TSANANI
CHAPTER 18
Zaune nake bisa kujera ina wanke kwanunkan da muka bata, yau ni kadai ce a gidan duk kaɗaici ya dame ni ya’yan Adda duk sun tafi islamiyya, sauri nake na ƙarasa abinda nake yi na tafi wajen Rukayya, mu yi hirar mu ta xumunci, farin ciki ne lullube da zuciyata sbd na san izuddeen ya kusa zama mallakina har abada, sallamar da Adda tayi ne ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi. +
Tun kafin ta karaso take min murmushi “Amarya kin yi goshi, kinga abin arxikin da aka zubo miki kuwa? Abin dai sai wanda ya gani, kaya kamar ba da kuɗi yake siyan su ba, gaskiya yaron nan yana sonki da yawa”
Ta faɗa tare da karaso wa kusa da ni gami da cire mayafin da ke jikinta gefena ta samu ta xauna.
Cikin jin kunya nayi mata sannu da xuwa, ban nemi jin abubuwa da aka zuba min ba, sbd na san ina yin magana Adda xata ce ba ni da kunya, shi yasa na mayar da hankalina wajen aikina.
Sake yi min magana tayi.
“Baki ce komai ba Sa’adatu, ko alkunya kike min?”
A hankali nace
“To me xan ce Adda!?”
Murmushi tayi
“Yau dai kin ga damar yin shiru ne amma da sai kin tambayi komai da komai, tunda kin ji kunyata bari na faɗa miki, akwatu ashirin da hudu ya kawo miki, kuma kowacce cike take da kaya, har da sarkar gwal ya saka”
Da sauri na dafe kirjina.
“Ashirin da hudu kuma Adda? Gaskiya kayan sun min yawa ya xan yi da su”
Murmushi tayi
“Arziki da wadata ne yasa ya kawo miki, da ai bai miki ba da ba shi da shi, amma yanxu tunda yayi miki ai ba laifi bane sai ki godewa Allah, tare da fatan Allah ya baki ikon yi masa biyayya, domin izuddeen ɗan halak ne ya haifu, kinga kuwa ya cancanci kiyi masa komai matuƙar bai saɓa dokar Allah ba”
Kaina a ƙasa na amsa mata da “haka ne Adda”
Tashi tayi xata shiga daki.
“Yaushe xaki je gidan naku kiga kayan arzikin da aka yi miki”
Manyan idanuwana na xaro
“Haba dai Adda so kike innah salamatu ta saka ni a bakin duniya”
Siririyar dariya ta saki
“Kamar kuwa kin san yanxu a cikin jin haushin ki suke, kamar ke kika bawa kanki, sun manta Allah ne ke yin komai, kuma wannan hassadar baxa tasa su yi gaba ba, sai dai su yi baya”
Tana gama maganar ta shige dakinta.
Dama na san dole su ji baƙin cikin alkhairin da ya same ni, ni kaina ban yi xaton samun hakan ba ina kuma ga su, da suka ji abin babu zato ba tsammani dole su shiga damuwa.
Ƙarar da wayata tayi ne yasa ni saurin kai hannu wajenta, bakuwar number na gani da har baxan ɗauka ba sbd bana son d’aga number da ban sani ba, tashi nayi na shiga daki tare da kara wayar a kunnena cikin siririyar muryata nayi sallama.
Amsa min aka yi da
“Wa alaikumussalam”
Na so na gane Muryar mai maganar amma sbd an makale murya sai na kasa fahimtar mai maganar, kafin nace komai an sake yin magana.
“Malam Jibo ke magana, Sa’adatu ce ko?”
Ya karasa maganar tare da sakin siririyar dariya.
Bata fuska nayi gami da turo baki kamar mai maganar yana kallona na san ba kowa bane illa izuddeen.
“Babyna yau kuma kaine ka koma malam Jibo? Tabdi ashe kuwa zan fasa auren nan sbd baxan auri kaxamin ango ba”
Da sauri ya zare idanunshi tare da saita wayar a kunnun shi
“Sorry Babyna baxan sake ba, a yafe min”
Ya faɗa tare da tsugunnawa a ƙasa kamar tana ganin shi.
Dan turo baki nayi cikin sigar shagwaba nace
“Ni nayi fushi ma tunda ka haɗa kanka da Malam Jibo”
Murmushi yayi, cikin sigar tsokana yace.
“Na tuno miki da tsohuwa xuma ne fa, na san kin fi son malam Jibo fiye da yadda kike sona”
Ya fadi maganar tare da kanne idon shi guda daya.
A xuciyata ji nayi kamar nayi cilli da wayar sbd ya tuna min da abinda nafi tsana a rayuwata.Cikin marairaicewa na fara magana
“Dama baka sona ne xaka ce nafi son Malam Jibo a kanka, dama baka kishina ne zaka hada ni da shi, to me kake nufi da hakan?”
Yadda yaji hankalina ya tashi ne yasa ya shiga bani hakuri. +
“Yi hakuri Babyna ni fa na faɗa ne don a yi raha amma ke kanki kin san duk duniya idan akwai abinda na tsana bayan malam Jibo xai bi, nayi matuƙar kishi lokacin da kika xama mallakinsa, shi ne dalilin da ya sanya ni barin garin nan gaba ɗaya, sbd bana son na bude ido na kalle shi a matsayin mijinki, ta yaya zan kasa tsanar shi Sa’adatu? shi ne mutumin da ya so ruguza rayuwar iyalina, ya raba ni da ke a lokacin da nake tsananin buƙatar rayuwa da ke, yayi ƙoƙarin cin itaciyar da ba tasa ba, ni fargabata ɗaya ce ma Allah yasa bai shigar min hurumina ba”
Shiru nayi ba tare da na bashi amsa ba, a xuciyata nace lafiya naje gidan sa, kuma lafiya na dawo, amma baxan faɗa maka ba sai lokaci yayi xaka gane da kanka.
Cikin kasalalliyar murya ce
“Na san na bata miki rai sa’adatuna kiyi hakuri, ke nake so kuma bazan daina sonki ba, ko da a ce za a sanya mashi a ciro zuciyata daga cikin kirjina, zan hadiye dukkan wani zafi, zan jure kowace irin azaba matuƙar dai zan same ki a matsayin mallakina, ina fatan kema zaki kasance cikin sona, na tsawon rayuwa”
A sanyaye na amsa
“Insha Allah xan kasance cikin sonka da kaunar ka, baxan taɓa guje maka ba har abada, kalamanka sun yaye min dukkan damuwata, farin ciki mara misaltuwa kan ziyarci zuciyata a dukkan lokacin da na ji sautin muryarka, murmushinka babban abu ne da yake yayen damuwata, kaine ɗaya tilo da na dam’kawa ragamar zuciyata. Ni taka ce har abada”
Sauke ajiyar zuciya yayi wanda har sai da naji sautinsa a kunne na, lumshe idanu yayi har cikin zuciyarsa yake jin saukar kalamanta a kunnesa, ji yake kamar yayi fiffike ya dawo a daura musu aure ya huta da kewarta, a hankali ya fara yi mata magana.
“Alƙawari ne na ɗauka, ba zan taɓa barin damuwa ta wanzu a cikin zuciyar ki ba matuƙar muna a tare da juna, ina fatan nan da wani ɗan lokaci na tabbatar da hakan gare ki, bayan kin zamo mata a gare ni, ke kaɗai zuciyata ta amincewa sa’ar mata, kece mafarkina kuma kadarar da nake fatan na mallaka a rayuwata, na san matukar na same ki na gama dacewa”
Amsawa nayi da “Insha Allah”
Muryar shi ƙasa-ƙasa kamar me rad’a yace min.
“Xuciyarki tayi sanyi ko har yanxu akwai damuwa a cikinta?”
A hankali na d’aga baki nace.
“Babu damuwar komai a xuciyata sai tsantsar sonka da kaunarka”
Dan siririn murmushi ya saki.
“Yauwa naji dadi tunda haka ne bari na baki labarin mafarkin da nayi mana yau, kin shirya?”
Cike da kosawa na amsa masa da
“Na shirya ka san ni ina son komai matuƙar daga wajenka yake, na kosa naji abinda ka gani cikin mafarkin naka”
Murmushi yayi
“Kada kisa nace sai kin biya fa”
Ɗan harar shi nayi
“Fadi ko nawa ne xan biya ka, ka san yanxu ina da kuɗi”
Dariya ya ɗan yi
“Ba ki da abinda xaki biya ni a yanzu, ki bari idan muka yi aure ki cika min baki xaki gane ba ki da wayo”
Na gane abinda yake nufi shi yasa nayi shiru ba tare da na tanka masa ba.
Labarin mafarkin ya fara bani.
“Cikin dukkan mafarkan da nake yi bayan haduwata da ke, ban taɓa ganin wata rana da ta zo ta kuma wuce, ba tare da na ganmu tare a cikin wani lambu mai sanyaya zuciyar masoya ba, rayuwa ce mai daɗi ke gudana a tsakanin mu, ina fatan wannan rana ta bayyana a gare ni a zahiri ba a cikin mafarki ba”
Sunkuyar da kaina nayi a hankali nace “Ta kusa bayyana a gare mu nan ba da dadewa ba”
Murmushi yayi
“Wane irin tanadi kika yi mana a wannan lokacin”
Ban iya bashi amsa ba na san tsaf xai iya sakin layi a amsar da xan bashi
Godiyar abinda ya yi min a lefe nayi masa, tare da yi masa addu’ar Allah ya ninka arzikinsa, sallama yayi min tare da alkawarin zai cigaba da kulawa da rayuwata matuƙar yana numfashi.
Cike da farin ciki na ajiye wayar ina tuna kyawawan kalamansa.
Sallamar da aka yi a tsakar gida ne ta sanya ni fita don ganin masu sallama.
Ƙungiyar yan makarantar mu ne suka biyo sahuna sbd rashi sbd rashin xuwan da bana yi. +
A dakin Adda na sauke su sannan na kawo musu ruwa da lemo, dawo wa nayi muka xauna tare da su, bayan mun gaisa nake tambayar su labarin makaranta da kuma Mu’allim.
A nan suke faɗa min shugaban makarantar ne ya aiko su don jin abinda ya hana ni xuwa, a sanyaye na amsa musu da.
“An cire ni ne sbd xan canja gari a can xan cigaba da karatuna”
Basu ji daɗin rabuwa da nayi da su ba, sun nuna damuwar su a fili tare da yi min addu’ar Allah yasa haka ne ya fi alkhairi a gare ni, ko kaɗan ban fada musu za a yi min aure ba.
Tambayar inda mu’allim yake nayi.
Faɗa min suka yi ya daina xuwa makarantar gaba ɗaya tun bayan da na daina xuwa, su kansu sai da suka yi xargin ko da wani abu a tsakanin mu, faɗa musu nayi babu komai watakila ko wani uzurin ne ya tsare shi.
Mun dade muna hira da su sannan suka tafi gidajen su.Washe gari da safe bayan nayi wanka na kammala aikina, Innah ta kira ni a waya tace tana son ganina, ba don raina yaso ba haka na shirya na tafi gidan, tun lokacin da Baba yayi min korar kare gidan ya fice min a raina, ko kaɗan ban son abinda xai sa naje, nafi so ko ina da bukatar wani abu innata ta kawo min. musamman ma yanzu da su Innah Salamatu suka daɗa zafafa adawar su gare mu, bana so naje a faɗa min abinda xai hana ni bacci, haka dai na shiryar ba don na so ba na tafi, sai da na fara biyawa ta wajen Rukayya sbd ta raka ni. +
Tun daga soro nake jiyo haniyar jama’ar gidan, wannan ya tabbatar min da cewa dukansu suna tattare a tsakar gida suna gulma.
Cikin siririyar muryar mu mara hayaniya ballantana hargowa muka yi sallama, saurin sunkuyar da kaina nayi sbd wani irin kallo suke bi na da shi kamar basu taɓa ganina ba, babu wanda ya iya amsa mana sallamar mu, sai kallon mamaki da suke min, ko kala na canja musu oho.
Innah Salamatu da su A’isha duk suna wajen, wani kallo A’isha da zaliha suka watsa min gami da yin gefe da kawunan su, a ladabce muka tsugunna har ƙasa muka gaida innah, kamar dole haka ta amsa, ragowar matan gidan kuwa babu wacce ta amsa min, har yanzu dai kallon sama da ƙasa suke yi min gami da tabe baki kamar zasu yi min magana sai kuma suka fasa.
Tsaki suka sakar mana gaba ɗayan su gami da buga mana harara, a wannan karon lamarin su bai bani haushi ba sai ma dariya da naji na ƙoƙarin fito min, juya bayan mu kenan naji A’isha na magana.
“Innah wannan fa don taga xata auri mai kuɗi ne shi yasa ta fara jiji da kai, da bamu san asalin mutum bane sai yayi mana girman kai, Allah yasa dai mun san daga gidan ƙasa mutum ya fito kuma da gero aka raine shi”
Juyowa nayi kawai na kalleta tare da sakin siririn murmushi, wannan murmushin da nayi ba ƙaramin ‘kona musu rai yayi ba.
Nan fa suka fara habaici har da xagi ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba.
Sake kallon innarta tayi.
“Nima fa innah nayi wani sabon saurayi mai kuɗi mai ilimi kuma sananne ne a cikin unguwar nan, yace a sati biyu xai fito ya aure ni, akwatuna hamsin ma yace xai min, ba irin na wannan yar matsiyatan ba”
Ta karasa maganar tare da galla min harara.
Da sauri ta dubeta tare da rungumeta
“Alhamdulillah Allah ya share min hawayena shi yasa nake sonki A’isha kina da kishi sosai, gara dai ki kankaro mana mutuncin mu, ko don waɗanda basu gaji arxiki ba su daina yi mana kallon yan iska”
Ta ƙarasa maganar tare da mi’kewa tana daɗa janyota jikinta.
Kallon kallo kawai muke yi da Rukayya mamakin wannan muguwar dabi’ar tasu muke yi, a cikin maganganun da suke yi xaka fuskanci akwai tsantsar hassada da baƙin ciki, don haka bamu saurare su ba, shirun da muka yi ma ƙara musu wani baƙin cikin ya yi.
Kai tsaye dakin Innah muka shiga, cike da farin ciki ta tarbe mu, taji daɗin ganina a dakinta don tun lokacin da aka fitar da ni zuwa gidan malam jibo bata sake ganina a dakin ba, wajen zama muka samu tare da gaisawa da ita.
Gefen cinyarta na samu na kwanta.
“Oh!! Yaushe rabona da dakin nan har na manta, ta ƙarfin tsiya dai sai da aka so raba ni da ke Innah”
A kunyace ta ture kaina
“Ke dai ban san lokacin da xaki girma ba Sa’adatu ba ki da burin da ya wuce ki haye min cinya kamar wata yarinyar goye”
‘Bata fuska nayi
“Haba innata yaushe rabon da na hau cinyar ki, a lalace fa na kusa Shekara, ko bakya farin ciki da ganina ne na tashi na tafi wajen Addata, dama na fuskanci ta fi ji da ni”
Murmushi tayi
“A’a ya za a yi naƙi farin ciki da ganin ki Sa’adatu, halin nan naki na son jiki ne bana so, kije wajen Addar taki ita xata iya da wannan shashancin naki”
Rausayar da kai nayi
“Haba innata idan ban raɓi jikinki naji dadi ba jikin wa xan raɓa”Murmushi tayi kawai cikin jin kunya ta sake janye kaina daga jikinta, ban san me yasa innah ke jin kunyata ba, musamman da lokacin aurena ya matso ga shi dai, ba ni ce yarta ta fari ba, ko don ba tada wata yar bayan ni shi yasa take min alkunya ne.
Gyara zama nayi tare da kallon ta
“Innata gani naxo amsa kiran ki Allah yasa dai ba laifi nayi ba”
Bude bakinta kenan xata bani amsa, innah salamatu ta danno kofa tare da xaunawa a kusa da Rukayya sai faman muzurai take yi kamar wadda aka yi wa wani abu.
Kallon Innah tayi fuskarta ba annuri.
“Dama zuwa nayi na faɗa miki A’isha ma ta samu miji gobe ko jibi zai turo a yi maganar aure, mai kuɗin gaske ne akwatu hamsin yace xai mata”
Cike da farin ciki Innah ta dube ta
“Kai amma naji daɗi, haka muke so ƴaƴan mu duk su sami inda zasu huta Allah ya sanya alkhairi Allah yasa za a yi da mu”
Amsawa tayi da ameen tare da tashi ta bar dakin, tsakar gidan ta koma ta faɗa musu amsar da Inna ta bata, baka jiyo komai sai shewar su da ihu wai A’isha ta samo musu miji mai kuɗi.
Cike da nutsuwa na dubi Innah
“Wato innah ita dai babar su A’isha baxa ta bar halinta ba”
Girgiza kai innah tayi.
“Ai barin hali sai mutuwa kullum sai sun fito sun yi habaici, wannan ni’imar da Allah yayi mana ne basa so, shi yasa kullum da irin ƙaryar da suke kirkira wai dole dai sai an ce basu gaxa ba”
Hirar mu muka cigaba da yi cikin kwanciyar hankali, kayan gyaran jiki innah ta miko min.
“Kinga dama dalilin da yasa na kira ki, wannan kayan xaki karba ki kaiwa Addar ki, kayan gyaran jiki ne ki riƙa sha kullum, abinda yasa ban zo ba, sbd baxai yiwu na fita na bar kayan nan ba, kada a shigo a kwashi wani abin, yanzu ma ana ƙoƙarin gwada sata, Allah ne bai basu sa’a ba, shi yasa baxan fita na bar su ba”
Amsa mata nayi da “Haka ne Innah, Allah ya kare mu daga sharrin su”
Amsawa tayi da ameen
Cigaba muka yi da hira tare da bani shawarwarin da xasu amfane ni a zamantakewar aurena, tare da janyo hankalina a kan muhimmancin hakuri da irin sakayyar da Allah yake yiwa bayinsa masu hakuri, ta janyo hankalina a kan yawaita ibada da addu’a tare da dogaro da Allah a kan dukkan abinda ya shige min duhu.
Muna cikin maganar ne daga can nesa muka jiyo ihun A’isha, innah salamatu da zaliha sun sakata a daki suna ta jibgarta kamar Allah ya aiko su, har innah ta tashi xata fita muka dakatar da ita ni da Rukayya, don yanzu sai Innah Salamatu ta dawo da faɗan kanta taji daɗin faɗa mata magana mara daɗi, bata yi gardama ba ta dawo ta xauna.
Ragowar mutanen gidan mu ne suka karɓe ta da kyar, biyo ta suka yi tsakar gida suna ƙoƙarin sake rufeta da duka, a guje ta fita ta bar gidan.
Banda masifa Innah Salamatu babu abinda take yi, jama’ar gidan mu sun cika tsakar gida sai tambayarta suke yi dalilin dukan da take mata, amma ta kasa bayani sbd halin baƙin cikin da ta samu kanta, sai da zuciyarta tayi sanyi sannan ta fara magana.
“Wai a ce yarinyar nan ni xata xauna ta riƙa yiwa karya, tace min ta samu mijin aure mai kuɗi ashe ba kowa bane sai malam Jibo, wai yanzu shi take so idan ban aura mata shi ba mutuwa xata yi, ai kuwa wlh sai dai ta mutu ɗin ba ni da asara, don baxa ta janyo min abin kunya da xagi a unguwa ba”
Cike da mamaki suka hau salati.
“To fa ana wata ga wata, ita kuwa A’isha me ke damunta ko dai ba tada lafiyar ƙwaƙwalwa ne, amma banda haka me xata yi da Malam Jibo rashin miji hauka ne?”
Cikin jin haushi Innah tace.
“Idan ma ba tada lafiya ne wlh xata warke don wannan sam baxai yiwu ba, idan ma wani abin yayi mata yau ɗin nan zan je wajensa na ci masa mutunci ya warware, ni xai munafunta, ya ci amanata”
‘Dakinta ta koma zuciyarta tana yi mata wani irin bugu ji take kamar ta shige lahira sbd takaici, ga baƙin cikin alkhairin da ya samu Sa’adatu, ga kuma abinda A’isha take son had’ata da shi.
Sai a lokacin ta tuna da turaren da ya bata, a nan ta tabbatar wa da kanta duk wani abu a cikin turaren ya kulla shi.Komawa tayi ta kwanta zuciyar ta na yi mata wani irin xafi. +
Ni da Rukayya da Innah kuwa kasa magana muka yi, sbd irin wannan sakayyar da Allah yayi mana, ita ta bada shawarar a aurar da ni ga malam Jibo yau kuma ga ‘yarta ta faɗa kogin kaunarsa, ita ma sai taji irin radadin da muka ji ni da innata, ko kaɗan ban tausaya musu ba, sai ma godiya da na yiwa Allah da ya fara saka min xaluncin da aka yi min tun kafin a je lahira.
Har dare babu A’isha ba labarin dawowar ta, ko da Baba ya dawo ta bashi labarin abinda A’ishar tace bai wani damu ba, Allah ya sawwake kawai ya faɗa gami da shigewa dakinsa ya kyaleta.
Rufa mayafinta tayi da kanta ta fita nemanta, kai tsaye rumfar Malam jibo ta nufa inda yake xama tare da almajiran sa.
Tana nufar wajen taji yana magana ƙasa-ƙasa, don haka ta tsaya a gefe don jin abinda xai faɗa.
“Kiyi hakuri A’isha ki kwantar da hankalin ki, ko kowa ya guje ki ni nayi alkawarin kulawa da rayuwar ki, tunda kika zaɓe ni a matsayin masoyinki baxan baki kunya ba, kada ki damu da dukkan abinda innarki xata ce, ko tana so ko bata so sai na aureki na kawo ki gidana, kin haifa min ya’ya kin gama yi min komai tunda kika zaɓe ni a matsayin abokin rayuwar ki, ni kuma xan yi miki halacci”
A dai-dai lokacin ta shiga rumfar, jawo wuyan A’isha tayi ta fara jibgarta kamar Allah ya aikota, cike da ƙarfin hali malam Jibo ya shiga ƙoƙarin karɓar ta, amma sam ya kasa, cike da firgici ya fara yi mata magana.
“Menene haka Hajiya Salamatu ba ki da hankali ne sai kin je kin yi d’anyen aiki”
Kafin kace me rumfar ta cika da mutane suna kallon yadda xata kasance.
Bata saurare shi ba ta cigaba da dukanta har sai da taga ta fadi ƙasa ta daina motsi, sannan ta juyo ta kalle shi.
“Kai kuma tsohon munafuki tsohon najadu na dawo gare ka, duk wannan masifar kaine sila tun daga wannan turaren da ka bata bata sake dawo wa dai-dai ba, to wlh tun wuri ka warware aikinka kafin hukuma ta raba ni da kai”
A fusace ya dubeta
“Ba ni nace ina son yarki ba ita da kanta ta kawo kanta ta nuna sha’awar aurena, ni kuma tunda ta nuna tana sona ko ana muzuru ana shaho sai na aureta sai dai duk abinda xaki yi kiyi, ni kuma a shirye nake da ɗaukar mummunan mataki a kanki”
Wani irin kallo tayi masa
“Ni kake faɗawa haka Malam Jibo?? Ni xaka tozarta ka ci wa mutunci a gaban jama’a”
Kafin yayi magana ta ɗauki suturar Sallah ta maka masa a kansa, nan da nan jini ya fara xuba, mutanen da ke gurin ne suka kama shi tare da d’aure masa wajen sbd jiri ke kokarin kayar da shi. Kafin a yi ƙoƙarin kai shi chemist tuni numfashinsa ya fara yin sama-sama, wata irin kumfa na fitowa daga bakinsa.
Tana ganin haka ta kama hanyar tafiya gida, cike da firgici ta shigo dakinta ta wuce tana wani irin nishi.
Hayaniyar mutane muka ji sun danno tsakar gidan mu suna cewa Innah Salamatu ta kashe malam Jibo.
A razane muka fito don ganin abinda ke faruwa.Gaba ɗaya suka danno kai cikin gidan suna ƙoƙarin shiga d’akinta, da sauri innah ta ƙarasa wajen su tare da dakatar da su.
“Haba bayin Allah ya za a yi ku shigo cikin gidan matan aure haka kai tsaye ba sallama kuma kuna ƙoƙarin shiga dakinta ba tare da neman izini ba”
A fusace suka bata amsa
“Kin san irin ɓarnar da tayi ne da xaki kareta, mutum fa ta kashe, ko dan ba ɗanki aka kashe ba”
Dafe kirji muka yi gaba ɗaya muna salati, nan da nan innah ta hau kuka tausayin Innah Salamatu ne ya kamata, cikin jimami muka tambaye su wanda ta kashe.
A nan suke faɗa mana malam Jibo ne, kafin su kammala bamu amsa har fusatattu daga cikin su sun faɗa dakinta sun fito da ita.
Bin ta muka yi muna kuka har aka isa kofar gida, sauran mutan gidan mu kuwa sai guna-guni suke yi suna gulmar ta, babu wanda ya bada hakurin a kyaleta. mutanen unguwa ne suka taru a kofar gidan mu kowa na tofa albarkacin bakinsa, ba ƙaramin mutuncin gidan mu ta xubar ba, duk da cewa dai kowa ya sani halinta, ƙoƙarin kai ta wajen yan sanda aka yi, sai mai unguwa ne yace a dakata a jira babanmu ya dawo, shi kuma malam Jibo aka wuce da shi asibiti.
Taimakon gaggawa aka shiga bashi cikin ikon Allah ya farfaɗo a daren aka sallamo shi, ita kuwa A’isha babu wanda yake ta tata sbd masifar da uwarta ta dakko, a kwance take a daki tana ta numfarfashi Inna ce tasa aka kaita chemist aka bata magani.
A daren aka samu aka kashe case din ba tare da an je wajen hukuma ba, sai dai malam Jibo ya yi rantsuwa ko tana so ko bata so sai ya auri A’isha sai dai ta rataye kanta sbd baƙin ciki.
A ranar daga ni har Rukayya a gidan Innah muka kwana sbd tashin hankali, sai washe gari bayan rana ta d’aga muka koma gida, ina komawa na bawa Adda labarin halin da Innah Salamatu taso jefa kanta da ƴaƴanta, ba ƙaramin tausayi ta bata ba don abin gaba ɗaya babu daɗin ji.
***********
Shirye-shirye sun fara nisa don yau bai fi sati uku ne suka rage a daura min aure da izuddeen ba, a kullum akwai irin kalar gyaran jikin da xa a yi min, ko kofar gida bana fita sbd ana so jikina yayi kyau ya gyaru, Adda ce ta ɗauki nauyin komai har gida wata yar Sudan ke xuwa ta gyara ni.
Baya ga kayan mata da ake ta bani gaskiya Adda na matuƙar hidima da ni, sai dai fatan Allah ya bani ikon saka mata da abinda tayi min.
Sallamar Innah naji da sauri na ƙarasa wajenta ina yi mata sannu da xuwa.
Kallona tayi cike da kulawa.
“kinga wani kyau da kika yi Sa’adatu lallai gyara yana yi”
A kunyace na kalleta.
“Ai babu abinda xamu ce da Adda sai godiya innah, amma tana ƙoƙari sosai a kaina”
Riƙe da hannun junanmu muka shiga dakin Adda a kwance muka tarar da ita, tana ganin innah ta miƙe tana mata sannu da xuwa ruwa naje na kawo mata da abinci sannan na fita na basu guri.
Inna tazo wajan addah ne don su yi shawara akan maganar yadda za a yi da kayan dakin da za a siya min, tunda Babana a yanxu ba shi da ƙarfin da zai iya yi min komai da ake buƙata.
Kallon Adda tayi sannan ta fara magana.
“Kin ji dai dalilin da ya kawo ni gidan nan, tunda yanzu ba mu da halin kuɗin kayan dakin Sa’adatu ba mu da dalilin su, me xai hana a siyar da gonata guda ɗaya, don mu samu mu siya mata ‘yan kayan zamanin nan da ɗan abinda ba a rasa ba, kin ga dai yaron nan yayi mana hidima sosai kuma yadda naji ance ya gyara gidansa sosai bai kamata mu nuna rashin xuciya ba ko ya kika gani?”
Mayar da ajiyar zuciya Adda tayi
“Eh wlh yaya haka yayi dama anjima nake so nazo wajenki mu yi maganar sai kuma ga ki Allah ya kawo ki”
Tashi tayi ta shiga laluben kan gadonta, wata leda ta d’akko tare da mikawa innah.
“kinga wannan kuɗi ne Abban su Ihsan ya bayar a baki, yace babu yawa ki karba da hakuri, wannan kuma kuɗin wajan Dr ne da yake bawa Sa’adatu, shi ne muke ajiye wa, kinga duk su ma zasu taimaka a rage wani abin, sai mu shiga kasuwa mu siyo kayan kitchen da sauran abubuwan buƙata, a yadda nake so ma idan Allah yasa kuɗin sun yi ragowa sai a haɗa mata har da gararta insha Allah”
Farin ciki ne ya bayyana a fuskar Innah ba ƙaramin dadi taji ba.
“Kai Alhamdu na gode, shikenan duk abinda kika ce haka za a yi, Allah ya saka muku da alkhairi ALLAH ya bar mana zumuncin mu”
Amsawa tayi da “Ameen” +
********
zaune nake kan sallaya na idar da sallar azahar, Kur’ani ne a hannuna ina karantawa,
wayata naji tana qara, cikin nutsuwa na kai hannuna na ɗauka sunan Dr na gani yana yawo a kan wayar, a hankali na saka hannu na na danna.
Sallama nayi masa, cike da girmamawa ya amsa, shiru muka yi na wani ɗan lokaci, shi ne ya katse mana shirun cikin marairaicewa ya fara magana.
“Nayi fushi kanwata dama abin yar haka ne ko missed call dinki bana gani, wannan ya nuna bana ranki ko kaɗan kanwata, ko baki tambayi lafiyata ba ai kya kira ni ki tambayi yaranki ko?”
Cikin muryar tausayi kamar zanyi kuka nace
“Allah ya baka hakuri yayana wlh gaba ɗaya yanzu ba ni da wani ishashshan lokaci, amma kana raina kada kayi fushi da yar kanwar ka, ya aikin ya gida ina yarana?”
Siririyar ajiyar zuciya yayi
“Uhmm Sa’adatu kenan duk suna lafiya”
A hankali na sake tambayarsa
“To ina kawata ko Aunty Ruqayyah ma zan dinga ce mata?”
Siririyar dariya ya saki
“Ke dai kika sani wannan ai kun fi kusa, ko da yake yanzu mun fi kusa da ita, saura kaɗan ma ta dawo hannuna sai kin cike form xaki riƙa ganinta”
Da sauri nace
“A’a gaskiya ban yarda ba”
na faɗa ina mai jin dadin kalamansa.
Murmushi yayi
“Baza ki gane ba yarinya ni kin ƙi ma ki bari kiji abinda na bugo na faɗa miki”
A hankali nace
“To ina jinka yayana”
“Kiyi hakuri abin ne yazo min lokaci ɗaya, ban san biki ya matso haka ba, sai jiya Rukayya take faɗa min, dama so nake ki faɗawa Addah zan zo mu je da ke, ki zaɓi kayan da kike so na siya miki na aure tawa gudummar kenan”
Suman zaune nayi jina na wasu mintuna suka ɗauke, ji nake kamar ba da gaske yake ba
“Hello” ya faɗa
“Kina ji na kanwata?”
Cikin rawar murya na amsa
“Ina jinka yayana” ji nayi kuka na shirin kwace min.
A kasalance yace
“Aa kuka kuma zaki min kanwata? bama ‘yar haka fa da ke, kin xama jinina Sa’adatu duk abinda nayi miki ban yi asara ba, kece silar haɗa ni da macen da nake ganin xata xama gatana, zata bani farin cikin da na rasa a rayuwata, kin yi min komai Sa’adatu, duk abinda nayi miki ban yi asara ba”
A hankali nasa hannu na share hawayen da ke ƙoƙarin bata min fuskata.
“Na gode na gode yayana Allah ya raya zuri’a Allah yaji kan mahaifa”
na faɗa ina mai sake fashewa da wani sabon kukan”
Cike da damuwa yace
“Bari na kashe wayata idan kin gama kukan na sake kira, kin san bana jure zubar hawayen ki, idan da abinda na tsana shi ne naga idanun ki na xubda hawaye”
Da sauri ya kashe wayar.
Tashi nayi na fita ina zabgawa Addah kira da sauri ta fito muka haɗu a bakin kofar shiga dakinta, Allah ya tsare bamu yi karo ba.
Dubana Addah tayi “Menene Sa’adatu kike ta faman kirana haka”
ta faɗa tare da daura dankwalinta da ya kusa fad’uwa, a guje na faɗa jikinta ina dariya mai haɗe da kuka.
Muryata na rawa nace
“Dr ne Adda”
A hankali ta dube ni
“Ki faɗa min mana Sa’adatu me ya faru?”
Share hayawe nayi
“Addah wai cewa yayi na shirya gobe zai zo muje na zaɓi kayan dakin da zai siya min a matsayin gudunmawar sa”
Wani farin ciki ne ya lullube xuciyarta “Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah abin godia kai masha Allahu, Allah sarki wannan bawan Allah, Allah ya saka masa da alkhairi gaskiya doctor mai kaunar ki ne da gaskiya Allah ya biya shi da aljanna”
Wayar mijinta ta kira ta faɗa masa, shi ma ba ƙaramin farin ciki yayi da haka ba.A tsakar gida nake xaune ina gyara farcena, gefe guda kuma wayata na kunna ina sauraren karatun Kur’ani, kira’ar Sheikh Aliyu jabir, yana karatun ina bin sa, zuciyata fari tas take babu wani abu da ke damunta.
Daga cikin d’aki naji Adda na kwala min kira, ajiye kayan gyaran farcen nayi tare da shiga d’akinta. +
“Gani Adda”
Cikin nutsuwa ta dube ni.
“Kinga sa’adatu gani nayi ya kamata ki shirya ki je wajen yaya ki fada mata abin arxikin da doctor yayi mana, naga bai kamata mu ja baki mu yi shiru ba, kinga tana ta fadi tashin abinda xata samu dan asiri ya rufu bai kamata mu yi mata shiru ba”
To nace tare da mi’kewa dakina na shiga na canja kaya sannan na tafi gidanmu.
Cike da nutsuwa nake tafiya yau ji na nake a wani kasalance, kamar bana son taka kasa haka nake tafiya, kasancewar yau an tashi da matsananciyar rana ita ce ta kashe min dukkan gabobin jikina.
Kaina a sunkuye nake tafiya tare da kare fuskata da hannuna, nayi nisa da gida sosai bakin titi nake ƙoƙarin fita don samun dai-daita sahun da xai sada ni da gidan mu.
Ji nayi an sha gabana tare da kiran sunana cikin wata siririyar murya.
A firgice na d’ago, lokaci guda muka sauke ido a fuskar junanmu, takaitaccen murmushi ya sakar min wanda ya sanya kyawawan hakoransa bayyana. Saurin sunkuyar da kaina nayi sbd ban san da wane irin ido xan kalle shi ba.
kiran sunana yayi, tare da kura min manyan Idanunsa.
Lokaci guda na tsinci kaina cikin jin matsananciyar kunyarsa da nauyinsa, ji nayi ina ma ƙasa ta tsage na shige cikinta, don ban taɓa tsammanin xan haɗu da shi a irin wannan lokacin ba, nayi tunanin har abada baxan sake ganin shi ba, nadama ce ta bayyana a fuskata da kyar na iya bude baki na amsa da “Na’am, ina wuni mu’allim”
Yar siririyar dariya ya saki.
“Yau na zama sirikinki ne Sa’adatu ki saki ranki mu yi magana, dama ina ta addu’a Allah ya nuna min ranar da xan ganki na faɗa miki abinda ke raina”
Saurin d’agowa nayi na kalle shi.
“Menene a ranka, da har kake so ka ganni ka faɗa min?”
Gyara tsayuwa yayi gami da sanya hannun shi cikn aljihu
” Na tsorata ki ko sa’ar mata?”
Ya faɗa tare da kafe ni da manyan idanunsa.
Girgiza kai nayi alamar a’a
A hankali ya cigaba da magana.
“Tun bayan rabuwata da ke na shiga cikin matsanancin tashin hankali da damuwa, amma da na du’kufa da addu’a sai Allah ya sanya min nutsuwa, tsanar da nayi miki ta bar xuciyata, na koma jinki a raina tamkar yar uwata ta jini, tabbas dole na shiga damuwa sbd na rasa mace mafi sa’a nutsuwa da hankali, amma bayan nayi naxari sai na gano cewa duk abinda bai
zo hannuna ba, to ba rabona bane, da a ce na sameki na san nafi kowane namiji sa’ar abokiyar rayuwa, amma a rayuwa kana nake ne Allah na nashi, kuma matar mutum kabarin shi,, Allah bai yarda xamu rayu a inuwa ɗaya ba muna matsayin ma’aurata, ina sonki Sa’adatu xan kuma kasance cikin sonki har abada, albishir dina a gare ki shi ne ki saki ranki kada ki riƙa ji a ranki, kamar kin yaudari wani mutun a rayuwar ki, kisa a ranki Allah ne bai yarda xan aure ki ba ina yi miki fatan alkhairi”
Sauke doguwar ajiyar zuciya nayi a sanyaye na d’ago ido na kalle shi.
“Na gode da ka fahimce ni mu’allim, wlh kullum da kai nake kwana a raina, ina tunanin halin da na jefa ka a ciki, a kullum ina addu’a a kan Allah ya ganar da kai cewa ban yaudare ka ba, yau dai Allah ya amsa addu’ata na gode da soyayyar ka gare ni”
Na ƙarasa maganar ina mai sunkuyar da kaina ƙasa.
Dan murmushi yayi
“Kada ki damu Sa’adatu, ni ɗan uwanki ne mai son cigabanki, tabbas na san izuddeen ya fi dace wa da ke, shi ya fi cancanta ya aureki, don haka ina yi muku fatan alkhairi Allah ya baku xaman lafiya”
Amsawa nayi da ameen
Wani abu ya miko min a leda.
“Karbi wannan gudunmawa ta ce, na dade ina yawo da ita duk inda xani da ita nake tafiya, burina kawai na ganki ko naga wanda ya sanki, don na bashi ya kawo miki”
A ladabce na sa hannu na karba tare da yi masa godiya, sallama yayi min yana tafe yana waigena tare da yi min sallamar ban kwana.
Jikina a sanyaye naja kafa na nufi gidanmu,a soro na tarar da innah Salamatu da wani makocin mu salele mai dalilin aure, tana ganina ta sha jinin jikinta, sallama nayi musu jiki a sanyaye ya amsa min ita kuwa bi na tayi da wata muguwar harara, ko da na gaisheta bata amsa min ba, sai shi ne ya amsa. ina bada baya naji tana faɗa masa wata magana. +
Yi maza mu gama magana na koma gida naji abinda munafukar yarinyar nan taxo da shi, kaga wannan da kake gani ba yar arxiki bace, da ita da uwarta su suka yi asiri suka hana yayana aure, dan Allah ga hotunan su nan ka bada himma ka samo musu miji, a kwanakin nan da suka rage nake so a yi bakin su tare da ita, bana so ta tafi ta bar su.
Gyaran murya yayi
“Ai kuwa Hajiya kin kawo kuka inda za a share miki, akwai wani dattijon mai kuɗi a garin nan da yake neman matar aure, a cikin sati ɗaya yace min na nemo masa matar aure ko nawa ne xai kashe matuƙar dai xata amince da shi, dama ina ta tunanin yarinyar da za a haɗa shi da ita, kin san kuma wani abin daɗin Hajiya ita kadai xata xauna ba kishiya duk matansa basa nan sun fita sbd mugun halin su”
Da sauri ta tari numfashinsa tana murmushi
“Kai Alhamdulillah haka nake so salele shi yasa nake ji kai, dan Allah a yi masa magana ni nafi damuwa da lamarin A’isha ita ce wannan ɗan tsibbun ya sako ta a gaba, bana so aikinsa yayi tasiri a kansa nafi so na gaggauta na aurar da ita ko xai hakura ya kyaleta”
Cike da mamaki ya dubeta.
“Ai kuwa kiyi gaggawar aurar da ita, don malam jibo ba shi da sanyi indai ya so samun abu to fa ba makawa sai ya same shi”
Hankali a tashe ta kuma cewa
“Ni dai ka taimaka salele, wai ya ma sunan wanda yace ka samo masa matar auren?”
Ta faɗa tare da bayar da hankalinta gare shi.
Sunanshi Alhaji yawale mai gyada, na san kina da labarinsa irin tarin dukiyar da Allah ya bashi, don duk garin nan babu wanda bai san shi ba”
Girgiza kai tayi, cikin farin ciki take masa magana.
“Ai kuwa da alama xai yi saki don naji ance yana da mugun kuɗi, kuma ni abinda ya ƙara burge ni da shi ita kadai xata xauna babu kishiya, kaga duk gidan nan ba tada Sa’a kenan”
Murmushi yayi
“Sosai ma kuwa ke dai kiyi addu’a Allah yasa tayi masa”
Murmushi tayi
“Xata yi masa ma ai A’isha akwai kyau da kwalliya dole tayi masa, mummuna ma ta samu mai sonta ballantana kuma kyakkyawa”
“Haka ne Hajiya”
Sallama suka yi, sai da ta bashi dubu biyu wadda xai saka kati a waya da kuma kuɗin motar zirga-zirga.
Saka kaina nayi na shiga cikin gida xuciyata cike da fargabar irin mijin da A’isha xata aura, don har gara ta auri malam Jibo a kan dai ta auri yawale mai gyada, bai san komai ba banda auri saki ya’ya ne dashi sun fi talatin, kowanne uwarsa daban, bai san cin su ba bai san shan su ba, haka ya’yan suke kara xube tamkar marasa galihu, ga duka da cin mutuncin mata da yake yi wannan dalilin yasa babu matar da take iya zama da shi, sannan kuma gidansa babu abinci ba suttura, uwa uba kuma ga dukan mace da yake yi, matuƙar mace ta samu ciki ticket din xamanta a gidansa ya kare, wannan dalilin yasa ya tara ya’ya da yawa, kowanne uwarsa daban. Amma son xuciya irinta Innah Salamatu duk bata gano wannan matsalar tasa ba sai murna da take yi xata aurar da yarta.
Dakin Innah na shiga sallah na tarar tana yi don haka na nemi guri na xauna.A hankali ta juyo ta dube ni tana mai yin murmushi.
“Sannu da gida innah” na faɗa tare da ƙarasa wa kusa da ita.
Cikin sakin fuska ta amsa min.
Ledar kayan na miƙa mata.
“Innah kin ga abinda wani malamin mu ya bani kyauta” +
Hannu ta miko na bata kayan, a hankali ta shiga buɗewa.
“Masha Allah, Allah ya saka masa da alkhairi”
Da ameen na amsa
“Alkur’ani ne da sallaya a ciki, sai kuma wata yar ƙaramar envelop a gefe, a hankali ta buɗe kuɗi ne a ciki naira dubu biyar, tausayin mu’allim ne ya kama ni na san ba ƙaramin ƙarfin hali yayi ba, wajen bani kuɗin nan duba da yanayin da ake ciki na rashin kudi, kuma har yanzu bai samu babban aiki ba, sosai Inna take saka masa albarka ina amsawa da ameen.
Juyowa tayi ta dube ni
“Me kike ganin za a yi da kuɗin Sa’adatu?”
Cike da ladabi nace
“Ki bar shi Innah, kiyi wata buƙatar da su, ke da kike da hidima a gabanki”
“Allah yayi miki albarka Sa’adatu” ta faɗa tare da shafa kaina.
Labarin nauyin da doctor ya ɗauke mana na shiga bata, ba ƙaramin farin ciki tayi da hakan ba, a ranar ban dad’e ba na koma gida sbd mai gyara min jiki xata zo.
Washe gari muka tafi da doctor da Rukayya muka siyo dukkan kayan da ake buƙata, ba ƙananan kudi ya kashe min ba abin dai sai wanda ya gani, izuddeen kuwa ya gama tsara gidan sa, don su Adda sun je sun gano har sun fara yin jere, na tabbatar duk wanda baya kaunata idan yaje gidana yaga irin duniyar da aka shirya min ranar baxai iya bacci ba.
********
Kwana ki na ta shud’ewa kullum lokacin biki sake ‘karato wa yake yi, don yau kwanaki goma ne kaɗai suka rage, innah da Adda saratu sun bada himma sosai wajen gyaran min jikina, tun daga kan gyaran fata har zuwa gyaran ciki, ba karamin kyau nayi ba, idan ka kalle ni sai kayi da gaske zaka gane ni, saboda wani irin kyau da nayi na amsa sunana n amarya, nayi kyau sosai kamar ba ni bace Sa’adatun da ba, kallon fuskata na shiga yi a mudubi cikin xuciyata nake yaba ƙoƙarin da mai gyaran jikin ke yi a kaina, kawai sai na tsinci kaina cikin sakin wani kayataccen murmushi, saboda yau izuddeen dina zai zo, na san matuƙar yayi tozali da ni ba ƙaramin farin ciki zai yi ba, don rabon da ya ganni an kusa kwana goma, saboda yanayin aikinsa, gyara fuskata na shiga yi wani kayataccen les na saka sky blue, mayafin da na yafa ma sky blue din ne, na feshe dukkan ilahirin jikina da turare mai kamshi, sake kallon fuskata nayi cikin zuciyata na furta, Allah sarki abin sona na san yana ganina xan sanya shi shiga wani yanayi, na faɗa tare da yin murmushi.
Wayata naji tana ringing mai daɗi saboda sauti na musamman na saka wa number shi duk lokacin da naji irin wannan ringing din na san mai kirana.
A nutse na ɗauki wayar na karata a kunnena
“Amincin Allah ya tabbata a gare ki raina na ƙaraso kiyi sauri ki fito ina da buƙatar ganin kyakykyawar fuskar ki”
Yana gama faɗa ya kashe wayar bai jira amsar da xan bashi ba.
A hanzarce na karawa jikina turare, na fito duk inda na tsaya sai na bar record ɗin kamshi, ga wanda ake min amfani da shi a gyaran jiki, ga kuma wanda na ƙara xubawa jikina, ƙarasa wa dakin Adda nayi, tare da leka kaina cikin dakinta.
“Addah zan je yazo” na faɗa ina ƙoƙarin kwasar kujerun da xamu xauna a kansu.
“ki gaida shi” tace min
A nutse nake tafiya ina taku mai cike da nutsuwa da jan hankali
Cikin sassarfa ya taho yana sakar min kyakkyawan murmushi kamar zai rungume ni, saurin kaucewa nayi
A marairaice ya ƙaraso wajena tare da tsayawa dab da ni, cikin kasalalliyar murya yace
“Kada ki hana ni Sa’adatu kefa tawa ce”
Murmushi nayi kaɗan.
“Saurin me kake yi haka an kusa fa saura kadan kayi hakuri lokacin ka ya kusa”
Komawa yayi ya jingina kansa da kyauran soron.
“Baza ki gane yadda nake ji a kanki bane, bazan iya jure rashinki ba sa’ar mata kin gama da ni wlh ina sonki sosai, amma na hakura kamar yadda kika ce saura kaɗan idan kika shigo hannuna xaki gane”
Kasa nayi da kaina ban iya bashi amsa ba, kafe nayi yayi da ido
“Me yasa baki ce komai ba sa’ar mata?”
A hankali na d’ago tare da sauke ajiyar zuciya.
“Kanka dai kawai ka sani amma ka san ni kaina bazan iya rayuwa ba, matuƙar bana tare da kai”
Marairaice fuska nayi cikin sigar shagwaba nace +
“uhm uhm ko ma fa gaisawa bamu yi ba”
Ɗan murmushi ya saki tare da jan hancina.
“Ai laifinki ne kece duk kika wani ruda ni, tunda nake ban taɓa jin wani abu a kanki ba irin wanda naji yau ba, gaskiya wannan mai gyaran jikin ko nawa ne zan biyata ta ƙara fito min da ke amaryata, kinga yadda kika zama kuwa, tabarakallah Masha Allah”
Ya faɗa tare da lumshe manyan idanunsa.
Hannuwana nasa na rufe fuskata ina dariya kasa-kasa mamaki nake yi a raina, ko yaushe izuddeen ya xama mara kunya haka, ko da wasa a da baya kawo min irin wannan maganar, amma tunda yaga auren mu ya matso hirar shi bata wuce irin wannan.
Sake kallona yayi
“To ya shirye-shirye da fatan dai komai yana tafiya dai-dai”
Kaina a sunkuye na amsa da
“Alhamdulillah”
A hankali ya janyo kujerar da na ajiye masa ya zauna.
“Dama nazo ne naji wane irin shirye shirye ku ka tsara zaku yi ke da kawayen ki”
Cikin nutsuwa nace
“Ni gaskiya walima kawai zan yi bana son dinner din nan da ake yi, sai kuma yinin da su innah zasu yi ya isa”
Tsare ni yayi da ido
“Tabdi ashe akwai rigima kenan, baki isa ba wlh dinner zamu yi, abokaina na wajen aiki ma sun haɗa mana dinner kuma ban isa nace baza a yi ba, kinga dole ki jingine wannan ra’ayin naki a bi nawa”
A shagwabe nace
“Amma kasan….”
Kafin na ƙarasa ya dakatar da ni
“Ba fa zan ji komai ba kawai ki zama cikin shiri ni har na gama buga IV kinga ba fashi kenan”
Ganin yaƙi sauka daga kan ra’ayinsa ne yasa na amsa da
“To shikenan Allah yasa a yi taro lafiya a gama lafiya”
“Ameen” ya faɗa yana mai miko min wata leda
“Wanan shi ne invitation card din ki fara rabawa kawayan ki sannan kuma akwai kuɗi a ciki kiyi amfani da su wajen walimar taki, kayan da zamu yi amfani da su an tanadar mana komai lokaci kawai ake jira”
A ladabce na karba
“Na gode Allah ya saka da alkhairi”
“Ba komai Sa’adatu zan yi komai don naga na faranta miki, kin yi min halacci”
murmushi nayi wanda ya sanya hakorana bayyana
“Ai ni ya fi can-canta na fadi haka, kaine kayi min halacci kuma baxan manta da abinda kayi min ba har abada fatana na riƙa faranta maka a kowane lokaci”
Bai ce min komai ba sai murmushi da yayi tare da sake matsowa daf da ni, ina jin saukar numfashinsa a fuskata.
“Wai ma saura kwana nawa mu mallaki junanmu?”
ya fada yana leka fuskata, hannu na d’aga masa ina dariya cikin sigar tsokana nace
“saura kwana goma sha biyar”
Harara ya sakar min
“kaji muguwa zata ƙara min kwana ki, idan suka kai kwana goma sha biyar ai sai na mutu”
ya faɗa yana alamar kamar zai yi kuka.
Dariya ce ta kama ni, cike da zaulaya nace
“Duk hakurin da kayi a baya bai sa ka mutu ba sai yanzu da aski yaxo gaban goshi”
Girgiza min kai yayi
“Ke yarinya ce baxa ki gane ba, ni har kin fara bata min rai ma tunda haka ne xan wuce na kyale ki, tunda bakya sona”A marairaice nace
“Sorry my lovely husband baxan sake faɗa ba, ina sonka kuma muna tare har abada”
Murmushi yayi
“To shikenan zan tafi Sa’adatu kinga gobe zan koma wajan aiki, bai zama lallai mu ƙara haɗuwa ba sbd yanayin aikina, ina jin sai ranar daurin aure, sbd ana i gobe daurin aure zan taho da yan office din mu, Kinga baxai yiwu nazo wajenki ba, kada ki damu zamu riƙa waya kuma duk abinda kike buƙata ki gaya min zan sa a kawo miki”
Hawaye naji na ƙoƙarin fito min
“Yanzu baxan sake ganinka ba har sai ranar daurin aure ni Allah ban yarda ba”
Lallabani ya shiga yi har sai da na hakura.
“Allah ya kaika lafiya ya dawo min da kai lafiya Allah ya tsare min kai Allah ya sanya alkhairi a cikin rayuwar auran mu”
Sauke ajiyar zuciya yayi
“Ameen na gode mace ta gari
Ki gaida mutan gidan”
A haka muka yi sallama cikin kewar junanmu.