TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 2

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 2

A bakin gate ta iske abokan tafiyarta, nan su ka mata caa kowa da abin da yake tambayarta. “Cewa yayi yana sonki hala” shine tambayar da ya fi tsaya mata, Zulaikha dai bata ce komi ba don ta san ita ɗin mai laifi ce. “Haka kawai sai ya ce yana so na? A wajen photocopy fa muka haɗu kwanaki banda canji ya bada Naira 20 din ni shaf na manta ma” ta samu kanta da zabga ƙarya don bata son wani abu ya fito na abin da ke tsakanin ta da Dee. “Har na fara murna, don wallahi ko ni da nake matar aure ina kyasa Dee Yusuf, in fa ya ce yana sonki mu ɗin gaba ɗayanmu za mu shiga wani sawu na masu aji ne” Faɗin Zuwaira da su ke kira da maman Jaafar. Ajinsu ɗaya, a shekarun za ta girme su amma kuma ƙawarsu ce, yanzu ma kasuwar da za su shiga ita za su raka siyayya. Ba ta ce komi ba amma ita da ta san alkawarin da ke kanta ta san hakan ba mai yiwuwa bane ko da a ce shi ɗin kimtsattse ne ba tambaɗaɗɗe kamar yanda ta ke kallonsa ba. Da hirar Dee Yusuf su ka isa kasuwa, ita dai jin su take yi don ba su isa kasuwa ba har sai da kawayen ta su ka hasko kalan yaran da za su haifa in aurenta da Dee Yusuf ya tabbata. Daga kasuwa gidajensu su ka wuce suna fatan Allah ya Raya su zuwa sati biyu da karatun zango na biyu zai kankama. Sai a lokacin Amatullah ta samu ta keɓe da Zulaikha saboda su biyun hanyarsu ɗaya. “In kashe ni za a yi ma kawai a kashe ko? ke babu abin da yayi tsalle ya tsinka miki mari” Amatullah ta ce tana hararar Zulaikha. “Afuwan bibty, kin san na yi tunanin in na tsaya saura ma za su tsaya kuma ba zamu iya daƙile zancen ba, me ya ce miki?” ta ƙarasa tana mai neman karin bayani akan abin da ya wakana tsakanin kawarta da dodonta. “Me kuwa zai ce min, da na gaji da tsayuwa ba tare da ya ce komi ba na yi wucewata na bar shi tsaye” Amatullah ta samu kanta da yin ƙarya a karo na biyu. ‘wai me ye kike ɓoyewa ne’ ta samu zuciyar ta da faɗi. ‘ai sirri da daɗi’ ɗayan sashi na zuciyar ta ke bada wannan amsar. “Toh Allah shiga tsakanin nagari da mugu” ta tsinkayi zulaikha da faɗin haka. “Aameen” tace tana canza labarin su zuwa ga batun jarrabawar da su ka yi a ranar. *** Sai da la’asar ta shiga gidan su, nan ta iske yan uwa da iyayensu kowa yai mata murnar kammala jarrabawa da fatan samun nasara. “Baba mun dawo, ya karfin jikinka” tace yayin da ta shiga ɗakin baban Sasa, Shima addu’a ya bi ta da shi sannan ya ce da ita “Ina so na shaida aurenku Baiwar Allah! Na ce a kira min Saifu, don ba zan so ƙasa ya rufe ido na ban cika ba, tun da har Allah ya bani tsawon ran kaiwa lokacin da duk kuka isa aure” jin sa take yi yayin da idanunta ke kallon laɓɓansa yana faɗa mata su, sai a lokacin ta ga tsantsan kamanninta da shi, sai a lokacin ta ke yarda da zancen da ake na suna kama da Saifullah don tun tana yarinya ta haddace babu mai kama da Baban Sasa sama da Saifullah. “kin yi shiru Amatu” yace yana taɓo ta. “Baaba, ashe haka nake kama da kai” tace tana dariya ƙasa ƙasa, shi ma sai ya shiga dariya. “kin ga kenan duk wanda ya shiga gidanku zai tuna da ni ya min addu’a” ya ce cikin dariya. Haka su ka dinga tsokanar juna cikin nishadi, kiran sallan magariba ne ya tayar da ita bayan ta sa masa ruwan alwala a buta. *** Yana zaune a harabar sashin su a jami’ar kimiyya na gwamnatin ƙasar Rasha da ke birnin Moscow watau MATI Russian State Technological University Moscow, tattaunawa su ke yi da abokan karatunsa akan sabuwar injimin da su ke kerawa don wani baje koli da jami’ar ke shirin aiwatarwa nan da kwana biyar, a nan wayarsa ta ɗauki ƙara. Kamar ba zai ɗauka ba amma jin kiɗan da ya tanadar ma jininsa ne ya sa shi saurin ɗauka, tsoronsa kar a ce Baban Sasa ne ya rasu, don shi ya san son da yake ma tsohon nan ko iyayen sa albarka. “excuse me” ya ce yana mai zuwa gefe tare da tattara duk wani natsuwa da ya mallaka ya doka sallama bayan ya ɗaga. “Saifuna ba zaka dawo in ganka ba” yace cikin halin ciwo. “Alkawari Baba ba zan ƙara sati biyu ba, kai dai kar ka yarda ka bi su ko sun zo ɗaukan ka” yace cikin shaƙiyanci hakan ya sanya baban Sasa tuntsirewa da dariya. Ya tambaye shi jikin sa, da sauran ahlin nan ya amsa yana mai ƙara jin jinjina masa zancen zuwansa. A haka su ka yi sallama, ya koma wajen abokan karatunsa yana mai ba su hakuri. Kwana goma ya ƙara akan ranar da su ka yi waya jirgi ya sauke shi a filin jirgin sama na murtala Muhammad da ke birnin ikko ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare. Kallo ɗaya za ka masa ka san bakin fata ne duk da rinewar da fatarsa ta yi ya rikiɗe kamar wani bakin bature. Shi ɗin ba wani dogo bane sannan babu mai kiransa gajere, zanensa na mallawa na kwance a gefen fuskarsa hakan na ɗaya daga cikin abin da ke ƙara maida fuskarsa abin kauna ga mata kamar yadda wata budurwar sa ta faɗa masa. Daga ikko jirgin da ke tashi zuwa Kaduna ƙarfe shida na safiyar washegari ya bi, daga nan ya ɗauki shatar mota har Amaru. Babu zato su ka tsinkayi muryarsa yana sallama, nan gida ya kacame da murna, duk ihun da ake Amatullah na zaune a ɗaki bata ko motsa ba cike take da fargaba da tsoro, cigaba da karatun ta tayi a cikin littafin Nurturing Eeman in children na Dr Aisha Hamdan. Wannan shine ɗabi’ar da ta fi so in ba ta komi toh ta samu littafin ƙaruwa na addini ta dinga karantawa. *** Tun da ya shigo gidan idon sa ke kan yan matan da yake gani yana kasa kunnen wacce za a kira da Amatullah, dukkansu babu na yarwa saboda wasun su na da gaɓa-gaɓan jiki wasu kuma yan firit amma duk kyawawa ne daidai misali. Bai manta hotonta da ya gani ƙarshe shekarun goma da suka wuce ba, ko a lokacin ya san ita din mai kyauce da abokansa za su yaba da ita. Bare kuma yanzu da aka ce ta shiga Jami’a, ya san zai same ta da wayewa, dan shi a rayuwar sa ya na san wayayyiyar mace. Sunaye mabambamta ya ke ji ana kira duk babu Amatullah har dai ya hakura tare da sa ran ko tana makaranta ne. Washegari Zulaikha ta kawo mata ziyara tare da duba jikin Baban Sasa, sun fito za ta raka ta ne su ka ci karo da shi a ƙofar gida. Sun gaisa cikin mutunci su ka wuce yana mamakin yanda duk in da ya gilma cikin zaria mata sanye da zumbura zumburan hijabi, su wainnan ma abin takaici har da safa ko me su ke rufewa oho ‘watakila kutare ne’ ya samu zuciyar sa da fadin haka. Tsaki yayi ya cigaba da abin da yake a kan wayarsa, a haka ta dawo, ta sanya kafa ɗaya kenan a cikin gidan kenan ta jiyo muryar yar gidan goggonsu ta bayanta tana fadin “A’ah su Amatullah yan boko ne a garin” Hakan ya sanya ta juyowa cikin fara’a tace “A’ah su matan aure ne a garin” nan su ka sa dariya, Hakan ya zama sarar su duk suka haɗu sai su yi amfani da kasancewarsu abokan wasanta su gasa mata magana akan rashin aure da boko. Shi ke nan da sun kira ta yar boko sai ta kira su matan aure.7 STORY CONTINUES BELOW Gaida Saifullahi tayi ya amsa kamar ya haɗe su ya maƙure, bakin cikin da ya saukar masa ba ƙarami bane don kwata-kwata bai sa ma ransa ko a mafarki aure zai haɗa shi da bagidajiya ba. “Kai impossible!!!” ya faɗi Yana mai mikewa zuwa cikin gida don dai ya tabbatar wannan mai lullube jiki kamar raguwar kuturta ce matar da yake hasko su tare. Yaro ya gani a yana wasa a tsakar gida daidai inda yake wajen zaman baban Sasa, tuno murnar da yake ciki lokacin da ya faɗi albishir din haihuwan yarinyar da aka ƙaƙaba masa da ada murna yake amma a yau gani yake babu bakin fata sama da haka. “kai shiga ka kira min Amatullah” yace ma Yaron cikin tsawa-tsawa, a firgice Yaron yayi cikin gida yana mai kiranta. Sai da ta ɓata kusan minti talatin kafin ta fito wanda hakan yayi nasaran ƙara harzuka shi. Sanye take cikin hijabi ruwan bunsuru ko ganin atamfar da ke karkashi ba ayi, baƙar safa ce a kafafunta hannayenta duk suna cikin hijabi Hakan ya sanya babu abin da ya bayyana a gareshi face fuskarta. “Assalamu Alaikum” tace cikin sanyin murya, kallon ta yake, fuskar nan nata sai sheƙi yake yi saboda rashin hoda, amma hakan bai hana kyawunta fitowa ba. “ina yini” ta ƙara duk da kunnuwanta ba su ji ya amsa sallamar da tayi ba. Nan ma bai amsa ba, sai ta basar ta tsaya abin ta. Kallonta yake tun daga kai har ƙafa yana jin wani kyankyaminta na cika shi. “Kinga, this will be the first and the last time da magana zai haɗamu, you better find your self a husband, amma ba Saif ba!, ki sani cewa akwai Tazara a tsakanin mu! Bana na san kauyanci! Ba na san gidadanci!! Kinga malam Sambo da ya kika yi allo a wajensa, shi yafi dacewa da ke not an engineer” Yana gama faɗi ya tsidda miyau ya wuce ya barta a daskare. Da kyar ta iya jan kafafun ta ta shige gida, idanun ta cike da kwallar bakin ciki, shin ita bagidajiya ce? Toh me mai ta ma sa na kauyanci da gidadanci?. Abun da ta ringa jinjinawa cikin ranta kenan. *** Tun daga ranar ba su sake haɗuwa ba, ta kiyaye haɗuwarsu ta maida hankali a karance-karancenta. Yau ma kamar kullum zaune take tana karatun “You can be the Happiest woman in the world” na Dr. Aid Al-Qarni, ta baje a falonsu, sanye take da riga da skirt dinkin zamani da ya ɗame ta, nan ta jiyo sallamarsa, bai jira amsarta ba ya kutso ciki, wani irin tsalle tayi ta jawo hijabinta da ta sarkafa a jikin ƙofa ta shiga kokuwan sawa, da ya ke hankalin sa na bisa wayar sa da ya ke ta faman dannawa nan ta ci sa’ar sanya hijabin kafin ya ankara da ita, har dan nufashi ta ke mayarwa cike da godiyar Allah. Kallon ta ya ke cike da kyama ya furta “Ina goggon” “Suna wajen baban Sasa” tace masa. Har ya juya zai fita sai kuma ya sake dawowa, idanun sa kan ta ya kira sunan ta “Amatullah!”8 Daga idanun ta ta yi ta dube shi ba tare da ta amsa ba, irin kallan wulakancin da ta gani a idanun sa ya sa ta yi saurin kawar da kai. Bai gushe ba, ya cigaba da magana cike da nuna isa. “Ina so ki fahimce ni, ba na son ki ba na kaunar ki, sam ba ki min ba, akwai yarinyar da na ke so…..” Kamar takobi haka ta ji maganar ta shi ta soki kirjin ta. Shi kuwa ko a jikin sa ya kara da “dama biyayya ya sanya da zan yi jihadi na aure ki, toh amma sam ban yi tsammanin haka ki ke ba, ni wayayye ne, ina bukatar wayayyiyar mace cikin rayuwa ta!! Na tabbatar cikin samarin unguwar nan ba za a rasa local champion da ke son ki ba, ki rufa ma kan ki asiri ki fito da shi, na tabbatar idan su ka ga dukkannin mu da wanda mu ke so, Baban Sasa zai janye wannan alkawari na shi mai muni, kin gane ko?” Har ya kare maganan shi idanun Amatullah na kan ƴan yatsunta da ta ke wasa da su, tun da take a rayuwarta ba’a ta taba wayan gari ta na ƙin wani ko wata cikin ran ta ba, sai na wannan bawan Allah da ake shirin ɗaura ma ta aure da shi, ba don komai ba sai don kyama da ya nuna kiri kiri gare ta. “Ba da ke na ke magana ba?”11 Shiru ta masa kamar ma ba ta san yanayi ba wanda hakan ba karamin sosa ma sa rai yayi ba, Wai yarinya bagidajiya bakauyiya sai shegen girman kai da jin kai. A fusace ya furta ” Wato ki na ji na ba za ki tankaba ko? Toh ki saurare ni da kyau! Muddin ki ka bari aka ɗaura wannan aure tsakaninmu, ki ka shigo gida na wallahi sai na lahira ya fi ki jin dadi!!! Bagidajiya sakarya kawai!!!!!!!” Ya na gama magana ya fice a fusace, nan Amatullah ta kwantar da kan ta bisa kujera yayinda kwallan da ta yi kokarin rikewa su ka shiga gasar kwarranya daga idanun ta, fadi ta ke “Inna lillaahi wa inna ilaihi rajiun, ya Allah ban iya ba, ya Allah ka iya min! Ya Allah min takangar karfe da wannan bawa na ka Agithnee Yaa mugithu!”4 A wannan halin Gwaggo ta same ta, cikin tashin hankalin ganin halin da Amatullah ta ke ciki ta shiga tambayar ba’asi. Duk zurfin ciki irin na Amatullah ba ta boye mata ba, ta kwashe duk yanda su ka yi da Saifullahi tun daga ranar da su ka fara magana har zuwa yau. Jikin Gwaggo yayi sanyi, ta na mai duban Amatullah wacce in banda sauke ajiyar zuciya babu abin da ta ke yi tsabagen kukan da ta sha. Cike da tausayawa ta ce ” Amatullah ni na haife ki, ba zan so na cutar da ke ba, Baban Sasa mai kaunar ki ne, ba zai cutar da ke ba, ina mai baki shawara ki karfafa addu’a ga ubangijin ki, Allah zai fishe ki alkhairi. Amma ko da wasa kar ki tunkari Baban Sasa da wannan batun, shi Saifullahi da ya ke ganin an ma sa ba daidai ba shi ya je ya same shi ………” “Wallahil azim Gwaggo ba na san shi nima!!” Amatullah ta katseta cikin kuka. “Shhhhh! Kar na sake jin kin furta haka, ki dai yi addu’a, ki rufa mana asiri kar a ji wannan magana daga bangaranmu, ki bari shi can ya je ya shaida mu su, kin ji ko?” Kai ta gyada alamar “eh”3 “Tashi ki yo alwala ki yi sallah na san ko azahar ba ki samu kin yi ba, Allah ya yi miki albarka, kar da ki yarda maganar ta dame ki, idan ya rasa ki shi yayi rashi babba, babu kauyanci ko gidadanci tattare da ke Amatullah, sai tarbiya, kunya da yakana. Allah wadar wayewar ta shi da ya ke so. Inshallahu Allah zai shige mana gaba”2 Da haka ta sami kwarin gwiwar dauro alwala. Nan ta kalli gabas ta shiga kai kukan ta ga mai duka. *** Amatullah ba ta sake jin dadin gidan nan ba sai ranar Allah ya sa ta koma makaranta. Duk yanda kalaman Saifullahi su ka so tunzurata ta sami Baban Sasa ta akan rushe maganar auren su abin ya ci tura, ta yi kokarin jurewa ba dan komai ba sai dai alkawarin da daukarwa kan ta da Gwaggo, na duk kiyayyar da take ma Saifullahi ba dai a ji maganar daga bakin ta ba kamar yadda ya ke da buri, sai dai aji daga wajansa. Sati biyun da ta yi a gida har ta rame, ta rage walwala da kuzari. Kullum cikin tunani ta ke hatta lectures ma ba ta samu ta mayar da hankali ta gane a cikin aji. Tun Zulaikha na tambayar abin da ke damun ta, har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido. Yanzun ma daga aji su ka fito, tun da Lecturer ya shiga har ya fita babu abin da ta gane, gaba daya hankalin ta ba ya ajin. Tunanin lafazin Saifullahi na cewar idan ta sake aka aura ma ta shi sai na lahira ya fi ta jin dadi ne ya addabi rayuwatar. “Haba mana Amatullah!!!” Zulaikha ce ta faɗa ta na me jijjaga kafadar Amatullah, wacce ta yi firgit ta dawo daga kogin tunanin da ta tsunduma. Ajiyar zuciya ta saki ta na mai duban Zulaikha ta ce “Afuwan yar uwa, me ki ke cewa?” Cikin damuwa Zulaikha ta furta “Wai me ke damun ki ne Amatullah? Yau sati guda da dawowar mu na lura gaba daya kin canza, kai wannan damuwar da ki ke ciki har tafi sanda ki ka mari Dee Yusuf…..” “Dee Yusuf…..” Amatullah ta maimata, ikon Allah ashe akwai damuwar da zai sa ta manta da Dee Yusuf duk tsoran sa da take ji, abun da ta fada cikin ranta kenan, ta tsinci kan ta tana kewan ganin shi, a zahiri kuma cewa ta yi “ke ni na sha’afa da lamarin wannan mutumin shaf, Allah ya amsa addu’a ta ya min katangar karfe da shi” “Idan ba Dee Yusuf ba menene damuwar ki Amatullah” Zulaikha ta sake tambaya. Kallon Zulaikha ta ke cikin nazari, kamar yanda ta ke sanye da hijabi, ita ma Zulaikha hijabin ne jikin ta, har kasa kuwa. Kai ta girgiza ta na mai fadin “I’m very fine, kar ki damu dani kawata, bari na je KIL akwai wani littafi da na ke nema, daga nan sai na bi wannan course din da mu ka yi wallahi, wallahi sam ban gane shi ba” Cikin nuna rashin gamsuwa Zulaikha ta amsa ma ta da “Ba dai za ki faɗa min abin da ke damun ki ba, ai shikenan duk sanda ki ka shirya magana ina nan Amatullah, adawo lafiya, Ni ban zuwa KIL daga dawowa ta makaranta” Dariya Amatullah ta yi jin furincin Zulaikha na ba za ta je library ba. ” Dama ai na san ba zuwa za ki yi ba shi ya sa ban mi ki tayi ba, kin ga tafiya ta, sai na dawo” “Allah ya raba ki da ganin Dee… ” Cewar Zulaikha cikin zolaya, juyawa Amatullah ta yi ta na murmushi, akaro na farko da ta ke jin da za ta gan shi ma ai ba wani abu ba ne, duk kauyancin ta ya na jure tsayuwa da ita, ba kamar Saifullahi ba …. Nan ta kwabi zuciyar ta daga tunanin Dee Yusuf har tana gama shi da Saifullahi. Cikin sauri kan ta a kasa ta nufi hanyar da za ta sada ta da KIL. Ta gaban library ta hangi taran samari, dan haka ko da ta zo dab da su sai ta yi kasa da idanun ta, kafafun ta har hardewa su ke tsabagen tsarguwar kar dai kallon ta su ke, musammam yanzu da ta san ita ɗin bagidajiya ce yar kauye a cewar Saifullahi. Ilai kuwa ashe tun tahowar ta ya kafa mata idanu, gaba ɗaya hankalin sa na kan ta yana mamakin yanda a duniya ya sha ganin mata ma su saka hijabi ba wai a ABU kadai ba, amma bai taɓa ganin wacce shigar ke mata kyau ba kamar Amatullah. Ta gaban su ta gifta, ya tabbatar ba ta lura da shi ba, hankali kwance ya daɗa gyara tsayuwa, cikin ran sa faɗi ya ke “Amatullah! Amatullah!! ina nan biye da ke, na yi kewan ganin ki Mama nah”Guys bari na ɗan shiga library kaɗan, I will catch up with you ko zuwa anjima ne, yeah?” Cewar Dee Yusuf yayinda abokan Alutan na shi su ka zuba ma sa idanu cike da mamaki, ɗaya daga cikin su ne ya ce+ “Dee kai fa ka takura lalle sai mun haɗu akan wannan maganar, hakan nan kuma ka ce za ka shiga library bayan ba a kashe ta ba?” “Abi o help me ask him abeg!! Me ma za ka yi a library? Kowa dai yasan ba wajan ka ba ne, rannan ma da ka shiga raban shan mari ne ya kai ka!”8 Hamza abokin Dee Yusuf ke magana, wanda dama cikin su shi kaɗai ne ajin su ɗaya, ɗakin baccin su ɗaya, sau da yawa mutane na musu kallon yan uwa ko aminai, tun zuwan su aji ɗaya dukkansu aka basu gurbin karanta Human anatomy a maimakon MBBS da ya ke zaɓinsu, tun a lokacin suke tare saboda su duka biyun masu nacin karatu ne da hazaƙa, kuma duk shaƙiyanci tare su ke yi hakan bai hana su samun lamba ta ɗaya (first class) a duk jarrabawar da su ke yi. . Jin batun Hamza ya sa su kwashewa da dariya, shi kuwa Dee murmushi kawai ya yi, ya na ɗan sosa ƙeya ya ce “Ina wannan course din? Amatology da na ce maka na kasa gane shi? Ka tuna shi? Shi na ke so na je na duba ASAP ko Allah ya sa a dace” Cikin ɗaukan haske Hamza ya dara, ya na mai bashi hannu su ka tafa ya furta “Oya na go kafin ka jawa kan ka spill over, ka san dai final year mu ke, kuma second semester, in dai ba ka dace ba you better change the course, ka yi add and drop kawai a wuce wajen….” “Kai karya ne wallahi Sec Gen guda da spill over!!!!!!” Daya daga cikin su ya fada cikin kuranta Dee Yusuf, shi kuwa gogan hannu biyu ya tusa cikin aljihun wandon sa. Yau ma sanye cike cikin kananan kaya, bakar riga mai karamar hannu, da shudin wando. Juyawa yayi sai da yayi taku hudu sannan ya sake juyowa fuskar sa dauke da murmushi ya ke kallan Hamza, ya ce “Baba in dai kan Amatology ne ba spill over 1 ba ko idan har spill over 2 ne sai dai na yi, ba zan yi add and drop ba, na rantse ma ka da Allah!!” Ya na gama faɗi yayi gaba, ya na jiyo ihun su wanda hakan ya tabbatar ma sa cewa Hamza ya fasa kwai, sauran abokan siyasar na su sun fahimci wannan course din da ya ke magana ba kowa ba ne face yar budurwa. *** Amatullah kuwa ko da ta shiga library, maimakon ta duba littafin da ta zo nema kamar yanda ta faɗawa Zulaikha, sai ta tsinci kanta da neman wannan wajen da ta fara haɗuwa da Dee Yusuf, nan ta samu ta zauna, cikin ran ta kuwa ta na karyata yakinin wani ɓangare na zuciyar ta na ina ma Allah ya sake haɗa ta da shi, ko babu komai duk gidadancinta shi ya nemi yayi abota da ita, duk da dai ta sha maimatawa zuciyar ta da ahir babu abota tsakanin namiji da mace. Littafin da ta ke rubuce rubuce ta dauko, daidai shafin course din da su ka gama ba da dadewa ba, wato CHEM 132 ta buɗe, da ke ita theory na ba ta wuya, gashi wannan duk structures ne gaba ɗaya sanda malamin ya ke mu su bayani hankalin ta ba ya wajen. Tagumi ta yi ta na mai karewa rubutun na ta kallo, rubutun dai ita ta yi shi, amma gaba ɗaya kan ta ya kulle sai kawai ta kifa kan ta bisa teburi idanun ta rufe, littafin bude gaban ta. Bai yi mamakin ganin ta inda zuciyar shi ke da yakinin taradda ita ba. Yanayin da ya ganta ciki ne ya sanya shi zama a kujerar da ke kallan na ta a hankali gudun kar ya tada ita, littafin na ta ya ja gaban sa. Wato yanda Allah ya ma Amatullah kyau da tsari haka ma rubutun ta ya ke. Dee ya tsinci kan sa da shafa rubutun da ɗan yatsa yayinda murmushi ya maye kyakkyawar fuskar shi mai cike da kwarjini, ba dan komai ba sai don ganin course din da Amatullah ke karantawa course ne da ya ke kwararre akai. Kamshin turaren kamfanin Tomford ya bakunci hancin ta kuma ya kasa gushewa ya sanya ta bude idanu, nan su ka yi ido huɗu. Tuni ta yi zumbur ta tashi zaune ta na mai gyara hijabin ta da ya dan kwanta mata a jiki sanadiyyar kwanciyar da ta yi kan sa. “Uhum” Yayi gyaran murya cikin zolaya sannan ya kara da “Sallama gare ki Mama nah, salamu alaikum” STORY CONTINUES BELOW “Waalaikumus salam!! Ni ba Mamarka ba ce ba!!!! Sunana Amatullah!!!” Amatullah ta tsinci kan ta tana mai amsa sallamar Dee Yusuf a karo na farko a rayuwatar ta duk da a tsiwace ta amsa masa. Cike da jin dadi ya ce2 “Kai yau kin amsa sallama ta? Wannan farin cikin ina zan kai shi Mama nah?” Kwayar idanun ta ta kada, irin sai kuma ka ta yi. Hannu ta mi ka da niyar karɓan littafin ta daga hannun shi, ganin ya janye littafin ya ɓoye a bayan shi ya sanya ta yin karfin halin kai idanun ta cikin na shi wanda karfin idanun shi ya haifar ma ta da faduwar gaba, da sauri ta yi kasa da na ta idanun ta na mai tasbihi cikin zuciyar ta. Shiru ne ya biyo baya, ita dai ba ta kara ɗaga ido ta kalle shi ba, shi kuma ya zuba ma ta na mujiya. Jin shirun yayi yawa ya sanya ta furta “Wai me ka ke so ne? Na fada ma ka babu abota tsakanin mace da namiji…..” “Amma akwai soyayya ko Mama nah?” Ya katse ta, maganar ta sa ta zo mata a bazata, ta ma kasa ba shi amsa kallan sa kawai ta ke. Hakan ya ba shi damar sake furta ” Ba ki amsa min ba, akwai soyayya tsakanin Mace da Namiji?” Da kyar kamar mai rada ta furta “Akwai……” “To ki zaba ko dai ki yi abota ko soyayya….”2 “Ina da mijin da zan aura!” Amatullah ta tsinci kanta ta na mai bashi amsa cikin faɗa faɗa. Hannu ya daga alamar kwantar da hankalin ki, kana ya ce “Yi hakuri Mama nah ki fahimce ni, yanzu ina laifi idan ina so na kulla kyakkyawar alaka da mu’amala a tsakanin mu?” “Me zai