TSANANI
CHAPTER 13
‘Daya daga cikin kujerun da na ajiye masa ya samu ya xauna yana fuskanta ta, tsananin kunyarsa da kwarjinin sa ne suka kamani, cikin kasalalliyar murya nace “mu’allim barka da dare” kafin ya amsa sai da ya bi ni da wani mayataccen kallo wanda yasa nayi saurin sunkuyar da kaina sannan ya daga baki yace “lafiya lau Sa’adatu” tun daga wannan maganar da nayi ban ƙara cewa komai ba, gyaran murya yayi min har yanzu idanunsa na kaina ya kasa ɗauke idonsa daga kallona, jikina har rawa yake yi ni ban saba da irin wannan kallon ba. +
A hankali ya daga bakinsa yace “Na san dole za kiyi mamakin ganina a wajenki kuma a dai-dai wannan lokacin, sbd baki taɓa tsammanin hakan daga gare ni ba” kaina a sunkuye na amsa masa da “eh”
Gyara xama yayi cikin siririyar muryar shi ya cigaba da cewa “Tun bayan lokacin da kika bani labarin irin halin da kika tsinci kanki na kasa samun nutsuwa, hankalina ya tashi naji idan har ban kasance cikin rayuwarki na tallafa miki ba nima baxan iya cigaba da rayuwa mai daɗi ba, da fatan dai dukkan damuwa da fargabar da tsohon mijinki ya sanya ki a ciki kin manta da ita, ina fatan kuma xaki karkade xuciyarki ki manta da labarinsa da dukkan abinda ya shafe shi, ina so ki saki jiki da ni nayi miki sabon dashen farin ciki a rayuwarki, ina fatan dai ban miki shishshigi ba”
Duk maganar da yake yi kaina na sunkuye na kasa magana, kunyar shi ce ta mamaye ni, sake tsare ni yayi da manyan idanunsa yana tambaya ta, “baki ce komai ba Sa’adatu”
A takaice na amsa masa da na amince.
Sake kwantar da muryarsa yayi yace min dago ki kalle ni kiga sakon da ke cikin idanuna, na san shi kaɗai xai baku amsar abinda ke kunshe a cikin zuciyata.
A hankali na dago na kalle shi, Muna haɗa ido ya kashe min kyakkyawan idanunsa gami da sakar min kyakkyawan murmushi, da sauri na sunkuyar da kaina, sbd idanunsa baxa su jure kallon kwayar idanunsa ba, soyayyarsu na gani sosai a cikin su.
Murmushi yayi “me yasa kika yi saurin ɗauke idonki?”
Ban bashi amsa ba sai wasa kawai da nake yi da yatsun hannuna.
Na lura da shi sosai farin ciki ne ya mamaye shi, fuskarsa a sake ya kuma cewa.
“Me yasa kika yi saurin amincewa da ni Sa’adatu don a kallon da kika min nima naga soyayyata a idonki?”
Sadda kaina nayi ina cigaba wasa da yan yatsuna “na tabbatar da cewa a wajenka ne kaɗai xan samu dukkan abinda na rasa a rayuwata, kana da kyawawan halayen da duk mace da kace kana so dole ne ta karbi soyayyarka, ga ka malami ga ka mai addini uwa uba kuma kai me kyau ne” ina gama fada na sa hannuwa na na rufe idanuna.
Murmushi naji yayi wanda sai da naji sautinsa a kunnena ” yanxu wannan duk ni kaɗai Sa’adatu anya baki yi son kai ba kuwa”?
Murmushi nayi tare da girgixa kaina alamar eh, haka muka kasance cikin farin ciki da nishadi sai naji na manta da komai a rayuwata, sbd na shiga wani sabon darasin rayuwa, wanda malaminsa ya kasance kwararre kuma masani a kan aikinsa.
Bai wani dade sosai ba ya tashi xai tafi, sai naji kamar nace ya dawo mu xauna mu cigaba da hira, sbd yadda kalamansa ke bin dukkan wani jini da sassan jikina, amma kuma kunya da nauyinsa da nake ji baxa su bari na fada masa ba, tabbas na san idan na roki wannan alfarmar xai min amma ni din ce baxan iya ba.Hannu yasa a aljihu ya miko min yar ƙaramar waya kirar Nokia, karbi wannan idan naje gida ina so xa mu yi magana, don ni gaskiya ban gaji da sauraren zazzakar muryarki ba. +
Makale kafada nayi alamar ya baxan karba ba, tsare ni yayi da ido ranshi a haɗe yace “Bana so idan na baki abu ki ƙi karba, da ni da ke mun xama abu daya”
Rausayar da kai nayi kamar xan yi kuka “Kada ka bani waya Game ta shagaltar da ni naƙi yi maka hadda ka dake ni” murmushi yayi wanda har sai da fararen hakoransa suka bayyana. “Ki karba ko ana dukan kowa kin san baxan daki gimbiyata ba, kuma ma ai wannan karama ce babu game din da xata ɗauke hankalin ki a ciki, ina so mu rika magana ne na rika jin lafiyar jikin ki” har ga Allah ban so karɓar wayar ba sbd yana amfani da abarsa amma ya ɗauka ya bani, sallama muka yi ya tafi.
Kwasar kujerun nayi na shigar da su gida, a inda na bar Adda a nan wajen na sameta, da gudu na ƙarasa wajenta na faɗa jikinta ina murna.
Kallona tayi tana mamakin yadda na shigo da farin ciki “lallai mu’allim yayi kamu, amma da doctor ne yace zai xo, da baxa a bashi dama ba”
Murmushi nayi kawai ba tare da na bata amsa ba, miƙa mata wayar da ya bani nayi, cikin farin ciki ta karba tana dubawa.
“Wato mu’allim da karfinsa ya faso baxai iya jure rashin jin muryarki ba shi ne har da baki waya to Allah ya riƙe miki Allah ya sanya alkhairi” amsawa nayi da ameen mun dade muna hira sannan kowa ya tafi dakinsa.
Wanka nayi na dauro alwala na saka kayan bacci, mamaki ne ya cika zuciyata ta yaya mutane hadaddu masu kyau da ilimi, suke rikicewa a kan soyayyata, na san banda ikon Allah babu yadda za a yi mu’allim ya so ni, ya fi ni komai na rayuwa, tunda ni ba wani kyau gare ni ba ya ninka kyauna sau ɗari, amma yanzu ya rikice a kaina da ni kadai yake so yayi rayuwa, gaskiya dole na godewa Allah don ba kowa Allah ya yi wa baiwar da yayi min ba, sai da nayi Sallah raka’a biyu nayi addu’a, ina shirin kwanciya naga kiransa, a hankali na kara wayar a kunnena tare da yin sallama, cikin kasalalliyar murya ya amsa min yana tambaya ta me yasa har yanzu ban yi bacci ba, amsa masa nayi da yanzu nake shirin kwanciya.
Kwantar da muryarsa yayi yana cewa “Ni kuwa kinga tunaninki ya hana ni bacci sai juyi nake yi ni kadai na rasa me ke damuna” rufe fuskata nayi kamar yana ganina ban bashi amsar maganar shi ba, na kawar da tunaninsa muka shiga wata hirar.
Mun ɗauki lokaci muna hira sannan muka yi sallama.
Juyi mu’allim yake yi yana jin wani sanyi da daɗi a ranshi, idan da abinda ya fi so a yanxu bai wuce farin cikin Sa’adatu ba, yarinyar ta riga da ta gama yi masa, yana ji a ransa baxa su ɗauki lokaci mai tsawo suna soyayya ba za a yi maganar auren su.
★★★★★★
Da gari ya waye ma da text message dinsa naci karo, kalamansa na musamman ne, kamar yadda komai nasa yake abin burgewa, sai da na gama komai na tafi makaranta, da naje aji sai na nuna kamar ba shi ne yazo wajena ba jiya, shi ma bai nuna ya sanni ba, yadda yake min a baya haka muka kasance har aka tashi.Innah ce xaune a tsakar gida tana ‘yan aikace-aikacen gida, yanzu rayuwar gidan tana yi mata dad’i sosai don ta samu sassaucin cin kashin da Innah Salamatu da ƴaƴanta suka yi mata shi kansa baban Sa’adatu ya gyara halinsa, don yanzu har girkin gidan tana yi. +
Yaro ne yayi sallama tare da karaso wa inda take cikin ladabi yace wai ana sallama da innar Sa’adatu, kallon mamaki ta bi shi da shi tare da xare hannunta daga robar da take tsintar shinkafa.
Wane ne yake kirana? amsa mata yayi da wani Mutum ne a waje, cikin mamaki ta sake cewa anya nan aka aiko ka kuwa ba can dakin aka ce maka ba.
Sake maimaita mata yayi da cewa wajenta aka aiko shi, cewa tayi ya faɗawa mai kiran nata ya shigo daga soro tana zuwa.
‘Daki ta shiga ta sako hijabinta tare da dakko tabarma ta fita, tana xuwa soron taga ashe makocin su ne Dr mukhtar. Da fara’arta ta ƙarasa wajensa tare da baxa masa tabarmar da taho da ita.
Lalale marhabun Dr ashe kaine a gidan namu, cikin sakin fuska ya amsa tare da xama a kan tabarmar, gaisawa suka yi sannan ya fara magana.
Dama doctor ne ya turo ni a kan Maganar nan da muka yi kwanaki da ke, to ya ji shiru ne har yanxu ba a sake cewa da shi komai ba, shi ne yace na sake dawowa naji a ina aka kwana, don shi a yadda yaso ma a yi magana da wuri sbd baya so abin ya dauki lokaci mai tsawo, kin san abokin nawa yanxu gauro ne sun rabu da matar shi ya karasa maganar yana murmushi.
Murmushi Innah tayi, to ai ba komai mu taimakon da Dr yayi mana baxa mu taɓa mantawa da shi ba, don haka ka faɗa masa na bashi dama yaje wajenta su daidaita kansu, amma yaje a ranakun asabar ko lahadi sbd yanxu tana zuwa makarantar islamiyya.
Doctor mukhtar yaji dadin jin labarin Sa’adatu tana xuwa makaranta, mun gode sosai da wannan damar da aka bamu Allah ya shige mana gaba.
Suna cikin maganar suka ji tafiya a bayan su da sauri suka waiwaya, ido biyu suka yi da baban Sa’adatu yana ta faman muzurai, ashe duk maganar da suke yi a kunnesa. Fuskarsa a daure ya fara tambayar Innah
Naji dukkan abinda kike shirin yi Kuma na gode, kin kyauta mero, abinda kika yi kin yi dai-dai.
Yanzu har isarki ta kai ki bayar min da auren ‘yata ba tare da iznina ba, sai dai kawai naji ana magana har kina cewa kin bada dama kamar ke kaɗai kika haifeta sbd kin raina ajawalina, wai ma wane doctor kike magana? Fada min naji wane ne da wannan ƙarfin halin.
D’aure fuska tayi sbd yanxu ita ma ta daina sakin fuska kamar da, kuma ta ɗan rage tsoro.
“Doctor din da Sa’adatu ta kwanta a asibitin sa ne shi ne yanzu yazo yana sonta”
Wani kallo ya bi ta da shi me kike faɗa min haka mero, kina nufin mutumin da ya ci mutuncina ya tozarta ni ya d’aure ne har adadin kwanaki uku a kurkuku, Sannan yayi silar kashe aure yata shi ne yanxu zai lallabo yace yana sonta da aure, tabbas maganar malam Jibo ta zama gaskiya da yace dama so yake ya kashe masa aure ya aureta, to wlh tun wuri kiyi gaggawar kwance wannan mugun kullin da kika yi, don baxan taɓa amincewa da wannan maganar ba, ko da hakan zai yi silar ajalina.Mayar da kallonsa yayi ga Dr mukhtar, kai kuma doctor Ina ganin mutuncin ka tun wuri ka fita daga wannan Maganar idan ba haka ba kaima xata kwabe da kai. +
Kallon mamaki kawai doctor mukhtar yake binsa da shi yana mamakin tijara irin ta malam Salisu.
A nutse Innah ta dube shi.
Nayi mamaki da ka shiga abinda ya shafi rayuwar Sa’adatu kaifa kace babu kai babu ita, kuma kada ta sake nuna ka a matsayin mahaifinta, to menene na damuwa don xata auri Wani mutum daban.
Wani abu yaji ya saukar masa a cikin jikinsa ya ji duk wani karfi da ke jikinsa ya neme shi ya rasa, mamakin kalaman Innah yake yi yaushe ta waye har ta koyi mayar masa da martani, bai taba tsammanin jin hakan daga gareta ba.
A sanyaye yace “Dama dole ki fadi haka mana tunda son xuciya da kwadayi sun rufe miki ido, shikenan yanxu ƙoƙarin fin karfina kike yi babu damar na saka doka a gidana sai kin karya min sbd kun raina min arxikina, kin samu masu xuga ki kina raina ni, to wlh baki isa ba indai ina doran kasa baxa a yi abin nan ba, kuma da kike cewa bana kaunar Sa’adatu na tabbatar da cewa na fi ki kaunarta, don ni duk abinda xai tseratar da ita daga halaka shi nake yi, amma ke kulllum burin ki ya za a yi ki jefata a hanyar shaidan don kawai ki samu kuɗi”.
Murmushi Innah tayi tare da bin sa da kallo yana ta kumfar baki, a fusace ya shiga cikin gida ya barta tare da doctor suna magana, sai da suka gama magana sannan ta shiga ciki tare da faɗa masa cewa ya faɗawa doctor duk lokacin da ya samu dama ya je ya ga Sa’adatu
Nade tabarmar da ta shimfida tayi, Sannan ta shiga cikin gida, dakinta ta shige jiyo Baban Sa’adatu tayi a dakin Innah Salamatu suna Magana.
A fusace ya shiga dakin tana ganin shi ta san ba lafiya ba, da sauri ta tashi ta tarbe shi tana tambayarsa.
Lafiya naga fuskarka a haka malam, me kuma ya sake faruwa sauke ajiyar zuciya yayi tare da cewa “waccen matar ce ta haɗa min takaici, wlh na rasa yadda xan yi da ita ƙoƙarin xame min masifar take yi a rayuwata, duk abinda ta san zai jefa ni a matsala shi take yi, gaba daya bata tausayinta, wlh ba don dokar da aka saka min a wajen hukuma ba da tuni na dade da sakinta”
Bayar da hankalinta tayi gare shi tare da gyara xama, Wani abin ta sake yi maka ne malam? labarin zuwan doctor mukhtar ya bata da abinda suka tattauna da innah.
Maimakon ranta ya ɓaci sai kawai ta saki wani murmushi cikin kissa ta fara Magana.
Haba Malam menene na damuwa don anxo maka da wannan maganar ai kai abin alfaharin ka ne, Allah ya kawo mana nama har gida, yanzu abinda ya rage mana shi ne mu bi duk hanyar da xamu bi don ganin damar ta dawo hannun mu.
Cikin rashin fahimtar abinda take nufi ya dubeta
Ban gane nufin ki ba salamatu, kuma gyara xama tayi “abinda za a yi kaje ka samu doctor din kayi masa magana kace kaji dukkan kudurinsa da alfarmar da yake nema a wajenka, kace xaka yi masa ka nuna komai ya wuce a wajenka, kayi ƙoƙari ya xama amininka ya xamto baya jin maganar kowa sai taka har ita uwar yarinyar, ta haka xaka shigar da bukatar ka, sai kace yazo yaga A’isha ko zaliha ka nuna masa sun fi Sa’adatu kyau da komai, tunda dai kaga mutumin nan mai kuɗi ne sosai xamu samu abubuwa da yawa a hannunsa, tunda yanxu ya’yan namu babu wanda yake zuwa wajensu, A’isha saurayinta tunda yace xai kawo kuɗi har yanzu shiru ko xance ya daina xuwa, ita kuwa zaliha kofarta ma a kulle take babu wanda yake ganinta yace yana sonta, kuma na san ba sharrin kowa ba ne illa wannan munafukar ta daki ita ce ta kulla asirin da babu wanda zai gansu yace yana so, ta ƙarasa maganar tana share hawaye, ka taimake ni malam kayi min wannan ƙoƙarin wlh ji nake yaran nan kamar a kaina suke na kosa na aurar da su, bana so wannan shegiyar mummunar yarinyar ta riga su aure sai su yi mana dariya ita da uwarta.
Shi kuwa duk abinda take faɗa masa jinta kawai yake yi, yaushe xai yi gangancin xama aminin doctor har abada baxai taɓa iyawa ba, sbd tsanar da yayi masa ba ‘yar karama bace. +
A xuciyarsa yace duk ba irin mugun halinki bane ya faɗa a kan ya’yan naki shikenan ba ki da aiki sai jafa’i, shi yasa duk ƴaƴan ba su da albarka, shi kansa ya san halin Innah Salamatu amma tsoronta baxai bari ya faɗa mata gaskiya ba.
Haka ya xauna ta riƙa yi masa Huduba amma shi ko a gefen silifas dinsa jinta kawai yake yana yi mata kallon mahaukaciya.
★★★★★★★
Yau mun samu ku san watanni biyu muna soyayya da mu’allim, kullum kaunarsa kara xurfi take yi a xuciyata, sbd a kullum kyawawan halayensa dada bayyana suke yi, duk wanda aka tambaya dangane da halinsa da mu’amalarsa alkhairi ake faɗa a kansa, yanzu har innah ta san da zamansa, abu ɗaya ke sanyaya min gwiwa idan na tuna da izuddeen dina, har yanzu na kasa cire soyayyarsa a xuciyata.
A kitchen nake tsaye ina yanka salad Kasancewar yau ba makaranta, Adda ce ta shigo ta tsaya bakin kofa tana kallona, da sauri na juyo don har na dan tsorata ma, murmushi tayi min tare da cewa amaryar doctor.
Dan turo baki nayi, haba Adda Amaryar mu’allim dai xaki ce ko ta izuddeen, ɗan murmushi tayi ke da baki ganshi ba kika sani ma ko duk ya fi su haduwa, ɗan juyar da kaina nayi haba dai Adda ki daina faɗa kada jinina ya hau.
Murmushi tayi nima da wasa nake yi Allah ya zaba mafi alkhairi, amsawa nayi da ameen.
Cigaba nayi da aikina, sake mayar da kallonta tayi gare ni.
Sa’adatu idan kin gama ki shirya yau doctor xai xo ku gaisa Yanzu ya kira abban su husna ya faɗa masa, a sanyaye na juyo na dubeta Kamar idona xasu kawo hawaye, ji nayi kamar nace mata ta faɗa masa kada yazo ina da wanda nake so, amma baxan iya yin hakan ba sbd ina ganin kimar Adda
A cikin zuciyata na amsa mata da to, girgixa kai tayi “naga alama kamar zuciyarki bata gama amincewa da doctor ba, alhalin kin san shi kin san wanene shi da dukkan halayensa, kada ki manta da karamcin da yayi mana, kada ki manta shi ne yayi mana sanadin fitar ki daga hannun tsohon mijinki”
Jikina ne yayi sanyi da kalamanta “haka ne Adda amma ni xuciyata gaba ɗaya tana wajen izuddeen ne da mu’allim idan ban auri ɗaya daga cikin su ba, baxan ji daɗin rayuwata ba, murmushi tayi shikenan ni dai ki fara shiri bana so ya zo ya jira ki.
Jikana ne duk yayi sanyi bana so na sake shigo da wani mutum cikin rayuwata ya tarwatsa min farin cikina, barin kitchen din nayi na shiga dakina.Ban wani yi kwalliya ba don raina a bace yake hijabina na xurma, fuskata sai faman maiko take yi, xama nayi ina jiran xuwansa, mijin Adda ne da kan sa yaxo ya kira ni yace min doctor ya xo, a salube na shiga daki na dakko masa sallaya na fita wajensa, shimfida masa nayi ina jiran shigowar sa, bin hanyar da xai shigo na riƙa yi da kallo, don ganin ta inda xai shigo. +
Wata hadaddiyar mota kirar Mercedes Benz yazo da ita mai launin baƙi, a hankali ya bude murfin motar ya fito fuskarsa dauke da murmushi, manyan kaya ne ɗinkin kufta mai launin blue a jikinsa yayi matuƙar kyau, kasancewar doctor kyakkyawan mutum ne sai dai ya ɗan fara manyanta dan xai kai shekara arba’in da biyar, sosai kamalarsa ta bayyana musamman da ya sanya manyan kaya, a hankali ya yake takowa har ya shigo soron, yana bi na da kallonsa mai matuƙar burgewa.
Shimfidar da nayi masa ya samu ya xauna ni kuma na xauna daga gefensa muna fuskantar junanmu, kamshin hadadden turarensa na dukan hancina, a ladabce na gaida shi, sunkuyar da kai nayi cike da jin kunya yayin da wani sashi na xuciyata ke cike da farin ciki da godewa Allah da yayi min baiwa mai yawa, banda ikon Allah na san babu abinda xai kawo doctor wajena, duk inda ake neman cikakken mutum mai kyau ilimi da addini tare da abin hannu ya kai wajen, tabbas babban abin alfahari ne a gare ni namijin kamar doctor faruq a ce shi yake so ya aure ni, idan aka ce na fitar da mace mafi sa’a a cikin dangin mu babu abinda zai hana na fitar da kaina.
Cikin kyakkyawar muryar sa ya amsa min da “lafiya lau sa’ar mata” wani daɗi ne ya daki kunnuwana ina jin dadi sosai idan aka kira ni da wannan sunan, sai ya tuna min da yayana salim don shi kadai ke kirana da wannan sunan.
Cigaba da magana yayi “Tabbas ina cikin farin ciki a wannan lokaci kuma na tabbatar da cewa na xo wajen da idan na miƙa kokon barata baxa a yi watsi da shi ba, yanayin karɓar da aka yi min shi ya tabbatar min da nafi kowane namijin sa’ar zaɓen abokiyar zama, ina fatan baza a ƙi karbar buƙatata ba”
Har yanxu kaina a sunkuye yake ban dago ba kuma ban bashi amsa ba, katse shirun da nayi yayi da cewa.
“Me yasa kika yi shiru Sa’adatu, ko dai docton naki bai miki bane?”
Ya katse min ɗan gajeran tunanin da nake yi.
Ɗan takaitaccen murmushi nayi “Ba tunani nake yi ba kawai dai nayi shiru ne sbd ban san me zan ce ba”
Murmushi ya ɗan yi gami da sukuyowa saitin kunnena, naga kamar kunyar mijinki kike ji sa’ar mata, ki saki ranki da mijinki kike magana don yanxu a raina ji nake har an bani ke.
Saurin dagowa nayi ina kallonsa wannan yar maganar tasa ta ɗan sosa min raina amma sai na kawar da wannan tunanin na dan yi murmushi wanda bai kai cikin zuciyata ba.
Cigaba yayi da magana, ki ajiye duk wani tunani sa’ar mata ban zo da niyyar yaudarar ki ba, aurenki naxo yi da gaske, duk da dai na san cewa baxa ki rasa masu sonki ba amma ina so duk kiyi watsi da su ki bani kyautar zuciyarki, na kasance mamallakin ta mai sanyata farin ciki a ko da yaushe, tsakani da Allah nake son auren ki kuma bana so na ɗauki lokaci mai tsawo ba tare da ke a cikin gidana ba, na san duk wadannan bayanan doctor mukhtar yayi miki, idan da so samu ne ma bana so ya wuce nan da sati biyu ko uku”
“Da sauri haka?” Na faɗa cikin muryata wacce kalaman doctor suka sanyayata.
Sake mayar da kallon shi yayi gare ni.
“to menene a ciki indai kina sona hakan nake buƙata, sbd a yanxu ba ni da aure zaman hakuri kawai nake yi, kuma ina bukatar na karbo yarana su dawo wajena sbd ban yarda da tarbiyyar gurin da suke ba”
Da sauri na dago Ina kallon shi tare da tambayar shi
“Dama ka taɓa aure?”
Cikin rawar murya ya amsa min
“Na taɓa aure sa’ar mata shekarar mu biyar da matar muka rabu muna da ya’ya biyu mata, sbd wani dalili wanda xan faɗa miki shi nan gaba idan kika zama mallakina, yanxu ku san watana tara babu mace, kinga ni abin tausayi ne namiji kamata lafiyayye babu matar aure, shi yasa na lallabo wajenki na san xaki share min hawaye na, kuma xaki riƙe min yayana amana shi yasa ma na zaɓeki ki xama abokiyar rayuwata” +
Sunkuyar da kaina nayi cike da tausayin shi a sanyaye na amsa masa da “insha Allah zaka same ni mai bin dukkan umarnin ka, amma me yasa baxa ka faɗa min dalilin rabuwar ku da matarka ba, don na san irin shirin da xan yi wanda zai sanya ka farin ciki na har abada”
A jiyar zuciya yayi tare da cewa.
“Ban yi niyyar bankada asirin iyalina ba, amma tunda kin bukaci jin abinda ya raba mu dole na faɗa miki, Sa’adatu tunda na auri matata ban san menene dadin aure ba, kullum cikin tashin hankali da bata min rai take, ban isa na sakata ko na hanata ba, bata san tayi min dukkan abinda xai faranta min raina ba, wannan dalilin ya tarwatsa tunanina har ya kai ga rabuwar mu, dan Allah ki yarda mu yi aure cikin sati biyu ki share min hawayena ki bani farin cikin shekaru biyar da na rasa a rayuwata”
Cikin tausayawa na dube shi. “Kayi hakuri insha Allah xan xamo mai share hawayenka mai sanyaka dariya, zan riƙe ƴaƴan ka tamkar ni na haife su, baxa kayi kuka da ni ba ko kaɗan”
Dan murmushi yayi.
“Naji dadin kalamanki sa’ar mata, tabbas na san na dace da mace ta gari, kin fi matata komai, kyau ilimi uwa uba kuma ga tarbiyya, wannan ya sa zuciyata ta kwadaitu da son rayuwa da ke”
Da sauri na dube shi, kawai dai xuga ni kake yi doctor amma ni ai bani daga cikin sahun mata masu kyau, kawai dai soyayya ce tasa kake min kallon mai kyau”
Yar dariya yayi gami da shafa dan kwantaccen sajen da ke fuskar sa “da gaske nake kin fita komai, ke yar baiwa ce kina da baiwoyi masu tarin yawa, amma ke baki san da su ba ni kaɗai nake iya ganin su”
Murmushi nayi gami da rufe idanuna da tafukan hannuna, a xuciyata nace na san kawai faɗa yake yi don yaji dadin bakinsa.
Murmushi yayi gami da lumshe idanun shi.
“Bari na tashi na gudu matar doctor yau ina da aiki mai yawa a asibiti ki kula min da kanki, kina da mijinki mai sonki da kaunar ki”
Gefen sa ya duba ya janyo wata ledar da ya taho da ita.
“Ga wannan naki ne kiyi amfani da shi”
Kaina a sunkuye nace “ka bar shi na gode” tsare ni yayi da ido “ki karba ke tawa ce komai na baki ban yi asara ba”
Karba nayi tare da yi masa godiya.
tashi tsaye yayi yana min sallama, murmushi yayi min “gobe ma sai na dawo don baxan iya hakuri ban yi tozali da kyakkyawar matata ba, da ina da hali ma yau za a daura mana aure na tafi da abata”
Kallon shi nayi kawai ban bashi amsa ba sai ɗan murmushi da nayi, har fita daga soron ya kama.
Yana tafe yana waigena, ban shiga gida ba har sai da naga ya hau motarsa ya tafi.
Da gudu na shiga gida tarar da Adda nayi a kitchen tana aiki, tana ganina ta hau murmushi, xube kayan da ya bani nayi a gabanta.
“Adda kin ji yadda doctor ya iya kalami kuwa, ya iya soyayya sosai amma Adda ya dyan fara manyata xai kai shekara arba’in da biyar” na karasa Maganar ina dan turo baki.
Murmushi tayi “lallai Sa’adatu har yanzu Akwai kuruciya a kanki, auren mai hankalin bai fi na wadannan kananan samarin ba, manyan maxa fa sun fi iya rike mace, kuma sun fi bata kulawa, ki tsaya kiyi karatun ta nutsu kafa kije ki cuci kanki” +
Rausayar da kaina nayi “Ni ba wannan ne yake damuna ba Adda ya taɓa aure fa har da ya’ya biyu amma sun rabu da matar, Allah bana son auren bazawari”
Saurin rufe idona nayi sbd nasan dole tayi min raddi.
“Inye lallai kin samu lafiya Sa’adatu, ke da kika auri kaxamin tsoho ko brush baya yi ga kazanta kin samu wannan kice bakya so, to xauna kallon ruwa kwado yayi miki kafa”
Kayan da ya bani ta shiga fito da shi lesina ne da atamfofi da takalma masu kyau, sai da ya kawo min kaya kala goma takalmi kala uku, gaskiya ya kashe min kuɗaɗen masu yawa, gefe guda kuma kwalin hadaddiyar waya ne kirar Samsung, har da sim card ya hado min, farin ciki ne ya bayyana a fuskata ganin yadda doctor yake son mayar da ni yar gayu dare daya, kamar ya san ba ni da wata sutturar kirki, wata envelope muka gani, da sauri Adda ta kai hannu ta shiga budewa, sababbin kuɗaɗe ne yan dari biyar zasu kai Kimanin dubu talatin, gefe guda kuma wata takarda ce yayi rubuta a ciki *_wannan kuɗin ɗinki ne sa’ar Mata ki karba ba yawa_*
Rungume takardar nayi ina murmushi, abinda ya bani mamaki shi ne yadda son doctor ke ƙoƙarin shiga zuciyata da wuri, tambayar kaina nayi ko dai so yake ya siye ni da kudinsa? Idan kuwa haka ne baxan bashi damar ya zamo abokin rayuwata ba.
addu’ar fatan alkhairi Adda tayi min sannan ta ajiye don nunawa mijinta abin arzikin da aka yi min, daki na tashi na shiga na fada kan gado ina godewa Allah, xuciyata cike take da farin ciki ban taba xaton xan samu irin wannan mijin ba a rayuwata, gefe guda kuma tunanin mu’allim da izuddeen na fara yi, ko yaya xan yi da soyayyar da suke min?? Wane hali xasu shiga idan na auri doctor na kyale su?? Wannan ita ce tambayar da na riƙa jefawa kaina wanda na rasa mai bani amsarta.