TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 3
Salamun alaikum”+ Ta faɗa cikin faɗuwar gaban abin da zai biyo baya. Juyowa yayi fuska murtuke, bin ta yayi da kallo tun daga sama har kasa, irin wannan kallon na hadarin kaji.4 A wulakance ya amsa da “Waalaikumus salam, na baki minti goma cal ki haɗo kayanki ki fito” Iya abinda ya ce kenan ya buɗe mota ya shige. “Ki haɗo kayan ki mu tafi?” Ta daɗa nanatawa cikin ranta, shikenan ta faru ta ƙare ramamme ya zagi maye. Karfin hali ta yi ta ƙarasa jikin motar, da ya ke ya ɗaga gilashin sai ta kwankwasa a hankali. Sai da yayi minti biyar kafin ya sauke tare da faɗin “Menene kuma? Ba ki ji abin da na ce ba ne?” “Dama cewa na yi ya jikin Baban Sasa?” “Oh so ki ke na ce ya mutu ko? Toh ya nan daram da ran sa……”6 “Alhamdulillah” Amatullah ta furta ta na mai ajiyar zuciya ta juya ba tare da ta sake tambayar ba’asi ba. Tana zancen zuci ta isa hostel, har ta wuce shi ba ta sani ba sai ji ta yi ya kira sunan ta “Amatullah?” Juyowa ta yi ta na mai murmushin yake domin ɓoye ma sa damuwar da ta ke ciki. Sanye ya ke cikin shadda brown ɗikin yar shara, kan sa sanye da irin wannan hular ta yarbawa, ƙafafunsa cikin baƙin takalmi, hannun shi mai sanye da baƙin agogo ɗauke da leda baka. Kallo daya za ka masa ka amince da jimla daya, “Dee Yusuf namiji ne”, namijin ma ɗan kwalisa, amma sam bai ɗaurawa kan sa girman kai kamar Saifullahi ba. Abin da Amatullah ke ayyanawa a ranta ke nan, a zahiri kuma cewa ta yi “Yi hakuri, wallahi ban gan ka ba ne, ka kira ni ko? A ɗaki na bar wayar” Kallo ɗaya ya mata ya gane damuwar da ke tattare da ita, haka kuma bai yi jinkirin tambayar dalili ba, ya na kokarin sanya idanun sa cikin na ta ya furta “You’re not ok, me ya faru? Ba ki da lafiya ne?” Kai ta girgiza al’amar “ah ah” kafin daga bisani ta kara da STORY CONTINUES BELOW “Lafiya lau na ke, dama Yaya na ne ya zo ya ce da ni ana nema na a gida, amma ina tunanin jikin kaka na ne yayi tsanani” Cike da tausayawa ya ce “Ayya Mama nah, Allah ya ba shi lafiya, Wai da na zo ne mu yi maganar nan da na ce mi ki ina son na fada mi ki, Amma babu komai sai kin dawo ma yi”8 Ba haka Amatullah ta so ba, duk da dai ta san maganar gizo ba ya wuce na koki, ta dade da dago jirgin sa, maganar ta sa dai ba zai wuce na soyayyar da ta ke gani a kwayar idanun sa ba kamar yanda ita ma ta ke jin sa cikin zuciyar ta, kuma ta ke mai fatan ji daga bakin sa, ba dan zuwan Saifullahi ba da ta ji. “Ko ya ki ka ce Mama nah” Dee Yusuf ne ya sake magana jin tayi shiru kamar mai tunani, cikin jin kunya ta ce “Eh sai na dawo din” Ledar hannun sa ya mika mata “Ga shi Allah ya sa za su yi mi ki, yar ajin mu na ga ta na siyarwa na mi ki sha’awar su…..”2 Ta na mai girgiza kai ta ce “Ah ah dan Allah kar dawainiyar ta yi yawa…..” Kallan da ya mata ya sa ta karbar ledar ba tare da sake masa mu su ba, ta na mai fadin “Allah ya saka da alkhairi” “Amen, toh maza je ki fito sai na raka ki ko? daga nan na gaisa da yayan ki…..” “Na shiga uku” 4 Cewar Amatullah domin kuwa ta manta da Saifullahi na jiran ta. “Wallahi na manta ya na jira na, na san yayi fushi ma, ka bari za ku gaisa wata rana, today is not a good day, na gode sosai”2 “Toh Mama nah, zan iya kiran ki ko?” Ta gyada kai alamar “eh” “Take care of yourself, a gaida mutan gida” “Za su ji” Tana gama fadin haka ta shige ciki da sauri dan kuwa ta san ta wuce minti goman da Saifullahi ya ba ta, yana nan ya cika yayi ɓam. Jakar ta kawai ta dauka, sai kuma ledar da Dee ya bata duk da dai har lokacin ba ta san me ledar ke dauke da shi ba. Zulaikha ba ta nan dan haka ba ta samu sun yi sallama ba, cike da fargaban wulakancin Saifullahi ta iske shi cikin mota kan sa kife bisa sitiyari. Bude motar ta yi tare da sallama, yanda ya dago kai ya kalle ta ne ys sa ta yi saurin shiga ta ja murfin motar ta rufe. Yanda ya figi motar ne kamar wanda za su tashi sama ya sanya Amatullah runtse idanu ta na mai addua’ar Allah ya kai su gida lafiya. STORY CONTINUES BELOW Tafiyar kurame su ka yi babu um babu um um har su ka isa gida. Isar su kofar gida tun kafin ya kashe motar ta fara kokarin fita, ga mamakin ta sa ya sa lock ya daɗa rufe motar ya na mai faɗin “Ji mana, ban gama da ke ba” Cike da alamun tambaya ta kalli fuskar sa, shi ma ɗin kallon ta ya ke ido cikin ido, dan haka sai ta yi kasa da na ta idanun. “Ba na son ki Amatullah, ba na kaunar ki, sanadiyyar ki Baban Sasa na so ya shiga rayuwa ta, shin ke ba ki da zuciya ne? Ko kare ya cinye ne……?”8 Ya na maganar ne a hankali be kuma fasa kallon ta ba, haka kuma hawayen da ke fita daga idanun Amatullah bai sa ya fasa maganar da ya ke ba2 “Hawaye? Ni ma haka na ke hawayen zuci Amatullah……ina da wacce na ke so, wayayyiya ba bagidajiya irin ki ba…….” “Dan Allah ka bude min kofa na shiga gida…..” Amatullah ta katse shi, domin kuwa zuciyar ta cika ta yi dam, kiris ta ke jira ta fashe. Ya bude baki zai bata amsa ganin fitowar Baba Zubairu ya sake shawara ya cire lock din. Hakan ya ba ta damar fitowa ta na mai share hawayen fuskar ta gudun kar Baba Zubairu ya gani, amma ina ya riga ya lura da ita. Idanun shi kan ta har ta karasa gaban shi ta durkusa har kasa ta gaishe shi. Yana mai duban ta ya ce “Amatullah lafiya kuwa na gan ki cikin damuwa haka har ki na hawaye?” “Laaaa ba hawaye ba ne abu ne ya fada idanuna, lafiya lau Baba komi Alhamdulillah, dama damuwar na Baban Sasa ne, da fatan jikin na sa da sauki” Ta bashi amsar ne ta na fara’ar yake. “Toh jikin Baban Sasa dai sai godiya kin san jikin tsufa. Ango an dawo? Ina fatan dai ba kai ne ka ɓatawa amaryar ta ka rai ba” Ya karasa maganar ne ya na kallan Saifullahi da ya iso gare su. Gaban Amatullah ne yayi mummnar faduwa jin an kira Saifullahi ango. Ba ta kara tsorata ba sai da ta ji amsar da Saifullahi ya bawa Baba Zubairu. “Ah ah Baba Zubairu, ina ga dai sati biyun da ku ke san sakawa ne bai mata ba” Yayi maganar ne cikin nishadi kai ba ka ce shine ke gasa mata magana duk lokacin da ya samu dama ba. Tashi ta yi da sauri gudun jin amsar da Baba Zubairu zai bayar, ta ce “Bari na shiga gida na ga su Baban Sasa” Ba ta ji ba ta gani, ba ta san amsar da su ka bata ba, haka ma ko da ta shiga gidan ma su mata maraba na yi amma ina babu wanda ta ke gani tsabagen tashin hankali. Dakin Gwoggon ta ta shige nan ta tadda ita zaune kan gado tana ta lissafin kudin kayan kitchen din da za su siyowa Amarya. Kamar daga sama ta ga Amatullah ta zube mata a gaba, hannyen ta biyu ta ruko kafar Gwoggo, kuka take ta na fad’in “Gwoggo ku rufa min asiri, ku ceto rayuwa ta wallahi Saifullahi ba ya kauna ta, ba ya so na ni ma ba na san shi kar ku aurar da ni ga makiyi na Gwoggo…….” STORY CONTINUES BELOW “Amatullah me zan gani? Yanzu ashe ba za ki ji magana ta ba Amatullah? Ki na tunanin za mu cutar da ke ne Amatullah?”6 Gwoggon ce ta ke magana cikin fada fada ganin Amatullah na neman kwance mata zani a kasuwa, ba ta gushe ba ta cigaba da fadin “Kin sani gidan nan idan aka dauke Baban Sasa da shi Mahaifan Saifu wa ke kaunar mu Amatullah? Yanzu ba za ki rufa mana asiri ba ashe? So ki ke zaman gidan nan ya gagare ni? Na ce da ke idan har Saifullahi ba ya kaunar ki, ke dai ki yi addua, amma kada ki bari matsalar ta fito daga gare mu, ashe ba za ki ji magana ta ba Amatullah? Ashe ban isa da ke ba? Yau ina ranar haihuwa?”3 Kai Amatullah ke girgiza mata, cikin shasshekar kuka ta saki kafar Gwaggo tare da fadin “Ki yafe min Gwaggo, zan kasance mai biyayya a gare ki, Allah ya huci zuciyar ki”6 Jin maganar Amatullah hankalin Gwaggo ya dan kwanta, nan ta cigaba da mata nasiha ta na mai nuna mata muhimmancin auren ta ga Saifullahi ba dan komai ba sai dan kara dankon zumunci.7 *** Ranar Amatullah ba ta sami kan ta ba sai bayan isha’i, shi kan shi Baban Sasa shiru yaji ta, ba ta je ta gaishe shi ba sai da ya aiko yaro yayi kiran ta. Gwaggo ce ta yi karyan ta yi bacci tun da ta dawo ta ke ciwon kai gudun kar Amatullah ta je wajan Baban Sasa da kumburarran idanu. Bayan ta idar da sallah, zaune cikin dakin ta bisa darduma, ta hangi ledar da Dee Yusuf ya ba ta sai sannan ta tuna tun fa da ta dawo aje kayan ko wayar ta ba ta sake dubawa ba, kuma ta ji karar wayar ba sau daya ba sau biyu ba, babu mamaki ma Dee din ya kira ta. Tashi ta yi ta dauko ledar tare da wayar , tsakiyar gadon tahaye yayinda ta zazzage ledar, idanun ta cike da kwallar farin ciki ganin hijabai gudu hudu sun zubo, sai kuma dan karamin Qur’ani da ta yi saurin riko shi kafin ya kai ga faduwa bisa gadon ta na mai furta2 “Astagafirullah” Ba ta san sanda ta rungume Qur’anin tare da hijaban ba, kamshin Dee Yusuf ke tashi daga cikin su, wani irin soyayya da ba ta taba yiwa da namiji ba ta ji ya na ratsa zuciyar ta. “Dee Yusuf”10 Ta ambaci sunan sa a hankali, wayan ta ne ya fara kara. Idanun ta rufe ba tare da ta duba wanda ke kira ba, tsabagen jin dadin kyautar da ya mata ta furta “Dee Yusuf, kai masoyi ne” “Da ki na da masoyi shi ne ki ka liƙe min haka kamar mayya?”24 Ya bata amsa a wulakance wanda hakan ya sa ta buɗe idanu tare da tashi zaune ta na kallon wayar, maimakon ta ga number Dee da ta yi zato sai ganin bakuwar number, ta sake karawa a kunnen ta domin tabbatar da Saifullahi ne ko kuwa kunnan ta ke zagi. Nan kuwa ya tabbatar mata shi din ne ta hanyar fadin STORY CONTINUES BELOW “Ko ba kya ji? If really you have a local champion that you love, wanda na ta tabbatar bagidaje ne irin ki me ya hana ki fadawa su Baban Sasa? Ai kwarya ta bi kwarya……” “Dakata Malam!!!!” Amatullah ce ta katse shi a fusace domin kuwa yau ya wuce gona da iri. Cikin tsiwa da dama ita gwana ce kawai ta na raga ma sa ne ta furta “Kar ka sake danganta Dee Yusuf da bagidaje domin kuwa babu abin da za ka nuna ma sa, sai dai shi ya nuna ma ka daraja da sanin kiman dan Adam!!!”8 Shiru Saifullahi yayi daga alama dai maganar ta yi masa bazata. Har ta na tunanin ya katse, sai kuma ta ji ya furta “Dee Yusuf din, ki na nufin shi ki ke so Amatullah?” “Eh shi na ke so, shi na ke kauna, daidai da second daya ban taba jin son ka a rai na ba Ya Saifullahi, ya fi ka komai, mutunci, kima, daraja da kuma sanin muhimmancin ƴa mace…..biyayya ne ya sa na ke iya jurewa har na ke iya sauraran wula……” “Kar ki damu Amatullah” Yayi saurin katseta cikin muryar lallashi ya ke magana da har ita kan ta Amatullah sai da ta duba wayar cike da mamakin furucin na sa, fadi ya ke “Ni dan uwan ki ne ba zan so a cutar da ke ba, inshaAllah zan yiwa Baban Sasa bayanin ba kya sona, ba za su mi ki dole ba tun da ba kya so na”8 Ya na gama magana ya kashe wayar ba tare da ya bata damar sake tanka masa ba. Mamaki da tsoro ne ya kama Amatullah ganin yanda Saifullahi ya canza lokaci guda, ta na mai addua’ar Allah ya sa sauki ne ya zo mata daga Allah. Nan ta kashe wayar dan kar ma ya sake kiran ta. *** Ɓangaran Saifullahi kuwa ya na aje wayar ya saki murmushin mugunta, domin kuwa yau Allah ya bashi sa’a haƙon sa ya cimma ruwa. Takalmi ya sanya, cikin sakar zuci ya fita neman su Baffannin shi da ya tabbatar zai same su a tare a wannan lokacin bisa ga al’adar su. 2 Zaune su ke ta wajen masallacin ƙofar gidan Jamoh, gaba ɗayansu in ka cire baba Salihu kamar yadda yaran su ke kiran su, watau mahaifin Amatullah da yanzu ya ke babban hedkwatan gidan rediyo Nijeriya da ke babban birnin tarayya. Baya shigowa zaria sai ƙarshen mako hakan ya sanya babu shi a zaman da su ka maida al’ada duk bayan sallan isha’i. Su kan yi hira da ya shafi zumunci da ma siyasa da rayuwa na yau da kullum. “Assalamu Alaikum” Saifullahi ya faɗi yana mai tsugunawa haɗe da sunkuyar da kansa kamar wanda yayi wa sarki ƙarya. “Ango ne da kansa” Baba Hamza ya faɗi cikin barkwanci wanda hakan ɗabi’arsa ce. Dariya aka yi duka, kafin aka ba shi damar faɗin bukatar da ya kawo shi. STORY CONTINUES BELOW Kara sunkuyar da kai yayi sannan ya ce “Don Allah Alfarma na ke nema a wajen ku a madadin Amatullah, ko babu alkawarin aure tsakanin mu kanwata ce da zan tsaya mata ta samu cikar burinta. Har ga Allah, na so haɗin nan Naji dadinsa ko don kaunar da Goggo mairo ke min amma tun da na faɗa mata musabbabin dawowata take kuka, tare da rokona na janye tana da wanda take so, Baba Zubairu kai ne sheda ai ka ganmu sanda mu ka dawo” 13 Ya ƙarasa domin kuwa yana da tabbacin Baba Zubairu ya kula da yanayin Amatullah ko da su ka shigo gida. “Dalla yi mana shiru sakarai, har mu zaka zo ka yi ma halin yan duniya? Tun da ka tafi ƙasar waje ka waiwayota? Yarinyar nan kowa shaida ne babu wanda ya taɓa mata sallama ta fita” mahaifinsa ne ya tareshi. “Yaushe za a mata sallama tana abar kyama” Saifullahi ya fada a ransa yana mai takaicin mahaifinsa. “A’a Anas, amma kuma duk sanda aka kira shi akanzancen auren haka ya ke tsallake kasashe ya amsa kiran ko, ita dai ce, ai tun da aka tura ta jamia nake tsoro” 2 Fadin Baba Idris wanda ya na cikin masu adawa da karatun ya mace, su yayansa a shekaru goma sha biyu yake aurar da su ko sakandire sai dai wacce ta yi a ɗakinta. “A’a ban ƙi taka ba, amma ku duba ku ga, daidai da wasika yaron nan bai taɓa aiko mata ba, zai aiko sakwanni dubu daga Babanmu sai goggon sa mairo ke da tsaraba, ai zuciya tana tare da wanda ke kyautata mata ne. Zuwan da yayi ƙarshe sai da innarsa ta ce ba ta ga ya kira yarinyar nan ko sau ɗaya ba, ku duba fa”3 Baba Anas ya sake fadi yana mai jin haushin Saifullah don shi ya sani sarai wannan duk shirin sa ne, ya ari bakin Amatullah ne don ya biya bukatar sa. “Toh in haka ne ya kamata a bata damarta, a kira ta aji wanda take so in ɗan gidan mutunci ne sai mu roki Babanmu ayi abin nan cikin mutuntawa” Baba Zubairu ya faɗi, take wani dadi ya cika Saifullah, yayin da baba Anas ya ji ba dadi don ba haka ya so ba. “Na amince amma rana ɗaya za a ɗaura aurensa da Nusaiba tun da itama zaune ta ke taƙi boko kuma babu miji” Baba Anas ya faɗi yana mai mikewa, nan duk wani farin ciki da ya lullube Saifullah ya ɓace ɓat, Nusaiba dai Jikan kanwar Jamo ce aka ɗauko ta daga ƙauyen farin kasa. Tun da ta gama aji shida ta ki makaranta, kanzantar ta da muninta ya sanya babu namijin arzikin da ya taɓa tunkarar ta da sunan so. 13 “Saifullah ka je za mu nemi Amatullah ɗin” fadin Baba Mahmuda. Nan ya tashi jiki a sanyaye, don a take ya iske ƙoshi ga shi zai yi kwanan yunwa kuma. 8 *** Da asuba bayan ta idar da sallar asuba ta gaida mahaifiyarta sannan ta ɗauko littafin da ta riko ta fara bitar karatunta. “Amatullah wai ki zo inji baban Sasa” Nasir Dan Baba Muhammad ya leko ya faɗi, hakan ya sanya ta ajiye littafin ta, ita kanta rashin ganin Baban Sasa tun dawowar ta ya tsaya mata a rai. Dakin Gwoggon ta ta shiga domin shaida mata kiran, amma sai ganin ta tayi sanye da hijabi, ta ce STORY CONTINUES BELOW “Ai har da ni kiran Amatullah, Allah dai ya sa lafiya” Tare su ka tafi, da sallamar su suka shiga dakin nan su ka tadda babanninta zaune da Shi kanshi Baban Sasa sai daga gefe Saifullah ya natsu kamar mutumin kirki. Gaban Amatullah ne ya shiga faduwa yayinda ta sami waje gefe guda ta zauna. Shi kuwa Saifu kallon nan da ya ke mata na kyama shi din ta hango a idonsa. 2 Gaida iyayen ta yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta gaida shi, don munafunci har da tambayarta ya ciwon kan da fatan ya lafa. Sai ya juya ga iyayen ya ce “Ai jiya ina rabuwa da ku na shiga na iske ta cikin matsanancin ciwon kai” 2 Mamaki ya cika Amatullah wani ciwon kai ta ke yi da yake maganar oho” Idanun ta ta kai ga fuskar Baban Sasa, ganin yanayin da ya ke babu annuri ya sa ta yi saurin sunkuyar da kai, ko shakka babu akwai abun da ya faru, tunanin da Amatullah ke yi cikin zuciyar ta kenan. “Amatullah ya mu ka yi da ke sanda za ki je Jami’a” Baban Sasa ya tambaya kai tsaye hakan ya sanya Amatullah daga kai ta kalle shi cikin jinjina tambayar. Kai ta kara sunkuyarwa kafin ta bashi amsa da “Alkawarin babu soyayya na ɗauka maka” “Yanzu me ya faru?” ya sake tambaya, nan ta yi shiru, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. Satar kallon Saifullah tayi, murmushin mugunta ya sakar mata. “Ke mu ke sauraro” Baba Zubairu ne ya yi magana. Baban Sasa ya kara da “Amatullah ki fada mana gaskiya, zamu baki abin da kike so, duk so na da auren ki da Saifullah babu dole a ciki, da gaske kina da wanda kuka daidaita?” Gaban ta ne yayi mummunar faduwa, kai shiga girgizawa alamar “ah ah” musammam da ta kai idanun ta kan mahaifiyar ta, ta ga irin kallan da ta ke aika mata cike da sakon magiya. 2 “Ki dena girgiza kai ki budi baki ki yi magana ke mu ke sauraro!” Baban Sasa ne yayi magana cikin nuna kosawa. Baki na rawa ta furta “Ban karya alkawarin da na dauka ma ka ba Baban Sasa, babu wani da mu ka sasanta da shi….”3 Daga Baban Sasa har su Baba Zubairu idanu su ka zubawa Saifullahi, Gwaggo kuwa sassanyar ajiyar zuciya ta saki. “Menene ma’anar haka Saifullahi? Shin da ma batun da ka same mu da shi yasasshen zance ne? Mu za ka mayar sakarkaru?” Mahaifin Saifu ne ka maganar a fusace. Shi kuwa gogan cikin rarrashi ya dubi Amatullah, budar bakin sa sai cewa yayi “Amatullah ki fada mu su gaskiya, kamar yadda na ce mi ki babu mai mi ki dole, mu duka ma su kaunar ki ne, dama na san ba za ki iya fada mu su ba dan girman alkawarin da ki ka daukarwa Baban Sasa, ni kuma ina dan uwan ki ba zan bari cutu ta sanadiya ta ba, hakan ya sa na yi recording wayar da mu ka yi a daren jiya….”17 Baki bude dan mamaki Amatullah ke duban sa, ba ta tsora ta sai da ta ga Saifullahi ya fito da wayar shi, ya shiga call recording ya kunna tuni muryar Saifullahi da Amatullah ya gwauraye dakin “Dee Yusuf din, ki na nufin shi ki ke so?” “Eh shi na ke so, shi na ke kauna, daidai da second daya ban taba jin san ka a rai na ba Ya Saifullahi, Dee Yusuf ya fi ka komai, mutunci, kima, daraja da kuma sanin muhimmancin diya mace…..biyayya shi ya sa na ke iya jurewa har na ke iya sauraran wula……” “Kar ki damu Amatullah”2 “Ni dan uwan ki ne ba zan so a cutar da ke ba, inshaAllah zan yiwa Baban Sasa bayanin ba kya sona, ba za su mi ki dole ba tun da ba kya sona”7 Ana kaiwa hakan recording ya dauke. Shiru ne ya biyo baya, Amatullah kuwa da za a tsaka jikin ta lokacin da ba za a ga jini ba tsabagen daskarewa da ta yi zaune kamar matacciya. Shirun da kowa yayi ba ƙaramin ɗagawa Amatullah hankali yayi ba, musammam da ta kai kallan ta ga Gwaggo, yanayin fuskar Gwaggo ne ya sanya hawaye zuba daga idanun ta. Cikin ranta fadi ta ke+ “Allah ya sa za ki yafe min Gwaggo” “Uhum” Gyaran muryar Baban Sasa ne ya dawo da Amatullah cikin hayyacin ta, nan ta tsincin kan ta tana mai faɗin ” Wallahi Baban Sasa na rantse da Allah ban karya alkawarin da na dauka ma ka ba….. wallahi, dama shi ne kullum ya ke cewa ba ya so na…..”2 “Shi wa?” Baban Sasa ya tambaya a dake, yayinda ya tsare Saifullahi da idanu. “Yaya Saifullahi” Ta bashi amsa cikin kuka. “Biri yayi kama da mutum, Ni na ce mu ku wannan yaron da kuke gani zai aikata, dena kuka Amatullah, me ma zai sa ka dauki muryar ta haka ba tare da izinin ta ba? Ka mata adalci kenan? ” Cewar Mahaifin Saifullahi ya na mai nuna shi da danyatsa, Saifullahi wanda be taba zatan Amatullah za ta ma sa haka ba shi ma kai ya sunkuyar cike da fargaba.4 “Saifullahi menene gaskiyar wannan maganar?” Cewar Baban Sasa ya na mai kallan Saifullahi, wanda ya dukar da kai cikin ladabi ya furta “Baban Sasa ni kuwa me zai sa na ki jini na? Me zai sa na ki Amatullah? Me zai sa na kasa son abin da ka ke so? Har ga Allah ina nan kan baka na na yi mu ku biyayya, shi ya sa ma na aje duk abun da na ke na taho daga uwa duniya domin cika ma ka buri, da wani ido zan kalle ka? Da wani baki zan furta kiyayya ga Amatullah gare ku?”4 Idan aka ɗauke Mahaifin Saifullahi da Amatullah babu wanda be gamsu da jawabin Saifullahi ba. Musammam Baban Sasa wanda har gyada kai ya ke cikin gamsuwa da jin dadi, ya furta “Na gode maka Saifullahi, yanda ka faranta min Allah ya faranta ma ka” Saifu kuwa wani dadi ne ya sake rufe shi, in da Amatullah ke fuskantar kishiyar haka musammam jin Baban Sasa ya ce “Ina Amatullah?” “Na’am Baba” “Na ji na amince ba ki karya alkawarin da ki ka ɗaukar min ba, Allah ya gani kauna ce ya sanya na so hadin auren nan tsakanin ku da ɗan uwan ki, amma yanayi ya nuna akwai dan targanda saboda haka ga umarni na gare ki……” Ya dan takaita yayinda idanun sa ke bisa bangon dakin kamar mai nazari. In banda kukan Amatullah babu abin da ke tashi cikin dakin. Kana ya nisa yayinda ya mayar da kallan sa ga Amatullah sannan ya furta “Ki shedawa ko shi wanene wanda ki ke biɗa, mun bashi sati biyu ya zo ya gabatar da kan shi a gare mu, daga randa sati biyun nan ya cika kuma babu wanda ya zo gare mu da batu na auren ki toh fa ku sheda ranar zan sanya auren Amatullah da Saifullahi wata biyu da izinin rabbil samawati…….”5 Yayin da hantar Amatullah ta kaɗa, shi kuwa shi kuwa Saifu bakin ciki ne ya sake lullube shi, wannan shi ne ga koshi ga kwanan yunwa, wannan masifa ta tsoho yaushe za ta kare ne haka! Mitar da ya ke ta yi cikin ran sa. Har Baban Sasa ya sallame su kowa yayi na shi wajan. Baba Anas Mahaifin Saifullahi ne ya kira shi daki domin yi masa nasiha akan abun da ya faru. Ita kuwa Amatullah dakin ta ta koma ta ci kukan ta ta koshi. Babban tashin hankalin ta shi ne shin ya za ta yi da fushin mahaifiyar ta da ta san ko shakka babu a kule ta ke d ita, sai kuma na tuggun da Saifullahi ya kulla mata. Tun da take a rayuwar ta ba ta taba soyayya ba, asali ma bata taba ji tana san wani da namiji cikin rayuwar ta ba face Dee Yusuf, shi kuma ba wai ya furta kalmar so a gare ta ba bare ta sa ran zai iya gabatar da kan sa cikin sati biyu domin kubucewa shiga hannun makirin namiji kamar Saifullahi. Abin da ke dan kwantar mata da hankali shi ne idan ta tuna Dee Yusuf ya na ta jaddada mata akwai maganar da ya ke so su yi, gwara ta koma makaranta idan ma son ta ya ke ya fada mata in ya so ta ce idan da gaske ya ke ya kawai ya zo ya gaida Baban Sasa, da wannan ta sami karfin gwiwar fitawo falo. Kallon da mahaifiyarta ta bi ta da shi ne tun a ɗakin baban Sasa ya kashe mata duk wani kwarin guiwa da take tunanin ta na da shi. Saifullah ya shammace ta, ba ta taɓa jin kunya irin na yau ba duk da ba wani tashin hankali bane iyayen su ka nuna duk da ransu bai so hakan ba. Tsoron keɓantuwarsu da mahaifiyarta take amma duk da haka ba ta fasa zaman jiranta ba tare da ɗauko mus’hafin da Dee ya bata ta shiga tilawa a cikin suratul Yusuf. Tana kai Ayar “WA’UFAWIDU AMRI ILALLAH..” taji wasu hawaye na zubo mata tare da jin wani irin ni’imomi na ratsa ta jini da ɓargo. Lallai Allah mai lura ne a kan bayinsa ta fassara karashen Ayar. ‘Gashi ya kawo miki ɗauki cikin ruwan sanyi, ku yi aurenku da Dee hankali kwance’ zuciyar ta mai kaunar tarayyarta da Dee ta fadi mata. ‘Amma ya za ki yi da fushin mahaifa? Shi Dee din ma ya fada miki yana son ki ne’ ɗayan zuciyarta mai fidda gaskiya ta nusar da ita, hakan ya sanya ta ji kawai babu abin da ya fi mata fiye da ta isa makaranta ta ga Dee Yusuf. Shigowar mahaifiyarta ya tsaida mata tunanin da take, bata ce da ita kanzil, amma kwatakwata babu wani rahama ko annuri a tattare da fuskarta. “Ki yi hakuri Gwaggo shi ya tunzura ni na fadi haka ban san zai yi recording ba” tace tana mai kama kafar mahaifiyarta cikin kuka. Janye kafafunta tayi, tace mata “Ai duk wanda yace shi bai haifu ba, zai yi fiye da wannan ma” ta janye jiki ta bar ɗakin. Duk yanda Amatullah ta so ta bata hakuri kafin ta tafi ya gagara saboda gaba ɗaya ba ta dawo ɗakin ba. Haka jiki a saɓule ta yi shirin komawa maranta, cikin shigar ta da ta saba wato hijab. A kofar gida ya ganta, ta tsayar da mai keke kenan domin fitar da ita titin da za ta hau Bus. “Malam jeka abin ka” ya faɗi yana kallon ɗan keke. Kallon sa take, in ba ƙarya idon ta ke mata ba farin ciki ne tsantsa a tattare da shi. “Mrs Danliti Yusuf ya dai? Zo na taimaka na rage mi ki hanya” yace yana mai buɗe mata motar, har ta yi niyyar wucewa ta hango Baba Muhammadu kuma idanunsa akansu. Murmushi ta sakar masa kana ta shiga ciki tana mai faɗaɗa murmushi ta. Suna wuce harabar gidan su ta gimtse fuska tare da fad’in “Menene amfanin hakan da ka ke yi? Menene afanin bata min suna a wajen iyayen mu? Menene amfanin mutum mai fuska biyu?” Shiru ya mata kamar ba zai amsa ba, kafin daga bisani ya ce “Kin san duk a cikin iyayenmu mata ban da sama da mahaifiyarki. Ba wai ina son bata ƙi a wajan iyayen mu ba ne, ba wai na ƙi ki bane fa. Akwai tazara a tsakanin mu, har ga Allah ke ba irin matar da na ke burin aure ba ce, you’re too local for my liking, ina san wayayyiyar mace ta burgewa wanda duk wanda ya ganta zai san ta amsa sunan ta mata ga Saif.” Ya fada ne ya na mai kallan ta ta wutsiyar ido, ya kara da “Kin ga wannan Danliti da ki ke so?…..”15 STORY CONTINUES BELOW “A point of correction, ba sunan shi Danliti ba Dee Yusuf sunan shi!!!” Ta katse shi cikin kuwa “Dee din menene shi?”5 Nan fa ɗaya dan kuwa ita kan ta ba ta sani ba, kuma ba ta damu da sani ba, ta dai fi dangata shi da Dauda, ko da yake maganar ce ba ta taba tasowa ba, amma kam yau idan ta ganshi za ta tambayi shi, da ma duk wani abu da ya shafe shi. Tunanin da take yi cikin zuciyar ta kenan. “Kin yi shiru kar ki ce min baki san cikakken sunan wanda ki ke ikirarin ki na so ba?” “Ina ruwan ka toh?” Kai ya girgiza ya ce “Babu fa, ruwa na shi ne ki lallabashi ya zo wajan Baban Sasa ko a samu a kashe maganar nan kowa ya huta, dan Allah ki taimake ni Amatullah” ya ƙarasa cikin lallashi. Bata iya ce masa komi ba, don ba ta da abin faɗa masa, bakin cikine ya tokare mata ƙirji ta ji ina ma kisa ya halalta da wuka za ta soka masa. Wa zai burge da matar da bai isa ya bada aronta ko dandanonta ga wani ba, watau shi zai yi aure ne ba don ibada ba sai don ya burge mutan duniya ko ina aka shiga a ce Saifullah Jamoh yana da haɗaɗiyar mata. Har ga Allah tsoran magana ta ke kar ya buye yana recording. Sai da ta ɓata fiye da minti bakwai kafin tace2 “Menene dalilin ka na kai ni makaranta? Na ce dai ba wani recording ka ke so ka yi ba?” Dariya ya saka duk da dai ba amsar da ya so ya ji daga bakin ta kenan ba. Kana ya ce “Toh ke ai godiya ya kamata ki min, gashi sanadiyyar haka an baki dama ki gabatar da Danlitin ki? Ni dai ki min wannan alfarma shi ya sa ma na kaskantar da kai zan kai ki makaranta” Ta na mai girgiza kai, kasa kasa ta furta “Assha ba ka da girma sai na jikin ka”9 “Me ki ka ce?” Ya tambaya cikin kokonton ko kunnan shi ke zagi. “Babu komai” Shiru ne ya biyo baya, har su ka isa makaranta babu wanda ya sake tankawa. Bayan sun isa, har ta bude mota za ta fita ya tsayar da ita ta hanyar fadin “Amatullah aure na da ke ba abu ba ne mai yiyuwa ba, ki tabbatar ki gujewa faruwar shi…….” Kallan shi ta yi cikin ido wanda hakan ya sanya bugun zuciyar shi karuwa domin kuwa be taba sanin haka kwayar idanun Amatullah ke da kyau da karfi ba, a dake ta furta “Kar ka damu, ni ma ba ka daga cikin mazan da na ke buri a ruyuwa ta, kai da zabin raina kamar haske da duhu ne, inshaAllah Allah zai min katangar karfe da kai!” Ta na gama magana ta fice tare da mayar masa da murfin mota ta rufe. Yayi kusan minti biyar bai motsaba, shi kan shi ya kasa gane dalilin zaman na shi, tsiwar Amatullah ne ko kuwa idanun ta ne.2 Amatullah kuwa tun da ta isa dakin su ta ke gwada numbar Dee Yusuf, dan Saifullahi ya dada tunzura ta, amma ina numbar ba ta shiga. Yanayin damur da ta ke ciki ya sanya Zulaikha fadin “Amatullah na san ko na tambaye ki ba za ki fada min damuwar ki ba, zan iya cewa tun haduwar ki da Dee Yusuf ba ki kara samin nutsuwa ba…..” “Eh Dee Yusuf, shi ne damuwa ta Zulaikha, tun dazu na ke kiran wayar shi ba ya shiga, sati biyu Baban Sasa ya ba ni, I need to talk to him ASAP, yana ta ce min akwai maganar da ya ke so mu yi, na san ba zai wuce na soyayyar da ya ke min ba, Ni ma Ina san shi Zulaikha, gwara mu hadu ya faɗa min ko Allah zai kawo min mafita….”7 Tana maganar ne kamar ta na faɗawa kan ta. Cikin rashin fahimta Zulaikha ta tashi tsaye, tana mai fad’in “Wata magana kuma? Satin biyu na me Baba Sasa ya ba ki? Me ke faruwa ne Amatullah? ” Kai Amatullah ta girgiza, ta na mai sanya hijabin da ta cire tun shigowar ta dakin ta ce “Zan mi ki bayani Zulaikha, bari na je na dawo….” “Amatullah…..” Zulaikha ce ta yi niyar tsayar da ita, ita kuwa Amatullah tuni ta yi hanyar fita ta na mai faɗin “Kar ki damu zan mi ki bayani anjima” Ta fice. Bakin gado Zulaikha ta samu ta zauna, cikin ranta kuwa ta na addua’ar Allah ya sa ba abunda ta ke zargi ba ne. *** Amatullah kuwa fitar da ta yi neman Dee Yusuf ta ke ruwa a jallo, duk da dai babu takamamman in da ta ke da yakinin ganin sa. Ba ta yi nisa da Queen Amina ba ta ji kamar ana bin ta a baya, ko da ta juya ta ga wanda ke biye da ita, yanayin da ta ke kallan shi ya sa shi fadin “Malama Amatullah ina ta magana ba ki ji ba, ko dai ba ki gane ni ba? Hamza? Abokin Dee?”2 Tuni ta faɗaɗa fara’ar ta, ta ce “Haka fa, yi hakuri ai ban ji ka ba ne, ina wuni?” “Lafiya lau Alhamdulillah, ko dan ba ki ga mutumin na ki ba ne?” Tana mai murmushi cike da jin kunya ta ce “Laa ko ɗaya, wayar shi ma ba ta shiga Allah ya sa lafiya” “Lafiya lau ya ke, ai kin san yau Thursday suna evening service ne shi ya sa, amma ina ga ai sun kusa tashi yanzu, kuma ni ma ta wajan na yi yanzu, ko za ki zo mu je?” Yayi maganar ne cikin ran sa ya fatan za ta amince domin ya sami damar hira da ita. Tsabagen idanun ta ya rufe ba ta da buri da ya wuce na ganin Dee Yusuf, sai ta amince, a na ta tunanin ba zai wuce in da su ka saba taran su na Alatu ba duk da dai ba ta gane menene service din da ya ke nufi ba. Tare su ka dauki hanya ya na ta jan ta da hira, tambayar course din ta da level din da ta ke da sauran su. Ta na bashi amsa ne a takaice, in ban da sakar zuci babu abun da ta ke. Ganin sun tsaya gaban katan Chochi da ke cikin makaranta, mutane na fitowa daga ganin alama sun tashi daga adduar yamma ne ta na mai waige waige ta ce12 “Ya mu ka tsaya a nan? A nan su ke service din ne?”6 “Eh mana, ai mostly nan su ka fi zuwa……yauwa gashi nan ma ya fito, Deee!”2 Hamza ya kulla ma sa kira ya na mai daga masa hannu, fitowar shi kenan, sanye cikin bakaken kaya riga da wando hatta takalmin kafar shi baki ne. Tsayawa yayi in da ya ke, ganin Amatullah da Hamza mamaki ne ya bayyana a fuskar shi, kafin daga bisani damuwa ya maye gurbin mamakin yayinda idanun sa suka sauka bisa fuskar Amatullah da ke tahowa gare shi, Hamza biye da ita. “Amatullah…….” Dee Yusuf ya kira sunan ta, ta na mai kallan littafin da ke makale cikin hammatar shi ta ce8 “Yusuf…….” “David can you please come?” Cewar wani Pastor da ya fito sanye da fararen kaya. Ga mamakin Amatullah sai ganin Dee ta yi ya juya ya na mai amsa da “Yes Pastor”16 Baki bude Amatullah ta ke kallon Dee Yusuf yayinda sunan da aka kira shi da shi ke ma ta ihu cikin zuciyar ta2 “David!!!! David!!!!David” Idanun ta kan Dee ta furta “Dama Sunan shi David?” Ta yi tambayar ne ciki ciki, amma hakan be hana Hamza ji ba wanda ya sha jinin jikin shi bayan fahimtar abin da ke faruwa, haka kuma ya kasa furta komai bare ya amsa mata tambayar da ta yi. Bayan Pastor ya sallame shi, Amatullah ta nufi in da ya ke. A hankali ta ke tafiya yayinda bugun zuciyar ta ke karuwa duk sanda ta daga kafa ta ajiye, haka shi ma Dee wanda ya tsura mata idanu har ta karaso gaban shi. “Yusuf menene addinini ka?” Ta tambaya ta na mai duban fuskar shi. “Amatullah da ma shi ne maganar da na ke so mu yi magana…..” “Menene addinin ka?” Ta katse shi cikin kosawa. “Christianity, I’m a Christian”10 Ya fada cikin yanayi mai wuyar fasaltuwa. Cikin sanyin jiki ta furta ” Ba ka fada min ba, all this while!!! God you should have told me……!” “Ba ki taba tambaya ta ba, but I tried to, I wanted to tell you Mamanah duk dai ina tsoran kada hakan ya zame mana tazara a tsakanin mu. Ina son ki Amatullah! ina kaunar ki Mamanah, dan Allah kar addini ya zama tazara a tsakanin mu Amatullah”9 Ji ta ke tamkar a mafarki, yau ga Dee ya na fada mata abin da take buri ta ji daga gare shi, sai dai kash ashe akwai tazara mafi girma a tsakanin su. Hawaye ne ya shiga zuba daga idanun ta, yayinda ta fara ja da baya ta na mai girgiza kai. Ganin ya na tahowa gare ta ya sanya ta juyawa cikin sauri-sauri gudu-gudu ta ɗauki hanyar hostel, ta na jin muryar sa ya na ƙwalla mata kira.2 Tsaye ya ke kamar gunki har ta ƙurewa ganinsa, Hamza wanda jikinsa ya riga ya gama sanyi ne ya matso gare shi tare da faɗin “Dee I’m very sorry, na zaci ta sani ai….” Hannu ya ɗaga masa alamar yayi shiru, kafin ya sauke hannun bisa kafadar Hamza, ka na ya ce “Kar ka damu aboki, I understand” Yana faɗin haka shi ma ɗin gaba yayi yabar Hamza nan tsaye. Amatullah kuwa ba za ta iya kwatanta halin da ta ke ciki ba, gaba ɗaya ji tayi ta rasa duk wani lakka a jikinta tana mai tsanan kanta. ” Christianity, I’m a Christian” kalamansa da ke yawo cikin kwakwalwarta, karin takaicinta ga mahaifiyarta na cikin matsanancin fushi da ita, ya za ta yi da iyayenta in su ka gano wanda ta ke so ɗin ba musulmi bane?5 “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel” ta faɗi tana mai rike wani ƙarfe saboda jirin da ya ɗibe ta. Daidai lokacin Zulaikha ta taho daga famfo in da ta ɗebo ruwa, a kan idon ta Amatullah ta tashi faɗuwa da kuma wasu mata da su ka taro ta. Ita ta yi musu jagora har ɗakinsu don babu nisa da inda abin ya faru.4 Ruwan sanyi zulaikha ta fita ta siyo bayan ta tabbatar da ta kwanta a kan gadonta, tare da kunna mata fanka. Duk a tunanin ta Baban Sasa ne ya cika. Cike da tausayi ta miƙa mata tare da umurtanta ta shanye. Ajiyar zuciya kawai Amatullah ke yi tana zubar da kwalla mai tsananin ciwo. “Kina tunanin Allah zai taɓa ɗaura ma bawa abin da ba zai iya ɗauka bane? Ina kika kai tawakallinki? Akwai wani rai da baya jiran mutuwa ne? Balle shi Baban Sasa ai kin san ko ba ciwo sa’o’insa nawa ke Raye?” ta faɗi cikin alhini.6 “Zulaikha in Baban Sasa yajin abin da na aikata take bakin cikina zai kashe shi, ban san ya zanyi ba” tace cikin gunjin kuka. Rungumo ta Zulaikha tayi tana shafa bayanta, tsoron tambayar ta me ta aikata tayi don ba ta son jin abin da ba ta taɓa tsammani ba. Shirun da Amatullah ta ji ne ya sanyata faɗin “Ashe Dee Yusuf Christian ne” tace kamar tana tsoron faɗi. “Na sani ai, menene abin damuwa? Ke dai ba ya koyar da ke bane?” Zulaikha ta ce cikin basarwa kamar bata daɗe da lura da soyayyar da ke gudana tsakanin Dee da Amatullah ba, tun da Amatullah ba ta furta mata itama ba ta yi tajasusi ba.2 “Ba kamar yadda kike tunani bane Zulaikha” nan ta faɗi mata duk abin da ke aukuwa tun da ga alkawarin aurenta da Baban Sasa ya ɗauka ranar da ta diro duniya har zuwa ga soyayyar ta ga Dee Yusuf, da kuma sati biyun da Baban Sasa ya ba ta ta gabatar da wanda ta ke so gare su. “Zulaikha wallahi soyayya irin wacce kana hango ka da mutum a aljanna na ke ma Dee Yusuf, ashe Ahlil Kitab ne, ashe haramci akan haramci nake aikatawa, ashe babu aure a tsakanin mu” tace cikin hawaye da Dana sani.4 “Kin san haramcin da kika aikata ɗaya ne, kin san haramun ne ciniki a cikin ciniki sai kika baje hajar da kin san an riga an siya” tace tana share kwallan da ya gangaro mata na tausayin kawarta.2 “kin san jimlar da ta fi kowace jimla zama ƙarya?” Zulaikha ta tambaya a sukwane. Girgiza kai Amatullah ta yi don bakin ta ya mata nauyi, istigfari kawai take a cikin zuciyarta. “Ina sonki/ka (I love you) Kinga kalmomin sun fi komi zama ƙarya, yau zaku wayi gari Kuna cikin soyayya kamar Romeo da Juliet gobe ku kasance kamar Saddam Hussain da George Bush. Saboda haka maza gyara kuskuren ki. Kin san illar da ke cikin fushin Gwaggo akanki? Kin san mahaifiya ko yaya ranta ya so su a dalilinka kamar zubar da Baraka ne a rayuwarka, san samu ki fara neman gafarar Gwaggo duk da dai ba da niyar ki bata mata hakan ya faru ba” Kai Amatullah ta gyada cikin gasgata abun da Zulaikha ta ce. Cikin shasshekar kuka ta ce2 STORY CONTINUES BELOW ” Na shiga uku Zulaikha, ya zan yi da wannan haramtacciyar soyayyar da ke cikin zuciya ta? Ko ina ba dadi, rana zafi inuwa ƙuna…..” “Ki roki Allah ya yaye mi ki, Allah ya kawo sauki cikin lamarin ki Amatullah, tashi maza ki yi sallah ki karanta qur’ani za ki sami sauki” Da wannan Amatullah ta tashi, alwala ta ɗauro nan ta dukufa gaban Allah cikin namen ɗoki2 *** Yanda Amatullah ke cikin baƙin ciki da alhani, ɓangaren Dee ma hakan ya ke, duk yanda ya so yayi magana da ita hakan ya gagara ba dan komai ba sai dan kashe waya da Amatullah ta yi, ya sha zuwa gaban Queen Amina ya zauna ko Allah ya sa ya gan ta, amma babu ita babu mai kama da ita, haka sati guda ya shude. Amatullah kuwa tsabagen gudun haɗuwa da Dee ya sa ta koma saka nikabi da safa, ta sha wucewa ta gan shi gaban Queen Amina, ko dai ya doka tagumi, ko ya na raba idanu, kuma ta san tabbas ita ya ke nema. Amma gudun abin da zai je ya dawo ya sa ta ƙauracewa kan ta ganin shi duk da kuwa ta na kewansa, sau dayawa idan ta tuna shi har kuka ta ke. Ranar da za su tafi mid-samester break da sassafe ta haɗa na ta ya nata ta yi gida, duk da dai gidan ma wani masifan ke jiran ta, musammam idan ta tuna fushin da Gwaggo da ta ke yi da ita, da kuma Saifullahi, gashi cikin satin biyun da Baban Sasa ya bata sati daya kacal ya rage mata. Kamar kullum, yau ma ya na fitowa daga lectures Queen Amina ya nufa. Kallo ɗaya za ka ma sa ka tabbatar da rashin kwanciyar hankalin da ke tattare da shi. Yanayin zirga zirgan dalibai ya ragu sanadiyyar hutun mako ɗaya da aka tafi, amma hakan bai hana Dee samun waje ya zauna ba idanunsa kan kofar Queen Amina. Kamar kullum yau ma Amatullah shiru, hannu ya sa ya ɗauko wayarsa, ya sake kira karo na ashirin kenan a ranar, abin da ya saba ji yau ma hakan aka ce, wato “The number you dialed is switched off”2 Cikin damuwa ya na shirin tashi ya tafi ya hango wata ta fito daga Queen Amina, idanun shi kan ta ya na mata kallon sani har ta motso kusa da shi, sai a sannan ya gane ta, ko shakka babu ta na daya daga cikin matan da ya taba ganin Amatullah da su. Cikin sauri ya tashi ya na mai fad’in “Salamun alaikum, sannu ko Mamanah”12 Ganin da ita ya ke ya sa ta tsaya cikin fara’a ta amsa da “Waalaikumus salam, sannun fa” Ta amsa a takaice. “Ni kuwa kamar na san ki, na taba ganin ki da Amatullah, ke kawar ta ce ko?” “Kwarai da gaske, ashe za ka gane ni, ina wuni ya karatu?” Cewar Maman Jafa’ar wacce farin cikin Dee ya gane ta ya mamaye fuskar ta. ” Lafiya lau, mun gode Allah. Ina mutuniyar ne? Ina fatan dai ba har ta wuce gida ba” Dee Yusuf ya tambaya ya na mai fatan samin hadin kai a wajen Maman Ja’afar. Maman Ja’afar kuwa wacce sam ba ta san halin da Amatullah ke ciki ba, zuciyar ta ɗaya ta ce “Ai fa tun sassafe ta wuce dan ko nima ban same ta ba, ka gwada wayar ta kuwa?” “Eh na kira a kashe, gashi kwatancan gidan na su da ta min ne ya dan kwanta min” Cewar Dee, cikin ran sa roko yake Allah ya sa Maman Ja’afar ta bashi abinda ya ke bukata. Nan ta ke Allah ya amsa ma sa, jin Maman Ja’afar na fadin2 “Ai fa gidan na su Amatullahi ne cikin lungu, bari in gwada sake yi ma ka kwatancen ko za ka gane…….”4 Nan ta kwantata masa gidan tsaf, Dee Yusuf na mai godiya su ka yi sallama. Maman Ja’afar kuwa cikin jin dadin ashe dai Amatullah da Dee soyayya ta habbaka har ya na neman gidan su shi ne ba ta fada mu su ba, Allah ya hada su kuwa za ta sha tsiya, ta tafi zuciyar ta cike da farin ciki.5 **** Komawar Amatullah gida bai sa ta samu wani kwanciyar hankali ba. Sai da ta gaishe da Baban Sasa da su baffaninta sannan ta shige gida. Daga Baban Sasa har su Baba Zubairu babu wanda ya mata maganar auren ta, ko na wanda ake jira ta turo, wanda hakan ba karamin sauki ta samu ba. Gwaggo kuwa ba ta sake zani ba, har ila yau fushi ta ke da diyar ta ta, dan haka bayan ta gaishe ta dakin ta ta shiga ta yi gum kamar daddawar daka. Da la’asar bayan ta idar da salla ne ta yanke hukuncin fita can babban tsakar gida ita ma ayi kai kawo da ita, duk da dai ta na tsoran abun da zai je ya dawo. Sanye ta ke cikin riga da siket dinkin atamfa, atamfar kore ne da ja. Sanin yanayin gidan na su ne ya sanya ta sanya hijabi. Ta tarar da duka matan gidan zaune a tsakar gida bisa ga al’adar zamantakewar gidan, kowacce mata na hidamar gaban ta, wato kujiba kujibar daura na dare, Matar Baba Zubairu ce ke mai daka, sai kuma matar Baba Muhamadu wacce ke yin tankade. Sauran yanran kuwa tare su ke da Mahaifiyar Saifullahi wacce su ke kira Hajiya tare da Gwaggo, kowa da nashi tiren dauke da shinkafa yar hausa sun dukufa ana ta tsinta. Ganin ta budar bakin mahaifiyar Saifullahi sai cewa ta yi “Ah ah su amare ashe ana ganin ku a tsakar gida?” Sai a sanannan kowa ya lura da ita, Gwaggo kuwa takaici ne ya sa ta dauke kai, dan tabbas ta san fitowar Amatullah tsakar gidan nan babu abin da zai jawo mata sai bacin rai.2 STORY CONTINUES BELOW “Sannun ku da aiki Hajiya” Cewar Amatullah yayinda ta sami waje kusa da daya daga cikin kanan na ta, ta na mai sa hannu cikin tsintar ba tare da ta kula da kallon da Hajiyar ta bi ta da shi ba, cikin ran ta kuwa fadi ta ce ba a banza Saifullahi ke da hali irin na sa ba, gado ba karya ba ne. Daga waje kuwa Saifullahi ne zaune bisa benci, abin duniya ne ya ishe shi, gashi dai sati ɗaya ya rage amma Amatullah shiru ta ki kawo wanda ta ke ikirarin masoyin ta ne, babban abin tashin hankalin sa bai wuce zaman Nigeria ba, Allah Allah ya ke ya hada ‘yan komatsan sa ya tafi. Ya na cikin wannan zurfin tunanin sam be ji alamun mota ba, bare ma ya san da tsayuwar ta. Haka kuma jin an furta3 “Kai yaro ya ka nan, nan ne gidan su Amatullah?” Bai sa shi daga kai balle ya kalli wanda ke tambayar da wanda aka tambaya ba. “Eh nan ne” “Shiga ka ce ta zo ana sallama da ita” Yaro ya amsa da toh, har yayi gaba ya dawo ya na mai faɗin “In jiwa zance?” Shiru yayi kamar mai nazari, kafin daga bisani ya furta “Ka ce in ji Dee Yusuf” Karaf a kunnan Saifullahi, tuni ya ɗago ya na mai duban gefan da mai maganar ke tsaye, jingine jikin mota, irin motar nan ne masu numfashi, yaro kuwa gida ya shige a guje domin kiran Amatullah. Kallon shi ya ke cike da mamakin abin da idanunsa ke gane masa, dan kuwa bai taba tsammanin wanda ya kai daidai da rabin Dee zai kusanci bagidajiya kamar Amatullah ba. Sanye ya ke cikin farar shadda gidzna dinkin nan da ake kira tazarce. Ba wani aiki shaddar ta sha ba amma yanayin kwarjini da jiki irin na Dee Yusuf sai kayan ya karbe shi kwarai. Hular kanshi zannabukar ba karamin Kara ma sa kyau ta yi ba, haka kuma takalmi har da agogon hannun sa babu wanda be sanya gwiwar Saifullahi sanyi ba, dan kuwa in dai kwarjini, wayewa da kuma ado ne kowa ya ga Dee sai dai ya shafa Fatiha.6 “Wai kuma Amatullah ya zo nema?”8 Tambayar da ya ke yiwa kan sa kenan yayinda yaji wani abu mai kama da kishi ya tokare masa kahon ciyarsa. Amatullah kuwa kamar daga sama sai ga yaro ya shigo, da karfin sa ya furta “Wai Amatullah ta zo in ji Deee Yusuf” Gaban ta yayi mummunar faduwa, tuni ta kai kallan ta ga Gwaggo wacce ta tsaya cak ba tare da ta dauke idanu daga kan tsintar da ta ke ba, sauran ahalin gidan kuwa idanu su ka zubawa Amatullah, musammam Hajiya wacce da ma kiris ta ke jira, aikuwa sai ta sa guda “Ayyiriri ahayye!! Ashe dai sirikin na mu ne a tafe…..”2 “Ka je ka ce ba na nan” Amatullah ce ta katse harguwar Hajiyar. In da shi kuma yaro ya sake juyawa da gudun shi. Hajiya na fadin “Toh fa, toh menene na munafuncin kin fita? Na ce dama abin da ki ke jira kenan?” Shiru Amatullah ta yi mata, in da ta ke rokan Allah ya rufa mata asiri Dee ya tafi, ko wa ya mata wannan aika aikan be kyauta mata ba. Yaro na fitowa ya dubi Dee wanda idan ya lura da Saifullahi toh sam bai nuna wata alama ba. Ya ce “Amatullah din ta ce ba nan….”2 Saifullahi ya tsinci kan shi ya na mai sakin numfashi, wanda hakan yayi daidai da saukar Baba Anas, kuma ya ji furacin yaro. Bayan ya sallami mai achaba, ya na duban Saifullahi ya ce “Saifullahi bako mu ka yi ne?” Ganin Mahaifin na sa Saifullahi ya taso, shi kuwa Dee karasowa yayi gaban Baba Anas har kasa ya durkusa ya gaishe shi. Hannu Baba Anas ya bashi ya na mai tada shi tsaye, idanun sa kan Saifullahi, shi kuwa Saifullahi cikin shan kamshi ya furta “Baba ni ma ganina da shi kenan, kamar Amatullah ya ce ya ke nema” STORY CONTINUES BELOW Jin haka Baba Anas ya dada faɗaɗa fara’a, cikin farin ciki ya furta “Assha, bakon Amatullah shi ne za ku bar shi a waje haka? Sannu da zuwa, shiga maza ka yiwa Amatullah magana, sai kuma ka kimtsa mu su wannan falon na zaure” Jigum Saifullahi yayi cikin jinjina maganar, shi ne ma zai je ya kira Amatullah?4 “Ba ka ji ba ne Saifullahi ka tsaya sororo kamar soko?”8 Cewar Baba Anas cikin nuna kulewa da yanda Saifullahi ya yi. Ran sa idan yayi dubu ya baci haka ya wuce ciki ya na jin Baba Anas na tambayar Dee ya manya da mutan gida. Ganin Amatullah wani saban bakin ciki na ya turnuke zuciyar Saifullahi, tsayawa yayi ya na duban ta takaici ya sa ya kasa bude baki ya aiwatar da sakon da Baba Anas ya aiko shi. Hajiya ce ta ce “Ah ah Saifu yaya ka shigo ka tsaya hakan nan? Na ce dai lafiya?” Kafin ya kai ga ba ta amsa Baba Anas ya shigo, tun daga soro ya ke fad’in “Kai Saifullahi ka fada mata? Ina Amatullahi din ne? Kai ka ji shasha nan ka zo ka yi tsaye?”2 Ya karasa maganar ne ya na duban Saifullahi wanda ya haɗe fuska kamar wanda be taɓa fara’a ba a rayuwar shi ba. Baba Anas na duban Amatullah wacce ke raba idanu ya ce “Ke Amatullah ba a shaida mi ki kina da bako a waje ba?” Kai ta girgiza al’amar ah ah dan fargaba ta kasa magana. “Ahaf kai kuwa Saifullahi ba ka yi kyawun hali ba, in dai wannan yaro na waje shi Amatullah ke bida wallahi ya min dadi, yaro ana ganin sa an ga dan manyan mutane, ga kamala ga kwarjini wallahi har kasa ya durkusa ya gaishe ni, maza ta shi ki je Amatullah, Allah ya sanya alkhairi, ya tabbatar mana da alkhairin sa” Jin haka ya sanya Gwaggo jin sanyi cikin ranta, ashe dai dan mutunci Amatullah ta samu. Taikaici da bakin ciki ya sanya Saifullahi ji kamar kasa ta bude ya shige, nan ya kara tsanar Amatullah. Juyawa kawai yayi ya fice ya bar mu su gidan. Amatullah kuwa da kyar kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta fita, kan ta a kasa ta wuce su Gwaggo, cikin ranta addua ta ke Allah ya sa kar Baban Sasa ya ji zuwan Dee, da niyar sallamar sa ba tare da bata lokaci ba ta isa ga falon da Baba Anas yayi masa iso. Dan karamin falo ne mai dauke da setin kujerun kushin. Karamar kujera ya samu ya zauna ya na mai sakar zuci, damuwar shi Allah ya sa kar fushin da Amatullahi ke yi da shi ya karu, musammam jin yaro ya ce ta ce a sheda ma sa ba ta nan. Sallaman ta da shigar ta falon lokaci daya ne, ganin ta kamar wacce aka jefo ya sanya Dee tashi tsaye, ya na mai idanun ta da ya cika da kwalla ya ce “Amatullah……” Hannu ta daga masa tare da faɗin2 ” Dakata malam! Ka rufa min asiri ka fita ka bar gidan nan!” “Amatullah……..” “Na ce ka fita!!!!!” Amatullah ta katse shi cikin tsawa da fada. Wanda hakan ba karamin motsa zuciyar Dee yayi ba, amma maimakon ya fita, sai ya koma ya zauna abin sa. Cike da takaici yayinda hawaye ke fita daga idanun ta, daya na bin daya, ta zo gaban shi ta tsugunna, cikin murya mai karya zuciya ta fara magana ” Me zai sa ka zo gidan mu bayan ka san babu aure a tsakanin mu? Me zai sa ka dada tayar min da hankali bayan tashin hankalin da na ke ciki? Ka rufa min asiri ka tafi, wallahi sati daya ya rage Baban Sasa ya saka ranar aure na da Saifullahi…..”2 Zufa ne ya fara keto masa, hannu ya sa ya cire hular kan shi yayinda shi ma din ya sauko daga kujera, farar shaddar da ke jikin sa bai hana shi zaman dirshen a kan carpet ba. Fadi ya ke “Me ka faruwa Amatullah?” “Ka tashi ka tafi!” Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani ya furta “zan tafi, na mi ki alkawarin zan tafi, Amma sai kin saurare ni, kin kuma faɗa min abin da ke faruwa, dan Allah, dan soyayyar da ki ke yiwa Allah” STORY CONTINUES BELOW Hawaye ta share, ka na ta ce “Zan faɗa ma ka, zan kuma saurare ka, amma ka sani wannan shi ne magana ta karshe da zai shiga tsakanin mu” Kai gyada mata alamar amincewa. Nan ta kwashe duka halin da ta ke ciki ta fada masa, ta kare da “Duk yanda na so kujewa auren Saifullahi dole sai na aure shi, duk yanda na so na ji furucin soyayya daga gare ka a banza, domin kuwa bakin alkalami ya bushe, tun ran gini tunran zane…….”2 yanda ya ke zaune dirshen kasa haka ita ma ta zauna, idanun sa sun kaɗa sun yi jawur, ji ya ke ina ma Amatullah halaltacciya ce a gare, da ya janyo ta jikin sa, ya rungume ta har sa ya yaye mata gaba daya damuwar ta, wanda ya ke sila da wanda ba shi ne sila ba. A hankali ya fara magana kamar haka “Ba mu da zabi akan addinin da aka haife mu da shi Amatullah, haka mu ka tashi mu ka tsinci kan mu ciki. Kamar yadda ki ka sani sunan mahaifina Yusuf, Musulmi ne kamar ke….”2 1983 “Duk wanda ke Department of Mass communication ya shaidi soyayyar da ke tsakanin Yusuf Haɗeja da Binta Sule. Duk da yana gaba da ita da shekara biyu hakan bai hana soyayyarsu tafiya yadda ya dace ba, Mahaifina asalinsa Fulanin Haɗeja ne, dogo ne fari kyayyawa mai cike da haiba. Ya fito gidan malanta, don a ƙaidar gidansu yaro baya wuce shekara goma sha ɗaya bai haddace ƙur’ani ba. Hakan ya kasance da shi. Ko da ya je ma iyayensa da zancen mahaifiyata ba su yi na’am ba kasancewar ta yar ƙasar gongola, sun ce garin su da nisa, da dadin baki ya sha kan iyayensa su ka amince amma bayan da bincikensu ya tabbatar masu da cewa mahaifiyata ma’abociyar littafi ce da soyayya ya sanya ta amsar musulunci, nan su ka tuɓure su ka ƙi. “Yusufa ka rasa matar da zaka aura sai wacce ta tuba a dalilin soyayyar ka” Baffansa Sheikhi ya faɗi cikin ɗacin rai. “Baffa ka dubi girman Allah kar ka haramta min abin Ubangiji ya halalta min” yace cikin hawaye. Kallonsa Baffan yayi na yan mintoci kafin ya ce “Sannu tatacce ɗan uwan koko, tun da ka matsa zan jagoranci komi” ya faɗi yana mai kauda kai, godiya mahaifi na ya shiga yi har sai da Baffan nasa ya ce ya tashi ya tafi. A karshen shekarar aka ɗaura auren iyaye na. Auren bai hana su kammala karatunsu ba duk da kasancewarsu ƙarkashin gandun mahaifansa. Rayuwa su ke cikin kwanciyar hankali matukar suna cikin garin Kano ne, amma da zarar sun isa Haɗeja duk wani kwanciyar hankali kan kare musu saboda kyara da mahaifiya ta ke samu daga yan uwan mahaifina, wasu kan kira ta da tubabba wasu ma kai tsaye arniya su ke kiran ta. Girkin da ake yi tare a cikin gidan aka ɗauke mata a bisa hujjar ba sa cin abincin arna. Takan zauna a ɗaki ta yi kuka, ta ji takaicin kasancewa cikin mutanen da basu darajar ɗan adam ba. Duk da cewa ta taso cikin al’ummar da akan samu bambancin addini a ahali ɗaya, ta san akwai karramawa ta musamman ga duk musulmin da ya zaɓi barin musulunci zuwa addinin Yesu kiristi duk kuwa da a can ba ta ganin ana wulakanta wainda su ka musulunta. A haka mahaifi na ya kammala jarrabawarsa ta karshe a fanin jarida tare da samun gurbin aiki a gidan rediyo Nijeriya Kaduna. Murna sosai su ka yi don a tunaninsu damar yin rayuwar farin ciki ne ya zo masu. “Wai naga se kumbure-kumbure ka ke, ni da za ka bari da kewa ma farin cikin nasaranmu yafi na kewan” tace tana jan kumatunsa, in idanunta ba su faɗi mata ƙarya ba hawaye ta gani kwance a idanunsa. “ina baƙin cikin halin da za ki shiga bayan na tafi, ki kula da kanki ki kula da ajiyar da ke tattare da ke” yace yana mai rungume ta, jikinta yayi sanyi, amma ta daure ta kara masa ƙarfin guiwa. Cikin kewan juna ya ɗauki jiki zuwa Kaduna in da zai ƙarasa duk wani abin da ake bukata don fara aiki.9 Ita ta raka shi har tasha in da ya shiga motar da za ta wuce da su sannan ta wuce makaranta in da za ta ɗauki darasi. Kwana uku bayan tafiyar sa tana gida tana nazarin littafanta aka yi sallama. Sai da ta yane jikinta da mayafi sannan ta fita, yayyin mijinta biyu ta iske tsaye kowanne fuskarsa turɓune. Gaida su tayi cikin sanyin jiki tana mai kaucewa daga bakin kofa don su shigo. “kulle gidan ki taho mu je” Nasiru ya faɗi a kausashe, faɗuwar gaba ta ji amma ba ta tuna komi na sharri ba. Babu wanda ya ce da ita komi har su ka isa Haɗeja, taron da ta gani a kofar gida ya sanya ta tunanin mutuwa a ka yi. “wa ye ya rasu?” ta ce a zuciyarta. Haka ta tsallake mazan waje ta shiga gida, duk da ta na ganin yadda ake bin ta da kallo. Dakin mahaifiyar babana ta isa, nan ta iske mutane zazzaune, gaida su tayi amma babu wanda ya amsa mata hakan bai hana mata zama ba, tana zaune wasu mata su ka shigo, “Yusufa kuma sa’i yayi, Ubangiji Allah ya rahama masa” su ka ce suna masu tashi bayan sun ƙarasa musu ta’aziyya. ‘Yusufa kuma sa’i yayi’ ta kara maimaitawa, tana mai fassara kowane kalma. ‘sa’i na nufin lokaci wani lokaci ake ma ta’aziyya?’ ta ce a ranta tana ƙaryata tunanin da ke yawo mata a kwakwalwa. Tashi ta yi a firgice ta yi waje dakin sheikhi ta isa idanunta a rufe, bata damu da maluman da aka yi ma masauki a ciki ba ta isa gareshi tana kuka “Baffa na ji ana Yusufa sa’i yayi? Me ya same shi? Don Allah ka faɗa min” tace cikin kuka da tashin hankali. “Dama tun kwanaki ukun nan ba a ɗauko ki ba?” ya tambaya cikin ɓacin rai. “Yau su Nasiru su ka zo bamu dade da isowa ba” tace tana share hawaye. “Binta ki yi hakuri, duk mai rai jiran lokaci yake yi. Yusuf ko kura ba su kai ba motar su ta hantsala. Yau kwanan sa uku a kushewa, sai kiyi hakuri” ya faɗi yana mai jin sabon radadin mutuwar. Bude baki yayi da niyyar cigaba da mata nasiha ya ga ta sulale ta suma. Kwana bakwai tayi tana jinya nan ma babu wanda ya kula da ita duk a dalilin tubabba ce musuluncinta bai cika ba. Bayan an sallame ta babu wanda ya mata bayanin takaba, sai ma juya mata baya da kowa yayi. Babu mai bata abinci, balle a san halin da ta ke ciki. Ranar da mahaifina ya cika kwanaki arba’in da rasuwa ta musu sallama ta koma makaranta, abin mamaki sai ta iske su Nasiru a ƙofar gida, ba su ce mata komi ba su ka kwashe komi na gidan da sunan gadon mahaifi na ne, ita kuma tun da tubabba ce ba ta da gadonsa. Tayi kuka sosai kamar ranta zai fita don hatta katifar kwanciyar su sai da suka ɗauka, cikin wannan yanayi ta shiga makaranta ko za ta samu kawar da za ta laɓata a hostel. “Binta Yusuf” ta ji an kira ta, share kwallan da ya zubo mata tayi ta juyo. “pastor Abu kai ne da kanka” tace cikin murmushi. Ba za ta mance karamcinsa ba don duk da kasancewarsa pastor ya goyi bayan aurenta da Yusuf sai dai shi bai so ta bar addininta ba. “Ina kika bar Yusuf” yace bayan sun gaisa, ba ta iya ɓoye hawayenta ba, ta ce masa “yau kwanan sa arba’in karkashin kasa” sai ta saki kuka, ganin suna kan hanya ne ya ja ta gefe. “kwana arba’in Binta kuma kike nan? Ba kin musulunta ba? Kin manta 4 month 10 days su ke yi? Gidan ku fa da musulmi. Tsaya su dangin sa ya su ka bari kika fito” yace cikin ɗacin rai. “sun ce basu yarda da musulunci na ba, sun ce ni tubabba ce, sun kira ni arniya” ta fadi cikin kuka, nan ta shiga fadin halin da ta ke ciki, shi kuma bai yi ƙasa a guiwa ba ya kaita gidansa. Daki ɗaya suka ware mata, nan take duk wani ibada nata, in ba wani kwakkwaran dalili ba, bara shiga makaranta. Mutane na ta shigowa mata ta’aziyya yayin da mabiya addinin kirista ke bata duk wani kulawa. Bayan ta rubuta jarrabawa ta je garinsu Hong na jihar Adamawa. Sai a lokacin iyayen ta su ka ji zancen rasuwar Yusuf, sun yi alhini kuma sun ji haushin halin da yar su ta shiga. Cikin ta na da wata tara ta haihu, lokacin ta hakura da musulunci ta koma addininta na gado, addinin da ke karrama duk wanda ya shige ta, addinin da ta ga basa nuna yatsa ga wasunsu. Washegarin haihuwarta yayan ta, Baffa na Haruna ya tashi tun daga hong har Haɗeja ya sanar masu da haihuwa, nan su ka ce da shi sun bar musu don basu da bukatar jinin arna. Yana dawowa ya sanya min suna David. Bayan shekara guda ta sake aure, mijin ta shi yayi min komai, dangin mijin ta su suka zame min dagin uba, su na sani Amatullahi…….”7 Nisawa yayi yayinda ya ke kallan furkar Amatullah, be gushe ba ya cigaba “Amatullah, na taso a matsayin Margi ba bahaɗeje ba, duk wani gata da yaro zai samu na samu daga mijin mahaifiya ta da Baffani na. Na taso cikin al’umma da zaki iya iske mata musulma miji kirista ko mata kirista miji musulmi….”4 Kan gwiwowin sa biyu ya tsaya yayinda hawaye ke zuba daga idanun sa, ya ce “Sanadiyyar abin da ya sami mahaifiya ta, Ni da ke Amatullah kowannan mu za mu iya yin addinin mu, Wallahi babu abin da zai hana ki musuluncinki, ki dubi girman Allah ki amince da aurena, in ma so kike na je Haɗeja dangin mahaifi na su zo neman aurena wallahi na amince. Kiyi min rai Amatullah, ki amince da son da nake maki…..”