UMM ADIYYAH CHAPTER 26 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 26 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

ya kamata ya tsayar da alaKarsu daga wajen wannan Kofar ko don gudun Korafi
daga sauran ma’aikatan. Ita kadai tana tafe tana ta murmushin da ba gaira ba dalili, har ta sha kwana inda ofishinta yake. Tana shiga jama’unta suka hau yi mata murna, amma daga bisani suka nuna rashin
jin dadiinsu na boyesu a duhu da ta yi.
“Ku yi hakuri ba haka na so ba, amma yanzu tunda kun sani shi kenan, zan maku cake na kawo wani sati, idan mun warware damuwar da ta kunno kai.”
Nan da nan kuma jikin kowa ya mutu. Saboda duka suna da labarin abin da ya faru.
Oga Musa ne ya matso teburinta, bayan awa daya da shigowarta aiki ya dan mika masu. Hannunsa rike da ‘yar jakarsa mai kyau na kwalin kyauta, “Hajiya ga wannan ba yawa. Muna tayaku murna. Allah bada zaman lafiya.” Ya fada cikin turanci. “Na gode sosai, ba sai kun shiga wahala ba fa.” Ta zaci na gaba dayansu ne kyautar, sai da kowa ya yi ta layin kawo nasa. Ta rasa inda za ta tsoma kanta, don jin dadi.
Wayarta ce ta yi Kara ta daga, “Maami, an tashi lafiya?” “Lafiya Alhamdulilah, ki na wurin aiki ne ko

ZAMU TASHI 

gida?” “Ina wurin aiki, wani abu ne?”
“Tun jiya Innayo ta iso daga Gombe, matar da na ce za ta rinKa taya ki zama, na
nemi wayarki ba ta shiga, ta Zaid kuma a kashe, da zan sa su FaruK su kai ta na ga
dai gwamma mun yi magana tukun. Umma ce ta samota cikin ‘yan-uwa, sai ki kula da ita da kyau.”
To na gode Maami. Idan na tashi zan biyo gidan. Yau ba ki fita bane?’ “Aikinmu da hutu ne? Ina wurin aiki, na bar ta dai a gidan.” “To shi kenan.” Ba ta fadawa Maami halin da ake ciki ba a

kamfanin, sai taje ta Www.bankinhausanovels.com.ng
sameta ta fada. Wunin ranar kowa ya Kwala saboda sai da suka canja taswirar tsaron kamfanin gaba
daya tare da ayyukan da suka yiwa jama‘a, bangaren kula da matsalolin kwastamomi kuwa can Zaid ya Kaura ma gaba daya yana ta amsa tambayoyin da
ake masu, da kuma bayanai kan cewa abubuwansu ba su samu matsala ba, take aka sake press release ta kafofin sada zumunta da na labarai, ba sai sun damu ba, amma ya zamo lallai su canja komansu dangane da Passwords gudun kar ai masu barna. Lokacin cin abinci da ya yi. Umm Adyya ta duba agogo hade da tambayar Hasan ko su Oga Akimu sun bar customer care? “Suna ciki har yanzu.” Ta san Zaid ya ma manta da batunsu, don haka ta fito da Maltinanta wanda Baba Masinja ya sayo mata da kek za ta ci. Ta balle hancin gwangwanin kenan, ta juya, ta Www.bankinhausanovels.com.ng
ga duka sun watse a ofis din, ta san dai sun yi sallah sun shigo kuma da sauran lokacin break, wata Kila yau a waje za su je cin abinci, don haka ta kurbi abin ta. “Hajiya ana nemanki a waje wurin parking wai za a ba ki saKo.” Kanta a kulle, ta gama tunani ba ta gane waye bane. “Sunana suka kira?”
“Eh ina ga daga gida ne, haka dai Baba masinja ya fada.” Mikewa ta yi cikin tunani, tana ji, tana gani ta bar dan kek dinta ta dau jakarta ta fita can waje. “Ba kyau Solo.” Ta ji muryarsa daga gefen babbar Kofar shiga kamfanin, motarsa na
ajiye a gefe kadan wurin fakin din Daraktocin kamfanin. Murmushi ta yi ta dago kanta, bude idanunta ta yi wato da gaske yake mata da ya
ce, idan ba taje ba, zai zo. Ga shi ya kirata waje. Ayo! “Na mayar ku na aiki ne ai.” “Sai na manta da Twinkle dina? Kin shirya?” “Fita za mu yi?” “Mu je sai ki gani.” “Amma yanzu lokacin break zai Kare.”
Ke dai ki shigo mana.” Ba yadda ta iya, haka ta fada cikin motar, ya tada ta. Wani Kawataccen wurin cin abinci suka shiga, sai lokacin ta ce, “Ba ka kira wayata ba.” Shafa aljihunsa ya yi ya ce, “Oh, ba ta wurina.” Tun jiya ko? Maami ta ce a kashe tun jiya tana nemanka ba ta samu ba.” Hannu ya sa ya bude Kofar motar hadle da kashe AC. “Meye ba ka fada min Yaya Zaid?” Ajiyar zuciya ya yi ya jinginu da kujerar motar. “Aikin ciki ne, ana tunanin har
wayoyinmu an tura wani mummunan virus, don haka saboda tsaro yanzu duka ana binciken wayoyin kowa da sauran na’urori.” “Amma ga tawa…”Za ki bada ita anjima kan mu je gida.” “Me ya sa ban bayar ba tun da safe?” Shiru ya yi bai ba ta amsa ba, har sai da ta nanata tambayarta ta. “Ni na ce su bari na karba da kaina.” Don Allah kar ka fara haka, ba amfani, yanzu ka ga su Charles din za su ga tamkar ka nuna son kai ne, no wonder dazu da na amsa waya, na ga Hasan na kallona.” Kashe wayar tata ta yi ta miKa masa.
Bai yi yunKurin karba ba. Don haka ta ajiye masa cikin ma’adanar da ke Kasan wurin sanya faifayin dis.
“Akwai abinda ban fada miki ba.” Ya fada hade da tsayar da ita daga yunKurin bude Kofar da take yi, shi ma ya ja tasa kofar ya rufe hade da kunna iyakwandishon din motar. Kallonsa take yi tana jiran bayanin sa. Ganin ya kalli Kasa ya sauke numfashi kan ya fara magana, tuni hannunta ya kai bakinta ta rufe. “Kar dai…” Gyada mata kai ya yi. “An bi diddigin mafarar barnar. An samu adireshin (ping address) barnar daga wayarki ne.” “Inna-Lillahi’ wa-Inna-Ilaihir-Raji’un…” A take Umm Adiyya ta ji Www.bankinhausanovels.com.ng kanta ya sara. “Ki kwantar da hankalinki. Bai kamata na fada miki wanann ba, duk da mai shi ya yi KoKari wurin boye takunsa, (Masking), amma sun bar abu guda, wanda ya nuna abin nan ta wayarki ko komfutarki aka yi. Tunanina daya, shi ne ba yadda za ayi wanda ya gwanance kan irin wannan ta’asar,
ya yi kuskuren barin burbudin shaida (breadcrumbs). Idan satar gaske ne, za su boye takunsu da kyau, wannan yana nufin abubuwa biyu, ko dai ana so a daura miki barnar, a bawa wani laifin ko kuwa ana so a bata min suna ta hanyar amfani da ke.” “Amma jiya ne fa aka san da batun aurenmu.” Duk na yi tunanin hakan, amma kuma ta iya yiwuwa koma waye ne ya dade yana shirinsa, wata dama kawai suke jira, kuma sai muka mika masu wannan damar jiya, da na gabatar da ke a matsayin matata. Don haka na ke so ki natsu ki yi tunani, tun fitowarmu jiya daga wurin taro, a ina ki ka bar wayarki da komfutarki? Domin ta imel na fi tunanin aka tura (virus) din.”
Ummu Adiyya kam kanta ya yi dumum, ba ta jin iska na shigar ta, hannu ta sa ta tallafo kanta da ya fara sarawa. Amma ni ba (programmer) bace, ta yaya za ayi ma na san…” Ki kwantar da hankalinki, babu wanda ya ce ke ce, kawai dai an yi amfani da
wayarki ce, wanda ba sai mai bincike ba, koma waye zai gane da gangan aka yi, tunda sun kare kansu sako-sako ne, yadda sun san programmers din da muke da su nan da nan za su gane hanyar. Sauko mu ci abinci, idan muka koma gida, sai ki yi tunani a natse.” “Ba ku buKatar ku duba wayar yanzu?” Charles ne kawai ya sani, na kuma fada masa zan kai masa da kaina, domin yana samun alamar nemansa (Trace), ni ya sanarwa lambar dakin da wayar take, nan ne na fahimci daga ofis dinku ne. Muna cikin wurin karbar wayar kwastamomi kuma na
tabbatar da cewa duka ‘yan ofis dinku suna can.
Saboda muna buKatar wayar kusa da Charles, Www.bankinhausanovels.com.ng
amma da na tambaye shi, ya nuna har lokacin na’urar tana ofishin. Lokacin na tambayi Baba Masinja ko ya ga wanda ya rage a ofis din (CE. Communication Engineering) shi ne ya fada min ke kadai kawai ya bari, don ya kai miki saKon ki.” Ita kam maimakon bayanan Zaid su warware mata kai, Kara kulle mata kan suka yi, don haka ta ce, “Mu shiga mu ci abinci, ina jin jiri.

***********

BABI NA ASHIRIN DA DAYA

Nan da nan fuskar Zaid ta takure cikin damuwa, “Kin tabbata ki na lafiya ko? (Are you alright?)” Kai ta gyada masa, “Kin yi fayau da yawa, mu je na kai ki gida.” “Lokacin ma ya Kare a nan ai, mu je kawai zan iya Karasawa ai.” Da gaske, ba inda za ki koma, bari na karbo miki abincin na maida ki gida, don Allah ki kwantar da hanakalinki, komai zai daidaita Inshaa-Allah.” Jinsa kawai ta yi tana gyada kai.
a cewar daga waje wani yana so ya kassara masu kasuwanci, ya kora masu
kwastamomi, amma ace a cikin ofis din mutumin yake, sannan ita aka zabi nata na’urar ko komfuta ko waya a saka, abinda za a saka, don a cuci kamfani, wannan ba Karamar magana bace.
Tana ta saKe-saKe da kwance-kwance, sai jin dawowarsa kawai ta yi cikin motar,
“Ba su sayar da cornflakes, sai dai ki yi haKuri da shinkafa.” Murmushi ta yi, ta san duk zolayarta yake yi, don ta sake. Ba yadda ba ta yi da shi
ba, amma ya ce gida za ta koma. Shi ya tafi da wayarta. Dole ta haKura. Bai bar
gidan ba sai da ta ci abincin, ya ce ta kwanta ta huta, kan la’asar shi zai koma ofis.
Yau ma sai da Issha’ ya shigo gidan, ya same ta cikin kyakkyawar shiga, tuni ya
mance da gajiyar da ya kwaso, haka dai ya cigaba da lallabata, don ya ga yadda
hankalinta ya tashi.
“An gama tsara komai yanzu kam, saura a gane wadanda suka aikata, saukin abin
muna da matakai na sauya takardu (Encryption Measures) zai kare yawancin
kwastamomi, damuwar ita ce, su wa ba zai kare ba? Za kuma mu gane su wa suka Www.bankinhausanovels.com.ng
yi, a hankali, sai dai zai dau lokaci, amma za a gane, Inshaa-Allah.”
Kai ta gyada masa, ta yi masa murmushi. Amma can cikin ranta ta san gagarumin aiki ne a gabansu.

***********

Washegari UmmAdiyya tana shiryawa, bayan ta yi wankan yamma ne, ta ji tsayuwar
motoci a harabar gidan, don haka ta Karasa shirinta da hijab dinta kan ta sauka,
tana isowa falon suna shigowa, wani ihu Umm Adiyya ta saka, ta yi kan Maami da
gudu ta rungumeta. “Kun ga min yarinya Za ta kada ni.”
Umm Adiyya ta rufe fuskarta tana ta dariya, “Maami shi ne ba ki ce min za ku zo ba?”
Sai kuma ganinta ya koma kan Abba, “Sannu da zuwa Abba, ku shigo ku zauna.”
Harara ta bankawa Faruk, “Kai Wallahi ba, shi ne ba za ka yi waya ka fada ba, bayan ka san kuna hanya.”
Ta rufe baki kenan, sai ga Fa’iz da Yaya Saadik, nade hanneyenta ta yi ta turbune
fuska, “Yaya SaadiK na yi babban fushi da kai, sai yau za ka zo?”
“Wai, wai, to ayi hakuri sarauniyar dirama, na sani ko ba ki gama darunki ba, na zo a hada da ni?”
Kulle fuska ta yi cikin jin kunya, sannan ta wuce kicin da sauri ta shiga hada masu
ababen tabawa, ba ta yi minti biyu a ciki ba, sai ga Zaid ya sameta a kicin din.
“Me ki ke hadiawa?” “Na gama yanzu zan fitar.”
“Bari na taya ki da wasu, ki na jin jirin za ki dauki wannan rusheshen tiren?” Ya fada hade da mata ‘yar hararar gefe. “Yi hakuri Malam, me ya yi zafi? Na gode, bare ma,
yau ina murna, duk abinda za ka yi min, ba zan bata raina ba.”
“Allah ko?” Tana dariya ta gyada masa kai. Ta dauki tire mai dauke da kayan tabe tabe ta nufi inda iyayenta da ‘yan-uwanta suke. Nan aka sake zaman sabon gaisuwa. “Ina Adda Zubaida?” “Yau sun fita ai ba su gida tun safe.” “Na zaci komawa ta yi ai, zan zo ai kan ta tafi Inshaa-Allah, za su kai Litinin ai ko?” Zamanki suke yi, da za su kai litinin din? Su fa gobe za su koma Inshaa-Allah.” Maami ta fada.
“Ah, Abba ka ga Adda Zubaida ko? Shi ne ko ta fada, daman an dade da min wariya a gidan nan.”
“To kun ga ta fara ko?” Faruk ne ya yi magana.
“Don Allah kai mana shiru, wa ya tambayeka? Allah yaron nan ka raina ni.” Kullum
sun fi fada da shi dama. Fa’iz shi shiru-shiru ne, bai da magana sam. Faruk ne har

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *