UKU BALA’I CHAPTER 15 KARSHE

UKU BALA’I CHAPTER 15 KARSHE

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Zazzaɓi ne mai zafi rufe ta, bata tare da kowa ya sanin ba, sai karkarwa take yi numfashinta na kai wa da kamo wa, sautin haduwar hakoranta sai bada sauti yake yi gabadaya ta jigata, cikin wani irin yanayin tun a

daren jiya.+

sosai take jin jikinta ba dadi, sosai take jin kamar akwai abin da ke shirin faruwa da ita, motsin da taji na shigowa ne ya sanyata kara kankame jikinta, zama taji anyi kusa da ita gami da yaye bargon da ta lulluba dashi, kara runtse idanuwanta tayi.

“Mariya”.

Taji sautin muryar Umma ta sauka a saitin kunnuwanta, numfashi taja kafun ta buɗe idanuwan nata a hankali, ta sauke su a saitin Umma.

“Me ke damun ki haka Mariya, sosai naji zazzaɓi a jikinki, me yasa haka mai yasa kike son cutar da kan ki ne, bayan kuma kin san wannan abin ba abin cutar bane gareki, mu ma iyayenki mun sani ba za mu so abin da zai cutar dake a duniyar nan ba”.

Ta karashe cikin sanyin muryar tana riko kafadunta, ta tayar da ita zaune, tana dubanta.

“Ban son haka Mariya, ya kamata ki ajje komai na fargaba da ke a zuciyarki duk wani bahagon zance da zaki ji zuciyarki da kwanyarki na kawo miki ki ajje su gefe, shaiɗan ne kawai ke miki kuwwa yaka so ya bata miki lamarin ki na alheri, ki kokarta ki mike lokaci tafiya yake yi nan da wasu awanni MATAR WANI zaki zama, karkashin wani zaki koma komai naki zai koma garesa, rayuwar taki ma kacokan zata bar hannunmu, mu iyayenki zata koma karkashin sa.

kin ga kuwa bai kamata ki saka wa zuciyarki wata damuwa ba zama ne muke fatan har gaban abada ayi shi, zama ne mai daraja da martaba da kuma hanyar tsira gareki da mu kanmu iyayenki, Mariya ina horar dake ki rike darajarki da ta mijinki ki anshe shi a matsayin miji na tabbara Hisham ba zai taba cutar dake ba, duk da dai ansan DAN ADAM ajizi ne amma bana SHAKKA akan sa, ke ma na san ba za a taba samun matsala ta fannin ki ba”.

Hayaniyar da ta kaure ne a tsakar gidan ya sanya Umma saurin mikewa ta fice, yan biki ne suka cika tsakar gidan, ga wasu tika-tikan tukwane da aka daura an banka masu wuta ko wani bangare ka duba na cikin gidan, zaka gane eh biki ne na musamman za ayi sa na masu rangwamin rufin asiri.

Haka abubuwa su kai ta tafiya, har misalin sha biyu da rabi, da yake daurin auren karfe daya ne nan da nan maza masu zuwa daurin aure suka fara shiri, amarya kuwa na can kudundune acikin daki, gabanta sai dukan uku-uku yake yi.

Zaune take tana faman rarraba idanu tana duban jikinta yarda ya canza lokaci guda yayi haske gami da laushi, ga wani kamshi da yake ta fesowa daga jikin nata lokaci-lokaci  take dago hannayenta tana kallo zane suke da lafiyayyan lalle baki da ja hakan ya kara ƙawata hannun nata sosai da sosai…

Wayar Umma ce ta dau kara, da sauri ta dube gefenta in da take ajje, sunan da ta gani a jikin wayar ne ya tsinkar mata da gaba, runtse idanu tayi zuciyarta na mikata wani mataki mai girman gaske tana jin yarda zuciyarta ke kara buɗewa da wani al’amari mai girma a gareta, sosai take jin wani shauƙi da begen Dr.Karami na kara bula mata jikinta ta ko ina, burinta da fatan ta za su cika muraɗin zuciyarta yau zai kasance tabbatacce.

A hankali ta kai hannunta ta dauki wayar gami da kaiwa kunnanta bayan ta latsa madannin ansa kira.

Wani numfashi mai sauti ta ji ya ajje, kafun ya saki wani murmushi da taji shi har kunnuwanta runtse idanu tayi, tana buɗe su sosai.

“Me yasa haka Mariya. kin san dai a irin wadannan lokutan sosai nake bukatar ki kusa dani ko na ji muryarki, amma tun jiya nake kiran wayar nan kin ki dagawa kin san kuwa yarda nake ji a raina, kin san kuwa irin damuwar da na shiga jiya zuwa wannan lokaci, ji nake yi kamar bani ba, zuciyata nake ji kamar ba ta kirjina kwata-kwata…”.

STORY CONTINUES BELOW

  Da sauri ta zare wayar daga kunnuwanta tana duban fuskar wayar, don tabbatar da wanda take waya dashi. jin abin take yi kamar a mafarki, gani take yi kamar ba Dr.Karamin da ta sani ba, sautin kalaman take ji suna ansawa a cikin kunnuwanta da zuciyarta suna haifar mata da kasala.

“kice wani abu mana Mariya Please, kin ganni nan yanzu haka na kasa shiryawa saboda rashin jin ki ko barci banyi ba jiya, sosai nake ji a jikina kamar akwai abin dake faruwa dake”.

Numfashi ta ja lokacin da ta mai da wayar kunnuwanta, tana jin yarda yake furucin nasa mai kokarin rikita mata lissafi, muryar take ji kamar batasa ba, muryar take ji ta sauya mata…

“Please ki ce wani abu da zai karamin karfin guiwa mana, na kasa shiryawa, kin ga Dr.Aqeel har ya gama shiryawa tun dazu yake kirana a waya, suna hanya amma ni nakasa aikata komai Mariya sosai nake jin wani iri a jikina, sosai nake jin kamar akwai abin da zai faru…”

Runtse idanu tayi gabanta yayi wani irin dokawa, mikewa tayi kan kafafuwanta kafunta ja numfashi mai tsayi.

“Nima haka nake ji a jikina, ban san dalili ba”.

Ta fadi da wata irin murya mai taushi, wacce bata san tana da irinta ba.

“Yaa Rabbi!!”.

Ya furta da sauti, kafun ya saki muryarsa sosai.

“Dafatan dai ba wani abu bane yake damun ki ba, Mariya Please fada min abin da ke damun ki…ko da yake bari na zo yanzu kin ji…”.

  “A,a ba sai kazo ba, ba komai Allah..”.

Ina! tun kafin ta ida zancenta har ya kashe wayar, sosai taji jikinta yayi sanyi komawa tayi ta zauna ragwaf! tana mai da numfashi bata san abin da ke damunta ba, gabadaya take jin wani iri a jikinta, kamar bata da lafiya.

Sallamar da akayi ne ya katse mata hanzari, wasu mataye guda biyu suka shigo fuskarsu kunshe da murmushi suka isa gareta kallo daya tayi musu ta gane su waye, itama murmushin yaƙe tayi musu kafun ta hadiye abin da take ji ya tsaya mata a makoshi.

“Ya kamata ki tashi ki yi wanka fa, lokaci tafiya yake yi kin ga har su Baffa sun wuce wajan daurin auren”.

Wani irin bugu taji gabanta yayi runtse idanu tayi, kafun ta buɗe su a saitin su, tana duban su daya bayan daya, wannan rana sosai take jin ta tana haifar mata da wani yanayi a zuciyarta, da ma jiki baki daya. komai take jin yana sauya mata komai na duniyar take ji yana canzawa.

“Yaa Mariya..Yaa Mariya”.

Mu’azzam ne ya shigo da gudu har yana kokarin faduwa, Mariya ta kai hannu ta riko shi tana dubansa.

“Kizo wai inji…”.

Da sauri ta rufe masa baki, tana ajje numfashi. a zuciyarta ta shiga mamaki da tu’ajibi akan zuwan Dr.Karami, don ta tabbata shi ne ba wani ba. tana mamakin sa cikin yan kwanakinnan musamman irin kulawa da yake bata, numfashi ta ja kafun ta dubi su Asiya da suka zuba mata idanu, kau da kai tayi  yarda zata fita ne take tunani ta tabbata ba za a bar ta ba, amma zuciyarta sai tunzurata take yi akan ta fita taje domin kuwa ita akaran kanta tana son ganin sa.

Mikewa tayi ta ja hannu Mu’azzam sukayi tsakar gida, su dai su Asiya ba su ce mata komai ba, sai bin ta suke da kallo, ba su gano abin dake faruwa ba.

STORY CONTINUES BELOW

  A hankali suka karasa tsakiyar tsakar gidan hankalin yan biki duk yana wajan aikin da suke, kara sauko da gyalen jikinta tayi, ya rufe mata fuska sosai, sai da ta tabbatar ba Umma a wajan da sauri ta fada soro sannan suka tsaya ta dubi Mu’azzam.

“Dr.Karami ne?”.

Gyaɗa kai yayi. Batare da ta sake cewa dashi komai ba, suka nufi waje can ta hango shi jikin motarsa, jikinsa sanye da riga da wando kananu wani haske taga ya kara yi mata gami da kwarjini kau da kan ta tayi, zuciyarta na mikata matakin son Dr.karami da take jin yana kara narkar da zuciyarta.

Sam bai lura da su ba sai da ya dago kansa daga wayar da ake ta faman kiransa ya kasa dagawa, da sauri ya shiga takowa garesu ji yake yi kamar fizgarsa ake yi idanuwansa gabadaya suna kan Mariya ya kasa dauke su, har ya iso inda take tsaye bai sani ba numfashi ya ja lokacin da yaji wani kamshi mai ratsa zuciya na dukan hancin sa, idanu sosai ya zuba mata kafun ya shafi fuskarsa.

“Me ke faruwa ne?”.

“Ba komai”.

Ta bashi ansa a daidai lokacin wayarsa ta sake daukar burari da sauri suka dubeta su duka,  sunan kawunsa ya gani da sauri ya daga, ba tare da yace komai ba na yan sakanni ya numfasa.

“Ga ni nan zuwa Kawu, ina kan hanya yanzu haka kayi hakuri”.

Ya fadi yana sauke wayar, idanu ta kura masa kafun ta ce.

“Sai da nace karka zo, don Allah ka tafi na san suna can suna jiranka”.

Tana gama fadin haka ta juya cikin gida da sauri, tana jin yana kiranta amma ko ta kan sa ba ta bi ba, saboda yanayin da take jin dukan zuciyarta.

*****

Misalin karfe daya da mintina ashirin aka shaida  daurin auren DR.HISHAM MUKHTAR KARAMI da MARIYA BELLO GWADA sannan na DR.AQEEL MUNKA’IL da BASEERA HARUNA SA’AD daga karshe aka daura na HAFSAT DANLITI da HUZAIF ABDURRAZAQ.

MARIYA &DR.KARAMIN

2

BASEERA&DR.AQEEL

sosai babbar masallacin juma’an garin Gwada ya cika, sai kace ranar idi gabadaya ma garin in ka shiga zaka gane ana gagarumin biki, Angwaye biyu bakin su a buɗe cike da farin ciki da muraɗan jindadi, haka yan uwa da abokanan arzuki, sai dai Ango daya in ka kalle shi kamar bakin kumurci haka ya koma, domin ana gama daurin auren ya bar wajan zuciyarsa yake ji tana zafi da raɗaɗi bai so zuwa ba kawai don ba yarda ya iya ne huzaif wannan ranar ta

kasance masa ta bakin cikida takaici a filin duniyarsa, bai taba zaton abin zai tabbata ba sai yau, sosai yayi kudiri a zuciyarsa sai ya baiwa Hafsat mamaki sai ta gwammace zaman gidan yari da gidansa, sai ya gana mata azabar da sai tafi kaunar mutuwar da ita.

  Misalin karfe biyar na yamma aka shirya  hadaddiyar Dinner a Hdyro hotel dake cikin Birnin  Minna, sosai liyafan ta hadu waje ya cika makil amare da angwaye sun sha kyau na musamman kowa ka gani fuskarsa kunshe da farin ciki da jin dadi.

Misalin karfe tara aka tashi ko wacce amarya da ta wagarta suka nufi gidan su, zuwa lokacin Mariya ta gama sadakarwar komai ya tabbata, ta zama matar Dr.karami sosai take jin zuciyarta na buɗewa tana kara haifar mata da son sa, komai take ji nata na duniya ta mika masa.

  Lokaci lokaci take dauke hawayen da suke kwaranyo mata musamman in ta tuna rayuwarta a can baya, yarda ta kasance wai yau ita ce a wannan mataki ikon Allah kenan.

Ko da suka koma gida nasiha sosai akayi musu mai ratsa jiki da zuciyar duk wani wanda yake zaune a wajan, Mariya kuka take yi mara sauti tana jin yarda a yau za ta rabu da Ummanta, zata rabu da Abban ta da Mu’azzam din ta, lokaci guda ta tuna lokacin da Dr.Karami yake cewa da ita anya zata iya rabu da Mu’azzam yarda take nuna masa so da kulawa?.

  Tabbas yau ga ranar ta zo ranar da zata koma wani gida na daban, gidan da Umma tayi mata fatan zama na har abada.

  A banagaren Hafsat kuwa rigima ce ta kaure sosai domin suna zuwa gidan amarya suka tadda su Assama’u sun kasa sun tsare tun daga lokacin da Hafsat ta sako kafar cikin gidan bayan an gama artabu wajan daukota don sai da akayi dak’yar sannan aka aiko da mota daya abin  ya kara tayar mata da hankali ganin irin luntsuma luntsumar motocin da aka zo daukar Mariya da su sun yi jejir gwano a kofar gida hakan ya kara tabbatar mata da cewa Huzaif da gaske bai kaunarta.

  Numfashi ta ja wasu hawaye su zubo mata a kunci zuciyarta take ji tana sanar da ita irin kalubalan da zata fuskatan tun a yanzu a daren farkonta an fara yi mata rashin mutunci da wulakanta wanda suka kawo ta ina ga kuma an barta ita kadai ta san Huzaif da su Assama’u romanta ne kawai kila ba za su sha ba…BAYAN WANI LOKACI…

Sosai take kuka ta mike kan kafafuwanta gabadaya take jin jikinta wani iri, ga wani zafi da radadi dake jinsa a duk wata gaɓa ta jikinta nayi mata, bata taba zaton muguntar Huzaif ta kai haka ba, bata taba zaton rashin imanin nasa ya kai haka ba, ta yi zaton zaman na nasu zai sauya tayi zaton zasu fahimci juna, ashe ba haka bane duk inda take zaton Huzaif ya shalle tunaninta da nazarinta.

A hankali ta shiga dafa bango tana jan kafafuwanta har ta isa kofar toilet ta buɗe ta shiga, zuciyarta take ji tana kuna da suya ji take yi kamar zuciyar zata faso son sa na nan har yanzu ba abin da ya ragu, sai ma kara buɗewa da zuciyarta take yi da son sa.

Ruwa mai dumi ta cika kwarmin wanka da shi sannan ta shiga sosai zafin ke ratsata ta ko ina, sosai take jin zafin na kaiwa duk wani sashi da gurbi da take jin yana ansawa.

Runtse idanu tayi lokaci guda ta buɗe, sosai take jin rashin nadama akan son Huzaif alkawari tayi ko da yana yankar naman jikinta zata zauna dashi har karshen numfashinta, ta gwamma ce ta ji azabar gidan miji da dai ta koma waccan bakin gidan na Goggo Marka, ta koyi rayuwa tun daga irin cin zarafi da cin mutunci da gori da ta ake mata a wannan gidan ta tabbata in ba tayi wasa ba su

Assama’u so suke su fidda ita, amma zata jajirce zata nemi gafarar Allah ya yafe mata laifukanta ta sani abubuwan da ta aikata ne yake bibiyarta ba komai ba a duniyar rayuwarta.

Ta jima kafun ta tsane jikinta ta fito sam ba ta lura da mutum dake tsaye bakin kofa ba yana ta faman sakar mata wani irin kallo, sai da ta zauna bakin gadonta sannan ta lura dashi gabanta taji ya yanke ya fadi runtse idanu tayi tana tuna artabun da suka kwasa a jiya zuwa yau, goshin sa ta kalla kinkimeman bandeji ta gani

runtse idanu tayi tana tuna fadawa da Huzaif yayi jikin Mirrow ya fasa masa goshi, sosai ya yanke shi don jiya ta ga ta shin hankali bata taba zaton Huzaif zai rayuwa ba, musamman irin jinin da ta ga ya zubar da irin sambatun da yake yi.

A hankali ya shiga takowa ya iso gareta gefenta ya zauna fuskarta da wani irin yanayi mai cike da alamun nadama idanuwansa sun kada sunyi jajir gabanta ne ya yanke ya fadi sosai take kokwanto akan abin take hangowa cikin idanuwansa tausayi abin ya bata mamaki.

*****

Hajiya Layla ce ta dubi Khairiyya dake zaune ta zabga tagumi LAMARIN DUNIYA gabadaya ya kara hargitsa mata lissafi, komai na duniyar take jin sa wani iri babu dadi, duk da a yanzu bata da wata matsala a rayuwarta wacce zata addabeta amma in ta tuna wacece ita sai taji zuciyarta na kuna gami da suya, hawaye suka zirnano mata a hankali ta dauke su tana ajiyar zuciya.

“Khairiyya!”.

Hajiya Layla ta fadi da sauti a muryarta mai cike da rarrashi da karfafa mata gwiwa akan lamarin rayuwar da suke ciki a yanzu, kusa da ita ta karasa tana toshe bakinta jin tari na kokarin sarke ta, a hankali ta zauna tana mai yatsine fuska alamun akwai abin da ke damunta na rashin jindadi.

“Haba mana Khairiyya. bana so nake ganin ki cikin wannan yanayin gabadaya sai naji babu dadi, na rokeki ki mai da komai ba komai ba duba za kiyi da baya da irin rayuwar da mu kasance da kuma yanzu, ai abubuwa sun yi sauki kuma kisan ita rayuwa ba ko yaushe take zama daidai ba, kuma ba wani bawa a doron duniyar nan da zai ce miki ya dawwama a farinciki da kwanciyar hankali a rayuwa kowa da yarda Allah ya ke kunsa masa matsalarsa, sai dai ace ta wani bawan tafi ta wani”.

STORY CONTINUES BELOW

Ta karashe tarin na kara sarke ta, da sauri Khairiyya ta dube ta cikin yanayi na tausayawa.

“Maama kin sha maganinki kuwa?”.

Gyaɗa mata kai tayi gami da sakin murmushi kafun ta dafa kafaɗarta.

“Khairiyya Ina son mu sake zama na biyu dake, kuma ina so wannan zaman ya zama na karshe tsakanina dake, sannan ki sani ba zan tursasaki ba sannan ba zan yi miki dole b,a ni dai fata na kawai ki samu kwanciyar hankali ako ina kike shine BURINA sannan shi abin da na fi bukata a duniyar nan, Khairiyya so nake yi na zama sanadi na wanzuwar farin cikin ki har kashen numfashinmu a doron duniyar nan…”.

“Maamaa”.

Khairiyya ta fadi da alamun rigima a muryarta, kafun ta juyo sosai ta fuskance ta tana bayyana wani kunshin murmushi, wanda ta san zai kara kwantarwa Hajiya Layla da hankali.

“Ina jin ki faɗa mani menene zan anshe shi a duk yarda ya zo mani, zan yi AMANNA dashi BURINA a duniyar nan shine na faranta miki, kullum na ganki cikin farin ciki Maama kece farincikina kece komai a rayuwata kece kika zama tsanin ganin rayuwata ta gyaru…”.

Hawaye ne suka kwanranyo mata da sauri ta kau da kanta, tana jin yarda zuciyarta ke kara buɗewa farinciki na kara samun gurbi a cikinta.

“Maganar Alhaji Abdulwahaab Khairiyya ina muka kwana?”.

Ta fadi tana saka idanuwanta cikin na Khairiyya, so take yi ta hango gaskiya, so take yi ta gano in da Khairiyyar ta dosa da batun, so take yi ta ga yanayin ta ko na sauyi a yarda ta dauki maganar a yanzu.

Numfashi taja gami da fesarwa kafun ta mike kan kafafuwanta, zuciyarta take ji tana kara buɗewa kaunar da Hajiya Layla take nuna mata bata san da mai zata saka mata ba, ta nuna mata so ta nuna mata kauna tayi tattalinta ta bata duk wani lokacinta, sannan ta bata farincikin daidai iyawarta ya kamata ita ma ta nuna mata godiyarta sannan ta anshi duk wani abu da ta zo dashi, hakan zai kara tabbatar wa Hajiya Layla da cewa sun zama UWA DA ‘YA.

“Maama na lura dai so kike yi ki samu suruki”.

Ta fadi fuskarta da murmushi ita ma Hajiya Layla murmushi take yi kafun ta mike tana faɗar.

“Ba suruki kadai ba har da jikokina nake so na gani, kafun lokacina yayi so nake yi ni dake ki saman mana DANGI da zuri’a, zan yi alfahari da hakan sannan ko na mutu zan san nima ina da dangi”.

Ta karashe da kwalla a idanuwanta.

“ki anshe shi a matsayin miji na san Alhaji Abdulwahaab zai rike ki a yarda kike zai kula min dake, zai tattale ki zai zama MIJIN MARAINIYA a gareki, na san ba zaki taba kokawa ba duk da dai an san DAN ADAM ajizi ne, amma a zuciyata fata nake ke da Alhaji Abdulwahaab ku zamo abu daya har a gidan aljanna”.

“Shikenan Maama nifa wannan kukan naki ne bana so, Allah ki dai batun Alhaji Abdulwahaab kuma ai tuni labari ya sauya kawai fadi miki ne ban yi ba”.

Zaro idanu Hajiya Layla tayi cikin alamun mamaki, kafun ta kai wa Khairiyya dukan wasa ta goce.

“Ja’ira dama kallona kawai kike yi, ina kidina ina rawa ta ko? Allah ya shirya min ke ni nan na saki baki ina cewa sai na hada miki da tsayuwar dare ayi auren nan, ashe tuni kin mai dani wata kakarki to ai shikenan Allah yasa hakan shine yafi zama alheri a garemu ga baki daya, Allah yasa fatan da muke ya tabbata Allah ya kau da duk wata fitina da abin ki Allah ya kare miki rayuwa ‘yata Allah ya kawo zuri’a tagari kiyi ta haifar mani tagwaye”.

STORY CONTINUES BELOW

Ta karashe tana goge hawayen da suke zubo mata ta jawo Khairiyya jikinta ta rungumeta sosai suke jin wata natsuwa da kwanciyar hankali na wanzuwa garesu.

“Ameen Yaa Rabbi Maama na”.

Khairiyya ta ansa muryarta na rawa.

******

Da Sallama ya shigo cikin gidan, yana bin duk wata kusurwa da kallo yarda gidan ya dawo tsaf! komai ya zama sabo zuciyarsa yake ji tana kara buɗewa da farinciki gami da kwanciyar hankali, ba abin da zai ce sai godiya ga Allah da kuma

Dr.Karami da ya zama sanadin samun waraka a rayuwarsu duban jikinsa yayi kafun ya sake duban gidan kwalla suka tarun masa kafun ya dauke su, a hankali ya shiga takawa yana isa dakin Umma, daga labulan yayi bakin sa da Sallama.

Zaune take gabanta da katuwar roba mai cike da CAKE tana lissafawa jin sallamar maigidan ne ya sanyata tsagaitawa, ta ansa sallama tana kokarin mikewa ta anso kayan hannunsa ya iso da sauri yana fadin.

“Matar nan kin zama Hajiya fa Kasuwancin nan ya anshe ki sosai kin yiwa ‘yata wayo ita da koya ke da karbe sana’ar”.

Murmushi tayi kafun tace.

“Yo da zaman banza ai gwanda aiki kishiya kuma ai bani nace ta bar mani ba kuma ko ma kace na anshe mata ai ba gida daya muke ba ita za ta iyayin nata a gidan auren ta kowa ya ci da rabon sa”.

Zama yayi yana mai fadin.

“To Allah ya dafa mana kin ga na shagon ma da kika kai shekaran jiya kusan karewa na lura Cake din nan yana karbuwa sosai wajan jama’a da mutum yaji cikin sa yana masa yaƙi sai ya zo ya hada da lemo sai ki ga ya dawo hayyacinsa”.

Murmushi tayi batare da ta kara cewa komai ba, amma zuciyarta tana goɗewa Allah tana shiwa Dr.Karami Albarka yarda ya fiddo dasu daga cikin kangin rayuwa ya baiwa mijinta jali ya buɗe shagon kayan bukata na rayuwa gashi ita ma sanadin karatun ‘yarta ta samu sana’ar yi ba abin da zata cewa Allah sai godiya da fatan karin kwanciyar hankali daga gareshi.

“Wai ina karya jali yake ne?”.

Ya tambaya yana murmushi, dubansa tayi.

“Au kai ma Mariya ta bar maka sara ko ɗan nawa ne karya jali ai yanzu na uwarsa ne ko ya karya ba damuwa wata rana shi zai daura…yana can ya tafi Islamiyya”.

Dakin ne ya dau shiru na dan lokaci, kafun Bello ya ja dogon numfashi ya dubi Umma.

“kisan mi ina labarin yan matan nan da nace miki mun hadu da su wajan mutanan nan da suke garkuwa da mutane?”.

Umma ta gyaɗa kai tana gyara zamanta ya cigaba da fadin.

“Yanzu a shagon Alhaji Adamu mai bulawus na gan su an nuna a talabjin ashe lokacin da na bar su tana da juna biyu shugaban tawagar na su shi yayi mata a cikin sauran yan matan ma akwai masu juna biyu duk sun haihuwa yau na ga shari’ar da aka yi musu yau aka yanke musu zaman gidan kaso na rai da rai duk kan su su kuma yan matan gwamnati ta dauki nauyin rayuwarsu saboda kin san garin na su an kone duka sannan duk an kashe iyayen su ba su da kowa ba su da komai yanzu naji tausayin su sosai”.

Umma ta dauke hawayen da suka zubo mata domin ta jima tana tuna wannan labarin na mutanan da suka kama mata miji sannan da yan matan da ya bata labari akan su.

“Allah ya sa iyakar wahalar rayuwarsu kenan Allah ya jibanci lamarin su su kuma wadannan mutane Allah yayi mana tsari da irin su ya kare mana rayuwa da ta yan uwanmu daga fadawa hannun su”.

“Ameen Ya Rabbi”.

Ya ansa jiki a sanyaye yana mikewa.

“Ka duba Jin Goggo fa don Allah Malam bai kamata ace kana mata haka ba, ita ma uwa ce a gareka duk wani abu da tayi maka na cutarwa ina rokon Alfarma ka yafe mata, rayuwar duniyar nan ba komai bane…”.

“Naji kuma ai ni tuni na yafe mata, kowa dai yayi na gari dan kan sa”.

“Malam don Allah ka manta komai a rayuwarka da tayi maka, ita ma ai tayi nadama ko halin da take a ciki yanzu yaci ace ka tausaya mata”.

Bai sake fadin komai ba ya fice daga cikin dakin, tsayawa yayi yana kallon dakin Goggo Marka kamar ba zai je ba, sai kuma ya taka a hankali ya isa kofar dakin daga labule yayi can karshen gado ya hangota gabadaya ta gama yankwanewa idanuwanta a buɗe tarwai sai dai ba su da amfanin komai kusan watanni hudu kenan cutar MAKANTA ta lokaci guda ta kama ta tun da akayi wata iska kura ta shigar mata idanu shikenan ta makance kuma dama gashi tana faman da cutar hawan jini da tayi mata mugun kamu har ta kashe mata ɓarin jiki tashima bata iyayi daga kwanciya sai kwanciya…TAUFEEQ AQEEL MUNKA’IL.+

*****

“Mai Ciki”.

Kamar daga sama taji sautin muryar Bassera na fadin haka, cikin dariya a hankali ta mike tana gyara doguwar rigar dake jikinta, ta taka hankali ta nufi kofar fuskar da murmushi, Handle din ta rike gami da buɗewa.

Baseera ce tsaye, hannunta sarke da na Dr.Aqeel hankalinsa gabadaya na wajan wayar da yake yi sai ɗan ta TAUFEEQ dake sagale a kafaɗar Dr.Aqeel din.

Numfashi Mariya ta ja kafun ta zaro idanu waje, da sauri ta koma ciki tana mai kwalawa Dr.karami kira, da yake kicin. Wai yana yi mata wainar

fulawa tunda ta tashi take kwadayinta shi kuwa ya zage sai yayi bayan kuma tace zata aikawa Umma tayi mata, yace bai amince ba shi ma ya iya.

Da sauri ya fito idanuwansa sun yi jajir, hannunsa rike da cokali fuskar gefe guda duk Manja, bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba ta shiga nuna masa kofar shigowa falon tana yi masa alama da baki amma ya kasa gane wa, sai ma harara da wurga mata yana fadin.

“Ni ko ai ko ba za ki ci wainar nan ba tun da abin ya zama haka…”.

Bai karasa ba Baseera ta bayyana cikin falon, duban su tayi kafun ta sauke idanuwanta a saitin Dr.Ƙarami da yayi wiki-wiki dashi.

“Iyee ba shakka, likita kai ne haka”.

Ta fadi tana kwashewa da dariya, a sa’ilin da Dr.Aqeel ya sanyo kai shima yana kokarin sauke TAUFEEQ a kafaɗarsa, ganin abin da ke faruwa ya sanya shi isa cikin falon da sauri ya kwantar da Taufeeq da ya yi barci ya zauna gami da zabga tagumi yana kallon Dr.Karami, kafun lokaci guda ya kwashe da dariya.

STORY CONTINUES BELOW

“Aboki ashe kai ma kuku ka zama tabbas arzuki yaci uban na da, an sai da gida an sai yashi”.

Gabadayan su suka kwashe da dariya, kafun Dr.Karami ya juya da sauri ya fada kicin, yana tuntsirar dariya shima.

“Billahillazi baki da M matar nan yanzu Doctor guda ya zama kukun ki”.

Baseera ta fadi tana duban Mariya, taɓe baki tayi tana mai cewa.

“Dadin abin ai ba ni kadai ake yi wa wannan gatan ba na ga wata mike kafa take yi ta tura mijin nata kicin ya yi ta fama da cokali a hannunsa”.

“Rabu da ita Maman Jawwad yanzu haka kafun mu fito, nifa nayi girkin wai bata da lafiya ba yarda na iya haka na shiga na zabga girkin kuma saboda rashin tsoron Allah ta miki kafa ta buɗe ciki ta ci”.

Dr.Aqeel ya fadi yana marere cewa alamun ya ji jiki wani kallo Baseera tayi masa kafun ta ce dashi.

“Au haka ma zaka ce? to shi kenan tun da kace haka da ga yau raba girki za mu din ga yi da kai, kowa ya din ga yin kwana bibbiyu”.

Zaro idanu yayi gami da daura hannu aka, kamar wanda ya ga wani mugun abu ya shiga marmaɗi da idanu kamar wanda yayi wa sarki karya.

Baki Mariya ta saki ganin yarda yayi a daidai lokacin shi kuma Dr.Karami ya fito, hannunsa dauke da faranti shake da wainar fulawa taji manja ya iso gaban Mariya ya kalle ta sama da kasa kamshin wainar ta doki hancinta lokaci guda taji miyau dinta  ya tsinke, da sauri ta kai hannu zata dauka ya kau ce yana yi mata gwalo gaban Dr.Aqeel ya isa ya zauna ya dube shi.

“Wannan aikin maza, ne don haka  zo mu ci a tsakaninmu, in sun yi zuciya suyi na su mugani”.

Ya fadi yana daukar waina daya ya kai bakin sa kafun ya mike ya nufi firji ya buɗe ya dauko musu gorar ruwa da ta lemo masu rangwamin sanyi.

Baseera baki ta saki kafun ta dubi Mariya dake tsaye tana ta faman hadiye yawu, fuskarta duk tayi wani iri kamar zata fashe da kuka a hankali Baseera ta mike ta dube su.

“Dadin abin mu ba kutare bane, sannan kuma muna da hannun da za muyi bari ma ku gani”.

Tana fadin haka ta mike ta nufi in da Mariya take sai faman hadiyar yawu take ta rike hannunta suka nufi Kicin.

Da gudu Dr.Karami ya mike hannunsa da waina daya gaban su ya sha ya riko hannun Mariya gami da bude mata baki, ya tura mata wainar aiko kamar jira take ta shiga taunawa har tana kokarin kwarewa.

Baya Baseera tayi tana kallon ikon Allah kafun ta juya ta dubi nata Mijin da ya dauke kai yana ta faman kai loma bakinsa.

“IKON ALLAH”

Abin da ta fadi kenan tana rike haɓa.

*****

Karar faduwar abu ne ya sanyata fitowa daga kicin cikin sauri, sai faman jan kafa take yi da turtsetsen cikin ta tana cizon laɓɓanta daidai benen da zai kai ta sashinta kafarta ta turguɗe ta yo baya runtse idanu tayi don ta sadakar taje kasa har ta hango irin zabar da wahalar da zata sha jinta tayi jikin mutumin da bata taba zato ba, wani numfashi ta ajje a

daidai lokacin da ya riko mata kugunta ya haɗe da jikinta sosai kamshin turaren sa Dark-wood wanda ya rigaya ya zama jikinsa ya daki hancinta hakan ya kara sanyata lafewa a jikinsa.

STORY CONTINUES BELOW

Sun dau lokaci a haka kafun ya ja numfashi bayan ya gama shinshinar kamshin da ke fita daga cikin sumar kanta da ta sha gyara ta tufketa da rumbos.

“Kashe ni zaki yi ko Preety?”.

Ya fadi yana mai dago haɓarta da hannu daya, idanuwanta a runtse suke har zuwa wannan lokacin taki buɗe su ita kadai ta san yanayin da take ciki a wannan mataki, zuciyarta take ji tana mikata wata duniya ta daban mai cike da farin ciki na tsanani kaunar da take ji zuciyarta na kara narkewa ta mijin nata abin alfaharinta.

Iska ya shiga hura mata a idanu ta shiga motsa manyan kwayan idanuwanta ba tare da ta buɗe ba, wani murmushi na kara bayyana a saman ƙyankyawar fuskarta wacce tayi fayau ba digon ko tabo a jikinta laɓɓanta masu taushi da kalar ja sai faman motsa su take yi a hankali ta shiga buɗe idanuwanta daya bayan daya ta sauke su a saitin fuskarsa.

“Jawwad!”.

Ta fadi da wani irin sauti a muryarta kafun ta shiga kokarin mikewa daga lallausar jikin nasa da bata gajiya da kwanciya a kanshi kirjinsa da ya zame mata abin kwanciya a kullum in ba a nan ta kwanta ba ta taba jin dadi sannan ba ta iya barci.

“Me ya yi kuma?”.

Ba tace komai ba ta mike daga jikin nasa gabadaya ta kwace kanta daga rikon da yayi wa kugunta a hankali ta shiga takawa tana kokarin hawa sama amma jin yarda kugunta ya ansa ya sanyata tsayawa cak! tana mai cizon laɓɓanta.

“wash!!!”.

Da hanzari ya riko ta, yana mai duban inda ta rike.

“Ya dai me ke damun ki haka?”.

Turo bakin tayi gaba gami da taba kugun nata da take jin sa kamar zai karye.

“Shiyasa nace maki ki dawo dakin kasa da zama amma kin ki wannan benen so yake yi ya karya min bayan mata wallahi”.

Kafin ta ce wani abu caraf! ya sungume ta kamar wata Baby ya hadata da jikinsa sosai ita kuwa ta shiga kiciniyar kwace kanta amma ina rikon da yayi mata ba na wasa bane hakan yasanyata yin lamo a bayansa tana cizan masa kunne har suka isa dakinta da sauri tace dashi.

“Don Allah sauke ni Jawwad yana ciki fa!”.

“Ai baki isa ba wallahi sai na kai ki har ciki sannan na rama cizo na da kikayi mani”.

Jin abin ya yace ya sanyata marere cewa tana shagwaɓe baki alamun son yi kuka hakan da yaji da sauri ya sauke ta yana riko hannunta.

“Ai wallahi sai na rama haka kawai so kike yi ki rage mani farashi budurwa tace bata so na ko”.

Zaro idanu tayi waje tana dubansa gabanta taji ya yanke ya fadi kafun ta tako kusa dashi tana zira idanuwanta cikin nasa.

“Me kake cewa wacece gangancin da neman ciwon zuciya  take so ta zama MATAR MIJINA a garin nan?”.

Yanayin da ta nuna yayi matukar bashi mamaki bai hango wani razana ko tsoro a idanuwanta ba amma ya hango tsantsar so da kuma kishi na asali a cikin idanuwan nata.

“Abin da kika ji shi na fadi”.

Ya karashe yana rike Handle din kofar ya tura yana kokarin shiga ciki da sauri ta sha gabansa tana sake saka idanuwanta cikin nasa.

STORY CONTINUES BELOW

“Ban hango akasin gaskiya a idanuwanka ba bai kamata kake barin harshen ka na kokarin fadin abin da ba daidai ba”.

“Injiwa ya fada miki ba gaskiya nake fadi ba ai kina sauke mani TAGWAYE na zan dakaro miki sabuwar amarya fil a leda”.

Zaro idanu tayi kafun ta mai da kallonta zuwa cikinta ta shiga shafawa.

“Tagwaye fa kace ni gaskiya a,a cikina guda daya ne kacal zan haifa ba wani tagwaye”.

“Au! Wasa kika dauka to ai shikenan Allah ya kamu lokacin zaki ce na fada miki”.

Ya karashe da dariya sosai a fuskarsa ya fada cikin dakin, sake da baki ya barta tana bin sa da kallo, sannan ta bin cikin nata da yayi katoto ba

kamar cikin Jawwad ba gyaɗa kai ta shiga yi, a zuciyarta tana jin kamar maganar Dr.Karami gaskiya gabanta taji ya yanke ya fadi ba abin da ta tuna sai lokacin haihuwar Jawwad yarda aka sha artabu.

Wata dariya ce ta zo mata lokaci guda ta saketa  da gudu ta fada cikin dakin duban Dr.Karami tayi da ya baje a gadonta can gefe kuma Jawwad ne da kwalbar Humra din ta da ya tarwatsa ta da sauri ta isa gareshi yana ganinta ya mike yana shirin gudu ta riko shi sannan ta dubi Humra din da ta

kwarare a tsakar dakin sannan ta dubi Dr.Karami kara ta saki a razane ya tashi yana dubanta wani kallo ta watsa masa kafun ta turo baki gaba tana nuna masa Humra din ta dariya yayi kafun ya dubi Jawwad da yayi tsuru-tsuru.

“Ni fa ba ruwana ke da ɗanki ne jiya nan yayi mani barna zan dake shi kika hanani don haka sai ke kiji in dadi”.

Jin abin da yace yana kunshewa dariya hakan ya sanyata duban Jawwad ta talla ke masa keya ta shiga dire-dire da kafafu tana shagwaɓe fuska alamun son yin kuka.

Da sauri ya taso ya iso gareta ya kamota ya hadata da jikinsa sosai ya sanya bakinsa saitin kunnanta yana yi mata raɗa fizge kanta tayi ta tureshi bai ankara ba yaji ya faɗa kan gadon bin shi tayi tana kokarin turmushe shi yayi sauri matsawa gabadaya ta fada kan gadon binta yayi ya danne yana mai yi mata cakulkuli dariya ta shiga yi sai da yayi mata lilis da jiki sannan ya daga ta idanuwanta a rufe sai mai da numfashi take yi kiss ya manna mata a kumatu kafun ya riko

hannunta ya shiga kallonta zuciyarsa na kara buɗewa sosai a son ta GURBIN SO da ya bata a duk wani fanni na zuciyarsa yake ji yana kara buɗewa da kaunarta kaunar da har abada ba ya tunanin zai iya yiwa wata ƴa mace a filin duniyar nan.

“INA KAUNAR KI”.

Ya furta da wata irin murya da ta galabaitar da zuciyar Mariya a lokaci guda ji take yi zuciyarta na mikata wani waje na musamman mai tatttare da so da kauna zalla ta Dr Karamin ta sosai take jin zuciyar na kara buɗewa da kaunarsa sosai take jin duk bugun numfashinta na kara haifar da sabuwar kaunarsa a zuciyarta.

“INA KAUNAR KA”.

Ita ma ta fadi da wata murya da ta daki kunnuwansa runtse idanu yayi yana jin yarda bugun zuciyarsa ke karuwa saitinta yaje ya kwanta yana jawota cikinta sosai ya matse ta har sai da ta saki ƴar kara ta buɗe idanuwanta.

“Dady kai ko”.

Kamar daga sama suka jiyo muryar Jawwad na fadin haka da sauri suka dube shi don sun manta ma dashi a wajan gwalo Dr.karami yayi masa kafun ya mika masa hannu alamun ya taho da sauri yaje maimakon yaje wajan sa sai ya nufi wajan Mariya da sauri yana faɗawa jikinta.

Dukkansu ya hada ya matse a jikinsa yana furtawa Mariya kalamai zafafa da suka kara tabbatar mata da Dr.karami na tane ita kadai har gaban abada.

Karshe!!!

Alhamdulillah ala kulli halin!

Astgarufullah wa atubu ilai!

Yau Allah ya bani ikon sauke littafin nan nawa mai taken Uku Bala’i ina rokon Allah ya yafe mani kurakuran da nayi aciki ladan kuma Allah ya bamu mu duka da makaranta wannan labarin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *