TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 7
Rana ɗaya aka yi komai aka gama. La’asar na yi Baban Sasa ya ce a shirya amarya a kai ta ɗakin mijin ta. Nan fa amarya kuka har da majina, musammam da aka ce ta zo ta yiwa Gwaggo sallama.2 Hannayen ta biyu ta sa ta riƙe ƙafar Gwaggo da kyar aka iya bambare hannun aka wuce da ita ɓangaran Hajiya. Nan kuwa ruwan habaice habaice su ka sha daga dangin Hajiya. Haka ma Hajiya wacce ta dubi Amatullah da ke tsugunne gaban ta fuskar ta rufe da lafaya, buɗar bakin ta sai cewa ta yi ” Toh mu dai babu abin cewa tunda ta faru ta kare ramamme ya zagi maye, Allah dai ya sa za ki iya kula da mijin na ki, dadin ta dai namiji mijin mace hudu ne…..”2 “Bare ma ɗiyar ta mu ai san kowa kin wanda ya rasa ce, wajan kula da iya zaman duniya ba a ce mata komai, uwar gida sarautar mata ba, kowa ya zo bayan ki ya ke….” Cewar kanwar Gwaggo yayinda yan uwa Gwaggo su ka kara karfafa mata gwiwa da guɗa. “Toh ai sai ku tashi a kai ta, Allah ya sa a dace” “Allahumma amen” Cewar dangin Gwaggo, in da su ka tayar da Amatulah. Kamar yanda su yan uwan Hajiya da yayyan Saifullahi ba su fasa yada habaici ba haka su ma dangin Gwaggo ba su fasa guɗa ba. Ɗakin Baba Sasa aka kai Amatullah, nan aka tarad da Mahaifin ta tare da su Baba Zubairu da Baba Anas. Daya bayan ɗaya haka duka su ka mata faɗa tare da sanya albarka, ko da aka zo kan Mahaifin Amatullah sai cewa yayi “Tashi ki tafi dakin mijin ki ɗiyar albarka, duk abinda za ki yi ki yi da halin ki, ba ni da haufi kan ki, kin haifu Amatullah, Allah ya sanya mi ki albarka” Ya karasa maganar ne yayinda yar kwalla ke shirin fita daga idanunsa. Nan ma fa Amatullah ta ce ba ta tashi, aka yi aka yi, ta cije kuka ta ke harda wayyo Allah. Mahaifin ta ne da kan sa ya riko hannun ta, sannan ta yarda ta mike, har mota ya kai ta sannan ya barta hannun manya ya koma ciki. Yan uwa da abokan arziki su ka shige mota, aka dauki hanyar gidan amarya. *** Tafiya ce ɗoɗar daga Amaru zuwa filin mallawa da ke sabon layi, filin cikin na gadon su Baban Sasa ne ya mallaka, sanda ake yanka filayen ana siyarwa ya so ya siyar sai kuma ya yi tunanin gine shi. Babu laifi gidan ginin zamani ne, flat ne, drive in mai dauke da daki uku kowanne da bandakin shi ciki, da kuma madaidaicin kitchen, sai kuma katon falo guda. Su Zulaikha ne su ka yi kokarin zauna mata kafin ango ya zo kar a barta ita kadai. Amma shiru babu Saifullahi babu alamar shi, dan haka sallama su ka mata, ta na ji ta na gani su ka barta ita kaɗai duk magiyar ta da su zauna amma umurni ne daga baban Sasa cewa kada wanda ya kwana a gidan duk da hakan al’adar mutan zaria ne. Amatullah gwanar tsoro, suna fita ta sa mukulli ta garkame ɗakin ta, ta shige toilet ta dauro alwala bisa dadduma ta shiga jera salloli ta na rokan Allah sauki bisa lamarin ta, nan bacci mai nauyi ya sace ta. Yunwa ne ya tada ita da asubar fari. Sai da ta yi sallar asuba, ba tare da ta cire hijabin da ta yi sallah da shi ba, a hankali ta bude kofar ɗakinta ta ɗan leƙa falon, duhun da ta gani ya bata karfin gwiwar fitowa ta na mai haska falon da wayan ta domin neman hanyar kitchen. Babu shakka su Gwaggo sun tsantsara mata falon na ta da kayan alatu, kujerun ta ruwan zuma da kanana filullukan da aka jera ba karamin shiga yayi da labulen falon ba. Ganin kofofi hudu daya ya ɗan yi kusa da dakin ta, sai kuma ɗayan bangaran yamma kusa da kofar shigowa falon, sai kuma ɗayan wanda ke can gefe guda ya sa Amatullah ta yi turus, dan kuwa ba ta san wanene wanne cikin su ba, gashi yunwa ta ke ji kamar ta yi ihu. Lissafin ta wannan na kusa da ita zai iya kasancewa dakin mai gidan, wancan na kusa da kofa ya zama na baki, dan haka na can gefe shi ne kitchen, kai tsaye to nufe shi. Zuciyar ta daya ta kama mubudin kofar ta bude ta na mai tura kan ta ciki. Hasken wutan lantarki ne ya fara ziyarta idanun ta, kafin idanun ta ya gane mata wanda ke tsaye gaban fridge daga shi sai gajeran wando, ya bata baya hannun sa dauke da gorar ruwa. Da sauri ta juya cikin rawar jiki, wayar da ke hannun ta ce ta sullube ta faɗi kasa. Karar faduwar wayar ya sanya shi jiyowa fuskar shi cike da mamaki. Bacin rai ne ya maye gurbin mamakin da ya bayyana fuskar shi ganin Amatullah, cikin sauri da tsungunna ta dau wayar da niyar ficewa, ya dakatar da ita cikin tsawa ya ce “Ke wace irin bagidajiya ce wai? Zo nan Malama!” Tsayawa ta yi cak idanun ta kasa, ita ba ta fita ba, haka kuma ba ta karasa in da ya ke cikin kitchen ɗin ba. “Ba da ke na ke magana ba! Ki zo na ce!” Ya kara daka mata tsawa a karo na biyu in da ta tsinci kan ta tana mai karasawa gaban sa, da kyar ta yi karfin hali ta kai kallan ta ga fuskar sa ba tare da ta kalli kirgin sa ba, yanayin kallan takaici da ya ke mata ya sa ta sake yin ƙasa da na ta idon ka na ta furta “Ban san kana kitchen ɗin ba……” “Iya ka tarbiyar da aka koya mi ki kenan? Ba ki iya gaisuwa ba? Ga gidadanci ga rashin tarbiya….” Lebben na kasa ta cije cikin takaici da jin zafin furucin Saifullahi, kafin ta kai ga ba shi amsa sai ji ta ya ce “Bani hijabin nan!!!!!” Jin maganar kamar kunnen ta ke mata zagi ya sa ta ɗaga kai da sauri ta na mai fidda idanu. Kai ya girgiza ya ce “Yes kin ji ni da kyau, ki ciro hijabin jikin ki ki bani yanzun nan!!!!” Baya ta ja tana mai girgiza kai yayinda zuciyar ta ke dukan uku uku ta furta “Dan Allah dan annabi ka yi hakuri…..” “Dalla malama hakurin me ki ke bani, just do as I said ko kuwa ni na cire mi ki! you are so irritating!!!!” Hawaye ne ya fara zuba daga idanun ta, ganin ba ta da niyar bin umarnin shi ya sanya shi tinkarar ta, ganin haka itama ta fara ja da baya tana fadin “Menene haka wai ya Saifullahi?” “Just remove the damn thing and give it to me!” Jiki na rawa ta ciro hijabin, ta rike hannun ta idanun ta kallan kasa yayinda hawaye daya ke bin daya. Kallo ya bita da shi, kasancewar ba shiri bacci ya sace ta daren jiya, atamfar da aka kai ta da shi ne jikin ta. Kai ya girziza ya na mai nuna ta da hannu tun daga sama har kasa ya ce “Just imagine! Na tabbatar da wannan atamfar a jikin ki ki ka kwana tsabagen gidadanci! God you’re so local Amatullah!!!” Ya sa hannu ya fizge hijabin daga hannun ta ya yi wulgi da shi cikin kwandan sharan da ke cikin kitchen, in da Amatulah ta bi shi da kallo, kafin ta dawo da kallan ta ga Saifullahi. Ya na nuna ta da dan yatsa ya ce ” Ni Saifullahi, wanda aka ɗaura min auran ki akan dole, daga yau har ki karaci zaman ki gida, na umarce ki da ki dena saka waccan abu, Kar na sake ganin ki da hijabi Amatullah! Na haramta mi ki saka hijabi cikin gida na!!! Bagidajiya kawai!!!”2 Ya na gama magana ya fice yana huci kamar zaki. Ya bar Amatullah zube a kasa ta na sharbar kuka, shin ashe akwai ranar da za a haramta mata sanya hijabi? Kuma mijin ta? Wannan masifa har ina!6 “Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun” Furucin da ta ke yayinda tsanar Saifullahi ke kara ratsa zuciyar ta. Jan jiki ta yi zuwa ɗaki bayan ta nemi abin da za ta riƙe hanjinta da shi. Allah ya isa kuwa ta masa ya fi sau a ƙirga don ba ta ga dalilin da zai sa ya haramta mata sa hijab ba, haka kawai ta dinga tallan jikinta gareshi kamar wacce ba ta da kishin kanta. Da ire-iren tunanin nan ta kammala cin abincin, miƙe kafafu tayi ta jingina nan ma wani sabon bacci yayi awon gaba da ita. 4 Hayaniya ya tayar da ita sa’ilin da yan gidansu su ka iso wainda mafi akasarinsu innoninta ne, bayan ta gaida su, wasu na mata tsiya ne su ka sanya ta je ta yi wanka saboda masu shigowa ganin amarya. Atamfarta ta sanya ɗinkin riga da skirt, sosai ɗinkin ya zauna a jikinta, golden color din da ke jikin atamfar wanda ya sakaya cofee da peach ya fito da kalarta tare da bayyana madarar kyawun da ta mallaka. Hijab golden ta ɗinka ma kayan har ta ɗauko za ta sanya 5 “A matsayina na mijinki, na haramta miki sanya hijabi a cikin gida” take wasu hawaye su ka zubo mata, jujjuya hijabin ta ke a hannun ta hawayen ba su daina zubar mata ba, takaicin ta yanda cousins ɗinta maza ke kaikomo a cikin gidan suna taimakawa wajen ƙara kimtsa gidan. “Ga wannan ki yafa” cewar innarta Aisha, kallon gyalen ta yi, kamar ta ce A’a amma shakkar Innar tata da take yi yasa ta amsa. Ana faɗin matar soja sojace bata yarda ba sai akan innarta Aisha, don in ta rikide musamman akan abubuwa da ya jiɓinci ado da kwalliya sai ka rantse wani hafsin soja ne a fagen yaƙi. Gyaran da aka ma fuskarta da yanda ta yane jikinta da gyalen ya fito da ita ainun. “MaashaAllah! MaashaAllah!!” kawai ake faɗi, nan sai ta hau Saman gado fuskarta lulluɓe da gyalen amma tana iya hango su. “Ai ni jiya hankali na ya ɗauke wajen hidimar yaya mairo, a ce amarya da hijabi, kai ke kuwa izalarki ta yi yawa wallahi” inna Aisha ta faɗi tana mai yaba kyawun yar tata. Zamanta a legas ya sanya duk wani darun da aka yi ba ta da labari, itace ke bi ma Goggo Mairo, sun yi aure da mijinta tun tana shekaru goma sha huɗu shi kuma an yaye su a depot din zaria. Allah cikin ikonsa ya haɗa mijin nata da oga nagari ya masa hanya ya tura sa makarantar horar da sojaji ta NDA yayi shekaru biyar ya fita da anini. Yanzu har ya kai ga Jan wuya a aikin soja. “Ai yaya indo ni na rasa kamun jiki irin na Amatullah, su ne yan fatawar ko hoda mace ba ta sawa, amma wainda su ka san darajar mata sun san su ake kira first class ladies” faɗin Inna Hafsatu kanwar su goggo mairo ce, hakan ya sanya yan uwan hajiya da su ka shigo fita cikin sanyin jiki, da sun shigo suna musu yatsina ne. Suna fita kannen Goggo Mairo su ka sanya shewa. Haka su ka yini suna gyara da taya Amatullah zama sai da aka kira magariba sannan duk su ka watse a gidan, suna mai masu fatan Alkhairi. Kamar juya Amatullah ba ta jira shigowar Saifullah ba ta kulle ɗakinta, sai dai ta iya canza kaya zuwa na bacci kafin ta bi lafiyar gado. STORY CONTINUES BELOW *** Washagari da misalin karfe goma sha biyu Saifullahi ya isa Kano gidan su Ayush. Kamar yanda aka saba karɓar shi cikin mutunci da girmamawa haka yau ma aka masa. Duk da kasancewar ba wannan ne zuwan shi gidan na farko ba bai hana shi bin gidan da kallo ba tamkar bakauye tsabagen tarin dukiyar da ke gidan. 2 Falon baki aka sauke shi, in da ma su aiki su ke ta kai kawo wajen kawo masa abinci da kayan marmari. Sai bayan sun gama da minti ashirin sannan Ayush ta shigo ta na taku ɗai ɗai da rangwaɗa, baki da hanci da idanu gaba ɗaya Saifu ya saki ya na kallon ta. Sanye ta ke cikin doguwar riga ja, rigar ta kamata kwarai ta zauna jikin ta, ko mayafi ba ta saka ba, sai daurin da ta yi da kallabin kayan, irin wannan daurin da ake kira ture ka ga tsiya. Kusa da shi ta zauna kamar wacce za ta shige cikin sa. Tuni kamshin turaren kamafanin the body shop ya mamaye hancin sa. Fuskarsa cike da fara’a ya ruko hannun ta ya na mai faɗin “Ayush mine, queen of beauty” Idanun ta kaɗa ta yi fari, cikin kissa ta ce “Saif Man, wallahi na yi kewan ka ina fata dai ka zo min da sakon turo iyayen ka su kawo gaisuwa, tun da dai ka ki yarda mu yi maganar a waya” Hannun ta ya saki, yayinda ya shafa kyeyar sa cikin kame kame ya ce “Haba mana ke kuwa, daga zuwa babu sannu bare ya hanya?” 2 Kunya ne ya rufe ta, kana ta ce “Afuwan, Dad ne ya ke ta min maganar wallahi. Ya hanya? Hope ka iso lafiya” “Lafiya lau Alhamdulillah, dan bani ruwa ni zafi ma na ke ji’ “Kai Mine duk AC da ke busowa ka ce zafi? Ko dai ba ka da lafiya ne?” Cewar Ayush yayinda ta zuba masa ruwan ta mika masa. Sai da ya sha kofi biyu, ga mamakin Ayush har zufa ya ke. “Lafiya lau na ke, oya gist me, have you missed me?” Nan ya fara Jan ta da hira, tun tana biye ma sa, har ta gaji ta sake tambayar abin da ke ran ta. “Aisha……” Jin ya kira ta da sunan ta na ainihi ya sanya ta dagowa da sauri ta na duban shi. “Ki yafe min na zo mi ki da labari mai muni, wallahil azim ba da san rai na aka yi ba, kuma na mi ki alkawarin hakan ba zai sa a fasa auren mu ba……” “What are you saying ne? Ka yi min gwari gwari dan Allah” Ta katse shi cikin nuna gajiyawa. Hannun ta ya sake rikowa sannan ya ce “An daura min aure da yar uwa ta…..” “Hahahahahahaah” Ayush ta katse shi da dariya mai cike da keta. Cikin yanayin firgici da tsoro ya ke duban ta, sai da ta yi dariyar mai isar ta har da kwalla sannan ta furta “You must be kidding me, Kai amma Mine ka iya zolaya wallahi, dan kuwa wannan wasan na ka ai tsokana ne” “I’m serious Ayush, wallahi I’m serious…” “Bura uban nan kayyasa!!!!! Ni za ka kalla ka yiwa wannan maganar Saifullahi? Ka kalli tsabar idona ka ce min an yi maka auren dole? Do you think I’m stupid?” 2 “Ayush calm down, ina san ki, ina kaunar ki, wallahi ba zan iya zama da bagidajiyar da aka aura min ba, I want to marry you…..” “Get out!!!” STORY CONTINUES BELOW Cewar Ayush yayinda da ta tashi tsaye, hanyar fita ta masa nuni da shi tare da sake faɗin “Get out!!!!??” Jiki sanyaye ya tashi, a hankali ya furta “Ayush, listen……..” “Damn you!!!!! Fitar mana daga gida Malam” Jiki sanyaye Saifullahi ya fice. Sai da ya fita sannan ta saki kukan da ya tsaya mata can karkashin makogoro, duniyar nan babu wanda ta tsana kamar Saifullahi. Saifullahi na fita daga gidan masallaci ya nufa yayi sallah ko zuciyar sa ta dan yi sanyi. Yana idarwa ya shiga Kiran wayar Ayush amma ta ki dagawa. Haka ya ɗauki hanyar Zaria ba tare da ya tsaya neman abinci ba, yayinda tsanar Amatullah ke kara ratsa zuciyar sa. *** Ranar da Amatulah ta cika kwana biyar gidan miji Maman Jafa’ar da Zulaikha suka kawo mata ziyara. Ranar Amatulah murna kamar ta goya su. Daki su ka zauna, Zulaikha ce ta takura ita lalle sai ta ga ango, Amatullah ta Kira shi su gaisa. Amatullah da ta yi kokarin buye mu su halin da ta ke ciki, tuni ta fashe mu su da kuka, nan takwashe komai ta fada musu, ta kare da “Kuma rabona da ganin shi cikin gidan nan kwana uku kenan…..” “Ki na nufin ba gidan ya ke kwana ba?” Cewar Maman Ja’afar cike da jimami “In ma nan ya ke kwana ban sani ba, babu abin da ke hada mu” “Toh ai Amatullah laifin ki ne wallahi, mace kamar ki, mace har mace akwai namijin da ya isa ya wulakantaki Amatullah? Wai tsaya duk tarin littafan da na haɗa ki da shi karatunsu ya tashi a banza kenan?” 4 Maman Ja’afar ta faɗa cikin nuna ɓacin rai, ita kuwa Zulaikha tagumi ta yi ta ma rasa na cewa. “Ba dai ya haramta mi ki saka hijabi ba? Toh ai kuwa ya tsokanowa kan sa rashin kwanciyar hankali daga yau Amatullah kanana kaya shi ne kayan sakawar ki, ki karkada masa kugu a sannu zai dawo tafin hannun ki sai yanda ki ka yi da shi….” “Ayya mana Maman Ja’afar….” 2 Cewar Amatullah, kunya ne ya rufe ta. Ita kuwa Zulaikha shewa ta yi tare da faɗin “I trust you Maman Ja’afar, Amma fa mutuniyar ban ji ta na da kananan kaya fa” “Kar ki damu, gashi ai dama na ruko guda biyu, short gown ne duka, kuma in sha Allah ni da kai na zan shiga kasuwa na karo mata” 2 Jakarta ta bude, ta fito da kayan ta mikawa Amatullah tare da faɗin “Oya tashi ki saka mu gani” “Caf wannan mitsitsiyar rigar zan saka?” “Eh yanzu ma kuwa Amatullah” “Gaskiya ba zan iya ba sai ka ce wata yar iska?” 3 “Ni da na kawo mi ki halan ni ce yar iska” Cewar Maman Ja’afar cikin gatse, in da Zulaikha ta kwashe da dariyar mugunta. “Ni ah ah ba haka na ke nufi ba Maman Ja’afar, kayan ne…..” “Idan ba haka ki ke nufi ba toh ki saka kayan mu gani” Amatullah na gunguni ta shige bayi, sai da tai kusan minti goma da saka kayan amma ta kasa fitowa, Zulaikha ce ta buɗe bayin ba ta san sanda ta saka ihu ba, kunya ya rufe Amatullah kamar ta nitse. Riga ce koriya, mai dan ƙaramin hannu iya ka gwuiwa, duk da dai ba wani kama ta yayi ba amma yanayin dirin Amatullah ya sanya rigar kayatuwa jikin ta. STORY CONTINUES BELOW Da zuga suka sanya ta sake gwada dayar, wacce ta ke jar body fitting gown mai tafiya da hankalin duk wani mai kallo, rigar mara hannu ce kuma bata karasa gwiwa ba. Ba ƙaramin kyau Amatullah ta yi ba kamar aljana. “Tsira da aminci ya tabbata ga mahaliccin wannan halitar” Cewar Maman Ja’afar, in da Zulaikha ta kara da “Wow, wallahi kin haɗu Amatullah babu karya!!!” Ita dai Amatullah ta kasa sakewa gaban su ma, bare kuma uwa uba uban gayyar. “Fisabilillahi wannan ba sutura ba ce…..” “Ai dai yau dinnan za ki saka, yamma na yi ki wanka na tsantsara mi ki ado Amatullah, sai Mijin ki ya kasa gane ki” Maman Ja’afar ta faɗa cikin jaddadawa. “Yo ina ma zai ganni, na manta rabon da na ji motsin shi” “Yau kuwa za ki ji” Duka suka sa dariya, ita kuwa kayan ta cire cikin ranta ta na faɗin sa ga wacce za ta saka kayan. Sai da su ka yinan mata, bayan la’asar kamar yanda Maman Ja’afar ta ce , wanka ta tursasa Amatullah ta yi, sai da ta yi mata kwalliya kafin su yi diramar sanya kaya. Ganin an fi karfin ta Amatullah ta sanya yar karamar jar rigar da Maman Ja’afar ta zaba ma ta, ta na mai kudirin cire kayan da sun tafi. Ita kanta ta san ta yi kyau na burgewa da ban sha’awa. Ga body komai cif cif da ta taka sai komai ya motsa. “Big sai bigi babban goro sai magogin karfe..” Zulaikha ce ta ke mata kirari. “Bari Zulaikha, irin su Amatullah ake kira da zaratan mata….” “Ni dai ku bar zigani haka dan Allah” Amatullah ta katse ta tana mai tifke gashin ta da ribon. Nan fa baki su ka ce za su yi halin su. Amatullah ta ja hijabi za ta saka domin rakiya Maman Ja’afar ta kwace tana faɗin “An dai haramta mi ki sanya hijabi cikin gida” 2 Baki bude Amatullah ta bata amsa da “Haka zan fita na raka ku toh? Kai jama’a Allah ya sauwake na fita haka” “Ke Malama wa ya ce fita za ki yi? Iyakar ki bakin kofar falon ki ko gate ba za ki kai ba, dan haka mayar da wukar” Akwatin lafen ta ta bude ba tare da basu amsa ba, kayan kwalliya ta dauka har da body spray da sabulu, ta zuba a leda. Ba su fasa tsokanar ta ba har ta raka su, kayan ta ba su tare da godiya, ji take kamar ta bi su kawai su koma makaranta ta huta. Ran ta ba dadi su ka yi sallama ta rufe kofar falon. Har za ta shiga ɗakin ta ji an kwankwasa kofa, zuciyar ta daya su Zulaikha ne su ka yi mantawa ta koma ta na faɗin “Na face duk wacce ta yi mantuwa ya zama nawa” Yayin da ta bude kofar, ganin wanda ke tsaye gaban ta ya sanya ta mummunar faduwar gaba. Saifullahi ne sanye cikin kanana kaya, farar riga mara hannu da bakin wando. Kallan da ya bi ta da shi tun daga sama har kasa ne ya sa ta tuna da yanayin shigar da ta yi, ‘Kai amma su Zulaikha sun cuce ni!’ abin da ta ce cikin ran ta kenan yayinda ta juya ciki da sauri da niyar komawa dakin ta, nan Saifullahi ya sami damar karewa bayan ta kallo, sai da ya bari ta kai dab da kofar dakin ta ya ce “Malama tsaya!” Turis ta yi ta tsaya, dan kunya kamar kasa ta tsage ta shige. Ta kasa juyowa ta kalle shi, In da ta ke ya karasa duk ya bi ya susuce. Cikin kame kame ya ce STORY CONTINUES BELOW “Ba ki iya sannu da zuwa ba ko? Haka aka koya mi ki?” 2 “Sannun da zuwa” Ta furta da sauri ba tare da ta juya ta kalle shi ba. “Ba za ki juyo ki kalle ni ba iye Amat? Haka mace ta ke yiwa mijin ta sannu da zuwa a garin ku?” Jikin ta ne ya fara rawa, yayin da ta juyo a hankali. Ganin yanda idanun Saifullahi su ka fara juyewa cikin wani yanayi ya sanya ta saurin yin ƙasa da idanun ta. Muryar shi ƙasa ƙasa ya kai hannun shi ga na ta, ya ce “Bari na koya mi ki yanda ake yiwa miji sannu da zuwa Amat” Ba ta ankara ba sai ga ta jikin shi, ba karamin firgita ta yi ganin yanda ya kamkame ta ya na mayar da numfashi. Kuka ta sakar masa mai karfi ta na faɗin 2 “Dan Allah Ya Saifullahi ka yi hakuri, wallahi ba zan sake ba” Maimakon ya sake ta, sai ji ta yi ya fara shafa bayan ta, nan fa Amatullah ta yi kicin kicin ta shiga ture shi, har Allah ya ba ta iko ta kwaci kan ta, Saifullahi yayi baya kamar wanda ke shirin faduwa. 3 Cikin zafin nama ta shige dakin ta tare da sa mukulli ta kulle. Ta faɗa kan gado ta na kukan da ita kan ta ba ta san dalilin sa ba. 3 Kamar wanda kwai ya fashe haka Saifullahi ya ja jikin sa ya zauna kan kujera. Ya san Amatullah ta na da diri amma bai taɓa tsammanin za ta iya rikita shi haka ba, ace kamar shi Saifullahi bagidajiya irin Amatullah ta sanya hankalin shi ya gushe haka! “Hasbunallahu wa ni’imal wakil” Cewar shi a sarari, ya kara da “Kai dama hajar da Baban Sasa ke hango min kenan, gwara na kwashi rabo na na mure tunda kuwa halak dina ce, kan uba Amatullah mace ce!!!” 3 Kai ya ci gaba da jinjinawa dan kuwa dai jikin sa ya mutu murus, gashi Ayush ta dena daga wayar sa, ta kuma ki ma sa reply na sakonnin alkawarin auren ta da ya ke tura mata kullum bare ya kira ta ko a waya ne ya rage zafi. Nan yayi kwance inda surar Amatullah ke ma sa gizo. Sai da aka kira magariba ta iya tashi ta yi sallah. Bayan ta idar ne ta kira Maman Ja’afar ta na mata mitar masifar da ta jaza mata ranar. Ta kare da “Dama Ya Saifullahi dan iska ne Maman Jafa’ar!!!” 6 Dariya ta yi mata, ita lamarin daidai ya mata sannan ta yiwa Amatullah faɗa da Kar ta sake ture mijin ta, haramun ne, itama ai mai sani ce ta san tsinuwar malaiku dai babban lamari ne. Nasiha ta mata sosai, ta kara jaddada mata gobe goben nan za ta aiko da sauran kayan. Ita kuwa Amatullah ta ce Allah kashe ta ba za ta sake saka irin kayan ba. Da haka su ka yi sallama Maman Ja’afar na murna ta kira Zulaikha ta labar ta mata. Amatullah ba ta kara yarda ta fita daga dakin ta ba bare ta haɗu da Saifullahi, daren ranar haka ta kwana da yunwa. **** Washagari da safe, sai da ta tabbatar ba ta jin motsin Saifullahi ta fito kitchen sanye da material shudi, riga da siket ne ya karbe ta kwarai. Yunwar da ta ke ji ya sanya ta yagar buredi ta na ci hakan nan kafin indomie din da ta daura ya nuna. Daf da kunen ta ta ji ya furta “Ni ki ke gudu ko Amat?” Da sauri ta ja gefe, yayin da da hanjin cikin ta ya kaɗa ganin Saifullahi tsaye gaban ta, kamar ranan yau ma daga shi sai gajeran wando. Idanun ta a kasa ta ce “Ina kwana?” “Lafiya lau, ki dafa da ni ina jiran ki falo” 2 Ya na gama magana ya fice. Bin shi ta yi da kallo cike da mamaki, yau kuma ita ce za ta dafa ma sa abinci? Yau ga saban salo barawo da sallama. STORY CONTINUES BELOW Ruwan indomie ɗin ta kara, ta dafa da shi din, tare da soya kwai. Ko da ta kai ma sa sai ya dage sai ta zauna sunci tare. Kai ta girgiza ma sa ta ce “Nawa ya na kitchen ai” “Toh dauko ki zauna ki ci anan ina kallan ki”3 Hakan kuwa aka yi, ita kan tun abin yana ba ta mamaki har ya fara ba ta tsoro. Saifullahi kuwa jikin Amatullah ya ke yiwa, babu abinda ke burge shi nan duniya kamar sura da diran Amatullah. 2 Sama sama haka ta caccaki indomie duk ta kasa nutsuwa, gashi Saifullahi bai sa ka riga ba haka ya zauna mata hankali kwance ya na yi ya na kallan ta ta wutsiyar ido. Ta shi ta yi za ta shiga kitchen, ya tsayar da ita tare da tambayar “Ina za ki? Har kin yi me?” “Na koshi ne ……” “Gudun mijin ki ke Amat?” Shiru ta masa tana jinjina maganar cikin ranta. Jin ba ta da niyar amsa masa ya kara da “Je ki aje plate din ki dawo” Da sauri ta wuce kitchen. Maimakon ta yi yanda ya ce mata sai ta bige da wanke wanke da gyaran kitchen, tun ya na sa ran komawar ta ya gaji ya bita kitchen din. Ganin ta na tana aiki na ba gyara ba dalili ya rabu da ita, ya san duk daren dadewa za ta shigo hannu, ‘duk wayon amarya sai an sha miyar ta’ 2 Da wannan tunanin ya shirya ya fice yana mai saƙe-saƙe a zuciyar sa. Kwanakin da su ka biyo baya rashin ji daga Ayush da kuma wasan ɓoyo da Amatullah ke yi ya sanya shi ɗaukan alwashin kyale ta har iya adadin zaman ta a gidanshi kafin yacillar da ita ya auro Ayush dinsa. Nan ya shiga takaicin kansa da ba kansa laifin cin amanar Ayush na kallon watan ta a matsayin abar marmari. *** Kwanci tashi asarar mai rai, auren Saifullah ya cika wata biyu ras, wanda duk an yi shine cikin hutun karshen shekara na su Amatullah. Duk zaman nan shi ma Saifullah yana gida, sau da yawa ya kan baje a falo yana kallo ne. Babu abin da ke haɗa su da ya wuce gaisuwa, ta yi girki ya ci, ya gayyato abokai su zauna su ci. Tun ranar da su ka fara zuwa Amatullah ta koma a guje ta sanya hijabi bai sake yarda ta fito ba, ya gwammace ta yi abincin ta bar shi a kitchen ya je ya ɗauko da a ce matarsa ce ta zo ga abokansa bulum bulum cikin hijabi. Yau ɗinma kamar kullum, fankasau ta yi masu da miyar hanta. Bayan dawowarta daga makaranta in da su ka fara registration ɗin sabon Zango. “Baaba kai dai ka mana zarra Billahil lazi, kai mace har mace, ga kyau ga diri ga iya girki. Wallahi ka more aure, na san a can wajen ma abin ba kanta wannan teɓa da ka fara ajiyewa” cewa Yunus abokin Saifullah na tun sakandire. “Ka san abin da ya ke ƙara birge ni, yarinyar nan ustaziyya ce, jiya na ganta a Samaru wallahi ta rufe masa kayansa amma wallahi tafiyarta ma cikin hijabi abin sha’awa ne. Saif ka gode Allah, Sadiya na nan nayi nayi ta dinga sa pashmina ma gyalen ta ƙi tana tafe ana bin ta da heys! ” Salis ya ce yana mai jan tsaki. Wani loma da su ka sake kaiwa baki ba su san sanda su ka ce ” Allah ya ma Amatullah albarka” sai da su ka faɗi sannan su ka kwashe da dariya. “Ba fa santi bane, amma girkin nan ya kai kololuwa wajen shiga kwanya” Yunus ya faɗi. Shi kuwa Saifullah wani yanayi ya shiga yan mai jin kansa na ƙara girma, murmushi yayi yana mai kallon abokansa. Duk sun san Ayush, sun san tsakanin sa da ita, amma ba su yarda da alkawarin da ya ce ya ɗauka mata ba, gani su ke yayi ne kawai don jin dadin bakinsa. STORY CONTINUES BELOW “Kun ci amanar Ayush! Duniya babu wani nawa da ta aminta da shi sama da ku biyun nan amma kuma nan ku ke koɗa wata” yace yana taɓe baki haɗe da girgiza kai. “Jamoh!!!” Salis ya kira shi da sunan da in ana zancen gaskiya yake kiransa da shi. “Ka san Allah ɗaya! Amatullah ce full option amma Ayush tsohuwa da ina mai yakinin in baku zo sa’a ba toh tabbas ta girme ka. Ita auren Jari za ka yi da ita, wannan kuma matar da za ta tarbiyyantar da yayanku. Ko ba komi ai zaka ci abinci mai gina jiki” yace yana kai lomar karshe tare da kora ruwa. 2 Nushi Saifullah ya kai masa amma ya kauce. “Ku taso mu fita in kun gama ci” Saifullah ya ce a dake. Nan su ka shiga bambamta masa Amatullah da Ayush tun zuciyar sa na ƙaryatawa har ta gaji ta yarda gaskiyar kenan. Tun bayan fitar su ta kimtsa wajen ta sanya turaren wuta tare da kunna kallo. Tashar Iqra TV ta kunna tana sauraron shirin da ake akan da’awa. A nan wajen bacci yayi awon gaba da ita. Sanye take da doguwar riga mara hannu, gaban rigar an masa kwalliya da duwatsu masu kyau. Kallar rigar na ruwan ƙasa ya kwanta sosai a jikinta, ɗame ta da rigar tayi ya bayyana halittar Allah da ke jikinta. Ya shigo daga rakiyan su Yunus inda su ka shiga Congo ya siyo fura don ya lura tana so. Bai san iya lokacin da ya ɗauka yana ƙare mata kallo ba, karshe dai tsintar kansa yayi lullube da ita. Cikin mafarki ta ji alamun mutum tattare da ita, a hankali da baƙin abubuwan da ta ke ji ya sanya ta tabbatar da gaskiya ce ba mafarki ba. Buɗe baki ta yi don yin ihu take ya liƙe mata shi da nasa. Ba ta san yanayin ba, wannan shine mafari, ba za ta iya tantance me take ciki ba ta ji gaba ɗaya an ɗaga ta. Bai ɓata lokacin kauda doguwar rigar ba balle aika mata sakwanni hakanan bai ɗauki doguwar lokaci ba ya gauraya kwayoyin halittarsu su ka tabbata ɗaya. *** Kiran Sallar magariba yayi daidai da samun natsuwarsa, kallon ta yake cikin mamaki da takaici. Tsaki ya ja kana ya tashi ya shige banɗaki in da yayi wanka ya fice masallaci. 1 Sai a lokacin Amatullah ta saki kukan da ta dinga maƙewa, kuka sosai ta ke yi duk da cikin ranta ta gode ma Allah da ya bata ikon rike mutuncin ta har sai da ta miƙa shi ga mijin aure ba mijin dandi ba. Tunawa da littafan da ta karanta tayi, ta tuna yanda miji ke surar matarsa zuwa banɗaki ya mata wanka ya bata kyaututtuka amma ita ba ta tsira da komai ba sai tsaki. ‘Ai ke ma ba ki suma ba, ance ana suma ne’ wata sashi na zuciyarta ta faɗi mata hakan.. “Toh ai bai dade ba, su an ce ana yin awanni, toh ko bai da lafiya ne” ta faɗi a sarari sai da ta fadi sanan ta ji kunyar kanta. 2 A hankali ta isa banɗaki ta yi wanka, ta lallaba ta bada farali. Nan ma godiya ta yi ga Allah da ya tsare ta sannan ta roke shi da ya ƙara kare ta daga afkawa sharrin zina. *** Kwana uku aka ɗauka duk dare sai ya zo gare ta kuma duk zuwa kyautan tsaki ya ke bin ta da shi. Washegarin na huɗu ne ya tsare ta ya ce “Wai ke ina iliminki yaje ne, ko yarinya yar shekara goma sha biyu aka aura ta san yanda za ta yi sarrafa amma ke kin wani baje kin bar mutum da aiki, mtswwwww” ya fice ya barta cikin ƙunan rai da tunani. Wannan wani irin abu ne, kullum ya je sai ya dawo amma kuma bai hana a bi ta da tsaki ba. Ta tuna littafin da ta karanta ƙarshe auren dole aka musu amma tun da ya tara da ita sau ɗaya ya bata kyaututtuka haɗe da yi mata alkawura, ba za ta manta labarin ba don ganin kamanceceniya da yake da su amma ita ga shi ta ga akasin haka. Shima ranar da takaici ya fita, haduwar da yayi da su Yunus ne ya sa ya faɗi masu damuwar shi. “Kun sa na kula yarinyar nan amma in ban da takaici ba abin da take cusa min, in kana neman bahar maliya ka sameta ka gama samun komi amma wallahi yanda kuka san sanda haka fa take min” yace cikin takaici. 2 “Hahahhhhhh wayyo Saif, kace a gajimare kake yawo, ai daga ganinta ka san can wajen natural spice gareshi” Yunus ya ce cikin shakiyanci. “Natural spice din banza, ai bai kamata ta maida min shi abu mai wahala ba” ya kara faɗi a ƙufule. “Kaga Saif, duk ba wani tashin hankali bane, Kaga am very sure ita ba kallon porn take ba, ita ba karanta explicit abubuwa take ba, ita kuma ba wai yar hannu bace wai ba za ka gode Allah ba. Ka dena haɗa aure da duniyanci Saif, koya mata ka mori ƙuruciyarta ni dai shawaran da zan baka kenan. In ba ta iya ba ai kana da Ayush, ita sai tayi maka abin da Amatullah ta kasa maka” Salis ya ce masa yana mai tabo kafadunsa. Da wannan tunanin ya dan ji salama har ya cire alwashin da ya ɗauka akan ba zai sake kallon ta ba.Kalamansa sun tsaya mata a rai, duk iya tunanin ta rasa gane mai hakan ya ke nufi, ita dai ta san ba ta ji azaban da ake lissafawa a littafan hausa ba duk da dai ba za ta ce babu zafin ba, sannan bata ga an yi tun dare har asuba ba, sannan kwatakwata mintunan da yayi bai kai wanda ta karanta ba. Ita ba ta abin daɗi a ciki ba.5 “A haka kuma wasu ke kwasan zunubi da shi” ta ce tana mai ƙarasawa da jan tsaki. Wayarta ta ɗauko tana mai tunanin ko ta kira goggonta ne, amma kunyar da ya rufe ta bayan ta tuna haka ya sanya ta yi ma kanta dariya. “Inna Hafsatu” tace a bayyane tana tunawa da kanwar goggo Mairo, wacce ita ce karamar su baki ɗaya. Sau da yawa idan inna Hafsatu na bukatar shawara, Amatullah ta ke nema su ci su suɗe tsakaninsu. Latsa lambar ta yi, bugu biyu a na uku ta ɗauka “ɗiyata amarya!” tace cikin dariya da farin ciki. Ita kanta Amatullah dariya ta yi sannan su ka gaisa, bayan nan sai ta yi shiru tana tunanin ta ina za ta fara. “Darling Daughter ko dai in zo ne” Inna hafsatu tace ganin da alamu Amatullah na da magana a bakin ta. “A’a fa, dama, Hmmmn dama shine wai ban iya komi ba” tace kamar ta sa kuka don ji tayi ta gama tona asirin ta watau dai yanzu innarta ta san me suke yi.6 ” Ai shi kuma dai, ai a hankali ne abin, ba wanda aka haifa da iyawa” tace mata, jin haka Amatullah ta samu ƙarfin cigaba da faɗin “kuma fa Shima ɗin baya kai asuba fa, kwatakwata 20min fa, sannan wani kyauta wani alkawura duk baya yi ko duk rashin iyawan ne”8 Dariya sosai inna Hafsatu tayi kana tace “A ina kika ji anayi tun dare har asuba, sannan wani kyauta kuma za a baki”3 “Kai inna ai na karanta littafan hausa da dama na ga duk haka ake yi” tace iya gaskiyanta. “Toh ke girki kala nawa kike masa kafin ya farka baccin” inna ta tambaya, shiru Amatullah tayi, don duk tunanin ta akan yin girki kala kala kafin ya farka ya kan kulle, ta kan masa farfesu dai duk rana breakfast ko dinner amma ba ma za ta iya yin girke-girke da taga ana lissafa wa ba.6 “kin yi shiru Darling” inna ta katse mata tunanin ta. ” Kinga Amatullah ki ajiye rayuwar novel ki rungumi rayuwar zahiri. Mijinki mijinki ne, in ba mai shan magani ba babu mai lafiya da zai yi awa yana abu ɗaya, sannan ai ke ba injin ba ce, zancen kyaututtuka in ya baki ci da sha, bai wulakanta ki ba, bai barki cikin tsumma ba ai gama miki duk wani soyayya. Aikin me yake yi da zai baki mota ko wani ubansu kyauta kawai don kin rike mutuncin kanki?3 Ai kyautan kenan ya ƙara daraja ki, sannan duk wulakancinsa ba zai taɓa danganta ki da matar banza ba. Zancen baki iya ba, ki duba ki ga abin da ya miki ki kwatanta hakan, kina lakantar me yafi so. Sannan kar ki manta Addu’oi. Ina Littafin Gidan Aurena, ki karanta it can serve as a guide Kuma da Addu’oi a ciki don samun kan mijinki” haka inna Hafsatu ta dinga mata nasiha da bayanai har sai da ta tabbatar da ta fahimta sannan su ka yi sallama.4 Da karfinta ta tashi ta shiga kitchen nan ɗin ma abincin da ta san yana so ta shiga haɗa masa, farar shinkafa da miyar ganye amma maimakon taushe sauce take masa ya ji nama da hanta. Duba fridge ta yi ta ga suna da sauran kankana ta yi haramar yi masa lemun kankana da madara. *** Cikin ikon Allah sai da ta kammala komi har ta yi wanka kafin ya shigo bayan la’asar, sanye ta ke da doguwar riga ta atamfa amma gaba ɗaya bai wuce guiwanta ba. Dinkin ya kamata daga sama sai ƙasan aka yi mata kamar lema hakan yayi daidai da zamansa a kan mazaunanta ya fito da kyawu ta. STORY CONTINUES BELOW Hoda kawai ta sa a fuskar ta, kanta kuma da ya ji kitso ta barshi a buɗe. Babu abin da ke fita daga jikinta sai ƙamshi. Tun da tace masa sannu da zuwa uffan bata sake haɗa su ba, amma tana zaune a kujera ya natsu yana cin abinci haɗe da kora lemun. “akwai saura da yawa” yace bayan ya idar da na gabansa, shiru tayi kamar hankalinta na ga talabijin sai da ya sake maimaita mata sannan ta yi firgigit ta amsa da akwai. “Zuba ma Baban Sasa ki zo mu je mu kai masa” yace yana mikewa. Wani murna ta ji bata san lokacin da ta rungume shi ta baya ba, shi kuma a hankali ya juyo da ita, kallon da yake mata duk ya tafi da imaninta. “Kin san ban masa godiya daga ƙasan zuciya ta ba, yau zan masa, don ba ƙaramin gata ya min ba, Ubangiji Allah ya miki Albarka Amatullah”13 ya faɗi yana mai haɗa laɓɓansu. Yanda ta saki jiki ya bashi mamaki, ita kanta sai a lokacin ta san garɗin abin. Bayan yan mintuna su ka je don su shirya zuwa ga Baban Sasa. *** “Yaya Amatullah oyoyo!” da yaran gidan ke faɗi ya isa ga kunnuwan matan gidan, sosai mahaifiyarta ta shiga farin ciki haka baba Anas da ke zaune yana sauraron radiyo France shirin almuru. Tare su ka shigo tamkar wasu taurari, sanye yake da shadda wanda ya ji aikin hannu ruwan samaniya, hulansa yayi daidai da kalar aikin jikin shaddan. Ita kuma Amatullah sanye take da material fari mai adon fulawa na kaloli, ta ɗaura hijabi ja wanda ya shiga da jan da ke cikin fulawar, kafunta sanye da takalmi ja mai tsini. Babu wani ado a fuskarta face hodar da ta sanya don rage maiƙon fuska. Fuskar nan tata cike da annuri, ji take kamar ta sheƙa a guje ta ga goggo maironta. Sanin da ta masa na son aji ya sa ta danne murnarta har su ka isa ɗakin Baban Sasa a tare. Shima zaune ya ke yana kallon Aljazeera su ka yi sallama su ka shiga. Wangale bakin da ya yi kaɗai ya isa ya bayyana farin cikin da ya ke ciki. Nan su ka zube su ka gaishe shi, ya amsa yana mai shi masu albarka. Kwandon abinci da Saifullah ya riko ya ajiye gabansa yana mai cewa “Kaci ka ji irin daɗin da ake ciyar da ni, kai Tsohon nan ka fi kowa iya match making” ya ƙarasa cikin tsokana.4 Zama su ka gyara da su ka ga da gaske baban Sasa santi yake bayan Saifullah ya zuba masa abincin. Suna cikin masa shaƙiyanci su Baba Anas su ka shigo, nan Amatullah ta ji duk wani kunyar duniya ya rufe ta. Gaishe su tayi ta tashi sum za ta fice, take Saifullahi ya tashi ya bi bayanta, ya bar iyayensu da mamaki. “Allah ya saka da Aljanna Babanmu, ka gansu ko” Baba Anas yace cikin murna, nan saura su ka shiga farin ciki suna fadin yanda Saifullah ya yi ƙiba. “Ai tsatson Mairo gwanaye ne a mallaka, ku duba ku ga, yaron nan ba so yake ba amma yanzu ya zama bindi. Kaico!” Baba mahmuda ya faɗi wanda hakan ya ɗanyi tasiri a zukatan wasu daga cikinsu.2 “Ko me zata yi ta daɗe bata yi ba, balle wannan girki haka, kai ko zaku ɗanɗana ne” Baban Sasa yace yana tura musu raguwar abincin nan sai su ka yi shiru. *** A cikin gida ɗakin Hajiya ya ja ta, bayan sun gaida matan da ke wajen gida, ji tayi kamar ta rusa kuka ganin yanda ya hakince a kujera. Hajiya ma da ke zaune in ban da tururi babu abin da zuciyarta ke mata ganin fara’ar da Saifullah ke ma Amatullah da yanda ya ke sako ta a cikin hirar su. Rasa yanda za ta yi ta cusa ma Amatullah haushi bayan ta fito da turarruka biyu ta ba hajiya a sunan nata da na Baba Anas, Saifullah da bai san da turare ba ya dinga shi mata albarka ba tare da ya ba hajiya damar cewa uffan ba.2 STORY CONTINUES BELOW “Hajiya wallahi turarruka ne masu shegen tsada kin gansu, ni ban ma san ta riko muku ba, ke abin da kike da pocket money dinki Kenan” ita dai Amatullah murmushi kawai ta ke yi, duk da bata san darajan turaren ba, zuwan da mahaifin ta yayi ne ya bata da umurnin duk ranar da ta je gida ta kai a hajiya da baba Anas. “Toh ni in ba don ka faɗi ba ai sai in ce yan uku da hamsin ne” tace tana yatsina. Dariya Saifullah yayi ba tare da ya auno komi ba. Su ka cigaba da hira, anan ne Hajiya ta ce. “Ni kuwa ina Ayush ne? Yaushe za aje gaisuwa ne?” tace tana tsare shi da ido, kallon Amatullah yayi cikin sauri ya ga babu wani sauyi a fuskar ta, haka kawai ya tsinci kanshi da jin haushin hajiya, bai ce da ita kanzil ba, sai da ta sake maimaitawa.1 “Hajiya da kin manta da Ayush da duk yafi, ba ta ban damar yi mata bayani ba, ta daina ɗaukan wayata, ni bata sake nema na ba sai ɗazu, na ga kiranta sau uku duk ba wanda na ɗauka” yace kai tsaye. Duk da Amatullah ta ji ɗacin zancen sa ta ɗaure ba tare da ta nuna masu ba, tashi yayi yana riko ta kamar mai koyon tsayawa tare da faɗin “Muje wajen goggona sharp sharp mu wuce” Kamar jela haka ta bi shi tana mai ma hajiya sallama. Takaici bai rufe ta ba sai duk yanda ta so su keɓe da mahaifiyarta bai bari ba, zama yayi ya dinga janta da hira kamar Saifullah kafin dawowarshi daga Rasha. Nan su ka ci abincin dare ba su suka bar gidan ba sai bayan sallan magariba. Tun da su ka dauki hanya maganar Hajiya ce ke damun zuciyar ta, dan haka ta yanke hukuncin tarar aradu da ka, ta mai nisawa ta furta “Yaya Saifullahi wacece Ayush?” Kallon ta yayi na wani ɗan lokaci, har ta fitar da ran jin amsa daga gare shi ta ji ya ce “Budurwa ta ce………” Gaban Amatullah ya faɗi, shi kuwa gogan na ta ko a jikin sa bai gushe ba ya cigaba da faɗin ” ita na so aura kafin Baban Sasa ya aura min ke, kuma har yanzu ban fitar da ran za ta zama mata a gare ni ba”2 Ya karasa maganar ya na duban ta da wutsiyar idanu. Daurewa ta yi duk da bakin kishin da ya tukare ta a kirji, ta na mai murmushin ya ke ta furta “Ai namiji mijin mace huɗu ne, Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa”2 Shi ma din murmushin ya sakar mata yayinda da ya saki numfashi da shi kan sa bai san ya rike, kana ya ce “Dadi na da ke hankali Amatullah, Aameen dan rasulillahi” Haka su ka cigaba da tafiya, ya na ɗan jan ta da hira amma ita Allah Allah ya ke su isa gida ko ta samu ta shiga dakin ta yi kuka ko ta ji sauki a ran ta. Ko da su ka isa dakin ta ta shige, cikin bandaki ta sha kukan ta, sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi wanka da alwala. Da wuri ta kwanta dan kada ma Saifullahi ya rabe, shi ma Saifullahi da tun a mota ya gano halin da ta ke ciki, daren ranar sarara mata yayi, ya na mai fatan daga ranar dai ba za ta dauki sarar hana shi hakkin sa ba, dan kuwa in dai wannan ko gaban Baban Sasa sa je.4 *** Rayuwar su suke gwanin ban sha’awa, in da ta yi watsi da maganar Ayush ta mayar da hankalin ta wajan kula da mijin ta. Ba ta wasa da cikin sa, tana masa biyayya sosai sannan ta fannin ƙishinsa kullum cikin koyon salon da za ta kashe masa ƙishinsa ta ke, shi ma baya gajiya da koyar da ita. Ranakun karatun ta shi ke kaita ya ɗauko ta, sannan duk wani abin da ba ta fahimta ba duk da aji biyu karatun fannin kwas dinsu ne mafi akasari yana kokarin nuna mata. Lokaci ya ware mata wajen karatu, ya kan fita ya bar mata gidan tayi karatun ta, lectures ko ƙarfe bakwai aka sanya sai ya tabbatar da ba ta makara ba. Uwa uba baya gajiya da gayyatarta makwanci, ba ta san lokacin da ta zama majuniniya a soyayyarsu ba. Duk kulawar da ya ke nuna mata bai hana masa yin waya da Ayush ba, wacce daga baya da kan ta ta kira Saifullahi ta ba shi hakuri, ta kuma amince da auren ta da zai yi a matsayin mata ta biyu, Amma fa da sharaɗin tun da auren dole ya ce aka ma sa, kada ya kuskura ta ji sun hada shimfiɗa da matar shi bare ta ji tana da juna biyu.4 Jin ta kawai Saifullahi yayi dan kuwa aikin gama ya gama, bare kuma babu yanda za a yi yana ganin mace kamar Amatullah ya zuba mata idanu, shi ma ya san da Ayush ta san wacece matar da aka aura masa da ba ta yi wannan yasshesshen zancen ba. Ya kan kai mata ziyara lokaci zuwa lokaci kuma ya mata alkawarin zai aure ta matsayin matarsa ta biyu kuma ta ƙarshe nan da shekara daya da rabi, yanda Babab Sasa ba zai hana shi kara aure ba. Bai ɓoye ma Amatullah ba don a cewarsa kar ta yaudari kanta. Sannu a hankali su ka cika shekara da aure, a ranar ya mata kyautan zinari na naira dubu dari biyu da hamsin. “Kinga kin zama min haske tun cikin 2009 har 2010, ina fatan ki zama tauraruwa, wata kuma ranar da zata dinga haska rayuwata har ƙarshen ta. Amatullah ke ɗin Alkhairi ce, na gode” yace yayin da yake miƙa mata. Ji tayi gaba ɗaya ba ta da wani damuwa, nan ta ƙara son mijinta, ta kuma so Baban Sasa don shi ya zama silar samun gatanta. “Na Gode Saahib, Ubangiji Allah ya bar mu tare har a Aljanna” tace tana mai rungume shi.3 Sati uku bayan cikar su shekara ɗaya yayi daidai da lokacin ganin baƙon watanta, amma shiru ake ji, ga duk wani alamu na zuwansa ta gani amma shiru babu shi babu alamunsa. Inna Hafsatu ta kira ta faɗa mata, nan ta mata alkawarin biyowa in ta taso daga aiki. “Alhamdulillah!!! Amatullah addu’ar mu ta amsu, bayan shekara ɗaya fa, Alhamdulillah!!” tace bayan ta ɗaga tsinken gwajin cikin da ya nuna Amatullah na ɗauke da shi, rufe fuska Amatullah tayi cike da jin kunyar innarta. ” Daina kunya, ciki da ubansa, kar na zama babbar kwabo da na yi ma Saifullah albishir” tace cikin dariya. Nan ta bata shawarwari tare da mata addu’ar samun sauki wajen rainon ciki da haihuwa sannan ta tafi. *** Faɗin irin ƙosawar da Amatullah ta shiga akan dawowar Saifullah wanda ya je Kano wajen Ayush. Ji tayi kamar ta masa waya don ta hango farin cikin da zai yi in ta faɗa masa. Tashi tayi ta kimtsa tare da shirya masa abinci, sannan ta samu waje ta zauna tana duban agogo. Biyar da minti shida ya shigo, nan ta rungume shi cikin tsantsan farin ciki. Kallon ta yayi cikin murmushi yace “Hala mafarki kika yi bazan dawo ba” “Haba Saahib, kawai dai farin cikin samun ka a matsayin miji nake kullu yaumin” tace tana kanne masa idanu. Sai bayan ya gama cin abinci ya miƙe ƙafa yana bata labari ne ta ɗauko masa tsinken da ba ta yar ba. Kallon ta yake a sheƙe, cike da tuhuma da son musanta zargin sa, ganin yayi shiru ya sa tace “Saahib duba fa, kyautar Allah bayan shekara ɗaya” tace tana mai tsananin farin ciki. “Ni wallahi ban taɓa ganin Jarababba irin ki ba, har yaushe aka yi auren da za ki ƙunso ciki” yace a hasale wanda hakan ya sa ta yin mutuwar zaune. “Saahib shekara ɗaya fa, ba wayonmu ko dabara fa” tace a marairaice. “will you shut up!” yace cikin tsawa. Hango ta haihu yake yi shike nan yan biyunsa zubewa za su yi, ita kanta buɗewa za ta yi, ba zai sake jin daɗin da yake ji ba, ga Alkawarin da ya tabbatar ma Ayush ita za ta fara haihuwa a gidansa.2 “Allah ya isa! Allah ya isa Amatullah!! Me ya sa kika bari ciki ya shiga, muna zaman lafiya abun mu why? Why Amatullah” ya ce a rikice yana mai jifa da kofin tangaran din da ke kusa da shi.13 Take ya tarwatse gaba ɗaya. Riko ta yayi idanunsa cikin nata ya ce “kina so na?” bata iya amsawa ba sai gyaɗa kai da ta yi. “Muje a cire abin nan, mu cigaba da rayuwar mu hankali kwance kinji” ji tayi gaba ɗaya ba za ta iya masa musu ba. Ta gwammace ta zubar da cikin, ta gwammace ta jira har zuwa lokacin da zai shirya haihuwa su haihu.4 Ba musu ta tashi ta shiga daki ta ciro hijabinta.