sa ka so kulla alaka da bagidajiya yar kauye kamar ni?”3 Ga mamakin ta sai gashi ya murtuke fuska, cikin nuna rashin jin dadin maganar ta ya ce ” Saboda me ya sa? Saboda me ya sa za ki danganta kan ki da wannan sunaye?” “Saboda haka wasu mazan su ka dauki mata ma su sanya hijabi irina, duka matan makarantar nan ba su ishe ka abota ba ko soyayya sai ni Amatullah yar kauye…..” “Shhhhhhhhhh” Ya katse ta ta hanyar dora yatsan sa bisa leben sa, yana duban idanun ta wanda su ka cika da kwalla ya furta “Hijabi ko suturta jiki abu ne mai muhimmanci ga addini, abu mai daraja shi ake suturtawa, fitar da tsaraici shi ne kauyenci da gidadanci Mama nah, hijabin ki abun sha’awa ne ga duk wanda ya san darajar diya mace…..”2 Baki ta buɗe ta na kallon shi, bai gushe ba ya cigaba “Duk Namiji da ya dauki rufe jiki a matsayin gidadanci jahili ne Mamanah, da sutura ba ta da muhimmanci da dabbobi ma za su sanya ai, sutura ita ce banbancin mutum da dabba, hijabin ki shi ne banbancin ki da sauran mata…..”2 Ya na gama magana ya aje mata littafin ta, tashi tsaye yayi, ya na mai tusa hannun sa cikkin aljihu, ya fitar da yar takarda da biro yayi rubutu, kana ya ce ” CHEM 132 is my favorite, in ki na bukatar haske kan shi ga number ta ki kira ni, na barki lafiya” Ya juya ya na wannan tafiyar tashi cike da takama, Bayan shi ta bi da kallo, mutanen da su ka san shi sai daga ma sa hannu su ke mata da maza, shi ma ya na mayar mu su, har ya fice. Kai bisa teburi ta kifa, yayinda zafafa hawayen da ba ta san na menene ba su ka shiga gangarowa daga idanun ta. Kiran sallah ya nusar da ita zaman da tayi, ba ta yi mamakin ganin gaban hijabinta a jike da hawaye ba saboda ita kanta ba ta san iya lokacin da ta ɗauka tana zubar kwalla ba. Mamaki, Farin ciki, Nadama su ne su ka cika ƙirjinta. Ba komi ya bata mamaki ba sai kalaman Dee Yusuf don su ne abu na ƙarshe da ta yi tsammanin ji daga bakinsa. Kalaman sun sanya ta farin ciki don tun bayan kalaman Saifullah ta sadakar babu namijin da ke mata kallon mace mai daraja, don har ta danganta rashin samun mashinshini da kasancewarta bagidajiya. Ta Yi Nadama ba ko kaɗan ba don ba tare da ta san waye Dee Yusuf ba ta alakanta shi da mutum mara kamun kai, tambaɗaɗɗe kawai don ya taɓa ta. ‘Kuma ai yana rungume mata’ wata sashi na zuciyarta ce ta nemi kare ta. Amma hakan bai hana nadama cika zuciyarta ba. Da wannan yanayi ukun ta haɗe kayanta ta kama hanyar hostel, kalaman Saifullah yayin da ya ke kiranta bagidajiya, baƙauyiya cikin murya mai cike da ƙyama su ka dinga dawo mata a kwanya yayin da take tafiya, bakinciki na gaf da mamaye mata zuciya ta jiyo muryar Dee Yusuf daga can ƙasan zuciyarta yana faɗin. ‘Hijabi ko suturta jiki abu ne mai muhimmanci ga addini, abu mai daraja shi ake suturtawa, fitar da tsaraici shi ne kauyenci da gidadanci Mama nah, hijabin ki abun sha’awa ne ga duk wanda ya san darajar diya mace’2 Wannan ya bata ƙwarin guiwar ƙarasawa ɗaki cikin farin ciki, tasbihi take tana mai gode ma Allah da ya jefo mata Dee Yusuf cikin rayuwa. Tana shiga ɗaki ta yi wani murmushi tare da faɗin “Saifullah ba zan auri malamin Allo ba, amma za ka raina kanka in ka ga mijin bagidajiya, Mark my words, today 28th April 2009” Dariya ta yi bayan ta ankara ga kanta take magana ba wai Saifullah ba. Nan ta shiga yi ma kanta dariya tare da jin takaicin kanta. ‘Ta ya ma na fara wannan tunanin?’ ta tambayi kanta a zuciya tana mai jan tsaki, take sai ta sake kwashewa da dariya tana fadin “Oh! Su Amatullah, watau daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaƙi” kan gado ta kwanta hannayen biyu ta sa ta rufe fuskar ta cike da kunya da yanayi na jin dadi yayinda ta ke yiwa kan ta dariya Haka ta ƙarasa yininta cikin matsanancin farin ciki, wanda ya kasa ɓoyuwa ga Zulaikha da ta shigo ɗakin daga baya.3 “mutumiyas me muka samu ne” ta tambayeta bayan sun zauna cin abinci. Kallon ta Amatullah ta yi cikin murmushi ba tare da cewa komi ba, sai da ta cinye ɗanwaken ta, ta sha ruwa sannan ta kalli Zulaikha tace “Ɗazu kin ishe ni me ke damu na, yanzu kuma kina me muka samu, ɗazu ina cikin yanayin tuna mutuwa yanzu kuma tunawa nayi da ɗimbin rahmomin ubangiji da ya tanadar ma duk macen da ta kiyaye dokokin Allah tun daga shiga, mu’amala da ibadunta sai na ga in Allah ya yarda mun shallake” ta karanto mata yayin da zancen Dee ke mata echo a zuciya.2 “Ubangiji Allah ya sa mu dace, ciwon Baban Sasa ya sa ki tunawa da mutuwa, Amatullah ciwo ba mutuwa bane, sannan sau da dama jinya kan zama Rahama ga bawa. Insha Allah zai ji sauki” Zulaikha tace cikin sigar rarrashi, faɗin haka ya sanya wasu zafafan hawaye gangarowa daga idon Amatullah, ba don komi ba ambaton Baban Sasa ya sanya gaba ɗaya Amatullah ta tsinci kanta cikin yankewar kauna daga samun wani miji bayan Saifullah da ya ke kallon ta a matsayin kazanta. Hakuri Zulaikha ta cigaba da bata, tana faɗi mata kissoshi da jinyoyi su ka zama Rahama ga bawa, ciki har da kissan Annabin Allah Annabi Ayyuba Alaihis salam, wanda ciwo ya ci shi ya ci shi ya zama babu abin da yake faɗi sai RABBI INNIE MASSANIYAD-DURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEEN kuma Allah ya amsa masa ya bashi lafiya kamar ba wanda ya yi jinya ba. Kalaman Zulaikha sun yi tasiri wajen tuna mata da girman Allah, da kuma kasancewarsa maji rokon bawansa. 2 *** Washe gari sun tashi kamar kullum, shirin zuwa ɗaukan darasi su kayi sanye da hijabansu, Amatullah ta fita cike da buri da addu’ar ɗaura ido akan Dee Yusuf, har sun shirya fita ta tuna da karin maganar hausawa na ‘idan kana da kyau ka ƙara da wanka’ nan ta ɗauki kwalli ta sanya ta ɗan shafa hoda kaɗan, ganin kallon da yan ɗakin ke mata ya sanya ta fadin 2 “Fuskar ce naga duk naso, kar a ce ina shafa mangyaɗa” nan suka sanya dariya suna tsokanar ta. 5 “Wallahi an ci amanar kyau, yanzu wai haka kike kyakkyawa amma kike sakaci” Salma Ateeku ta ce, nan su ka sa dariya. “Anty Sophie Wai haka” tace tana kallon kawar salma da suke zaune tare Safiyyah Jibril amma anty Sophie su ke ce mata. 3 “Sosai Amatullah, kin yi kyau sosai, ga lip balm can ki sanya, you look so cute and take away” Anty Sophie tace cikin jinjinawa. Da haka suka fice zuwa aji, sun kammala na farko suna zaune zaman jiran wanda za su shiga ƙarfe goma sha biyu ne Maman Jafar ta ja su zuwa community market tana son duba ma Jafar dinta drawing book. Tafe suke suna hira kamar ko yaushe, tun daga nesa ta hango shi tare da yan mata biyu daga ganin shigarsu za ka ce arna ne ko kuma marasa kishin jikin su, ta gefen sa kuma wani namiji zaune cikin shigan English wears, zaune suke gefen Faculty of engineering irin zaman nan nane da juna, akan idonta ɗaya ta saka hannu a aljihun gaban rigarsa ta ciro kudi saboda sanye yake da kaftani da wando har ma da hula kalan sararin samaniya. Ba ta san me ya tokare mata a kirji ba, hakan ba ta san sanda hawaye su ka gangaro mata ba, hannu ta sa ta share, Jikinsa ne ya bashi ana kallonsa yana ɗaga ido sai ga ta gaban shi, sun hada idanu. Kauda da fuska tayi ta cigaba da magana duk da kirjinta bai fasa mata nauyi ba, da haka su ka isa Com market. A ɓangaren Dee Yusuf kuwa bai taɓa zaton ganinta a wannan lokacin ba duk da dai ba wai ya ɗauki ganin shi cikin course mate din shi da ta yi ba a matsayin laifi, sai dai yanda ta ga daya daga cikin su na zarar kudi daga aljihun shi ta karfi da ya ji ne da kuma yanayin da ya ga fuskar Amatullah ne bai ma sa dadi ba. STORY CONTINUES BELOW Yunkurin tashi yayi don bin ta nan wayar sa ta ɗauki kuka, ganin mahaifiyarsa ce ya sanya shi ɗauka cikin ladabi. Gaisheta yayi tare da tambayar lafiyan Ahlin gidansu. ” Gawar Baffanka Haruna na hanya, tun da karatun bai yi zafi ba ka kamo hanya don kar ka rasa janaza” tace cikin sigar Alhini, tunawa da mutuwar Baffan nasa yayan mahaifinsa ya sa shi sanyin jiki. 2 “Mummy ya wajen su mimi toh, bana son na tuna mutuwar nan fa” yace cikin dauriya, mimi autan mai rasuwa ce da kowa ya shaida shaƙuwarsu. “Sun je tarbo shi, ya aka iya abin da ake jira kullum” ta fadi tana mai kara nanata masa mahimmancin zuwansa janaza. Anan yayi sallama da abokansa tare da fada masu zai wuce Kano ya kwana washegari ya wuce garin su Don halarta makoki da janaiza. Ko da su ka juyo don komawa in da za su yi darasi. Su ka iske babu Dee Yusuf a wajen, nan Amatullah ta kara cika da takaici don a lokacin ta tabbatar da cewa shi ɗin ba wai ya dauke ta yanda take tunani bane. Tun daga ranar take sa ran ganinsa tare da sa ma ranta duk suka haɗu sai ta masa tambayar dalilinsa na rashin bin dokokin ubangiji, sai ta tambaye shi me yasa ba zai dinga rungumar garwashin wuta ba akan ya dinga rungumar matan da ba muharramansa ba? Kamar ya san abin da ke ranta ya ɓace ɓat, tun tana ƙirga kwanaki har aka yi sati ɗaya ba ta ganshi ba, haka ta cigaba da zuwa ɗaukan darasi tare da yin muraji’ar darussan kar ya cunkushe mata, hakan kuma bai hana mata tunanin Dee Yusuf ba da son jin dalilin da ya sa ta dena jin sa.2 *** Bayan Sallar isha’i, dakin su Amatullah cike da yan kallon series wanda Zulaikha ta saba tara mu sa, tun Amatullah na kokawa ta ce ana hana ta karatu, har ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido. Kwance ta ke bisa daddumar sallah. Ta idar da sallar isha’i kenan ta yi kwance ta na sana’ar ta ta da ta zaman mata jiki kwana kin nan, wato tunanin Dee Yusuf na dalilin bacewar sa da kuma muhawarar da zuciyar ta ke tafkawa na kiran shi dan ta ji lafiya tunda dai Allah ya sa ya rubuta ma ta numbar shi a dan littafin ta. Cikin gargadi zuciyar ta ke ayya na mata ” Toh ke Amatullah ina ruwan ki da shi da har za ki addabi kan ki da tunanin shi? Har ki na tunanin kiran shi don zub da aji?” Wani bangaran zuciyar ta kuma ta ji an furta “Menene zubda aji dan ka kula me kula ka? Ai mai kaunar ka ya fi mai kin ka ko yaya ne. Ina laifi idan kin kira kin ji ko lafiya? Idan kuma wani mummnan abu ne ya same shi fa? Irin haka ne sai dai kawai ka ji an wayi gari babu mutum, mutum ya mutu…..” Firgit ta yi ta tashi tsaye jin batun mutuwa, da saurin ta ta nufi jakar ta, littafin nan ta dauka tare da zare wayar ta daga jikin chaji, su Zulaikha na tambayar lafiya? Ina za ta je kuma? Amma ina nuni kawai ta yi mu su da hannu alamar tana zuwa, ta fice. Waje mara hanayi ta samu daga waje, hannu na rawa ta kwafi numbar cikin wayar ta. Sai da ta gama kwafewa tas sai kuma ta kasa danna kira. Da kyar ta sami karfin gwiwar dannawa amma kafin ya fara ringing ta yi sauri ta katse. Ta na mai dafe kirji saboda tsabagen faɗuwa da ta ji gaban ta na yi ta dan takaita kusan mintin ta biyar cikin wannan hali, sannan ta kara kiran numbar cikin ikon Allah sai gashi ya fara ringing. Jin wayar ta kusa katsewa ba tare da an daga ba ya sa ta sakin ajiyar zuciya, hakan yayi daidai da daukar wayar yayinda ta jin muryar shi ya daki dodan kunan ta ya na mai fadin “Hello?” Maimakon ta amsa, sai tsuntar kan ta tayi ta na mai runtsa idanu. “Hello? Who is that please? Wanene?” “Amatullah” Ta fada cikin rada yayinda ta ci saukar numfashin sa daga dayan bangaran na alamun ajiyar zuciya. “Amatullah…..” 2 Ya sake maimaitawa. “Kin dauki tsahon lokaci kafin ki kira ni ba, har na fara fidda rai Mama nah….” Shiru Amatullah ta kasa magana, ji ta yi kamar an daure bakin ta. Be gushe ba ya kara da “Kin ji ni shiru ko? Tafiya na yi an mana mutuwa ne na tafi jana’iza gida amma gobe zan dawo tunda kin kira ni” “Allah sarki waye ya rasu?” Ta tambaya a takaice. “Baffan mu ne” “Allah ya ma sa rahama” “Ameeen Mamanah, thank you very much for the prayer” “You’re welcome” Ta kara amsa ma sa a taikace. Sai kuma ta yi shiru. Cikin zolaya ya furta ” Shin akwai abun da ya kamata ki fada min” Cikin tsarguwa kardai ya dago jirgin ta na tunanin shi da ya mamaye zuciyar ta ta furta “Eeeeh? Na’am? Dama CHEM 132 na kasa ganewa…..” “Are you sure shi kaɗai ne?” Ya katseta cikin zolaya. Ta na wasa da yatsun kafar ta, cikin jin kunya ta ce ” Shi kaɗai ne” “Toh Mamanah Allah ya kai mu gobe da na dawo zan kira ki sai mu sami lokaci da wajen bita ko?” Maimakon ta amsa masa sai ta tsinci kanta ta na gyada kai alamar “eh” sanan ta kara da “Na gode sai da safe, Allah ya kawo ka lafiya….” “Ameeen ameen” Cewar Dee Yusuf, ta na shirin katse wayar ta ji ya furta “Amatullah” Har cikin zuciyar ta taji kiran, a hankali ta furta “Na’am” “I’ve missed you so much” Kasa bashi amsa ta yi, fuskar ɗauke da murmushi ta katse wayar. Hannu biyu ta sa ta rufe fuskar ta. Kusan mintuna talatin ta yi nan zaune ta na ta sakar zuci, kafin daga bisani ta koma ɗakin zuciyar ta cike da farin ciki. Washegari kamar yadda ya ma ta alkawari ya na dawowa ya mata waya domin shaida mata ya dawo. Babu damar zuwa library, ɗaya daga cikin ajin su Amatullah su ka zaɓa in da su ka yi za su hadu bayan la’asar. Amatullah ta so gayyatar Zulaikha zuwa karatun amma ta nuna mata ita ba ta da bukata, babu laifi ta na gane course din. Ranar wuni tayi tana duba lokaci. Tana idar da sallar la’asar duk da marar ta na mata ciwo alamar ta kusa fara al’adar ta, hakan bai hana ta fara shiri ba. Atamfa ta sa fara Mai adon koran ganye. Dinkin ya zauna a jikin ta ya mata cicif da ke Amatullah irin matan nan ne da Allah ya ma sura mai kyau. Wata kawar Zulaikha da ta shigo dakin wacce tun da Amatullah ta sanya atamfar ta ke bin ta da kallo ta kasa daurewa ta ce “mashaAllah wannan jiki na ki Amatullah, gashi kullum ki na cikin hijabi abin ki dan kuwa da mazan makarantar nan zasu gan ki babu wannan hijabi ai da an sami matsala” Kafin Amatullah ta bata amsa Zulaikha ta ce “Da hijabin ma makaleta su ke, ba ki ga yanda Dee…..” “Zulaikha!” Amatullah ta katseta cikin gargadi. Kafada Zulaikha ta daga ta sauke tare da fadin “Toh baki na kanin kafata” “Ya dai fi mi ki sauki, kun ga tafiya ta ni”5 Hijabin ta ta zura, ta na jiyo kawar Zulaikha na tambayar wani Dee ta ke nufi, cikin ran ta ta ce kwa dai ji da shi. Tun daga nesa ya hango ta tafe. Sanye ya ke cikin farar shadda dinkin jamfa, tsaye gaban ajin da su ka yi za su hadu, jingi ne jikin bango kafafun sa harde, hannun sa biyu cikin aljihun sa. ya kura ma ta ido tamkar karo na farko da ya fara ganin ta kenan. Komai game da Amatullah birge shi ya ke. Kamannin ta, kamalar ta, tafiyar ta, muryar ta…….. “Salamun’alaikum” Muryarta ce ta katse masa tunanin da ya ke, fuskarsa cike da murmushi ya furta “Wa’alaikum salam Mama nah, na yi kewar wannan muryar Mama nah”6 Murmusawa ta yi cike da kunya ta ce “Ka dawo lafiya? Ya hakuri kuma?” Baki bude ya ke kallon ta har sai da ta tsargu, ta ce “Lafiya me ya faru?”4 “Murmushi? Ni kike ma murmushi Amatullah? Ahhh my ancestors will be proud of me o!!! I’ve made it in life!”2 Dariya Amatullah ta ke sosai ta ma kasa bashi amsa. Dee Yusuf ya kara da “Alhamdulillah Mama nah, hakuri mun gode Allah. Ina san dariyar ki, dan Allah kar ki dena” Ganin dai idan ta biye shi nan za su tsaya ya ta sakin baki ta daga littafin da take dauke da shi tare da furta “Our tutorial Sir?” Ya na mai murmushi ya nuna mata hanyar shiga anjin ya na mai furta “Yes Ma’am, Lady first” Cikin jin kunya ta wuce gaba, ya na biye da ita su ka shiga ajin. Mutane kalilan su ka tadda ciki, hakan ya ba su damar yin karatun cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Dee Yusuf ya iya koyarwa kwarai da gaske tamkar dama sana’ar shi kenan. Wajan awanni biyu ya dauka ya na koyar da ita har sai da aka kira magariba ya ce da ita. “Toh Mama nah ya kamata mu tsaya anan ko? Kin ga lokacin sallah yayi” Kai ta gyada masa alamar “eh” cikin ranta kuwa cewa ta yi ka dai je ka yi sallah, ni kam Allah ya kawo min sauki yanzu yanzun nan. Har kofar hostel ya rakata, ya tsaya su yi sallama Amatullah ta ce “Kar na sa ka yi missing sallah, na gode gwarai” Yana murmushi ya ke duba agogo, kana ya ce “Ina fatan dai kin gane?” Kai gyada alamar “eh” sannan ta kara da “Sai Allah ya kai mu gobe?” “Toh Mama nah, sai anjima” Sai da ta tabbatar ya tafi sannan ta shige hostel zuciyar ta cike da annashuwa, da a ce Dee Yusuf ne Malamin su ai da ba haka ba.6 *** Bayan sati biyu, zaune su ke a ajin da yan Agric Education ke ɗaukan darasi a can sashin horar da malamai (Faculty of Education), Jakanta ne su ka sanya marabi tsakaninsu, bayanin Bond yake mata yadda ba a taɓa mata ba, fahimtarsa take cikin haddacewa. Kallonsa ta yi tare da fadin “me ya sa ka zaɓi anatomy maimakon chemistry? Ban taɓa ganin wanda koyar da chemistry ya ma kyau ba sama da kai” Murmushi ya bi ta da shi, sanyin muryarta na ratsa shi. “Ni kuwa menene sirrin muryar nan taki, zan so jin sa yana mai rera waƙa” yace yana basar da tambayar da ta yi masa. “Ayya mana Yusuf, maimakon ka so jin ayoyin Allah da muryar” dariya yayi cikin basarwa ya ce “Kuma fa, yauwa dama akwai abin da nake so na fada miki” ya ƙarasa cikin tattaro duk wani natsuwa na shi, nan gabanta ya shiga faɗi cikin sauri, bata shirya ma jin maganar ba duk da ya daɗe yana cewa za su yi, kullum ya ce sai ta kawo dalilin fasawa yau ba ta san me za ta ce masa ba. “Uhmm ina jin ka” tace masa, duk da ta san zancen bai wuce na tona asirin zuciyarsa wanda ƙwayar idanunsa sun daɗe da tonawa. “Amatology 10CU”aka ce daidai san da ya ɓude baki da niyyar magana. Hamza ne ya bayyana gaban su, sanye cikin riga mara hannu da wando wanda be kai har kasa ba. Amatullah ya tsurawa idanu, idan ya san da Zaman Dee Yusuf be nuna alama ba. Cikin kokarin boye rashin jin dadin ganin sa Dee ya ce ” Amatullah meet Hamza, aminina” Yana mai murmushin yake, Hamza kuwa tuni ya gano rashin jin daɗin ganinsa da Dee ya yi. Zama tsayuwa yayi a kujerar da ke gabansu, kallon Amatullah yake na ƙurilla wanda har hakan ya saukar mata da rashin natsuwa. “Malam tashi mu wuce dama mun gama tutorial ɗin yau, sai mun yi waya mamanah” ya faɗi cikin ɓacin rai, yafi kowa sanin halin abokinsa Hamza, ko kara aka ɗaura ma zani in dai zai samu dama toh sai ya kwance, hakan na daga cikin dalilin da ya hana masa ganin Amatullah duk yadda ya so yi. A ɓangaren Hamza kuwa ayyanawa ransa mallakar Amatullah a shimfiɗarsa yayi ko da hakan na nufin ɓata duk wani alaka tsakanin sa da Dee Yusuf. Ba a san ransa ba, haka yana ji yana gani su ka yi sallama da ita, yau ko rakiya ba ta samu ba, nan ya bar ta, ya ja Hamza su ka fice.6 *** “wa ya faɗa maka inda nake?” Dee Yusuf ya samu kansa da faɗi bayan sun yi tafiyar kurame na dan wasu mintoci “Facebook” ya faɗi yana dariyar ƙeta, “Baba ashe babbar Haja ka samu shi yasa kake ɓoyeta, oboi fully loaded ina ma zan ganta without Hijab” ya ƙara faɗi yana mai kwatanta surarta da hannunsa. Baƙin ciki sosai ya cika Dee Yusuf har ya rasa abin da zai ce. Kafin daga bisani ya tsaya cak, gaban Hamza ya sha, ya na mai daura hannu bisa kafar Hamza ya ke kallan sa ido cikin ido ya furta “Hamza Amatullah mace ce mai daraja a guna, ina rokan ka arziki ka tauna harshen ka kafin ka furta lafazi dangane da ita, na yafe ma ka yanzu, Amma na rantse maka da Allah ka kuskura ka sake sai na bata ma ka!!!!!” Bai ƙara komi ba ya wuce ya barshi a nan, shi kan shi Hamza yayi mamakin Amininsa, kamar yadda Dee ya cika da mamakin kansa, wai shine da kishin mace har haka. Addu’a ya shiga yi bayan ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun simintin da ke gaban hostel ɗinsu na Danfodio. “Yaa Ubangiji kar ka sanya Amatullah juyan baya bayan na yaye mata lullubin da ke tattare da ni. *** Tun bayan da ya amsa kiran Baban Sasa yake cikin ƙunci, gaba ɗaya tunaninsa ya ɗauke akan musababbin kiran. ” In ba so kake ƙasa su rufen ido ba ka dawo a ɗaura aurenku” kalaman baban Sasa su ka dawo masa kamar a lokacin ya ke faɗi masa. “Watau wannan bagidajiyar ba ta ji magana ba kenan” ya fadi ya mai jan tsuki, da aka aka kira su jirgin su zai tashi. Jiki a sanyaye ya Mike ya isa inda ake bukatar su, ba don soyayyarsa da Baban Sasa ba babu abin da zai sa ya koma Nijeriya a wannan lokacin. Duk kwanakin da ya ɗauka kafin isowa Nijeriya bai ga daɗewarsu ba illa ma sauri da ya masa, hakan ya sa da ya tsinci kansa a kofar gidan Jamoh kamar yadda ake kiran gidan ya ji gaba ɗaya ya tsani kasancewarsa ahlin gidan. An yi murna da zuwan sa, tarbo na musamman mahaifiyar Amatullah ta yi masa wanda hakan al’adar ta ne tun yana ƙarami. Sai da ya ci yayi Nak sannan ya fara ganin gari, da yake shi ba mai wasu abokai bane tun asalinsa balle yanzu da yake ganin zama cikin masu ƙaramin tunani na nufin koma baya, duk da ma’anar ƙaramin tunani a wajen Saifu daban yake da saura.2 *** “A sanya biki nan da sati biyu, mu ne dangin amarya mu ne dangin ango” fadin baba Zubairu kasancewarsa babba gaba ɗaya a gidan ya sanya ba wand ya ja da zancen sa. “Kai Saifullah sai ka samu lokaci ka je ka ɗauko kanwar taka don ta san halin da ake ciki” Baba Anas mahaifi ga Saifullah ya fadi. Shi dai Saifullah bakin cikin duniya ya taru ya cika masa ƙirji, bai ce komi na sannan bai iya gardama ba ya tashi ya mike. Bai jira wani ɓata lokaci ba samaru ya wuce. Amatullah na zaune tana jiran kiran Dee Yusuf inda ya kan ce da ta fito zuwa koyon karatu. Karan wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, ganin lambar a kulle ya sanya ta saurin ɗauka don a tsammaninta Dee ne bai network ya sanya haka nan. “Ki fito wajen basket ball din ku” aka ce haɗe da kashe wayar, kamannin muryar da na mahaifansu ne ya sanya ta tunanin ko daga gidan su ne. ‘kila Baban Sasa ya samu cikawa’ tace tana mai share hawayen da ya gangaro mata na rashin madafa. Cikin sauri ta ja hijabin ta ba tare da ta damu ta dubi kan ta a madubi ba bare ta dan gyara maikon da ke fuskar ta, ta fice fuuu don ba za ta so abin da take tunani su tabbata ba.4 Isar ta wajan basketball ta tsaya cak ganin wanda ke tsaye bakin mota, duk da dai baya ya bata hannun cikin aljihu bai sa ta kasa gane shi ba, ba ta san lokacin da ta fara tasbihi ta na mai neman tsari daga ubangijin ta, fad’i ta ke “Allahumma ajirni fi musibati…….”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *