TSANANI
CHAPTER 4
Tun lokacin da innah salamatu ta je gidan su Izuddeen Mama bata ƙara samun kwanciyar hankali ba kullum a cikin tunanin yadda zata bullowa al’amarin take yi, ga shi ta kasa fadawa kowa kuma ta kasa tunkarar Izuddeen da maganar, ita kaɗai ta bar abin a ranta yana yi mata yawo, saboda har yanzu hankalinta ya kasa kwanciya a kan gaskiya ta faɗa mata ko akasin haka
Yau dai ta yanke shawarar faɗa masa ko zata ji sanyi a ranta, tashi tayi da kanta ta nufi dakinsa, sai dai tayi rashin Sa’a baya nan dakin nasa a kulle, dawowa cikin gida tayi sannan ta ɗauki waya ta kira shi cewa tana kiransa da gaggawa.
Yayi nisa da gida amma haka ya daure ya juyo saboda yadda mama ta jaddada masa cewa tana son ganinsa da gaggawa. Gabansa ne ya riƙa faduwa Allah yasa dai alkhairi ne yasa ta kira shi don tunda suke bata taɓa yi masa irin wannan kiran ba.
A daki ya sameta tayi tagumi tana tunani, har yayi sallama bata san ya shigo ba sai a karo na biyu da ya sake yi sannan ta san da shigowarsa, cike da mamaki ya karasa wajenta tare da xama a ƙaramar kujerar da ke gefenta, fuskarsa bayyane da damuwa”mama lafiya yau na ganki a irin wannan halin me yake damunki? tunda nake ban taɓa ganin damuwa a bayyane a fuskar ki ba irin yau, ga shi kuma naga kina min kiran gaggawa Allah yasa dai lafiya
Mayar da ajiyar zuciya tayi.
“Zan iya cewa lafiya amma ba lafiya ba, amma muna fatan Allah ya tabbatar da lafiyar zuwa nan gaba, Allah ya kawo mafita ya nuna mana gaskiya a kan tunanin da muke yi”
Cikin kulawa ya amsa da “Ameen amma ban fahimci maganganun ki ba Mama”.
Murmushi tayi “zaka fahimta ne ɗana ka bari xan faɗa maka komai”
Shiru suka yi na wani dan lokaci sannan tace.
“Abinda yasa na kiraka matsala ce dangane da kai kuma ina so ta xama sirri tsakanina da kai, don bana so kowa yaji abinda ke tsakanin mu, amma kuma ina rokonka ka fada min gaskiyar abinda ka sani kada ka munafunce ni”
Jikin Izuddeen ne ya dau rawa “wani abin aka ce nayi mama” jinjina kai tayi “Baka yi komai ba amma dai ana zargin ka aikata, don haka ka kwantar da hankalinka ba wani abin damuwa bane”
Gabansa ne yake ta dukan uku-uku jira kawai yake ya ji abinda zata fada, “ina saurarenki mama wlh na kosa naji laifin da nayi miki”
“Dama daga gidansu yarinyar da kake nema ne…….” gabansa ne ya yanke ya fadi dama tunda yaga matar nan da wayar da ya bawa Sa’adatu a hannunta ya san wani abin ne ya kawo ta addu’a yake yi a zuciyarsa Allah yasa dai ba cewa aka yi an raba shi da ita ba, da sauri yace
“wani abin aka ce nayi mama?”
Dakatar da shi tayi “A’a ka tsaya ka saurare ni mana” hankalin shi ya bata gaba ɗaya yana saurarenta.
“Ta zo ta faɗa min cewa yarinyar da kake nema ba yarinyar kirki bace, bin maxa take sanadiyyar hakan ta xubar da ciki ba adadi, Sannan kaima kuma tana ƙoƙarin janye hankalinka kuna lalata da juna saboda daɗin abinda take maka ne yasa ka bata kyautar waya ka ganta nan ma a hannuna
Miƙa masa wayar tayi ya gani sannan ta mayar da ita gefenta sannan ta cigaba da magana. “wannan dalilin yasa taxo da kanta ta sanar mana gudun kada mu yi kitso da kwarkwata” kafin ta kammala fada idanun Izuddeen yayi jawur kamar zai yi kuka, yanzu Sa’adatun tasa nutsatstsiyar yarinya kamila za a jefa da wannan kalmar, yarinyar da bata san komai ba sama da ibada da xuwa makaranta, bai san lokacin da ya sawa mama kuka ba.
“wlh Mama duk abubuwan nan da ake fada sharri aka yi min, kuma ita ma yarinyar sharri aka yi mata, Sa’adatun da take kamila za a jefa da wannan kalmar sannan nima a yi min sharri, wlh ban yafewa matar nan ba Allah ya bi min hakkina, don ta zubar min da mutuncina a idonki” cike da kulawa ta fara yi masa magana “Ni fa dama ban yarda da abinda take fada ba kawai dai na ji ta ne, sbd har cewa tayi kaje ka nemi ɗaya daga cikin ƴaƴanta kaga ya tabbata auren yarinyar ne bata so shi yasa taxo ta kulla wannan sharrin, dalilin da yasa na same ka kenan na fada maka yadda muka yi da ita, don mu warware bakin xaren kaga bai kamata na yanke hukunci a bisa rashin sani ba, nice mahaifiyar ka Izuddeen nafi kowa sanin halinka, gaba daya ban yarda da abinda ta fada min ba, ka kwantar da hankalinka xan fadawa babanka a je a bincika a tabbatar da gaskiyar abinda take fada”
Izuddeen ya dade a xaune bai tashi ba yana kukan takaicin jifansa da aka yi da zina, shi da ko hannun mace bai taɓa tabawa ba shi xa a yiwa kazafin zina, ya ji xafin abinda matar nan tayi masa kuma ya dauri aniyar duk lokacin da ya gano ko wace ce ita, sai ya ɗauki matakin Shari’a a kanta
Bayan ya tashi daga dakin Mama gidan su Rukayya ya wuce, yaro ya aika ya kirata a tsakar gida ya sameta tana tankade, cike da nutsuwa yaron ya fada mata cewa ana sallama da ita,tayi mamakin jin ana sallama da ita saboda ta san mai sonta baya nan da yake ba a gari yake aiki ba, kuma indai zai zo sai ya sanar mata.
Hijabinta ta saka tare da leka kanta dakin umma “umma ana kirana a kofar gida zan leka naji mai kirana” amsa min tayi da to
Leka kainta tayi kafin ta fita, hango Izuddeen tayi jingine da machine dinsa, yana ganinta ya taho da sauri da ganinsa yaƙe yake don ga damuwa nan bayyane a fuskarsa.
Cikin sakin fuska ta karɓe shi tare da cewa.
“yau kuma an tuna da ni kenan xiyara aka kawo min” a gintse ya amsa mata da “eh ai girmanki ne ranki ya dade” shigo da shi soro tayi tare da cewa “bari na samo maka abin zama” bai musa mata ba ta shiga gida ta dakko masa farar kujera ajiye masa tayi sannan ta nemi gefe ta zauna tana fuskantar sa.
yadda taga fuskarsa ba walwala ne yasa ta fahimci yana cikin damuwa.
Sun ɗauki lokaci mai dan tsawo kafin kowa yace da dan uwansa wani abu, ita ce tayi ƙarfin halin yin magana.
“Daga wajen kawar tawa kake ne ka biyo ka gaishe ni” ta ƙarasa maganar tana ɗan murmushi.
Ajiyar zuciya yayi tare da cewa “Daga gida nake na shigo wajenki ne don ki ɗan ƙara min haske game da abinda yake damuna” cikin mamaki tace
“to!!! Me kuma ya faru da kai mijin kawata?” Kafin ya faɗa mata abinda ya faru idanunsa sun yi ja kamar zai yi hawaye, sai da zuciyarsa ta ɗan yi sanyi sannan ya kwashe dukkan abinda ya gudana tsakaninsa da Mama ya faɗa mata
Tunda ta ji inda maganar ta dosa ta gano makircin innah salamatu ne, don sun ji lokacin da take fadawa Baba dawowar ta daga gidan su Izuddeen.
Girgiza kai kawai Rukayya take yi ta rasa bakin magana sai can tace “bazan boye maka dukkan irin rayuwar da Sa’adatu take yi a gidan su ba, xan iya cewa rayuwa ce irin ta tatsuniyar yar mowa da yar bora, tsananin tsana da kiyayya kishiyar mahaifiyarta da yayanta suke mata wacce ba tada asali ballantana toshe, kuma ita ce taje gidanku ta kulla wannan sharrin, hatta abinda Baban Sa’adatu yayi maka ranar da kaje wajenta duk da sa hannunta, na san ka fahimci abubuwa da yawa a ɗan xuwan da kake yi, xaka san cewa Sa’adatu da mahaifiyarta rayuwar hakuri suke yi, kada kayi mamakin dukkan abinda zasu faɗa a kanta zasu iya fadin abinda ya fi haka ma, tunda babu soyayyarta a zuciyarsu da suna da hali da tuni sun koreta daga gidan ita da mahaifiyarta, fatana a gare ka shi ne ka bincika komai kafin ka yanke hukunci, na san ba kai tsaye kaxo kace kana son Sa’adatu ba sai da ka binciki dabiunta kafin kace kana sonta, ka kwantar da hankalin ka a kan abinda aka faɗa maka, kayi naxari sosai kafin ka yanke hukunci”
numfashi mai zafi Izuddeen ya fitar daga bakinsa “nima ba cewa nayi na yarda ba kawai naxo na tambaye ki ne sbd abin ya daure min kai na san wannan duk ba halinta bane, kuma ba Sa’adatu kadai abin ya taɓa ba har da ni, tunda gashi nima tace min lalata nake yi da ita, sauki ɗaya na samu da iyayena suka kasance mutane masu nazari da tunani, da wasu ne da tuni ba wannan zancen ake yi ba, amma xan bincika iyayena ma xasu taya ni mu gano bakin xaren, bana so bikinmu ya dauki wani lokaci saboda mu yi maganin makiyan mu” +
Rukayya taji dadin maganganun Izuddeen musamman da yace ya yarda da kawarta, kuma za su yi aure nan ba da jimawa ba, sun ɗan yi hira kadan sannan ya tashi ya tafi.
bata iya shiga gida ba gidan su Sa’adatu ta zarce, a soro na biyu ta tarar da taron mutane kanta ta tambaya ko me yake faruwa a gidan haka, danna kanta tayi cikin gidan tare da cire takalminta kasancewar baxa ta iya wucewa da takalmi ba saboda shimfidar da aka yi.
Wata magana ta ji ana yi wacce ta daki kunneta kamar saukar aradu taji an fadi wani abu, da sauri ta juyo ta tsaya gefe don sauraren abinda suke tattaunawa, kamar daga sama taji an ce…………….Magana ta ji ana yi ƙasa-ƙasa har bata iya jin abinda suke fada saboda ta fuskanci kamar tattaunawar sirri suke yi shi yasa basa so wani ya fahimci abinda suke cewa, ƙara bada hankalinta gare su tayi don a yadda taji salon zancen kamar maganar Sa’adatu ake yi, don ta ji kusan duk kalmar da xa a fada sai an ambaci sunan Sa’adatu, kuma dama tunda ta ga wannan tarin jama’ar ta san an taru ne saboda ita.
Ji tayi an kwalawa Sa’adatun kira, cikin mintunan da basu wuce biyu ba ta gabata a gaban taron jama’ar da suka haɗu sbd ita. +
A ladabce ta gaishe su, amma ga mamakin Rukayya bata ji sun amsa ba, wani dattijo taji ya fara magana “yanzu dan Allah wannan hanyar da kika dakko mai bullewa ce kuwa, kina ganin hanya ce da zata sadaki da tafarkin tsira, kina yarinya yar asali mutuniyar kirki yar mutanen kirki xaki bata rawarki da tsalle, xaki daka ta yaro ɗan masu kuɗi ki lalace iskancin naki har ya kai ki fara kawo shi gida yana abin kunya da ke, naga alama so kike kiyi cikin shege ko? to mu hakan baxai faru da zuri’ar mu ba, yanxu xamu yi maganin abin, amma kai kayi ganganci tun farko malam yarinya kamar wannan shekara sha tara baka aurar da ita ba ai dole haka ta afku, idan ma miji ta rasa me xai hana mu baxa kayi mana magana mu kawo mata ba, sai ka kyale yan iska su lalata maka ita”
Neman yawu nayi na rasa a bakina kululin baƙin ciki ya toshe min makoshina, duk da cewa ana dan sanyi amma haka naji xufa na yanko min, yanzu a ce duk jama’ar nan saboda ni suka taru? Kannen kakana ne da suke xaune a wani kauye da ake kira Bankaura, ina kyautata zaton jiya Baba ya je ya sanar da su Wannan sharrin da ake kulla min, shi ne yau suka zo ku san su goma duk a kan maganata
Ita ma Rukayya da ke soro irin halin da ta tsinci kanta kenan, jiri ta ji na shirin dibanta don haka ta nemi waje ta tsugunna.
Wajen ne yayi shiru kowa na sauraren bayanin Baba musa, sai da ya gama magana tsaf Baba ya karbe shi.
“Ni fa dama Baba na dade ina xargin Sa’adatu da wannan aikin saboda a lokuta da dama ina ganinta da abubuwan da ba ni na siya mata ba, kuma mahaifiyarta ma ba tada kudin siya mata, amma ko menene ita uwar ke bata goyon baya salamatu na iya kokari wajen kula da tarbiyyar ta sai take ganin kamar takura mata take yi, ina rokonku dan Allah ku tafi da ita Bankauran ta xauna a can ko zata ƙara hankali, sannan kafin nan da sati biyu xan turo mijin da na bayar da ita sadaka a daura musu aure kowa ya huta”
Hawaye masu xafi suka riƙa sauka a kan kuncina, wace irin rayuwa ake so nayi a kauye? Tunda nake ban taɓa sati guda a can ba sannan yanxu dare daya a ce can xan koma da rayuwa, wane hali innah xata shiga idan na tafi na barta, kawai niyyar kashe ni ake yi da raina
Da farin ciki ɗaya kanin kakan nawa ya amsa “kwarai kuwa kayi tunani malam Salisu can din ne gatanta kuma shi ne ya fi dacewa da ita, dama an ce duk wanda ya bar gida gida ya barshi, taje can ta shiga cikin yan uwanta tayi aiki, a haka ma xata koyi wasu sana’o’in tunda duk yan uwanta noma suke yi ita ma ya kamata ta shiga ciki tayi tarayya da su”
Gaba daya suka amince da komawata Bankaura, cikin fushi Baba yace na tashi na hado kayana, da gudu na shiga daki ina kuka, tambayata innah take yi dalilin kukana amma na kasa bata amsa saboda takaicin shekara da shekaru da ya cika xuciyata, ita ma ganin halin da nake ciki ne ya sanya ta kuka, innah salamatu ce ta dage mana labule tare da cewa “tafiya dole a yi ta, baxa mu xauna da yar iska a cikin gidan mu ba”
Sai a lokacin innah ta gano dalilin kukana tambayata ta shiga yi
“Sa’adatu kokar ki malam yayi daga gidan nan ko kuma me”??? +
Hawayen da ya cika idona na share “cewa yayi sai na bi su Baba musa Bankaura wai baxan xauna masa a gida na lalace ba”
Kwalla ce ta cika idon innah
“Allah sarki rayuwa Allah kaine Allah, ka saka mana wannan cutar da ake mana” kafin innah ta rufe baki har Baba ya shigo dakin cike da fushi yake mata magana.
“Munafuka wato kin sakata a gaba kina kitsa mata sharri ko, na lura da ke duk dokar da xan yi a cikin gidan nan sai kin rusata, ke dama kike goya mata baya har ta lalacewa, idan har kika bari ta dakko min abin kunya wlh kin gama xaman gidan nan, kuma xuwan Sa’adatu Bankaura ya xama dole saboda ‘yata ce ba ‘yarki ba ina da iko da ita, ki taka a hankali kafin na ci miki xarafi”
Mayar da kallonsa yayi gare ni “ke tashi ki dakko kayanki kafin nayi ƙasa-kasa da ke” A sanyaye na tashi na nufi inda jakar kayana take, a hankali nake xakulo su kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.
Sake daka min tsawa yayi “za kiyi aiki da jikinki ko sai naxo nan” kayana kala uku na dauka na xuba a leda, tankada ni waje yayi tare da cewa “shege mu je ja’ira” har na bar daki innah na sunkuye tana kuka, nima kukan nake har na fita ina waiwayenta.
A soro na biyu na tarar da su sun yi cirko-cirko suna jirana, idona a rufe na fita xuwa soron farko ji nayi an riko hannuna a hankali na bude idona, Rukayya na gani ta sha kuka har ta gaji, cikin kukan take min magana “wlh kada ki bi su Sa’adatu ki gudu, babu alheri a ransu neman ruguza miki rayuwa suke yi”
Daga soron Baba ya jiyota, ita ma cin mutunci yayi mata ba shiri ta tafi gida tana ta rusa uban kuka
A dai-daita sahu aka kawo mana don xuwa tasha, ni na fara hawa sannan sauran kakannin nawa suka bi bayana, babu wanda ya rarrashe ni ballantana na sa ran za a bani hakuri ko za a ji tausayina zuwa gaba.
Har muka isa tasha abinda nake yi kenan, sauke kayana nayi na samu gefe na tsaya, su kuwa sun kafa min ido kamar masu gadina, fakar idonsu nayi na ajiye kayan a kan wata mota, ina lura da basa kallona na gudu na bar musu kayan a wajen, gudu nake cin karfina ban san ina na nufa ba ni kaina.Gudu nake cin karfina kamar zan tashi sama burina kawai na bace daga inda suke, Mutane sai bi na da kallon mamaki suke sbd ganin budurwa kamata na gudu abin mamakin ne, har sai da naga nayi nisa da su sosai sannan na samu nutsuwa, tsayawa nayi don na huta, a bakin wata bishiya na zauna ina ta maida numfashi, sai da na dawo na huta sosai sannan na ci-gaba da tafiya, nayi tunanin na gudu gidan wata kakata kanwar Baba tunda tana sona sosai na san xata rufa min asiri, amma sai fasa sbd idan suka bincika zasu iya gano ni a can, yanke shawarar tafiya gidan kanwar innah nayi Adda saratu, ban bata lokaci ba na kama hanyar tafiya gidanta. +
***********
A ɓangaren kannen kakan Sa’adatu kuwa basu ankara bata nan ba sai da aka zo shiga mota, ɗaya daga cikin su ne ya lura da bacewar ta, a firgice ya dubi ragowar yan uwan tafiyar tasa “yarinyar nan fa bata nan kamar gudu tayi”
Da sauri suka baxu a cikin tashar kowa yana duba inda Sa’adatu ta shiga, ga mamakinsu sam basu ganta ba hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, a tunaninsu ko gida ta koma abinka da mutanen karkara duk cikinsu babu mai waya ballantana su kira gidansu su ji ko nan ta dawo, haka suka hakura suka ƙara koma gidan su Sa’adatu ko xasu sameta
A Kofar gida suka ci karo da mahaifinta kallon mamaki ya bi su da shi gami da mikewa tsaye yana tambayarsu “Baba lafiya naga kun dawo?” Girgiza kai dattijon yayi “Hmmm Salisu yarinyar nan sai ta Allah kawai, don duk inda kake neman shu’uma ta kai, sai da ta san yadda tayi ta gudu sannan hankalinta ya kwanta, a gaskiya kayi sakaci da tarbiyyar yarka, tunda ta saba da yawo zai yi wuya ko aure tayi ta zauna”
Dafe kai mahaifin Sa’adatu yayi wani gumin tashin hankali ne ya riƙa yanko masa, cikin sarkewar harshe yake magana “ko ma menene uwarta ce ta fara jawowa ita ce ta dorata a tafarkin da take yanxu, sannan wannan kawar tata ita ma ta taimaka wajen lalacewar ta shi ma saurayin haka”
jajanta masa suka riƙa yi ko gidan basu sake shiga ba suka kama hanyar ƙauyen su.
A fusace ya shiga gida tun daga soro yake kwalawa innar Sa’adatu kira mutanen gidan na jin irin kiran da yake yi mata suka fito saboda sun san ci mata mutunci zai yi, cikin kakkausar murya ya fara magana
“Burinki na son lalacewar Sa’adatu ya cika kin hure mata kunne ta bi saurayi yawon iskanci, dokar da na saka kin karyata, duk shirina a kan yarinyar nan kin xuga min, tunda haka kika zaba mu zuba, a cikin minti biyu nake so ki tattara kayanki ki bar min gidana idan kinga kin xauna a gidan nan sai dai idan tare da Sa’a ku ka dawo”
jikin innah a sanyaye ta miƙe ta shiga haɗa kayanta ita abin yayi mata dad’i dama ta gaji da wannan zaman kaskancin da take yi, kullum cikin xagi da cin zarafi, yanzu fargabarta ɗaya bata san inda yarta take ba, ta san Sa’adatu da kamun kai baxa tayi wani abu da zai xubar mata da mutuncinta ba amma duk da haka tana jin ba daɗi a ranta saboda sharrin xamani.
Mutanen gidan sai murna suke suna ta habaici Sa’adatu ta tafi yawon iskanci. Innah salamatu ke cewa
“Yadda kika fita kin fita kenan ba dawowa mun ci gida ni da yayana” ko kallonta innah bata yi ba ta fice ta kyale su
A soro taci karo da salim, har ƙasa ya tsugunna ya gaidata cikin farin ciki ta amsa, tambayarta ya hau yi “ina zuwa innah na ganki da kaya haka” labarin abinda ya faru da Sa’adatu ta bashi, ransa yayi matuƙar ɓaci, hakuri ya riƙa bawa innah kada ta saka damuwar hakan a ranta wata rana komai xai wuce, ɗari biyu ya bata yace ta hau mota.
A fusace ya shiga cikin gidan, innah salamatu na ganinsa ta hau magana “yauwa Gara da Allah ya kawo ka, ana yi maka gata ana raba ka da yar iskar yarinyar nan kana nacewa to gashi nan dai yanzu ta gudu”
Ba ƙaramin zafin maganar innah salamatu yaji ba, salim yaro ne mai tarbiyya baya yiwa manya rashin kunya amma yau tunda ta tsokano shi sai ya mayar mata da martani cikin fushi yake mata magana “ina ruwan ki dani indai kin san irin wannan maganar xaki rika fada kada ki sake yi min magana Sa’adatu yar uwata ce ta fi ki kusa da ni, duk rintsi duk wuya dole a ce kanwata ce, don haka sai na damu da dukkan halin da take ciki, duk ba ku kuka tunxarata ta aikata abinda ta aikata yanzu ba, kun hanata abinci kun hanata walwala kun hanata wanda take so, kun jefeta da zina wanda ina da yakinin duk tafi yayanku tarbiyya, sannan sbd zalunci yanxu kun dauke ta kun ce sai kun mayar da ita kauye, ya ku ke so tayi da rayuwarta, shi kenan so kuke yi ta zauna ku kasheta da baƙin ciki” +
Dakinsa ya wuce ya kyaleta ta saki baki tana mamakin maganganun salim, tanbayar kanta take yaushe yaron nan yayi baki haka?? Lallai idan ba su yi taka tsantsan ba wata rana zai kwance musu aiki
Dakinsa ya shiga yana xuwa ya faɗa kan ƙaramar katifarsa, kwanciyar rigingine yayi yana tunanin rayuwar Sa’adatu, yayi alkawarin indai yana doran ƙasa baxai bari ta tagayyara ba.
Shi kuwa baban Sa’adatu tun bayan fitar innah daga gidan shima ya fita, bai xarce ko ina ba sai gidan su Izuddeen, a Kofar gida ya same shi tare da abokansa suna hira bai lura da xuwansa ba sai kawai ji yayi an shako shi ta baya, cike da mamaki ya juya don ganin wanda ya riƙe shi haka.
Baban Sa’adatu ya gani yana yi masa kallo mai cike da tsana, a ladabce yace “lafiya Baba??” Wani kallo yayi masa tare da cewa “lafiyar kenan, ina ka boye min yata, ka fito min da Sa’adatu ?”
A razane yace “ban gane Abinda kake nufi ba”
“Zaka san baka gane abinda nake nufi ba idan ka ji ka a hannun hukuma” abokan Izuddeen ne suka fara tambayar baban Sa’adatu “malam mai ya faru haka kaxo ka shake shi, a matsayinka na babban mutum ai bai kamata ka kama shi da kokawa ba, tunda a haife ka haife shi” cika shi yayi yana haki “wannan yaron da ku ke gani azzalumi ne ya lalata min ‘ya sannan yanzu ya hure mata kunne ta gudu watakila ma shi ne ya boye ta” kallon kallo suka hau yi kowa yana mamakin abinda yake faɗa, kasa magana suka yi sbd maganar ta daure musu kai, mayar da kallonsu ga Izuddeen suka yi
“Gaskiya ne abinda ya faɗa?”
Shi kuma saboda takaici ya kasa magana sai dai ja da idanunsa suka yi, sai da ya gama tijara sannan ya tafi ya kyale su, binsa suka yi da kallo har ya kule.
Komawa suka yi suka zauna suna tambayar Izuddeen “menene alaƙarka da wannan mutumin ɗan tijara , gashi ya xo har kofar gida xai zubar maka da mutunci”
Labarin soyayyarsu da Sa’adatu ya hau basu dukkansu sun fahimci halin mahaifin nata, kuma sun gano cewa ba kaunar yar tasa yake yi ba, gaba daya suka shiga gida suka shaidawa Mama yadda suka yi da malam Salisu, ba ƙaramin takaici taji ba saboda abinda yayi masa, a wannan lokacin ta tashi ta shiga wajen mahaifin Izuddeen ta shaida masa abinda ke faruwa, tunda dama ya san Izuddeen na san yar aurensu da yarinyar, shi ma ransa ya ɓaci sosai, sa wa yayi aka kira shi ya tambaye shi yadda suka yi.
Cike da tausasawa da kamala yake magana.
“Faɗa min gaskiyar abinda ya haɗa ka da wannan mutumin, bana so ka rage min komai kuma bana so kayi min karya” kan Izuddeen a sunkuye ya fara magana.
“Wlh Baba tun bayan korar da yayi min daga gidan sa ban sake komawa ba, kuma bana waya da yarsa hasali ma na cireta daga rayuwata, yanzu kuma kawai ina zaune sai yaxo ya shake ni wai na fito masa da yarsa da na boye, kuma ko abokaina za a tambaya babu macen da take shigo min dakina ku ma nasan zaku yi min wannan shaidar”Shiru mahaifinsa yayi yana nazarin maganganunsa, “tashi kaje xan sake neman ka” +
Cike da ladabi ya tashi fitarsa kofar gida kenan yaga Baban Sa’adatu tare da yan sanda, yana ganinsu ya tsaya don ya san bakinsa ne, suna karasowa ya nuna shi, tafiya suka yi da shi sauran abokansa ne suka je gida suka faɗa an tafi da Izuddeen, ana tafiya da shi suka bi bayansa su da ragowar yayan gidansu.Bayan an kai Izuddeen police station tafiya Baban Sa’adatu yayi ya kyale shi, tare da alkawarin kada a sake shi har sai ya fito masa da yarsa, ko da yan uwan su Izuddeen suka je duk iya bakin ƙoƙarin da suka yi don ganin an bada belinsa hakan ya gagara sbd dole sai babanta yana nan xa a kashe case din, haka suka taho suka kyale shi ba da don ransu ya so ba.
Tunda ya bar police station bai xame ko ina ba sai gidansu Rukayya a kulle ya tarar da kofar gidan, wani irin bugun rashin mutunci ya riƙa yi, ummansu ce ta fito da kanta ta bude don ganin mai bugun, bata yi mamakin ganinsa a wannan yanayin ba, don ta san ko wanene malam Salisu kuma ta san kalar tijararsa baya ragawa kowa wannan dalilin yasa da yawan makota basa shiga harkarsa duk abinda zai yi sai dai su zuba masa ido. +
Fuskarta a daure take tambayarsa “lafiya dai ko malam?” Shi ma a yatsine ya amsa mata “ina ‘yata da ku ka boye min?” cikin rashin fahimtar abinda yake nufi ta sake tambayarsa “Ban gane abinda kake nufi ba yi min dalla dalla yadda zan fahimta” gyara tsayuwa yayi “ina yarki Rukayya ita ce ta xuga min yata ta gudu ta bar gida ki fada mata wlh ta fadi inda Sa’adatu take ko kuma hukuma ta raba mu” wani kallo umma ta jefa masa wanda sai da ya shiga hankalinsa “Rukayya ba tada hannu wajen batan Sa’adatu mugun halinka da masifarka ita ta tunxurata ta gudu, kaje ka fara tuhumar kanka da matarka kafin ka tuhumi wasu, duk halin da yarka ta samu kanta a ciki kai ka fara jefata don haka kanka zaka zarga ba wasu ba” tana gama faɗar haka ta mayar da kofarta ta kulle ta bar shi tsaye yana naxari.
Gida ya koma yana ta masifa innah salamatu ce ta tarbe shi tana tambayarsa ko lafiya, faɗa mata yadda suka yi da Izuddeen da kuma mahaifiyar Rukayya yayi, zuga shi ta hau yi a kan kada ya yarda ya dauki mataki ta kuma bashi shawarar tafiya wajen Malam Jibo a kan yaxo a daura aure ko bata nan, in yaso idan ta dawo sai a kaita.
Yaji dadin wannan zugar da tayi masa, a nan take ya tashi ya nufi wajensa.
Tun a hanya yake ta tunanin Sa’adatu ya san dukkan halin da ya jefata a ciki shi ne sila amma ko kadan baya nadamar hakan sbd an riga an dasa masa tsanar yarinyar a xuciyarsa, kai tsaye makarantar sa ya wuce sai kuma bai same shi a can ba, don haka kai tsaye ya wuce gidansa, a soro ya same yana lazimi bari yayi ya ƙarasa sannan suka gaisa.
Cikin karamci ya karɓe shi tare da shigar da shi shagon da ke soro sbd yadda ya ganshi ya san tattaunawar sirri ce ta kawo shi.
Zaunawa suka yi suna fuskantar juna kafin Baban Sa’adatu yayi magana Malam Jibo yace “ina muka kwana a maganar mu?” Cikin nuna tsananin damuwa yace “wlh Malam ina shirye-shiryen zuwa na sameka a kan maganar kwatsam shekaran jiya ta gudu” dafe kirji yayi “Ta gudu fa kace subhanallahi ya aka yi haka ta faru” jinjina kai yayi “Hudubar saurayi ce ta hure mata kunne shi ya yaudareta ya tunxurata ta gudu”
Shiru malam Jibo yayi yana tunani “To ai malam kai kayi sanya wajen tabbatuwar Maganar nan tun lokacin da ka same ni da maganar ya kamata a ce kayi wani abu amma kayi banxa da abin idan nayi maka magana sai kace zaka neme ni”
Mayar da ajiyar zuciya yayi “akasi aka samu malam kamar dauke min hankalina aka yi a kan maganar, ka gyara inda zaka ajiyeta na baka ita sadaka kada kayi lefe kada kayi komai sadaki ma na yafe maka xan bata dan wani abin idan ka shirya kayi min magana, gobe ko jibi nake so a daura aure” yana gama maganar ya tashi. wani dadi ne ya sauka a zuciyar malam Jibo Allah ya bashi kifi daga sama gasashshe, yarinya kamar Sa’adatu ai abin alfaharinsa ne a ce ya aureta, godiya yayi masa har kofar gida ya rako shi suna ta tattauna maganar.
Har ya juya xai tafi ya sake juyowa “Au malam na manta ban fada maka ba” mayar da kallonsa yayi gare shi tare da cewa “ina jinka”
“Kada ka manta Sa’adatu ta ba yarinyar kirki bace ta riga ta saba da yawo banxa kana ganin xata iya xaman aure da kai?”
Wani murmushi malam Jibo yayi “Ba matsala don ka samu mafita aka yi auren nan ko?? To Sa’adatu ta shigo hannun da babu rabuwa har abada sai dai mutuwa, ko nan da can bata isa ta je ba sai dai idan ni na bata izni xata xauna tayi ibada kamar yadda kowacce mace take yi ka kwantar da hankalin ka
Ba ƙaramin dadin maganar yaji ba yana farin ciki ya nufi gida don sanarwa innah salamatu.