UMM ADIYYAH CHAPTER 27 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 27 BY AZIZA IDRIS GOMBE

               Www.bankinhausanovels.com.ng 



MUN TSAYA 

Tana dariya ta gyada masa kai. Ta dauki tire mai dauke da kayan tabe tabe ta nufi inda iyayenta da ‘yan-uwanta suke. Nan aka sake zaman sabon gaisuwa. “Ina Adda Zubaida?” “Yau sun fita ai ba su gida tun safe.” “Na zaci komawa ta yi ai, zan zo ai kan ta tafi Inshaa-Allah, za su kai Litinin ai ko?” Zamanki suke yi, da za su kai litinin din? Su fa gobe za su koma Inshaa-Allah.” Maami ta fada.
“Ah, Abba ka ga Adda Zubaida ko? Shi ne ko ta fada, daman an dade da min wariya a gidan nan.”
“To kun ga ta fara ko?” Faruk ne ya yi magana.
“Don Allah kai mana shiru, wa ya tambayeka? Allah yaron nan ka raina ni.” Kullum
sun fi fada da shi dama. Fa’iz shi shiru-shiru ne, bai da magana sam. Faruk ne har

ZAMU TASHI 

Asmau bai bari ba, idan ‘yan tsiyar nasa suka motsa, bare yana ganin sun fi Adiyya tsawo, sai dai duk da haka, idan lokacin ba ta girmanta ya yi, suna ba ta, don sun san Maami ba wasa. “Adda Ummu ki ka biyewa wannan, zai kai ki ya baroki. Ni dai cake dinki za ki Kunsa min na je da shi, tunda ki ka taho Maami, ta Ki ta yi mana.” Fa’iz ya fada. A‘a haba kai, ta yi abin ta, na taron baki kuma za ka jide mata ne?” Maami ta fada tana duban Fa’iz, amma a faKaice, kallon gidan take yi da kyau, ta ga yadda ‘yarta take kula da gidan ko kuwa ba ta kula. Abba yana gama wayar da yake yi, ya ce “To mun gaisheku, mu kam za mu wuce.” Haba, Abba ai ko numfashi ba ku mayar ba, na tafiya daga mota zuwa cikin gida, ku dan zauna mana?” Murmushi ne a fuskar Zaid. Maami dai tana ta leKawa tana kula da su biyun, ta ga ko za ta ga da matsala,

amma dai duk leKe leKenta ba ta hango alamar hakan ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ma kula da murmushin fuskokinsu ne, duk da dai Zaid cin kamar a gajiye yake. Amma dai tana tunanin ba wata matsala, ko zuwan yau din ma Abba ya Ki, wai zasu je su takurawa yara, ita dai ta ce ta fi so taje ta gani da idonta, ko komai ya daidaita. Duk da Zubaida da ta je gida ta fada mata komai lafiya, gani da ido aka ce yafi sako. “Abba to ai ba ku shiga kun ga wurin ba.” Zaid ya fada yana fara’a. “Ah shiga wani wuri kuma, sai ka ce mata? Ai mun ga wuri kam. Allah sanya alheri ya kade fitina.” “Ameen Ya Rabbi.”
“Sai ku dage da addu’o’i sosai, don yanzu wani Karin girma ne ya sameku, dukan ku biyun, sai kun yi taka-tsantsan, ku riKa hakuri kuma da juna, ku tsare dokokin Allah, shi kenan sai ku samu zaman lafiya.”
“Inshaa-Allah Abba, mun gode Allah ya Kara girma.”
Ummu Adiyya ce ta kwabe fuska za tayi masu kuka. Abba yace, “Oh, Mamana ke dai ki yi ta abu kamar yarinya, dole su Faruk suke damunki ashe.”
“To Abba ni kadai ce baza ka ga wurina ba, bayan ka ga wurin Adda Asma da ka je Kaduna? Mitin ku ke yi ne, da ki ka san na je gidan nata?” Tsuru-tsuru ta yi da idanu, don yawaicin lokuta taron kan waya (Conference Call) suke hadawa su uku matan,
wataran da Maami su yi dan Kuskus dinsu ba tare da su Abba da ‘yan mazan sun sani ba, ba tantama hakan aka yi amfani da shi wurin hada shirin aurenta da Yaya Zaid, sai aka wareta a cikin shirin. Da Umm Www.bankinhausanovels.com.ng Adiyya ta dage dai, sai da Abba da Maami suka shiga suka ga wuri. Abba dai ya kafe akan ba zai hau sama ba. TO menene? Ba Addu’a bace, kuma an yi? Ai ba sai na gani ba. Allah yayi maku albarka. Ya azurtaku duniya da lahira. Ya kuma raba ku da duk wani sharri.” Dukansu suka amsa da ameen, har da ‘yan rakiyar ganin gida. Sai kin zo bikin Yaya Saadik, yanzu kam ke da gida.” Faruk ya fada cikin zolaya,
yana nuna mata, ita kam ta bar gida yanzu kam.
“Maami me ya sa ake min wariya ne, yaushe kuma aka sa bikin Yaya Saadik?’ “Rabu da shirirtar Faruk fa, yau da safe ne aka tsayar, nan da sati shida Inshaa
Alalh.” To Allah ya nuna mana. ya sa ayi lafiya. Yaya Saadik, zuwa Gombe ya kama mu za ka ce.”
Zaid ne ya yi gyarar murya, duka aka sa dariya. “To kin ji yana wurin ma ba ki masa magana ba, ke kuwa gandoki har kin fara shirin tafiya.” Maami ta fada suna dariya, suka raka su har waje.
Ganin motoci biyu, Faruk, Fa’iz da Yaya Saadik sun shiga guda daya, sai Abba da Maami kuma a guda daya, ta harde a gefen mijinta abin ta.
Umm Adiyya ta ce, “Haba na yi ta tunanin yadda ku ka taho, ashe tafiyar ta Hajiya da Alhaji aka yi.”
Abba murmushi ya yi, ya kada kai. Maami ko ta ja kunnenta, kan ta shiga motar “Kaji min yarinya dai, ku kadai ne ku ka iya yawon gaban motar aka ce miki?” Ta fada a hankali, saboda kunnen Zaid wanda yake can bangarensu Saadik, suna sallama. Dariya Umm Adiyya ta yi, lokacin da Zaid ya koma gefenta ya tsaya, suna daga masu hannu har suka fita. A hankali ya je kusa da ita daidai kunnenta ya ce, “Yau
cry-cry ba za ta yi kuka bane?”
“Yaya Zaid! Sai aka ce maka kuma na zamo famfo mai tsiyayar hawaye? Me zai sa na yi kuka?” “Abin da ya sa ki ka yi ta yi randa aka kawo min ke gidana.” Bude baki ta yi ta kasa rufewa. Yana dariya ya juya ya yi cikin gida. Ta bi shi a baya, da sauri, “Ka daina min haka da gaske, don ka ga ina kula ka ko? Zan shareka ne ai. Ba ruwana da kai kuma.”
Juyowa ya yi bayan ta shigo, ita kuwa ta tsaya cak! Yadda ba za su yi karo ba, taku daya ya Kara ta koma baya, ya Kara daya, ta Kara matsawa baya, idanunta sun yi fiki-fiki. A hankali ya duka daf da fuskarta. Sai da ta ji fitar numfashinta ya canza
sauti, amma murmushi tayi masa a hankali, sannan ta ce, “Hankali dai ga can Innayo.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya Salaam! Shaf ya manta yanzu ba su kadai bane a gidan, tun jiya da dare, bayan ya taso aiki ya wuce gidan Maami ya taho da ‘yar dattijuwar da za ta taya Umm Adiyya zama da wasu aikace-aikacen.
Gaskiya za a takura masa da yawa. Yana juyawa. Umm Adiyya ta tsere daga wurin, ta haura sama da bunjumemen hijabinta. Ganin bai ga kowa ba, ya sa ya shafa kansa yana murmushi hade da kada kai. Bai
yi wata-wata ba, ya bi bayanta, murda makullin Kofar da yake yi ne, bayan ya shigo dakin, ya sa Umm Adiiyya ta shiga raba idanu. “Wai ke nan, wayo ko? Yanzu wa na ritsa a nan?’ Ka yi hakuri, na tuba ba zan sake ba.” “Ba za ki sake me ba?”
“Tsokana.” Ta fada tana kallon yadda yake takowa a hankali. “Na ji na haKura, amma Zo nan.” “To ai ka hakura, sai ka fita ai.” Lalle ma yarinyar nan, ki zo na ce miki.” Ya fada har da hada gira, shi a dole ya
tsume. Allah na fi son daya Yaya Zaid din, kai ka na da fada” Daure fuska ya yi kamar da gaske, “Oh ashe biyu gareki. Yaya Zaid din, zo ki fada min, me wancan yake miki, ki ka fi sonsa?” Ya fadi
a lokacin da ya riko hannayenta cikin nasa. “Har ma a gabana za ki fada ko?” Tana dariya mara KakKautawa ta ce, “To ai shi ya fi kirki, baida fada sai lallashi, da magana a hankali, da taushin lafazi. Kuma…” “Kuma me?” “Kuma baya matsa min kamar kai.” “Hmm, I will like to meet him, ina zaune zai min Kwacen mata.” Hannu ya sa a bayanta ya riKota zuwa jikin sa, ba shiri ta riko kafatunsa cikin zuKan
wani numfashi, “Da gaske idan ka so kai ma za ka zama shi, na tuba ba zan sakeba.”
“Ga ki ‘yar kucila, sai tsokana da tsoron tsiya. By the way, sake fada na ji?””Me din kuma?”
“Abinda ki ka ce akan daya Yaya Zaid din.” “Ya fi kirki…A’a.” “Na fi son daya Yaya Zaid din.” Ta nanata a hankali. Goshinsu ya hada, ya sa hancinsa yana shafar nata hancin, tuni ta fara jin
wadannan Kananan zut-zut din suna yi a cikin jininta da jikinta, wayyo ita. Yaya Zaid zai Karasata. “Me ki ke jira?” Ya fada Kasa-Kasa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Na’am?” Ta numfasa a sanyaye, idanunta a lumshe ba ta ko iya bude su, saboda yanayin da ta ke ciki.
“Na san ki na so, go ahead, ba abinda zance miki.”
“Uhm-Uhm na Ki.” Ta fada hade da make kafadarta. Hannunsa ta ji a wuyanta ya Kara riKota da kyau. “Yaya Zaid…” “Just do it.” Yau ta ga ta kanta. Tunani ta shiga yi, ta yadda za ta zille masa, amma ta kasa tuno komai, don haka ta yi sauri ta yi abinda yake so, ta yi yunKurin matsawa baya. Amma ta ji ta cikin riKonsa Kam! Har yanzu. Ina! Yarinya da gaske darasina ya fi Karfin wannan.” Lokacin ne ya idasa nufinsa, yayi mata kyakkyawar riko, ya sumbaceta kamar ba gobe, “Gobe idan na tambayeki,
irin haka za ki yi, ba kamar wasan yara ba.”
Ba shiri ta hau girgiza masa kai, ita dai burinta ya bar ta, ta sarara.Na bar abu a wuta.”
“Cabdijan! Meye amfanin wanda ki ka kawo, ta katse min hanzarina kenan, ba inda za kije. Ta duba miki girkin.” “Yau na bani.” “Tukun na dai, yanzu za ki fara. Sake fada na ji?” “Na fi son daya Yaya Zaid din.” Ta Kara maimaitawa. Tana dariya. Ya shiga nuna mata wani salon daban kuma. Fada da kyau yadda ya dace, tamkar daya Yaya Zaid din ne a gabanki.”Ana behabbak Kathiran. (Ina sonka sosai)” Lumshe idanunsa ya yi, lokacin da ya ji
duk duniya ba wanda ya kai shi farin-ciki a daidai wannan lokacin. Alhamdulillahi, Twinkle. Allah Ya bar min ke. Allah ya bar min ke.” Irin riKon da yayi mata, tamkar zai mayar da ita cikin jikin sa ne, ya sa ta san irin shauKin da yake ciki. A wannan lokacin mancewa ta yi ita ma da dukkan wasu matsalolin da suke fuskanta. Ba abin da take ji, sai mijinta, abin sonta.

******

Amma dai za mu kwana ko?”
“Ke dai ki yi shiri, ban san yadda za ta kasance ba. Idan mun gama yau, za mu juyo.” Don Allah ka bar ni na kwana? Na yi kewar Adda Asma’, kuma na san idan mun hadu, ba za ta bar ni na yi bacci ba, ka santa da surutu da labarai. Na kwana dai irin dayan nan ko biyu haka, tunda ka ga Litinin ma Easter ne babu aiki.” Tana ganin kallon da yayi mata, ta shiga taitayinta, tuni ta langabe fuska, ta san ba Www.bankinhausanovels.com.ng
zai taba yarda ba. “Ka yi hakuri mana?” Dariya ya yi ya ce, “Ba wanda ya kai ki iya bada cin hanci, wannan idanun naki sun iya sawa ayi miki yadda ki ke so, kwana daya kacal amma! Ina ki ke so na shiga.
Idan ki ka kwana biyu nesa da ni? Za ki sa mutane su bude Kofar Extra daki kenan, Kaura zan yi.”
Dariya take yi ta ce, “Haba dai Kaura.” To shi kenan, kin dauka wasa ne ko?” Tuni ta shiga taitayinta, “A’a na isa? Na gode.” Sai kuma ta ce. “Yayyy.” Ta fada tana murna har da dan rawarta. Shi kuwa ya
shiririce cikin kallonta, yana jin wani sonta na Kara shigarsa, tana nan ‘yar dagwas da ita tamkar ya boye abarsa.

***********

Tun isarsu take Allah-Allah su isa gidan Adda Asma, amma Sai gidan wani abokinsa ya fara kai ta, suka gaisa tukuna, sannan suka wuce gidan Asman da ke (Gwamna Road).
Cikin murna sosai Asma’ ta tari Umm Adiyya. “Adda Asma’ za ki kada ni.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *