TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 8

TAZARAR DAJE TSAKANINMU CHAPTER 8

Ko da ta fito tashi yayi tsaye su ka fice, a mota ya kira Salis ko yana asibitinsa kasancewarsa likita ma’aikaci a asibitin gwamnati na Gambo sawaba, mahaifin sa kuma ya buɗe masa nashi a cikin GRA, mutane na son asibitin saboda kwarewarsu da kula da marasa lafiya.+ Minti Ashirin ya ɗauke su kafin su ka isa Umjad clinic and maternity. A dirare Amatullah ta gaida Salis don cike take da waswasi duk da cewa a shirye take da ta yi komi don farin cikin mijinta. Ai ko ba komi Aljannarta na ƙarkashin ƙafafunsa ne, da wannan take ba kanta haƙuri da ƙwarin gwuiwa.5 “Bari mu yi scan mu ga girman cikin don kamar ya fi wata ɗaya fa” Salis ya ce bayan ya ɗan dudduba ta. “Kai likita ban son shegantaka, watan nan ne kawai ta yi ɓatan sa amma duk saura suna zuwa” Saifullah ya ce a ƙufule, shi kawai so yayi a mata allura ko ya bata kwaya ta haɗiya cikin ya zube.3 “Engr. Ai wasu ma har su haihu su na yi, wasu in sun kammala wata ukun farko, wasu sai ya kai shida, amma mafi akasari daga ciki ya shiga wata ɗaya ko sati biyu yake ɗaukewa” Da haka ya tura ta scanning wannan ake yi a wani sashi na asibitin. Saifullah bai yarda ta tafi ita ɗaya ba, tare su ka je bayan an tabbatar da a matse take aka sa ta hawa gadon gwaji.2 “yaushe kika ce kin ga hailan ki ƙarshe, first date of your last period” ya ƙarasa cikin turanci ganin bata fahimci hausar ba, bai san cewa tsananin tsurewa ne da tunane tunane ya cika mata ciki. ” 5th August” tace kai tsaye “Wow, Kuna cikin ƴan baiwa” ya ce yana kallon allon kwamfutarsa yana cigaba da dudduba ta, bayan ya gama ya fitar da sakamako ya basu don maida ma Salis. “Ai na faɗi maka, kallo ɗaya na mata na san ya wuce haka, cikin ta satinsa goma sha biyar da kwana uku ko ba kwana uku (15weeks +/- 3days)” Salis ya faɗi yana mai addu’a a ranshi ko Saifullah zai canza shawara.2 “Sai a burge shi kawai Salis, ni dai ya fita, ban shirya zama uba ba, beside kwatakwata yaushe aka yi auren, ace mace daga an kalle ta se ciki” ya ce cikin fushi yana mai bankawa Amatullah harara. Ganin haka Salis ya bashi takarda ya sa hannu, itama ta sa hannu akan da amincewarta za ayi. “Za ka iya zama da ita sanda za a cire…..” “Ina ba zan iya ba, just let me know idan ka gama” Yana gama fadin haka ko kallan Amatullah wanda idanun ta su ka ciko da hawaye bai yi ba, ya sa ƙafa ya fice. Dakin da aka tanada na musammam Wanda ake kira da Gynae Emergency Room Dr Salis ya shigar da ita, hankalin Amatullah bai tashi ba sai da ta ga wani gado dan siriri, gefe da gefen sa wasu karafuna ne. Dr Salis na mai duban Amatullah ya ce “Madam zan ba ki dama ki shirya kafin nan an gama sterilizing kayan aikin, wannan gadon za ki hau, and remove your pant please” Ya na gama maganar ya juya ya fice.1 ‘and remove your pant please’ Maganar da ya tsaya mata a rai kenan, kallan gadon ta ke cikin tashin hankali, komai na dakin ma abin tsoro ne. A sanyaye ta zame pant din ta, ta ninke ta sa a jaka. Amma sai ta kasa hawa kan gadon, hawayen da take ta kokarin rikewa tuni suka fara gangarowa bisa kuncin ta, yayin da ta ke gogewa da bayan hannun ta. Bayan minti goma Dr Salis ya shigo dauke wani ɗan tire. Amatullah ta bi tiren da idanu in da idanun ta su ka yi kacibus da kananan karafuna, wasu kamar aska, sai mai ɗan lankwasa kamar kugiya, sai wasu kamar kananan wuka, da wasu ma su zubin almakashi.2 “Madam da fatan kin shirya, before then zan mi ki allura, ta Pentazocine domin kashe zafin wajan ko?” Cewar Dr Salis ya na mai sanya safa a hannun shi. Sai da ya mata allurar kafin ya sake cire safar hannun ya fita. Kusan minti biyar ya sake ɗauka kafin ya dawo, ganin har lokacin Amatullah ba ta hau gadon ba ya ce da ita STORY CONTINUES BELOW “bisimillah madam, ki cire zanin ki ki hau gadon” “Shin ba ku da Doctor mace ne?” Cewar Amatullah cikin tashin hankali. Murmushi Dr Salis yayi, kana ya ce “Unfortunately babu, Amma kar ki damu ai duk cikin neman lafiya ne, ni ma ina da iyali kamar ke a gida” “Za ka bari a yiwa iyalin ka abin da za ka min yanzu? Za ka bari a zubar mata da ciki? “4 Ta sake tambayar sa. Ya na mai yamutsa fuska ya ce “Idan iyalina ba ta da lafiya kuma babu Doctor mace sai namiji why not? But batun bari a zubar da cikin wannan ra’ayin ki ne ke da mijin ki ai” Shiru ta yi tana mai duban gadon, hannun ta bisa cikin ta. “Idan kin shirya please” Dr Salis ya sake maimaitawa a karo na biyu. Jiki sanyaye Amatullah ta cire zanin jikin ta ya rage sai under siket, yayinda da ta tattare hijabin ta zuwa wuya. A hankali ta haye bisa gadon. Ganin Dr Salis ya gyara karafunan da ke gefe da gefen gadon yayinda da ya umarce ta da ta sanya kowacce kafa bisa karafunan yanda kafafun ta za su bude sosai ya sanya Amatullah girgiza kai. Cikin kokarin ganar da Amatullah ya ce “Madam in ba ki saka kafafunki na ɗaure su jikin karfen nan ba, za ki iya zube kafafun ina cikin aiki kuma hakan zai iya jawo matsala……” Ga mamakin shi sai ganin Amatullah yayi ta diro daga gadon ta na mai sakin hijabin ta, ta ja zanin ta daura. Hannun ta rike da jakar ta ta dubi Dr Salis ta ce “Ka kira shi ka sheda ma sa na ki baka haɗin kai, dan kuwa wallahi babu wanda ya isa ya min abin da ka ke shirin yi min!!!!”2 Ta na gama fadin haka ta fice, shi kuwa Dr Salis har cikin ran sa ya ji dadin maganar Amatullah. ‘ashe dai da sauran wayon ta’ cewar Dr Salis cikin ransa. Hankali kwance ya kira Saifullahi ya shaida masa halin da ake ciki. Kamar zai yi hauka dan bacin rai inda ya zo ya tadda Amatullah tsaye bakin kofar Dr Salis. “Malama me ki ke yi anan? Me ya sa ba ki tsaya an cire mi ki wannan abin ba?” Kallan sa ta ke cikin Ido, duk wani shakka na shi da ta ke ji ya gushi, cikin dakewa ta ce “Kai na ke jira ka kai ni gida, wannan abin da ka ke so a cire ba zai yiyu ba, ina san abu na idan kai ba ka so…….”2 Takaici ya sa ya kasa ba ta amsa, cikin bacin rai ya shiga zirga zirga, ya kai ya kawo. Ita dai Amatullah ta zubawa sarautar Allah ido. Cikin wannan hali Dr Salis ya fito ya same su “Ya za ka min haka Dr Salis bayan na saka hannu a cire mata wannan jarabar?”2 “Ya ka ke so na yi bayan Madam ta ce ba ta so? I can’t force her you know, Zai dai fi kyau ku kara shawara……” “Malama wuce mu tafi!” Ya katse Dr Salis, ya wuce fuuu, in da Amatulah ta bi bayan shi. Yanda ya ke tuka motar kamar zai tashi sama, ita dai adduar ta su isa lafiya. Gashi allurar da aka mata ya dan fara saka ta jiri, haka kuma duka jikin ta ya mutu. Suna isa tun kafin ta fito daga mota ya riga ta fita, a falo ta taddashi ya na ta kai kawo kamar wanda ya hadiyi gatari. Sim sim ta shige shi za ta wuce dakin ta ya daga ya tsayar da ita ta hanyar daka mata matsawa “Malama ji mana!!!!!” Amatullah ta tsaya, gaban ta ya sha ya na mai nuna ta da dan yatsa ya ce “Wato komai aka haɗa da jaki sai ya ci kara, so ina so ki zaɓa ko ni ko cikin da ke jikin ki!!!!”2 Kasa magana ta yi, kai kawai ta ke girgiza masa yayinda hawaye ke gudana daga idanun ta. “Malama dallah ki amsa min!!!!” STORY CONTINUES BELOW “Ya Saifullahi dan Allah ka yi hakuri…..” “Ni ko wannan abin da ke cikin ki?” Hannu ta kai ga cikin ta, ta dago idanun ta ta sanya cikin na shi, murya a sanyaye ta ce “Ciki na, na zaɓi ɗan da ya ke ciki na….”6 Kallan ta ya ke tsana karara cikin idanun sa “Amatullah yau kin tabbatar mi ni ke butulu ce! Kin zaɓi cikin ki? Fine! Very fine ki je ki auri cikin na ki!! Shashasha bagidajiya!!!!”3 Ya juya ya fita a fusace. Baki buɗe ta bi bayan shi da kallo, a karo na farko ta nemi kuka ta rasa, fadi ta ke “Inna lillahi wa inna ilaihi ilaihi rajiun” Ta fada ta kara maimaitawa. Jikin ta babu nauyi saboda allurar da aka mata, haka ta lallaba ta shiga daki, ba ta san sanda bacci ya sace ta ba.2 *** Washagari kamar yanda ta saba ta haɗa masa karin kumallo, amma shiru ya ki fitowa daga dakin sa. Gashi lecture din sassafe gare ta, na 8:30, kuma test za a mu su. Saifullahi da idan ta na da lecture din safiya karfe bakwai shirya tsaf sun ɗauki hanya. Ganin shirun yayi yawa ta je ta buga masa kofa, har ta fitar da rai za a bude kofar, sai gashi ya bude, sanye cikin singileti da gajeran wando. Kallan banza ya bi ta da shi, ya na mika ya furta “Malama lafiya?” Tana inina dan shakkar amsar da zai ba ta, ta ce “Dama school…ka manta ..dama ina da lecture din safe” “Oh toh shi cikin na ki ba zai kai ki makaranta ba?” “Ya Saifullahi………” Hannu ya daga mata tare da faɗin “Shut up!!! Duk sanda ki ka shirya zubar da wannan abin da ki ke dauke da shi toh sai ki tafi makarantar, but for now ki saka a ranki cikin ki ki ke aure, kuma wallahi ki ka saka kafa ki bar gidan nan wallahi sai na lahira ya fi ki kin daɗi! Bagidajiya kawai!”7 Ya na gama magana ya ja kofa ya mayar ya rufe. Kuka Amatullah ta saki mai karfi har da shashsheka, da sauri ta koma ɗakin ta, in da ta ɗauki wayar ta, numbar Baban Sasa ta shiga kira, bugu na uku Baban Sasa ya dauka ya na mai faɗin “Amaryar yau kewata ake da sassafe?” Maimakon ya yaji muryar Amatullah cikin walwala kamar yanda ya saba ji, sai ji ta yi tana kuka har da shashsheka, ta ma kasa magana. “Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!!! Lafiya Amatullah? Ina Saifullahi? Me ya same shi? Wani abu ne ya same shi” “Dama shi ne ya ce ba zan je makaranta ba ….” “Akan wani dalilin kuma????” Baban Sasa ya tambaya cikin nuna bacin rai “Wai dan na ce…..Wai dan ina dauke. . wai dan….” Amatullah ta tsinci kan ta tana mai kame kame, jin haka Baban Sasa ya ce “Wai dan me Amatullah?” Wuf Saifullahi ya fuzge wayar, dama tun da ya juyo kukan Amatullah ya san za a rina, hankalin sa ya kasa kwanciya ya biyo bayan ta, ya kuwa tadda ta tana shirin shaidawa Baban Sasa halin da su ke ciki. “Baban Sasa, shagwaba ce irin na Amatullah” “Shagwaba irin na Amatullah? Me ya sa ka hana ta zuwa makaranta?” “Ba hana ta zuwa makaranta na yi ba, yanzun haka ma shirin kai ta makarantar, ka san halin matar ta ka ne sai a sannu” Shiru Baban Sasa yayi kafin daga bisani ya ce ya bawa Amatullah wayar. Maimakon ya bata wayar, sai ya saka ta handsfree, ya na mai yi mata gargadi ta san amsar da za ta bawa Baban Sasa. “Amatullah shin akwai wani damuwa na bayan zuwa makarantar?” Idanun ta kan Saifullahi ta ke girgiza mata kai, Amatullah ta ce “Ah ah Baban Sasa, dama shi ne kawai” “Kin tabbatar? Kar ki boye min komai” “Babu komai Baban Sasa” “Maza ki shirya yanzu zai kai ki, Allah ya mu ku albarka” Ta amsa masa da amen. Saifullahi na kashe wayar maimakon ya bata, sai ya tusa shi aljihun sa, baki bude Amatullah ke duban shi. Ganin ya juya ya fice daga ɗakin ta biyo shi da sauri zuwa falo, ko a jikin sa ya wuce zai shige dakin sa ta yi saurin tsayar da shi “Wallahi Yaya Saifullahi test gare ni, idan na yi missing carry over ce……” Ya na murmushin mugunta ya ke kallan ta “Toh ke a na ki wautan makarantar zan kai ki? Saurare ni da kyau, Wallahi! Wallahi! Wallahi! Babu ke babu makaranta matukar ba ki yarda an zubar da wannan abin da ke cikin ki ba!!!!”5 Yayi maganar ne ya na mai nuni ga cikin ta, bai gushe ba ya kara da “Ba ke mai Baban Sasa ba? Sai ki je gida ki fada ma sa ai, shashasha, ba carry over ba, Allah ya sa spill over ne!!! What a local human being!!!!!”2 Fuuu ya wuce dakin sa, in da Amatulah ta bishi da kallo, hannun ta bisa kirjin ta tsabagen zafi da zuciyar ta ke mata. Ɗakinta ta koma, ta ɗauko jakar ta da take ɗan ajiyar ta, ko da ta ƙirga chanjin da ke ciki ko makaranta ba zai kai ta ba, balle ayi maganar dawo da ita gida. Bakin gado ta zauna tana zancen zuci. Ta san duk abin nan da Saifullahi ke mata dan cikin da take ɗauke da shi ne, cikin da ba ita ta sakawa kan ta, tsabagen rashin adalci irin na mijin ta. Nan ta sha alwashin hafe cikin ko da kuwa hakan na nufin karshen zaman ta da Saifullah ne.2 Wasa wasa Amatullah na ji ta na gani ya hana ta zuwa makaranta, wayar ta kuma ya kashe, Su Gwoggo kuma ya tsara mu su karyar wayar Amatullah ta sami matsala, idan kuma suka kira daga ya ce ta na makaranta nan za ta wuni, sai ya ce ta na bayi. Tun abin ba ya damun Gwaggo har ta fara tunanin ko lafiya. Gashi ko abinci idan ta girka ba ya ci balle a kai ga magana mai daɗi ta shiga tsakanin su. Duniya ta yiwa Amatullah zafi, ji ta ke kamar ta na gidan kurkuku har tsawan kwana uku. A na hudun ne da safe Saifullahi na fita, itama ta sanya hijabin ta. Dan kudin da ke hannun ta ta biya kudin mota ba ta zame ko ina ba sai gida. A zaure ta tadda Baban Sasa zaune bisa tabarma tare da Baba Anas. Yanda ta shigo mu su afujajan kamar an koro ta ne ya sa suka tsora, in da a tare su ke tambayar lafiya? Gaban Baban Sasa ta zauna ta na kuka hawaye ɗaya na bin ɗaya, ta ce “Baban Sasa ya hana ni zuwa makaranta, kwana uku kenan ya hana ni, ya ki kai ni ya kuma ki ba ni kudin mota da na tafi…..” “Innalillahi wainnailaihi rajiun, wai shi Saifullahi ya hana ki zuwa makaranta? Bayan nan ya zo ya gaishe mu kafin ya shige cikin gida ya ce da mu ya dawo daga kai ki makaranta ne? Shin dama ba lafiya lau ku ke zaune ba Amatullah? Me ya sa ba ki kira kin sheda mana a waya ba?” Tambayoyin da Baba Sasa ya jero mata kenan. Shi kuwa Baba Anas gyada kai kawai ya ke. “Wallahi Baban Sasa karya ya ke, ya hana ni zuwa makarantar, hatta wayar ma shi ya kwace tun ranar da na kira… ..” “Daina rantsuwa Amatullah, wallahi idan dai Saifullahi ne zai aika, jairi ka na ganin shi sim sim yaran nan bai da girma sai na jikin sa!” Baba Anas ne ya katse ta. Cike da bacin rai ya tashi ya shiga ciki a fusace kafar shi ko takalmi Babu. Baban Sasa kuwa shi har a lokacin bai yarda Saifullahi zai iya aikata hakan ba, duk da kuwa Amatullah ba ta taba masa karya ba. A dakin Hajiya ya tadda shi, yayi rashe rashe ya na cin wainar gero da kunu. Kallo ɗaya ya yiwa mahaifin na sa ya tabbatar da bacin ran da ke tattare da shi “Babu shakka, dole ka rashe a nan kana cin kumallo hankali kwance tun da ka hana ‘yar mutane zuwa makaranta” Cewar Baba Anas ya na kallan sa cike da takaici, in da Saifullahi ya kware ya na mai fuzar da wainar da ya kai bakin sa jin maganar da mahaifin na shi yayi, har ya na kwarewa. Baba Anas bai kula da kwarewar da Saifullahi yayi ba, ya kara da “Matar ka tana zaure, ka taho maza ka yiwa Baban Sasa dalilin hana ta zuwa makarantar da ka yi har tsahon kwana uku, da kuma dalilin kwace wayar ta da ka yi, mugu azzalumi! “3 Har ya juya zai tafi ya dawo, ya na mai nuna sa da dan yatsa ya ce “Ka tabbatar ka na da kwakkwarar hujja na aikata wannan zalincin, ka da ka manta na ɗau alkawarin yanda ka yiwa Amatullah kwatankwacin yanda zan yiwa uwar ka….”2 Furucin yayi daidai da fitowar Hajiya daga uwar daka, ta na mai sallallami ta ta ke tambayar Baba Anas ko lafiya. Saifullahi ya nuna da danyatsa ya ce “Ga ki ga shi ai! Ka da ka sake ka kara minti biyar cikin gidan nan! Ka fito maza ka same mu!” Ya juya ya fita a fusace. Saifullahi ma aje abinci yayi ya biyo bayan sa, Hajiya na tambayar ba’asi ya ce da ita ta jira zai mata bayani. Shigar sa zauren ya tadda Amatullah zaune kusa da Baban Sasa har lokacin ba ta dena kuka ba. Bakin ciki da takaicin ganin ta ne ya tokare ma sa ƙirji, Baba Sasa kuwa bin shi yayi da kallo mai wuyar fassara. In da Baba Anas ke bin shi da harara. Kusa da Amatulah ya tsungunna, cikin nuna kulawa ya ce STORY CONTINUES BELOW “Amatullah me ya faru? Me ya sa ki ka zo gida ki dagawa Baban Sasa hankali? Ba kya la’akari da rashin lafiyar shi ……” “Ungo nan!” Baban Sasa ne ya masa dakuwa, kana ya kara da “Kai din ka yi la’akari da rashin lafiyar ta wa ne da za ka hana diyar mutane zuwa makaranta? Akan wani dalilin ma?” “Ban fa hana ta zuwa makaranta ba Baban Sasa…..”3 “Wallahi ya hana ni, rabona da makaranta kwana uku kenan!” Kallan sa su ke in da yayi kasa da na sa kan. “Yau da na tambaye ka na ina yarinyar nan ta ke ina ka ce ka baro ta?” Baban Sasa ya sake tambayar shi, shiru ka ke ji Saifullahi ya kasa amsa masa. “Shirun da ka yi ta tabbatar mana da gaskiyar Amatullah, menene hujjar ka?” Shiru ka ke ji, duk bakin Saifullahi yau Amatullah ta daure shi da jijiyoyin sa, bai taɓa tsammanin za ta masa haka ba. “Tun da shi ya ka sa amsa mana, ke Amatullah sai ki fada mana, a wani dalili ya hana ki zuwa makaranta?” Cikin faduwar gaba Saifullahi ya daga kai, ya kai kallan sa ga Amatullah, ita ma din kallan sa ta ke. Idanun sa cike da magiya ya ke duban ta, cikin dabara ya dan girgiza mata kai alamar ta rufa masa asiri. Amatullah ta kawar da kan ta da sauri. “Ke mu ke sauraro Amatullah, kada ki ji komai ki faɗa mana gaskiya, idan ba ki faɗa mana damuwar ki ba wa za ki faɗa mana” Cewar Baba Anas wanda ya lura da irin kallan da Saifullahi ya ke mata. Murya sanyaye ba tare da ta sake yarda sun hada idanu da Saifullahi ba ta ce “Wai cewa yayi….dama cewa yayi sai an zubar…..” Nauyi ya sa ta kakare ta kasa karasa maganar, Saifullahi kuwa kallan ta ya ke cikin fargaba, cikin ran sa ya ke ‘ashe yarinyar nan ba matar rufin asiri ba ce!!’6 “Sai an zubar da me? Baba Anas da ya fara dago jirgen ne ya tambaye ta, cikin adduar Allah ya sa zatan shi ba daidai ba ne “Juna biyun da na ke dauke da shi……”3 “Laa ilaha illa Allahu Muhammadu rasulillahi sallallahu alaihi wasallam!!!” Baba Anas ne ya doka Salati, in da shi kuwa Baba Sasa hannun ya sa bisa kirjin sa tsabagen yanda maganar ta dake shi. “Kai Saifullahi ba ka da daraja! Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun” Faɗin Baban Anas cikin jimami, shi kuwa Saifullahi ji yayi kamar ya rufe Amatullah da duka tsabagen sabon tsanar ta da ya ji ya mamaye zuciyar shi. Kai a sunkuye ya furta “Ba wai na ce a zubar da cikin ba ne dan wani mummunar manufa, gani na yi fama ta ke da makaranta yanzu aka ce ta yi nauyi ko ta haihu wahala za ta sha, ita a wahale abin da ta haifa a wahale karshen ta ma karatun na ta ya lalace……..”3 “Ungu nan!” Baban Sasa da har yanzu hannun sa ke bisa kirjin sa ne ya katse shi ta hanyar masa dakuwa. “Dan tselan uwa kai!!! Ka damu da makarantar ta shi ne ka hana ta zuwa makaranta har tsahon kwana uku? Yau na yi danasanin aura maka yarinya mai daraja irin Amatullah, da gaskiyar ka Anas wannan yaro be da daraja! Ashe dan aure zai guji dan sa na aure….? Har ka hana yar mutane zuwa makaranta saboda ta ki aikata mugun nufin ka!! Wannan rayuwa ina za ta kai mu……. ” Baban Sasa ya fashe da kuka. Hakan ba karamin tadawa Amatullah hankali yayi ba, shi kuwa Baba Anas daɗa hasala yayi in da ya rufe Saifullahi da zagi ta inda ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Sai da aka dau wasu mintina kafin a samu Baban Sasa ya yi shiru. Ya na mai share hawaye da hannun rigar sa ya ce4 “Wallahi Saifullahi ka ba ni kunya, ka ci mutuncin zumunci! Albasa ba ta yi halin ruwa ba” “Allah ya ba ka hakuri Baban Sasa, na yi kuskure ina mai neman afuwan ku” Cewar Saifullahi, cikin ran sa kuwa lissafin yanda za mayarwa da Amatullah kwatankwacin tozarcin da ta masa a yau, dan gani ya ke duniya ba shi da makiyi da ya wuce ita.3 “Wallahi, wallahi, wallahi ba ka bi na bashin rantsuwa ciwon kai idan Amatullah ta yi a sanadiyar cikin nan, kuma ya zamanto kai ne sila Allah ya isa ba zan kuma yafe ma ka ba!” Baba Anas ya furta ya na mai nuna shi da dan yatsa. Kana ya kara da “Makaranta wajibi ne, ko da wasa kada ka kuskura na ji ka sake hana ta zuwa makaranta, wallahi sai na tsine maka Saifullahi!” A firgice ya dago ya na duban Baba Anas, in da ya girgiza masa kai cikin jaddadawa ya ce “Kwarai da gaske! Kalle ni da kyau! Ba ka isa ka shiga tsakanin mu ba, ba isa ka ɓata zumuntar mu ba, ka yi kaɗan! Ilimin ka da wayon ka su amfana ma ka da komai ba! Allah wadar da ilimi irin na ka! A sanadiyar ka mahaifina ya zubda hawaye wanda ni ina ɗan sa ban saka ya zubar ba, sai kai jika! Allah wadar na ka ya lalace. … ” “Ah ah Anas kada ka masa baki, yanzun ma yaya bare kuma ka masa baki! Ace ɗan sunnah ya ki ɗan sunnah?” Cewar Baban Sasa, “kai Saifullahi ka ba ni kunya, albasa ba ta yi halin ruwa ba!” Saifullahi da ya gama haɗa zufa faɗi ya ke “A yi hakuri Baban Sasa, in sha Allah za a gyara” “Ina wayar ta da ka karbe” “Dama ba karbewa na yi ba, sabuwa na yi niyar siya mata, Amma in sha Allah zan mayar mata da kayan ta” “Eh ka gaggauta mayar mata da shi! Yanzu karfe nawa ki ke da lecture?” Baba Anas ya tambayi Amatullah, ta wutsiyar idanu ta dubi Saifullahi, ganin yanda ya ke kallonta ta kasan idanu cike da tsana ya sanya ya yin karya, ta ce2 “Dama na safiya ne, kuma lokacin ya kure yanzu, sai dai gobe idan Allah ya kai mu” “Allah ya kai mu, kai ka ji Saifullahi gobe ta na da makaranta, ka kai ta, ka kuma dauko ta, kuma juna biyu in ka ga ba ta haife shi ba toh Allah ya rubuta dama ba zai zo duniya ba, Amma ciki dai sai ta haife, ta shi ki shiga ciki Allah ya maki albarka” Dama umarnin da ta ke jira kenan. Cikin sauri ta tashi ta shige ciki, nan ta bar Saifullahi gaban su Baban Sasa har lokacin ba su daina masa faɗa ba. Gwaggo ta yi mamakin ganin ta dan a tunaninta Amatullah na makaranta. Kamar yanda ta faɗawa su Baban Sasa haka ta labartawa Gwaggo. Sam Gwaggo ba ta ji daɗin yanda ta yiwa Saifullahi ba, a cewar ta me ya sa ba ta fara faɗa ma ta ba. Hajiya kuwa idan ran ta yayi dubu ya baci musammam yanda Baba Anas ya haɗa ta da Saifullahi ya mu su wankin babban mayafi. Bayan fitar Baba Anas Hajiya ta dada jaddawa Saifullahi maganar auren Ayush, ta ba shi shawarar ya fito fili ya shaidawa su Baban Sasa muradin shi na kara aure. Sai da yamma likis Amatullah ta yiwa Gwaggo sallama ta koma gida dan kuwa mijin na ta tun azahar ya bar gidan. Haka ta wayi gari ba tare da ta sanya shi a idanun ta ba, sai gani ta yi ya aje mata kudi bisa centre table tare da yar takarda wanda aka rubuta “Jikar Baban Sasa ina da tabbacin wannan zai kai ki makaranta ya dawo da ke” Ko da ta dirga da gaske zai kai ta din ya dawo da ita, sai dai iyakan abin da zai mata kenan, babu batun kudin cin abinci. “Oh ni Amatullah ciki ya jawo min zama da yunwa, amfanin sana’a kanan! Allah na rokeka ka ganar da miji na” Cewar Amatullah yayinda ta zura kudin cikin jakar ta. Dakin Saifullahi ta je, kofa a rufe, da kwankwasa ta ji shiru sai ta yanke hukuncin kila ba ya ma gidan. Bayan ta tabbatar ta aje masa komai na karin kumallo ta ɗauki hanya. Saifullahi kuwa tun sassafe ya ɗauki hanyar Abuja domin karbar offer din aikin da ya samu a ministry of power and housing a matsayin injiniya. Ya doka sammako ne ba dan komai ba sai saboda ganin Amatullah da ba ya son yi, dan gani ya ke idan su ka hadu Allah kaɗai ya san yanda zai kasance tsakanin su tsabagen haushi da tsanar ta da ya yi. Ranar da yunwa Amatullah ta wuni, in da ta yi danasanin rashin kullo wani abinci da ba ta yi daga gida ba. Ganin abincin Saifullahi yanda ta barshi ya tabbatar mata Saifullahi ba ya gida. Cikin sosawar rai da damuwa ta shiga kiran wayar shi, Amma babu amsa har ta hakura. Abincin na shi ta ci, da niyar girka ma sa wani. Hakan ko ta yi amma har bayan Isha’i babu Saifullahi, ta fara tsorata ta na kokarin kiran Baban Sasa sai gashi ya dawo. “Sannu da zuwa ya Saifullahi” Cewar Amatullah in da ta tashi ta na kokarin karbar jakar hannun shi. Hannu ya daga mata cike da hantara ya ce “Ke tafi can!! Wa ya ce mi ki ina bukatar sannun ki bare ki karbi jakar hannu na? Salon ki ƙala min sharri gun Baban Sasa ki ce na haɗa ki da jaka mai nauyi ɗan gwal din na ki ya zube?” “Ya Saif….” “Yiwa mutane shiru dallah!” Ya tsayar da ita ta hanyar daka mata tsawa. Shiru ta yi tana duban shi har ya shige dakin sa. Yanda ta jera masa abinci haka ta sake kwashe su da safe, kamar jiya yau ma ya aje mata kudin mota babu na abinci. Haka ta ɗauki kuɗin ta na mai rokan Allah ya sa ya gane, dan kuwa dai ba karamin kewan mijin ta take ba, yanda ya kaurace mata ba ta jin za ta iya jurewa. Karin kumallan da ta yi musu ta ɗan ɗiba cikin yar karamar kula ta saka a jaka, dan kuwa jiya ta ji a jikin ta. Haka rayuwa ta kasancewa Amatullah har tsahon sati guda suna zaman doya da manja. Ranar da ya kaiwa Baban Sasa offer letter ɗin shi ranar ya masa batun karo auren da ya ke son yi. Baba Anas wanda ya zo ya tadda Saifullahi na shaidawa Baban Sasa lamarin ne ya so ya hana. A hasale ya ce da Saifullahi ” Shin har yaushe ka yi auren da za ka zo mana da maganar kai gaisuwa wajan wata kuma? Kai mai gudun haihuwa ina kai ina kara aure?” Shiru Saifullahi yayi ya na mai dukar da kai. Duk da maganar ta sosawa Baban Sasa rai, sai ya kawar da san zuciya ya na mai murmushi ya ce ” Ai ina ga Anas zai fi kyau mu kalli wannan magana ta shi ta fuskar arziki, ka ji dai yace yarinyar nan tun kafin auren shi da Amatulah su ke tare, duk da kuwa ya san da maganar alkawarin da na ɗauka, kuma gashi yanzu ya sami aiki Alhamdulillah, kuma karin aure abu ne da Allah ya halatta mana, fatan mu Allah ya sanya alkhairi” STORY CONTINUES BELOW Farin cikin ran Saifullahi ba ya misaltuwa. A lokacin ya ji duk wani bakin cikin Amatullah da ya kunsa sanadiyar kawo shi kara da ta yi ya gushe. Ta je ta yi ta haihuwa ta lalace tunda zai auri Ayush din shi ya more rayuwa. “Sai ka shaidawa Anas sunan mahaifin yarinyar da unguwar da su ke dan a yi bincike ko cikin satin nan ko? Idan Allah ya sa aka sami yanda ake so zuwa karshen wata sai a kai gaisuwa kamar yanda ka bukata” Cewar Baban Sasa ya na mai duban Saifullahi da farin ciki ya bayyana karara a fuskar shi. “Toh Baban Sasa na gode kwarai Allah ya kara lafiya, bari na je na rubutu yanzun nan ma” Cike da annashuwa ya tashi ya shige ciki ba tare da ya tsaya jin amsar Baban Sasa ba. Baba Anas na mai girgiza kai ya ce “Ka ga yanda yaran nan ya ke rawan kai! Allah ya sa ba lasisin wulakanta mana diya ya samu ba” Baban Sasa na mai jinjina kai ya ce “Ko shakka ba na yi Saifullahi ba zai wulakanta Amatullah ba, Amma tun ranar da Amatulah ta kawo karar sa wajan mu, na dan yi danasanin auren nan, Allah ya sa karshen danasanin kenan” “Amen dan son Rasulillahi” Cewar Baba Anas. Kamar yanda ya ce ba a jima ba ya kawo takarda mai ɗauke da sunan mahaifin Ayush da sunan unguwar da su ke a Kano ya bawa Baba Anas kafin ya mu su sallama ya tafi. Ranar ba Saifullahi ba hatta Hajiya wuni su ka yi cikin farin ciki. Amatullah kuwa ko da ta dawo daga makaranta a gajiye, gashi zuciyar ta na tashi ta yi amai ranar ya kai su uku, gashi ko ta yi girki ma ba ci Saifullahi ya ke yi ba sai ta yi kwanciyar ta falo. Nan bacci ya fara ɗaukar ta sama sama. Kamar daga sama ta ji ana tashin ta. Cikin wannan hali Saifullahi ya dawo ya tadda ita. Ganin babu kular abinci ya tabbatar mishi cewa yau ba ta kawo ma sa abinci ba yanda ya saba gani, kai tsaye kitchen ya nufa ba dan yana jin yunwa ba, sai dan ya tabbatar da abin da ya ke zato. Aikuwa dai zatan shi ya tabbatar ba ta yi girkin ba. Falo ya sake dawowa ya na duban ta. Yanda ta yi rashe rashe ta na bacci hankalin ta kwance ba karamin kular da shi ta yi ba. Wato ta samu hutu ta dena girki tunda ba ya cin abinci maimakon ta zo ta lallabe shi ta bashi hakuri ganin ya dena cin abincin ta yanda yayi zato. Ransa bai kara baci ba sai da ta gyara kwanciya ta na mai ajiyar zuciya yayinda rigar jikin ta ya dan daga, dan shafaffen cikin ta ada wanda ya dan tasa yanzu ya bayyana gare shi, kallan cikin ya ke cike da takaici ya san nan da wani dan watanni cikin zai zama kato kamar kwarya, duk wannan shape din na ta ɓaci zai yi ta koma kamar buntuntuna. ‘gwara ma na aje girmen kai na more rayuwa ta kafin cikin ya girma ta zama mara fasali!’ Cewar Saifullahi cikin ran sa yayinda sha’awar ta ya taso masa har cikin ran sa. Dakin sa ya nufa yayi wanka sannan ya fito. Nan ya tadda ta tana ta baccin ta har lokacin ba ta tashi ba. Cikin takaici ya shiga kiran sunan ta “Amatullah! Ke Amatullah!!” Cikin magagin bacci ta ke duban Saifullahi da ya ke tsaye gaban ta “Malama ina abinci na?” Tambayar da ya jefe ta da shi kenan. A hankali ta murje idanu, kana ta tashi zaune duk da jirin da ke dibar ta. Kallan sa ta ke cikin nuna rashin fahimtar maganar da ya furta mata. Ganin haka ya sake faɗin “Kin dena ji ne? Na ce ina abinci na?” Sai da ta yi hamma, ta na mai rufe bakin ta da tafin hannun ta sannan ta ce “Ganin ka dena cin abincin ne gashi kuma ba dadi na ke ji ba ya sa ban dafa ba Ya Saifullahi” Amsar ta ba ƙaramin batawa Saifullahi rai ta yi ba, a fusace ya ce “Idan ba ballagaza ba wace mace za ta yi tunani irin na ki? Mijin ki ya dena cin abincin ki maimakon ki duba dalilin yin haka ki bashi hakuri ina ke lasisin dena girkin gaba daya ki ka samu ko?” STORY CONTINUES BELOW “Ayya mana ya Saifullahi, me ya sa ba ka min adalci ne saboda Allah da manzan sa? Kullum fa ina ma ka girkin nan kafin na je makaranta na aje maka, Amma haka zan dawo na kwashe kaya na, hakan kuma ba zai hana na maka na dare ba, shi ma haka zan kwasa da safe ba tare da ka taba ba, dan yau daya ban iya yi ba saboda ba na jin dadi sai ya zama matsala? Wani dalili zan tambaye ka bayan na riga na san dalilin na ka ba zai wuce na cikin da na ke dauke da shi ba?” A fusace ya na mai nuna ta da dan yatsa ya ce “Ni ke mayarwa magana haka? Har kin iya tsaurin idanun da za ki iya mayar min da martani?” Amatullah na mai dafe kai tsabagen yanda ta ji ya na sara mata ta ce “Auzubillahi minan shaidanir rajim!” “Ni ne shaidani Amatullah? Ni ne shaidanin na ki?” Cikin sanyi ta na mai kaskantar da kai ta ce “Allah ya ba ka hakuri, dan Allah ka yi hakuri wallahi ba na jin dadi Ya Saifullahi, Allah ya huci zuciyar ka” Ya na mai huci kamar maciji ya ce “Malama ba hakurin ki na ke bukata ba! Ki tashi ki shiga kitchen ki dafa min abinci, tuwon shinkafa na ke so da miyar bushesshen kubewa” Kallan sa ta ke cike da mamakin rashin imanin sa, a hankali ta ce “Wallahi ban da lafiya….” “Ina ruwa na? Ba ke ki ka zabi ki yi rashin lafiyar ba! Ki tashi ki dafa min dinner jor!” Ya koma kujera ya kame ya na hura hanci. A daddafe Amatullah ta tashi ta shiga kitchen jiri na dibar ta haka ta kokarta ta daura tuwan nan. Kafin ta gama ta zauna a kasan kitchen din ya kai sau goma. Ko da ta gama ta shiga falo ɗauke da kula sai ganin shi ta yi da robar take away gaban shi, ya hakimce ya na cin fried rice da kaza. Idanu cike da kwalla ta ce “Ayya mana ya Saifullahi, duk wahalar nan da ka bani ashe ka na da abin da za ka ci dan Allah? Me ya sa haka?” “Saboda na isa, dole sai na ci abin da ki ka dafa ne? Ina da damar canza shawara” Kular ta aje in da ta saba ba tare da ta sake tanka masa ba ta shige dakin ta. Shi kuwa dadi har ran shi dan ko shakka babu ya san yau ba karamin kuntatawa Amatullah yayi ba. Ta na yin sallar Isha’i ta yi wanka ta bi lafiyar gado tsabagen yanda ta ke jin jikin ta, gashi gobe ta na da sammako lecture din safe gare ta. Ba ta yi cikakken awa da kwanciya ba bacci ya dan sace ta sai ji ta yi mutum kusa da ita. Hankali tashe ta ce “Ya Saifullahi lafiya?” Dankuwa ba ta yi zatan zai shigo mata ba. Cike da takama ya na mai jawo ta jikin sa ba tare da ya damu da kunna wutar dakin ba ya ce “Hakki na za ki bani” Hankalin Amatullah ba karamin tashi yayi ba jin abun da ya zo da shi, kana cikin magiya ta ce “Dan girman Allah ka yi hakuri, wallahi, wallahi ban da lafiya ya Saifullahi, ka bari na sami sauki….” “Ki na nufin na bari ki haihu? Wa ya ce mi ki za ki sami lafiya muddin ba haihuwa ki ka yi ba ko zubar da cikin nan? Ba zan iya jira ba, hakki na nake so yanzu ma kuwa…” Ganin abin da ya taka ya sanya Amatullah ta yi shiru ba ta sake tanka masa ba, kyele shi ta yi yayi kidin sa yayi rawan sa, sai hawaye da ke bin kuncin ta daya bayan daya. Sai da ya gama biyawa kan sa bukata ba tare da ya tausaya mata ba sannan ya ja gefe yayi kwanciyar shi. Tsanar da ba ta taba yiwa wani ɗan adam ba haka ta ji na Saifullahi na ratsa zuciyar ta. A daddafe ta shige bayi domin ji take ba za ta iya kara minti biyar ba ba tare da ta yi wanka ba. Ta yi wankan ne tana mai fatan ba za ta fito ta tadda shi a dakin ba, Amma abin takaici haka ta fito ta ga ya kunna wutar dakin in da yayi rashe rashe bisa kan gado ya na waya. Kallan sa ta yi cike da takaici Jin ya na furta STORY CONTINUES BELOW “Haba mana Ayush kin san yanda na ke san ki kuwa? Ke kaɗai ce macen da na ke kauna, sauran mata ai suna su ka tara…… ” Amatullah na mai kawar da kai ta bude wardrobe din ta domin neman wata rigar baccin, tsabagen tsanar Saifullahi ya sa ba ta san mayar da wanda ta cire, Jin Saifullahi ya ce “Albishirin ki toh? Baban Sasa ya amince next week za su zo kawo kudin aure gidan ku…….” Cak Amatullah ta tsaya yayinda wani sabon jiri ya shiga kwasan ta har sai da ta sami waje gaban wardrobe din ta zauna dirshen. Saifullahi kuwa da ya lura da halin da maganar ta shi ya sanya Amatullah ciki tuni ya cigaba da jaddada soyayyar shi ga Aysuh. Zafafan hawaye ne su ka shiga fita daga idanun ta, ta na mai neman taimakon ubangiji ta samu ta ja wani doguwar riga da Allah ya sa ta kai hannun ta kan shi, tana rike da rigar ta bar masa dakin. A falon ta sanya kayan ta, kan doguwar kujera ta kwanta, maganar Saifullahi ke mata yawo a kunne ‘Albishirin ki toh? Baban Sasa ya amince next week za su zo kawo kudin aure gidan ku’ Duk da dai ta san yayi ne dan ya bakanta mata, kuma ya ci nasara kwaran gaske. Ta na mai tuhumar Baban Sasa akan amincewa da yayi akan auren Aysuh, duk da dai ba za ta yarda ba sai ta tabbatar da maganar tukun, dan kuwa idan haka ne da Baban Sasa bai kyauta mata ba cewar Amatullah cikin ran ta in da Tasha kukan ta ta koshi, ta na ji Saifullahi ya koma dakin sa amma ta kasa tashi ta koma na ta, sai wajan ukun dare bacci barowo ya sace ta. **** Washagari ta nemi izinin zuwa gida idan ta tashi daga makaranta, ya hana ta. Dan haka sai a waya ta samu ta yi magana da Gwaggo. Yanda Gwaggon ta ke mata hanya hanya na game da batun auren Saifullahi ya tabbatar mata da maganar hakan ta ke. Gaba ɗaya ta rasa nutsuwa, hatta lectures din ranar kasa gane su ta yi. Gashi Saifullahi ya fito mata da saban salo na neman hakkin sa duk dare, kuma bayan ya gama kuma ya kira Aysuh a waya Amatullah na ji ta na gani, idan ta yi magana ya ce matar da zai aura ne ko za ta hana shi abin da Allah ya halatta ma sa ne. Ranar da abin ya ishi Amatullah ta yanke hukuncin zuwa gida gun Baban Sasa sai ta taradda Saifullahi ya riga ta, ya je wai Baban Sasa ya kira Amatullah ya mata nasiha, jin zai kara aure gaba daya ta tayar da hankalin ta, shi tsoran sa kar wani abu ya same ta ko ɗan da take ɗauke da shi. Dan takaici ma kasa magana ta yi sai hawaye kawai, shi kuwa Baban Sasa da ya hau magana ya yarda da shi musammam ya san yanda mata ke daukar maganar kishiya tuni ya shiga mata nasiha da rarrashi, har da kada ta bashi kunya yana yaban ta sallah ta kasa alwala. Hajiyar Saifullahi kuwa ko da Gwaggo ta takura Amatullah ta je ta gaishe ta sai ta hau ta da faɗa , har ta na fadin da ba a auren a auri Amatullah. Wannan tashin hankalin da kuma ɗan laulayin da Amatulah ke fama da shi ya sa ta zama koma baya a makaranta, gaba ɗaya ta zama mara nutsuwa dan ko tayi karatun ma ba koda yaushe ya ke shiga ba, haka kuma ta na yawan fashi saboda rashin cikakken lafiya. A wani asibitin na gwamnati Saifullahi ya mata rigista na awo, cewar shi abubuwa sun masa yawa ba zai iya kai ta na kudi ba, aure ne gaban shi dan kuwa ba gaisuwa ba, hatta ranar auren shi da Ayush an saka, wata tara cif. A wannan hali jarabawa ta gabato har ta yi yi ta gama a daddafe. *** Cikin Amatullah na wata takwas aka kafe mu su result din first semester, haka kuma ana saura sati biyu su fara exam din second semester. Da in ta ji mutane na kiran sakamakon jarrabawa da dodon bango dariya ta ke yi, amma wannan karan ta tabbatar da zancen su zahir ne. A daddafe ta iso inda ake manna sakamako da sanarwa (notice board) Bayan sun ji labarin an manna. “Wannan ai mugunta ce, a rasa yaushe za a manna sai ana sati biyu mu fara jarrabawa” maman Jaafar ta faɗi cikin mita, da isar su kowa ya shiga duba na shi. GPA dinta ta duba kafin komai, wanda hakan ya girgiza mata kayan ciki don kuwa 1.26 ta gani, tana matsawa Ramin gaba na CGPA ta iske 2.13, motsin da yaron cikin ta ke yi bai sa ta duba sashin darrusa nan ta iske duk sun dawo mata. “Inna lillaahi wa inna ilaihi raji’un” ta ce tana mai zama a ginin da aka ma fulawowi da ke gefen su. Ko wancan jarrabawar ta fita da 4.51 dinta, duk wanda ya Santa ya san ta a matsayin ɗaliba mai daraja ɗaya (first class student). Addu’a ta shiga yi a zuciyar ta don neman ɗauki da agaji wajen Ubangiji. “muguntar ABU akan ki yau Amatullah, ba fa zai yiwu ba” cewar Maman Jaafar da itama sakamakon ya rikita wa hankali. “Kin manta C courses uku muka yi kuma duk Kinga ban zarce 47 ba” Amatullah tace cikin ƙarfin guiwa. “Even though, mu ka dai samu B balle ke, ni takaici na ba wai kasancewarsu C courses ba, kowannensu lamba uku (3 credit unit) gareshi, sannan chain prerequisite ne fa taso Amatullah mu je mu ji ina matsalar take” Maman Jaafar ta ce tana kamo hannunta, bata ce komi ba sannan ba ta Mike ba. A cikin darrusa bakwai ta ci guda biyu, ta faɗi biyar. Wanda duk son mai sonta bai da abin da zai ce da ita da ya wuce za ta sake maimaita aji uku. A rayuwar ta Sam ba ta san wani abu wai shi damuwa ba sai a Yan watannin baya. Shafo cikin ta tayi cike da so da kaunar abin da ke ciki duk da tana da masaniyar yana da hannu a faduwar ta jarrabawa. “Allah ya fi mu sanin daidai maman Jaafar” tace tana mai murmushi. Ba kawayenta kaɗai ba gaba ɗaya faculty of pharmaceutical sciences an girgiza da sakamakon Amatullah S. Jamoh, maluma da dama sun girgiza saboda an jinjinawa kokarin ta a shekaru biyun farkon ta a jamiar. *** Sai dare ta samu ta kira mahaifinta, bayan ta kammala duk wani abin da ta san Saifullah na bukata sannan ta shige ɗaki. Kuka sosai ta sanya masa tana faɗi masa sakamakon ta. “Babanmu Saura sati biyu jarrabawa, ko na yi ba zan gyara ba sai ma in ɓata, wallahi komi ban iya ba, Babanmu kar a yi withdrawing ɗina” tace cikin Kuka mai tsuma rai. Shiru yayi yana sauraren ta don shi Sam bai san ta inda zai kamo zaren ba. Ya dade da sanin tana cikin damuwa ɓoye masa ake hakan ya sanya shi mata aiken kudi lokaci zuwa lokaci. “a ina kike zuwa awo” ya samu kansa da tambayar ta. Shiru ya biyo baya don bata son yi masa ƙarya kuma ba ta son sa shi cikin damuwa. “ki samo medical report Sai ki yi deferring semester ɗin, inshaAllah shekara mai zuwa zaki dawo kan digadiganki” yace ganin ta yi shiru. Nasiha ya cigaba da yi mata yana mai faɗi mata mahimmancin da ke tattare da lafiyarta fiye da komi. A haka su ka yi sallama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *