UMM ADIYYAH CHAPTER 16 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
dole ya tsaya ta koma baya, sannan suka cigaba da tafiya. Yana kallonta ta madubin baya, ta rufe fuska sai KunKuni take yi. Tun jiya da aka kai ta gidansa, yake cikin fargaba, bai zaci ma za ta kwana ba tare da ta gudu ba. Wannan ya sa koda ya yanke shawarar zuwa yiwa su Mama sallama, ya ji Www.bankinhausanovels.com.ng hankalinsa zai fi kwanciya, idan ya wuce da ita, domin bai yarda da ita ba, ya san Za ta iya aikata koma meye. Tare suka jera da su Maryam a hanyarsu ta Gomben. Kansa ya daure gaba daya.
Ta dagula masa rayuwa, shi yanzu ba wanda ya fi ji irin Fatima, duk abin nan da ake ciki ta yi haKuri ba ta ce komai ba, sai yadda ya ce, haka take binsa, amma ga wannan ‘yar kucilar, sai wahala take ba shi.
Tunda suka dauki hanya, ba su tsaya ko ina ba, sai da suka isa Bauchi. Ya biya ta
(Bauchi Club), ya saya masu nama da ruwa da su Juice. Jin da ta yi anyi Parking ne, ya Sa ta san tsayawa suka yi. Amma taurin kai ya sa ta Ki dagowa ta dubi ma inda suke. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tana ji lokacin da aka kawo masa order din da ya bayar, amma ta Ki motsawa. Har sunanta ya kira akan ta tashi ta karbi nama ta ci, ta Ki kula shi. Haka ya rabu da ita, ya ajiye Kunshin naman. Gabaki daya Kamshi ya cikata a bayan motar, sai hadiye
yawu take yi cikinta na kiran ciroma. Bai sake waiwayarta ba, har suka isa Kofar Gombe. Ta ga dai da gaske wucewa za su yi.
ZAMU TASHI
“Na dauka za mu yi sallah a gidan Adda Zubaida.” Ta fada. KaiKaito da idanunsa ya yi, ya kalleta ta cikin madubi, tana zaune tana murza idanu. Kau da kansa ya yi ya Ki kulata. “Yaya Zaid da kai na ke magana fa, ko sallar ma ka daina yi ne?”
Ashe kin iya magana? Ai ban ji ki ba ne. Sannan ban ga daman tsayawa ba.” Ba kyau dai wasa da sallah, a’ha.” Ta fada cikin kada harshe. Bai kula ta ba, ya
Kara taka totir din motar. Lokacin da mutane suka tsaya yin sallar, ke ki na ina?” Keyarsa take harara yanzu kuma. Hade da kau da kai, ta kalli windo ta cika tim saura ta fashe. “Yaushe ka tsaya?” Bai kula ta ba, saboda dazu da suka isa Jos, tayi barci, ya yi ta kiran sunanta, ganin ta Ki kula shi, ya san da gangan take yi, don bata barci mai nauyi. Don haka ya bude mata Kofar mota ya yi sallarsa, ya dawo sukaci-gaba da tafiya a tunaninsa, tana fashin sallar
ne. Har suka shiga Gombe ba ta sake masa magana ba, haka shi ma. Ga yunwa ta sa cikinta sai Kugi yake yi, ba daman ta ci namansa. Gabanta ne ya fadi da ta gansu a Kofar gidan Baffa Abdu, shi kenan yanzu kam
duniya ta san ta zama matar Zaid. A dole ta KaKalo murmushi ta maKala a fuskarta. Ai tun daga Kofar gida ‘yan tarba suka tare su.”Maraba da baKin birni.” Anty ce ta fada tana daga Kofar kicin, wanda yake tsakar gidan. Umm Adiyya tuni ta shiga zazzare idanu tana kallon Kasa. A hankali ta dago idanu ta yi mata murmushin dole. “Sannunku da hanya, yanzu ko Ummu A. Take cewa za ta kiraku a waya ta ji shirun ya yi yawa. Ba ku iso da wuri ba.”Zaid ya cire hular kansa ya ce, “Da yake ba mu taso da wuri ba, kuma mun yi ta tsaye-tsaye a hanya.” “Mu Karasa ciki, su Maryam ma ba su shigo ba ko?” Antin ta tambaya.
Suna bayanmu daf, kenan, na zaci za mu samesu a nan ma, don mun yi ratse ratse.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Umm Adiyya ba shiri ta ji an cafketa cikin murna. Fadeela ce. Juyawa ta yi tana mata dariya “Burinki ki Karasa ni ko?” Yaya hanya Anty Ummu?” Ta fada tana ‘yar dariya. Fadeela ma Kanwar Zaid ce da
take aji uku na sakandire, tun safe suke tsimayin zuwan Yayan nasu da amaryarsa. Zaid na kallonsu ya ce, “Ke meye haka kuma? Sai kin kai min Twinkle dina Kasa kike so, ko meye?” Umm Adiyya kam ware idanu ta yi tana kallon wani sabon salo, wai kaza ta ji shiKar dare. Wai ita ce Twinkle dinsa? Kai Yaya Zaid kam diramarsa sai shi, munafuncinsa kuma ya kai Kololuwa. Bayan sun gaisa da su Ummu A. Da Anty ne a falo sauran ‘yan-uwanta suka yi ta yanyameta daya bayan daya, ana masu murnar aurensu. Tana farin-cikin ganin yan-uwanta, amma baKin-cikin Zaid ya dusashe komai. Bari na shiga mu gaisa da su Mama na yi sallah.” Tuni ya miKe, saboda jin kirar sallar la’asar da ya ji ana yi. Daidai shigowar su Maryam kenan, ya sa suka daina kallon-kallo, ya yi wucewarsa masallaci.
***********
Mike Kafafunsa ya yi a kan gadon Maman, ya jinginu da allon gado, yana Kare mata kallo daga inda take zaune a gaban kujerar dakin. Kallonta dai na kullum ne a Kunshe a fuskarta. “Ummu, zuba maku abincin mana kafin ya yi sanyi.” Mama ce ta fiddata daga saKe-saKen hanyoyin da za ta iya shaKe Zaid a wannan lokacin ko zai daina mata wannan kallon da yake yi. Tana matuKar jin yunwa, don har wani luuu! Haka kanta ke yi, amma ba ta son cin abincin a gaban sa. Ga Mama ta yi masu hidima kuloli kala-kala a
jere dakin nata, ga wasu kwanuka
masu kyau a shaKare da soyayyun kaji, wasu an masu hadin miyar yaji, wasu kuma haka nan, banda farfesun kayan ciki, ga su salak-salak nan, kai ka ce fati za a yi. Duk don Zaid dinta da amaryarsa.
Ba abin Umm Adiyya ta musa ba, ba yadda ta iya, haka ta miKe. Sai dai tashinta tsaye ke da wuya, wani jiri ne ya kwasheta a nan wurin ta zube
Kasa, da sauri Zaid ya miKe, amma kan ya isa inda take, ta facmdi. Salati Mama ta sa, Lafiya dai? Daman ba ta jin dadi ne hala?” Hannu ya sa ya dagata zuwa kan gado, yana taba fuskarta ko za ta farka, amma ina, da sauri ya juya zai dauki ruwa, ya samu Mama na riKe da kofin ruwan a hannuta, karba ya yi ba tare da ya amsa mata tambayarta ba. “Adiyya!” Ya fadi sunanta Kasa-Kasa hade da shafe fusarta da ruwa. A hankali ta motsa. Sai da ta dauki minti biyu tana kallon duru-duru. Sannan ta ga fuskarsa tangaran! A saman kanta, da sauri ta zabura za ta zauna, ya yi saurin riKeta, ya maidata jikin filo. Ki yi a hankali, kin ga bari na hada maki Tea ki sha, kin ji?” Yana tantaman rashin lafiya ke damunta, sai dai baya raba daya biyu, abin nata har da yunwa, don yau kaf bata sa komai a cikinta ba, sannan bayan kawota da aka yi jiya, bai yi tsammanin taci abinci ba. Mama ce ta fita daga dakin, domin Www.bankinhausanovels.com.ng debo ruwan zafi. Me ki ke tunani ne za ki zauna da yunwa? Kin ga abinda ki ka jawo ai.” Ina ruwanka da yunwata? Ai ba ka Ki na zarce ba, ka ji dadi, tunda burinka kenan.” Wani kallo ya sakar mata, sai da ta ji kamar Kugin cikinta ya Karu don tsoro. Muryar
Mama ce ta sa ya fasa matse bakin rashin kunyar.
MiKewa ya yi ya karbi tray din da ta shigo da shi. Da kansa ya hada gudun kar su Mama su zargi cewa abin nasu ba dadi Ita kam Umm Adiyya kunya da munduKu duk sun bi sun cikata, sai riKeta yake yi yana ba ta Tea a baki, a gaban Maman. Kamar ta naushe shi take ji, tana sane yasan da su biyu ne, ba za ta yarda ya ma zo kusa da ita ba, shi ya sa yake zaKewa
gaban Mama. “Malam da yunwa ka bar matar taka ne? Ta tambayi Zaid kamar yadda take kiransa
kasancewar mai sunan Babanta ne. “Yaushe aka taba yin haka, ku kun saba niKar hanya ba tsayawa, ka dauko yarinya, ai sai ka bi ka nema mata abinci, ba ku yi ta dinke titi ba, ciki babu komai. Ba ta abincin ta ci sosai ko Karfin jikinta zai dawo.”
“Mama kin san yanayin cin abincin nasu ai, sai a tsaKuri kadan, ba za a tsaya a Koshi da kyau ba, su nan gaye.” Shigowar Anty, domin duba Umm Adiyya ne tace, “Eh, idan ta zage ciki ta yi ta duri a gabanka kuma ka ce ta faye ci ba. Kar ka yarda ka matsawa ‘yata dama. Fita ka bamu wuri, mu kula da ita da kyau. Ka ji sharri, zai ce wai ta tsaKuri kadan. Na
sanka Zaid da shegen baKin hali, yanzu haka ba ka saya mata abincin bane. Ga ka da uzzurawa mutane, idan za ayi tafiya, ka rinKa ku fito, ku fito kenan.”
Zaid ya saki baki yana kallon ikon Allah, “Yau kuma ashe uwa tana canzawa da ban sani ba, Anty Adiyya yau ta shiga tsakaninmu.” “A’’a tafi dai can wurin Umma Wata Kila ka samu mazauni, ba ka kula min da’ya da kyau kam, ba za mu shirya ba.” Yana kallon yadda Adiyyan take kallonsa ta Kasan
idanu da murmushi Kunshe a fuskarta. Ya san ba Karamin dadi take ji ba, an titsiye
shi, don haka ya kai hannu ya shafo gefen fuskarta, “Ki kula da kanki Twinkle. Bari naje kar su Anty su cinye ni danye.” Umm Adiyya kunya kamar ta nutse cikin Kasa, ba ta Karasa sandarewa ba, sai da
ya duKa ya sumbaci gefen fuskarta. Da da wuKa a hannunta, yau za ta dabawa Zaid.
“Oya Malam, waje Road, ka ga min wata tsiya a nan, mu za ka gwadawa kula da ita a yanzu, bayan asirinka ya tonu?” Mama kam murmushi kawai ta yi, ta kawar da kai. Zaid ko ya fice yana dariyar
mugunta a ransa. Anty ce ta Karasa ba ta abincin tana fadiin, “Wannan Yayan naku bai da kirki, ki daina biye masa ki na cin abinci kan lokaci, kin ji ko?” Ita kam gyada kai kawai ta yi. Ko sunan Zaid ta Www.bankinhausanovels.com.ng tsani ji, bare a alaKanta ta da shi. Ba wanda ya tambayesu me ya sa ba a taho da Fatima ba, hakan sam bai mata dadi ba, don haka, wayarta ta dauka ta kirata a waya. Ta sanar da ita isarsu lafiya.
Fatima ta yi murmushi ta ce, “Ya yi kyau, ku gaida su Mama don Allah.” Za su ji Inshaa Allah.”
Har Umm Adiyya za ta ajiye ne, ta ji ta ce, “Yaya Zaid na kusa ne?” Zaro idanu ta yi waje, kar dai bai mata waya ba? “Ya dan fita, amma zai kiraki idan ya shigo, wayar ta sa ce ba caji.” Ta maka wannan Karyar ce, don sam haka nan taga gaba daya a tafiyar Fatima akafi Kwara.
************
“Fatima tana jirar wayarka.” Ta fada masa a taKaice. Kallonta ya yi kai a kulle, kafin ya fahimci me take nufi. “Ke ki ka kirata?” Ba ta ba shi amsa ba, ta ci-gaba da cin Awararta, tana dandanan yaji. Wanda ta sa Fadeela ta nemo mata, domin soyayyarta da awara bai da geji, idan ta ritsa shi, ta kan ci shi a matsayin abincin rana. “Wai ke bakin ki baya hutawa ne da ci?” Ina ruwanka da ni cikinka ko nawa?” Lumshe idanunsa ya yi, yana sauke numfashi a hankali, “Look, na fahimci duk abinda ki ke yi, ba komai bane, sai don kin ga ba na so. Ki min alfarma daya, kar ki riKa yi a gaban jama’a.” Daga gira daya ta yi, “Oh, ka na nufin kar na bada kai a cikin jama’a? Kar ka damu, ba kai kadai ka iya acting ba, bare a gano ni, Love.” Ta fad tana lome awarar da ya rage na Karshe hade da lumshe idanu don santi, ta karkade yajin a cikin farantin gabanta.
Yatsina fuska ya yi ya ce, “Don Allah ki koyi KirKirar abu na gaske, Love dai?” To me ka ke so na ce maka? Ko kai ba haka ka fada ba? Sweetheart ko Darling ka
ke so na ce maka? Duka tsoffin yayi ne, hmm bari mu ga H. Ya yi maka?” Tsuke idanu ya yi yana girgiza kansa, alamar Kosawa da sha’aninta. “Yarinta na
damunki har yanzu.” Yawwa, H. Ya yi maka kenan. H. For Hypocrite.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba zato ba tsammani ta ji wani azaba ya ziyarci bakinta, dalle mata baki ya yi da yatsarsa. “Ki Kara fada ki gani.” An fada din, mugu kawai, kuma sai na fadawa Anty.” Ta Kara juya idanunta hadee da turo baki kamar za ta yi kuka. Saura kiris! Ya kwashe da dariya, ga tsokana ga tsoro, ga saurin kuka ga
shagwaha.” Adiyya, shekarunki nawa ma?” Ba ta kula shi ba ta miKe da farantin hannunta ta nufi hanyar waje, “Ka je ka tambayi Maami, tunda kun fi kusa.”
Wuni suka yi suna zagaya gidan ‘yan-uwa ranar, fuska a sake, ba mai cewa akwai matsala a tsakaninsu. Duk inda suka je kallo ake masu, ba ta raba daya biyu, sun yi mamakin rashin ganin Fatima ne, ko ba komai ai tare aka yi aurensu, ita ma da sai
ya kawota, amma ya zabi ya daukota ita kadai.
Suna hanyarsu ta komawa gidan Baffa Abdu ne, ta dube shi ta ce, “Yaya Zaid? Me ya sa ka daukoni ni kadai?” Shiru ya yi jim! Har ta zaci ba zai amsa mata tambayar da ta yi masa bane, sai kuma ya dubi bangaren da take zaune. “Saboda ban yarda da ke ba.” Baki ta bude, don mamaki, “Me ka ke nufi ba ka yarda da ni ba? Kona maka gida zan yi, ko me?” “Za ki iya guduwa, na san hali.” Dariya ta yi iya isarta ta ce, “Cewa za ka yi ba ka yarda da matsayinka a tare da ni ba, idan dai haka ne. Domin da ka san kana da matsayi a raina, da ba abinda zai sa maka tsoron guduwana daga gidanka.” Shiru ya yi bai ba ta amsa ba. Kansa ya yi dif, bai san ma meye abin yi ba, lokaci
daya rayuwarsa ta juya ta dagule, duk a sanadiyar wannan yarinyar. “Kin rikita min rayuwa Adiyya.” Ya fada Kasa-Kasa game da sauke ajiyar zuciya.
Murmushi mai daci ta yi ba tare da ta kalle shi ba ta ce, “Nima na tsaneka Yaya Zaid.” Damke sitiyerin motar ya yi, ya Kara taka wuta. “Meye abin yi?” Ya tambaya tamkar bai ji abinda ta fada ba. “Ka rabu da ni kawai.” Murmushi ya yi mai sauti. “Baya cikin zabi, buKatar ba ta samu amsuwa ba.” Juyowa ta yi ta harare shi. “To me ka ke tunanin shi ne mafita, baya ga wannan dama? Ai ba wata mafitar da ta wuce wannan.” Wannan karon dubanta ya yi kadan, sannan suka sha kwanan isa gida. “Ki koyi so
na, saboda koda so, ko babu a gun Allah da kowa ma ke matata ce. Kuma Allah na Www.bankinhausanovels.com.ng
iya kama ki akan duk wani batanci da za kiyi min. Ni kuma kin ga ba zan so hakan ba ko kuwa, matata?” Ya Karasa hade da daga mata girarsa cikin murmushi.
***********?
BABI NA SHA HUDU
A ko yaushe idan ta fara tunanin Zaid ya yi hankali, yana magana ta masu hankali, sai ya nuna mata KwaKwalwarsa a juye take. “Kullum ina mamakin yadda aka yi har AZ ya kai haka a ci-gaba, na tabbata sa hannunsu Femi ne, ba yadda za a yi a yadda ka ke tunani, ya zama kai ka kai kamfanin matsayin da yake yanzu.” “Ouch!” Ya fada dai-dai lokacin da ya tsaya a gaban gidansu. Da sauri Adiyya ta juyo ta dube shi. “Me ya faru?” Kura mata idanu ya yi sannan ya ce, “Never challenge a man’s intelligence.” Fita yayi ya bude mata Kofar motar, sannan ya rufe, bayan ta shige ciki, bai bi bayanta ba. Lambar Fatima ya nema.
**********
Tunda ya sauketa a gida, ta wuce dakin su Maryam, haka kawai ta ji ba ta cika son ma ta zauna cikin jama’a ba, domin duk inda hirar ta je ta dawo, to kanta da Yaya Zaid yake sauka. Ita kuma kallonsu kawai take yi, yadda suka gama daukar matsayi
na musamman suka damKa masa, koda yake ko don yadda yake kula da su yake nuna masu Kauna yake kyautata masu, dole su yi zaton shi gagarumin mutumin arziki ne. Bata san me yake nufi da Www.bankinhausanovels.com.ng kalamansa na Karshe ba, amma tabbas ta san ta tabo inda yake masa ciwo. Wannan ya sa ta murmushi. Dan kunnayenta ta cire, sannan ta fada bandaki, don ta dan watsa ruwa.
Ko kafin su Maryam su gama abinda suke yi, su shigo ta bi lafiyar gado, kasancewar ya fada mata da safe za su kama hanya, wannan ya sa ta kwanta da wuri, sai dai kan barcin ya dauketa, saKo ya shigo wayarta. “Sweet dreams Twinkle, keep being yourself.” Kwarai saKon ya daure mata kai, ba ta san me yake nufi ba, don haka ta rabu da shi, ta san duk a cikin salon sa na tsokanarta ne, don ranta ya Baci a banza. Addu’a ta yi ta shafa abin ta, ta fara KoKarin mance damuwar Zaid a karo na farko, tun
randa ta gan shi a ofis dinsa, wanda wannan rana daya kadai ta juya dukkan al’amuran rayuwarta.
Komai da yadda Allah ya tsarawa bawansa, ba abinda za ta ce game da wannan
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG