UKU BALA’I CHAPTER 12
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsaye yake jikin motarsa ya harɗe hannayensa saman kirji idanuwansa sunyi mici-mici alamun bacin rai duban ta yayi a karo na ba adadi ya na jan tsaki kamar harshensa zai tsinke.+
“Baki da hankali Hafsat na lura kan ki rawa yake yi dakikanci da jahilci su ne suke karanta miki karatun hauka kika zo kina sauke mani to ba zan dauka ba don na rantse da Allah na fiki tashanci duk akuyancin ki”.
Ya fadi yana mai kara tsuke fuska Hafsat dake tsaye sai faman jinjiga take yi kamar wacce ake kaɗawa gangi duban sa tayi sosai cikin takaici da rashin abin yi.
“Huzaif haka ma zaka ce dani ga mari ga tsinka jaka to wallahi ba ka isa ba kayi kadan an gaya maka zan dauki rainin wayon ka ne duk wani ihukan banza da zakayi mani wallahi ba za suyi tasiri akai na ba”.
Tun daga kasa ya fara kallon ta yana yatsine fuska kamar wanda ya ga sabon kashi sai da yayi mata kallon tsaf! Sannan ya tsartar da yawu ya juya yana kokarin buɗe motarsa ya shi gami da fadin.
“In da na san wannan haukar zakiyi mani da kika kira ni wallahi ba abin da zai kawo ke na rantse da Allah da ga yau zamu raba jaha don ba zaki dauko kamayamaya ki jona min ba ina zaune kalau ki jaza min salalar tsiya an gaya miki ban san halin da kike ciki bane ban san abin da kike yi bane wato gani karkatacciyar kuka mai dadin hawa ko to kin yi kadan Huzaif daban yake ba irin mazajen da za ki wanke tas! bane”.
Ganin da tayi yana kokarin faɗawa cikin motarsa da sauri ta zabura ta isa gareshi gami da rike murfin motar da ya buɗe kallon ta yayi ido cikin idanu itama kallon shi take yi kafun ta kau da kai.
“Kasan Allah Huzaif yarda muka dama tare da kai wallahi sai mun shanye shi a filin duniyar nan ba wani na miji da nake hulda dashi sama da kai kaima kasan haka amma saboda tsabar ka raina mani wayo shine zaka nuna min halin-ko-in-kula gaskiya da sake”.
Kallon ta yake yi sosai cikin tsana da takaici wai har wannan kucakar yarinyar ce za ta dubi tsabar idanunsa tana masa rashin kunya shi kam! bai san tsautsayin da ya hadashi da wannan mahaukaciyar yarinyar ba har sukayi tarayya bai san ina tunaninsa ya shiga ba bai san ina hankalinsa da lissafin sa suka fada ba har hakan ta faru a gareshi.
Daga hannu yayi kamar zai kwaɗa mata mari da sauri ta ja da baya tana mazurai hakan da ya gani ya bashi daman faɗawa cikin motar da sauri yana kokarin rufewa ita kuma tayi hanzarin riko murfin saura kadan ya datse mata hannu kallonsa take idanuwanta sun kada sunyi jajir kwalla sai surnano mata suke yi kau da kai tayi cikin raunanniyar murya.
“Huzaif bai kamata kayi mani haka ba kai kan ka ka sani ba ni da wani wanda muke hulda dashi sai kai amma na ga kana kokarin baɗa min kasa a ido kana kokarin bari na da masifa da bala’i ya kamata kayi tunani mana…”.
Wata tsawa ya daka mata gami da zaro idanuwansa waje da sauri ta saki murfin motar ta ja baya fitowa yayi gabadaya yana nuna ta da yatsa bakin sa sai rawa yake yi kamar wanda zai ci babu.
“Karki sake karki soma don wallahi in har kikayi kokarin laƙa mani wannnan abin kin ji na rantse danginku gabadaya sai na daure su har igiya tayi rara don ba zan dauki Nosense things din nan ba”.
Kallon sa take yi cike da mamaki maganganunsa ne suke mata yawo a kwanya ji take yi jiri na kwasarta kamar zata watse a kasa runtse idanu tayi don ba ta gasgata wai Huzaif bane ya daka mata tsawa har yake fada mata wadannan kalamai ina ba zai taba yuwuwa bane.
Buɗe idanuwanta tayi sosai akan sa tana dubansa.
“Kasan Allah Huzaif baka isa ba”..
STORY CONTINUES BELOW
Ta fadi tana takowa gareshi wuyar rigarsa ta cafka ta rike gam! ta shiga zazzaga masa rashin mutuncin tana faman firirita da girgije-girgije takaici ya kule shi bai san lokacin da ya dauketa da wani wawan mari ba
wanda ya sanyata sakin kara ta runtse idanu wasu taurari ta ga su na yi mata yawo a saman kai gabadaya ji tayi duniyar na juya mata buɗe idanunta tayi hannayenta dafe da kunci kallonsa take yi da wani irin yanayin wanda bata taba zaton zata samu kanta a cikin ba wai Huzaifa ne ya mareta ina mafarki ne wannan ba gaskiya ba zata so ta farka daga
wannan dogon malalacin barcin da take yi laɓɓanta ta tura cikin baki gabadaya cizawa tayi jin zafi ya sanyata tabbatar da cewa eh da gaske ne komai ke faruwa.
Juyawa tayi tana duban layin nasu mutanan da suke kai kawo ta hango suna kallonsu hakan yayi matukar bata mata rai ba ta san lokacin da ita ma ta fidda hannu ta zabga masa mari ba tana faman huci kamar wata kububuwa idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kwallar da take makale da ita ta sake zubowa.
Shikam! A bazata yaji marin hakan ba karamin rikita shi yayi don sosai ya ji marin hannu ya saka da sauri ya shafi kuncin nasa sannan ya dubi hannun nasa mamaki ya turnuke shi tare da bakin ciki da takaici yau karo na biyu kenan a duniyar nan ‘YA MACE na daga hannunta ta na marin sa bai san mai ya sa ba kuma abin takaici kananan yara kamar
wadannan kuma yan gida daya runtse idanu yayi zuciyarsa na shiga wani irin kunci hannunsa ya sake kai wa fuskarsa ya shafi wajan da ya ji marin kafin ya buɗe lokaci guda ya cafko wuyan ta ba tare da tayi zato ba sosai ya rike mata makoshi ta shiga kakari idanunta sukayo waje sosai dukansa tashiga yi amma ina ko a jikinsa sai ma idanunsa da ya saka cikin nata cikin tsantsar bakin ciki da jin haushi.
Sai da ya ga numfashin ta na kokarin kufce mata sannan ya watsar da ita akasa ta baje tana faman rike wuyanta sai murkususu take yi da sauri ya fada cikin motarsa ya ja ya bar layin.
Izuwa lokacin sosai mutanan layin sukayi cincirindo suna kallon ikon Allah ba wanda yayi kokarin zuwa ya kwace ta domin sun jima da sanin halin rashin kirki irin na Hafsat kuma akan idanunsa mafiya yawan lokaci Huzaif yake zuwa ya dauke ta ya fita da ita ba irin bakin halin da ba su sani ba da rashin mutunci da suke yi ita da Huzaif.
Mariya dake tsaye tun dazu bakin kofa idanuwanta na faman tsiyayar da hawaye takaici duniya duk ya gama cika mata zuciya hawaye sai faman safa da marwa suke yi takaici take yi yarda ɗa namiji yake
wulakanta mata yar’uwa a gaban idanunta girgiza kai ta shiga yi abin na ci mata rai ba ta son abin da zai sake daga mata hankali a wannan matakin wanda take ciki ma ya ishe.
Ba tayi mamakin abin da Huzaif yayi ba don kadan daga aikin sa sosai take tuna kalamansa a ranar farko da suka fara haduwa sosai take tuna
yaudararsa da yayi mata baza ta taba mantawa ba hannu ta sa ta shafe fuskar ta a hankali ta shiga takowa zuciyarta na kara curewa waje guda har ta iso wajan da Hafsat take durkushe tana ta faman rusar kuka dafa kafaɗar tayi.
“Bai kama ta ki zauna kan layi kina kuka ba wannnan ba mutuncin ki bane sannan bai kamata ki zauna kina fada da namijin da kika san yafi karfin ki ba…”.
Wata irin tsawa ta daka mata gami da bige mata hannu da sauri Mariya ta ja baya tana dubanta cikin mamaki dago idanuwanta tayi wanda suka gama kaɗawa sukayi jajir ta watsa mata wani mugun kallo.
“Ina ruwan ki ko gayyarki nayi tsohuwar munafuka duk ba dake aka hada baki aka kashe mani rayuwa ba kuma wallahi ki rubuta ki ajje yarda na gamu da bala’in nan ke ma ki tsumayi naki don ba zan shiga duniyar takaici ni kadai ba”.
STORY CONTINUES BELOW
Da sauri Mariya ta waro idanuwa waje tana ambatar ‘Innalillahi wa inna ilair raji’un’. juyawa tayi ta dubi mutanan da sukayi cirko-cirko suna kallonsu wani takaicin ya sake kular da ita da sauri ta bar wajan
idanuwanta na zubda hawaye ta fada cikin gida sai faman jan numfashi take yi kamar ranta zai fita.
Umma dake zaune ta dube ta ganin yanayin da ta shigo ya sanyata mikewa ta nufi cikin dakin zube ta hangeta saman katifa sai faman numfarfashi take yi.
“Lafiyar ki kuwa Mariya me ke damun ki ne haka?”.
Dago jajanyen idanuwanta tayi ta dubi Umma tana faman cizon laɓɓa.
“Hafsat ga ta can a waje suna dambe da namiji Umma mutane sun hadu sai kallon su suke yi”.
Gaban Umma ne ya yanke ya fadi tana ambato innalillahi gami dafe kirji idanuwanta a waje.
“Fada fa kika ce?”.
Kai ta daga mata gami da komawa ta kwanta zuciyarta sai nukurkusa take yi kanta na faman juya mata.
Jikin Umma sosai yayi sanyi a hankali taja jiki ta koma ta zauna gefe guda gami da zabga tagumi abin duniya duk ya damu yayi mata yawa tausayin Hafsat take yi tun lokacin da ta lura da halin da take ciki duk da Goggo bata fada mata ba amma ita ta gane ai irin wannan abun ba ya buya koman daren dadewa sai ya bayya abu daya take gudu shine Abulle ta sani don sai ta fi kowa shiga tashin hankali.
“Wai Umma me ke damun Hafsat ne yanayin da naji suna hayaniya da Huzaif kamar akwai abin da ya shiga tsakanin su ne wanda shi kuma bai yarda shine mai laifi ba…ko dai Hafsat…”.
Sai kuma tayi shiru ta kasa fadin abin da tayi niyya ganin irin kallon da Umma ta watsa mata na gargaɗi.
“Ba ruwanki Mariya ki kame bakin ki ban son abin tashin hankali wanda nake ciki ma ya ishe ni kin san dai halin Goggo yanzun nan ta sauke miki laifin…”..
Dago labulan da akayi ne ya sanya Umma saurin tsuke bakin ta Goggo ce ta fado dakin tana zuwa ta damki Mariya ta shiga jibga sai da tayi mata duka sosai Umma na kallo ba tare da ta ce da ita komai ba itama Mariya bata ko motsa ba.
“Wato ke saboda kin dauki mugun abu irin na dangin uwarki shine zaki saka saurayi yayi wa Hafsat cin mutunci akan titi haka ko to wallahi ba ki isa ba yarda kika sanya aka ci mata mutunci to wallahi ke ma sai kin samu daidai dake…”.
“A,a kam Allah ba zai taba daura mata laifin da bata san dashi ba ai duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan dako”.
Kamar daga sama suka jiyo muryar gabadaya suka juya da sauri Abulle ce tsaye idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kallo daya zaka yi mata ka gane tashin hankalin da take ciki mai girman gaske duban su tayi daya bayan daya kafun ta ja wani numfashi mai zafi ta dubi Goggo.
“Meye laifinta Goggo akan me zaki dake ta ai ba ita ce sanadi ba komai ya faru ita waccen maras hankalin wacce bata san darajar kanta da kimar ta ba ita zaki je ki daka saboda tsakaninku ne ku kukayi kidin ku kuma ku zakuyi rawar ku”.
Hawayen da take makalewa suka zubo zuciyarta take ji tana harbawa kamar zata faso kirjin ta ta fito ga wani irin nauyin da kanta yayi idanuwanta suna lumshewa a hankali taji duniyar na juya mata kokarin juya tayi domin fice wa amma ina lokaci guda kafafuwanta suka lauye suka watsar da ita akasa da hanzari umma ta isa gareta cikin tashin
hankali bata san lokacin da ta fashe da kuka ba dama ta san za ayi haka.
Jinjigata ta shiga yi amma ina ba alamun motsi a jikinta da sauri Mariya ta mike tayi waje da gudu ta kamfato ruwa ta kawo Umma ta watsa mata amma ina ba alamun motsawa duban Goggo tayi dake tsaye kamar wacce aka dasa sosai jikin ta yayi sanyi amma ta kasa tabuka komai.
Sake sheka mata ruwanta yi sosai wani numfashi ta ja kirjinta yayi wata irin harbawa da sauri Umma ta dagota idanuwanta da suke rufe ta buɗe su kadan hawaye masu tsananin zafi suka zubo mata laɓɓanta taa ciza cikin yanayi na takaicin zuci da ciwon rai ta shiga fadin.
“Allah na tuba Allah ka yafe mani laifinukana in har sanadin haka ka jarabe ni da wannan kaddara na gode Allah ka yafe mani”.
Wani kuka ne ya kwace mata ciki karfin hali ta shiga kokarin mikewa amma ina ta kasa komawa tayi ta zauna gami da jingina da bango tana mai runtse idanu zuciyarta take ji tana kartawa kanta na sarawa cikin wani irin tashin hankali wai ita ce yau ‘yar cikinta ta dauko mata abin magana abin da za ayi tur! da ita da zuri’arta abin da zai bi duk wani nata ana tsine musu ita kam! ya zatayi da wannna rayuwar Hafsat ta gama da ita ta gama kashe mata rayuwa.
“Kiyi Hakuri Zainabu ki dauki komai a matsayin rubutun ALKALAMIN ƘADDARA a gareki”.
Wani murmushi tayi mai ciwo tare da duban Goggo da tayi wuki-wuki kamar wacce tayi wa sarki karya ta kau da kai.
“Umman Mariya in ban yi hakuri ba ya zan yi cuta ce an gama cuta ta ba yarda zan yi wai ace ni ce yau ‘yar cikina ta dauko min magana ni dai na san ban yiwa iyaye na haka ba sannan ban cutar da ‘ya’yan wasu ba ban zalunci mijina ba”.
Girgiza kai ta ke yi domin ita kadai ta san tashin hankalin da take ciki ji take yi kamar ta hadiyi zuciya ta bar duniyar nan Takure take waje daya sai fama rusar kuka take yi idanuwan nan nata sunyi luhu-luhu kamar wacce aka watsawa barkono zuciyarta take ji tana zafi
gami da raɗaɗi wai ita ce Huzaif yayi wa haka mutumin da ta baiwa duk yardarta da kaunar ta ta mika masa duk wata ragama ta rayuwarta ta amince dashi ta yarda dashi amma yau ita ce yake daga hannu yana mari yana kiran ta jahila mahaukaciya kaicon wannan rayuwar.
Kuka ta sake rushewa dashi tana dukan cikin ta kamar wata sabuwar hauka Goggo ce tashigo a daidai wannan lokacin ganin abin da take yi ya sanya ta kurma ihu ta isa gareta tana rirrike ta.
“Haba Hafsatu kalau kike kuwa me ye haka kikayi?”.
“Goggo ki bar ni kam ki kyale ni wai ni Huzaif zai ciwa mutunci har da duka akan layi akan gaskiya”.
“Kiyi shiru nace miki ki kyale shi wallahi Allah sai ya gane bashi da wayo sai ya shaki bakin ciki kamar yarda ya shaka miki…”.
Abulle ta dago labulan dakin ta shigo fuskarta da wani murmushi wanda yafi kuka ciwo hannu ta harɗe a kirjin ta sai da ta kare musu kallo kafun ta nisa zuciyarta na kara suya.
“ai in har mutum yace son zuciya zai biyewa to tabbas yana tare da tsintar kan sa cikin takaicin rayuwa Goggo da ma kin dai cewa zaku dauki mataki ai aikin gama ya rigaya ya gama mai
yayi saura sai ta zauna a yarda take so ba dai haka ta zabawa rayuwarta ba ita ba wanda ya isa yayi mata magana ta dauke shi mutumin kirki ita sai dai ta zauna tayi son ranta to ai gashi nan ta gani a kwanon ta ba zan yi miki baki ba Hafsat amma za ki ji a jikinki da kuma duniyar rayuwarki ai duk wanda ya dama haka zai sha”.
Rushewa da kuka Hafsat ta sake yi tana rike kanta da take jin yana barazanar tarwatse wa ba abin da ke ci mata rai da tura mata bakin ciki sai yarda Huzaif yayi mata sosai
zuciyarta take suya da kuna sosai take jin zuciyarta na sake buɗe wani fili mai girman gaske wani irin mahaukacin so taji na kawo mata farmaki a zuciyarta mikewa tayi idanuwanta a runtse sai faman tagaɗi take yi kamar wacce ta kora kayan maye.
Da sauri Goggo Marka ta mike ganin tana kokarin ficewa daga dakin riko ta tayi tana mai cewa.
“Ina kuma zaki cikin wannan yanayin..”.
Bata idar da maganar ta ta ba ta fizge hannunta tana mai duban Goggo bayan ta buɗe idanuwanta hawaye sai ambaliya suke yi.
Hakan ba karamin kara batawa Abulle rai yayi ba ganin yarda Hafsat din tayi wa Goggo kamar wata
tsaranta mikewa tayi cikin tsananin bacin rai lokaci guda ta fidda hannu ta dauke ta da mari ji kake tas! ta sake kifeta da wani barin tayi tangal tangal tana kokarin faduwa dafe da kuncinta.
Duban Abulle ta shiga yi idanuwan ta buɗe sosai zuciyarta take zafi da wani irin raɗaɗi ga wani abu mai girma da taji ya tokare mata makoshi.
“Banza maras hankali wanda bata san ciwon kan ta ba Allah ya wadaran naka dai ya lalace wallahi ki ko kunya ba kiji ba ko nadama ba za kiyi ba akan abin da kika dauko wa
rayuwarki…ko da yake na lura har yanzu ba ki san ke wacece ba shiyasa amma akwai rana na nan zuwa zaki san Annabi ya faku”.
Bata tsaya sauraron jin kalaman Abulle ba ta bankaɗe labulan dakin ta ficewarta cikin tsananin tashin hankali mai girman gaske.
STORY CONTINUES BELOW
Kuka ne ya kwacewa Abulle da baya da baya ta ja ta jingina da bango zuciyarta sai faman kartawa take yi gabadaya al’amarin Hafsat ya bata tsoro yanayin da ta ga tana kallon ta yayi matukar caza mata kwanya ba ta san ya akayi ba bata san har yaushe Hafsat ta zama haka ba tana mata
magana amma yanayin kallon da take mata gabadaya ba wani alamun tsoro ko runsunawa a matsayin ta na mahaifiyarta anya kuwa ba laifi tayi wa Allah mai girma ba ya jarabe ta da Hafsat?.
Girgiza kai ta shiga yi ranar da take tsoro kenan a rayuwarta ranar da Hafsat zata so fin karfin ta a duniyar nan ba abin da ke daga mata hankali ya hanata natsuwar rayuwa kamar Hafsat duk cikin ‘ya’yanta ita ce
kangararriya kuma Allah na gani ba wacce ta zama sanadin komai sai Mahiafiyarta sosai abin ke taba mata zuciya tayi fadan tayi rarrashin amma ina ta nuna bacin ranta sai ma ake nuna tsanar ‘yarta take yi kaicon wannan rayuwa.
Dago kai tayi ta dubi Goggo dake zaune bakin gado ta zabga tagumi kallo daya zaka yi mata ka gane kamar abin bai wani ɗaɗata da kasa ba amma akwai alamun sanyi a jikinta musamman yarda ta ga Abulle ta shiga yanayin tashin hankali.
“Abin da nake ta faman tunasar dake kenan Goggo amma kin kasa gane wa Hafsat mace ce abu kalilan ne zai bata mata rayuwa sangartar da kike nuna mata da wai sunan so ne wallahi BA SO BA NE domin ba in da zai kai ta yanzu mai gari ya waya don Allah Goggo yanzu in wannan abin yafita mai kike zaton zai faru na rantse da Allah ko ruwa gagararmu sha zai yi”.
Gyaɗa kai kawai Goggo take yi tana faman turo baki gaba.
“Ai da rufe ni da duka kikayi shine zan san na bata miki rai ko kuma ni na saka Hafsat dauko mana magana a duniyar nan ai ba wanda ya kai ni bakin ciki kan wannan lamarin kuma ai ba kanta farau ba balle ta zama karau uban kowa yana da nashi kashin a gindin sa don haka ban ga wanda zai takura wa Hafsat ba akan abin da tayi ai ba da gangan tayi ba Yaudaren ɗa namiji ne ta gamu da ita da kuma makircin wadancan mutanen…”.
“Goggo!”.
Abulle ta fadi da muryar sauti don maganar tayi matukar tunzura mata zuciya da sauri ta mike ta dubi Goggo ji take yi kamar ta daura hannu akai ta kurma ihu ko ta samu saukin wahalar zuciya da zafin ruhi da take ji.
“Goggo ni ban ga amfanin daukar hakkin wanda ba su da laifi ba kuma na rantse da Allah in har kika ci gaba da tsanar su Mariya da uwarta
wallahi sai hakkin su ya kama ki domin na lura a duniyar nan ba wacce kika tsana kamar ita duk biyayyar da take miki da cin kashin da kike mata ba ta taba daga kai ta dube ki ba tunda ta shigo gidan nan abun dai daya ne matsalar ki take fama da ita kullum ba ta da sauki anya kuwa rayuwa za ta yuwu a haka”.
Tana gama fadin haka ta juya da sauri ta fice daga cikin dakin cike da tashin hankali mai girman gaske bata san ya za tayi yanzu ba bata san mai ya dace tayi ba ta san dai Allah kadai ne zai yi mata maganin matsalar ta Allah na gani bata da laifi ta san ƙaddara ce kuma ta ansa da wannan tunanin zucin ta fice daga cikin gidan
zuciyarta na harbawa da yarda zata tunkari mijinta da wannan al’amarin domin kuwa ya jima yana cewa Hafsat ta dawo gida amma ba yarda ta iya ta nuna masa yayi hakuri ba wani abu tun yana hakurin har yawan maganganun da ake yi akan Hafsat ya fara tunzura shi to ina ga yanzu yaji wannan bakin labarin.
****
Hafsat kuwa tun da ta fice daga cikin gidan ta dau hanya zuciyarta sai an gizata take yi akan kawai ta tafi gidan su Huzaif domin ba za ta iya zama ba a halin da ake yanzu dole ta je ta same shi duk wacce za a yi sai dai ayi
STORY CONTINUES BELOW
domin kuwa sosai take jin wani mahaukacin son sa na kara nakarkar mata da zuciya yana bubbuɗe mata duk wani sashi na jikin ta yana samun matsugun ni sosai take ta jin ta a tashin hankali wanda tun da take a rayuwarta ba ta taba zaton haka ba yau rana daya gabadaya komai ya kwance mata.
Kuka sosai take yi na zuciya domin hawayen sun ki zubowa tashin hankalin dake kara rikita ta shine yarda mahaifiyarta take kallon ta ta tabbata in kowa zai yi mata uzuri ban da mahaifiyar domin ita kadai ne ta san halin da ta tsinci kanta a ciki a daidai wannan lokacin.
Tafiya sosai tayi wacce akaran kanta ba ta san tayi taba ita dai ta san jefa kafafuwanta kawai take yi a in da taji sun sauka har izuwa lokacin da ta isa inda take zaton gidan su Huzaif ne sosai gaban ta ya shiga faduwa ba ta san mai zata ce ba bata san ya zata kalli mutanan gidan ba shin zuwa zata yi ta ce musu ɗan su yayi mata ciki ko ya ya.
Girgizai kai ta shiga yi zuciyarta na faman harbawa tsoro da fargaba duk suka dire mata lokaci guda numfashi ta ja kafun ta dubi tankameman Get din gidan a hankali ta kai hannu ta shiga kwankwasawa daga can ciki taji motsin ana zare sakata mai gadi ne ya leko ya dube ta sama da kasa ganin ta a hargitse alamun akwai abun da ke damun ta hakan ya sanya shi tambayarta ko lafiya?.
Hawaye ne suka balle mata da sauri ta dauke su sannan ta ce.
“Don Allah wajan mutannan gidan nan na zo wajan Mahaifiyar Huzaif”.
Sake kallon ta yayi sama da kasa kafun ya ce.
“Ko lafiya kike niman ta?”.
Runtse idanu tayi domin ita dai bata san abin da za ta ce da shi ba a halin da take yanzu in zai bar ta tashi kawai ya barta.
Gefe ya ja alamun bata hanya don ya lura tana wani mataki na tashin hankali a hankali ta shiga share fuskarta sannan ta saka kafar cikin gidan tana takawa zuciyarta na kara curewa waje guda tayi tafiya kadan ta ja burki ta tsaya a tsakar gidan tana mai da numfashi tunani kawai take yi ta yarda zata shiga gidan nan ba ta san a wani matsayi zata je ba ita kanta ya gama kulle.
A hankali ta shiga jan kafafuwanta tana mai da numfashi har ta isa babbar kofar da zai sadata da cikin falon Handle din ta rike ta murɗa idanuwanta a runtse gabanta na tsanarta bugu jin kofar ta buɗe ya sanyata tura kanta gaba gadi domin ta sadakar duk abin da zai faru sai dai ya faru.
Zaune suke kowannan su fuskarsa a cure da alamun bacin rai motsin shigowar da akayi ne ya sanya macen dake tafaman sababi ta tsagaita gabadayan su suka juyo suna duban Hafsat da tayi wiki-wiki kamar wacce tayi wa sarki laifi Huzaif da ke zaune can gefe yana ta faman kumbure-kumbure ganin Hafsat da yayi kamar daga sama bai san lokacijln da ya mike ba cikin yanayi na firgici da tashin hankali yana nunata da hannu bakin sa sai rawa yake yi.
“Ke! Uban me ya kawo ki gidan nan ban ce karki sake kokarin shigowa rayuwa ta b…”.
Tun kafun ya idar yaji saukar lafiyayyan mari yayi taga taga kamar zai fadi kasa hannunsa saman kuncin sa runtse idanu yayi kafun ya buɗe su akan mahaifin sa da ke tsaye yana ta faman huci da hannu ya nuna shi bakin sa na rawa magana yake
kokarin yi amma ya kasa tari ne ya sarke shi da sauri ya dafe kirjin sa ya koma ya zauna gami da runtse idanu a hankali tarin ya laɓa amma bai buɗe idanuwansa ba zuciyarsa yake ji tana faman zafi bai san abin da ke damun Huzaif ba gabadaya ya rasa gane kan sa sosai yake fuskarta matsala akan ɗa daya tak! da yake dashi.
“Ya akayi baiwar Allah?”.
Maihaifiyar Huzaif ta fadi tana duban Hafsat da izuwa lokacin ta fara dana sanin zuwa gidan su Huzaif
idanuwanta su ka kawo ruwa sosai hannu ta saka ta dauke su ta fara kokarin yin magana da sauri Huzaif yayi tsalle ya dire gabanta yana
famam tunkuɗata waje ita kuwa ta ki tafiya mahaifiyarsa ce ta iso ta riko hannun Hafsat ta dube ta cikin yanayi na rashin wasa.
“Na san ɗana zai iya yin komai don ya cutar dake tunda na ganki cikin wannan halin na tabbatar akwai abin da yayi miki ki faɗa min na rantse miki zan bi miki hakkin ki kuma daga kan ki zai gane hakki ba wasa bane da yake ganin daukarsa ba komai bane”.
Sosai Hafsat taji wani iri gabanta ne ya shiga faduwa tunanin take yi ta fadi kowa yaji in ta fadi tana da tabbacin zata iya samun abin da take so kuma zata iya rasa wa sannan in taki fadi ta tabbata Huzaif zai yi nasara a akanta.
Bakin ta na rawa hawaye na mata zuba sosai ta dubi Huzaif girgiza mata kai yake yi yanayin sa lokaci guda ya sauya tsoro sosai ya bayyana a
fuskarsa kau da kai tayi jin yarda zuciyarta ke kokarin tausaya masa da yanayin da yake ciki sosai take jin GURBIN SO da ta bashi yana kokarin rinjayar haushin sa da take ji.
“Uhmm dama…kawai dai”.
Sai kuma ta shiga taba cikin ta tana runtse idanu.
Mutuwar tsaye Mahaifiyar Huzaif tayi ta shiga ambaton innalillahi wa inna ilahiri raji’un shi kuwa mahaifinsa da ya buɗe idanu lokacin da ya ji Hafsat ta fara magana ganin abin da take nuna wa ba karamin kaɗa ‘yan hancin sa sukayi ba mikewa yayi cikin tsananin bacin rai da kunar zuciya.
“Ke muje ki kai ni gidanku yanzun nan Hajiya maganar gaskiya Huzaif na lura aure yake so kuma wallahi in har ina numfashi a doron kasar nan wannan lamarin shine na karshe wanda zai dauko mani ya hanani
kwanciyar hankali wallahi tallahi kin ji na rantse sai Huzaif ya auri wannan yarinyar ko da kuwa hakan na nufin numfashin sa zai yanke daga lokacin da na saka limami ya daura musu auren”.
Yana gama fadin haka ya fizgi hannun Hafsat yayi waje da ita ba Mahaifiyar Huzaif kadai ba hatta shi kasan din mutuwar tsaye yayi domin bai taba zaton hakan ba duban sa tayi fuskarta da murmushi mai tafe da hawaye ta
juya cikin sauri tayi sama shi kuwa kwakkwarar motsi kasawa yayi kan sa ya ji yana juya masa lokaci guda yasaka hannayensa duk biyun ya dafe shi gabansa na tsananta faduwa wani firgici yaji shi a ciki musamman akan furucin mahaifinsa wanda ya tabbatar ai iya tabbata…Ba karamin tashin hankali Hafsat tashiga ba lokacin da taji mahaifin Huzaif yana ta faman sababi tun da suka dauko hanya ko hadiyar yawu ba yayi idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir kamar jan gauta ita kan ta tayi dana sanin zuwan ta gidan.
“Ban dan dakikan ci kina ‘ya mace har ki zauna namiji ya yaudareki da banzayen kalaman sa ya nemi kashe miki rayuwa a banza a wofi bayan ke kan ki in mai tunani ce ya kamata tun kafin haka ta faru in son ki yake yi tsakani da Allah sai ya fito kuyi aure duk uwar da za kuyi ba wanda zai hana ku amma da yake kan ki a tukunya yake kika saki baki kika aminci da zancen Huzaif wanda ni kaina mahaifin sa Allah na gani ina fargaba akan sa da halayen sa ban
san abin da yake damun ku ba ‘ya’ya mata a yanzu da yawan ku maza na amfani da ku wajan saka muku son su wanda zai hana ku ganin laifin su sam! wasun ku basa gane SON GASKIYA da SON SHA’AWA”.
Kwaɓa yayi gami da dukan sitiyarin motar sai faman jan tsaki yake yi kamar zai tsinke harshen sa.
Numfashi ta ja gami da haɗiye wani abu da taji ya tsaya mata a makoshi lokaci guda zufa ta shiga karyo mata sosai ta tsorata dashi ji take yi kamar tace ya tsaya ta sauka amma ina ta kasa.
Cikin wannan yanayin da kwatancen da take masa suka iso kofar gidan parking yayi sannn ya juyo ya dube ta ganin tayi wiki-wiki da idanu ya sanya shi galla masa harara domin shi dai ba ya ganin laifin maza kamar yarda yake ganin laifin mata domin ba yarda za ayi kina ‘ya mace har ki bari namiji ya yaudare ki ba tare da yardar ki ba in har kika nuna masa ba ki yarda ba ai ba dole zai yi miki ba ai so ba hauka bane.
“Maza ki je kiyi mani sallama da mahaifin ki”.
Ware idanu tayi gabanta ya yanke ya fadi ita a rayuwarta har mantawa take yi tana da wani mutum wai mahaifi sosai taji wani irin yanayi a zuciyarta yau rana daya taji takaici rashin baiwa mahaifinta lokacin sa yau ga ranar sa ta zo shin da wani idanu zata je ta dube shi bata je masa da kayan alheri ba sai na akasin sa ta san dai ba zata fara ba don ta san izuwa wannan lokacin labari ya kai kunnansa.
“Dake fa nake ko ba nan ne gidan naku ba?”.
Mahaifin Huzaif ya katse ta da sauri ciki firgici har tana buge koshin ta a jikin motar ta buɗe murfin ta fito sai faman rarraba idanu ta ke yi sosai ta lura da mutanan layin na ta kallonta da wani irin yanayi ita kanta sai ta ji ba dadi ba yarda ta iya haka ta ja kafafuwanta ta nubi cikin gidan kirjinta na dokawa da tashin hankali.
A tsakar gida ta tadda Mariya na wanki kallo ta bi ta shi kafun ta kau da kai ita kan ta Mariyar kallon ta take amma bata ce da ita komai ba sai yanayim tausayi da ya bayyana a gareta sosai ta lura da abin da take zargi din da gaske din dai cikin ne domin gashi nan har ya fito don ita da duk ba ta lura ba.
Hafsat na shiga cikin dakin ta tadda Goggo Marka zaune tallaɓe da haɓa abin duniya duk yabi yayi mata yawa ganin Hafsat ta shigo ya sanya ta mikewa cikin hanzari.
“Ke kuma ina kika je cikin wannan halin so kike yi jama’a su fuskanci halin da kike ciki ne?”.
Kau da kai tayi tare da cizon laɓɓa ba tare da tace da ita komai ba.
“Dake nake Hafsat kika yi banza dani”.
Turo baki tayi tare da cewa.
“Zuwa nayi gidan su Huzaif na sanar da iyayensa yanzu haka tare da mahaifin sa nake domin yace sai ya zo ya sami mahaifina”.
STORY CONTINUES BELOW
Gaban Goggo Marka ne ya yanke ya fadi lokaci guda idanuwanta sukayo waje ta daura hannu akai.
“Mun shiga uku in mahaifin ki ya san wannan lamarin ai mun boni”.
Dubanta Hafsat ta shiga yi ganin yanayin da ta shiga takaici ya sake kume ta.
“Yana waje fa yana jira don cewa yayi nayi masa sallama da mahaifina”.
Da hanzari Goggo Marka ta figi zanin dake rataye ta yafa tayi waje zuciyarta da wani kudiri da ta dauka cikin kankanin lokaci har tuntube take yi wajan saurin tana fita hango shi tayi jikin motarsa ganin hakan ya sanyata tsayawa tana tunanin kafun ta canza fuska ta isa gareshi sam bai lura da ita ba sai ji yayi an bubbuga masa jikin mota da sauri ya juyo ya dube ta
ganin ta ya sanya shi rinsinawa yana gaishe ta mai makon ta amsa sai ma wani wulakantaccen kallo da ta watsa masa.
“Ina tsinannan ɗan naka ma ci amana Allah ya wadaran ɗa irin naka”.
Duban ta ya shiga yi domin jin maganganun nata yake yi kamar ba gaske ba sai da ya sake dubanta sosai yaga yarda take faman kallon sa a wulakance ya bashi tabbacin kila ita ce mahaifiyar Hafsat sosai yaji ɗacin maganar da tayi a ransa amma sai yaki nuna mata tunda a girme ta girmeshi.
“Ayi hakuri Baba kin san sha’anin ‘ya’yan namu na wannan zamanin ka haife su ne baka haifi halin su ba…”.
“Ni rufe mani baki kaji ko ai dole kace haka tun da ɗan ka ya gama da jikata ya cuce ta maganar gaskiya ba zan yarda ba dole kasan abin yi tun kafin wannan abin kunyar ya bazu a jama’a su sani don wallahi ba zan lamun ta ba”.
Duban ta yake yi da mamaki yarda ta hakikance tana ta faman zabga masa magana kamar shine yayi wa ‘yarta ta ciki ko ya ce jikarta kamar yarda ta fadi ba zai yi mamaki ba lura da yayi ita tsohuwa ce kuma zai yarda da cewa RIKON KAKA bai yi ba don ya tabbata in da a hannun iyayenta wannan yarinyar take hakan ba zai taba faruwa ba in har sun san abin da suke yi.
“Ayi hakuri Baba ina mahaifin ta yake”.
Wani irin dokawa gabanta yayi jin ya ambaci mahaifin Hafsat yake nema nan da nan jikin ta ya shiga rawa da sauri ta dube shi.
“Baya nan Allah yayi masa rasuwa…kasan abin da za ayi kawai asirinmu a rufe ni da kai da ‘ya’yan namu a zubda cikin nan tun kafin kowa ya sani ina ga haka shine mafita garemu…”.
“Zubar wa kuma bayan laifin da aka aikawa ubangiji sannan a sake yin wani laifin anya kuwa kina tausayin jikar nan taki anya kuwa kina son ku rabauta ke da ita to a gaskiya ba za ayi haka dani ba abu daya zan iya yi
muku shine na aurawa jikarki ɗana ni nayi wannan alkawarin sannan ba za ayi auren ba har sai ta haife abin da ke cikinta ina ga wannan shi kadai ne mafita a garemu”.
Duban sa Goggo ta shiga yi cikin wani irin yanayi na rashin baiwa maganar tasa muhimmanci.
“In kuwa haka ne sai dai ta koma gidan ku da zama don Allah na gani ba zan zauna da ita a zo ana zunɗena da gulma ta ba”.
Mamaki ne ya sake turnuke shi yau ya kara tabbatar da sakaci da rashin alfanun rikon kakan musamman ga ‘ya’ya mata yanzu mai gari ya waya anya kuwa iyayen yarinyar nan sun san halin da ‘yar su take ciki kuwa? Sosai yaji haushin yarda take
maganganun ta don haka ya dube ta.
STORY CONTINUES BELOW
“In har ba zaki yarda da abin da nace ba sai dai kowa ya kama gabansa don ba damuwa ta bace jikar ki ce zata shiga cikin gagarin rayuwa ina ma laifina akan kokarin da nayi”.
Yana gama fadin haka ya fada cikin motarsa ya ja ya tafi ya bar Goggo Marka sake da baki sai faman sababin take yi ganin mutane sun fara dawo da hankalin su gareta ya sanyata juyawa ta na fadin.
“Aifa na kurya masu gansa kuka a idanu an bazo mani”.
*****
Abu kamar wasa lamari sai kara rincaɓewa yake yi a wajan Hafsat tun ranar da mahaifin Huzaif ya zo ko kafarsa ba ta sake gani ba sannan ga Goggo Marka ta saka ta gaba a na cikin haka mahaifinta yayi wa gidan tsinke ba karamin kaɗuwa tayi ba ita da Goggo Marka idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir kallo daya za kayi masa ya baka tausayin don tashin hankali iyakar karshensa ya shiga cikin sa duban Hafsat yayi.
“Ni Mahaifin ki ne amma daidai da rana daya ba ki taba bani wannan matsayin nawa ba Hafsat ni na haifeki amma ni da banza duk daya ni da uwarki ba wanda kike gani da gashi rayuwarki kike yi yarda kike so baki da mai kwaɓa ko ma an kwaɓe kin Goggo gani take yi kamar matsa miki ake yi yanzu wa gari ya waya iyee ke ba ki cikin kwanciyar hankali mu iyayenki da mu ka san kina da hakki akanmu mu ma ba mu da kwanciyar hankali yanzu uwarki na can bata da lafiya kuma ba wanda ya zama sanadi sai ke”.
Wasu hawaye masu dumi suka zubo masa kau da kai yayi cikin dauriya.
“Hafsat tunda kika taso a matsayin ki na ‘ya mace mai rauni mai makon ki yi kokarin tsare rayuwarki amma ki ka ki kika nuna ba wanda ya isa dake ke a tunanin ki wannan rawar kai da kike yi shi zai sa an gan ki da mutunci kina tunanin wannnan rayuwar da kika daukarwa kan ki akwai na mijin da zai gan ki da mutunci har yace zai iya zama dake a matsayin matar aure ina! ba wani ɗa namiji da zai auri
jahila ko wani namji burin sa ya samarwa ‘ya’yansa uwa ta gari ke ba abin kwaikwayo bane ga ‘yar uwarki ba abin da ba kuyi mata ba ba abin da ba ku ce mata ba akan neman ilmi da take yi haka kuke jifan ta da mugayen kalamai yanzu wa gari ya waye ke da ita waye yake da nasara a rayuwarsa na tabbata yanzu Mariya duk wani
namiji mai hankali mai natsuwa zai so ace ta zama matarsa amma ke fa a yanzu kina tunanin ko wanda yayi miki wannan aikin zai aure ki ne ina! ko ma ya yarda zai aure ki to wallahi ba zai taba ganin ki da mutunci ba ke da banza duk daya zai dauke ku”.
Goge hawayen da suka zubo masa yayi gami da girgiza kai.
“Yanzu kika fara shiga tashin hankalin rayuwa in har kika ce ba zaki sauya ba”.
Yana fadin haka yafice zuciyarsa cunkushe da tashin hankali.
Goggo Marka dake can gefe tun dazu tayi wiki-wiki da ita duk abin duniya yabi ya dame ta ta rasa me za tayi maganar tun tana boye wa har an fara ganowa duban Hafsat tayi.
“Hafsat wai me ya kamata muyi ne yanzu don ni gaskiya na fara tsorata da lamarin ko gidan iyayen naki zaki koma?”.
Wani duban rashin fahimta Hafsat tayi mata zuciyarta na zafi me Goggo marka take nufi da wannan maganar ta ta da take fadi girgiza kai tayi cike da kunar rai.
“Kamar ya na koma gidan iyayena Goggo kina kallon fa abin da Babana yace sannan kuma kice na koma bayan ba a gabansu komai ya same ni ba”.
“To ya kike so in yi ne kowa ya zo kaina zai sauke matsalarsa kamar a kai na ne wannan lamarin ya fara faruwa ni gaskiya na gaji gwanda ki koma gaban iyayenki ko kuma kisan yarda zakiyi ki sami Huzaifa din akan maganar auren ku da mahaifin sa ya zo dashi”.
Hawaye ne suka shiga zubo mata cike da takaicin yarda Goggo Marka ke nuna mata ta fara gajiyawa da ganin ta mikewa tayi sai faman tangaɗi take yi ga cikin nata ya bayyana sosai.
“Ni Goggo kike hantara ni kike cewa kin gaji da ganina kenan dama ba son Allah kike yi mani ba dama kin rabani da iyayena ne don ki bata min rayuwa”.
Gyaɗa kai ta shiga yi hawaye na sake balle mata.
“Shikenan Goggo amma ki sani wallahi ba in da zani domin ba laifin iyaye don haka ba zai je na kara tayar musu da hankali ba a nan zan zauna in ma haihuwar ce sai dai nayi ta a nan sai dai duk abin da zai faru ya faru”.
Ta karashe tana galla mata harara cike da takaici Mikewa Goggo Marka ta yi ta iso gareta.
“Hafsat ni kike fadawa wannan maganar haka?”.
“An fada miki kin cancanta ne shiyasa kuma wallahi takaicin nan tare dake za mu shanye shi”.
Mamaki ne ya cikata ganin yarda Hafsat ke mata magana cikin tsawa-tsawa kamar zata kai mata bugu bata gama shan mamaki ba sai da ta ga Hafsat ta tsartar da yawu ta bankaɗe labule ta fice daga cikin dakin…Runtse idanu tayi daidai lokacin da ya isa inda take tsaye kwankwarar motsi ta kasa yi zuciyarta sai faman harbawa take yi kamar zata faso kirji ta fito waje kwanyarta take ji tana yawo dauke da wani irin hayaniya mai kama da saukar a radu buɗe idanunta tayi a karo na ba adadi ta sauke a saitin inda fuskarsa take sai faman sauke mata wani+
shu’umammen murmushi yake yi wanda yake kara rikita mata duk wani tunani nata da natsuwarta.
Bata san ya za tayi ba zuciyarta gabadaya ta gama tafiya a duniyar Dr.karami lokaci mai tsayi tayi
kokarin kwatar kanta amma abin ya ci turo sai ma abin da ya cigaba sosai take jin zuciyarta na kara matsewa da kaunarsa kaunar da take jin ta tana kara hayayyafar ‘ya’ya wanda ba za ta iya cewa ga adadin su ba kaunar ce zallarta ba tare da hadi ba wanda ta jima da AMANNA akan haka kaunar Dr.Karami kamar halitta ce da Allah yayi mata tun lokacin da zai busa mata numfashi.
Wani numfashi ta sake ja a daidai lokacin da taji takunsa na kusantowa gareta yana kara sautin bugun zuciyarta ko wani sashi na jikinta take jin yana narkewa kafafuwanta jin su take yi kamar ba za su dauke taba.
“Mariya!!!”.
Ya fadi da wani irin sautin da ya sanyata sumar tsaye gami da sadakarwa zuciyarta ta tarwatse da sautin zazzakar muryarsa mai dauke da wani sirrin mai kokarin fallasa sirrin dake boye a bayan zuciyarta.
Buɗe bakinta tayi ta shiga kokarin buɗewa domin ansawa amma hakan ya gagara sai ma motsi da laɓɓanta suke yi amma ta kasa furta wata kalma wacce zata taimaka mata domin dawowa hayyacinta.
Idanuwansa ne suka sarke cikin nata a bazata wanda hakan ya sagar mata da duk wata gaɓa ta jikinta wanda za ta taimaka mata wajan kwatar kanta daga barin kallonsa wani maganakisu take hangowa yana zabarin duk wani sirrin dake cikin idanuwansa yana sarkewa da nata.
Wani yin kuri tayi mai tafe da numfashi ta kau da kanta tana faman ajiyar zuciya wani murmushi ne mai girman gaske ya bayyana akan k’yank’yawar fuskarta sai faman kaɗa kwayar idanuwanta take yi.
Ba zato ko tsammani taga mutum ya durkushe a gabanta da sauri tayi kokarin ja baya amma sai taji kamar an kafe mata kafafu ne dago idanuwansa yayi ya sauke a saitin nata tare da kokarin kamo hannunta guda wanda ta rufe rabin fuskarta dashi.
“Ina son ki Mariya zuciyata ta gama gajiwa so ne kawai a cikin ta yake zarge ko wani sashi da loko na cikin ta GURBIN SO da na baki wanda ya kasance ke kadai ce a cikin sa so nake yi ki bani damar da zan farfaɗo dashi daga sumar da yayi na wucin gani kice dani kina so na zan zamo ABOKIN RAYUWA a gareki”.
‘Yaa Rabbi!!”.
Ta fadi cikin bugun zuciya kankame jikinta tashiga yi domin ta rasa me zata yi ta rasa ma a wata duniyar take a wannan halin ta kasa sarrafa kanta gani take yi kamar ba ita ba gani take yi kamar wata Mariyar ce ba ita ba wai Dr.Karami akan gwuiwowin sa yana neman SO gareta shine yake fada mata kalaman da suke kokarin tarwatsa mata zuciya da kwanya ba
zata iya ganin sa a haka ba ba zata iya sakin kunnuwanta taji kalaman da yake fadi kanta yayi kadan ya dauka komai zai iya faruwa zuciyarta zata iya fashewa da kaunarsa kaunar da take hangota tafi duk wata kauna da masoya suke nuna wa junansu.
Bata taba zaton zata tsinci kanta a wannan matakin ba bata taba zaton zuciyarta zata iya sakewa haka ba har ta saurari irin wannan kalaman…
“Ki ce wani abu mana duniyar nan a yanzu mu kadai ne a cikinta karki bari kunya tayi miki SAGEGEDUWA ki fito fili ba wanda zai ganki ki kalle ni a matsayin ni kadai ne babu kowa ki kalle ni a a matsayin wanda shine a matsayin ABOKIN RAYUWA a gareki”.
STORY CONTINUES BELOW
‘Anya kuwa?’.
Ta fadi cikin zuciyarta da k’yar.
Dan yatsarta na tsakiya taji ya kama gabadaya ji tayi wani irin Shock ya kamata duk wata kofar dake jikinta runtse idanu tayi tana mai jan
numfashi kamar zata shiɗe da sauri ta shiga ambaton ‘Yaa Ilahi!’. Kafun ta shiga kokarin kwatar kanta amma ina shigar zobe da taji cikin dan yatsar nata ne ya sanyata sakin jiki sosai ji da tayi ya sakar mata hannu ya
sanyata ja da baya da sauri tana mai da numfashi buɗe idanuwanta tayi saitin hannunta da take ji kamar ba nata ba duban hannun nata tayi wani hadadden Zobe ta gani sai k’yalli yake yi ruwan Gold mai tsananin kyau da burgewa sosai taji wani iri a zuciyarta da saurin ta dube shi shima ita yake duba idanuwansa sun yi wani kala kamar ruwan Rose sai sheki suke yi.

“Please My Pretty Say something to me?”.
Ya fadi da wata kwantacciyar murya wacce zata iya rantsewa ba tasa bane in ba don ta ganshi a gabanta ba sannan laɓɓansa na motsawa cikin wani irin salo wanda yake kara rikita mata tunanin kwanyarta.
Hannun ta dago mai zobe a ciki ta shiga kallon zoben tana tabawa da dayan hannun nata wasu abubuwa taji kamar sako suna shiga jikinta a duk sa’ilin da ta murza zoben harufan dake jiki suke kara sanyata jin wani iri kyallin da suke a tare ne suke kara sanya zuciyarta son zoben.
“Duniyar nan ina so ta zamo tamu mu kadai ki dubi duk girman ta da fadin ta ki saka a ranki mu kadai ne a ciki ba wani wanda zai fado cikin ta har ya so ba mu wata matsala”.
Dam! taji gabanta ya bugu jin furucin sa zuciyarta ne ta mikata wani mataki mai girma da nisa ‘Dr.Aqeel’ zuciyarta ta bankado mata runtse idanu tayi sosai wani sashi ya shiga kawo mata shi tana kara kamba mashi a gareta kai ta shiga girgizawa a hankali wasu hawaye suka tarun mata a GURBIN IDO bata so ba bata so abin da zai kara rikita mata rayuwa a irin
wannan lokacin mai girman gaske a gareta tashin hankali take tsoro bata so a sake komawa gidan jiya so take yi duniyar ace ta cigaba da wanzuwa a wannan matakin da take ciki a yanzu amma bata tunanin haka zata kasance dole ta hakura dole ne…
“Kuka!!!”.
Ta ji muryarsa kamar an hura sarewa gabadaya taji kunnuwanta sun dauka kwanyarta ta dau sautin sosai ji tayi tana yawo kamar zata zube a kasa.
“Mariya kukan me kike yi haka…fada min please ko na ɓata miki rai ne?”.
Yanayin yarda yake maganar ya kara narkar mata da zuciya a tausayin sa ta sani tana son sa amma bata san yarda zatayi da Dr.Aqeel ba shima yayi mata HALACCI bata so ace ita tayi masa BUTULCI girgiza kai ta shiga yi.
STORY CONTINUES BELOW
‘Ba yarda zaki yi dole ki zaɓi daya don mace bata auren NAMIJI sama da daya’.
Zuciyarta ta fadi mata hannayenta ta saka ta rufe kunnuwanta ji take yi kamar furucin zuciyarta da take kamar a bayyane yake.
‘Dr.Aqeel’.
Ta fadi a zuciyarta sai dai abin da bata sani ba shine maganar da tayi a bayyana take.
Dr.Karami da ya tunkaro wajanta don rarrashi jin abin da tace ya sanya shi saurin jar burki yana mai watsa mata wani irin kallo mai cike da tuhuma da zargi lokaci guda ya ji zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri runtse idanunsa yayi sannan ya buɗe akanta.
Ita kanta a jikin ta taji yarda kallon nasa ke ɓulata hakan ya tabbatar mata akwai abin da tayi wanda ya sanya shi yi mata irin wannan kallon dago idanun ta tayi ta dube shi da sauri ta kau da kanta zuciyarta tayi wani irin dokawa.
“Mariya da gaske kike abin da najiyewa kunnuwa na gaskiya ne?”.
Ya fadi muryarsa da zafi a cikinta wani iri taji jikinta nayi mata sosai ta gano laifin don haka da sauri ta shiga girgiza kai zuciyarta na rikicewa da tashin hankalin da ta hango a idanunsa sosai taji kanta na cakuɗewa yana mikata wani mataki wanda bata taba jin ta a cikin sa ba.
“Karki ce mani shine kar ki ce mani zuciyarki na gareshi karki ce mani shine mai GURBIN SO a zuciyarki bani ba don Allah Mariya na roke ki karki buɗe bakin ki ki sanar da ni gaskiya ne na san karya kunnuwa suka jiye mani Please Don’t say anything”.
Ya karashe cikin jarumtar zuciyarsa da yake jinta kamar zata tarwatse numfashi yake ja a hankali da sauri ya daga hannayensa duk biyun ya dafe kan sa da su wani irin juyawa yake jin kansa nayi kamar zai tarwatse gida biyu.
Laɓɓanta ta tura cikin bakin ta tana cizawa kuskuren da take ji tayi take son ya zama a mafarki ba gaske ba ba za ta iya cigaba da kallon Dr.Karami a yarda take ganinnsa a yanzu cikin wani irin yanayi da take jin yana karta mata zuciya.
“kai ne…”.
Ta fadi da kyar zuciyarta na yinkurawa kamar zata tarwatse hakan ya hanata karasa abin da tayi niyyar fadi.
“Ni ne me Mariya fadi nine me don Alalh ki bude bakinki ki fadi naji ko zuciyar tawa zata rangwanta min daga ciwon da ta tsomani a ciki”.
Juyawa tayi da sauri tana kokarin barin wajan da sauri ya riko mata hannu ya matse sosai har sai da tayi kara mai dan sauti dubanta yake yi cikin idanunta da suka kaɗa sukayi jajir.
“Ba zan sake ki ba har sai kin fada min matsayi na”.
“Ina son ka Dr.Karami kai ne mallakin zuciyata..amma ka sani ina tsoron butulci…”.
A hankali ya sassauta mata rikon da yayi mata wani murmushi na bayyana a saman fuskarsa ya shiga girgiza kai.
“ba a so dole sannan kyautatawa daban so shima daban karki ce don Dr.Aqeel ya taimaka miki a rayuwa haka na nufin sai kin so shi a,a ban ce karki so shi ba amma ba wai wanda zai cutar dake ba ki ajje batun sa a gefe ki anshi SO na mu rayu tare”.
Girgiza kai take yi a hankali tana dauke hawayen da suke zubo mata maganar tasa take jin ta wani iri a zuciyarta da kwanyarta laɓɓanta ta shiga motsawa alamun son yin magana amma ta kasa sai murza zoben hannunta take yi.
“Mariya!!”.
Ya ambata cikin wani irin yanayi mai tafe da mamaki da al’ajabi da sauri ta dube shi ganin yana kallon kofar gidan su ya sanya itama ta juya da sauri ware idanu tayi waje ganin Hafsat ta leko ko mayafi babu ga turtsetsen ciki a gabanta runtse idanu tayi kafun ta dubeshi zuciyarta na dokawa da sauri-sauri.
Kallon tuhuma yake yi musu su dukan biyun kafun ya ja numfashi ya dubi Mariya wacce itama izuwa wannan lokacin ta dawo da dubanta gareshi kwalla ne suka kawowa idanuwanta farmaki da sauri ta hadiye su.
“Me kenan Mariya me ke faruwa ne da Hafsat haka karki ce mani…”.
Shiru yayi cikin yanayin tausayi yana girgiza kai don ya tabbatar da zarginsa ganin yarda Mariya ta rikice.
“Allah ya kyauta”.
ya sake fadi ganin Mariya bata da niyar cewa komai sake kallon Hafsat yayi wacce itama a daidai wannan lokacin idanuwanta na kansa kau da kai yayi cikin faduwar gaba da sauri ya juya ya koma cikin motarsa wata katuwar leda ya fiddo da ita ya ajje gaban Mariya kafin ya juya da sauri ya koma cikin motarsa zuciyarsa nayi masa zafi sosai.
Sakin baki tayi tana kallonsa har ya ja motar bayan ya dago mata hannu ya wuce sannan ta sungumi ledar jiki a sanyaye tayi hanyar gida har zuwa lokacin Hafsat na tsaye bakin kofar ko motsi ba tayi ba.
“Haba don Allah Hafsat haka da kike yi fa wallahi bai dace ba zubda mutunci ne kike yi duk wanda ya ganki a haka dole yayi miki wani kallo na daban”.
Gyatsi ne tayi kafun ta kalli hannun Mariya ta kau da kai.
“Meye naki a ciki ko kina tsoron kar Dr.Karami yayi zargin duk daya ne”.
‘Allah yayi min tsari da aikata mugun abu irin wannan’.
Mariya ta fadi da sauri cikin zuciyarta gami da raɓa Hafsat tayi shigewarta cikin gida zuciyarta da takaicin halin Hafsat duk da abinda ya faru da ita amma har yanzu ba za tayi karatun ta natsu ba ta saita rayuwarta sosai take
jin bakin ciki da takaicin halin da Hafsat ta tsinci kanta sosai abin ke taba mata zuciya amma ita Hafsat ta kasa fahimtar ta na daukar da take yi mata na ‘yar uwa ciki daya…Tunani kawai take yi akan yarda zata anshi Dr.Karami lokaci guda bayan kuma ta san akwai wani akasa ko da yake ya kamata izuwa wannan lokaci ta saukaka wa kanta domin samun natsuwar zuciyarta.+
Amma ta yaya hakan zai kasance ta yaya hakan zata faru bata sani ba bata san yarda zata dauki lamarin ba sosai take jin kamar bata kyautawa Dr.Aqeel ba in tayi duba da yanayin dake tsakaninta dashi.
“So daban kyautatawa daban”.
Ta jiyo wani sashi na zuciyarta na dauko mata wani sashi na zancen Dr.Karami da ya faɗa mata.
“Amma ai kyautatawa na haifar da so da kauna ga mutane biyu? Kuma ai kyautatawa na cikin abin da ke haifar da so ga zukatan dangin rai”.
Ta fadi tana tura laɓɓanta cikin baki tana cizawa a hankali juyi tayi daga kwance da take ta mai da idanuwanta suna kallon sama sosai take jin
zuciyarta da kwanyarta na mikata wani mataki na musamman wanda zata so ace ta rayuwa a cikin sa har gaban abada amma kuma bata zaton haka ganin lamarin take kawai a labarin kanzon kurege ba zai taba tabbata ba.
Numfashi ta ja tana mai da numfashe idanuwanta a hankali ta buɗe su ta dago dan yatsen hannunta wanda yake dauke da zoben da Dr.Karami ya sanya mata kallonsa take yi zuciyarta na kara buɗewa da kaunarsa ji take yi duk wani GURBIN SO na zuciyarta Dr.Karami yana kokarin mamayewa cikin yan kwanakin nan sosai take jin ta a wani mataki na farin cikin zuciya wacce ta cika da kauna zallarta.
Zata so ace rayuwar ta mika a haka za ta so ace rayuwar ta cigaba da tafiya a haka amma ina! akwai wani wajan da za a kin tafiyar ta sani ALKALAMIN ƘADDARA zai iya zano mata wani abu mai girman gaske ya dora mata a matsayin JARRABI izuwa wannan lokaci ta rigaya ta saba sosai da sosai bata tunanin akwai kaddarar da zata fado rayuwarta bata yi kokarin ganin ta cinye ta ba.
Gabanta ne ya doka da sauri ta mike tana ambatar ‘Hasbunallahu wa ni’imal wakil Yaa Hayyu Yaa Kayyum’.
Idanuwanta ta zaro sosai hannayenta saman kirjin ta tana jin yarda BUGUN ZUCIYARTA ke kara tsananta.
“ME KE FARUWA?”.
Ta fadi tana jan numfashi da sauri ta shiga kokarin mikewa ji tayi duk ilahirin jikinta ya dauki sanyi kamar an doke mata duk wata gaɓa dake jikin ta a hankali ta shiga taka
kafafuwanta kanta ko dan kwali babu yalwataccen gashin kanta ya baje sosai har zuwa fuskarta da sauri ta janyeshi zuwa baya ba tare da ta sanya dankwali ba tayi hanyar waje a bakin kofa ta tsaya tana ajiyar zuciya Umma ta gani zaune ta zabga tagumi da sauri ta isa gareta ta taɓa ta amma ba alamaun ta san ta zo wajan.
“Umma!”.
Mariya ta fadi da sauti a muryarta tana mai jinjigata a hankali taja wani dogon numfashi ta dago idanuwanta da suka dan kaɗa ta dubi Mariya kafun ta kau da su cikin wani irin yanayi na damuwa.
“Umma lafiya na ganki haka?”.
Murmushi kadan tayi wanda da ka kalle ta zaka gane na dole ne girgiza kai tayi tana cizon laɓɓa.
“Mariya mahaifin ki shi na tuna wani mafarki mara dadi nayi a yanzu a nan zaune ina gangaɗi sosai naji na tsorata”.
Ware idanu Mariya tayi jin abin da Umma ta fadi ko dai wani abu na shirin faruwa ne domin itama taji irin yanayin a yanzu zuciyarta ta sake bugawa hannun Umma ta kamo ta danke sosai cikin nata.
STORY CONTINUES BELOW
“Anya Umma Abbana ba ya cikin matsala zuciyata sosai take hasashen haka ina tsoro Umma ya kamata ace ko ina yake ya bayyana muna tsananin bukatarsa hakurinmu umma…”.
“Mariya to ya za muyi da ƙaddarar Allah haka ya tsara mana a rayuwa dole hakan sai ta faru fatana dai duk in da yake tsayin shekarun nan Allah ya bayyana mana shi”.
Hawaye ne suka kwaranyo wa Mariya a idanu da sauri ta saka bayan hannunta tana shafe su tana mikewa kan kafafuwan ta sosai take ji a zuciyarta mahaifinta duk inda yake baya cikin dadi da farinciki gami da kwanciyar hankali sosai take jin fargaba da tsoro a zuciyarta tana son ganin mahaifinta tana so ta sanya shi a idaniyar ta sosai take kewarsa.
A kullum sai tayi tunaninsa tana son ta ganshi tana so ya dawo cikin duniyarsu su rayu tare zuciyarta sosai take zafi duk sa’ilin da ta tuna lokacin da mahaifinta ya bar su ciki
mawuyacin hali ta sani kaunar da yake nuna musu ba zai sanyashi guje musu ba ta tabbata akwai abin da ya sanyashi barin su ya mika wani wajan tsayin lokaci mai girman gaske…
****
Saukarta kenan daga Napep tana kokarin shiga gidan su Mariya taji anyi mata Horn bata yi zaton da ita ake ba sai da taji ana tayi ba
ƙanƙautawa sannan ta juya ta kalli in ta tajiyo horn na tashi ta gefen idanu Dr.Aqeel ne tsaye kafarsa daya a waje daya cikin motar ware idanu tayi gami da juyowa tana duban sa ba tare da ta ce kala ba.
A hankali ya kulle motar ya shiga takowa gareta harɗe hannayenta tayi a kirji tana kallonsa Up and Down cikin wani irin yanayi zuciyarta na suffan ta mata tsarin halintarsa na cikakken namiji wanda ya hada duk wani abu da mace ke bukata a wajan namiji sanye yake cikin kananun kaya suit light blue wanda tayi matukar yi masa kyau hannunsa daure da hadadden agogon Rolex mai tsananin kyau….
Da sauri ta ja numfashi sa’ilin da taji daddar kamshin turarensa ya daki hancinta da sauri ta kau da idanuwanta daga barin kallon sa.
“Halin dai naki na nan na shan kamshi Baseera”.
Duban sa ta sake yi gami da murmushin gefen kumatu.
“In dai ba mugun hali bane ai da sauki”.
Ta fadin tana kallon wani gefe daban.
Nishin da taji yayi ne mai sauti ya sanyata duban sa da sauri cikin alamun tuhuma yanayinsa ta ga ya sauya gabadaya kamar wanda ba shi da lafiya laɓɓansa ya tura cikin baki yana cizawa.
“Ban san mai zai ce miki ba Baseera na san kin fahimci halin da nake ciki akan ƙawarki ina son ta sosai zuciyata take dakon sonta ya kamata izuwa wannan lokaci ace ta bani dama son ta nake yi so zallarsa”.
Tunda ya fara magana take kallonsa da mamaki namiji har namiji amma so ya mai dashi wani iri kau da kai tayi zuciyarta na jin haushin yanayin da ta ga yana nunawa AKAN SO.
“Dr.Aqeel kenan nifa wannan lamarin naku na rasa gane kan sa wallahi abu yaki ci ya ki cinyewa kun saka min ƙawata a gaba sai faman figarta kuke yi kun hanata sakat! bayan kuma ku kan ku kun sani ba yarda za ayi dukkanku ku aure ta dole sai dai daya a cikin ku”.
“Ni nake son ta Baseera amma ta kasa sanin haka”.
“Su ma sauran ai son ta suke yi ko ya dai kamata ace kun kafa teburin Sulhu a tsakanin ku ku barwa daya in kuma ba za ku iya ba gaskiya dole ku rabu da ita wani ya aureta daban tun da kun kasa hakurar da zuciyarku akan sonta”.
STORY CONTINUES BELOW
girgiza kai yayi yana jin yarda zuciyarsa ke kara buɗewa da son Mariya ya lura har yanzu Baseera bata san SO ba shi yasa bata dauki lamarin nashi da girma ba.
“Zan kama kafa dake”.
“Ban yarda ba”.
“Saboda me?”.
“Ba zan iya bane gaskiya ba zan takura mata ba”.
runtse idanu yayi kafun ya buɗe su akan ta da wani rin yanayi kallon ta yake yi sosai da sosai zuciyarsa na mikashi wani mataki mai girman gaske kwanyarsa yake ji ta shiga yawo dashi wani sashi na daban tana buɗe masa shafi-shafin wasu lamuraka masu girman.
“Zan takura miki”.
Ya fadi da wani irin yanayi a muryarsa ita kanta sai da taji tsigar jikinta ta mike numfashi ta ja.
“Zaka iya takura mani amma bana tunanin takurawar taka za tayi amfani”.
“Dole tayi amfani ki rubuta ki ajje daga yau ina tare da ke har ranar da BURINA zai cika”.
ya fadi muryarsa da zurfi a cikinta dubansa tayi da murmushi a fuskarta.
“MU ZUBA MU GANI”.
Ita ma ta fadi da murya mai sauti da sauri ta juya ta doshi kofar gidan gabanta na dokawa sosai taji a jikinta kallon ta yake yi sosai take jin kafafuwanta kamar za su zubda ita me Dr.Aqeel ke nufi da ita sosai taji wani iri a jikinta sosai take jin kamar wani abu na faru kwanyarta taji tana yamutsewa zuciyarta na matsewa tana mikata wani mataki mai girman gaske.
Tana shiga cikin soron gidan ta jingina da bango tana mai da numfashi idanuwanta a lumshe sai da ta shafe dakiku kafun ta ja kafafuwanta da taji sun yi mata sanyi ta shiga cikin gidan.
ba kowa a tsakar gidan hakan ya bata damar zarcewa bangaren su Mariya bakinta dauke da Sallama ba ansa ta ba haka ya sanya ta sake yin sallamar nan ma ba a ansata ba labulan dakin ta daga can ta hango Mariya rigingine a gado idanuwanta na kallon saman dakin da sauri ta zare takalman ta ta shiga cikin dakin ba tare da ta sani ba har ta zauna
bakin gadon hannunta ta kalla zoben da ta gani ne ya sanyata ware idanu cike da mamaki ga dariya na kokarin kwace mata da sauri ta sanya hannu ta rufe bakinta sai da ta gama karewa zoben kallo sannan ta daka mata duka.
A firgice ta mike tana shirin zurawa a guje ganin Baseera ya sanyata sakin jiki tayi kasa ta zauna tana mai da numfashi gami da dafe kirji.
“Mtss Allah ya kyauta miki ai wannan sai ki firgita mutum ya zura da gudu”.
Dariya Baseera tayi gami da kamo hannun Mariya mai zobe ta kalla sannan ta daga idanuwanta ta kalle ta cikin tuhuma tana mai sakin murmushi hakan da Mariya ta gani ya sanya fizge hannunta ita ma tana dariya.
“Mariya!!”.
Baseera ta fadi da murya mai zurfi kafun ta dafa kafaɗarta muryarta tayi kasa sosai.
“Ya kamata zuwa wannan lokacin ki san matsaya a rayuwarki rayuwa baza ta taba daidai a wannan matakin ba da kike kai a yanzu kuruciyarki zaki duba karki yasar da ita a banza a wofi wajan sanyawa kan ki damuwa don Allah na roke ki Mariya ki san abin yi Umma za ki duba nasan ta fiki shiga tashin hankali akan wannan lamarin sai dai ba zata nuna miki hakan ba”.
Cikin rashin fahimta Mariya ke dubanta.
“wai shin me kike nufi ne?”.
“Kin fi kowa sani Mariya akan maganar ki da wadannan mutanan ne ya kamata ki tsaida guda daya gwani kin ga yanzu haka Dr.Aqeel yana kofar gidan nan don na tabbata ya dade da zuwa a nan na tadda shi”.
Da sauri ta dafe kirji gami da zaro idanu waje.
“waje fa kika ce Baseera na shiga uku”.
“Ba ki shiga uku ba zabi ne naki”.
Shiru Mariya tayi tana runtse idanu kafun ta riko Hannun Baseera.
“Baseera akwai matsala akwai abin da baki sani ba wanda na boye miki maganar gaskiya ina tsoron yanayin nan da muke ciki kisan a halin yanzu Hafsat na nan dauke da juna biyu kuma Huzaif ne sila…”.
Fizge hannunta Baseera tayi ta mike tsaye jikinta har ɓari yake yi idanuwanta a warwaje laɓɓanta sai motsawa suke yi alamun tana son yin magana amma ta kasa numfashi ta ja kafun ta runtse idanu ta buɗe su.
“me ki ke son ce mani Mariya Huzaif din da na sani Yaa Rabbi!”.
dafe kanta tayi gami da komawa ta zauna zuciyarta na matsewa da wani irin yanayi.
“Garin ya ya hakan ta faru Mariya?”.
Girgiza kai ta shiga yi kafun ta ciji laɓɓanta.
“Baseera Alfarma nake nema gareki”.
ta fadi tana kamo hannayenta Baseera da jikin ta ya gama yin la’asar ta sarke da nata tana faman matsewa zuciyarta na bugawa da wani irin yanayi mai girman gaske.
maganar take ji tana yi mata nauyi maganar da take so ta fadiwa Baseera bata san ya zata dauke ta ba tana tsoron taki amincewa ba tana son
wani abu na rashin jin dadi ya gilma a tsakaninsu in taji bukatarta ta dago idanunta tayi da suka kaɗa ta dubi Baseera wacce itama izuwa wannan lokacin gabadaya hankalinta ta mai dashi wajan ta idanuwanta na zagayawa a gareta tana jin yarda zuciyoyin su su dukan biyun ke bugawa da sauri sauri….
Yawwa yawwa Gud morning All my loves😘😘
Dafatan kun tashi lafiya ya gida ya kowa da kowa to ga Breakfast ja kawo muku ya ku ka ganshi da zafin sa fa wallahi hot💥💥💥
Yawwa ya ku gan shi ne me za ku iya cewa game da wannan shafin
Ga Dr.Aqeel ya zo ga kuma Baseera ta zo ita ma
Wata magana ce ta alfarma Mariya ke son nema wajan Baseera
Tofa!
Ko me kuma yake shirin faruwa ne???🙆🙆🙆🙆🙆