UKU BALA’I CHAPTER 13
Www.bankinhausanovels.com.ng
Numfashi taja mai zurfi kafun ta tura laɓɓanta cikin baki tana cizawa idanuwanta har zuwa wannan lokaci suna kan Baseera zuciyarta sai kara harɓawa take yi da sauri-sauri fargabarta da tsoronta suna kara daɗuwa sosai take hango rashin yarda da amincewa gami da rigima cikin idanun Baseera wacce tayi mata fakare tana yi mata kallon tuhuma.
‘Ya za ta dauki lamarin in na sanar da ita anya kuwa zata yarda har ta aminci da bukatata?’.
Mariya ta fadi haka a ranta tana kara matse hannun Baseera a cikin nata.
“wai me ke faruwa ne?”.
Baseera ta fada gabanta ita ma na cigaba da faduwa.
“Baseera ki Auri Dr.Aqeel”.
Ta fadi tana runtse idanunta sosai a cikin jikinta take jin wani iri zuciyarta na matsewa da wani irin yanayi da yake mikata wani mataki mai girman gaske.
Dariya Baseera tayi cikin rashin baiwa batun muhimmanci sosai tana kallon Mariya da idanunwanta ke a rufe.
“Ban gane ba Mariya me kike nufi kin san kuwa abin da kike cewa?”.
Buɗe idanunta tayi sosai wanda suka kaɗa sukayi jajir ganin hakan yasanya Baseera nutsuwa tana kallon ta lokaci guda zuciyarta ta buga da wani irin tsoro da ya mamaye duk ilahirin jikinta.
Gyaɗa kai Mariya ta shiga yi kafun ta motsa laɓɓanta.
“Ki taimaka ki auri Dr.Aqeel Baseera”.
Ta sake fadi tana kara kusanto Baseera fizge hannunta tayi gami da mikewa kallon Mariya take yi da wani irin yanayi kafun ta ja da baya sosai tana sake yi mata wani kallo mai
kama da na tsoro ita kanta Mariya ta tsoro ta da irin kallon da take yi mata mikewa tayi tana takowa in da take ta sake riko hannunta tana sarkewa da nata.
“Ki taimaka Baseera ki aure shi wannan hanyar ce kawai nake hango mana mafita a gareni da kowa ma”.
Kallonta take yi sake da baki kwanyarta take ji tana mikata wani mataki mai kokarin kona mata kwanya zuciyarta take ji tana harbawa da sauri-sauri.
“Ki taimaka ki aure shi na san za ku dace kuma za ku so juna”.
“Ba zan iya ba Mariya ba za ayi wannan cin amanar dani ba”.
Ta fadi tana fizge hannayenta tana kokarin ficewa daga cikin dakin da sauri Mariya ta riko ta sosai ta juyo da ita idanuwanta suka kawo kwalla sosai cikin rawar murya Mariya ta fara magana.
“Karki kawo cin amana a wannan lamarin Baseera ni nace na amince miki kuma na san ba haramun bane don haka don Allah ki anshi bukatata hakan ne zai tabbatar da amincin ƙawancenmu”.
“Ki yi hakuri ba zan iya ba Mariya”.
“Ki taimaka ki auri Dr.Aqeel Baseera ba za kiyi da na sani ba ni za ki taimakawa”.
“Mariya….!”.
Da sauri Mariya ta kai hannunta ta rufe mata baki tana girgiza kai hawaye na sauko mata saman fuska.
“ko MATAR MIJINA kika zama Baseera ba zan taba da na sani ba domin na san halin ki kuma na san ba zaki taba abin da zai cutar dani ba Baseera matsayin yar’uwa kike a wajena kina da matsayi mai girma a gareni ki anshi bukatata ki daure karki ce dani a,a”.
STORY CONTINUES BELOW
Runtse idanu Baseera tayi tana jin zuciyarta na mikata wani mataki mai girman gaske gabadaya komai ya cunkushe mata ta rasa wani tunani ma zatayi ba ta taba zato ko
tsammanin Mariya wannan bukatar zata nema a gareta ba in da ta san haka ce zata faru ba abin da zai kawo ta wannan gidan amma ina ALKALAMIN KADDARA ya zano mata rubutun da sai ta zo ta karance shi.
‘Anya ba cin amana in ta yarda da batun Mariya anya hakan ya dace bata jin son Dr.Aqeel a ranta ba ta jin sun dace a tsakanin ita dashi to in ita ta yarda shi fa a yarda ta ga yana mayan son Mariya an ya kuwa zai dube ta da idanun kirki har ya anshe ta a matsayin matar aure gareshi ina! ba zata yarda taje in da ba a son ta ba ba za ta je in da ba za a ganta da mutunci da kima ba ba zata yarda ta shiga in da za a din ga yi mata kallon kamar dole akayi masa ba’.
Nazarin da ta shiga yi da zuciyarta kenan cikin wani irin yanayi tsoro da fargaba na kara bayyana a gareta.
‘Mariya ta cancanci komai fiye da haka za ta so ace sanadin ta ta samu farin ciki za ta so ace ta sanadin ta rayuwarta ta sauya ta dawo mai armashi amma ta ya ya hakan zata kasance bata tunanin auren Dr.Aqeel shine mafita’.
Kamar Mariya ta san nazarin da take yi da zuciyarta dubanta tayi cikin kara narkar da murya da son biyan bukatar ta duk da tana jin wani iri a zuciyarta ta.
“Ki daina shakka ko fargaba akan Dr.Aqeel Baseera zai so ki ba zai taba wufutar dake ba so zai yi miki mai an suna so zallar sa karki sake ki saka wa zuciyarki fargaba ko tsoro”.
Hannu ta saka tana dauke hawanyen fuskarta tana mai kokarin zaunar da Baseera amma ta kiya ta kwace kanta.
“Gida zan tafi Mariya kaina ciwo yake yi don Allah rabu dani zan yi tunani”.
“Ban yarda ba Baseera ba zan yarda ki fice daga cikin gidan nan ba har sai kin ansa mani bukatata in kuwa har baki an sa ba to na tabbata amincin dake tsakaninmu ba kai ya kawo ba wallahi tallahi Baseera ko mijin da nake aure ki ka zo ki ka nuna kina so wallahi zan yarje miki ki zama MATAR MIJINA”.
Da mamaki Baseera ke dubanta fuskarta na sakin wani murmushi wanda yafi kuka ciwo sosai ta kamo hannun Mariya ta saka a nata.
“ki daina kiran amincin dake tsakani na dake kina danganta shi da wannan lamarin ni nace miki ki bari nayi tunani ba yarda za ayi na ansa wannan batun lokaci daya Mariya ba sauki fa lamarin nan gareshi ba duba zakiyi da shi Dr.Aqeel ba shi yace yana so na ba ke yake so kina tunanin in ya ji batun nan zai yarda har ya dube ni da kima da mutunci ya anshe ni amatsayin da kike kokarin daura ni?”.
Murmushi ita ma tayi zuciyarta na kara matsewa.
“Alkawari nayi miki zai so ki so da bai taba yi wa wata ‘ya mace…”.
“Ya isa haka Mariya maganar ta isa haka ki daina danganta KALMAR SO a wannan bahagon tunanin naki mara tushe kece mace ta farko kuma ta karshe da Dr.Aqeel yayi wa son da ba zai sake yi ma wata mace ba a duniyar…”.
“Na karya taki Baseera a wannan matakin ni nace miki in har kika aminci da Dr.Aqeel sai yayi miki so fiye da wanda yayi mani a filin duniyar nan ki rubuta wannan ki ajje ni dai BURINA ki amince”.
Kanta ta dafe da take jin yana sara mata maganganun Mariya suna kokarin saka mata ciwon kai bata san yarda za tayi da ita ba amma Allah na gani zuciyarta na fargaba kan lamarin nan.
STORY CONTINUES BELOW
“ki je ki samu yardarsa in har ya amince nima na amince”.
Tana gama fadin haka da sauri ta kwace kanta ta fice daga cikin dakin zuciyarta da kwanyarta sai hayaki suke yi kamar za su kama da wuta duniyar take ji tana juya mata kafafuwanta take ji suna kokarin zubda ita ga wani zafi da take ji tun daga kasan ruhinta har zuciyarta komai kallon sa take yi kamar a mafarki ba gaske ba laɓɓanta take turawa cikin baki tana cizawa gami da runtse idanuwa.
Dafe kanta Mariya tayi gami da jan kafafuwanta da take jin su ita ma suna kokarin zubda ita kasa ga wani hayaniya da take ji a kwanyarta zuciyarta take ji tana harbawa da sauri-sauri idanuwanta a runtse ta isa bakin gadon ta zauna tana faman fadin.
“Yaa Hayyu Yaa Kayyum”.
Numfashi take fiddawa a hankali zuciyarta na kara mikata wani mataki abin da tayi ne a yanzu take jin wani banbarakwai ji take yi kamar ba gaske ba ji take yi kamar cikin barcinta ne komai ke faruwa girgiza kai ta shiga yi kafun ta buɗe idanuwanta wanda suka gajiya da kaɗawa sosai zuwa ja murmushi ta saki gami da rufe fuskarta da tafukan hannayenta ta fada kan gadon ta baya.
Tunanin ta yarda zata fuskanci Dr.Aqeel take yi ba ta san ta yarda zai dauki maganar ba in ta je masa da ita bata san duban da zai yi mata ba akan wannan maganar anya ba zai ce ta yaudare shi ba anya ba zai ce ta ci amanarsa ba anya ba zai ce tayi masa BUTULCI ba?.
Tunanin da take ta faman yi kenan zuciyarta kuma ta kasu kashi biyu bangare daya na bata kwarin gwuiwar tunkararsa dayan barin kuma yana tsoratar da ita yanayin da za su kwashe da Dr.Aqeel sosai ta ji ko ina na jikinta yana sanya kwanyarta na kara rikicewa da rigimar da
zuciyarta ke hango mata za su kwasa da Dr.Aqeel a maganar nan ya kamata tayi wani tunani dole ne ta nemo hanyar da da zata samawar kanta mafita sannan ta samu cikar fatanta da burinta.
*******
Kai kawo kawai take yi tsakiyar dakin gabadaya ta hargitse yarda ka san wacce ta kwato kanta daga gidan mahaukata hannayenta saman kai sai yamutsa sumar kan ta take yi lokaci-lokaci take tsayawa tana jan numfashi tun da ta dawo gida ta rasa gane kanta maganganun Mariya ne kawai ke yi mata safa da marwa gabadaya take jin kwanyarta na kamawa da wuta ga
zuciyarta na ta faman kokarin fallewa da gudu daga kirjinta tashin hankalinta na daɗuwa ji take yi gabadaya duniyar na sauya mata ji take yi kamar ba ita ba.
Saitin katon Mirrow da ke dakin ta isa ta tsaya tana kallon kanta ta cikinsa l fuskarta take shafawa tana runtse idanu gani take yi kamar ba ita ba gani take yi kamar wata Baseerar aka ajje aka dauke ta ainihin.
‘Ta ya ya za ta so Dr.Aqeel bayan sun taba soyayya da ƙawarta aminiyarta ta kut-da-kut anya kuwa zata iya zuciyarta take ji kamar ba zata amince ba ji take yi kamar zaman kishi za su yi da Mariya ji take yi kamar in ta amince Mariya zata dauke a maciyar amana a gareta’.
Zuciyarta ce take ta faman dauko mata wannan maganganun suna kara rikita mata lissafi kofar dakin da taji an taba ne ya sanyata saurin juyawa Yah Tareeq ne ya shigo ganin yanayin da take ya sanya shi saurin isowa gareta yana yi mata kallon tuhuma.
“Me ke damun ki Sister?”.
Ya fadi yana kokarin riko hannunta da sauri ta ja da baya dafe da kai ta zauna bakin gado tana mai da numfashi harɗe hannaye yayi a kirjinsa yana dubanta cikin wani irin yanayi kafun ya isa kusa da ita ya zauna kan loka din kusa da gadon.
“Tambayarki nake me ke damun ki kin yi mani shiru”.
“Yah Tareeq bana jin dadi ne don Allah ka yi shiru bana son surutu”.
Da mamaki ya dube ta ganin yanayin da take ciki ya tabbatar masa da gaskiyar abin da tace mikewa yayi yana kokarin fita har ya kai bakin kofa sai kuma ya tsaya gami da
juyowa ya dube ta ita ma shi take duba dawowa yayi da baya hakan ya sanyata runtse idanu so take yi ya fita so take yi ta zauna ita kadai zaman kadaici take so kwanyarta take so ta sauke daga hayakin da take yi tana bukatar zaman ita kadai domin samun mafita akan wannan Bahagon lamarin da yake kokarin rikita mata lissafin rayuwa.
Kusa da ita ya zo ya zauna bata ce dashi komai ba har zuwa lokacin idanuwanta a rufe suke tana faman jan numfashi da sauri-sauri.
“Sister wai shin ya maganar nan ta mu ne har yanzu ba ki ce dani komai ba lokaci tafiya yake yi?”.
Duban sa tayi ta gefe idanuwanta a zazzare ji take yi kamar ta kwala ihu don haushin abin da yake cewa da ita so yake yi ya sake rikita mata lissafi bayan tashin hankalin da take ciki laɓɓanta ta tura cikin baki ta ciza da karfi har sai da ta dan saki kara ta dube shi sosai sai fama gyaɗa kai take yi.
“Yah Tareeq ka san me nake so da kai?”.
Girgiza yayi cikin mutuwa jiki ganin yarda tayi masa maganar.
“Ka taimawa kan ka ka taimaka min ka bar maganar nan don ba zata taba yuwu ba ne Yah Tareeq kayi hakuri ka je ka nemi wata matar amma ba Mariya ba don a halin da ake yanzu bana tunanin za ta iya dubanka har ta anshi tayin ka in har ba so kake yi abubuwa su lalace ba”.
Zaro idanu yayi waje sosai gami da mikewa cikin hanzari ya shiga kokarin magana amma Baseera ta dakatar dashi bayan ta mike idanuwanta sun kara kaɗawa sun yi jajir.
“Don Allah na roke ka Yah Tareeq wallahi tallahi abi nan ba zai taba yuwuwa ba kawai bata lokacin mu za muyi sannan kuma kayi dakon son da ba zai yi maka amfani ba sai ma matsala da zai ja maka kawai kayi hakuri ka nemi wata ZABIN ALLAH shine kawai mafita”.
Tana gama fadin haka ta koma ragwaf! ta zauna dafe kansa yayi da yaji yana juya masa kamar zai zubda shi ya shiga ambaton Allah a hankali ya fara jin saukin zafin zuciyarsa kallon Baseera yayi yanayin da yake ganinta a ciki ya tabbatar masa da abin da take gaya masa da sauri yaja jiki yana hada hanya ya fice daga cikin dakin dagowa tayi ta dube shi bayan taji alamun ficewarsa ta girgiza kai ta koma ta kwanta.Gabanta take ji yana faduwa sosai da sosai ga wani irin yanayi da take jin gangar jikinta na shiga runtse idanu tayi a daidai lokacin da Umma ta shigo cikin dakin dauke da bokitin Cake da ta gama yi can gefe ta ajje shi sannan ta juyo ta dubi Mariya da tayi shiru kamar wacce ake yiwa wasiyya girgiza kai tayi kafun ta motsa laɓɓanta.+
“Kin ga Cake din nan na yau ya bani mamaki kamar ba yarda ake yi ba wallahi yayi albarka sosai”.
Ta fadi tana mai zaunawa gefe gudu har zuwa lokacin idanuwan Mariya na buɗe sai faman ajiyar numfashi take yi hannu ta kai saman kirjinta ta dafa gami da buɗe idanuwan nata tana duban Umma.
Murmushin yak’e ta sakar mata kafun ta mike ta iso gareta jikinta a sanyaye.
“Umma jikina nake ji wani iri wallahi ga kirjina sai bugawa yake yi kamar wani abu zai faru dani tun safe nake jin haka”.
Dubanta Umma tayi idanuwanta na yawatawa akanta so take yi ta hango wani abu da zai bata ko tabbacin abin da yake damun Mariyar.
“Addu’a kawai zaki tayi Mariya irin haka in yana samun bawa musamman faduwa gaba Innalillahi wa inna ilaihir raji’un ake so ya ta maimaitawa”.
Gyaɗa kai tayi tana juyar da ganinta zuwa ga bokitin Cake din sannan ta juyo ta dubi Umma.
“Yayi auki fa a hakan ma na gani…ko da yake Birin gidanmu ba ya nan shiyasa Cake din bai shiga uku ba”.
Mariya ta fadi tana murmushi ita ma Umma murmushi tayi don ta gano da Mu’azzam take….
Da gudu ya fado cikin dakin yana hak’i ya fada jikin Umma dukkan su suka dube shi da mamaki dago fuskarsa yayi ya dubi Umma sannan ya dubi Mariya.
“Ga wasu mutane nan a kofar gida su hudu har da masu kayan fulani”.
Gaban Mariya ne ya yanke ya fadi kamar yarda yake yi mata tun dazu da sauri ta dubi Umma dafe da kirji yanayin ta ya sauya lokaci guda.
Ita kanta Umma ta ji faduwar gaban sosai don sai da taji cikinta yayi kara zuciyarta na tsalle kamar zata fito waje.
“Wai cewa yayi na zo na sanar daku nan gidan su ka zo daya daga cikin mutanan yace mani haka kuma yana kama da Yah Mariy….”.
Wata irin zabura Mariya tayi ta mike kan kafafuwanta idanuwanta a warwaje bugun zuciyarta take ji yana sauyawa sosai haka kawai take ji a jikinta akwai abin da ke faruwa.
Umma kuwa rintse idanu tayi tana ambaton sunayen Allah da dukkan wata addu’a da ta zo mata baki haka kawai ta ji a jikinta akwai kamshin wani abu muhimmi a batun Mu’azzam.
“Yace fa ku zo yanzu Umma”.
Ya fadi ya na mai jan hannun Mariya bayan ya tashi daga jikin Umma a hankali Mariya ta shiga bin sa kamar rakumi da ak’ala tana kallon Umma ita kanta Umma rasa abin yi tayi domin gabadaya take jin wata gajiya da kasala ta dirar mata a jiki lokaci guda ga wani bugu da zuciyarta take ta faman yi ba ƙanƙautawa laɓɓanta tashiga motsawa ta na son yi wa
Mariya magana amma kamar an dora mata katon dutse a harshe hannunta tayi mata nuni dashi ta dauki mayafi .
Duban jikinta tayi ita sam ta manta ma da kayan dake jikinta a hankali ta kwace kanta daga hannun Mu’azzam ta ja kafafuwanta da take jin su kamar za su zubda ita kasa ta janyo hijabin Umma ta zira ajikinta fita tayi cikin kokarin saita kanta Mu’azzam na gaba tana biye dashi har suka isa soron gidan nan ta ci burki ta tsaya jin
STORY CONTINUES BELOW
yarda zuciyarta take dokawa da sauri-sauri jingina tayi da bango tana mai da numfashi Mu’azzam shi kam idanu ya zuba mata har ta gama shan sharafinta ta taka a hankali suka cigaba da tafiya har suka isa kofar gida sai dai me.
Abin da Mariya ta gani ne ya kusan kashe ta da ranta runtse idanuwanta tayi sosai tana mai daura hannu aka ta kurma ihu gabadaya ta sulale zuwa kasa da sauri suka yo kanta ba wanda ya tabata ganin Babbar mace ce duban Mu’azzam sukayi gabadayan su kafun Baffa yace.
“Me ya same ta?”.
“Mu’azzam da yayi firi-firi da idanu cikin yanayi na tsorata.
“Yah Mariya”.
Ya fadi ai Bello na jin haka ya sake dubanta sosai zuciyarsa da kwamyarsa suka mika shi wani mataki mai tsayin gaske da ya gama shuɗewa sosai yaji wani irin abu ya dokar masa zuciya mai girman gaske.
‘Mariya’.
Ya furta hakan a ransa yana sake muntsuka idanunsa yana saukewa akanta juyawa yayi da sauri ya fizgo gorar ruwan dake rataye a jikin Ja’e ya balle kanta ya shiga kwarara mata kamar yarda hawaye lokaci guda suka shiga zubo masa a fuska wani dogon numfashi ta ja gami da buɗe idanunta ganin mutanan dake kanta ya sanyata saurin runtse ido tana furta.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un”.
Da karfi komai ganin sa take yi kamar ba gaske ba sosai zuciyarta ta tsorata ta sosai take jin jikinta wani iri gani take yi kamar a mafarki ba gaske ba laɓɓanta ta tura cikin bakinta tana cizawa zafin da yake ratsa ta ne ya tabbatar mata da GASKIYAR LAMARI da sauri ta sake ware idanunta.
Fuskar dake saitin ta take kallo fuskar da take hango hawaye suna zuba a samanta fuskar da ta jima tana cigiya fuskar da ta bace mata a rayuwa tsayin shekaru wai ita ce yau take gani kunnuwanta ta rufe da tafukan hanayenta gami da sake runtse idanu zuciyarta na harbawa da wani irin yanayi wanda ba za ta ce ga matsayin da zata ajje shi ba.
“Mariya”.
Muryar da ta shuɗe sama da shekaru bakwai ita ce yau take jinta a saitin ta tana ambatar sunanta muryar da tayi kewarta muryar da kullum take yabonta da shi mata albarka yau ita ce ta dawo gareta bayan shuɗewar lokaci.
Wani irin kuka ne taji ya zo mata da saurin ta rufe bakinta amma ina sai da sautin sa ya fita da sauri ta shiga kokarin mikewa amma ina ta kasa gaɓɓanta take ji kamar an doke mata su kamar daga sama taji hannaye da tajima da saninsu sun riko mata
kafaɗu cikin wani irin yanayi suna mikar da ita kan kafafuwanta wani numfashi take ja mai tafe da kuka buɗe idanuwanta tayi sa’ilin da taji ana dauke mata hawayen fuska sosai take kallon sa da wani irin yanayi na mamaki da tu’ajibi gani take yi kamar bashi ba gani take yi kamar gizo yake yi mata hannayenta ta shiga dagawa tana kokarin kai fuskarsa amma ta kasa da sauri ta shiga ja da baya tana duban sauran fuskokin wanda bata shaida su ba amma a jikinta take jin wani irin yanayi game da su.
Da gudu tayi cikin gida kamar wacce za a sace a soro suka ci karo da Umma da Mu’azzam a hargitse domin tun lokacin da ya ga ta fadi din nan ya kwasa yayi cikin gida yana kiran Umma.
Kallon ta Umma take yi da wani irin yanayi gabanta take ji yana yankewa yana faduwa hawayen da ta gani a fuskar Mariya ya kara rikita mata lissafi da sauri ta riko hannunta jikinta sai faman ɓari yake yi bakinta na karkarwa.
STORY CONTINUES BELOW
“Su waye Mariya…tambayarki nake yi su waye?”.
Yanayin da take maganar kawai ya isa ya tabbatar maka da cewa sosai take cikin firgici Mariya da ta ga yanayin da Umma ke ciki ya sanyata sake rushewa da kuka kafun ta tsagaita da cewa.
“Umma Allah yasa ba mafarki nake yi ba gaskiya ne Abbana ne…”.
Da sauri ta sake ta tana ja da baya gabanta na kara tsananta bugawa kafafuwanta take ji suna lauyewa idanuwanta suna lullubewa lokaci guda taji duniyar na juya mata kwanyarta na ansa kuwwa sosai jingina tayi da bango tana maida numfashi kafun ta zabura kamar wacce aka tsikara tayi hanyan waje da sauri a daidai lokacin shikuma ya sanyo kai cikin gida cikin rashin
tsammani suka bangaji juna taga-taga Umma tayi zata fadi dama ba wani karfin jiki take dashi ba da sauri ya rikota gabadaya jikinsu ya dauki wani irin yanayi runtse idanu Umma tayi sosai tana jin yarda jikinta ke ansawa da wasu bakin lamari masu girman gaske gareta.
A hankali ta shiga kokarin buɗe idanuwanta tana saukewa gareshi bakinta dauke da addu’a don gani take yi kamar a mafarki ba gaske ba jikinta na rawa ta dago hannunta tana shafe fuskarsa lokaci guda wasu
hawaye suka shiga kwaranyo mata a fuska zuciyarta na kara matsewa kwanyarta take ji kamar za ta kama da wuta a hankali ta zare jikinta daga na shi tana ja da baya kallonsa take yi a yanzu cikin tuhuma shi kansa ya hango hakan da sauri ya dube ta amma ita juyawa tayi tana kokarin komawa cikin gida.
“Tare da su Baffa nake”.
Da saurin Maganganun nasa suka bugar mata zuciya da kwanya lokaci guda jinin jikinta da numfashinta sukayi tsayawar wucin gadi ji tayi kamar ba a duniya take ba
kunnuwanta sai faman maimaita maganar da Bello yayi suke wani GWAURON NUMFASHI taja da take jin kamar zai fasa mata kirji tsoro ne sosai ya bayyana a gareta maganar take ji kamar ba gaske ba so take yi ta gasgata zuciyarta take jin tana ansawa tana amanna da batun juyawa tayi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ta dube shi wani kuka mai girma taji yana zuwa mata zuciyarta na buɗe wani wawaken ciwo da ta jima tana jinyarsa.
A hankali ya isa gareta yana riko hannayenta gami da girgiza kai idanuwanta sai faman bin shi da kallo suke komai take ji kamar almara gani take yi ko a cikin barcinta hakan ba zai faru ba amma zuciyarta sai kara karfafa mata guiwa take yi a kan ta yarda.
Mariya da Mu’azzam suka iso garesu kallon kallo suka shiga yi a tsakaninsu Bello na duban su Mariya da Mu’azzam yana kuma duban Umma wacce ta zama wata butun butumi a tsaye zuciyarta take ji tana mikata wani mataki mai girma dauke da tashin hankali da ciwon rai ciwo ne mai girma zuciyarta ta fama mata shi wanda take ta jinyarsa ya kasa warkewa.
Duban Mariya yayi yana son yin magana amma ya kasa wani irin yanayi yake jin kansa a ciki ji yake yi kamar ba shi ba.
Sallamar da su Baffa sukayi ne ya sanya Umma mutuwar tsaye zuciyarta tayi wani bugun da sai da kirjinta ya daga da saurin ta runtse idanun tare da yin cikin gida da sauri sai faman hada hanye take yi.
A daidai lokacin da suka shigo ta karasa shigewa cikin gidan don haka Bello yayi musu jagora suka karasa shiga sai bin gidan suke yi da kallo Baffa na faman gyaɗa kai zuciyarsa na matsewa da ciwon da yake ji yana motsa masa tsayin lokaci wai shine yau a garin Gwada garin da yayi wa kansa alkawarin ba zai taba
WAIWAYE izuwa gareshi ba yau shine a ciki a kuma gidan da ‘yarsa take aure wacce ita ce silar barin sa garin hawaye idanuwansa suka kawo da sauri ya shafe su ciki da nadamar abin da ya aikata wanda yake jin ya cuci kansa sannan ya cuci ‘yarsa.
STORY CONTINUES BELOW
Har cikin dakin su ka shiga zaune take ta hada kai da kafafuwanta zuciyarta na ta faman harbawa da wani tashin hankali mai girman gaske sallamar da taji Muryar Baffa na yi ne ya kara jefata tashin hankali runtse idanuwanta tayi gami da sake kankame kanta da sauri Mariya ta isa gareta ta zauna gefenta ganin halin da mahaifiyar tata take ciki ya sanya ta duban su Baffa da sukayi carko-carko a tsakar dakin lokaci guda kirjinta taji ya buga kallon Baffa ta shiga yi
zuciyarta na dauko mata wani lamari da tunanin mai girma da take son ta tabbatar da gaskiya a kansa can kasar zuciyarta take furta ‘Baffa’ da sauri ta sake duban Umma sannan ta dubi Baffa zaro idanu tayi waje ta shiga nuna shi da yatsa laɓɓanta sai motsawa suke yi.
“Umma dago kanki wannan kamar Baffanki?”.
Mariya ta fadi Muryarta na rawa sosai Baffa da ke tsaye a hankali ya tako ya iso garesu hannun Umma ya riko wanda taji rikon a bazata sosai ta firgita tare da kau da kanta domin bata son kallonsa ta san ita mai laifi ne laifin ta mai girma ne a gareshi.
“HABEEBA!”.
Ta ji ya ambaci sunanta da muryar mai laushi wacce rabon da taji ta har ta manta dago kanta tayi wanda sukayi face-gace da hawaye ta sauke a fuskarsa murmushi ta ga yanayi mata hakan ba karamin mamaki ya bata ba bakin ta na rawa.
“Baffa na san ni mai laifi ce ban cancanta ka dube ni ba ban cancan ci ka zo gareni ba Baffa na tuba na san na kuntata maka na san na dasa maka ciwo a zuciya shiyasa tun da na rabu da kai har yau ban samu natsuwa da kwanciyar hankali ba…”.
“Habeeba”.
Ya sake fadi da muryarsa mai taushi gami da nuna mata alamun tayi shiru hakan yayi matukar bata mamaki wai Baffanta ne haka yau shine yake yi mata magana a cikin salama ba zata taba manta ranar da ya rabu da ita ba ya mikata a hannun Bello yace ya yafeta amma yaushi ne a gareta abun yayi matukar daure mata kai sake runtse idanu tayi don ita har yanzu ba ta yarda wai Baffa da Bello bane a gabanta.
“Habeeba ki daina fadin haka ni Mahaifinki ne nasan na dauki hakkinki na sanya ki cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali a dalilin son zuciya irin tawa ina neman afuwanki ki yafe mani nima na yafe miki duk wani laifi da ki kayi mani ga mijin ki nan ya fada min komai”.
Wani kuka ne ya sake sarke ta shiga yin sa ba kankautawa ba wanda bai tausaya mata ba cikin dakin Ja’e da Iro su kan su sai da suka ji tausayin yayar ta su gwuiwowinta a kasa take neman afuwan Baffa Mariya da Mu’azzam suma haka suke yi suna taya ta rokon Baffa kamar yarda suka ga tana yi sai da suka shafe tsayin lokaci a haka kafun suka yi shiru nan dakin ya dau shiru.
Baffa ya shiga karanta mata komai da ya faru da Bello don sam! Umma kamar ba tayi maraba dashi ba sosai yayi mata bayani sannan ta yarda shima ya kora mata da irin matsalolin da ya fuskata da irin SIRAƊIN RAYUWA da ya fada sosai Umma tayi kuka jin irin bala’in da mijinta ya fada ciki musamman da taji yace bai san lokacin da ya tafi ya bar su ba shi dai kawai ya tsincin kansa a wani waje ne.
“Wai hayaniyar me nake ji ne cikin dakin nan tun dazu kamar gidan yan barik…”.
Guntse sauran maganar ta tayi daidai lokacin da ta daga labule idanuwanta suka sauka kan na Bello da ya kafe ta da idanu hannunsa rungume da Mu’azzam mutuwar tsaye tayi kafun ta dawo hayyacinta tana duban mutannan cikin dakin daya bayan daya idanuwa a warwaje kamar wacce tayi wa sarki karya bakinta ya fara motsi jikinta yana rawa ta shiga fadin.
“Bello dama kana duniyar nan”.
Da sauri ya ansata da murmushi a fuskarsa.
“Ga zahiri kin gani Goggo Marka”.
Da sauri ta juya tayi waje har tana tuntube dukansu suƙa hada idanusu kowa da abinda ke ransa…Hajiya Layla ce ta dubeshi a karo na ba adadi zuciyarta na mikata wani mataki na tausayi amma so take yi ta kwace kanta domin sam Dr.Erena ba abin tausayi bane ba abin ma a tsaya ana sauraron batutuwan da yake yi bane na rashin hanyyaci.+
sosai zuciyarta take kuna gami da suya kwanyarta take ji tana kokarin kamawa da wuta laɓɓanta ta shiga motsawa tana kokarin yin magana amma ta kasa sai ma wani tari da ya zo mata da sauri ta koma gefe nesa da inda Dr.Erena yake a kwance saman gadon asibiti yana ta faman
numfarfashi gabadaya ya sauya daga kamanininsa yayi wani irin baki ga idanuwansa da sukayi jajir sunyo waje sosai bakinsa ya karkace ya koma ɓarin dama fuskarsa gabadaya duk ta mokaɗe.
Tari take yi sosai wanda har sai da ya kaita zaunawa tana dafe da kirjinta hannu daya kuma ta rufe bakinta dashi sosai tarin take jinsa yana mata ciwo daga cikinta har zuwa kirjinta da take ji kamar zai fashe.
Areefa dake zaune can gefe daya takure gabadaya ita kanta tayi zuru-zuru kamar wacce ta tashi daga amai da gudawa mikewa tayi da sauri gami da daukar gorar ruwa ta nufi wajanta gami da riko mata hannu sai dai me? Abin da ta gani ya sanyata saurin ja da baya tana duban hannun Hajiya Layla da ta cire daga bakinta
sosai idanuwanta sukayo waje wani bakin abu ne mai kauri gami da yauk’i yake zubowa daga bakinta runtse idanu Areefa tayi sannan ta buɗe mikar da Hajiya Layla tayi ta kai ta Toilet ta wanke mata baki sannan suka fito.
Gefe guda ta zauna tana ta faman mai da numfashi kamar wacce tayi gudun ceton rai.
Sosai zuciyar Areefa ta karye sosai take jin wani irin abu nayi mata ciwo a zuciyarta tsoro na kara bayyana yanayin da take ganin Hajiya Layla a ciki ba karamin tashin hankali yake saka bata ba tun yau ba ta lura da ita tana cikin matsala amma take boye mata ko tayi mata magana su je asibiti a dubata cewa take yi a,a ta barshi akwai maganin da take sha a da can baya tana dadewa bata yi ba amma yanzu a wuni sai tayi tari yafi a lissafa.
Motsin buɗe kofa ne ya katse mata tunanin zucin da take yi da sauri ta dubi kofar Alhaji Abdulwahaab ne ya shigo fuskarsa a tanke kamar ba a taba halittar fara’a fuskar ta shi ba duban su yayi su duka ganin yanayin da Hajiya Layla ke ciki ya sanya shi tsaida kallonsa a kanta.
“Hajiya Layla ya ya dai na ganki cikin wannan yanayin?”.
Girgiza kai tayi ba tare da tace dashi komai ba can gefe yayi ya dauko Remote dake kan loka din gadon asibitin ya shiga Control din Tv bango da yake a kusurwar dakin na dama a can sama a hankali ya shiga canza tasha har ya zo kan tashar NSTV MINNA sannan ya tsaya yana mai maida hannayensa duka baya ya juyo ya dubesu suma shi suke duba bai ce musu komai ba har illa nuni da yayi musu su mai da hankalin su kan labaran da ake yi cikin harshen turanci.
A hankali ka shiga labarai hankalin su na kai har aka zo in da ya kusan kashe su a zaune Areefa ce ta mike da sauri tana nuna Tv da dan yatsarta dake ta faman rawa Company din Dr.Erena na ne aka nuna yan kwana kwana na ta aikin kokarin kashe wutar da take ta faman ci akan sa kamar WUTAR DAJI sosai mutane suka cika wajan sai faman kallo ake yi yan kwanakwana na ta aikin su amma ina kamar kara rura wutar ake yi.
Dr.Erena da yake cikin halin rashin hayyaci da yake Tv din na saitin sa idanuwansa na kan Tv din ganin abin da ake haskowa ya kara rikita masa jiki da sauri ya shiga mutsu-mutsu yana faman kakari yana kokarin daga yatsarsa amma ya kasa dukkan su duban sa suka shiga yi ba wanda ya motsa suka cigaba da kallon su ihun da yake kurmawa ne da wani irin kuka kamar na kare ya kara rikita dakin da sauri Alhaji Abdulwahaab ya kashe TV din tare da komawa gefe ya harɗe hannayensa yana duban su Areefa da hankalin su ya gama tashi.
STORY CONTINUES BELOW
“Ajiya cikin dare Company ya kama da wuta ba tare da kowa ya sani ba tun misalin karfe biyu na dare a halin da ake yanzu duk masu gadin Company din sun mutu wajajen Asuba ne aka ankara da wutar nan aka sanar da yan kwana-kwana suka iso to dai har zuwa wannan lokacin ba suyi nasarar kashe wutar ba kuma sai kara ci take yi yanzu haka fitar da nayi can na nufa manaja din ne ya kira ni yake sanar dani abin da ke faruwa”.
Ya karashe cikin nuna halin-ko-in-kula yana duban Dr.Erena da ya gama ficewa daga hayyacinsa gabadaya ya muttsuke jikinsa yana ta faman kartar fuskarsa.
Jinin da yake zuba a bakinsa ne bakinkirin ga hannayensa da ya saka ya shake wuyansa a hankali ya dinga ihu mai tsananin kara lokaci guda ya tiko kasa yana numfashi kirjinsa na faman dagawa lokaci guda kuma ya tsagaita ya daina motsi gabadaya.
“Kun ga ku tashi mu bar asibitin nan tun kafin wahalar mutumin nan ta kashe mu ai mun yi masa na Allah tunda har muka kawo shi asibiti mukayi jinyarsa ta kwanaki”.
Ya fadi yana duban su kafin ya shiga toshe hancinsa wani irin warine yaji ya karaɗe dakin gabadaya da sauri ya juya ya fice ji yayi kan sa na juyawa Hajiya Layla ce ta dubi Areefa da tayi tsaye cikin tsananin tashin hankali ganin yarda Dr.Erena ya koma kamar bashi ba wani irin tsoro da fargaba suka shige ta ta daga hannu tana kokarin nuna shi da sauri Hajiya Layla ta riko mata hannu suka fice daga cikin dakin.
Alhaji Abdulwahaab suka hango tafe da wani likita cikin hanzari ya iso garesu gami da duban su kafin yasaka kai cikin dakin runtse idanu yayi ganin yarda Dr.Erena suffar ta juye ta koma kamar ta kare a hankali ya taka hannunsa toshe da hancinsa jin warin da yake yi dubansa ya shiga yi kafun ya tabo wuyansa sannan ya shiga auna shi sosai ya tsorata ganin baya numfashi sake auna shi yayi domin tabbatar da abin da yake zargi mikewa yayi kan kafafuwansa.
Yana kokarin fita ya ji wani kuka mai kama dana kare ya karaɗe dakin shi kansa sai da ya tsora ta da sauri ya juya ya dube shi gani yayi ya dawo hayyacinsa yana numfashi kusa dashi likitan ya karasa bakinsa ya gani yana motsi magana yake yi amma bata fita sai da yayi tari gami da watso wani bakin jini sannan sunan Areefa ya fito daga bakinsa yana faman nuna kofar waje jikinsa sai karkarwa yake yi juyawa likita yayi ya dubi kofar gami da mikewa ya fita can ya hango su har sun kusan barin bangaren kwala musu kira yayi gabadayan su suka juyo yayi musu nuni da hannu da su dawo.
Ko kallon arzuki ba suyi masa ba sai da yayi musu magiya sannan Areefa da Hajiya Layla suka dawo jan su yayi cikin daki suna shiga suka tadda Dr.Erena magashiyan likita ne ya isa gareshi gami da dago hannunsa ya saki ya fadi ragwaf da dauri ya sake duba sa saidai ina tuni lokaci yayi.
Numfashi ya ja mai karfi gami da mikewa kan kafafuwansa yana duban su gyaɗa kai ya shiga yi.
“Allah yayi masa cikawa”.
Zaro idanu sukayi waje gabadayan su kafun Hajiya Layla ta dubi Dr.Erena wani irin yanayi ta ji ta a ciki zuciyarta na kara tsorata wata irin nadama da kaicon wannan rayuwar tayi sosai take jin zuciyarta na mikata wani mataki na tsoro wai yau Dr.Erena ne haka cikin wulakantaccen yanayi cikin yanayin da ko kallonsa ba za ayi ba batare da an kau da kai ba wai yau Dr.Erena na ne haka duniya kenan mai yayi duniya kenan wacce ba ma tabbata ba kuma ba aljanna ba.
Da sauri ta dubi Areefa wacce jikinta ya gama yin sanyi sosai idanuwanta du cika da kwalla hannunta ta kama tana kokarin fidda su daga cikin dakin likitan ne ya tsaida su yana mai fadin.
“Sai ku zo ku dauki gawar ko domin yi mata suttura”.
Ko ta kan sa ba su bi ma shima bai damu ba duk a nasa tunanin mutuwarce duk ta ruɗa su haka shimfiɗar gadon ya janyo ya lullube gawar gami da ficewa daga cikin dakin yana jan kofar.
STORY CONTINUES BELOW
******
Kwance take tayi ruf! da ciki tunanin duniya duk yabi ya dame ta gaɓadaya duniyar take ji ta tsana komai na cikinta ya daina burgeta zuciyarta sosai ta tsorata ba abin da take tunawa sai yarda ta ga Dr.Erena ya koma kamar bashi ba halittarsa gabadaya ta sauya kamar ba ta DAN’ADAM ba Company din sa take tunawa yarda taga yana ci da wuta tunda take a rayuwarta bata taba ganin harshen wuta na tashi kamar igiya ba sai ranar wuta har kore-kore take yi yarda taga ana watsa ruwa amma kamar ana kara rura wutar hakan yayi matukar daure mata kai.
Dafa kafadar da ta ji anyi ne ya sanya ta saurin jan numfashi gami da dawowa hayyacinta mikewa tayi ta zauna tana duban fuskar Hajiya Layla da murmushin yak’e zama tayi bakin gadon itama tana dubanta cikin wani irin yanayi kafun ta ja numfashi ita ma.
“KHAIRIYYA!”.
Ta fadi da wata kwantacciyar murya da sauri Areefa ta dubeta jin ta kira sunanta na asali.
“Ya kamata ace kin ajje komai a gefe na sani batun Dr.Erena na ne ke damun ki ba wani abu ba kuma ya kamata ki ajje batun sa agefe shi ai duniyarsa ta kare”.
Gyaɗa kai Areefa tayi gami da goge kwallar da ta zubo masa.
“Maama zuciyata nake jin wani iri wallahi babu dadi tsoro nake ji yanayin da na ganshi a ciki”.
“Khairiyya kenan ai duk wanda yace zai kauce hanyar Allah yana aikata abin da ransa ke so aiko ba zai taba ganin daidai a rayuwarsa ba kin ga dai Dr.Erena kin ga yarda rayuwarsa ta kare a duniyar nan baki daya
kamar ba a taba yin mai sunansa ba kina dai ganin dukiyar da ya tara da kadarori amma ba su yi masa amfani ba kin ga kenan duniyar ma bakidayanta ba komai bane wajan Allah balle kuma bawa da yake a cikinta yake abin da ransa ke so”.
Gyaɗa kai Kawai take yi tana jin wani tsoro na kara ratsa mata zuciya da duk wani sashi na jikinta sosai ta firgita da yanayin wannan rayuwa a wannan duniyar.
“in har son zuciya zai zama ado ga dan’adam to tabbas yana cikin gagarin rayuwa in har dan’adam zai daura wa kansa buri na son abun duniya to yana tare da tashin hankali”.
ta sake fadi tana riko hannayen Khairiyya idanuwanta na kawo kwalla.
“Khairiyya ki yafe mani na san nayi miki laifi mai girman gaske a filin duniyarki ina da hannu dumu-dumu wajan fadawarki wannan bala’in da kika fuskarta ina mai rokon afuwarki a karo na ba a dadi Khairiyya nayi dana sanin mu’amala da Dr.Erena nayi nadama nayi kaico in da nasan wannan rayuwar zan zaba miki wallahi ba zan taba amincewa da bukatarsa ba…”.
Da sauri Khairiyya ta kai hannunta saitin bakinta tana rufewa.
“A,a Maama ki daina fadin haka dama can tun fil’azal ALKALAMIN ƘADDARA ya rubuto min hakan sai ya faru a gareni ba laifin ki a ciki”.
Wani kuka ne ya kwacewa Hajiya Layla sake damke hannun Khairiyya tayi tana jin wani irin kauna da sonta na kara ratsa mata zuciya da dukkan gangar jikinta sosai take jin Khairiyya kamar ita ta haife ta.
“Ban san iyaye na ba san nan na rayuwa cikin kazamar rayuwa gashi ni ba aure nayi ba bare na samu wata zuri’a da za su jibance ni ina cikin UKU BALA’I a rayuwa ta Khairiyya…”.
Da sauri ta sake rufe mata baki hawaye na wanke mata fuska itama.
“Ki daina fadin haka Maama kina da dangi kina da zuri’a ni duk zan zame miki duk wadannan abubuwan da kika rasa a rayuwa ki dauke ni a matsayin ‘Ya Maama ki rikeni har karshen rayuwa mu rayu tare cikin MARAICI da ALKALAMIN ƘADDARA ya zano mana a rayuwar nan tamu”.
Sosai ta rungumeta ta matse ta a jikinta wani kuka ne sukeyi gabadayan su mai taba zuciya da ruhi kuka suke yi gabadaya sun fice daga hayyacin su an rasa mai rarrashin dan’uwansa a tsakaninsu sai da
sukayi mai isar su sannan Khairiyya ta kokarta tayi shiru tana rarrashin Hajiya Layla wacce kukan nata ya kasa tsagaitawa sai yinsa take yi mai hade da tari kamar ranta zai fita…Duban idanuwanta yake yi dauke da wani irin yanayi mai taba zuciyar masoya wanda suka tsumu cikin kugin soyayya da kaunar juna fuskarsa sai kara yalwatuwa take yi da murmushi mai girman gaske janye idanuwansa yayi lokaci guda yana mai da numfashi kafun ya motsa laɓɓansa.+
“Mariya kin yi shiru baki ce komai”.
Murmushi ita ma tayi gami da tura dan yatsanta guda cikin baki kafun ta shiga kokarin magana.
“Duniyarnan a yanzu jin ta nake kamar ba wanda ya kai ni farinciki a cikinta”.
Cikin mamaki da tuhuma yake dubanta jin abin da tace dashi sosai yake ji a zuciyarsa wani iri yanayi musamman yarda ya ga ta saki jiki dashi yau rana daya tana dariya gami da murmushin da yake kokarin hallaka masa zuciya.
“me ke faruwa ne Preety? da alamun zuciyoyi sun kusan barin kunci zuwa farinciki”.
Runtse idanu tayi gami da buɗe su sosai akan sa kafun ta juya ta kalli kofar gidansu.
“Mahaifina ya dawo”.
Zare idanu yayi cikin mamaki da kuma al’ajabi bakin sa yake motsawa yana son yin magana amma ya kasa wani farinciki ya ke jin kansa a ciki a daidai wannan lokaci da bai taba
tsammani ba lokaci guda yaji kamar an watsa shi cikin aljanna don farin cikin da sauri ya kara takowa zuwa gareta kamar zai hade jikinsa da nata da sauri ta ja baya da murmushi afuskarta.
“Are you Seriuos?”.
Ya fadi yana mai tallaɓe haɓarsa sai faman zabga murmushi yake yi gyaɗa masa kai tayi da sauri ya juya yana kokarin tunkarar kofar gidan da sauri ta daga masa hannu tana mai sanya idanuwanta cikin nasa.
“Me kenan kake kokarin yi?”.
“Oh God! don Allah ki bar ni naje na gan shi kin ji kuwa yarda zuciyata take farin ciki kin ji irin dadin da nake ji a wannan ranar sosai nake jina a wani mataki mai girma wanda na jima ban shige shi ba ZUCIYARMU DAYA ne ni dake abu daya muka zama dole na tayaki farinciki dole na nuna kauna ga yanayin da kike ciki ayanzu”.
Yana gama fadin haka ya riko hannayenta ya fara kokarin janta da sauri ta fizge tana dubansa lokaci guda ta daure fuska tamau kamar ba ita bace mai dariya da farinciki yanzu idanuwanta take amfani da su tana tura masa hukuncin kuskuren da yayi a yanzu abin da ta tsana abin da bata so shine yau yayi mata tana soron irin wannan yanayin sam bata so ko
numfashi suna hadawa da ɗa namiji domin kuwa sosai ta tsorata dashi musamman ganin halin da Hafsat ta shiga A DALILIN ƊA NAMIJI duk da dai ita har da yardarta da amincewarta domin ba yarda za ayi namiji ya saka mace yin abu dole ba tare da amincewarta.
Sosai ya gane yayi kuskure sosai yake jin kallon da take masa yana bula masa jiki yana yanke masa hukunci mai girma runtse idanu yayi ganin yarda fuskar tata ta sauya a lokaci guda.
“Kiyi hakuri Mariya hakan ba halina bane ban yi da wata manufa ba dokin farincikin ki ne shi ya je fani a wannan matakin da na so aikata kuskure mafi girma a gareki”.
Kau da kanta tayi batare da ta ce dashi kala ba ta fara tafiya domin komawa cikin gida shi kansa ya tsorota sosai ganin yanayin da take ciki a hankali ya fara bin ta a baya tana jin ta kunsa amma tayi banza dashi domin kuwa sai ta nuna masa kuskurensa ko da kuwa ba da gangan yayi ba.
STORY CONTINUES BELOW
Ko da suka isa cikin soro juyowa kawai tayi ta dubeshi ta dauke kanta hakan ya sanya shi saurin tsayawa sai faman ware idanu yake yi yana jin yarda zuciyarsa ke wani irin abu kamar zata faso kirji ta fito waje.
Bai san gangancin da ya kai shi aikata haka ba bai san tsautsayi da ruɗun da ya shige shi ba har ya aikata haka ba yake kokarin yiwa kasan salalar tsiya ya manta rabon da ya ga bacin ran Mariya amma yau daya abi sa kuskuren sa yana kokarin yi wa kansa SAGEGEDUWA…
Motsin da yaji ne ya sanya shi saurin dawowa hayyacinsa daga duniyar tunani Mu’azzam ya gani tsaye hannunsa dauke da babbar sallaya da sauri ya isa gareshi yana kamo hannusa gami da durkusawa gabansa yana kallon sa cikin idanuwansa da wani irin yanayi riko sosai yayi wa Mu’azzam har sai da ya fara mutsu-mutsun kwace kansa.
“Dagaske Abba ya dawo?”.
Ya tambayeshi don ya rasa ma abin da zai ce dashi fuskarsa yake kallo kamar ta Mariya sak! Runtse idanu yayi kafun yaja wani dogon numfashi ganin yarda Mu’azzam ke kallon sa kamar a tsora ce.
Sakin sa yayi gami da mikewa ya anshi Sallayar ya shimfida Mu’azzam ya juya yana kokarin komawa ciki ya riko shi gami da jan sa a jikinsa suka zauna kan sallayar.
Sun dauki lokaci a haka Dr.Karami sai faman tambayarsa yake tun yana ɗari-ɗari dashi har ya saki jiki dashi yana bashi labarin abin da ya sani suna cikin haka sai ga Abban ya fito da sauri Dr.Karami ya shiga kokarin mikewa yana sauka daga kan Sallayar yana zubewa cikin girmamawa da ladabi da sauri Abba ya riko shi fuskarsa da murmushi a cikinta.
“Haba Hisham meye kuma haka kake yi sai kace wani karamin yaro tashi ka koma ka zauna”.
Ya fadi yana mika masa hannu suyi musabaha amma Dr.Karami sai wani nokewa yake yi yana mai jawo Mu’azzam yana zaunar dashi kan cinyarsa.
Soron ne ya dau shiru na yan dakikai kafun Dr.Karami ya kara kasa da kai cikin murya kasa-kasa ya shiga yi masa jaje akan abin da ya faru.
“Bakomai Hisham komai da ka ga ya faru a duniyar nan to dama tun fil’azal Allah ya rubuto shi a KUNDIN ƘADDARARMU”.
Ya nisa gami da sake duban Dr.Karami sosai, da kansa ke kasa wata kunya ce yaji ta lullube shi tun da yake bai taba yin haka ba yau ce rana ta farko duk sai ya jishi wani banbarakwai.
“Ban san da bakin da zance da kai komai ba, ban san da wasu irin kalamai zan yi maka godiya ba, Hisham kayi mani komai a rayuwa kayi mani abin da ko dangina da yan’uwana bana tunanin akwai wanda zai iya hakan. Sosai naji dadi sosai naji farin ciki zuciyata ta jima tana kuna da takaici acan cikin wahalar da na tsinci kai na ban damu da tawa rayuwar ba sai ta IYALINA sosai nayi kuka nayi bakin ciki akan rashin basu kariya a ga rayuwarsu musamman a yarda na bar su na shiga tashin hankali tashin hankali mai girman gaske na tsani kai na tsani rayuwar da nayi dalilin ban san halin da IYALINA suke ciki ba…”.
“Abba da ka daina TUNA BAYA abin da ya wuce ya rigaya ya wuce kuma komai ya faru damu a duniyar nan ALKALAMIN ƘADDARA ne sila ba a son ranka komai ya faru ba ba wai kayi haka bane da wata manufa Allah ya ƙaddara sai ka je wani wajan ka rayu akwai abin da Allah ya gani ya sanya ya turaka wata duniyar kayi rayuwa”.
Dr.Karami ya fadi muryarsa can kasa sai faman wasa yake yi da yatsun hannun Mu’azzam.
Hawaye Abba ya goge wanda bai san sun zubo masa ba sai da ya ji dumin su a hankali ya shiga baiwa Dr.Karami labarin rayuwar da ya tsinci kan sa har izuwa haduwarsu da Baffa…
STORY CONTINUES BELOW
Sosai ya ji zuciyarsa wani iri sosai yaji tausayin su Mariya ya kamashi dago kai yayi ya dubi Abba da idanuwansa ke ta faman ZUBAR KWALLA zuciyarsa yaji tana kara matsewa da kaunar ahalin nan masu ciki da SADAUKARWA da kaunar juna su musamman yarda yaji AKAN SO suka fada wannan rayuwar su dukan su ashe haka akewa SO BIYAYYA ashe haka ake sadauƙar da komai da kowa a rungumi masoyi ashe shi bai ma yi so ba.
Numfashi yaja mai karfi yana sake duban Abba wanda ya shafe fuskarsa kamar bai yi kukan ba sosai yake duban Dr.Karami yana jin wata kaunarsa na ratsa masa zuciya sosai yake jin zai iya yarda ya zama mijin ‘yarsa domin ya yi amanna dashi da kuma irin nagartarsa ya tabbata ‘yarsa ba zata koka ba a gidan sa so yake yi yayi masa magana amma ya kasa so yake yi yaji daga bakin sa in har ya furta KALMAR SO ga Mariya shi kuwa zai masa tukuici da ita.
A hankali Dr.Karami ya shiga kokarin tashi alamun tafiya sallama sukayi ya mike har zuwa lokacin Mu’azzam na like dashi hannu ya saka ya zaro kudi masu dan dama ya ajje kan sallayar ya juya yana kokarin tafiya.
“HISHAM!”.
Yaji Abba da wata irin muryar mai girma da zurfi a jikinsa yake ji kamar akwai abin da yayi ba daidai ba da sauri ya juyo ya dubi Abba kallon da ya ga yanayi masa yayi matukar bugar masa da zuciya sai dai murmushin da ya gani kuma ya bashi mamaki.
“Zo ka dauki kudin ka don Allah”.
Ya fadi shima yana mikewa yana kara faɗaɗa murmushin sa, kuri yayi masa da idanu wani irin kwarjini ya ga yanayi masa magana yake so yayi amma ya kasa a hankali ya ja kafafuwansa ya iso gami da sanya hannu ya dauki kuɗaɗen.
“Abba kayi Hakuri…”.
“Bakomai Hisham hidimar za tayi yawa ka gaishe da Hajiyar taka”.
Ya fadi yana mai juyawa ya koma cikin gida cike da farin ciki da kwanciyar hankali yarda yaga halayen Dr.Karami dama tuni Umma duk ta karance masa komai da komai da yake faruwa.
Dr.Karami hannusa rike da na Mu’azzam suka isa bakin motarsa ya buɗe wata katuwar leda ya dauko ya mika masa kafun ya sake dauko wata ya bashi.
“Wannan taka ce kai kadai ko Yah Mariya karka baiwa wannan kuma Umma za ka kaiwa”.
Dariya yayi gami da fadin ‘Nagode’ sannan ya juya ya fara tafiya yana daga masa hannu shima hannu yake daga masa yana jin kaunar wannan Iyalin na kara ratsa masa zuciya da ruhinsa..
*****
Da mamaki yake dubanta zuciyarsa na yayyagewa da tashin hankali bai taba zaton abin da zata fada masa ba kenan bai taba zaton in ya zo abin da zai tadda ba kenan in da yasan
wannan bakar maganar zai tadda da bai zo ba zuciyarsa kara matsewa take yi da tashin hankali idanuwansa sun kaɗa sun yi ja duk wani farinciki da ya jima yana yi tun da yaji ta sanar dashi dawowar mahaifinta har rawar jiki yake yi wajan zuwa taya ta murna sai dai ashe ba nan gizo ke sakar ba.
numfashi yake ja wanda yake jin sa kamar zai tafi masa da ransa duban ta yasake yi karo ba adadi kanta akasa yake yana hango yarda hawaye ke zubowa saman kuncin ta wani irim rauni ya sake jin zuciyarsa tana kara mikashi a ciki, hannayensa duk biyu ya dafe kansa dashi da yake jin yana faman kumbura kamar zai tarwatse laɓɓasa ya tura cikin bakin sa yana cizawa.
“Mariya dama bakya so na dama duk BIYAYYAR SO da nake yi akan ki ta banza ce ashe akwai ranar da zaki nuna min iyakata haba! Mariya don Allah karki ce dani wannan maganar gaskiya ce don Allah ki ce wasa kike yi”.
Ya fadi yana jin duniyar na kara yamutse masa da wani irin tashin hankali mai girman gaske dago idanuwanta tayi wanda suka kaɗa sukayi jajir bakin ta sai rawa yake yi hannayenta dafe da kirjnta da take ji kamar zai tarwatse ita kanta ta san tayi ganganci ba ta san abin da yasa ta aikata hakan ba abin da take gudu kenan nayin BUTULCI ga Dr.Aqeel ta san batayi masa adalci ba batayi wa ita kanta adalci ba numfashi ta ja kafun ta sake dubansa sosai.
“Kayi hakuri Dr.Aqeel ban yi haka don na tsane ka ba hasali ma ni ce mai son ka da kaunar k…”.
“Ya isa haka ki daina yiwa so karya akai na kawai ki fito fili kice bani kike so ba wani na kike so”.
Runtse idanu tayi tana jin sautin muryarsa mai sauti tana dukan zuciyarta da kwanyarta wani kuka ne ya kwace mata da sauri ta rufe bakinta jikinta ya shiga rawa numfashinta ya shiga tsittsinkewa hakan da Dr.Aqeel ya gani ya kara rikita shi da sauri ya iso gareta ji yake yi kamar ya rikota ya hadata da jikinsa ya rarrashe ta.
“Kayi hakuri na san ban kyauta maka ba na san naci amanar soyayyarmu amma ina so ka dube ni da idon basira sannan ka fahimce ni ban yi haka don in tozarta ka ba ban yi haka don ba na son ka ba in da bana son ka ba yarda za ayi har nake tsayuwa da kai in da bana son ka ba yarda za ayi na bar zuciyata ta kauna ce ka ka sani ni da Baseera abu daya ne duk wani abu da kake tsammanin zaka samu gareni na kulawa da biyayya a
soyayarka zaka samu a gareta fiye ma da haka hasali ma Baseera tafi ni komai da komai na rayuwa ina rokonka don Allah don Annabi ka dauki Baseera kamar yarda kake dauka ta ka sannan ina so kayi mata so kamar yarda kake yi mani koma fiye da hakan don Allah na roke ka in har son da kake yi mani kana so na kara gasgata shi to ina so ka komar dashi kanta”.
Ta fadi cikin rawar murya a hankali ta shiga ja da baya idanuwanta na kara ballewa da hawaye hannu ta daga masa kafun ta juya cikin sauri ta fada cikin gida.
Runtse idanu yayi maganganunta yake ji suna yi masa yawo akai zuciyarsa yake ji tana kara matsewa da kalamanta da sauri ya ja jiki kafafuwansa yake ji suna harɗewa kamar za su zubda shi kasa ya fada cikin motarsa tare da yi mata key ya fizgeta ya fice daga cikin unguwar zuciyarsa na wani irin mataki wanda ba zai ce gashi ba…Sosai ya kasa gane kansa komai yake jinsa yana sauya masa lokaci guda zuciyarsa yake ji tana harbawa da wani irin yanayi mai raɗaɗi a zuciya bai san yarda zai yi ba bai san abin da ya kamata yayi ba zuciyarsa ta cushe kwanyarsa sai hayaki take yi kamar zata kama da wuta duniyar gabadaya yake ji tana kai komo dashi jin sa yake kamar bashi ba kamar wani daban aka dauko aka ajje.+
Numfashi yasake ja karo na ba a dadi yau kusan kwana uku kenan yana jinyar kansa kokari yake yi ya saita kansa amma hakan ya gagara zuciyarsa taki amanna akan abin da ake so yayi sosai yake jin GURBIN SO mai girma wanda ya baiwa Mariya ba zai iya barinsa ya so wata daban ba baya tunanin hakan zai iya
kasantuwa son Mariya ta zama komai nashi ita ce rayuwarsa dama numfashin sa baya tunanin rayuwarsa zata yi karko in har ba soyayyar Mariya bace tadawo gareshi sosai yake kallon kansa a matsayin GAWA DA RAI.
Hannayensa duka biyu ya dafe kansa da su yana faman jan numfashi mikewa yayi kan gadon yayi zaman dirshan gami da zabga tagumi
yawatawa ya shiga yi da idanuwansa komai gani yake yi yana sauya masa komai yake ganin baya burgesa a filin duniyar nan komai yake ji kamar ciwo ne a gareshi zuciyarsa yake ji tana matsewa da wani irin tashin hankali mai girman gaske ji yake yi ko wani sashi da lungu na zuciyarsa na kara yayyagewa da son Mariya kokari yake yi ko zai iya abun da ta bukata amma ji yake yi kamar kara rura wutar sonta ake yi a zuciyarsa.
A hankali ya zuro kafafuwansa zuwa kasa ya mike akan su jikinsa sanye da kayan barci farare masu dingo blue maballin gaban rigar ya gyara da ya fice ya zura silifas din dake yashe a kasa toilet ya nufa cikin rashin kwarin jiki da na zuciya.
Yana shiga ya sakarwa kansa shawa mai ruwan dumi sosai yake jin ruwan na ratse shi ta ko ina zuciyarsa dake zafi yake jin tana sauka kadan-kadan runtse idanuwansa yayi yana furta.
“Yaa Hayyu Yaa Kayyum”.
Kusan minti ashirin ya shafe a toilet din kafun ya wanke bakinsa gami da dauro tawul a kugunsa da wani kuma a hannunsa yana tsane kansa da sajen fuskarsa da yake karawa fuskart asa kyau da kwarjini fitowa yayi ya tsaya gaban Mirrow yana kallon kansa sosai yake hango ramar da yayi shi kadai ya san wahalar da yake sha shi kadai ya san azabar da zuciyarsa take kawo masa gabadaya ya daina jin dadin
komai WALWALAR ZUCIYA gabadaya yanzu bai samunta har ya manta yaushe rabonsa ya jidadi da nishadi a duniyarsa.
Numfashi ya ja gami da juyawa ya nufi sif din dake manne da bangon dakin buɗewa yayi yana kallon ko wani sashi na cikin sa kaya ne makil a cikinsa a shirye hannu ya sa ya shiga dagawa yana kallo so yake yi ya zabi wanda zai saka amma gabadaya
kayan ma jin su yake yi wani iri ya jima a tsaye yana zarowa yana mai dawa ya rasa wanda zai dauko lokaci kankani duk ya yamotse sif din kafin ya zaro wani lallausar yaɗi light-blue mai dikon dark anyi masa dinkin zamani wanda ya fita sosai.
Bakin gado ya ajje su sannan ya juya ya koma wajan Mirrow din fuskarsa ya dan gyara sannan ya koma ya zura kayan a jikinsa wanda sukayi
matukar hawan sa sosai suka kara fidda masa da kyansa gami da kwarji agogon Rolex ya daura a hannunsa gami da kafa hularsa wacce ta hau kayan sosai takalmin kafarsa sau ciki baki sai daukar idanu yake yi glass ya saka a idanuwansa wanda ya kara sirrinta yanayin da yake ciki.
Key din motarsa ya dauka gami da wayoyin sa bayan ya feshe jikinsa da daɗaɗar turarurruka masu sanyin kamshi a hankali ya shiga taka kafafuwanta yanayin sa kadai zai nuna maka ba ya cikin nishadin zuciya saidai cikar halintarsa da mazatakarsa da ka kalla zaka gane namiji hadadde mai ansa sunan sa na mijin.
STORY CONTINUES BELOW
Kokari yake yi ya aikata abin da zuciyarsa take hana shi so yake yi ya koyi wannan rayuwar da aka zaɓar masa bashi ya zaɓa ba so yake yi ya koyi rayuwar da ake cewa ba zai yi nadama akan ta ba so yake yi ya matse zuciyarsa ta koyi abin da ake so ta koya so yake yi a wannan ranar komai ya canza so yake yi zuciyarsa da koyi kaunar wacce ake so ya mikawa soyayayarsa ya sani SO ƘADDARAR ZUCIYA ne so ne kadai ke wahalar da ita ya sata cikin duk wani kunci da gangar jiki zai wahala shi ma.
Da wannan tunanin ya isa gaban sabuwar motarsa kirar Benz mai kalar baki sai faman daukar idanu take yi sai da ya kare mata kallo yau ne rana ta biyu da zai hau ta tun da yayo odarta haka kawai yaji yana bukatar ya fita da ita daga can nesa ya hango mai gadin sa hannu ya daga masa da gudu ya iso gareshi yana mai kwasar gaisuwa kafun ya mike ya nufi wajan Get ya hangame shi a daidai lokacin shi kuma Dr.Aqeel ya shige motar har yayi mata key ya doshi Get din a hankali har ya fice mai gadi nayi masa a dawo lafiya sannan ya mai da Get din ya rufe.
****
Gabanta ne ya yanke ya fadi sallamar da tayi ba ta karasa ta ba taja burki ta tsaya sai faman rarraba idanu take yi shi kuwa ya kafe ta da idanu kamar zai haɗiyeta hakan ya kara rikita mata lissafi ji tayi kamar ta juya ta falle da gudu amma jin muryar Hajiya ya sanyataa motsa kafafuwanta da
take jin su kamar za su zubda ita kasa a hankali ta shiga takawa tana karasa cikin falon ko ina na jikinta rawa kawai yake yi ga wani dokawa da gabanta ke yi musamman irin kallon da ta ga Tareeq na yi mata kau da kai tayi shiyasa sam bata son zuwa gidan nan ko don saboda shi ba ta son irin abin da yake yi mata.
“Ina yini Mami”.
Mariya ta fadi bayan ta isa gareta ta zauna.
“Lafiya lau Mariya ya gida ya su Umman taki da Abban naki?”.
Gyaɗa kai tayi kafun ta ansa da cewa.
“Lafiya lau duk suna gaishe ku”.
Daga nan bata sake tsinkawa ba sai Mami ce ta sake cewa.
“Shekaran jiya ai mun je kina Islamiyya ba mu tadda ki ba”.
Murmushi tayi gami da kokarin mikewa.
“Umma ta gaya min Mami Allah ya saka da alheri ya kara buɗe gami da rufin asiri…”.
“Mariya kar ki sake kin ji ko ai mun zama daya komai aka yi muku a gidan nan ai ba faduwa bane kun zama yan uwanmu mu ma haka duk an zama abu daya…mutuniyar taki tana ciki kisan dai san halinta kullum tana kunshe a daki kamar mai zaman takaba”.
Dariya ta sake yi sannan cikin hanzari ta nufi sama sashin Baseera zaune ta same ta hannunta rike da littafi da sauri ta karasa kusa da ita ta zauna sam hankalinta ba ya jikinta domin tunani take yi ba wai karatun littafin ba da sauri Mariya ta zungurar mata
kafaɗa a firgice ta dube ta ganin Mariya ya sanyata zaro idanu waje tana mai da numfashi ta shiga motsa laɓɓanta tana son yin magana amma ta kasa.
“Kin kyauta Baseera wato shi ne kika dauke mani kafa ko kirana ma da kike yi a wayar Umma kin daina sabida na yi miki laifi mai girma ko har da ya kai kiyi mani hukunci irin haka….Hmm Hakuri na zo na baki akan abin da nayi miki ba daidai…”.
Da sauri Baseera ta rufe mata baki wasu kwalla na taruwa a idanunta ta shiga girgiza kai .
“Ba haka bane wallahi ba na jindadi ne…”.
STORY CONTINUES BELOW
Turo kofar da akayi ne ya sanya Baseera saurin yin shiru tana goge fuskarta Mami ce ta shigo duban su tayi ganin yanayin da suke ciki batare da tace komai ba sosai suka gane kallon zargin wani abu take yi musu.
“Baseera kin yi bako”.
Abin da ta fadi kenan ta fice daga cikin dakin gaban Baseera ya buga gami da duban Mariya da ita ma idanuwanta suke kanta kallan kallo suke yi wa juna kafun Mariya tayi murmushi tana mai dafa kafaɗarta.
“Kin yi bako aka ce”.
Runtse idanu Baseera tayi tana jin yarda gabanta ke yankewa ya na faduwa.
“Ban san waye ba Mariya ba muyi da wani zai zo waje na…”.
Daga mata hannu tayi tare da mikewa tana kamo kafarta doguwar riga ce a jikinta don haka ta janyo mata gyalan rigar ta yafa mata fuskarta ba wata baci tayi ba don haka ta ja hannunta suka fice.
A harabar gidan suka hango mota girke da sauri suka dubi juna gaban Mariya ne ya fadi tana tunano inda ta san motar nan sosai ta ke ji a ranta ta taba ganinta amma ta rasa waye mai ita…
Bata gama tunanin tuno mai motar ba ta ga an buɗe kofar ana kokarin fitowa da sauri ta runtse idanu jin yarda kirjinta ya doka rikon da taji Baseera tayi mata ne jikinta na
karkarwa tana jin yarda take kokarin yi mata magana amma ta kasa hakan ya tabbatar mata da zarginta da sauri ta zare hannunta daga na Baseera tana kokarin juyawa ta koma ciki amma jin amon muryar sa ya sanyata tsayawa cak! tana mai da numfashi takun takalminsa da yake tunkaro su hakan ya kara rikita mata lissafi ta kara danke idanuwanta kamshin
turarensa take ji ya dokar mata hanci zuciyarta take ji tana matsewa da wani irin yanayi tana mikata wani mataki bata san ya za tayi ba bata san da wani idanu zata kalle shi ba sosai take jin rashin adalcin da tayi masa a ranta haka kawai take jin wata kunyarsa ta ratsa ta.
“Gani na zo domin yiwa so biyayya Mariya abin da kika bukata shi na zo yi domin tabbatar da abin da kike tsammanin ba haka bane”.
Wata irin bugawa taji zuciyarta tayi da sauri ta juyo gami da buɗe idanuwanta da suka kaɗa sosai ta dubi Baseera da tayi fakare da idanu tana dubansu daya bayan daya zuciyarta na bugawa da tashin hankali ashe da gaske Mariya take ashe abinda take faɗi mata zatayi ashe zata yi din da gaske.
girgiza kai ta shiga yi tana saka idanuwanta cikin na Mariya da ta gama shiga wani yanayi mai wuyar fassaruwa.
“Ban gane ba Mariya mai hakan ke nufi?”.
“Soyayyarta ta sadaukar gareki”.
Zare idanu Baseera fuskarta da wani irin yanayi mai girma a zuciyarta sosai take jin zuciyarta na matsewa da tashin hankali maganganun Dr.Aqeel take jin su wani iri a gareta sosai take jin suna hawa mata kai hannunta taji Mariya ta kama ta damke sosai da sauri ta dago ta dube ta idanuwanta ta gani cike da hawaye suna kokarim zuba.
“Kin yi mani alkawari in har ya amince ke ma zaki amince don Allah karki watsa min kasa a idanu Baseera ki dubi Dr.Aqeel a matsayin masoyi mai kaunarki tsakani da Allah kiyi mani wannan sadaukarwar don Allah ban taba neman alfarma gareki ba sai yau don Allah ki anshe ta”.
Fizge hannunta Baseera tayi tana mai da numfashi zuciyarta take ji tana bugawa da wani irin yanayi.
“A,a Mariya ba na tunanin hakan za ta faru karki takurawa zuciyoyin da ba sa kaunar junansu karki yi kokarin hada abin da kika san ba zai taba faruwa ba karki hada abin da kika san zuciyoyi ba za su samu farin ciki ba”.
Ta fadi muryarta na rawa wasu hawaye na zubo mata a hankali ta shiga ja da baya tana girgiza kai.
A daidai lokacin shi kuma Dr.Aqeel ya kara takowa kusa da su sosai zuciyarsa yake ji tana matsewa da kuna gami da radadi runtse idanu yayi kafun ya buɗe su akan Mariya wacce gabadaya ta gama shiga wani yanayi idanu suka hada tayi saurin dauke nata zuciyarta na harbawa da sauri-sauri.
“BASEERA!”.
muryar Dr.Aqeel ta doki kunnuwanta sautin na ansawa a kwanyar zuciyarta na buɗewa sosai tsayawa tayi cak! tana mai da numfashi kafun ta dube shi kallonta yake yi da wani irin yanayi wanda ba zata ce ga matsayin da zata ajje shi ba.
“Na anshi soyayarki in har zaki iya bani nima zan baki zuciyata gabadayanta”.
Ya fadi yana mai runtse idanuwansa zuciyarsa yake ji tana matsewa da wani irin yanayi mai kokarin haifar da bugun zuciyar sosai yake jin idanuwansa na zafi da raɗaɗi ko ina na jikinsa yake jin lokaci guda ya tsaya jinin jikinsa yake ji ya shiga gudu da sauri-sauri kwanyarsa yake ji tana hayaki kamar zata kama da wuta.
Mariya kuwa mutuwar tsaye tayi ba abin da take fadi sai ‘Innalillahi wa inna ilaihir raji’un’ wata katangar tashin hankali ne taji ta rikito mata hannayensa duk biyun ta saka ta dafe kirjinta da take jin yana barazanar tarwatsewa kanta taji ya shiga
dokawa kamar zai rabe biyu muryar Dr.Aqeel da taji yana furta kalaman so jin saukar su take kamar garwashi wuta runtse idanu tayi gami da kokarin saita kanta kafun ta taka kafafuwanta da take jin su kamar za su watsar da ita kasa hannayenta ta kamo ta sarke a cikin nata.
Idanuwansu suka sarke da juna murmushi Mariya tayi mai tafe da hawaye.
“Ki amince ke ma Baseera zuciyoyinku su kasance waje daya su rayu tare su zama abu daya har gaban abada”.
Girgiza kai Baseera ta shiga yi idanuwanta na kara ballewa da hawaye a hankali ta zare hannayenta gami da duban inda Dr.Aqeel yake wani kallo tayi masa kafun ta juya cikin hanzari tayi cikin gida.
Mai da numfashi Mariya tayi tare da duban Dr.Aqeel shima ita yake kallo kafun ya girgiza kai yana cizon laɓɓa wani murmushi yayi tare da juyawa ya nufi motarsa…
Kalas!!!
Ta faru ta kare
Meye na damuwa Mariya ke fa ce kika ce ayi haka sun yi miki biyayya na ga kuma kina sallallami
Dr.Aqeel kayi kokari fa in ni nr ba zan iya ba
Ko da yake naga Baseerar kamar bata yi amanna ba har yanzu
Irin wannan hadin haka Allah ya saukaka
Mu dai yan kallo ne muna gefe