TSINTAR AYA BY

BILLY GALADANCHI

Duk yawan mutanen dake bayansa suna k’ok’arin ganin sun take gabansa da bayansa hakan yaci tura, sabida yanayin sauri da Hamood keyi, saurin kuwa tamkar ze tashi sama haka yakeji, sabida lokaci zuwa lokaci yakan wurga kallonsa zuwaga agogon hannun sa yana me k’ara sarrafa k’afafunsa zuwa ga d’an sassarfa, tafiya dabata wuce ta mintuna uku ba ya sauya akalar k’afan nashi daga sassarfa zuwa d’an gudu lokaci d’aya yana tattare hannayen rigar sa zuwa sama. Mabiyan nasa ma gudun suka soma tamkar wasu zararraru haka suka dawo acikin fadar kowa se kallon su yake ido k’asa sabida sunsan halin Hamood yanzun nan zece kana kallon sa kai munafiki ne. A sukwane suka k’arasa cikin fadar, a tsaitsaye ya taradda d’aukacin dattawan fadar da kuma  masu babban muk’ami acikin fadar kamar su waziri,sarkin yak’i, Magatakarda da sauransu.Dukkansu sunyi layi gefe da gefe sunbar fili a tsakiyar su inda dagacen zaka hango me martaba a zaune saman wata kujerar mulki ta alfarma wacce aka k’era da zallan ruwan zinariya rubuce a saman ta an rubuta Daulatul Dinar! Be wani b’ata lokaci ba wurin k’arasawa kusa da me martaba lokaci d’aya ya sunkuya yana nuna alamar gaisuwa amma bakinsa be motsa ba babu kuma alamun ze motsa d’in! Kallon k’ur me martaba ke masa na wani lokaci yayinda wasu lafiyayyaun mintuna goma suka wuce amma har lokacin Hammood be gayar da Mahaifin nasa ba! gyaran murya murya Me martaba yayi inda sabo ya saba da halin Hamood d’in, wasu ‘yan dak’ik’un seconds suka shud’e kafin yace.

“Hammood Menene dalilinka na kawo ‘yan mata acikin fada? kana sani kuwa cewa hakan babban laifine da wannan masarautar bazata iya gafarta maka akanshi ba!Idan kana wajen masarautar kayi abinda kakeso mahaliccinka na kallon ka. Amma anan bazamu lamunta ba, sabida haka daga yau karna kumajin makamanciyar wannan halin a fadar nan” Shiru wurin ya d’auka na wuccin gadi, tsakanin mintuna da dak’ik’u an samu shud’ewar kusan minti talatin amma be motsa ba be d’ago kansa ba bakuma ze motsa d’inba kamar yanda koda ba gaskiya bane baze tab’a iya musawa ba. Shirun dayayi yawa ne ya sanya Me martaba cewa dashi

“You are dismiss” Be jira komai ba a sukwane ya mik’e tare da k’ara sauke kai k’asa alamun girmamawa sannan ya juya a hanzarce kamar yanda yazo yana shirin barin wurin kusa da galadima ya tsaya suka kalli juna, lokaci d’aya galadima ya d’auke kansa shikuwa seda ya gama k’are masa kallo sannan ya wuce cikin hanzari.

     zuwa wannan lokacin gudu yakeyi amma idansa duka biyu a rufe yake, yayinda mabiyansa ke biye dashi cikin tashin hankali. Timing dama yake sabida haka adaidai sanda ya iso inda yakeson tsayawa sekuwa ya tsaya d’in yana mayarda numfarfashi sama sama, Babban cikin mabiyansa ya kalla sannan ya d’aga hannu ya masa nuni da cewar ya bashi biro da paper. Atake jikin su duka ya mutu dan kuwa sunsan an tsokano musu yau, a hanzarce ya rubuta

“Nextweek” ya mik’awa mutumin shikuwa jikinsa har rawa yake ya wurgawa takardan kallon baya ya karb’a sannan yace yana russunawa

“Sun dad’e sosai suna jiranka yallab’ai, dan Allah a dubawa uzurin su” Lumshe idansa yayi sannan ya bud’esu ya zuba tas akan mutumin sannan ya kuma yi masa nuni da biro da paper, da hanzari ya k’ara mik’o masa matsakaiciyar Joter…

“Kainane yake ciwo, kayi musu dukkanin abinda ya dace ka bani bayani a rubuce, kada ka manta ina kallon komai”

“Nagode da wannan karamcin yallab’ai, i will send ur doc right away” Murmushin gefen baki ya sakar masa sannan yad’anje baya da baya da gudu kafin ya juya ya runtuma aguje sekace wanda yake gasan tsere!
   K’ofar part d’in nasa da kanshi ya bud’e ya shiga ciki, ma’aikatan dake gyaran k’asa ya tsaya ya k’urewa kallo sosai dukkanininsu sesuka zube suna kawo gaisuwa dukda yake sun tabbatar da cewar bawai ze tab’a amsa gaisuwar tasu bane, Lumshe idansa yayi sanda standing AC dake parlorn ya watso masa wani had’add’en sanyi da k’amshi sannan ya zube hannayensa duka a aljihun sa ya haura saman batare dayace dasu ci kanku ba. Yara ‘yan mata biyu dake k’ok’arin gyaran b’angaren basusan da zuwan saba kwata kwata, wannan ya sanya me ‘yan shekarun aciki take nunawa k’aramar wani hoto

“kalli da kyau ki gani Amina, yana magana fa, ba abinda ya iya se tsagwaran iskanci, amma mu sekace ba matan ba ya iya sha mana mur, kalli dai a hoton nan yanda ya rungune wannan macen sekace matarsa, uban kowa kuma yasan cewar be tab’a aure ba, haka zezo da mata da maza acikin gidan nan ayita sowa aci asha amma dazaran ya fito seki nemi koda murmushi a fuskar sa ki rasa tsinanne” k’aramar ciki ce ta karb’a da cewa

“Lallai ma, inatajin labarin mutumin nan, masarautar nan kowa ya bud’i baki prince Mood dai prince Mood, nina zata wani kamilalle ne ashe aminin shed’an ne” Dariya dukkansu sukayi kafin suka tafa suna shewa. Tamkar beji me sukace ba haka ya wuce batare dayace dasu kanzil.ba ya shiga bedroom dayake mallakin sa a part d’in. Sosai ganinsa ya firgita k’aramar harta riga babbar zubewa tana k’ok’arin gayar dashi muryanta yanata faman rawa, For the very first time ya waigo ya k’arewa dukkansu kallo, suna tsugune dazaka saurara a wannan a lokacin dakaji yanda cikin kowaccen su yake bada sauti k’uuuu alamun cewar tabbas k’ir suke jira su b’arke da zawo! batare daya ce dasu kanzil ba ya shiga d’aki abunsa, Babbar ce ta soma mik’ewa

“kurma ne dama kamar yanda akace uwarsa ma kurma ce, ni tunda nake dashi bantab’ajin maganar saba” Kallon ta Amina tayi

“Amma yanajin duk abinda ake cewa, cutar kurumtar ce dai ban saniba ko tabbas ce danko yanzu indai ba kurman bane ya dace yaji me muke cewa akanshi” Dariya siririya Babbar tayi sannan tace

“Ni idan naga ire iren hotunan nan a part d’in san nan se inga kamar tas yakejin komai damuke cewa, amma idan muna zaginsa ya kamamu kuma baice komai ba se inga kamar tabbas bayaji d’in,to amma fa komai a rubuce yake bayar dashi, idan an masa magana seya baka amsa a rubuce kinga dai inhar yana fahimtar maganar ka toko tabbas yana jin magana ba kurma bane” Cigaba da goge gogen da take tayi kafin tace

“Koma dai yanaji ko bayaji kanshi akeji, ni gwarama da naya magana akan wancen D’an galidaman me kafirin girman kan tsiya sarakan iya zagi” haka sukayita tsigarar wanda basaso har xuwa lokacin sa suka kammala ayyukansu tatas.


Wayarsa dake kusa dashi ya janyo ya soma k'ok'arin aika sak'o kamar yanda yakeyi kullum sabida baya magana, yajima sosai rik'e da wayar a hannunsa yana aika sak'on shima kuma ana dawo masa dashi, rayuwar tana masa tsananin zafi zuciyar sa tana masa suya, mesa kowa baya sansa ne wai? me yayiwa mutane? akwai wani aibune a tattare dashi? waya matsawa a rayuwa? shidai gani yayi bako magana yake ba bare ace yana shiga harkar mutane, abinda Me martaba ya gaya masa ya tabbatar cewar galadima ne ya k'ulla masa wannan sharrin, kodai London ze koma ne? idan yabar musu garin yana ganin hakan shine mafi, A'ala agareshi kawai, amma ya zeyi da Mamin sa? ko duniya ze tara akanta ya tabbatar bazata tab'a bari  ya k'ara d'agawa agarin ba, shiyaya zeyi? Kwanciya yayi a hankali yabi lafiyar  lallausan katifar dake kan gadon ya kwanta tare da lumshe idansa, abubuwa da dama suke masa yawo akai, zabura yayi sannan ya zari wayarsa kamar ko yaushe da sassarfa yabar d'akin nashi zuwa k'asa kafin daga bisani yabar cikin gidan ma gaba d'aya da k'afarsa cikin sassarfa. Track suit ne ajikinsa kalar baki me ratsin ja da alamar mark ajiki me nuni da cewar kai tsaye kayan na k'irar kampanin Nike ne, Yanayi irin na zafi ya haddasa masa had'a uban gumi musamman dayake har yanzu gudu yake irin na masu motsa jiki, yayi tafiyar nisan zango dan kuwa har yaje ya zago ya dawo gaba d'aya, hankalin sane yakaishi akan matashiyar yarinyar daya gani xaune a gindin wata bishiyar baobab dake gefen wani gidan, tun sanda yabi ya wuce yaganta a wurin ga magarib tanayi yaya zata zauna a k'ark'ashin bishiyar kuka? wannan layin ba layi bane da mutane suke binsa shi kanshi dayake namiji kok'ari yake yaga cewar ya isa gida kafin sakkowar dubuwar daren nan to ita me take anan? dukda kanta acikin k'afafunta yake bawai yaga fuskarta bane ba amma ya tabbatar cewar yarinya ce k'arama sosai to menene haka kuma? tunawan da yayi cewan yanzu duniyar ba tabbas ya sanya ya d'auke kanshi daga dubanta kawai zuwa wani b'arin yaci gaba da gudunsa har zuwa lokacin daya isa masallacin k'ofar fada! Anan ya yada zango yayi alwala sanyin AC da fankar dake acikin masallacin sune suka busar dashi dankuwa duk tsananin gumin daya had'a tamkar gumin turare yakeyi, bebar masallacin ba seda ya sallaci isha kana ya d'aura da shafa'i da wutiri. Fitowar sa a masallacin yana k'ok'arin shiga cikin gidan seyaji zuciyar sa ta karkata akan son sanin halin da yarinyar cen take aciki, wani b'ari na zuciyar sa yana sanar dashi cewar tabbas yayi kuskure dabe ce tabar wurin ba amma shin ta iya karatu? 'yar bokoce? da wanne bakin ze mata magana? tunawa da hakan ne ya tilastashi jan burki zuwa shiga cikin gidan da sassarfa kamar ko yaushe, wata k'il Hamood yana ciwon dabaze iya tafiya bane a nutse kokuma hala aljanun gudu ne dashi dasam baze iya tafiya yanda kowa keyi ba se surfafa uban gudu. 

kamar kullum yauma aguje yashiga part d’in nasa dukda yake gudun dayake bawai wanda zesa kayi tunanin ana binsa abaya bane amma tabbas ko shakka babu gudun yakeyi, irin na maza majiya k’arfi wanda suke a murd’e tako ina! yauma kamar kullum yana jiwo surutun ma’aikatan sa suna gulmar sa amma ko kallon inda suke beyiba sabida bashida lokacin su ko kad’an shikam! a gurguje yayi wanka ya shirya tsaf tamkar wanda zeje club acikin k’ananun kaya harda facing cap ya mannawa idanshi farin gilashi k’al, ras dashi idan ka ganshi se tashin k’amshi yakeyi, zuciyar sa ba komai se tunanin waccen yarinyar ta k’asan bishiyar kuka anya kai yanzu ma ai ta tafi, ya furta bayan ya wurgawa agogon hannun sa kallo yaga k’arfe 8:30 ta buga hadda k’arin mintuna biyu! nisawa yayi sannan ya fice daga part d’in sedai wannan karon ba gudu yake ba Tafiya yakeyi tamkar wanda k’wai ya fashewa aciki!

Jikinta har rawa yakeyi sanda taga duhun yana yawa, babu abinda takeso illa taga wurgawar motar mominta, idan ta tsaya anan tabbas wani abu ze iya samunta sabida k'arfe takwas da rabi ya wuce abinda agogon wayarta ya iya nuna mata kenan,tafi gwammace dukan da Mommy sauda zata mata akan dai ace yau ta koma gidan ta tarar Bilal yana gidan, amma ganin lokaci ya tafi haka ya tilasta mata bin hanyar gidan cikin tsananin fad'uwar gaba da tashin hankali. Cikin sand'a ta tura gate d'in gidan ta shiga sannan a hanzarce ta lab'e bayan flower's dake gidan karaf taji an damk'o hannunta cikin ihu tace

“Wayyoo momy” Fizgota Bilal yayi yaja hannunta har cikin parlorn su, hijabin jikinta ya zare yana murmushi sannan yakai hannunsa yashafi k’irjinta. juyata yayi ta fuskanci gaba shikuma ya manna k’irjin sa asaman bayanta hannayensa suna kan nonuwan ta, hab’arsa ya d’aura akan wuyanta sannan yace

“Ke banza ce Hafsat, ke bakisan arzik’iba, yadai dace ki sani ni jibi zan koma makaranta kuma kota k’arfin tsiya sena biya buk’atana akanki, wannan karon idan kika ce zaki gudu bundigar dana nuna miki zan saka in harbeki sekin shek’a lahira wlh” Jikinta yana rawa tace

“Bilal dan Allah kaji tsoron Allah, ka taimakeni ban maka komai ba ni marainiya ce kada ka lalatamun rayuwa” Zip d’in rigarta ya zuge ya zame har k’asa sannan yana dariyar mugunta yakai hannun sa ya b’alle botirin rigar mamanta, da lalubo ya shafko nonuwan ta,lumshe idansa yayi sannan yace cikin wani sauti “Asshhh shhhiiii, Haba Hafsat, tayaya zan rayu ban moreki ba, taya wannan lallausan maman naki zan bari su kufce a hannuna ban moresu ba, hak’uri kawai zakiyi” Runtse idan ta tayi ta soma ambatar sunan Allah a hankali, horn da aka rangad’a a bakin gate na gidan alamar dake nuni da cewar tabbas matar gidan ta iso shine ya tilastawa Bilal sakin Hafsat, cikin tsawa yace

“Tattare kayanki dan kutumar ubanki kije d’aki, ko alama na gani dake nuni da cewar na miki wani abu a fuskarki sena wulak’antaki wlh, oya now” Jikinta yana b’ari ta d’auki hijabinta da sauran rigarta tayi hanyar d’akin daya mallakin ta, rufe kanta tayi ta suturta jikinta kan nononta da Bilal ya matsa yana mata tsananin zogi sabida zuwan period d’inta, jitake inama k’asa ya bud’e ta shiga tsabar bak’in ciki, itama ace tanada dangi masu kirki, inama ace ita Hafsat a nemi wani a k’auye a had’ata aure dashi ta dena ganin Bilal, data huta data huta da wannan kayan bak’in cikin datake kwasa a rayuwa!


 Daga bakin gate kuwa Bilal ne ya bud'ewa hajiyar sa k'ofa ta shigo da mota, a small parking lot dabaze wuce d'aukar mota biyu ba tayi parking tuleliyar Lexus d'in ta fara k'al C350 model, kafin ta fito a motar bayan tayi parking ta zuge glass ta zube idanta a kansa, shikuwa cikin sassarfa yazo wurinta suka kafe juna da ido, dan kishingid'a  tayi ajikin sit na motar cikin wata murya tace

“Malam Garba fa? har yau basu dawo ba kuma bakuyi waya ba” Sosa kansa yayi sannan yace

“Nakira su d’azu yace dani se gobe zasu dawo” Nisawa tayi sannan tace tana kafeshi da ido

“Bilal Nagaji, tausa nakeso, da wannan abin yau kuma sune suka motsa, acikin bayan motar nan akwai gasassun kaji hud’u, na k’aramar leda sune na ‘yar shara, sauran namune yau kaza nakeso kaci nikuma in fanshe ajikin ka” Murmushi yayi

“Momy aiko baki bani kaza ba se yanda kikayi dani, ni nakine momy aurema se idan kin yadda zanyi” Yamutse fuska tayi

“Bilal banason shiririta wane irin aure kuma? aure kam aiba yanzu ba seka k’ara girma tukunna” Murmushi yayi bece komai ba

“Ka nutsu kasan me kake karnajika da shirmen ‘yan mata, maida aure banan kusa ba, idan bakayi sallah ba kaje kayi dan yanzu nake buk’atar ganinka a b’angare na” To yace cikin girmamawa sannan ya kwashi kayan zuwa cikin gida….

Yar shara kuwa bayan ta karb’i Namanta a hannun Momy umarni aka bata akan karta kuskura ta k’ara fitowa waje se washe gari, haka nan ake rufeta ata wajen d’akin ta tanaji tana gani…… Lokacin dabefi sa’a d’aya ba kawai ta soma jiyo kururuwar muryan momy dana Bilal da irin wannan Shiiii Aaaa dayake mata duk sanda yake yagalgalarta, tunda su Baba Lami sujayi tafiya take cikin wannan halin, tagaji da wannan ihun, tagaji da wannan halin anya bazata gayawa Baba Lami ba kuwa, anya shirun nan zeyi kuwa, Momy da Bilal lalata sukeyi ita ta sani mesa momy zatayiwa su Baba Ladi haka, mesa zata zalunci ubangijinta akan me zata b’ata yaro k’arami? Sautin ihun su yana k’aruwa takai yatsunta duka biyu masu zaman manunai ta toshe kunnuwanta bazata iyaba inama zata iya kawar da kanta akan wannan bak’ar rayuwar? shin dabata hutaba wai, kai bazata shiru ba tabbas idan ta gayawa Baba Lami gaskia itama zata iya kub’uta a hannun Bilal, tabbas zata gaya mata cewan shida Momy lalata sukeyi.!!!!


 *Washe gari*

Bilal yana zaune da momy a parlor suna breakfast, wannan karon ‘yar sha tana jinsu, a tsammaninsu bata gane abinda suke fad’a amma sarai tana jinsu, mopping d’inta kawai takeyi, hajiyar ce tace

“Bilal naga jiya ka k’ara himma sosai, ban saniba ko hakan baya rasa nasaba da kudad’en dana kashe wurin mayar da tsohuwa yarinya” Murmushi yayi

“Kai sosai abubuwan suka k’ayatar jiya wlh, nayi matuk’ar jin dad’in komai da komai, gabaki d’ayan hanyar shiga garin seta matse sabida yawan mutane ga kuma tsantsin ruwan saman da aka lafta abin ba’a cewa komai” Dariya shak’iyanci tayi

“Ni karka saka na makara dan Allah, yaro k’arami dakai se iya zubo zance” Dariya sukayi a tare sannan suka mik’e dukkansu.

*** Su Baba Lami sun dawo, kuma lokaci d’aya ‘Yar sha tayi summoning courage na gayawa Baba Lami abinda takeda yak’inin shi yake faruwa, sedai kuma yanayin fuskar Baba Lami kad’ai ya isa ya nuna mata cewar ba’a karb’i maganar tata da muhimmanci ba! Isowar Momy gida keda wuya se kukan Baba Lami tajiyo a parlor

“Yanzu hajiya ace yarinyar dakika rik’a tsakani da Allah dukda abinda ubanta da uwarta suka aikata kika taimaketa da mugun sharrin dazata biki kenan? me kika tsare mata arayuwa? maganar bazan iya gaya miki itaba sabida nauyinta amma ita tazo ta maimaita da bakinta” Jikin ‘yar shara (Hafsat) ne ya fara rawa sosai sabida tsoro ta k’ure a toilet anata kiranta amma bata fitoba, seda momy taje ta fincikota sannan ta fito tanata zare ido, Baba Lami tace

“Ke ‘Yar sha maimaita abinda kikazo kika gayamun Hajiya da yaro sunayi agidan nan” Jikinta rawa yakeyi sosai yanzu kam har fitsari ya soma fito mata tace

“Baba Lami dan Allah ki rufamun asiri” Mari Baba Lami takai mata

“Na rufa miki asiri kamar yaya? kina neman tona mana asiri kice in rufe naki, kimga hajiya zuwa tayi tana gayamun waikeda yaro Lalata kukeyi kullum cikin dare nan yake kwana sanda bama nan” Da mamaki momy ta kalli’Yar sha sannan tace

“Hoo yaron zamani, Lallai na yarda duniya tayi gurb’acewar dabazata gyaruba sesa gyaran Allah, kokin san dabakwa nan bilal k’ararta ya kawomun, fita takeyi idan na fita na zaneta namata fad’a shine zaki dawo da sharrin akanmu? ko shakka banayi wannan yarinyar dalilin kenan dayasa mutan garinsu ma bame sonta, amma ni bazance miki komai ba, bari Bilal yazo ya maidaki garinku tunkan kinb’atan suna agari, aniyarki ta biki Yar shara” Haka suka tasata agaba da uwar Bilal da momy suka mata tatas!

 kuka ta kwanayi a wannan daren babu k'auk'autawa, washe gari bilal da duka ya tashi mata tamkar ze kashe ta, haka suka fita akan ze kaita garinsu insunso su kasheta, ita tasan cewar bilal baze barta ta rayu a farin cikiba, tanada yak'inin cewan abinda yakeso ajikimta baze hak'uraba harse ya karb'a.

DOWNLOAD COMPLETE BELOW ⬇️