UMM ADIYYAH CHAPTER 24 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 24 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 



MUN TSAYA 

Dariya aka yi gaba daya, “Abu na Karshe kuma shi ne, ina son na gabatar maku da macen da ta bada babban gudumawa wurin assasa (AZ IT Consultants and Services), Mrs. Umm Adiyya Zubair. My wife, My life.” Cak! Duniyar Umm Adiyya ta tsaya, ba ta taba tsammanin Zaid zai kira sunanta ba, ko ma ya gabatar da ita ba, gaba daya ta rasa inda za ta sa kanta, ga tafi yi ake yi, tana jin Hasan yana ta bayani wa na gefensa, irin ai department dinsu daya da itama. Www.bankinhausanovels.com.ng
Jamila ce ta riKo hannunta cikin jin dadi, gauraye da mamaki. “Lalle Hajiya mun tayaki murna, shi ne ki na ji dazu ina magana, ki kai shiru?” Jamila ta kuskusawa Umm Adiyya. Murmushi ta mata kawai, sannan ta sunkuyar da kanta. Muryar Mr. Femi ne ya ratsa su, yana dariya ya ce, “Da alama tana jin kunyarku ne, amma kar ku damu, za ku iya zuwa gidanta cin abinci, za ku ci har sai kun ture, ba ta
kunyar ciyar da abinci mai dadii.Daga nan wuri ya kaure da bayanai na farinciki, masu yiwa Zaid da Adiyya murna na yi, haka aka ci abinci a wurin, aka sha abin sha, aka yi nak! Sannan aka watse a
taron, tare da bada sauran ranar a matsayin half day wa duka ma’aikatan.

**************

Ta gama jan zif din jakar komfutarta ne ta ga takalmansa a gabanta, alamun ya shigo, duk da ta riga ta ji Kamshinsa kan ta ga takalman. Hannu ta ga ya miKa mata akan ta ba shi jakar, noKe kai ta yi tace, ““O’o, yaya Za kai min ha…” Sshhh, zo mu je zan miki bayani.” Ta san ba bayanin da zai mata, an dai yi abu kuma yanzu abokan aikinta za su na mata kallo na daban.

ZAMU TASHI 

Ganin ta turbune fuska ne, ya rage murya kaddan a mota, hade da dora hannunsa kan nata a saman giyar motar, “Hey, kuma da tsammani ki ke yi na sa ido mutane suna kawo miki take-in lunches, suna kallar min mata ba tare da sun san suna shiga hurumin da ba nasu ba? Of course, kowa ya kamata ya san you own The Boss, so su yi hankali da matata.”
Adiyya ko dariya ya so ya ba ta, amma ta riKe, wato dama yana kula da sintirin Oga Musa kenan. “To Boss Man mai mata, ka iya yin gabatarwar ai a iya wurinmu sai ka tara dukka ofis abinka.”

Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ni ina ruwana? Abinda yake da muhimmanci, shi ne yanzu kam kowa ya san ke matata ce, hakan ya fiye min kuma komai.” Ya fada tare da daga hannunta ya kai bakin sa ya sumbata. Umm Adfiyya sai da ta ji ya tsirga ta har tafin Kafafunta. Ba ta zare hannunta ba, haka ya ci-gaba da riKe mata hannu yana tuKi da hannu dlaya. Har suka koma gida.

********

Suna shiga gida ne ta ga wayar Fatima na shigowa, nan da nan fuskarta ta sauya daga yawaitan fara’a.
“Ina zuwa.” Ta fadawa Zaid, wanda ya wuce falonsa kai tsaye, ita kuma sama ta fara
haurawa kafin ta danna amsa kira, bayan kiran farkon ta datse. “Assalamu-Alaikum.”
“Wa’alaikumussalam, kar ki zargeni na sani ya fada miki komai, na san ni ce mutum na karshe da za ki so yiwa magana amma zan miki bayani…” Ba zan yi maganar nan da ke ba Fatima.” Don Allah ki yi haKuri, na so na fada miki tun ba yau ba, shi da Maami suka hanani. Ki yi haKuri please, please, Wallahi albarkacinki ya ci na amince. Kin san ba zan so duk abinda zai cutar da ke ba. In fact, zan zo ma na ba ki haKuri da kaina.” “Shi kenan ya shige.”
“Huhn?” Mamaki ne ya yi matuKar kama Fatima, ta zaci duk randa abin ya fito fili Adiyya za ta yi watandanta ta raba, hakan ne ya sa da Maami da Zaid suka samu Mamanta da ita da wannan shiri ta Ki amincewa da farko, amma ganin duka sun damu har ma Babanta ya ce ta amince, ya sa ta yarda, sannan maimakon Umm A. Ta mammasifeta, cewa ta yi ya shige? Na san kowa baya wuce Kaddararsa. Allah kuma ya sa sai hakan ta faru, koda taimakonki ko Www.bankinhausanovels.com.ng babu da za su san yadda aka yi suka yi abinsu, don haka ba komai. Na gode.” Murmushi mai sauti ta dan yi, sannan ta Kara da, “Besides he is not that bad. Ba wai ina fada miki, ki fara samun ideas a kanki ba, ba zan bar ki ba wannan karon.” Daga daya bangaren ne Fatima ta sa Kara har da tsallen murna, “Yiiiihuhu, kai na ji dadiin wannan al’amarin, kwantar da hankalinki, tamkar tsummu a randa ‘yar uwa, nina kai Mahmoud dina ina? Allah ya bar so da
Kauna, to wai da da ki ke ta borin ki ke haukar ki meye dalili? Da kin yi wa kanki salalar tsiya, ki tsaya kallon ruwa…” An dai wuce gun, ki bar tone-tone.”
“Allah I hail Yaya Zaid, zan tura Mahmoud ya dau Kwas.” Kar ki fada min, shi ma yana cikin shirin naku? Da har na ji tausayinsa na mayar an maka shi da Kasa ne aka masa Kwace.” ““A’a dole, ai da shi a tafiyar kar ya ji jita-jita a gari matarsa ta yi aure.” Umm Adiyya ta yi dariya ta girgiza kanta, “Ban san ki na so na da yawa haka ba, har
ki ka sadauKar min da kanki, na gode Allah ya bar zumunci.” Ba komai. Allah ba ku zaman lafiya ya kade fitina. Don Allah a riKe mana yayanmu da kyau. Wallahi har kuka sai da ya kusa yi kan na amince.”
Ke ban son rashin mutumci, mijin nawa ne zai miki kuka? “To ya ga kin kwayance, kin sa Baffa Abdu yana so ya masa terere, yana sane sarai. Baffa Abdu zai samo miki wani mijin ne, da bai matsa hannu ba, ya zo min da batun wai wani Dan Bauchi yana so ya hure miki idanu, kuma shi yana matuKar sonki, ga
shi yanzu kun yi fada, kin dage ba kya sonsa, idan ki ka ga da gaske zai aureni, wata Kila ki amince.”
“Sannunku da shirin fim. Nan gaba ki ka sake ki san da cewa ba za ki share ba, bari ki ji in fadia miki, yanzu ma kin ci albarkacin na huce ne.” Ko kuma yarinya ta ga love ba.” “Fatima Abdullahi Nafada!” Fatima na dariya ta kashe wayar. Adiyya ta kada kai, sannan ita ma ta cire tata wayar a kunne, juyowar da za ta yi ne, ta gan shi a bakin Kofa yana bin ta da kallo.
murmushi ya mata, ya yi mata nuni da ta matso kusa.
Bai yi sanya ba ya riKo hannunta yana kallonta, “Ki yi haKuri da muka sakaki a wannan yanayin, ba zan gaji da ba ki haKuri ba Lumshe idanunta ta yi, sannan ta ce, “Ya shige na fahimta. Amma dai zan so na san
yadda har kuka saka Baffa Maikano a wannan shirin naku ya amince.” “Idan na fada miki, ni dan gata ne, ki rinKa yarda.” Ya fada hade da janta zuwa cikin
Dakin ya zaunar da ita a kujerar da ke gaban Www.bankinhausanovels.com.ng gadonta, sannan shi ma ya zauna a gefenta daf.
“Ai yanzu ma na ga zahiri, tunda kowa kai ya zaba ya bar ni.” Wa ya ce miki? Ke ki ka gama min komai, da kika Ki batun nan a gaban Abba, domin ba Karamin tunzura shi hakan ya yi ba. Wannan ya Sa ya je nema min auren Fatima.” Ganin idanunta sun bude, ya sa ya ci-gaba. “Yes there was a proposal. To fa da aka
je ne Baffa MaiKanon ya sanar da Abba, ai ta yi magana da wani mai sonta har ma iyayensa suna zuwa ba da dadewa ba, kin san shi ma wayeyye ne ba zai yarda ya yiwa Fatima dole ba. Amma duk da haka ya ce zai yi magana, idan mun daidaita shi Kenan, sai abin ya koma kaina da ita. Jin wannan ya ba ni Karfin gwiwa, don haka na sanar da Maami abinda ake ciki, na kuma fada mata har lokacin ke na ke so. Ita kuwa ba yadda za ayi ta je ta ce na fasa auren Fatima, sannan a komar da aure kanki, don haka ta ce ba za ta iya min komai ba. Wurin Baffa Maikanon na je ban boye masa komai ba, na fada masa ina sonki kuma su Maami da Abba sun yi fushi, don mun yi fada suna so na auri Fatiman, don hakane, hakan ya sa ya kira Abba ya nemi ganin sa. Ban san me ya canzawa Maami ra’ayi ba, da kanta ta tafi Kaduna suka yi magana da Mamansu Fatima. Maami da Maman Fatima ne suka shirya hakan. Abba ya so ya Ki. Baffa Maikano ya ce anyi an gama. Baa sanar da kowa batun Fatima zan aura ba, har sai da aka tashi bikin, wannan yasa su Adda Zubaida suka zo har ma aka zabi masu zuwa biki Abuja. Sai da aka daura aure maganar ta fito akan da ke aka daura, ba da Fatima ba, hakan ya hana ki fahimci komai, har lokacin bikin ya zo.” Ajiyar zuciya ta yi, sannan ta ce, “Kun yi Www.bankinhausanovels.com.ng KoKari.” Shi kenan, abinda za ki ce?” “Me zan ce to? Abinda ya riga ya faru ya wuce? Allah ya kade mana fitintinun da ke cikin zaman. Kamar yadda na fada maka komai ya wuce.” Ka san habar ta, daidai gefen wuyanta ya duKa ya sumbata, “Na gode.” Murmushi tayi har kumatunta suka loba ciki. Mashaa Allah, ana behabbik katheeran.” Zaid ya fadia yana kallon kyawawan idanunta. Rufe idanunta ta yi yadda ya Kura mata kallo, “Yaya Zaid yaushe ka zama balarabe?” Ki na mamaki ne? Akan sonki ko bacanise sai na zama ai Twinkle, ki shirya ina jiranki mu yi hira.” “Na dai shiga aikin kicin ko?’ “Koma menene, amma dai ki san ba zan bar ganganki ba, kwana daya kacal! Kin gama riKeni.” Murmushi ta yi ta wuce bangaren adana kayan sawanta, ta shiga neman kaya masu sauKin sakawa da za ta yi amfani da su idan ta yi wanka. Tana kallon kayan cikin wardrobe din ne ya tsaya a gefenta, ya sa hannu ya fito da wata riga tourquise blue, ta turawa ce guntun gown marar hannu, tana da siffar lema ta Kasa yadda duk juyi
take buduwa ta baje. Yayin da saman rigar take tsuke. Zare idanu ta yi tana kallon rigar, ta bude baki ta rufe, ta sake budewa, “Yaya zan sa wannan?” “Ba kayanki bane?’ Eh, amma, yaya za ayi na…” Shi na ke so ki saka min. Besides kuma me ya rage…?” Dole ta yi tsit, ta sa hannu ta karbi rigar hade da dunKuleta a bayanta. Yana dariya ya fice a dakin, don shi ma ya je ya watsa ruwa ya canza kaya, kasancewar zafi ya fara shigowa. Ta yi minti goma tana kallon kayan tana tunani, ta saba saka su riga da wandon jeans da ma sauran english wears, amma ? Ina za ta saka su? Ta tabbatar kuma Www.bankinhausanovels.com.ng wannan ba a kayayyakinta suke ba, sai dai idan a kayan aure aka sako mata. Wannan yana nufin Yaya Zaid ne ya saya kenan ko wa? Ba ta ma san wa ya hada masa kayan auren ba. Ta dai taba ganinsu gaban Maami a tunaninta na Fatima ne kamar yadda aka fada mata wannan ma ya Sa ba ta zauna ta kalla ba, don kishin da ya turniKe ta. Haka dai ta daure ta saka, ta tufke kanta da ribbon din da ya shiga da kayan, ta feshe jikinta da turare, ba ta damu da kwalliya mai nauyi ba, hoda ta murza, sai
gazal ta kuma shafa wetlips. Dan-kunne siriri dogo mai fareren duwatsu ta maKala a
kunnenta. Ita kanta da ta kalli kanta a madubi, sai da ta ji balli-Balli, ganin yadda ta Kara komawa kamar doll baby don kyau. Amma tana tunanin yadda za ta je gaban Yaya Zaid, a haka har ma ta yi masu girki. Karar wayarta ce ta dawo da ita daga tunaninta, ta ga dai aune-aune ba zai kai ta ko
ina ba, dole ta daure ta fita. Ajiyar zuciya ta yi tamkar za ta tari aradu da ka. Ta nufi Kofar fita daga cakin.

*********

BABI NA ASHIRIN

Tatacciyar madara ce a hannun Zaid yana sha a hankali, lokacin da idanunsa suka kai Kofar kicin din dai-dai lokacin Umm Adiyya take shigowa, tsayar da kofin ya yi daidai bakinsa na ‘yan daKiKu, mancewa ya yi da inda yake, ko abinda yake yi.
Gaba daya ta gama hautsina masa lissafi. Allah kadai ya san yadda aka yi, yau ya iya tabuka wani abin a ofis, bai wuce inda take aiki ya nemi su koma gida ba, sannan yanzu ga shi ya janyowa kansa.
Bai san yaya zai rayu idan ba Adiyya a cikin rayuwar ta sa ba. Wata baiwa ce Allah ya masa ta hanyarta, saboda shi kam ya haKikKance ya gama samun abinda zai nema na duniya kam. Da ya san cikin sauKi zai sameta har ma ta amince ba tare da girmansa ya fadii ba, yaushe zai kalli wata ‘ya mace bayanta?
Ya san yanayin tashinsa cikin abokai da rayuwar da ya yi a waje, inda suke cudanya da mata har ma a mance da cewa wannan mace ce ko namiji, ya Kara ingiza shi zuwa rayuwar da har ya janyo masa fushin Allah, ga kuma bacin ran Adiyyarsa,
yanzu da ya sameta, yanzu ne ya san meye rayuwa.
Murmushi ya yi mata da ya ga yadda take tafe a takure cikin rigar da ya dawo da ita
tamkar a sace don kyau. Sannan ya miKe ya isa inda take, “Ki jirani minti aya.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *