UMM ADIYYAH CHAPTER 28 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 28 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

ban san yadda za ta kasance ba. Idan mun gama yau, za mu juyo.” Don Allah ka bar ni na kwana? Na yi kewar Adda Asma’, kuma na san idan mun hadu, ba za ta bar ni na yi bacci ba, ka santa da surutu da labarai. Na kwana dai irin dayan

nan ko biyu haka, tunda ka ga Litinin ma Easter ne babu aiki.” Tana ganin kallon da yayi mata, ta shiga taitayinta, tuni ta langabe fuska, ta san ba Www.bankinhausanovels.com.ng
zai taba yarda ba. “Ka yi hakuri mana?” Dariya ya yi ya ce, “Ba wanda ya kai ki iya bada cin hanci, wannan idanun naki sun iya sawa ayi miki yadda ki ke so, kwana daya kacal amma! Ina ki ke so na shiga.
Idan ki ka kwana biyu nesa da ni? Za ki sa mutane su bude Kofar Extra daki kenan, Kaura zan yi.”
Dariya take yi ta ce, “Haba dai Kaura.” To shi kenan, kin dauka wasa ne ko?” Tuni ta shiga taitayinta, “A’a na isa? Na gode.” Sai kuma ta ce. “Yayyy.” Ta fada tana murna har da dan rawarta. Shi kuwa ya
shiririce cikin kallonta, yana jin wani sonta na Kara shigarsa, tana nan ‘yar dagwas da ita tamkar ya boye abarsa.

***********

Tun isarsu take Allah-Allah su isa gidan Adda Asma, amma Sai gidan wani abokinsa ya fara kai ta, suka gaisa tukuna, sannan suka wuce gidan Asman da ke (Gwamna Road).
Cikin murna sosai Asma’ ta tari Umm Adiyya. “Adda Asma’ za ki kada ni.

ZAMU TASHI 

“Allah kadai ya san inda ku ka tsaya tuntuni, kun barni da kallon Kofa. Yaya su Maami? Shi ne ko tabi ku, ku zo tare ko?” Lallai ma kin san Maami wane zuwa za ta yi ba dalili?” Uhum, kar ta damu za a sa ma mata dalili. Ina zuwa, zauna bari na je na kaiwa
Yaya Zaid ruwa, idan sun hadu da Zunnurain, ba su jin kamar su rabu. Nan ya barta ta yi la’asar, shi
kuma da Zunnurain suka wuce ofis dinsu na Kadunan,
inda za su tabbatar da cikakken tsaron da suka gindaya bai dawo ba. Sai can kusan magariba ya dauketa zuwa gidan Baffa Mai Kano. Gaba daya wani iri take ji. Musamman idan ta tuno su Mama suna sane da duk artabun da aka sha a kanta, dangane da aurenta da Zaid, amma ba yadda ta iya, ko yau ko gobe, dole su hadu. Kyakkyawar tarba suka samu a gidan Baffa Mai Kano. Umm Adiyya dai dole ta

Www.bankinhausanovels.com.ng
zamo kurman dole, sai murmushi kawai da sunne kai. Maman Fatima ko ‘yar ba ruwa na, Sai cewa ta yi.
“Ikon Allah, yau dai ga Malam ga Ummunsa, tamkar ba za mu ji Karshen zancen ba, na tabbata Kaduna ta dawo masa tamkar unguwa, duk don Ummunsa. To da fatan kana kula min da ‘yata, ba wai ka matsa ba ka je ka yi ta yi mata irin halin nan da ku ka tsiri yi.”
Zaid dariya ya yi yana sunne kai, “Mama ana KoKartawa.” To ya yi kyau.” Ta fada cike da fara’a. “Mun sameku lafiya?” ‘Lafiya lau Alhadulillahi, dazu Fati take ce min sun yi waya da Ummun ku na hanya,
muka yi ta zuba idanu shiru, ba ta samu wayarku ba.”
“Asma’ ce ta rike mu can wurinta, amma Umm Adiyya tana nan har gobe, nan zata maku hira.”
“To ya yi ai. Baban naku ma yanzu ya shigo gida, bari na duba shi, sai ku gaisa. Ina labarin su Zubaida kuma Ummu?” “Lafiyansu lau Mama.” Can falon Baffa MaiKanon suka shiga, suka gaisa, nasiha ya masu mai shiga jiki, ya hada da saka albarka. Na ji dadin ganinku Kwarai, zumunci ai yana da dadi, idan ka na da rai da lafiya ne, ka ke yinsa, randa babu kai, ai komai ya Kare.” “Haka ne Baffa. Mun gode sosai.”
Falon Maman suka koma, ba a dade ba, da shigowarsu kuwa, sai ga Fatima ta dawo daga gidan yarta da ke Unguwar Dosa, nan kuwa aka shiga yiwa Umm Adiyya
tsiya. Zaid kam miKewa ya yi ya bar su, ya ce zai dawo can anjima. Anjiman bai dade ba, domin tara na dare, sai ga wayarsa. “Ga-ni, sai ki shirya mu tafi.”
“Yaya Zaid, Mama ta ce na kwana kawai da safe sai mu Karasa zagayen da bamu yin ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Shi ne ki ka bari saida na taho tukun ki ke gaya min? Ai tunda na zo, sai dai ki fito, yaya za ki yi da Asma’ da ki ka bari tana jiranki?” “Ina zuwa.” Ta fada hade da kashe wayar. Murmushi ta yi ta dau jakarta, ganin idon su Azeema da Fatima ba ta son yin maganar a gabansu, wannan ya sa ta kashe
wayar. “Bari na kai masa Charger dinnsa.”
Uhm-Uhm dai Ummu A. fadi gaskiya, wannan kashe murya haka, duk kin gama birkita mana Yayanmu, za ki wani noke da Charger, idan sai da safe ne, ki fada, mu cewa Mama abu ne ya taso ki ka wuce.” Zare idanu Umm Adiyya ta yi. “Ba ki da kunya yarinyar nan, don kuma ni na fi kowa rashin ta ido, sai na wuce ba sallama? Yanzu zan shigo. Kuma ke ma za ki yi auren nan dai, muna nan za kuma mu rama.” Suna dariyarta, ta fita a falon zuwa Kofar gida, inda ta samu Zaid ya yi nisa wurin tabe-taben wayarsa.
Gefensa ta tsaya a jikin window, shi kuwa ya
ki budewa, don haka ta Kwankwasa,
ko ya dago ya dubeta bare ya ce wani abu, zagayawa ta yi ta bude Kofar ta bar taa bude.
“Yaya Zaid, please, yaya zan ce da Mama zan tafi? Cewa ta yi na kwana anan fa. Adda Asman sai na je mata gobe.”Ba tare da ya ce mata komai ba, ya fita, ya bude boot din motar ya fitar da dan
karamin akwatinta, kasancewar dama ba ta sauke kayanta ba. Malam Iliya Mai-gadi ya bawa jakar, ya ce ya shiga mata da ita ciki. Ita dai kallo daya tayi masa, ta san ba har zuci bane ya amince da zaman nata. To meye a cikin gun barci? Idan da mai tada Kura ma dai Adda Asma’ ce, da ta ce za ta zo mata. “Sai da safe.” Yau ta ga bone, tsakaninsa da Allah fushi ya yi. “Don Allah kar ranka ya Baci, idan
ka na so, ka shigo ka fadawa Maman Fatiman. “Umm Adiyya, sai da safe.” Ya fada hade da shiga motar ya tada ita. Yau kuma Umm Adiyya take. Wani abin sai Yaya Zaid, murmushin dole kawai ta yi, “Allah
tashe mu lafiya.” Ta ba shi amsa. Jiki a sanyaye ta koma cikin gidan, wayar Adda Asma’ ce ta cireta a tunaninta. “Kuma sai na ji ki shiru.” Maman Fatima ce ta riKeni, da sassafe zan zo miki In shaa-Allah, tunda ina nan ki yi haKuri don Allah.” “Tafdi! Ai ba ki isa ba, ki ka sa na tiki aiki.” Yaya Zaid zai zo, ki ba shi duk abinda ki ka yi, zai kawo min.” An ki a bayar din, daga can ku wuce idan kuka ga dama, kin gama sawa na tsara mana komai, sannan za ki wani ce…” “Ki yi hakuri don Allah.” Karfe takwas.” Takwas? Yaushe suka tashi, da zan masu bankwana takwas.”
“Oho, kan ki kwanta da dare, ki ce masu sammako za kiyi.” “Ban san wanda ya fi kafiya ba da naci tsakanin ke da Yaya Zaid, shi har ma ya fi ki fushi.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ehm-Ehm.” Adda Asma’ ta gyara muryarta hafe da yin tari. “Ki gama dai duka, sai da safe, ina tsakar gidan mutane, kin tsayar da ni kamar wata marar gaskiya.” Allah tashe mu. Da gaske da kaina zan zo, ki ka wuce takwas.” “Ki kira dan-uwanki don yadda ya bar nan, ban yi tsammanin zan gan shi nan da kwana biyu ba.” “Ahaf kamar da gaske.””

**********

Da alama hasashenta ne zai yi aiki, domin kuwa ko saKon Zaid babu a wayarta, har suka shiga barci, don haka ita ta tsara nata sakon ta tura masa.
“Yayana ka yi min sassauci, ka karbi ban hakurina. Allah kuma ya huci zuciyarka. Sam ban yi niyyar hakan ba.” Bayan mintuna da yawa, babu amsarsa, ta sake tura masa wani saKon, “Da gaske
na kasa barci, ban ji amsarka ba. Sorry, na ma rike kunnena kuma da zafi har Kwalla sai da na yi.”
Minti guda ya yi yawa, sai ga wayarsa, ko gama Kara ba ta yi ba, ta daga. A shagwafe ta amsa da gasken ta yi hawaye, don rabon da ta gan shi a tsume, tun
kan su shirya, sai dai wani dalilin ya kawo masa haka, ba ita ba. “Adiyya, kiyi bacci. Ni ban yi fushi da ke ba.” “Allah? To me ya sa kaki Kirana?” “Babu komai.”
Kara tsumewa ta yi tamkar tana gabansa, “Eh amma…” “Amma me?” Ba zan iya fada ba yanzu.” Ta rage murya, gaba daya tamkar tana gudun kar a
ritsata. Ba Karamar dariya ta bawa Zaid ba.”Twinkle dina yi barci abin ki, ba abinda ki ke sa ran Zaid, sai farin-ciki da annashuwa. Idan kuma ki ka ci-gaba da min magana da wannan muryar ta ki, yanzu zan zo na tafi da ke daga gidan Maman. Saboda haka ki kwanta ki yi barci, ina zuwa
da safe Inshaa-Allah.” “Ba da sassafe ba dai ko?”
“Abinda ki ka ji kawai a maganar tawa kenan?”
“Na ji duka, na gode, sai da safe.” Ya Allah! Twinkle I miss you already.” Wani yawu ne ya shige mata wuya, ba shiri, ta hau tari. Sai da ya gama mata sannu, sannan ya ce, “Kin faye tsoro, wannan na yau ne kawai, idan ki ka kai gobe kam, sai yaya kenan?”
“Yaya Zaid!” Ba shiri ta katse wayar, tana ta murmushi ita kadai, burinta dai ya huce kuma ya sauko daga guntun fushinsa. Washegari da la’asar suka bar Kaduna suka dauki hanya. Wannan satin kaf aiki tukuru suka sa a gaba, don Kara inganta matakan tsaronsu, sannan aiki ya ci-gaba
da gudana kamar da, a bangare guda kuma ana ci-gaba da gudanar da bincike Kasa-Kasa, saboda sun san koma waye ne, yanzu lafawa zai yi, da duk wasu
abubuwan da suka san zai janyo hankulansu garesu.

BABI NA ASHIRIN DA BIYU

Zuwa lokacin bikin Saadik da Saudat, ba wanda zai ga Zaid da Umm Adiyya ya ce a wani ģaba a wani kuma lokacin suka taba alKawarin shaKe juna. Tsabar yadda yake ririta ta, ita kuma take ba shi dukan kulawa. A cikin ribibi ma da hatsaniyar bikin a Gombe, lokaci take sama masa, tunda ya yi Korafin ta share shi wuni guda ko ta neme shi. Ganin suna ta harKalla irin ta abokan ango ne, ya sa Umm Adiyya ta diririce gaba daya, motsi kadan ta yi tsaki. Har dai Asma’ da su Maryam da suke dakin suka fara mata tsiya, amma ba ta tanka masu ba, har sai da suka rage ita da Www.bankinhausanovels.com.ng Asmaa a dakin yar-uwarta, ta sake dauko maganar.
“Meye ki ke ta wani abin nan, aka ce miki wannan mijin naki yana da sukunin kallon wasu bayan ke ne?”
“A dai bar zancen Adda Asma’, amma maza kuma ina ruwansu. Ni sam ban son wannan sha’anin abokan angon na ke yi ba, daga nan wata ta liKewa mijin mutum.Dariya sosai Asma ta yi, “Ikon Allah. Su mijin mutum manya. Ummu A. Ki na sha’aninki Wallahi. Wai ina Adiyyar da ta yi birgima a falon Abba ne?”
“Adda Asma’ dadina da ke Wallahi kin faye tone-tone, duk a cikin so ne.” Ta fada tana juya idanunta.
“Na ko ga alama. Wallahi Yaya Zaid ya gama bude miki idanu.” Ta fada tana gutsuran gwaibar ta.
“Wai ni meye ne haka, tun dazu gwaiba daya kin kasa gama cinyewa, sai gutsura kike yi kadan-kadan?”
“Za ki yi bayani ne kwanan nan, ki cire idanunki akan gwaibata.” Umm Adiyya ta dubi ‘yar-uwarta ta kwashe da dariya. “Oho! Yayyy.” Zuwa ta yi ta
rungume Asma’ cikin murna, “Iye-Iye, haba dai ni ma nace. Uhm-Uhm! To Allah ya raba lafiya.”
“Saura naki mu ga me za ki ci, ki na min dariya.”
“Ah ni kam tukuna dai. “Yar Karama ta da ni? Yaushe na kula da kaina bare wani baby?”
Harara Asma’ ta banka mata, ta ja tsaki. “Mtsww! Sallama zai miki? Me za ki tsaya jira?” “Da gaske fa, ni tsoro ma na ke ji. Yadda na ga Adda Zubaida ta sha wuyar nan.”
“Ke ma kin san wannan wajibi ne, ki cire a ranki, ko wace mace sai ta fuskanci hakan, don haka idan za ki cire tsoro ma a ranki, gara ki cire, ki yi ki gama da wuri.” Murmushi kawai ta yiwa Adda Asma, ba tare da ta Kara fada mata komai ba.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *