya sa ta tashi don bai san me zai ce ma iyayenta ba in ta mutu. Awa uku yayi zaune yana jira kafin likita ya fito ya nemi ganin sa a ofishin sa. “Gaskiya akwai abin da ta sha da ya nemi ɓarar da cikin jikinta, an yi hoto cikin na nan ɗan sati goma sha biyu da kwana uku. Sai ta huta sosai, sannan sai ta kiyaye abin da za ta dinga kaiwa bakin ta saboda lafiyanta da na yaron” yace masa bayan sun gaisa 2 “Na gode Dr.” Saifullah yace yana miƙa masa hannu. Sai yamma lis suka koma gida bayan ta sha ledan ruwa ta dawo da ƙarfinta kaɗan. “Don Allah Ayush kiyi hakuri, kinga garin gajen hakuri kin sa rayuwarki a hatsari. Gobe nake da niyyar kaiki fa, amma kin kasa yarda da ni, yanzu Dr yace any attempt is a threat to your life” yace yana share kwalla, shi hawayen farin ciki yake na yanda Allah ya kare masa ɗan cikin sa, ita kuwa gani take hawayen so da tausayin ta yake yi. 2 “Naji, amma gaskiya mu bar gidan can, na tsani gidan ni shine kawai damuwata da kai” tace a wahalce. “daga kin haihu zan kama mana haya, it’s a promise. Yanzu kiyi hakuri, ko don samun masu miki hidima ki yi hakuri” haka ya dinga bata baki har su ka isa gida. 2 Nan ya shiga ɗakin hajiya ya tasa su Najaatu ya sanya su gyara gidan da sanya turare. Suna kammalawa ya sa su yin girkin da za su ci. Ba su suka samu kansu ba sai wajen bakwai na dare sannan suka sallame ta ba tare da sun bata ki cokali ta lasa ba. Tun daga ranar Ayush ta maida Najaatu mai aikin ta Sam babu kyautatawa balle tausayawa. A rana sai ta mata girki kala biyar, kala shida ita ba a bata taci ba sannan Ayush ba lallai ta ci ba, a ƙarshe sai ta iske a wanke wanke an ajiye ta wanke raguwa. 2 Ba ta taɓa fadi ba amma ta fara ba almajirai raguwan abincin da ta gani cikin wanke wanke. Haka ya faru yau, ta yi farfesun kifi, tun yanka biyu da Ayush ta ci ta ajiye saura, Saifullah da ya zo ya dan taɓa kaɗan aka bar kifi cikin tukunya. Ko da Najaatu ta ga tukunyar a cikin wanke wanke sai ta fita ta nemi Almajirai ta basu da sauran cuscus su sake. Ta shigo da tukunyar kenan Ayush ta fito inda take wankewaken ta ganta da tukunyar abinci. Ba ta tambayi ba’asi ba kawai ta fara dukanta, duka sosai ta ko ina. “Shegiya ɓarauniya meye na kwasan min abinci ki kai ma mayunwaciyar uwar ki, ba cewa nayi ki wanke ba? Ko baki nayi?” 4 tace cikin hayagaga wanda hakan ya tunzura Najaatu ta tunkuɗeta da faɗin “uwar ki dai na aika mawa” hakan yayi daidai da shigowar Saifullah da Hajiya da aka je aka faɗa mata kamar dukan Najaatu ake. 2 “Baki da hankali ne Naja, uwar wa kike kira haka, da kika tunkuɗeta in wani abin ya same ta fa?” ya ce yana taro Ayush. “ai ba laifin ta bane, ka ga wacce ke aiko min ita nan, kai ba zaman gidan nan kake ba, ni kuma bana son ka dinga ganin bakinsu wallahi kashe ni suke da niyyar yi” Ayush ta ce tana rushewa da kuka. 2 “Ke Naja me ya haɗa ku” faɗin Goggo da ta shigo Sasan don a idon ta Najaatu tayi rabon abincin. Tiryan Tiryan ta faɗi masu buɗe bakin Saifullah sai cewa “Toh in ba sata ba me kika yi? cewa aka yi ki ba almajirai, don ta ce uwar ki kika kai ma abincin ƙarya tayi? Ko ba ɗan kuka ke jawo wa uwarsa jifa ba” ya faɗi yana yunkurin marin Naja. 8 “Saifullah a kan ido na ta sake ma Almajirai” Goggo ta faɗi tana mai janye Najaatu. “Toh Goggo in ba hajiya ta kai mawa ba ai hajiya ta sanyata, gaskiya hajiya ki fitar da idon ki akan iyali na, ke kenan ki rasa wacce za kiyi gasa da ita sai matar ɗanki? Ina aka ce dole se na ciyar da ke tunda kina da miji, in dadin kike son ci mijinki ya miki itama mijinta ke mata Haba ” yace cikin tsawa tsawa, Hajiya mutuwar tsaye tayi tana nuna shi da yatsa. 4 ” Ni Saifullahi, ni ta kan mace? Allah ya isa nono… ” 2 ” A’a hajiya kar ki masa. Yi hakuri, muje don Allah ” Goggo tace tana kamo ta, sai a lokacin hajiya ta tuna goggo fa mahaifiyar Amatullah ce, kuma yanzu ita ce ke tallafo ta a lokacin da rayuwa ke shirin kayar da ita. ki yafe min, ina Amatullah ita ma na yi mata ba daidai ba, a yafe ni” 2 Cewar Hajiya ta na mai share kwalla. Kai Gwaggo ta girgiza ta ce “ah ah sam ban taɓa rike ki cikin rai na ba, balle kuma Amatullah da take ɗiyar ki, Allah ya yafe mana baki daya” 2 “Aameen ya Allah, na gode Allah ya saka da alkhairi, ya bawa Amatullah miji na gari” 2 Gwaggo na mai darawa ta ce “Ai kuwa dai Allah ya riga ya bata, sai dai fatan Allah ya ara mana rai mu sha biki” 2 Cike da mamaki Hajiya ta ce “Toh madallah, Aameen, ko gun su Baban yaran nan kin ga kuwa ban ji ba” “Eh ai dazun nan shi Baba Anas da Baban ne tare da mahaifin Amatullah su ka yanke hukuncin, idan Allah ya tabbatar nan da wata daya ma su ke so a yi auren” 2 Gwaggo ta karasa maganar daidai lokacin da su ka zo mararrabar bangaran na su. Nan ta yiwa Hajiya sallama tare da bata shawarar fita sabgar Saifullahi da matar sa. Ta bar Hajiya cikin tunanin ko wanene mijin da Amatullah ta samu haka? 2 *** Dee Yusuf kuwa tun da Mimi ta faɗa masa Amatullah ta fita idda ya ke mata naci, yayi yayi Amatullah ta dinga zuwa office din sa, ta ƙi, dan haka in dai ba shi da aji toh lalle za ka ga motar shi department din su Amatullah, ko kunya ba ya ji a matsayin shi na malami cikin makarantar. Duk in da aka gama lectures kuwa shi ne ke mayar da su gidan daliban da Mimi ta ke. 2 Kamar yanda su ka saba, zaune su ke dan harabar gidan Mimi, kasancewar waje ne mai sirri. Tun da ya ɗauko su daga makaranta ya lura da yanayin Amatullah, kamar ta na cikin damuwa. Amatullah ta na zaune da shi ne, Amma zuciyar ta tunanin wayar da ta yi da Baba Anas a safiyar ranar ne, maganar sa ke ta dawo mata cikin ran ta, “Amatullah na kira ne a matsayin waliyin auren ki da Baba ya bani, ya ba ni wuka da nama akan hukunci da hidimar auren ki, shin akwai wanda kuka sasanta? Idan akwai ki sheda masa muna so mu gan shi gobe idan Allah ya kai mu, bayan magariba in Sha Allah…..” 2 “Amatullah!” Da sauri ya dago ta na kallon Dee da ya kira sunan ta a karo na uku. “Wai menene?” “Babu” Ta bashi amsa a takaice. Shiru yayi ya na nazari akan ta, ita kuwa rasa yanda za ta tunkare shi da maganar Baba Anas ta ke “Maman Emjay stop behaving like a chikala! Please kin riga kin wuce wajan!” Abin da Mimi ta ce mata kenan lokacin da ta faɗa mata yanda su ka yi da Baba Anas, ta kuma ce mata ba ta san yanda za ta faɗa masa ba. Kamar wacce ake zaro maganar daga bakin ta ta ce “Baba Anas ya kira ni, ya ce ya na so ya gan ka gobe after magrib” 2 “A haba da Allah?” Cewar Dee ya na mai washe baki, cike da ɗoki ya ce “Halan cewa zai yi ya bani ke for better for better” 2 “In sha Allah” Cewar Amatullah ba tare da ta san sanda kalmar ya fito daga bakin ta ba. Hakan ba ƙaramin burge Dee yayi ba, ya ce STORY CONTINUES BELOW “Iyye ashe dai ana so ake ta ja min aji har haka” “Ayya mana Dee” Cewar Amatullah ta na mai rufe fuskar ta da tafin hannun ta. Ita dai duk sanda take tare da Dee ta kanji ta kamar ƴar budurwa, ta kasa gane yanda aka yi ya ke saka ta cikin wannan yanayi. “Oh ba ki Sona?” Ta girgiza kai alamar ah ah, Dee ya ce “no ban yarda da maganar kurame ba, tun da mu ke da ke ba ki taɓa furta kalmar so gare ni ba Amatullah, do you even love me?” Amatullah ta sunkayar da kai, ta ce “Yes I do” “Yes you do what? Look at me Amatullah” A hankali ta ɗago kan ta su ka haɗa ido. Idanun shi cikin na ta ya ce “Say you love me” Murya can kasan makogaro ta ce “I love you……” 2 Idanu ya lumshe sannan ya sake buɗewa, wani kyau da kwarjini ya ƙara a idanun Amatullah da ya sanya ta kasa daina kallon sa, wanda hakan ya sanya shi shagala da kallon kwayar idanun ta da ke sheki. Ya kara faɗin “Kara faɗa min dan Allah, Say you love me….” “I love you Dawood, I will always do with all my heart” 4 Idanun sa cike da kwallar farin ciki ya ce “Na sha mafarkin wannan ranar, kullum cikin kewar ki na ke, daidai da sakan daya ban daina son ki ba Amatullah duk da TAZARAR DA KE TSAKANINMU a lokaci” 2 Kasa ta yi da na ta idanun ta cike da nishadi da jin dadi. Ta ce “Thank you” “For what?” Fuskarta ɗauke da murmushi mai kayatarwa ta amsa masa da “For not giving up on me” Kallon juna su ke yi cike da so da kauna, haka su cigaba da soyayya cikin Jin dadi da annashuwa kamar ba za su rabu da juna ba a ranar. *** Washagari Dee ya amsa kiran Baba Anas in da ya umarce shi da ya turo iyayen sa a yi maganar aure. Ranar Dee har sujjada yayi ya godewa Allah. Mahaifiyar shi ya fara shaidawa kafin ya nufi Haɗeja gun dangin Mahaifin sa. Sun so ace Amatullah budurwa ce kasancewar Dee bai taba aure ba, Amma haka babu yanda za su yi su ka niki gari sai ga su a birnin zazzau, in da aka yi maganar aure, aka sanya wata ɗaya kacal ranar daurin aure. 3 Tun da aka saka ranar bikin Amatullah ta dawo gida, gun Mama ta sauka in da Mama ta shiga tsuma ta tana mata gyara na musamman kai ka ce wannan aure shi ne na fari. 2 Ana saura sati biyu aka kawo lefe, ita kan ta Aysuh hadiyar zuciya ne kawai ba ta yi ba tsabagen yawa da haɗuwan kayan lefan Amatullah, dan kuwa rabin sa Saifullahi bai yi mata ba. Ganin lefen ya sa ta ji ta na so ta ga Dee ta kuma san shin dan gidan wanene haka? 2 Saifullahi kuwa bai tabbatar da tazaran da ke tsakanin sa da Amatullah ba sai randa akan idanun sa Baba Anas ya karbi sadakin Amatullah daga hannun wakili Dee Yusuf. Kuka yake wiwi ba tare da ya damu da jama’ar da ke gurin ba, tsabagen takaici ranar sai da ya fara tunanin anya kuwa Baba Anas mahaifin sa ne? 6 Shi kuwa ango sanye cikin farar shadda ya sha dinkin babban riga da aka yi mata aiki da farar zare, da ka gan shi ka ga angon zamani. Nan gaban gidan ya tsaya tare da abokan sa ya kira Mimi ya ce ta fito masa da amaryar sa ba zai iya tafiya ba idan har bai gan ta ba. 2 STORY CONTINUES BELOW Amatullah da ta sha ado cikin farin leshi, ta yi kyau matuka har sheki ta ke. Jin umarnin Dee ta fara girgizawa Mimi kai, ita kuwa ta ce 2 “Toh ango yanzu za mu fito” Ta na aje wayar ta ɗauko farar lafaya ta ce da Amatullah “Oya we no go do hijab today, maza tashi ki naɗa mu fita Dee na jiran mu” “Ni gaskiya ba zani ko ina ba!” “Wallahi sai kin je!” Nan musu ya kaure har sai da su Mama suka sa baki, Mama ce da kanta ta nada mata lafaya, hannun ta cikin na Mimi su ka nufo kofar gida, ashe Dee ya shigo daga zaure, ya na ganin su ya karasa gaban Amatullah, ya janyo ta jikin sa ya rungume ta tare da faɗin “you’re mine Amatullah, you’re my halal!” 4 Mimi ta saka guɗa yayin da Amatullah ta ke kokarin zillewa daga jikin Dee cike da kunya. Yana dariya ya sake ta tare da fadin “Lalle akwai rigima Mama nah, dole fa ki saba zama jiki na” Cike da kunya Amatullah ta ce “Ayya mana!” Duka dariya su ke mata, yayin da su ka fito waje hannun ta cikin na ango, duk yanda ta so ta kwace ya hana ta. Saifullahi da ya ke waje tuni ya shige mota ya bar wajen ganin yanda Dee ke nan nan da Amatullah, ana ta daukan hoto tare da yan uwa da abokan arziki. A daren ranar aka kai Amatullah gidan Dee ke zangon shanu gidan ya tsaru ainun irin wannan ginin zamanin ne da ake kira aljannan duniya. Da Ƴan uwan Dee da aka kai amarya da su sun nuna karbuwar Amatullah gare su, musammam yanda su ke jin labarin ta gurin Dee da Mimi. 2 Sai bayan da kowa ya watse Dee ya shigo gidan shi kaɗai dauke da ledar sa na kaza da yourgot. Ganin har lokacin Amatullah ba ta daina kuka na shi ya sa ya zauna ya rarrashe kayan sa, dan ya tabbatar har da kuka rashin Emjay ta ke. Sai da ta yi shiru sannan ya sa ta dauro alwala su ka yi sallah. Kan ta ya dafa yayi mata addua tare da tambayar hukunce hukunce na game da wanka, da kuma abin da ya danganci sallah, ba dan ya fita sani ba kamar yanda ya ce mata, sai dan su kara karuwa da juna. Ita kanta ta yi mamakin yanda Dee ke bin kaidojin musulunci tamkar dama ciki aka haife shi. Yanda ya ga Amatullah ta na dan rabe rabe ya gane sam ba ta sake da shi ba, cikin dabara ya jawo ta falo, nan ya sata gaba sai ta ci abinci. Haka nan ta ɗan tsattsakura, cikin sauri ta tashi ta ce bari ta je ta kwanta. Maimakon ta shiga ɗakin sa, sai ta wuce na ta ɗakin . Bin ta yayi da kallo ya na mai murmushi a zahiri kuma cewa yayi “Amatullah ni mai hakuri ne, balle yanzu da babu wani tazara a tsakanin mu?” 2 Ya gyara zama ya na mai ƙara yiwa Allah godiya da hasken da ya bashi, lallai musulunci haske ne a rayuwar sa, haka zalika Amatullah haske ce a rayuwar sa, wannan shi ne haske kan haske. Amatullah kuwa ko da ta je ɗakin ta, wanka ta yi, ta sanya kayan baccin ta tabi lafiyar gado. Amma sai ta nemi bacci a idanun ta ta rasa duk da kuwa ta kashe wutar dakin. Kusan minti ashirin ta yi kwance ta juya nan ta juya nan. Jin alamar an buɗe kofar ta an shigo tuni gaban ta ya shiga faduwa. Ba ta gasgata shigowa Dee yayi ba sai da ta ji ya kwanta bayan ta ya na mai janyo ta jikin sa. Ta yi kokarin kwacewa ya ce “Shhhhhhhhh tsaya mana Mama nah, babu abinda zan mi ki” Yanda ya yayi maganar tare da kwantar da kan sa jikin ta ya sanya ta daina kokarin kwacewa. Cikin jin dadi Dee ya ce “That’s my Girl” Amatullah ta saki sansayyar ajiyar zuciya duk da har lokacin ba ta saki jikin ta ba. “Amatullah?” Amatullah ta amsa da “um” Dee ya ce “You know I love you ko?” Amatullah ta amsa da “um” “Owk, ina so ki saki jikin ji, just relax and sleep owk?” Jin haka ta ce “um” Amma cikin ranta cewa ta yi “Relax a ina bayan ka kamkame ni haka!” A zahiri kuma sai ta ɗan saki jikin ta, Dee na mai faɗa mata kalaman soyayya har bacci ya sace ta. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *