UMM ADIYYAH CHAPTER 25 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 25 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Bai san yaya zai rayu idan ba Adiyya a cikin rayuwar ta sa ba. Wata baiwa ce Allah ya masa ta hanyarta, saboda shi kam ya haKikKance ya gama samun abinda zai nema na duniya kam. Da ya san cikin sauKi zai sameta har ma ta amince ba tare da girmansa ya fadii ba, yaushe zai kalli wata ‘ya mace bayanta?
Ya san yanayin tashinsa cikin abokai da rayuwar da ya yi a waje, inda suke cudanya da mata har ma a mance da cewa wannan mace ce ko namiji, ya Kara ingiza shi zuwa rayuwar da har ya janyo masa fushin Allah, ga kuma bacin ran Adiyyarsa,
yanzu da ya sameta, yanzu ne ya san meye rayuwa.
Murmushi ya yi mata da ya ga yadda take tafe a takure cikin rigar da ya dawo da ita
tamkar a sace don kyau. Sannan ya miKe ya isa inda take, “Ki jirani minti aya.”

ZAMU TASHI 

Wuceta ya yi tana masa duban taraddadi, bai Karasa minti dayan ba ma ya dawo inda ya bar ta a tsaye.
Wani farin madaidaicin mayafi marar nauyi ya yafa mata a saman kafadarta guda, ya sumbaci saman daya kafadfar tata, sannan ya rufe mata shi, “Na ga alama aiki ne ja a gaba na kan mu gama cire wannan kunyar.” Ya rada mata cikin kunnenta. Yana sane da yadda gaba daya ta saki a jikin sa. “Za mu iya girkin kuwa?” Ya tambaya yana Kara cusa kansa a kwarmin wuyanta, yana jiyo Kamshinta. Gyarar murya ta yi, ta matsa daga riKonsa, “Za mu iya mana.” ‘Dauke kansa ya yi, saboda kar ta tsargu da yawa, “Me zan taya ki to?” “Ka zauna kawai

yanzu zan hada, tuwo zan mana.” “Ba zai dade ba?” A’a ba ka ce za ka rinKa ban labari ba? Yanzu za mu gama, Sai dai idan zaka tayani gyaran ganye kuma to.” Zare idanu ya yi cikin mamaki, sai kuma ya ce, “Yaya na iya kawo a miki, amma idan ki ka ga karare a cikin miyarki, kar ki ce nine. “Dadinta dai kai ma za ka ci.” Dariya ya yi Www.bankinhausanovels.com.ng sosai, sannan ya karbi wuKar da ta miKo masa, ita kuma ta wuce sink wanke ganyen. Kunya ka ke ji, kar a zo a ganka da wuKa a hannu?” Kin manta rainon Maami kenan, idan ki na so ma yau har miyar sai a miki.” Uhmm, tsaya dai a yankan ganyen, idan ba ka cire yatsunka ba, sai ka daura miyar.” Yana dariya, yaji wayarsa tana Kara, hannu ya sa ya daga ta daga kan kitchen Island din, sunan da ya gani a kan Screen ne ya ba shi mamaki, cikin lokaci daya fuskarsa ta sauya. Ya danna wayar, “Hello.” Hadle da juyawa don ya Saurari mai wayar da kyau. “Gani nan zuwa.” Ya fada bayan ya dade yana sauraren daya Bangaren. Juyowar da zai yi ne. Umm Adiyya ta kula da duk wata alamar wasa da nishadii sun bar fuskarsa. We have a breach,(Mun samu matsala) sun shige mu.” Ya fada yana sosa goshinsa da babbar yatsar hannunsa da ke riKe da wayarsa. “Damn it!”
“Inna-Lillahi’ wa-Inna-[lair-Raji’un.” Umm Adiyya ta fada tare da matsowa kusa da inda yake tsaye. “Garin yaya?” Charles ne ya kirani yanzu daga security.” “Yaya yawan barnar?” “Data. Data breach.” Gabanta ne ta ji ya fadi, wanda ya fi muni kenan. “Kaje, bari na gama wannan.” Ganin bai motsa bane, ya sa ta dube shi, “Yaya Zaid, ya zama lallai a fadawa ma’aikatan da ma clients (Kwastamomi), saboda komai na iya faruwa, ba a san don wa aka yi Barnar ba, ko kuma me suke da shi game da mutanen ba, ba a san su waye bane, komai na iya faruwa.”
“Haka ne, bari na kira Femi.” Yana tafe yana waya, ya gama da abokin kasuwancinsa, ya kira babba a kowane bangaren kamfanin ya ba su oda kai tsaye
akan su yi gaggawar canja mabudansu na shiga shafukan kamfanin. (Passwords). Hankalinsa ba Www.bankinhausanovels.com.ng Karamin tashi ya yi ba, yaya aka yi hakan ta faru, bayan duk irin matakan tsaron da suke dauka don kare ayyukan da suke yi da wanda suka yiwa jama’a? Yaya za ayi suna maKala na’urorin tsaro wa jama’a, ace su an shigo har kamfaninsu an masu satar suna (Identity theft)? Har ya isa tunanin hanyoyin shawo kan matsalolin yake yi, don haka yana isa ofis, wajajen shida da rabi, ya tarar da rabin ma’‘aikatan suna jiransa, domin su hau aikin kare kansu daga wannan mummunar barnar da ta shafe su. Yana ji wasu su ce wata Kila abokan hamayya ne na kasuwanci irin nasu, wasu suce wata Kila a dalilin wani mutum ne daga cikin kwastommominsu aka yi masu haka. Zaid Abdur-Rahman kallonsu kawai yake yi, shi ba ta nan ne damuwarsa ba. Damuwarsa ita ce zuwa yaushe za su gama assasa gyaran da suke yi. Kafin a gama kwashe sirri mafi girma da suka taba aiki a kai? Agogonta ta kalla a karo na bila adadin. Daidai lokacin da ta ji Malam Kawu yana bude get din gidan, ta mike zuwa kasa, tana jiran isowarsa, ta san ba Karamin aiki suka sha ba, kasancewar tuntuni ba ta samun wayarsa. Kallo daya kuwa ta yi masa, ta san hasashenta ya zamo gaskiya. Matsawa ta yi
daga bakin Kofar bayan ta bude masa. “Sannu da dawowa.”
“Yawwa. Sorry na bar ki, ki na jira.” Ya fada yana kallon yadda duk idanunta suka nuna damuwarta Karara. Kafin kallonsa ya koma kan farar Gypsy Gown da ke jikinta, wanda aka surka da launin ruwan dorawa. Siririn hannu gare shi, ga wani sansanyar
Kamshi da gidan da ma ita kanta take yi. “Yaya ku ka Karasa? Wayoyinka ba sa shiga tun dazu.” Ta tambaya cikin damuwa. Bai amsa mata ba, maimakon hakan jawota ya yi jikin sa, yana shaKar Kamshinta,
ya dauketa a bazata, don haka ta daskare cikin riKonsa, ba shiri ta yi shiru ba ta maimaita tambayar ba. Ba ni abinci na ci.” Ya fada Kasa-Kasa, tamkar tsabar gajiya muryarsa da Kyar take fita. Www.bankinhausanovels.com.ng
Juyawa ta yi zuwa tebur din cin abinci inda ta riga ta jera masa nasa, bayan ta fitar da na waje. Abin sha mai sanyi, ta fito masa da shi wanda ta hada da daren. Shi ta fara mika masa, sannan ta zuba abincin. Juyawan da za ta yi ne, ta ga ya shimfida darduma a gefen teburin abinsa, nan ta sauke kayan abincin, ta zauna a gefe. Yaya ki ka zauna, ke ba za ki ci bane?”Ka gama ci tukun, bari na kwashe sauran kayan na wanke.” Wani kallo ya yi mata tukun, sai da ta kau da kanta, “Zauna mu ci, yaya za ki zauna
da yunwa har goma na dare ba ki ci abinci ba, za mu bata da ke, idan ki na barin Twinkle dina da yunwa fa.” “To hankalina ya kasa kwanciya, ban san me ake ciki ba, ko na saka, ba iya ci zan yi ba ” “Yanzu tunda na dawo matso mu ci.” Hannu ta sa a robar wanke hannun da ta ajiye masa ta wanke hannunta, tana
Kokarin sakawa a plate din ne, ya hanata.
“Aikin ya isa mana kuma, bayan kin dafa, ai sai ki huta yanzu kam. Ke dai kawai tauna ne naki, inda hali ma sai a tauna miki.”
Dariya ta yi, ta riga ta san yana cikin damuwa kawai KoKarin kawar da hakan yake yi ta hanyar jan ta da hira. Bude bakinta ta yi kadan, ya sa mata abincin a baki, yana ci yana ba ta har suka kammala, suka kwashe kayan zuwa kicin. Tana dauraye kwanukan ne ta kula da yadda Zaid ya yi shiru, hankalinsa ya yi nisa. Goge hannunta ta yi jikin tawul din goge hannu dake rataye a jikin windon kicin din, ta je kusa da shi ta dafa hannunsa a hankali. “Yaya Zaid, me ya faru a ofis?” Lumshe idanunsa ya yi ya mata murmushi. “Kar ka ce babu, domin na san akwai, kai ba mai yawan fadawa tunani bane.” Daga girarsa daya ya yi yana dubanta hade da mata murmushin gefe, sai da zuciyarta ta girgiza. “Da gaske? Tun yaushe aka san abubuwan da na ke yi da wanda ba na yi?”
Kau da idanunta ta yi, ita ma da nata murmushin, ta dan juya su. “Wannan ba shi da muhimmanci, kawai dai idan akwai abida yake damunka, don Allah ka fada, ba na son ganin ka haka cikin damuwa.” Cije lebensa ya yi na Kasa ya rike da hakoransa hade da jawota kusa da shi ya dorata kan Kafafunsa, “Hmmm, ban sani ba ai da tuntuni na zo na fada miki, na ce Twinkle ina Www.bankinhausanovels.com.ng cikin damuwar soyayyarki, ki taimaka ki aureni, kin ga da tuni mun huta wannan zagayen danwaken.”
Make kafadarsa ta yi ta ce, “Haka ake tambayar aure? So unromantic.” Ta juya idanunta tana kada kai. “Ke! Ki dai fadi gaskiya. Kin ga hadadden dan fillo duk kin rude kin kasa samun sukuni, na san duk wannan kukan ma kukan Karya ne, ana so ana kaiwa kasuwa.” Jan numfashi ta yi hade da zare idanu, “Yaya Zaid! yaushe na rude? Kuma ku kan gaske ne idan ba ka yarda ba, kuma na yi maka ka gani.”
Rufa min asiri, mai kukan wata biyu. Amma dai mu je zuwa asirinki zai tonu watarana, ni na san yadda zan yi kuma.” Ganin ya fara shisshige mata ne cikin wasu sabbin salon da sai a wurin Yaya Zaid take
gani, ya sa ta matsar da kanta gefe,
Maganar gaskiya ba ka fada min ba dai kar ka zaci na manta.” Wai ke ko yaushe Kwakwalwarki akan aiki take tunani ne? Ki huta don Allah, ba wani abu. Zo mu je mu shiga. A gajiye na ke lis! Sai an hada da wasu dabarun yau kam na ga alama.” Da sauri ta sauka daga kan Kafafunsa, yana dariyarta ya tashi daga kan kujera mai tsawon da ke kicin din inda suka fi zama a gidan. Bai dai Kara bari ta dago maganar wurin aiki ba bare matsalar da ke hannu. Ko ma
menene ya jibanci matsalar aiki gobe a koma masa, amma yanzu yana da amaryar da take buKatar kula da daukar darussa.

***********

Yau ma tare suka isa wurin aikin nasu. Kowa ya gansu, sai ya juyo ya sake kallonsu. Musamman da aka yi sanarwar jiya. Ummu Adiyya ji take yi kowa ita yake kallo. Cikin murya Kasa-Kasa ta ce masa, “Split (Mu raba hanya).” Dariya ya yi mai dan sauti ya saKala hannunsa cikin nata, ai a take ta tsaya cak! A kusa da Kofar shiga babban falon tarbar baKin. “Da gaske Yaya Zaid, gun aiki ne fa, kowa mu yake kallo.” “To na ji na Kyaleki, yi gaba, kuma a zo cin abincin rana a ofis dina ko kuwa ki ganni.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba shiri ta gyada masa kai, don dai ya saketa, tuni ta hango Ruth da Abigail suna dariya Kasa-Kasa daga cikin falon tarban bakin, suna Kus-Kus. Ta rasa me ruwan mutane da gulma, da ba ace ita matarsa bace, zai zamo abin magana, an fada ma ba su tsira ba. Koda yake a matsayinsa na shugaban kamfani
ya kamata ya tsayar da alaKarsu daga wajen wannan Kofar ko don gudun Korafi
daga sauran ma’aikatan. Ita kadai tana tafe tana ta murmushin da ba gaira ba dalili, har ta sha kwana inda ofishinta yake. Tana shiga jama’unta suka hau yi mata murna, amma daga bisani suka nuna rashin
jin dadiinsu na boyesu a duhu da ta yi.
“Ku yi hakuri ba haka na so ba, amma yanzu tunda kun sani shi kenan, zan maku cake na kawo wani sati, idan mun warware damuwar da ta kunno kai.”
Nan da nan kuma jikin kowa ya mutu. Saboda duka suna da labarin abin da ya faru.
Oga Musa ne ya matso teburinta, bayan awa daya da shigowarta aiki ya dan mika masu. Hannunsa rike da ‘yar jakarsa mai kyau na kwalin kyauta, “Hajiya ga wannan ba yawa. Muna tayaku murna. Allah bada zaman lafiya.” Ya fada cikin turanci. “Na gode sosai, ba sai kun shiga wahala ba fa.” Ta zaci na gaba dayansu ne kyautar, sai da kowa ya yi ta layin kawo nasa. Ta rasa inda za ta tsoma kanta, don jin dadi.
Wayarta ce ta yi Kara ta daga, “Maami, an tashi lafiya?” “Lafiya Alhamdulilah, ki na wurin aiki ne ko

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *