UMM ADIYYAH CHAPTER 23 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Allah Yai miki albarka, Adiyyata.” Yanzu kam ba tantama ta ji zuciyarta ta kumbura a Kirjinta, saura kawai ta fashe, idan fashewar zuciya abu mai kyau ne.Dama da gaske haka amare suke da kunya ko kuwa dai tawa ce ta daban?” “Yaya Zaid, don Allah ka bari.” Ta fada a shagwahe hade da karya wuya.
Abu na gaba da ta ji kawai, shi ne fuskarta a tafukan hannun Yaya Zaid, inda ya shiga sumbatarta a hankali. Da farko numfashinta ne ya tsaya cak! A lokacin da numfashin ya dawo kuma ta kanta ya dawo, ba tantama saboda wani jiri da ta ji ya
kwasheta daga zaune, wani luuu! Ta ji kanta yana mata. Sai da aka dauki tsawon mintoci, sannan ta fado duniyar da suke. A hankali ya sake ta, inda wani numfashi ya kubuce mata, hada idanun da za su yi
ZAMU TASHI
ne, yayi mata murmushi, ita ma haka ta mayar masa da martani hade da sadda kanta Kasa. “Taso mu je mu ci abinci.” Kirjinta ta dafe da sauri, “Lah! Ban ma yi ba fa tukun, daman idan na yi sallah ne na ke so na sauka na…” Relax. Ki yi sallar Issha’ an kusa a fara kira, idan mun fito, sai mu je mu ci abincin.”
Ta so ta ce masa a waje? Sai kuma ta yi tsut da bakin, don har yanzu zuciyarta Balli balli take mata.
*************
BABI NA GOMA SHA TARA
Tun bayan dawowarsu daga cin abincin, ta shige dakinta ta fesa wanka da ruwan turaren wankanta, ta yi shirin barci. Ba ta yi Karya ba jiya, da ta ce da Adda Zubaida tana Kamshi, don ba ta wasa da Kamshi ita kam. Tana tsakiyar kade gado ne. Zaid ya shigo dakin, sai da ta ji gabanta ya fadi. Amma fara’ar fuskarsa ya sa ta ji dama-dama. Bare fitarsu ta dazu sun yi hira sosai, ya ba ta labarai ya kuma Www.bankinhausanovels.com.ng saurari nata labaran. Duk da ba da yawa bane hirar tasu, amma dai ana samun ci-gaba. Isowa ya yi gefen
da take ya ajiye robar ruwan da ya shigo da shi dakin. “Na shigo da shi dazu ma.” Ta fada a tunaninta ya kawo mata ne. “Na sani, na Karo mana ne.” Zaro idanu ta yi, ba ta gane ya kawo masu ba? Yana nufin… Nan da nan ta shiga raba idanu, “Ya kamata ki nemi filter, duk abinda ki ke tunani yana nunawa a fuskar ki.” Ya fada yana dariya cikin sautin muryarsa mai dimautar da ita. Yana fadan hakan ko ta juya baya, ita a dole ta boye fuskar, ji take yi kamar ta natse cikin Kasa. “Ki shiga ki yi alwala, ki zo mu yi addu’a.” Ai da karatunta sarai ta san sallar godiya ga Allah yake nufi, tunda tun bayan
aurensu, yau ne suka samu natsuwa da sukuni har ma wai suke magana ta mutunci. Ina da alwala.” Ta fada Kasa-Kasa. “Good, ki shirya sai mu yi sallah, ki fara mana wannan addu’ar ko?” Murmushi ta yi, Kafarta na wasa da kafet din Kasan dakin. Sallayarta ta shimfida masa ita ta tsaya daga kan kafet dinta siriri na gefen kujerar dakinta, ya jasu a sallar nafila, cikin tsanaki. Bayan ya kammala masu addu’o’i ne, ya juyo yana fuskantarta, ya kula da yadda gaba daya ta yi narai-narai. “Twinkle ba dai tsoro ba, ban mance maganarmu ta jiya ba dai, ki kwantar da Www.bankinhausanovels.com.ng hankalinki.”’ Duk da wata ajiyar zuciya ta kufce mata, sai ta ji wani iri kuma ta rasa dalili. “Amma
dai kin san aje-aje wannan zuri’ar tawa da za mu shiga aljanna da su din nan, idan an amsa addu’o’inki, dole a same su kan a bar duniya ko?” Dariya take yi hade da sunne kanta cikin cinyoyinta, sa hannu ya yi ya dagota yaja ta Dangaren jikin sa ya ce, “Haba dai Twinkle, ina nan din za ki yi dariya a gefe, ai daga yanzu ga kafadarki nan, na yin dariya da kuka, duk sanda ki ka ji yi, ki zo kawai ki jinginu a jiki, ki yi son ranki.” Bude idanu ta yi kadan, “Lalle ma, ba za ka ba ni haKuri ba kenan, idan kuka na keyi?”
To na hanaki dariya ne, da zan hanaki kuka? Ki yi son ranki, idan kin gama sai na share miki hawaye.” Daure fuska ta dan yi, dan Karamin bakinta ko ya yi gaba cikin alamar fushi, numfashinsa yana sauka kan fuskarta. “Ka ma fi son na yi ta kukan kenan.”
“Wane ni Zaid, na isa na sa Twinkle dina kuka? Wa zai haska min rayuwar tawa to?” Kara gyara mata kwanciya ya yi a Kirjinsa, suna zaune shiru suna sauraren bugun zuKatan juna da numfashin juna.
“Za mu kwanta?” Ya rada mata a kunne, jin ta yi shiru da yawa, abin da ya ba shi dariya, shi ne ji ya yi ta maKe kafadarta alamar a’a. “cikin dariya yace, to in dai ki ka Kara minti biyu a nan, babu ruwan Zaid akan abin da duk ya faru.” Ba shiri ta zabura ta matsa baya, wanda ya sa ya tuntsure da dariya. “Duk dai wayon amarya…” Rufe idanunta ta yi tana dariya, “Yaya Zaid ba na so, ka bari.” MiKewa ya yi ya kashe wutan dakin hade da fadin “Sai da safe.” Nan da nan duhu ya gauraye dakin, a sanyaye ta amsa da. “Allah ya tashe mu lafiya.” Ba ta yi aune ba, ta ji ta a iska, ya daga ta cak! Hannu ta sa ta riKo shi da kyau, Yaya Zaid!” “Kawai cewa za ki yi na dawo, sai na dawo. Amma tunda kin ki fada… Sorry can’t help it. Ki tuna min, na ba ki wannan sassaucin
wani lokacin, amma ba yau ba.” Za ta yi magana ne, ya katseta da wata sumba mai juya tunani da mantar da ababe, ciki har da damuwowin duniya dama alfarmar da ta nema.
***********
Mamaki ne ya cika su da suka ji an kira babban taro, na kamfanin (General Meeting)
a safiyar cikin babban (Board Room). Amma kansu bai gama daurewa ba, sai da suka shiga suka ga an jera ababe na tabe-tabe da lashe-lashe da jiKa maKoshi.
Kowa sai kallon Dan-uwansa yake yi yana Kus-Kus, cikin son sanin abinda yake faruwa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ga shi yau har Engineer Sufyaan ya zo taron, wanda shi ne taya na uku na tafiyar da kamfanin nasu.
Umm Adiyya na zaune a gefen Jamila suna jira a fara gabatar da taron ne. Jamila ta dan rage murya ta ce, “Wannan ne daman SBS?” Kasancewar ba ta dade da zuwa ba ita ma, ba ta san daya mutumin ba. Umm
Adiyya ta amsa mata da kai, domin daga idonta zuwa inda Zaid ke tsaye da Femi da Engineer SBS, idanunsa suka sauka a kanta. Murmushi ya yi mata mai cike da alKawura, tana gab da kawar da kanta ne, ta ji
wani dal a ranta, saboda kashe mata idon da ya yi, duk da a faKaice ne, amma sai
da ta ji kunya kamar ta nutse Kasa, me yake tunani zai mata, wannan kallon cikin mutane sama da Talatin? Kau da kanta ta yi gefe, ta yi nata murmushin, tana jin Jamila sai zuba take yi, kan yadda masu kamfanin suka hadu na Kin Karawa.
“Ba wanda ya fi burgeni cikin sa kamar yayankin nan Oga Zaid, ba kya ganin yadda yake kama kansa, amma duk da haka baya ganin Kyashin ma’aikatansa, ya san
hakKin kowa. Ga ilimi, ga kyau. ‘yan gidanku duka kyawawa Hajiya Ummu.” Ba shiri Umm Adiyya ta juyo ta kalli Jamila, tana ganin yadda ta rufe idanu, ita a dole tana matowa kan Zaid. Murmushi kawai ta yi, ta kada kai, saboda ta san Jamila tana tsome tsundum cikin rashin sani ne. “Na ji labari, yana mutuwar son matarsa kuwa.” Adiyya ta fada tana kallon abokiyar
aikinta. A take Jamila ta tsume, hade da dan buga Kafa a Kasan tebur, “Ai bari ki ji, ba ki san haushin da na ji ba, da na samu labarin aurensa kwanan nan. Hmm.” Har da dan cizon yatsarta. Umm Adiiyya ko dariya kamar ya yi mata meye, haka ta yi ta dannewa. Gyarar muryar da suka ji ne, ya sa dakin ya yi tsit! Lokacin da zurfaffiyar muryar Engr. SBS ta fara kwararo bayani. Tunda ba kallon fuskar juna muka zo yi ba, ya dace mu fadi abinda ya sa muka tara kowa da kowa a nan, wasunku sun sanni, wasu kuwa ba su sanni ba, don haka zan
yi bayanin kaina da farko. Na ga Mr. Akim sai kallon kwanon kaji yake yi tun dazu kar yawunsa ya Kare tas.” Gaba daya dakin aka yi dariyar barkwancinsa, “Sunana Sufyaan Barkindo Sajoh, ina daya daga cikin jagororin kamfanin nan na bayan fage, dole na jinjinawa mutane biyun nan, wanda suke riKe da ragamar komai, suke saka Karfi da Karfe, don ganin
komai ya yiwu a nan, wanda a halin yanzu na ke Www.bankinhausanovels.com.ng farin-cikin sanar da ku, mun samu ta yin hadaka ta wata kwangila da wani babban kamfani a jihar Ohio da ke Kasar Amurka.” Dakin nan da nan ya dauki tafi da shewa. Cikin ‘yan sakanni aka kuma yin shiru.
Baya ga wannan babban abinda ya tara mu a nan, shi ne, na san kwanaki da yawa sun ji labarin Karuwar da dan-uwanmu ya samu na aure da ya yi, wanda saboda yadda abin ya kasance aka yi shi cikin gaggawa. Har ma wasu suka ce an masu rowar kajin biki.” Hasan ne ya shiga sunne kai, yana dallarawa Ayo harara, inda Ayo ya Ki kallonsa ya Kura tabarau dinsa kan Injiniyan da yake burge shi.
“To wannan taron na taya Engr. Zaid murnar aurensa ne daga bangaren kamfaninmu na (AZ IT Consultants and Services).” Bayan ya gama bayaninsa. Mr. Femi ma ya tashi ya yi nasa bayanin a gajarce hade da taya Zaid murnar aurensa. Lokacin da Zaid ya tsaya, domin ya yi jawabi, suit din jikin sa ya Kara fito da shi ya Kara masa Kwarjini, tamkar an gwada shi cif! Kan a dinka, ya bi jikin sa ya lafe.
Perfect cut. A tunanin Umm Adiyya.
Yana ta washe baki cikin farin-ciki, “Idan mutum yana da babban zuri’a da suke Kaunarsa har haka, ban san me zai nema ba kuma a rayuwa. Amma duk da haka kun riga kun sanni, ba na gajiya da neman Kari, don haka bayan na gode maku da wannan karramawar, ina barar addu’arku don na iya tafiyar da gidana, tamkar yadda na ke tafiyar da nan kamfanin har ma fiye da haka, saboda…” Kada kai ya yi, ya yi hucin numfashi, “Ina tabbatar maku, ba na son shiga hannun hagun Madam.”
Dariya aka yi gaba daya, “Abu na Karshe kuma shi ne, ina son na gabatar maku da macen da ta bada babban gudumawa wurin assasa (AZ IT Consultants and Services), Mrs. Umm Adiyya Zubair. My wife, My life.” Cak! Duniyar Umm Adiyya ta tsaya, ba ta taba tsammanin Zaid zai kira sunanta ba, ko ma ya gabatar da ita ba, gaba daya ta rasa inda za ta sa kanta, ga tafi yi ake yi, tana jin Hasan yana ta bayani wa na gefensa, irin ai department dinsu daya da itama. Www.bankinhausanovels.com.ng
Jamila ce ta riKo hannunta cikin jin dadi, gauraye da mamaki. “Lalle Hajiya mun tayaki murna, shi ne ki na ji dazu ina magana, ki kai shiru?” Jamila ta kuskusawa Umm Adiyya. Murmushi ta mata kawai, sannan ta sunkuyar da kanta. Muryar Mr. Femi ne ya ratsa su, yana dariya ya ce, “Da alama tana jin kunyarku ne, amma kar ku damu, za ku iya zuwa gidanta cin abinci, za ku ci har sai kun ture, ba ta
kunyar ciyar da abinci mai dadii.Daga nan wuri ya kaure da bayanai na farinciki, masu yiwa Zaid da Adiyya murna na yi, haka aka ci abinci a wurin, aka sha abin sha, aka yi nak! Sannan aka watse a
taron, tare da bada sauran ranar a matsayin half day wa duka ma’aikatan.
**************
Ta gama jan zif din jakar komfutarta ne ta ga takalmansa a gabanta, alamun ya shigo, duk da ta riga ta ji Kamshinsa kan ta ga takalman. Hannu ta ga ya miKa mata akan ta ba shi jakar, noKe kai ta yi tace, ““O’o, yaya Za kai min ha…” Sshhh, zo mu je zan miki bayani.” Ta san ba bayanin da zai mata, an dai yi abu kuma yanzu abokan aikinta za su na mata kallo na daban.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG