UKU BALA’I CHAPTER 1
Www.bankinhausanovels.com.ng
Jikinta ba abin da yake yi sai rawa kamar wacce ake kaɗawa gangi, ko wacce ruwan sama yayi wa dan karan duka na kin karawa.
A hankali ta isa kofar dakin, kallo daya za ka yiwa fuskarta, ka tabbatar akwai kayan damuwa a tattare da ita. ba ma na damuwa kadai ba, har da na tashin hankali. idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir. kamar wacce kayi wa surace da hayaki kwalla sun cika su.
A hankali ta sa hannunta mai kyarma ta yaye labulan dakin, gami da sallama da fadawa cikinsa.
Goggo Marka dake zaune tana faman kaɗin zare. da sauri ta dago ta dubeta, cikin yatsine fuska da tukuicin harara, ta mai da kanta ga kaɗin ta. Mareeya dake tsaye cikin rawar jiki, ganin irin kallon da Marka tayi mata ya fadan mata da gaba, ta san dama a yi haka. harara da yatsinar fuska a wajan Goggo Marka tamkar a jininta yake, in dai ta zo wajanta sai tayi mata haka, ta rasa dalili? tunaninta dai ya tsaya a haka yanayinta yake. amma in tayi duba sai ta ga ita kadai da Ummarta take yi wa haka. nisawa tayi, a lokacin kwallar da ta taru mata a idanu ta zubo.
“Goggo. Umma ta ba ta da lafiya tun jiya da dadddare…”.
Wani kallo ta watso mata, kafin ta saki zaren kaɗin da take yi. ta zabga tagumi kamar wacce akayi wa mutuwa, ta kure Mareeya da kallo kafin ta numfasa.
“sai kuma aka ce maki don bata da lafiya ni ce zan bata lafiya ko?. wai ke Mareeya wacce irin dakikiyar yarinya ce? ke a kullum sai kin nuna duhun kai irin na uwarki da kakanninki. in dai za kiyi abu ko”.
Kwalla ta ciko mata, cikin nisawa.
“kiyi hakuri Goggo…”.
“…ke dalla rufe mani baki, kuma kiyi maza ki fice mani daga daki, kafin na tashi na mangare ki. ban za kawai, jikan yar masu duhun kai, kai jama’a! Allah ya wadaran naka yalalace. nikam! Marka ina ganin kuturun kinibibi wajan nan, yarinya ki marere ce sai faman ɓari kike, ke mai uwa, kin zo sanar dani bata da lafiya, ko uban me zan mata ban sanin miki ba”.
kara narkewa tayi, kamar zata zube mata a kasa. izuwa lokacin hawaye sun fara zubo mata, ta shiga hada hannayenta waje guda bakinta na rawa.
“Ki taimaka Goggo na rokek…”.
Mahucin da ke kusa da ita ta dauka ta cillo mata shi, bai dire a ko ina ba sai saitin bakinta, hakan ya sanyata gimtse sauran maganarta ta. jin zafi da tayi ya sanyata saurin kai hannu ta dafe bakin ta wani zugi da raɗaɗi take jin laɓɓanta sun dauka, kamar za su fice daga mazauninsu.
Da sauri ta juya ta fice daga cikin dakin, cikin yanayi na raɗaɗin zuci da na laɓɓa. ta rasa abin da tayi wa Goggo Marka, take nuna mata halin-ko-in-kula, ta rasa mai ta tare mata cikin duniyarta, ta rasa mai yasa ta ke nuna musu kiyayya ita da uwarta. tun da take da ita daidai da rana daya bata taba jin ta furta kalma daya akan taba ko uwarta, mai dauke da Alheri. kullum aikin ta kenan nemo inda aibu yak,e ta makalawa rayuwarsu. ita dai tunda ta taso ba ta ga uwarta na nunawa Goggo Marka, wani halin rashin girma ko na cin mutunci ba. kullum cikin biyayya da girmamwa take. amma duk wannan bai hana Goggo Marka ci mata mutunci ba a gaban kowa, ko da kuwa gaban Babanta ne.
Kuka takeyi wanda bashi da sauti ko kadan, illa hawaye da suke fitar burgu daga idanuwanta, tana faman dauke su amma kamar kara tunkudosu ake. tana jin zafin zuciya da yarda kasar ruhinta ke raɗaɗi, idanuwanta in da sabo ya ci ace sun saba da halin da Goggo Marka, ke nuna mata ita da uwarta.
A hankali ta karasa dakin mahaifiyarta. kafin ta shiga sai da ta dauke hawayen fuskarta kaf. domin bata bukatar mahaifiyarta ta taga halin da take ciki, hakan zai kara tayar mata da hankali sosai. kofi ta dauka bisa randar ruwan dake kofar dakin, ta debo ta wanke fuskarta, sannan ta sanya haɓar zaninta ta tsane fuskarta tas. amma hakan bai hana a gane tayi kuka ba, domin idanunta sun kaɗa sunyi jajir, murmushin yaƙe ta kalato ta yafawa fuskarta, sannan ta shiga cikin dakin bakinta dauke da sallama.
Tsaye ta hango uwarta ta, sai faman hada gumi take yi tana kai kawo. kallo daya zakayi mata ka tabbatar tana cikin matsanancin yanayi, lakari da yarda take cizon laɓɓanta kamar zata cizgesu daga mazaunansu. fuskarta ta rine tayi jajir abin ka da farar mace. kallo daya Mareeya tayi mata ta kau da kai, jin kuka na shirin kawo mata ziyara, zuciyarta ta shiga bugu. ta sani uwarta na cikin yanayi na matsaninin ciwo, amma ta rasa mai ya kamata tayi domin taimakon, ta a matsayinta na ‘yarta wacce ta haifa a cikinta. waje daya taje in da take tunanin za ta samu waraka, amma anyi mata korar kare tare da bakaken maganganu.
“Mareeya ya akayi na ganki haka, mai ya sameki?”.
Habeeba ce ta fadi haka, cikin karfin hali da na zuciya. sai faman numfarfashi take, gumi na cigaba da karyo mata, kamar wacce ake juyewa bokitin ruwa.
yanayin sautin muryar Habeeba da maganarta, ba karamar rauni suka kaiwa zuciyar Mareeya ba. ji take kamar ta rushe da kuka saboda tsananin tausayin uwarta. jin amonta ya tabbatar mata tana cikin wani mataki mai tsananin wahalar da rai da ruhi, ta sani uwarta tana hakuri tana da juriya, da alamun a wannan fikirar hakurinta da juriyarta ba za su samu muhallin zama ba.
Juyawa tayi, ta fuskanci mahaifiyarta sosai. tana faman gyaɗa kai cin yanayi na tausayawa.
“lura da nayi da halin da kike ciki, ya sanya ni zuwa neman wani taimako daga wajan Goggo. amma hakan bai samu ba”.
ta karashe tana goge hawayen da suka zubo mata, tana jin yarda zuciyarta da kasar ruhi ke tsalle-tsalle cikin yanayi na tausayi da neman wata hanya domin samun mafita.
Habeeba ta gyada kai, tana mai sakin murmushi wanda daka kalla zaka san na dole ne, ba wai don wani farinciki akayi sa ba ko na tsuwa. to ina ma natsuwar take wacce ta rigaya ta falle da gudu ta bar duniyarta.
“Hmmm Mareeya kenan. kuma don kin je ba ta aminta ba shine ki kayi kuka?”.
Ta karashe tana mai kafe da kodaddun idanuwanta, wanda suke cikin hali na rashin nutsuwa.
Girgiza kai Mareeya tayi kafin ta dubi uwarta ta, murya da salon rauni.
“Umma gani nayi ita ce kusa damu shiyasa na yi tunanin ita yafi dacewa aje wajanta, ba wai aje waje ba. kuma gata a cikin gida, sai nake tunanin in har aka je waje aka nemo a matsayinta na babba ba za ta ji dadi ba. ashe ba haka bin yake ba, tunani na daban da hasashena akanta”.
ta karashe cikin rawar murya, mai son fashewa da kuka. a daidai lokacin ta ga uwarta ta, ta saki wani nishi wanda ya taho da wasu tawagar hawaye, da hanzarinta ta isa gareta, ta riko mata hannu.
“Umma ko Asibiti zamu tafi, Umma ko naje na kira Baba ne?”.
Abin da ta shiga fadi kenan, cikin yanayi na bugun zuciya, mai tattare da tsoron halin da ta ga uwarta ta aciki. bata tanka mata ba, illa numfashi da take ta faman ajjewa. lokaci lokaci hannunta na kan turtsetsen cikinta, wanda take jin duk wani hali da take ciki na wahala shine sanadi. shine yake rangwantar mata da jarumtar ta, ya ke rangwantar mata da kumajinta, da duk wani azanci nata.
Girgiza kai ta shiga yi, alamun a,a ba sai ta je ba. hakan ya kara rudar da ‘yar natsuwar Mareeya, nan ta shiga girgiza kai, ita ma tana sakin nishi mai dauke da son fashewa da kuka.
“a,a Umma. karki ce haka don Allah, kina bukatar taimako a halin da kike ciki, don Allah ki yarda a nemo mai taimaka miki ko kuma mu tafi asbiti”..
Girgiza mata kai ta cigaba da yi, tana jin wani irin ciwo mai tsananin karya jarumtar numfashi na kawo mata farmaki, ji take kamar numfashin ta zai katse, duniyar taji ta shiga juya mata kamar zata jirkitar da ita, ba abin da take ambato a ranta da kasar ruhinta sai ‘Innalillahi wa inna ilahir raji’un’.
Hawaye suka shiga digo mata wanda take jin su kamar garwashin wuta ne ake goga mata a fuska, hannun Mareeya ta rike gam! kamar zata tsinke shi, ita kanta Mareeya taji rikon da uwarta ta tayi mata, sosai da sauri ta dago kai ta dubeta, idanuwanta sai hawaye da suke digo.
“Umma ki ce wani abu nasan kina jin zafin ciwo sosai, don Allah ki bani izinin zuwa nayi wani abu, rayuwarki tana da matukar muhimmanci a duniyata”.
Izuwa lokacin Habeeba hayyacinta ya fara raguwa da ga gareta, kafafunta da take kansu suke taimaka mata wajan tsayi, ji tayi suna karkarwa alamun sun fara gajiya da rikita.
Da sauri ta ja jiki zuwa kasa, tana dafa Mareeya ta zauna kan lamusshasshiyar katifar dake yashe tsakar dakin, har zuwa wannan lokaci idanuwanta a rufe suke, ita kadai ta san irin raɗaɗin azabar da take ji, ita kadai ta san irin zafin da take ji yana ziyarta ta.
ɗan dake cikinta tana jin yarda yake juyi cikin wani irin yanayi na hanzari, yana tunkuɗo mata gurbin zuciya, ji take kamar zai tarwatsa mata kirji, zillo yake yi ta ko ina yana bugun ko wani sashi na cikin ta, ba abin da take hasashowa kanta a wannan matakin sai ficewar rai, domin ta gama yarjewa zuciyarta SILAR AJALINTA ya zo cikin duniyarta, matakin daukewar numfashinta ya iso rayuwarta, barin duniyar rayuwarta cikin yan dakiku take hangowa, lahirarta tana yi mata maraba lale, duniyarta nayi mata ban kwana.
Wani zillo da taji ɗan cikin nata yayi, da sauri ta durkushe bisa gwuiwowinta, tana faman sakin wahalallan numfashi wanda take jin fitar sa ma, wani raɗaɗi yake haifar mata a ruhi.
Sake damke hannun Mareeya tayi, wacce a wannan lokacin hawaye kawai take saki, tana kallon yarda mahaifiyarta ke yi cikin wahalallan yanayi ba abin zuciyarta ke hasaso mata sai uwarta ta mutuwa zata yi.
“Umma sakar min hannu don Allah, naje na nemo mai taimaka miki kinji”.
ta fadi cikin murya mai dauke da rawa da kuka a jikinta, ta shiga faman jan hannunta, domin kwacewa amma ina!. rikon da tayi mata ba mai sauki bane, kuka ta saki sosai tana jinjiga uwarta ta, tana rokon ta da ta sake ta, domin zuwa kiran wani ya taimaka mata.
A hankali taji hannun uwarta ta na buɗewa daga rikon da tayi mata, cikin yanayi na rashin karfi jikin. sagalo tayi tana kallon hannun nata wanda cikin dakiku ta sakar mata shi, hakan ya kara mata jarumta, da sauri ta mike har tana cin tuntube zata zube kasa, ta fice daga cikin dakin. ba in da ta dosa sai dakin Goggo Marka, ko sallama ba tayi ba, ta fada dakin ta zube a gabanta, har wannan lokacin ta nan tana aikin ta na kaɗi. ganin Mareeya zube a gabanta ya sanyata tsayawa cak! da abin da take yi. tana dubanta cikin haushi ji take kamar ta kwasheta da mari, hannu ta shiga nuna mata.
“Mareeya so ki ke yi ki nakasta ni, zaki fado min kai haka kamar buhun maiwa”.
cikin kuka Mareeya ta dago kai, gami da riko kafafuwanta.
“kiyi wa Allah Goggo ki taimaki Ummata karta mutu, na roke ki”.
Fincike kafarta tayi, gami da mikewa tsaye tana gyara daurin zaninta.
“kar uwarki ta mutu ko? wai shin in naje ni zan hanata mutuwa, ko ce miki akayi ni ce mala’ikan daukar rai ga mutum, kisan Allah in har baki tashi kin fice daga cikin dakin nan ba sai na karyaki, banza ‘yar masu duhun kai”.
Kuka take yi na zuciya har izuwa kasan ruhi, ji take yi zuciyarta na raɗaɗi gami da zafi, idanuwanta suna zugi gami da zubda zafafan hawaye. jikinta na rawa da karkarwa duniya gabadaya taji tana kai kawo da ita, ba abin da take hasasowa sai yanayin da mahaifiyarta take ciki, ta tabbata a wannan yanayin da take ciki bashi da maraba da hanyar mutuwa, duk da dai ba ta san ya ake mutuwa ba, amma ta san hanyar mutuwa ba dadi gareta ba.
Mikewa tayi tana duban Goggo Marka cikin hawaye.
“Goggo na roki da Allah da Annabi ki taimaka ma Mahaifiyata. ina rokonki ko da wani abu tayi miki wanda kike ganin ba zai sa ki taimaka mata ba, to ina so duk wani hukuncin da zuciyarki ta yarje miki kiyi akan ta to ya komo kai na. ni dai alfarma nake nema ki taimaka mata ba don halinta ba”.
Sagalo tayi da baki tana kallonta, in ka ganta sai ka rantse tausayi da jin kai ne ya sanyata haka. amma saboda rashin sanin daraja sai ta sake kwaɓe baki gami da kau da kai.
“ina gani bariki yau, ke yanzu Mareeya har kin yi girman da zaki sakar min magana haka to bari kiji ko Malam Lamiɗo (tana nufin kakan Mareeya) bai isa ya zo ya sani abin da ban yi niyya ba, don haka maza ki tashi ki fice mani daga daki, tun kafin na yi kutubal dake”.
Hannu ta sa tana dauke hawayen da suke zubo mata, wasu na biyo bayan su tana kallon Goggo Marka kallo ne take yi mata na bakinciki, tausayi da imani sam babu su zuciyarta. gyada kai tayi tana nufi kofar ficewa daga cikin dakin, ba tare da ta sake kallon inda Goggo take a tsaye ba, ta yi sagalo sai faman watsa mata kallon banza take yi.
Zuciyarta tayi matukar yin baki gami da kuntata, zafin rai da take ji yana ziyartatta ya sanyata sakin wani kuka mai dauke da tashin hankali da takaici da baki ciki.
Tsakar gidan ta tsaya, ta durkushe tana faman rerashi wanda ba shi da sauti, in ba kana kusa da ita bane ba za ka taba gane kuka takeyi ba. ta jima durkushe a wajan, domin rashin abinyi gabadaya kwakwalwarta ta cushe, ta rasa ina zata dosa, ta rasa meye abin yi, za ta so ace asibiti suka tafi kila can su samu taimako, sai dai ba anan gizo ke saƙar tasa ba, domin zata iya ratsewa rabon da suga naira biyar cikin dakin su mallakinsu ko ta ajiya sun fi karfin mako daya, to ina batun in sukaje asibiti ta sani kudi za a nema kafin ma akula mahaifiyarta ta shi kuma mahaifinta ba ta san inda zata same shi ba, rabon ta dashi yau kusan kwana uku kenan. ba ta san gun wanda za ta ba, ba su da yan uwa nan kurkusa balle taje domin su share musu hawaye, ba dangi wanda za ta ce gashi anan kusa wanda zai taimaka musu, ba ta san kowa ba, ba ta san gun wanda zata je ba, tunaninta ya tsaya cak ba ta da wata mafita.
Kamar daga sama taji an dafa mata kafada, cikin hanzari ta dago fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye, mahaifinta ta gani wata irin zabura tayi, ta mike tana kallonsa. hannunsa ta rike jiki na rawa.
“Baba Ummata ka taimaka min, za ta mutu na roke ka”.
Yanayin da ya ganta ya san shi saurin riko mata kafadu yana girgizata.
“mai ya sameta, tana ina?”.
baki na rawa ta nuna masa daki. da hanzari ya nufi dakin yana mai rike da hannunta suka yi dakin. duk abin da suke yi Goggo Marka na kallo, tana laɓe jikin labulan dakin ta tun da taji muryar Adamu ta leko tana ganin sun shiga dakin, ta fito tana murmushi ita ma dakin ta nufa, cikin hanzari yanayin da ta nuna a jikinta sai ka rantse da gaske taimakon za ta je yi.
Yana shiga ya tadda ta durkushe ganin haka, ya isa gareta da sauri yana ambaton. “innalillahi Habeeba meke faruwa ne, ko haihuwar ce?”.
ya rikota yana mai girgizata idanuwanta a rufe, ya durkusa gabatan ya tallabo haɓarta.
A daidai lokacin Goggo Marka ta iso tana marere cewa kamar gaske, ta isa garesu tana tafa hannu gami da salallami.
“me nake shirin gani haka Habeeba meke damuki, baki da lafiya amma ki ka ki sanar dani, haba habeeba sam haka bai dace ba”.
ta karashe cikin yanayi na rauni da tausayawa, rikota tayi tana mai cewa Adamu.
“ina tunanin haihuwa ce ta zo mata”.
gyada kai kawai yayi cikin yanayi na tsoro da halin da ya ga matar ta shi a cikin, tausayinta ya gama mamaye masa zuciya ya tabbata Habeeba tana cikin mawuyacin hali, lakari da yarda ya ganta aciki, wanda bai taba gani hakan ta faru a gareta ba, zuciyarsa ta shiga bugu da sauri ya dubi Goggo Marka.
“ko dai Asibiti zamu wuce da ita”.
Wata irin zabura tayi jin ya ambaci Asibiti.
“haba Adamu haihuwar ce sai mun tafi asibiti, ai ko can muka je in dai lokaci bai yi ba haka zamu ta zama har lokaci yayi, ko kuma su saka karti su ta jagwalgwalata har su yi mata illa ko kuma su dakusar mata da karfin nata, su saka ta haihuwar dole tun lokaci bai yi ba, kadai mu bi komai a hankali, in lokaci yayi zata haihu”.
ta fadi kamar gaske, tana faman rike Habeeba sai faman sannu take yi mata, sai ka rantse har kasar zuciyarta haka ne.
Ba yarda ya iya, haka ya gyada kai shi ma yana faman yi mata sannu. ita kuwa Mareeya mamaki da tu’ajibi ne suka cika ta, ta ma rasa abin cewa, ganin yarda Goggo Marka ta zage tana faman narkar da murya ita ala dole tausayi take ji, kamar ba ita bace ta gama kwashe mata albarka ba yanzu. girgiza kai tayi cikin yanayi na tsanar halin Goggo Marka.
“Maza ke kuma ki tashi ki fice daga dakin, kin zauna kin kure mutane da idanu”.
Goggo Marka ta fadi tana mai duban Mareeya tana galla mata harara ta gefen ido, ba wanda ya kula da hakan sai ita kadai kau da kai tayi, tana duban mahaifin nata wanda hankalinsa gabadaya yana kan matarsa, yana dubanta yana kallon yanayin da take ciki na tsananin wahala, zai so ace sun tafi asibiti da ita yana ganin haka shine kawai yafi dacewa, sai dai maganar Goggo Marka tayi masa katanga da hak,a ba don ya so ba ya dubi Mareeya da take ta faman ajiyar zuciya, hawaye sun cika mata idanu ya ja hannunta suka fice daga cikin dakin, zuciyarta sai faman azalzala take yi da tsoro don tana fargaban barin Goggo Marka da Uwarta ta kar tayi mata wani abu, domin irin kiyayyar da ta hango a idanuwanta komai za ta iya aikatawa.
Can nesa da dakin ya ja ta ya zaunar da ita, yana mai rarrashinta da ta bar kuka In Sha Allah uwarta za ta samu lafiya, ita dai gyada masa kai kawai take yi, amma ba ta hango hakan ba. hankalin ta gabadaya ya karkata izuwa wajan uwarta da kuma Goggo Marka da aka bari tare da ita, tsoro take ji.
Ba su jima da fitowa ba, Goggo Marka ta fito daga cikin dakin duk ta hada gumi kamar gaske. dubansu tayi gami da rausayar da kai ta wuce dakin ta, an jima kadan ta fito hannunta dauke da kullin abu, ba tare da tayi wa kowa magana ba ta samo kwano ta kwance kullin da ta ɗanko daga dakinta, wasu sauyoyi ne a ciki kwasa tayi ta zuba cikin kwanon mai dauke da ruwa ta shiga jujjuyawa, gaban Mareeya ya yanke ya fadi, ta zaro idanu tana kallon abin da take yi gabadaya hankalinta bai gamsu da abin da take yi ba, nan ta dubi Babanta, shima Goggo Marka yake kallo. sai da ta gama motsawa sannan ta mike ta nufi cikin dakin. da sauri ya tare ta da cewa.
“Goggo wannan kuma menene”.
Murmushi tayi gami da margaya kai.
“magani ne mace dake kan gwuiwa ake baiwa, domin samun sauki da kuma haihu sumulkalau ba tare da an samu matsala ba, yanzu ina bata shi in dai haihuwar ta zo to nan da nan zaka ga ta haihuwa abinta”.
Ba ta tsaya jin abin da za su ce ba ta fada cikin dakin. izuwa wannan lokacin Habeeba sai faman numfashi take yi da nishe-nishe lokaci lokaci, gumi ya gama game mata jiki gabadaya. isa tayi gareta ta rangwafa gami da tallabo haɓarta dake kasa, ba tare da komai ba ta tura mata kwanon mai dauke da jikanken sauyoyin, wani hamami ne da daci suka dake hancinta da harshenta da sauri ta kau kai, duk da tsananin da take ciki bai hana ta tsanar wannan abin da ake kokarin ba ta ba.
Goggo Marka ta na ganin haka ta sake kakaba mata tana mai kashe murya.
“hakuri zakiyi ki sha Habeeba, shi zai taimaka maki wajan samun saukin nakudar. duk wani ɗaci nashi daure wa zakiyi haka”.
ta sake kai maka shi baki nan ma kau da kai ta sake yi, cikin tsananin kin abin ta shiga numfarfashi, a lokacin nakuɗar ta sake motsa mata ji take yi kamar bayanta da kwankwasonta za su karye, ta dago da jajayen idanuwanta cikin rashin hayyaci ta dubi Goggo Marka wacce ta ke ganinta tana kasuwa gida bibbiyu a gareta, ta mai da kanta kasa tana mai sakin numfashi. ita kadai ta san halin da take ciki, ita kadai ta san azaba da raɗaɗi da take ji a kowa ni sashi na jikinta…Awa daya tsakani amma shiru kake ji, ba wani cigaba wanda za ace na a zo a gani, har hankula su saka ran samun natsuwa.
Malam Bello zuciyarsa ta gama karaya matuka, ji da yayi shiru ba alamun haihuwar, anyi ta ko ba ayi ta ba, ya rasa matsayar da zai ajje zancen zucin sa.
Numfashi yake ta faman ajjewa, sai ka rantse shima nakuɗar ce akan sa, ya dubi Mariya wacce ta ke cikin yanayi na faduwar gaba da rikitar zuci da ruhi, duk hannaye biyu ta saka ta tallabe haɓarta, idanuwanta sun yi jajir hakan ya kara tsinke masa natsuwar zuciyarsa, sai faman bugu take yi tana yaso masa wani banzan zance wanda ba shi da muradin ace ya tabbata cikin duniyarsa, in kuwa haka ya tabbata ko shakka ba ya yi zai fi kowa ruɗewa cikin duniyarnan. a hankali ya shiga ajje numfashi, yana kallon dakin da Matar tasa take wanda ya tabbata izuwa wannan lokacin mutuwa ta zo kusa da ita. Da wannan zancen zucin ya kokarta mikewa yana faman hirji kamar zai ci babu, ya doshi dakin cikin bugun zuciya da ruhi.
Yaye labulan yayi cikin rashin tabbacin abin da zai gani, duk da dai zuciyarsa tana yi masa kuwwa akan ba sauki sai wajan Allah. idanuwa da numfashinsa gami da bugun zuciyarsa a lokaci guda suka shiga rudu, ganin yanayin da ya ga Habeeba a ciki, da hanzari ya fada dakin ya dubi Goggo Marka, wacce ke zaune can gefe ta zubawa Habeeba idanu, ba wani alamun tashin hankali tattare da ita, maganar Malam Bello ne ta dawo da ita duniyar rauni, da kokarin yafawa fuskarta yanayin tausayi, ta shiga duban shi.
“ka gani ko, har yanzu ba alamun haihuwar ina ga dai lokaci ne baiyi ba, ko kuma juyi ne”.
Ta fadi cikin yanayi na kara narkewa a tausayi.
Gyada kai kawai yake yi, kamar wani kadangare yana faman jan numfashi yana ajjewa, idanuwansa da hankalinsa har da natsuwarsa duk suna kan matar sa, sake ajje numfashi mai kauri yayi.
“Goggo kawai mu tafi Asibiti”.
ya dasa aya yana kokarin isa wajan Habeeba. Da sauri ta tare shi.
“a,a mana Bello, mai yasa zaka nuna gajen hakuri ne, na fada maka in haihuwar nan ta zo yin ta za ayi, amma na ga alamun taurin kai za kayi. haba don Allah ko fa Asibitin muka je hakance zata kasance”.
Bai amince ba, bai yarda ba da maganar ta sam. bai hango ɗa mai ido ba cikin wannan lamarin, don haka ya dube ta sosai, cikin karyar da murya.
“Goggo zuwa Asibitin shine ya fi dacewa, domin zaman gidan ba karimin hatsari zai farar ba”.
Duban sa tayi, cikin shan kamshi.
“me ka ke nufi Bello, kana nufin a matsayina ba zan iya amsar haihuwar ba ne ko yaya?”.
Girgiza kai ya shiga yi, cikin yanayi na rashin natsuwa.
“ba haka bane Goggo, ya kamata ki fahimta wani abu, kin ga can asibiti in muka je ko ba haihuwa ba ce su sun san abin da ya dace suyi mata, domin ganin komai ya zo yarda ya dace, amma zaman gidan ba abin da zai haifar sai dai ya je fa mu a ruɗu da rashin abin yi kawai, sai dai mu sata gaba muna kallo”.
“ba in da za a kai ta Bello, na fada maka ka duba fa ka ga yanayin da take ciki, alamun ya nuna haihuwar gaf take da yin ta yanzu, in muka dauke ta cikin wannan halin komai zai iya faru a hanya, za ta iya haihuwa a titi me kenan akayi?”.
ta fadi cikin yanayi na rashin jin dadin maganganunsa, ta yafa wa fuskarta yanayin kamar gaske ta shiga cizon laɓɓa, sai ka rantse zage ta yayi tas.
Wani marainin nishi Habeeba ta saki, wanda da kaji amonsa kasan wahala ce tsagwaronta ba mis a cikin ta, hakan ya kara ruguza ‘yar natsuwar Bello, ya shiga dubanta sai faman fadin “Sannu” yake yana ji azuciyarsa har da can kasar ruhinsa kamar bai yi mata adalci ba, in har ya yarda da batun Goggo. sai dai kuma a wani bangaren in ya ki amsar maganar Goggo, kamar kin biyayya ce a gareta. duban Goggo yayi ya sake juwa wajan Habeeba, wanda ko tantama ba yayi mutuwa tana kurkusa da ita, in kuwa mutuwa ba ta zo ba to tabbas bakar izaya da wahala tana ɗawainiya da gangar jikinta da zuciyarta.
“kiyi hakuri Goggo, mu kai ta asibiti…”.
Wani kallo ta watsa masa, kafin ta fara magana cikin ɗaci.
“wai shin in tambayeka yau ta fara haihuwa ne a duniyarta, na dauka ta haifi Mariya kuma a gidan nan ta haifeta, ba tare da zuwa wani waje ba. to bari kaji na fada maka ba in da zata, a gida zata haihuwa kana kallo fa na bata magani rage zafin nakuda, da zuwan komai a sannu kuma da ka kalle ta za ka san maganin yayi aiki…”
Da sauri ta katse batunta, lokacin da taga wani ruwa ya fara gangarowa daga kasan Habeeba.
“ka gani ko. har faya ta fashe haihuwar ma ta zo nan kurkusa, sai ka fice ka bamu guri ko a nace”.
Ta kareshe tana galla masa harara. da sauri ya dubi Habeeba, yana kallon yarda ruwan da bai san na menene ba, yake zubowa daga jikinta wanda ya tabbatar da zancen Goggo din, amma bai amincewa kan sa ba, har can kasar ruhinsa. ba yarda ya iya haka ya fara jan jiki yana kallon Habeeba, yarda take wani irin nishi da murkususu kamar za a zare mata rai.
Zuciyarsa ta kara yin rauni, ganin yarda Habeeba ke shan wahala. in da yana da yarda zai yi da ya dauke mata wannan azabar ya daurawa kan sa, amma ina! ba hali, haihuwa mace ce kawai take da wannan alhakin nayin ta, wanda ba komai bane a cikin ta sai tsatsar azaba da wahala, tausayinta ya kara tsargar masa a jiki. da wannan yanayin ya isa inda Mariya take zaune, ta na ganinsa ta mike idanuwanta akansa, sai nar-nar suke alamun son zubda hawaye, tana kokarin yin magana ya yi saurin riketa ganin kuka na kokarin kufce mata, ya shiga girgiza kai kamar wani d’an kadangare.
“karki yi kuka Mariya, komai tsanani yana tare da sauki da yardar Allah, kuka sam bai ka mata ba…”
da sauri ta tareshi, tana mai gyada kai, hawayen da take boye su suka shiga zubowa, kamar an murde kan rubabben famfo.
“Abba Umma ta ina son ta, bana so na rasata don Allah ka taimaka mani ka taimaka mata, mu kai ta asibiti kar ta mutu ta bar mu cikin duniyar nan, ba zan iya rayuwa ba na rokeka”.
Ta karashe tana mai zubewa a kasa, kamar wacce aka bugewa gwiwowi ta shiga sakin kuka mai cin rai da tsuma zuciyar mai sauraro.
Kallonta yake yi, cikin wani irin hali na tausayawa zuciyarsa gabadaya ta gama raunacewa ji yake yi kamar ya daura hannu saman kai, ya zunduma ihu. wani radadi da zafi gami da zugi yake ji suna taso masa, tun daga kasar ruhi har zuciya gabansa sai amsa wani irin bugu yake yi mai dauke da kayan tashin hankali cikin sauri-sauri. dafe kai yayi da duk hannayensa ya rasa mai ya kamata yayi, ya rasa mai ya dace yayi, domin samo mafita akan wannan lamarin dake kokarin janyo masa tashin hankali. ya rasa da mai zai ji, ya sani Habeeba na cikin halin wahala dole ya nemi mafita, dole ya kai ta asibiti, in da yake tunanin nan ne kawai ya dace ace a halin da take yanzu tana can. sai dai wani hanzari ba gudu ba, Goggo Marka ta hana yin haka, ya rasa mai yasa ta kasa fahimtarsa, ya rasa mai ya sa taki yarda ta amshi rokonsa, ya rasa mai yasa take kokarin janyo masa abin da zai haifar masa da tashin hankali, taki fahimtarsa, taki gane matsalar da yake hangowa za su fad’a, ya kamata ta fahimta zamanin da da yanzu ba daya bane, komai ya sauya kamar yarda komai na cikin duniya ya sauya, haka zamani yake sauyawa da abubuwa masu dauke da karin haske ga duniyar dangin rai sai dai taki amincewa da cewa ZAMANI YA CANZA.
“Abba don Allah kar ka bari maganar Goggo tayi tasiri a zuciyarka, har ta hanaka ceto rai”.
Mariya ta fadi cikin rawar murya, tana duban mahaifin na ta, cikin kasalallan yanayi.
Gyada mata kai ya shiga yi, kafin ya ja jiki ya fice daga cikin gidan, ya bar ta nan tallabe da haɓa.
Bakin titi ya nufa, mai Napep ya dauko ya dire kofar gidan, ya ce dashi ya jira shi cikin gidan ya fada cikin jarumar zuciya, a daidai lokacin Goggo Marka ta fito daga cikin dakin a firgice saura kadan suyi karo, idanu ya zuba mata yanayin da ya ganta ya sanya gabansa tsananta bugawa, ita kanta Mariya ba karamar razana tayi ba da sauri ta bi bayan mahaifinta, ganin yanayin da yake ciki yana fadawa cikin dakin yayi daidai da karar da Habeeba ta saki, gami da bingirewa jini na malala ta karkashin ta, ga kan jariri ya yo waje bai san lokaci da ya isa gareta ya durkushe gami da tallabo haɓarta, zuciyarsa ta buga lokaci guda ganin da yayi ba alamun numfashi a jikin ta, hakan ya kara masa firgici, zabura yayi gami da ficewa waje, cirko-cirko ya tadda da su, Goggo Marka tallaɓe da haɓa kallo daya zakayi mata ka hango rashin gaskiya da firgici kwance a cikin idanuwanta, ita kuwa Mariya hannu ta daura akai ganin yarda mahaifinta ya fito, ta kurma ihu gami da zubewa kasa tana fadin.
“Shikenan rayuwa ta gurgunce a duniyata, shikenan na bani na lalace a rayuwar duniya, shikenan tsanin rayuwata ya karye…”.
Da sauri ya isa gareta, ya dago ta.
“Mariya daina fadin haka, wa ya sanar dake ta mutu, ta na nan da ranta”.
ya fadi yana mai juyar da kallon sa wajan Goggo Marka da tayi wuki-wuki kamar wacce tayi wa sarki karya, girgiza kai yayi, da sauri ya koma cikin dakin dalilin wasu lamura da zuciyarsa da kwakwalwarsa suka shiga sanar dashi, cikin jarumtar zuci da na jiki ya shiga gyara mata jiki, idanuwansa cike da hawaye ya dagota gabadaya ya rungume ta, ya fice daga cikin dakin cikin hanzari ba in da ya direta sai cikin Napep, shi kansa mai Napep din ya tsorata da yanayin da ya ganta aciki, da sauri ya shiga ciki gami da tayarwa, Malam Bello gabadaya ya gama ficewa daga hayyacin sa. kwalla da suka taru masa a idanu sai shatata suke kamar wani karamin yaro. har Napep ya fara kokarin tafiya, sai ga Mariya ta fallo a guje tana kuka, tana mai cewa da mai Napep din ya tsaya don Allah, amma Malam Bello ya ce su tafi kawai don yasan in har Mariya ta biyo su, kafin su kai sai hankalin su ya kara tashi musamman in da take nan a firgice, yana hangota tana daga masu hannu tana kiran su cikin muryar kuka. kai ya shiga girgiza mata, yana mai daga mata hannu alamun ta koma gida. amma ina kuka ta sake rushewa da shi gami da durkushewa, ta saki wani sabon kukan mai cin rai da tsuma zuciya, kuka take yi kamar ranta zai bar jikinta, wani zafi take ji tun daga kasar ruhinta har zuwa inda zuciyarta ke ajje. ta gama yanke tsammani akan sake ganin mahaifiyarta a duniyar rayuwarta dauke da numfashi, zuciyarta ta gama yarje mata sun yi rabuwa kenan har gaban abada, ba za su sake haduwa ba.
ta ji ma cikin wannan halin. kafin ta kokarta cikin jan jiki ta mike tana faman tangadi, duniyar gabadaya ji take tan juya mata, komai ya kwance mata, komai ya lalace cikin duniyarta, kayan farinciki tuni suka guje suka barta, ji take kamar zuciyarta zata tarwatse, kwakwalwarta ta na faman kai kawo cikin duniyar tashin hankali da rashin tsammanin samun sa, sannu a hankali take tafiya idanuwanta a rufe jefa kafa kawai take yi a duk in da taji kafar ta ta, ta bata damar haka, cikin ikon Allah ta isa kofar gida, tana kokarin sanya kai cikin soron, sukayi karo wani irin zafi da raɗaɗi ta ji goshin ta ya dauka, da sauri ta buɗe idanunta tana dafe goshinta, wasu zafafan hawaye suka zubo mata. Goggo Marka. ta gani tsaye idanuwanta akan ta, sai faman tsume fuska take yi. kau da kai Mariya tayi, tana mai jin zafi rai suns dago mata da duk wani numfashinta, ta fara kokarin rakuɓeta za ta wuce, wani wawan cafka ta yi wa wuyanta, ta dawo da ita gabanta.
“ke mai uwa ko, shine saboda rashin sanin darajar kai, ki ka zube a titi kina kwarar baki. to dan uban ki in ba duniyar kika dauke da ihu ba, za a kashe miki uwa ba ki cika Mariya jikan Lamiɗo ba shegiya bakar munahika kawai.
Girgiza kai ta shiga yi,hawaye na sake balle mata sam maganganun Goggo ba su taba mata zuciya ba, domin tashin hankalin da take ciki ya zarce duk wata bakar magana ko zagi da za ayi mata, hannu ta sanya ta dauke hawayen da suka cika mata idanu ba tare da ta sake bin ta kan Goggo ba, ta sake yinkurin shigewa cikin gidan. a wannan karon ba ta hanata ba, sai kwaɓa da tsaki da ta bi ta dashi.
Tunda suka dauki hanyar Asibiti, Malam Bello ke rungume da Habeeba. ba abin da yake yi sai zubar hawaye, har zuwa wannan lokaci jini bai daina zuba a jikinta ba, gabadaya shimfidar cikin Napep din ta baci shi kasan direban lokaci-lokaci yana juyowa ya dube su, domin ba karamar firgita yayi ba, sai faman zabga gudu yake yi kamar zai tashi sama, burin sa kawai su isa Asibiti, domin ceto ran Habeeba.
Mintina goma kacal ya kai su Asibitin baban alis, yayi Parking gami da direwa, da gudu yayi cikin Asibitin yana mai sanar da Nurses su taimaka wata ce ba ta da lafiya, yanayin da yake ciki na rashin hayyaci, sai ka rantse uwarsa ce ba lafiya amma Nurse din ba wanda ya bi ta kasan, kowa harkar gabansa yake yi, mutanan da suke zazzaune sai faman bin sa da kallo suke, cikin yanayi na tausayi, domin sun tabbata ba abu ne mai sauki zai firgita duniyar tunanin wannan matashin ba. tun yana neman daukin su, su kula shi amma ba wacce ta kulashi, sai da ya isa kusa da wani teburi ya shiga duban matar dake zaune, ta na ba da katin ganin likiti, ya dubeta.
“don Allah ku taimaka likita, haihuwa za tayi jini na ta zuba a jikinta”.
dago kanta dake sunkuye tayi, tana dubansa cikin gilashin dake fuskarta.
“ka je ku shigo da ita, sannan kuma ku kawo katin da take zuwa awo dashi, domin ba za a taba ta ba, har sai an bada kati”.
da mamaki ya shiga dubanta, ganin yarda ta nuna halin ko in kula akan lamarin. ji yayi kamar ya dauke ta da mari, amma ya kasa. da sauri ya juya zuciyarsa na zafi da radadi irin yanayin da ya ga Nurse sun nuna masa, da sauri ya isa wajan Napep, ya tarar Malam Bello, na kokarin fito da ita wacce a wannan lokaci kallo daya zaka yi mata, ka bawa zuciyarka amsa cewa ba ta da rai.
Cikin Asibitin yayi da ita tana rungume a hannunsa, mutane da yawa sun tsorota matuka da yanayin da suka ganta, suka shiga sallallami suna zaro idanu, Malam Bello, da ke rikice ya rasa ma in da zai yi da ita, sai faman zarya yake yi magana ma ta gagare shi, duk abin da yake da yawa Nurse na kallon sa, amma sai dai su ba banza ajiyarsa. ciki mutanan dake zaune a harabar asibitin wasu mata biyu suka iso gareshi,tare da taimaka masa, zuwa daya daga cikin dakin Asibitin. a daidai lokacin Nurse mai siyan da kati ta iso cikin dakin, tana duban Malam Bello. wanda gabadaya ya gama yin nisa da hayyacin sa. tambayarsa take, amma ya rasa bakin bata amsa, sai motsi yake yi da baki, daya daga cikin matan da suka taimaka masa ne ta dubi Nurse din.
“wannan ba fa shi ne mafita ba, ya kamata ko taimaka mata ki duba halin da wannan baiwar Allah take ciki, mana maganar kati duk ba shi da muhalli a halin da ake ciki, ceto ranta take bukata”.
Kau da kai tayi, tana mai ya tsine fuska.
“ke ma kin san haka ba za ta taba yuwuwa ba, dole sai da katin ta na shaidar ta na zuwa ganin likita, sannan za a kula da ita”.
Ta karashe maganar ta tana kokarin ficewa. da sauri dayar matar wacce da alamu haushi ya cikata, ta sha gabanta tana yi mata kallon na raina matsayin ki.
“wai ke kuwa kina da ita imani, baki san zafin da raɗaɗi bane a wajan haihuwa bane, ba ma haka ba, wannan fa yar uwarki ma cece, ya kamata ko don wannan matsayin da kuke daya ki taimaka mata”.
Kallo uku ahu tayi mata, kafin ta gyara zaman gilashin fuskarta.
“karki jefe ni da wasu kalamai munana, karki ga laifi ne akan wannan lamarin, ke kanki sani, duk wata mace mai ciki in dai ta zo haihuwa sai an bukaci katin zuwa awonta, kafin a dubata…”.
“wannan ba hujja mace malama”.
Mai Napep ya katse mata maganar da take yi, cikin zafin rai ya dora da cewa.
“wannan maganganun da kike duk na banza wallahi, na lura ba ki da imani sam ke da wasu likitocin da kuke aiki, in har haka likitoci suke sam ba su yi ba a duniyar nan ko daya, ke ba zan musu kudin goro ba, dama komai na duniya akwai na gari akwai kuma bara gurbi, to ke ki na sahun bara gurbin wallahi”.
Yanayin da yake maganar cikin zafin rai kamar zai rufeta da duka, ya fadar mata da gaba, nan ta shiga duban su daya bayan daya har takai ga Malam Bello, wanda idanuwansa gabadaya sun gama rinewa kamar wanda aka watsawa barkonon tsohuwa girgiza kai tayi gami da cewa daga dakin, adaidai lokacin Habeeba ta saki wani nishi wanda ya sanya gabadayansu suka dire akanta, numfashi take saki cikin wani irin wahalallan yanayi mai dauke da rashin hayyaci, idanuwanta a rufe amma hakan bai hana hawaye zubowa ba, Malam Bello ya isa gareta, gami da riko hannunta ya na ambatar sunanta, cikin murya mai taushi da tausayi, girgiza kai ya ga tana yi hawaye na kara balle mata, bakin sa na rawa ya shiga kokarin yin magana amma kamar wanda ka daurewa harshe maganar taki fitowa, ya shiga goge mata gumi dake ta faman tsantsafo mata a goshi. a daidai wannan lokaci wani dirkeken mutum, wanda da kallaeshi za ka gane babban likitane, yana gaba Nurse na biye dashi har ya iso inda Habeeba ke kwance, dubanta yayi sosai kafin ya komar da kallonsa izuwa wajan Malam Bello, wanda yake ta famam ajiyar zuciya.
“mai ya sa haka, mai yasa har kuka bari hakan ta kasance a gareta?”.
ya fadi cikin murya mai nuna bacin rai. Girgiza kai ya shiga yi cikin rashin abin cewa, likita ya sake dubanta.
“ina katin ta wanda take zuwa ganin likita da awo dashi”.
Nan ma girgiza kai yayi, alamun babu kenan.
Da sauri likitan ya dube shi cikin alamun zaro idanu waje, da madaukakin mamaki da kuma haushi.
“hakan da kuka yi sam bai da ce ba, ka ga yanzu kun haifar mata da matsala, domin duk wanda ya kalleta ya san tana cikin halin wahala, ya kamata kuke lura mace mai ciki tana bukatar taimako da kulawa da tattali, tun daga lokacin da ta samu ciki ya kamata ace tana zuwa Asibiti, a ko wani bayan sati uku tana ganin likita, hakan ne zai bata damar sanin halin da take ciki da abin dake cikin ta. kar ku ga laifin abinda wasu likitoci ke yi na rashin bada kulawa ga mai ciki, hakan na faruwa ne ta dalilin mai ciki da kum mijinta…”.
“kayi hakuri likita don Allah, a bar zancen nan, ya kamata ace ku san abin yi akan wannan baiwar Allah, domin tana cikin hali mara dadi”.
Daya daga cikin matan dake wajan ta fadi, cikin yanayi na rauni.
Murmushi likita yayi ,kafin ya shiga duban Habeeba, daga karshe ya umarce da su dauke ta domin zuwa dakin haihuwa, yana tsammanin haihuwar ce ta zo, cikin hanzari kuwa sukayi hakan. likitin ya kira Nurse uku, sukayi masa jagora domin kula da Habeeba, Malam Bello da sauran matan suka koma harabar Asibitin suka yi cirko-cirko, mai Napep nan yayi wa Malam Bello Sallama tare da fatan samun lafiya ga Habeeba ya tafi. ba tare da ya amshi ko sisin sa ba.
Sai da suka shafe mintina talatin, amma har zuwa lokacin ba alamun haihuwar za ta yiwu, tun likitar na tsammani har ya fara yanke tsammani. iya kokarin sa yayi amma bai kai ga ci ba, ga dai kan jariri a waje amma fitowarsa ya gagara, duk wani taimako yayi amma ina domin gabadaya jaririn ya cije ba alamun zai fito, dalilin kin buduwar kwankwason ta, yaki budewa balle jaririn ya fito, iya wahala Habeeba ta gamu da ita, shi kan sa jaririn wahala ta sheshi, ganin wanki hula na kokarin kai su dare, nan likiti ya fito ya ja hannun malam Bello, zuwa Office din sa, yayi masa bayani, ba karamar kaduwa yayi ba, nan likita yace in ya yarje ayi mata aiki, domin shine kadai mafita agareta, da ma jaririn domin kar azo ayi BIYU BABU.
Shiru yayi yana tunanin lamarin, ba wai aikin ne ba ya so ayi mata ba, a,a kudin aikin in da zai samo su, ita ce matsalar. domin kuwa a yanzu halin da ake ciki ko dubu biyu na sa takan sa ba shi da ita, balle wasu makudan kuɗaɗe da yake tsammanin za a nema a gareshi, numfashi ya ajje ya dubi likita wanda ya gama karantar halin da Malam Bello ya ke ciki.
“Likita ba wai ba zan iya sa hannu ba ne, a,a abin neman ne babu…”.
Hannu likita ya daga masa, yana kokarin yin magana. kamar daga sama Nurse ta fado cikin office ta dubi likita.
“Sir ina tunani za ta iya haihuwa da kanta…”.
Tun kafin ta dire, ya miki zumbur cikin hanzari, ya fice daga office din .Nurse ta biyo shi a baya tare da Malam Bello.
yana shiga dakin ya tadda sauran Nurse din akanta, yanayin da ya ganta da irin nishin da take saki ya kara sanya jin tausayinta, da sauri ya isa gareta, izuwa wannan lokacin kafaɗar jaririn ta yo waje, hakan ya tabbatar masa za ta iya haihuwar da kanta, a hankali ya fara kokarin janyo jaririn a hankali a hankali yake bi har ya zo matakin tsakiya, wato saitin cikin jaririn. a lokacin ta yi wani nishi mai dauke da wata hargitsattsiyar kara, wacce ta amsa kuwa gabadaya dakin. a sa’ilin da shi kuma jaririn ya fado duniya gabadaya. zubewa tayi daga kan gwuiwowinta numfashin ta na fita, cikin wani irin yanayi…Kuri likita yayi mata da idanu gabadaya hankalin sa da guntuwar natsuwar sa tana kan ta hannusa kuma yana mikawa nurses jaririn bayan ya yanke masa cibiya.+
Abubuwa ne suka shiga yi masa dirkar mikiya a kwakwalwa zuciyarsa na ta tunano masa wasu abubuwa da baya fatan ace sun faru da wannan baiwar Allah ajiyar numfashi yayi gami da saurin duban Nurses da suma hankalinsu na kanta ganin halin da take ciki na rai kwakwai mutu kwakwai.
“maza kuje ku gyara jaririn sannan kuma ku dauko gado domin daukarta don na lura tayi matukar gajiya da galabaita”.
Abin da likiti ya kokarta furtawa kenan cikin rashin tsammanin samun karfin daga laɓɓa har ya yi furuci gyaɗa kai yake yi yana gauraya kwayar idanuwansa cikin gurbin su laɓɓansa dake cikin bakin sa sai faman cizon su yake fuskarsa na kara bayyanar da rashin armashi da natsuwa.
Mikewa yayi cikin rashin kumaji duk wani azancin sa yana jin yarda yake kokarin kufce masa daurewa kawai yake yi yana yaki da batun da kwakwalwarsa da zuciyarsa suke ta sanar dashi ba zai so haka ba, ba ya faman haka ta kasance gyaɗa kai ya cigaba da yi kamar yana magana da wani ya ma rasa abin da ya dace yayi tunaninsa gabadaya ya wargaje sai akan abu daya wanda yake tsammmanin ba ɗa mai ido zai haifo ba.
Dawowar nurses ne ya dawo dashi daga duniyar fargaba da tsunduma ya shiga jan numfashi a hankali mai dauke da kayan tashin hankali
Ya dube su su duka yana mai kaɗa idanu yana mai yi musu nuni da ita nan suka shiga gyara mata jiki tamkar gawa haka suke sarrafa har suka kammala sannan suka daurata zaman gadon gami da gungurawa suka fice daga cikin dakin yana mai bin su da kallo numfashi ya ajje gami da jingina da jikin bango har zuwa lokacin zuciyarsa sai kokarin gasgata masa lamarin take wanda shi sam ba ya fatan hakan wuyar rigarsa ya gyara gami da jan jiki ya fice daga cikin dakin xan gefe ya hango Malam Bello tallabe da haba sai faman mazurai yake yi cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali kallo sosai likita ke bin sa da shi zuciyarsa na dauko tausayinsa tana jingina masa ta kowani bangare na sassan jikinsa sannu a hankali ya fara kokarin jan jiki ya isa gareshi amma sam bai san ya iso ba har sai da ya daf kafadarsa wata irin zabura yayi mai dauke da ajje wani gwauron numfashi idanuwansa fes kan likiti jikinsa yana rawa ya riko hannunsa.
“don Allah in har zaka yi furuci kayi wanda ba zai tafi da imanin zuciyata ba na rokeka”.
yanayin da yake sakin furucin da kyar yasan ya jikin likita kara sanyi ya shiga gyada masa kai.
“ta haihu…”.
shima ya fadi dakyar kamar wanda akayi wa dole idanuwansa na kan Malam Bello kamar yarda shi ma ya ke kallonsa zare hannunsa yayi saboda wani irin bugu da yaji ya kawo masa ziyara zuciya ya dubi Malam Bello.
“ina zuwa zan maka magana in an kammala gyara mata jiki sai ka zo ka ganta da baby ko”.
ya karashe cikin sakin murmushin yaƙe bai jira amsawar Malam Bello ba ya ja jiki da sauri ya nufi dakin hutu da aka kai Habeeba ya tura ya shiga har yanzu dai jiya-i-yau da sauri ya isa gareta yana duban nurses da sukayi carko-carko da alamun yanayin da suka ganta ya tafi da yar guntuwar jarumtarta su hannunta ya kamo bayan ya dan rankwafa zuwa gareta hannun ya shiga juyawa yana mai kai dayan hannun nasa izuwa wuyanta yana taba alamun nemon motsin numfashi cak! ya tsaya kamar wanda aka cewa in yayi kwankwarar motsi ba zai ji sautin saukar numfashin nata ba gyada kai yake yi cikin raguwar faduwar gaba jin saitin kirjinta yana harbawa alamun da rai a jikinta har zuwa wannan lokaci ajje numfashi yayi mai karfi kafin ya miki ya shiga binciken ta sosai tsayin wani lokaci bayan ya kammala ya umurci Nurses akan su dauko masa kayan karin jini cikin sauri suka fice gami da daukowa ruwa ya fara sak mata gami da yin wasu allurai a cikin ruwan sannan ya juya inda ya juyo jaririn na kuka inda aka kwantar dashi kallonsa yayi sosai ɗa namiji ne fari tas dashi kyankyawa mai kama da uwarsa.
STORY CONTINUES BELOW
Barin wajan yayi, ya yi hanyar fita waje. A bakin kofa ya tadda Malam Bello tsaye ya na jiran fitowarsu, da hanzari ya isa gareshi dauke da fuskar murna sai faman tallar hakoransa yake yi kamar wanda aka baiwa sabuwar amarya amma in ka lura sosai zaka tabbatar da murmushin na yaƙe ne cikin kokarin dauko jarumta ya dorawa kansa ya isa gareshi shima da ya hango shi cikin hanzari ya baza masa idanu yana takowa a hankali kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki lura da yayi fuskar likita da murmushi sai faduwar gabarda take wa kirjinsa bugun kato ta fara saurarawa yashiga ajje numfashihar suka iso ga juna suna shakar numfashi Malam Bello ya sake ajje numfashi yana mai gyara zaman hular kansa ya shiga jiki na ɓari ya dubeshi.
“likita ka ja min rai wallahi, don Allah sanar dani halin da ake ciki, ko na samu raguwar bugun katon da zuciyata ke yi”.
ya fadi yana kara kusanto shi kamar zai shige jikinsa idanuwansa fes akan sa.
zuciyar likita tayi matukar cilla cikin wani hali na ta rarrabi na rashin tabbas akan lamarin da yaji duniyar tunaninsa na shawagi dashi a ciki ya rasa mazaunan hankalisa sun ka sa zaman kalau ya tabbata zuciyarsa bata yi masa adalci ba in har ta dauko mata banzan tunanin nan wanda in har ya gasgatashi komai zai iya faruwa wani yake ya kinkimo ya daurawa fuskarsa tare da dafa kafadar Malam Bello.
“ta haihu lafiya an samu ɗa namiji ina tayaka murna…”.
Sautin ihun da ya dauki cikin asibitin gabadaya shi ya daskarar da duk wani motsi na mutanan cikinsa ya tafi da furucin su likita da yayi mutuwar tsaye idanuwansa fes akan na malam Bello wanda shi ma kallo daya zakayi masa ka tabbatar zuciyarsa ta shiga halin tsoro matuka da ihun da ya karaɗe cikin asibitin da saurilikita ya juya ya yi dakin da Habeeba take ba wai don ya na da yakinin daga dakin ihun ya fito ba kawai zuciyarsa ce ta ja linzamin hankalinsa izuwa dakin ilai kuwa yana kokarin shiga suka ci karo da Nurses cikin yanayi na firgici da razana bakin ta na rawa ta shiga nuna masa cikin dakin da hannuamma sam ta kasa kokarin fadin wani abu da zai zarewa likita yarjewa kansa Habeeba ce tayi wannan ihun da hanzari ya fada cikin dakin malam Bello dake bin su a baya shima a daidai lokacin ya fado ciki.
Zaune take taɗe jikinta waje daya hannayenta cikin kunnuwanta sai faman zabga ihu take yi jikin ta na faman kyarma kamar wacce akayi wa tsinannan duka. kan ta su kayi gabadayan su malam Bello yana isa ya zauna kusa da ita yana mai kokarin janye hannayenta daga kunnuwanta yana mai dago habatar idanuwanta ya gani sun kaɗa sunyi jajir sai hawaye da suke kwaranyowa gabansa yayi mugun faduwa ganin irin halinda take ciki na rashin hayyaci juya wa yayi da sauri ya dubi likita bakin sa na rawa shima likitan idanuwansa na kanta domin abin da yake tsoro ne ya faru domin kuma ko tantama ba yayi ta samu matsala akan ta gau da kai yayi daga kallon da Malam Bello ke yi masa ya isa kusa da Habeeba ya kira sunanta amma ba ta amsa ba domin bata san ma yanayi ba sam! duban Malam Bello yayi cikin murya mai dauke da rauni.
“yi mata magana sanar da ita kai wanene”.
da mamaki ya shiga duban likita jin abin da ya ce dashi gabadaya ya ji kansa na juyawa wasu lamura na tashin hankali yaji sun kawo masa hari ba shi ya mike yana nuna likita da hannu.
“ban gane zancen naka ba sam, taimaka kayi mani fashin baki, ta ya ya zaka ce na sanar da ita wanene ni, bayan nasan kuma mun san junanmu ba bakin fuskoki bane mu a tsakani don Allah likita ka fahimtar dani abin dake faruwa”.
Ya karashe yana mutsuttsuka wuyar rigarsa yana mai cizon laɓɓansa ransa sai faman daci da fargaba yake yi domin yarda ya lura da canjin likita ya tabbata akwai matsala a tsakanin rayuwa matarsa kukan da jaririn ya saki ne ya sanya shi saurin juya inda ya juyo kukan da sauri ya kara kusa da gadon da jaririn yake kwance sai faman wuntsil-wuntsil yake yi da kafafuwansa hannunsa cikin bakinsa da alamu yinwa yake ji bai san halin da duniyar ta sa ta zo masa dashi ba hannu ya saka yadauki jaririn wanda yake nannaɗe ido ya zuba sa sosai yana ƙare masa kallo zuciyaraa da kasar ruhinsa sai hasaso masa abubuwa suke yi ma bambanta so da kaunar ɗan nasa yaji sun tsargar masa a jiki da jinin dake gudana ta ko ina a gareshi.
STORY CONTINUES BELOW
Hannu ya saka ya dauko jaririn kafin ya juya na kallon likitan.
“kace mani wani abu don Allah ko na samu saukin kunar rai da na zucci”.
Idanuwa duk suka zuba masa ganin yarda yake magana cikin yanayi na wahalallan yanayi da rashin hayyaci.
Likita ya shiga gyaɗa kai kamar kadangare kafin ya nisa.
“ban san ya zan fara yi maka bayani ba amma dai zan ce maka ka yarda da ƙaddara ko wacce iri ce ta fado rayuwarka”.
“ƘADDARA”.
malam Bello ya furta kalmar cikin jan numfashi da fada ruɗani.
Ya shiga nazarin kalmar shi dai ana sa tunani ya san abin da ake nufi da ƙaddara akwai kaddara mai kayan farin ciki akwai kuma akasinta shi dai a yanzu ya san kaddarar sa ba mai dadi ba ce.
“likita kayi min bayani yarda zan fahimta zuciya ta na cikin bala’i”.
Ya fadi yana mai dauke gumin dake karyo masa kamar wanda ya fito daga surace hannunsa daya kuma jariri ne sai faman wuntsil-wuntsil yake yi yana tsotsar hannunsa alamun yunwa yake ji.
“…Uhmm nace ya kamata ka nemo wacce zata kula da ita na dan lokaci kafin komai ya zama daidai”.
Likita ne ya fadi haka cikin rashin abin cewa.
Kallon sa yake yi, kallo na tuhuma mai cike da son karin bayani akan komai, kallon sa yake yi na rashin yarda da yanayin da ya gan sa a ciki, kallon sa yake yi cikin bugun zuci da ruhi. idanuwansa ya shiga juyawa akan ko wani dayan su cikin yanayi na kara tsoro da fargaba gani yake yi kamar Habeeba mutuwa zatayi in da a kwance take zai iya cewa mutuwa tayi amma suke boye masa amma zaune take cikin wani irin yanayi wanda shi kan sa bai san a matsayar da zai ajje shi ba.
Nisawa yayi gami da juyawa ya ajje jaririn kafin ya dubi likita.
“bana tsammani zuciyata zata yarda da kai da sauran ma’aikatan ka, na lura kana boye min wani abu da yake boye, likita in kayi min haka ba ka yi mani adalci ba sam, kuma ba zan yafe maka ba”.
Magana yake yi wanda da ka kalle shi zaka tabbatar ba isasshen hayyaci a gareshi.
Gyaɗa kai likita yake yi tausayin sa na kara narkar masa da zuciya cikin jan jiki ya isa gareshi ya dafa kafadar sa.
“kayi hakuri kayi abin da nace”.
“bani da wannan natsuwar, ka taimaka”.
Idanu ya zuba masa sosai kamar wanda ya ga bakuwar fuska, bai san mai zai ce masa, ko ma ya samu abin cewa ba tabbacin zai iya kamar sa domin yasa dole abin da yake faruwa ya fado cikin abin da zai ce dashi.
“kai nake jira likita kace min ta haihu kayan farinciki kenan amma kuma naji kana kokarin dauko min kayan da za su ruɗani cikin wannan lokaci, na lura akwai abin dake kokarin faruwa, koma nace ya faru amma ka ki ka sanar dani”.
zuciyarsa ce ta fada masa da ya kawai fada masa domin ta san koman daren dadewa dole abin da ke boye ya fito fili.
Kallon Habeeba yayi wacce take takure waje daya kamar wacce ake kokarin cire mata wani abu daga jiki ta hada gwuiwa da kai sai sakin numfashi take yi kadan-kadai
“Uhmm…”.
Sai kuma yayi shiru yana duban Malam Bello ya ma rasa da mai zai fara wani tunani ya fado masa zuciya lokaci guda da sauri ya dubi Nurses ya ba su Umarni cikin yanayi na amfani da ido a take suka gane abin da yake nufi da sauri suka fice daga cikin dakin.
Malam Bello ya dubi Likita izuwa lokaci. Zargi da kokwanto akan sa ya fara samun mazauni sosai a zuciyarsa.
“ina ga kawai gida zaka ku tafi da ita tunda ta haihu lafiya…sai dai in ko wata matsalar ta faru sai ka dawo da ita”.
Tunda ya fara magana Malam Bello ke yi masa wani irin kallo mai dauke da TUHUMA hakan ya sanya jikin sa sanyi domin ya lura sam bai abince da batun sa ba.
Juyawa yayi da sauri ya fice daga cikin dakin ya barshi tsaye shanye da baki hannunsa ruke da ɗan jaririn da izuwa lokacin ya fara kuka mai sauti sosai.
kallon Habeeba yayi har yanzu dai tana nan yarda take isa yayi gareta yana mai zama kusa da ita.
“HABEEBA”.
ya kira sunanta cikin wata irin murya mai taushi.
ba ta dago ba, balle ya saka ran zata dago idanuwanta har ta sauke su akan sa, ko motsi ba ta yi ba, illa sautin ajje numfashi da take yi.
Sake kiran sunan nata yayi a karo na biyu nan ma bata dago ba balle kuma ya sa ran zatayi magana.
Tsayin lokaci suka dauka cikin haka shikuwa jaririn sai zunduma ihu yake yi sai faman jijjigashi yake yi amma ba alamun zai daina kukan mikewa yayi tsaye yana zarya cikin dakin yana duban Habeeba gabansa na kara tsinkewa da lamarin nata musamman da ya ga duk kukan da jaririn yake yi ko motsi bata yi ba.
Nurses ne suka shigo ba tare da sunyi masa magana ba suka kama hannun Habeeba suka fice da ita yana mai bin su da kallo kamar wani sauna abubuwa da yawa sun daure masa kai ya rasa a ciki wanne ya kamata ace yayi tunani akai da ya dauko zaren tufka tunanin nasa sai ya warware haka ya cigaba da zarya domin rashin abin yi kusan mintina biyar yana cikin wannan yanayi sai ga likita ya shigo yana duban sa.
“An kammala komai ka zo ku tafi don Allah ka kula da ita sosai domin ba karfin jiki gareta ba haihuwar ta bata wahala matuka kai kan ka sheda ne don haka a kula mun yi mata duk wani bincike da ya kamata, zamu hadaka da ma’aikaciyarmu daya domin akwai abin da muke bukata ta kula dashi”.
tunda ya fara magana yake gyaɗa kai cikin amincewa amma ba har zuci ba kawai rashin abin yi yayi ya bige da amsa maganar da ba yarda yayi da ita ba.
Duk halin da yake ciki Likita na lura da shi haka ya ja shi suka fice daga daki har zuwa inda motar da aka saka Habeeba tana zaune a takure kallo kawai ya bita da shi yana gyaɗa kai cikin rashin taka maimai in da zai ajje tunanin da yake yi akan ta.
gaban motar ya shiga rungume da jaririn can baya kuma Habeeba ce da Nurses zaune gefen ta sai direban da zai ja su.
Sosai da sosai likita ke tausayin su a zuciyarsa sai faman gyaɗa kai yake yi har ya ga tashin su suka bar harabar asibitin…Kamar wacce aka watso haka ta fado cikin gidan, kallo daya za kayi mata kayi tunani rainon dawanau ce gabadaya yana yin jikinta ba shi da maraba da wacce aka durbuɗe cikin jar kasa ana cakudawa har sai da aka ga ta canza launi aka sake ta.+
“Ahayye Yaro Ahayye Yaro,
A ƙyawu wata tafi wata a taku koni nafi”.
Waƙar da take ta faman yi kenan da tayi tafiya daya biyu za ta tsaya tana girgiza kugu gami da tafa hannu a haka har ta isa kofar daya daga cikin dakunan gidan ba sallama ta bankaɗe labule ta faɗa.
Goggo Marka dake zaune tana faman ƙadin zare zumbur tayi tana shirin arcewa don ba karamar tsoro taji ba wani irin kallo ta watsa mata bayan ta ga wacece.
“ke kam an yi ‘yar wofi wallahi ai wannan sai ki tsinkar min da gaba”.
turo baki tayi gama tana mai galla mata harara.
“Uhmm nikam Goggo ki daina ce mani ‘yar wofi”.
“ke dalla jaye ki bani waje yar banzar ‘ya mara hankali”.
“nikam ba ‘yar banza bace”.
ta fadi tana mai yatsine fuska.
Juyawa tayi zata fice daga cikin dakin da sauri Goggo Marka ta dakatar da ita ta hanyar cewa,
“haba ‘yar gidana ba ma haka dake, ina kuma zaki je?”.
ko sauraron ta bata yi ba ta kara azama wajan ficewa daga cikin dakin da sauri ta mike ta riko hannunsa cikin karya murya.
“haba hafsatutuna yar gidan Mati da Abulle jikanyar Goggo Marka yar gaban goshin Danliti kar kiyi fushi mana”.
Da alamun kirarin da akayi mata ya yi mata dadi shagwaɓe fuska tayi.
“Nikam in har kina zagina zan bar zuwan gidan ki ke kenan kullum zagin mutum”.
“yi hakuri na daina, yo ai kece da turawa mutum haushi ba ki iya abin hankali ba amma dai yi hakuri zo mu zauna in ji abin da ke faruwa”.
ba musu ta koma cikin dakin ta zauna ta shiga jayo kayan kaɗin Goggo Marka tana kokarin batawa da sauri ta buge mata hannu.
“nifa tsiya ta dake kenan ba kya gani ki kyale sai kin taba”.
harara ta galla mata.
“kwarankwatsi zan daina zuwa gidan ki ke abu kadan sai ki daki mutum ko ki zage shi”.
Hafsatu jikan Goggo Marka ce ba ta ji sosai da sosai rashin jinta ya wuce inda kake tsammani kullum cikin kawo wa uwarta korafi ake yi duka kuwa kullum cikin shan sa take amma ba abin da yake sauya zani ba wanda bai santa ba cikin kauyen nan iyaye da yawa ba sa son suka ga ‘ya’yansu da ita domin rashin jin ta da kangarewrta sau da dama in tayi laifi bata zaman gida domin tasan halin uwarta jibgarta take yi kamar Allah ne ya aiko ta shiyasa da tayi laifi sai ta kwaso jiki tayo gidan Goggi Marka wacce ita ce bata ganin laifinta ko fada ta tsokano in dai ta zo wajan ta sai dai ta balbale wanda ta tona da masifa da zagi a wajan Goggo Marka ta samu daurin gindi take tsula tsiyar ta yarda take so sai dai kuma wani abu dake faruwa tsakaninsu duk son da Goggo Marka take yi mata bai hana a dinga jin kan su ba kullum in har ta zo gidan ba ta barin sa ba suyi fada ba Goggo Marka bata da hakuri sam kamar zawo ita kuma Hafsatu ba ta ji kamar ‘yar Allah bani.
Mikewa Hafsatu tayi tana kokarin ficewa daga cikin dakin da sauri ta ce da ita.
“ina kuma za ki je?”.
Cikin rashin baiwa maganarta muhimmanci tace.
“aƙwai zafi yasin dakin ki sosai ba zan iya zama ba, bari na zauna waje”.
STORY CONTINUES BELOW
ba ta tsaya jin abin da zata ce da ita ba, ta bankaɗe labulan ta fice nan kofar dakin ta samu kujera yar tsugunno ta zauna ta shiga sakin yan waƙoƙin ta na shirme a zaunan ma rawa take yi.
Mariya dake kunshe cikin daki cikin wani irin yanayi na rashin tsammani komai na rayuwa domin ta gama yankewa kanta ta rabu da uwarta kenan tunanin ta sai wansafo mata abin da yake wakana da uwarta yake yi aceqar ai ta jima da matuwa gawarta kawai za a kawo gida lokaci-lokaci hawaye da suka zama abokan zamanta a wannan lokaci sai faman zubowa suke amma ko ta kan su ba ta bi don ta tabbata ko dauke su tayi ba abin da zai ragu daga tashin hankali da take ciki saboda komai na duniyarta ya kwance mata.
juyi take yi lokaci lokaci abubuqa sai faman kara yawa suke na tunanin zuci masu tayar hankali.
kamar wacce aka tsikara haka ta mike zumbur cikin taimakon jarumtar zuci jiki kuma a sake ta miki sai faman tangaɗi take yi kamar wacce ta baje aka idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kamar wacce akayi wa surace da barkonon tsohuwa sannu a hankali ta fara jan kafar ta har zuwa kofar dakin ta dage labulan ta fito ba ta lura da Hafsatu dake zaune ba can gefe guda ta shiga kokarin yin waje motsinta ne ya sanya Hafsatu dagowa daga abin da take yi ganin Mariya ya sanyata jan jaki domin ba shiri suke yi ba sam! Jininsu bai haduba.
sarai ta ji tsakin da aka ja amma ba ta tsaya daga tafiyar da take yi ba domin tashin hankalin da take ciki ya zarce ta tsaya neman ba’asi ko da bugun ta kuwa akayi a daidai soron gidan su ta tsinkayi tsayuwar Napep cikin wani irin karfi da bata san tana dashi ba ta kwasa yi waje a guje adaidai lokacin Mai Napep din ya tsaya turus! tayi ta tsaya ba tare da ta isa wajan da suke ba idanuwanta kuriii kan na mahaifiyarta abubuwa ne suka shiga yi mata shawagi akai gani take kamar ba gaske ba gani take kamar mafarki ne yake kokarin yaudararta.
ba ta san lokacin da Malam bello ya fito ba har ya biya mai Napep kudin sa Ya dubi Nurses.
“zaki kamo ta ku fito ko sai na taimaka muku”.
“barshi kawai shiga da jaririn cikin gida tukunna”.
Habeeba ya kalla har yanzu tana nan yarda take ba abun abin da ya canza domin tunda suka taho maganar duniya yayi mata amma ko tari bai ji tayi ba girgiza kai yayi gami da daukar hanyar cikin gidan Mariya da tajima cikin tunani ba ta san lokacin da ya iso ba ya dafa kafaɗarta firgigit tayi tana mai baza idanuwa kamar wacce zata arce kallon mahaifinta tayi da abin da ke hannunsa kanta taji yana juyawa gani takeyi kamar ba gaske gani take yi lamarin kamar ba faruwa yayi sai da taji ya ambaci sunanta tare da girgizata sannan ta tabbatar da abin da take zargi ta shiga duban jaririn ta na kallon mahaifinta murmudhi take ajjewa wanda bata san ya akayi ta samu damar yin sa ga ruwan hawaye sai kwaranyo mata suke.
Shima murmushin yayi mata wanda shi da ka kalle nashi bai kai zuci ba iyakarsa fatar baki.
“jeki ga Umman taki can”.
ba ta tsaya tanka masa ba tayi hanzarin barin wajansa ta nufi Napep in da ta hangi Nurse na kokarin fito da ita shi kuma ya fada cikin gidan.
tun kafin ta isa gabanta ya yi wani irin bugu lokaci guda taji wani irin yanayi ya ziyarce ta zuciyarta na sanar da ita an samu matsala, matsala babba.
da sauri ta isa gaban Nurse tana kallon ta cikin wani irin yanayi kamar mai son karin bayani kallon Ummanta tayi wacce ta zama tamkar rakumi da akala ba wani kuzari sam! a gareta sai yarda Nurse tayi da ita.
“NA SHIGA UKU!”.
Mariya ta fadi gami da riko Ummanta kallonta sosai Nurse tai jin abin da ta fadi girigaza kai tyi cikin yanayi na tausayi a haka suka rungumi Umma sukayi cikin gida da ita wacce a wannan lokacin sam bata san a ina take ba duniya ce ko lahira haka suka isa cikin gidan a lokacin Malam Bello ya fito daga cikin dakin ya na musu nuni da dakin ta ciki suka shigar da ita
STORY CONTINUES BELOW
Duk abin da ake yi Hafsatu tana nan zaune shanye da baki mamaki ne ya cika ta sosai ganin an shigo da Habeeba ya sanya ta saurin mikewa ta fada dakin Goggo Marka tana kiran ta.
“Goggo zo ki ga Umman Mariya ta haihu”.
dubanta ta shiga yi da mamaki don ita sam ta mance da cewa Habeeba na nakuɗa har sun ta fi asibiti cikin hanzari ta mike tana duban Hafsatu cikin murya kasa-kasa.
” wa ya ce miki ta haihu?”.
“yanzu naga sun shigo Malam rike da jinjiniya sai kuma wata mata ringome da Umman Mariya…”.
kuri tayi mata da idanu kamar mai son gano wani abu ita ma Hafsatun kallon ta tashiga yi cikin rashin abin yi
kwankwasa kofar da akayi ne duk ya sanya su zabura Goggo Marka ta kalli kofarta jin muryar Malam Bello wani takaici ya turnuke ta ba shiri ta saki hannun Hafsatu kamar bata san abin da ke faruwa ba ta bankaɗe labulan tana kokarin tura ashar harara ta saki gami da jan guntun tsaki juyar da kan ta tayi cikin dakin cikin kunkuni.
“gaskiya na shiha hakki wallahi, sai azo ai ta dannawa mutum sallama duk a firgita shi sai mutum yayu zaton mutuwa ce ta kawo farmaki”.
kasa-kasa tayi maganar amma sarai ya ji abin da take cewa ransa kuma ya sosi da maganar sai dai ya ki nuna hakan a fuska illa girgiza kai da yayi ya shiga kokarin yin magana.
“kiyi hakuri Goggo, dama zuwa nayi na sanar dake Habeeba ta haih…”.
dariyar da Hafsatu ta saki ne ya sanya shi kasa karasa maganar sa domin bai yi zaton tana cikin dakin ba sam!
ita ma Goggo Murmushi ta shiga saki, sai ka rantse na farinciki ne amma ina! ba haka bane duban sa tayi tun daga sama har kasa baki a kwaɓe.
“Ikon Allah. ashe shiyasa na ga sai faman ɓarin jiki ka ke yi kamar wanda ya ga sabuwar Amarya”.
Gyaɗa kai ya shiga yi jin maganganun da take fadi ya tabbata ba har zuci ba kawai magana ce a fakaice take dankara masa.
“Uhmm shi ne dama na zo na sanar dake…”.
bai dire ba, tayi saurin caɓewa.
“Gaskiya kam!”.
Ta sauke guntuwar maganarta ta da dubansa tana mai sakar masa yaƙe.
Shiru yayi yana ganin ikon Allah ran sa yayi matukar ɓaci musamman da ya lura dariyar da Hafsatu ke yi ta gayya ce da raini ita kuma Goggo ta hanashi sauke maganar da ya dauko nisawa yayi cikin haushi.
“ba wani babba don Allah Goggi ki zo ki yi wani abu”.
“…haka fa na manta ashe watan tashin asuba na da wankar jego ya kama Hafsatu zo muje zaman mursu”.
ta fadi tana mai duban Hafsatu da take ta faman dariya
Baki ciki iyaka Malam Bello ya shaka ji yake kamar ya fada cikin dakin ya shago Hafsatu ya jibga ko ya rage jin haushi amma ba damar haka don ya tabbata in har ya dake ta yau sai kowa ya ji a gari ga abin da yayi cikin rashin abin yi ya juya ya bar kofar dakin yana mai cizon laɓɓa.
Isar sa cikin dakin ya tadda Nurse ta gyara ko ita da taimakon Mariya wacce natsuwarta rabi da kwata ba ta tare da ita tana ga Ummanta wacce take girke waje guda ba Uhmm ba uhm-uhmm.
“ya kamata ace anyi wani abu izuwa wannan lokaci”.
Cikin rashin fahimta ya dubi Nurse yaka faman gyaɗa kai.
“kamar me kenan?”.
ya fadi cikin raunin murya da rashin abin yi domin ya tabbata kayan bukata ake nema wanda ya tabbata ba shi da karfin yin su don ko wuka za a daura masa a makoshi baya magani kudin da za ace za ayi bukatu na azo a gani.
“ya kamata ace izuwa yanzu an yiwa jiririn nan wanka itama.uwar kanta ta gyara jikin ta sannan kuma da abubuwan da za ta sanyawa cikinta”.
tun da ta dora zancenta yake faman binta da kallo yana gyaɗa kai cikin rashin abin yi ita kan ta Mariya kallon Nurse take yi domin abin da taji tana fadi to ta tabbata mahaifinta bai da wannan halin a yanzu haka ita sheda ce.
kamar wacce aka tsikara ta mike tayi tsakar gida gindin murhu ita isa ta janyo guntayen itace da karare ta hada ta tada wuta ganin wutar ta kama ta mike da sauri ta dauko katuwar tukunya wacce rabon da ta ga wuta anjima daurayeta tayi taje ta daura kan murhun sannan ta shiga debo ruwa tana zubawa a hankali har ta cika ta fam ta sanya murfi ta rufe tana mai sakin ajiyar zuciya tana bin tukunyar da kallo abubuwa da yawa suna yi mata yawo cikin kwakwalwa tausayin iyayenta sai kara raunata ta yake yi ji take yi kamar ta fice domin samo abin bukata sai dai tana tunanin in ta fita ina zata je wajan wa zata ba ta sani ba ita ba namiji bane balle taje tayi aikin karfi domin sabun abin taimakawa iyaye ita ‘ya mace ce kuma rauni gareta tana tsoron abin da zai kawo wa rayuwarta farmaki hawaye suka zubo mata hannu ta saka ta dauke su ta sake duban murhun wutar taga tana kokarin mutuwa da sauri ta durkushe tana hurawa da baki amma kamar kara kashe wutar take da sauri ta mike ta nemo wani yagalgalallan mahuci ta shiga fifitawa amma ina ba alamun wuta zata ci domin itacen yayi karanci sosai da sosai da sauru ta mike tayi waje yaye-yaye na ledoji da duk abin da ta san zai ci wuta tayo ta dawo ta shiga cusawa cikin murhun hayaki ya turnuke sosai nan da nan ta shiga tari idanuwanta suka kara rinewa zuwa jajaye suna zubda hawaye amma hakan bai hana ta kokarin tayar da wutar ba dakyar da gumin goshi wutar ta tashi bayan ta gama sharafin ta na hayaki ganin wuta ta kama ganga-ganga ya sanya yin zaman dirshan a wajan ta zabga tagumi tana kallon ikon Allah.
Abubuwa take tunawa marasa dadi a rayuwar nan tun da ta fadi duniya ta tsinci iyayenta cikin wannan hali na rashin dadi tana bukatar fidda su daga cikin ƘANGIN RAYUWA sai dai ta rasa ta ina zata fara tana si ta samowa iyayenta YANCI amma ta rasa mai ya dace tayi ita yarinya ce amma kuma ta fara fuskantar matsalar rayuwa tun kafin ta kai haka in ana haddace matsalolin rayuwa ya kamata ace ta haddace su akana ta rasa tana ina zata fara kokarin tunkaran rayuwar nan domin samo wa iyayenta farin ciki Sannu da kokari Mariya, Allah ya yi miki Albarka”.+
Kamar daga sama ta jiyo sautin mahaifin nata ya na furta kalaman.
da sauri ta shiga goge fuskarta tana faman ajje numfashi da kyar sai da tayi kokarin samowa kanta natsuwa sannan ta taso tana mai dubansa tana faman sakin yaƙe kamar wacce aka cewa in bata yi ba ranta za a dauka.
“bari na fita naga yarda Allah zai yi damu”.
ya sake magantuwa idanuwansa fes akanta yana faman gyaɗa kai cikin yanayi na tauyasawa dukkan nin su.
Sai da ta ajje numfashi mai rauni sannan ta nisa.
“Allah ya kiyaye hanya”.
tana fadin haka ta shiga kokarin gyara wutar da ta hura domin ba ta son wata magana ta sake shiga tsakaninsu don kukanta a wuya yake in kuwa ta fiye magana komai zai iya faruwa.
tana jin ta kusan sa har ya fice sannan ta saki ajiyar zuciya cikin ta cikin hali na sanyi ta ja shi domin kowa wajan mahaifiyarta tunanunnuka birjin cikin ranta.
“Ahhhh ashe dai ba haihuwar guzuma akayi ba”.
Goggo Marka da ke tsaye tun dazu tana kare musu kallo da yatsine yatsinan fuska ta fadi haka lokacin da Mariya ke kokarin shiga daki.
ba ta fahimci in da maganar ta dosa ba amma dai ta sakawa ranta cin fuska akayi mata gyaɗa kai kawai tayi ta kalleta na yan sakanni ta dauke kanta.
“munahika ni kike kallo haka, mara kunya ‘yar masu baki hali kalle ni da kyau ba dai zagina zaki yi ba don wallahi kika zage sai na dake ki dukan shan gishiri”.
da sauri ta fada cikin dakin don ba za iya jurar sauraron maganganun Goggo Marka ba ranta yayi matukar baci amma ba ta bari hakan yayi tasiri a fuskarta ba ta bar wa zuciyarta bakinta dauke da Sallama ta shiga dakin har yanzu Habeeba na nan yarda take can gefe kuma Nurses ringume da jariri dake ta faman rusar kuka tausayi da jiƙan duk ya gama jikin ta jingina tayi da bango ta na ajje numfashi idanuwanta kan mahaifiyarta abubuwa da yawa sunayi mata yawo akai amma ta rasa matsayar da za ta ajje tunaninta komai ya cakuɗe mata ya cinkushe mata ta kasa gane lamarin dake faruwa gabanta na faduwa sosai da sosai wanda ta hakikance akwai abin rashin natsuwa da yake shawagi cikin duniyarsu a yanzu.
Duban ta take yi cikin rashim abin yi komai ya kwance mata laɓɓanta sai rawa suke yi alamun ta na son cewa wani abu amma ta kasa hakan hawaye sai ambaliya sukeyi zuciyarta na tukuki ba abin da ke shawagi a kanta illa rayuwar da take ganin tana tunkaro su wacce ta hakikance ba tabbanci kayan kwanciyar hankali acikin ta sai wani nufi na Allah.
“gafaran ku dai masu jego”.
Muryar Goggo Marka ta karaɗe cikin dakin ba wanda ya dubeta tsakaninsu har ta gama shan sharafin ta sannan ta kaea tsakar dakin ta samu waje ta ajje kugunta tana mai duban Habeeba wacce take rakuɓe waje guda ta juya wajan Nurses dake ta faman jijjiga jaririn ta shiga yashe baki kamar gaske.
“kai Masha Allah mikon min shi nagan shi”.
ta fadi tana mai turawa Nurses hannunta da ta bata jaririn ba musu ta mika mata ita ma tana faman yashe baki amma ba kai zuci ba tunani ne ya ke mata shawagi cikin kai akan Goggo Marka don bata yi tsammanin akwai wata mace a gidan ba tunaninta kawai su Mariya ne gyaɗa kai tayi gami da ajje tunanin gefe ta shiga kokarin mikewa tana mai duban Habeeba .
“ni bari na koma bakin aiki tunda Baaba ta iso ko”.
ta fadi kamar mai son taji wata magana daga wajan Habeeba amma kamar a ajje dutse ko motsi sai Goggo Marka ce ta magantu.
STORY CONTINUES BELOW
“Ahhh ya haka kuma na dauka kece mai zaman wanka”.
Cikin rashin fahimta Nurses ta shiga dubanta tana mai gyada kai tunaninta na dazu yana kokarin rugujewa akan Goggo Marka a tunaninta a gidan take zaune ashe ba haka bane barka ta zo yi gyaɗa kai ta sake yi sannan ta nisa.
“A,a bani ba ce ni ma’aikaciyar asibiti ce”.
Kau da kai tayi ba tare da ta ce komai ba hakan da Nurse ta gani ya sanya ta isa kusa da Habeeba ta dafa kafadarta tana mai faman rausayar da kai tausayin ta sai kara tsargar mata yake tsayin mintina daya ta dauka sannan ta fara kokarin barin dakin bakin ta na yi musu fatan alheri.
Bayan fitar Nurses Goggo Marka ta numfasa tana mai duban Habeeba domin zuciyarta sai faman tsegumi take mata akan yanayin da ta ganta a ciki.
“na ganta cikin wani yanayi, me ke faruwa?”.
ta fadi tana mai kallon Mariya itama Mariyar ita take kallo cikin rashin abin cewa numfashi take ajje a hankali zuciyarta na faman harbawa kamar zata faso kirji ta fito.
“dake fa nake kika yi mani banza, komai halin kurmantaka kuke ne yau ke da uwar taki”.
“…uhmm nima ban sani ba”.
Cikin ci da zuci ta furta haka tana faman jingine kanta da bangon dakin domin wani iri take ji duniyarta na yi mata sai shawagi kanta ke yi kamar wata waina cikin tadda.
“kamar ya baki sani ba, nifa munafurci ne bana so kin ji ko”.
zuciyarta ta fara gajiya da lamarin Goggo Marka matuka. ji take yi muryarta nayi mata shawagi kamar zata tarwatsa mata kwanya cikin gajiya ta mike ta fice daga cikin dakin.
Hakan da Goggo Marka ta gani ya sanya ta sakin tsaki gami da kwaɓa.
“kin shiga uku da bakin halin ki”.
ta juya tana kallon Habeeba sosai da sosai take kallon ta tana son gano wani abu dake boye amma har tagama hangenta bata hango komai ba sai halin shiri da ta tsinta wanda ta rasa dalilinsa gyaɗa kai tayi gami da ajje jaririn kusa da Habeeba ta mike tana gyara daurin zaninta sai da ta karewa dakin kallo sannan ta fice.
Mariya durkushe bakin murhu sai faman kokari take domin ganin ruwanda ta daura yayi zafi ko da bai tafasa ba ta san hakan yafi babu haka ta cigaba da gyara wutar har zuwa wani lokaci cikin Ikon Allah ruwan ya tausa sosai da sosai da sauri ta mike ta nufi dakin Goggo Marka gaban na bugu domin ta rigaya tasan da kyar ta samu komai a dadin rai a wajan ta.
“ruwan ya tafasa”.
Dakyar ta furta hakan yanayi na rashin abin da za taji daga bakin Goggo Marka ilai kuwa magana ta caɓamata.
“ni meye nawa a ciki, na dauka tun da kika iya dafa ruwan wanka jego na ai za ki iya wankan ma”.
maganar tayi mata kuna a rai amma ba nuna haka a zahiri ba sai ta shiga sakin murmushin yaƙe tana faman gyaɗa kai.
“Uhmm Goggo kenan ba wai nayi gaban kaina ba ne kawai gani nayi hakan ma rage wani aiki ne…Uhmm ni dai rokona ki taimaka kiyi mata wankan”.
ta karashe cikin taushin murya mai cike da rarrashi.
dubanta take yi sosai tana jin maganganun da take fadi ta juyar da kallon ta zuwa ga Hafsatu dake yashe bisa gado tana faman kallon su.
“Amma dai…”.
“…Don Allah Goggo ki taimaka”.
Mariya tayi saurin tare ta tana mai hada hannayenta waje guda alamun roko idanuwanta tsaf! akan ta tana faman juya su kamar mai son fashewa da kuka.
Ba wanda ya tsake tsinkawa a tsakaninsu tsayin mitina uku sannan Goggo Marka ta mike ta fice daga cikin dakin Mariya na biye da ita har wajan murhun suka isa ta duba ruwan sai faman tafsa yake yi ta juya ta dubi Mariya.
STORY CONTINUES BELOW
“ni dai ba zan iya kwashe wannan tafasasshen ruwan ba tsakani har ga Allah don ba zan babbaka kaina ba”.
Gyaɗa kai Mariya tayi kafin tayi nishi.
“bari in kwashe ni zan iya”.
Ta fadi cikin sanyin murya mai dauke da rawa sosai cikin karfin zuwa tayi wajan dakin Ummanta wani babban daro ta dauko wanda suke wanki dashi ta girke gindin murhun sannan ta bude tukunyar ta saka kofin da ta dauko ta shi ga kwashewa tana zubawa cikin dauro a hankali duk da ruwan na fallatsar mata a jiki amma hakan bai hana daurewa ba ta cigaba da abin da take yi sai da ta ga ta zuba sosai kwatankwancin yarda zata iya dauka sannan ta kinkima tayi hanyar bandakin su wandake zagaye da langa-langa ta ajje ta fito nan ta cigaba da kwashe ruwan a wani botiki tana kaiwa tana zubawa har sai da ta cika sannan ta tsagaita ta dubi Goggo Marka da ke tsaye tun dazu tana kallon abin da take yi.
“na kwashe”.
“to yanzu ya za ayi kenan maganar ganyen wanka”.
Shiru Mariya tayi shaf ta mance da ganyen wanka da ake amfani dashi ko dayake ba abin mamaki bane rashin sanin haka gareta tun da ba sanin yarda ake yi tayi ba gyaɗa kai tayi cikin rashin abin yi.
“Goggo kawai ayi mata ako da tsumma ne domin naji ana cewa nayi dashi tun da lokaci ya kure in za ayi mata na yamma sai a samo ganyen ko”.
Yatsine fuska tayi gami da kau da kai.
“a ina kika taba jin anyi haka”.
Cikin sauri ta amsa mata.
“a rediyo naji ana hira in mace ta haihu za ta iya wanka da tawul ba dole sai ganye ba”.
sakin baki tayi tana kallon ta cikin mamaki.
“iyee Al’adun yahudawa kenan kike nufi za mu koma yi to ni dai ban san wannan falsafar taki ba ni dai A AL’ADATA ta hausa fulani da ganyen dogon yaro nasan ana wankan jego da wasu kuma dangin nau’ikan ganyayyaki domin akwai wani sirri da suke dauke dashi ni ban san wani ayi wankan jego da tsumma ko tawul ba…”.
“Don Allah Goggo ki taimaka”.
Mariya ta tare ta ganin tana kokarin cinye mata lokaci da suke dashi har ruwan wanka ya huce.
“ni fa ba zaki sakani yin al’adun yahudu ba in har ba za a samo ganyen wanka ba to ba dani ba”.
tana gama fadin haka ta fara kokarin shigewa dakin ta da sauri Mariya ta shagabanta ta shigayi mata magiya da rantsuwar cewa in tayi mata wannan ba zata sake yi mata ba ba tare da ganye ba magiya sosai tayi mata sannan ta yarda.
Mariya da kanta ta shiga dakinsu ta riko Ummanta domin ita Goggo ta ce sam ba zata taba jikinta ba haka da kyar da gumi ta fiddo ta daga cikin dakin sai faman nishi take yi domin gabadaya jikin Ummanta a sake yake ba abin da take yi sai yarda akayi da ita a haka har ta isa bandakin da ita kan wani dandamalin dutse dake tsakar bandakin da suke zama kan sa suna wanka.
Ficewa tayi ta ba su waje ta koma can kofar dakin su ta zauna tare da zabga tagumi abubuwa sai mata shawagi suke mara dadi da armashi kamar wacce aka tsikara ta mike da sauri tayi cikin daki can in da jaririn ke kwance ta isa ta dauke shi gami da rungumeshi tana jin wani irin a zuciyarta tausayin sa take ji da yanayin da ya samu duniyar aciki ta tabbata yarda take rayuwa haka in shi ma ya tashi zai yi sai dai ba za ta so haka ba za ta so ace rayuwarsa ta fice daban da tata da take yi zata so ace bai fuskanci wani matsi ko ukuba ta rayuwa ba za ta so ace ya tashi cikin kwanciyar hankali da muradan farinciki cikin duniyarsa sai dai ba tabbacin haka zata kasance sai wani iko na Allah domin za ta iya cewa yanzu shigo ya ga rayuwar duniyarsa tun daga fadowarsa ya fara ganin rikicin duniya.
Nisawa tayi gami da mai dashi ta kwantar ta fice daga cikin dakin wani karamin bahon wanka ta dauko ta zubo ruwan zafi ta sirka yarda take tunanin ba zai cutar dashi ba ko ya haifar mata da wata matsala dakin ta koma ta ajje ruwan sannan ta dauko shi zuciyar ta na faman buguwa tana tsoron abin da zai je ya dawo domin har kasar ruhinta tsoro ne fal ta yarda zatayi wa jariri wanka abin da bata san ya ake yi ba amma dai zata gwada ta gani domin ba zata iya barin kanin nata cikin wannan yanayi ba an haifeshi kusan a wanni amma ko ruwa vai gani ba.
Tsunbulashi tayi cikin ruwan cikin yanayi na faduwar gaba aiko sai ya saki kuka lokaci guda da sauri ta zare shi jikin ta na faman kyarma ta shiga kallonsa idanuwansa bude sai faman lumshe su yake yi kamar mai jin barci sake saka shi tayi sai dai a wannan karon bai yi kukan ba illa ajiyar zuciya da yayi hakan da ta gani ya bata kwarin gwuiwa fara wanke masa jiki a hankali haka ta cigaba da yi ko sabulu babu sai da ta wanke masa jiki sosai da sosai har sai da taji ruwan ya fara sanyi sannan ta zare shi daga ciki cikin kayanta ta dauko wani zani mai dama-dama ta sakashi aciki ta nannade.
Kiran ta taji Goggo Marka nayi da sauri ta mike rike da jinjirin ta yi waje tsaye ta tadda ita tayi jage jage da ruwa.
“ki je ki fito da ita”.
nar-nar tayi da ido kamar mai son fashewa da kuka.
“don Allah Goggo ki taimaka ki fito da ita wallahi ban zan iya ba dazu da kyar na samu na fito da ita kuma kin ga yaro ne a hannu na yanzu na gama masa wank…”.
ai ba ta dire zancen nata ba taji ta dauki sallallami tana tafa hannu kamar wacce ta ga mugun abu.
“Mariya wanka fa kika ce ke yanzu har kin san yarda za kiyi wa jariri wanka”.
nan da nan jikin ta ya fara rawa hawaye suka fara sankoma mata dama abin da take gudu kenan abin da take tsoron faruwarsa kenan Allah yasa ba wani abu ne zai same shi ba Allah ba ganganci tayi ba cikin rawar baki ta fara magana.
“Wallahi Allah ban yi…”.
cak! ta tsaya da zancen ta ganin Mahaifinta tsaye bakin kofa yana kallon ta nan da nan faduwar gabanta ya karu musamman da taga ya kafe da idanuwansa…