UMM ADIYYAH CHAPTER 30 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 30 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Oya mu je mu rama wannan barcin da na katse, amma dai kafin nan, ina jin yunwa.” “Lah, an ce fa ba kyau barci, ana gama cin abinci.” Ba zan iya barci kuma da yunwa ba, ko kunu ne ki ba ni.” “Abincin ma zan ba ka, me ya yi zafi, tunda akwai, an dafa ba babu ba?” Tare suka koma Kasa, inda ta hada masa Tea, ta sako masa abinci marar yawa, suka zauna, ya gama ci. Ita kuma ta taya shi shan Tea din.
Tana gamawa ta mike da gudu sai bandakin cikin falonsa, bin bayanta ya yi don ya
tsorata, gefenta ya tsaya yana mata sannu. Sai da ta wanke fuska, ta fito ya ce, “Me na fada miki?’
“Ba wanin nan madarar ce kawai ina ga da na sa, ba na hada ganyen shayi da madara, dama yau kuma na saka.” “Eh irin ke za ki yi kwadayinku na masu ciki ko?” Wai kai ba ka jin nauyi ne? Ka yi shiru mana.” Ta fada cikin turbune fuska a shagwabe. “Allah ya kai mu gobe.” Ya fada yana mata
dariya.

ZAMU TASHI 

Ga shi yanzu ta fito daga bandakin tana dubansa, shi ma kallonta yake yi yana jiran amsarta, kai ta gyada masa, kanta a Kasa tana murmushi, ba ta yi aune ba, ta ji ya sunkumeta gaba daya ya hau juya ta a dakin. Jin ta yi Kara ne ya sa ya yi saurin ajiyeta. Da gaske zan fara dri ni ma ko zan yi nauyi a daina min hajijiya.” Fuskarta ya bi yana barbadd mata Kananan sumba. “Yaya Zaid, wannan fa ba
kullum yake aiki ba.” Mu je to asibitin, na san duk daya ne ma.” Ba yadda ta iya haka ta bi shi, bini-bini har gaban likita.
Ita kanta Umm Adiyya gimtse dariyarta take yi, lokacin da likitar ta natsu tana dubansu, da gani ta saba ganin ire-iren wannan da ma wanda suka fi hakan, don haka ita ba ta damu ba, sai ma murmushi da ta yi, bayan Zaid ya ce, “Doctor, ga tanan na kawo ta, tana tsammani ne, amma dai a sake tabbatarwa, ayi mata kuma duk abinda ake yiwa masu ciki, a fada mata duk dokokin, don ta kiyaye, uhmm sannan…” ganin kallon da duka suke masa ne, ya ce, “Bari dai na fita na bar ki, ki yi

aikinki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Dariya Likitar ta yi ta ce, “Ba sai ka fita ba, za mu rubuta mata gwaje-gwaje yanzu, sai ta shiga (Lab) dinmu nan a debi jini da fitsari. Tana magana tana rubutu. Wani dadin da Umm Adiyya ba ta taba tsammanin za ta ji ba, idan ta samu wannan labarin, shi yake ratsata, har take ji kamar a sarari take tafiya. Zaid ko ya Ki barin ganganta ko na dakika daya ne.

*********

Barinsu asibiti da sati, komai ya gani na babies, saya yake yi ya kawo gida. “Ashe
kudinka za su Kare kan ayi haihuwar a cikin sati ukun ake wannan bidirin?” Murmushi ya yi ya riKota jikin sa, ya ce, “Adiyyata, babynki ne fa, dole na yi doki,
ke… zuri’ata za ta fito daga ke. Idan ban yi farin-ciki da zumudii ba, me ki ke so na yi?
Don haka ki zuba idanu kawai, ki sha kallo, and let me spoil you both.” Hannu ta sa ta rungume shi tsab! Idanunta a lumshe hade da yin ajiyar zuci. “Yaya
Zaid ban san kalmar da zan gode maka ba. Amma ina son ka sani har abada matsayinka ba zai ragu ba a zuciyata. Allah ya hadamu a aljannarsa, ya azurta mu da lafiya da hakuri da juna. Ya kuma ba mu ikon kiyaye dokokin sa.” Amin, Twinkle.”
Bayan ta sake shi ne, ya dubeta ya ce, “Yawwa saura batun suna.” Hande min boni. Yaya Zaid! Sai an kusa haihuwa ake zaben suna ai.” A’a mu fara shawara daga yanzu dai zai fi ko?” Dariya ta yi kawai, tana kada kanta.

*********

“Oh Adiyyah, ki na da kafiya.” Don Allah dai Yaya Zaid, ka ga ya dace ace Maryam guda dai, ba na nan, ai bai dace ba, ka san yadda muke da ita.” Ni gaskiya tafiyar da tsawo, kuma kin ga hanyar nan duk sai ki bi ku wahala. Yadda za a cikar nanma wa zai gane ba kya wurin?” Ta kasa amincewa balle yarda da batunsa. Koda ta mayarwa Maami yadda suka yi, sai cewa ta yi, “To ki haKura mana tunda yaki, kar hakan ya janyo wata matsalar kuma.” Maami fa wannan ne aure na farko da za ayi a cikin gidan tun bayan Www.bankinhausanovels.com.ng bikinmu, kuma a dakin Mama, ai bai dace ace ni ba na nan ba ko? Kawai haKurin dai zai yi na je. Ko flight, ba sai na bi ba”. To shi kenan, ki gwada masa maganar, amma idan ya dage, kar ki ja, komai ayi shi
cikin lumana, ai zama lafiya, ya fi zama dan Sarki.”
Ita dai tana jin Maami ne kawai, ba ta san wani
irin sabon iko bane hakan, lafiyarta
garau kuma ace ayi abinda zai janyo magana? Koda yake idan kuma ya Kin ba yadda ta iya. tunda shi ne sama da ita, kuma zamansa take yi, ba zaman kowa ba. Kwantar da kai ta yi ta gama tsara yadda za ta kawo masa maganar har ma ya amince.

**********

Tashinta ranar da safe, ba ta gan shi a akin ba, don haka ta yi tunanin ko wanka ya shiga? Ita ma ta wuce dakinta don ta shirya. Ta gama kimtsa ko ina, sannan ta koma Dakin nasa, baya bandaki, baya dakin, haka da ta sauka Kasa ma. To abin da ban
mamaki, don dai duk inda zai je, ya kan fada mata kafin ya fita. Innayo ta samu a kicen tana sa ruwan zafi a filas. Ina kwana Hajja Innayo?” Da yake hakan take kiranta wata rana. “Lafiya Hajiya, kin tashi lafiya?” “Alhamdulillahi. Yaya ya fita ne?”
“Eh, ya shigo ya dau abu a nan, sannan ya fice.
Okay. To zan dawo da wuri yau, ki bar abincin rana, sai na Zo nayi mana.” Bude kwanon abincin ta yi, ta ga Sinasir da farfesun naman rago, da ya yi luguf! A daya kwanon, tuni ta ji bakinta ya kawo ruwa. “Sannu da aiki, na gode.” “Ba komai Hajiya.”
Zama ta yi a wurin, tana cin abincin, tana neman layin Zaid, ta san duk yadda aka yi akwai abu a Kasa tsakaninsu. Amma sai Voice-mail wayar ta sa take shiga. Duk yadda take sha’awar cin abincin, ta kasa Karasa ci, haka ta kwashi warmers din ta saka a mota ta fita, wuri daya take tunanin shigewa, amma tana shiga ofis, don sa hannu da ajiye jakarta ta samu Oga Akim, ya hadata da wani aikin. Ta san abubuwa sun yi yawa a wannan Satuttukan. Saboda sabbin ayyukan da suka samu, bayan kuma na cikin kamfanin karan kansa. Ta dauki tsawon awa biyu Www.bankinhausanovels.com.ng tana aikin, da ta kammala ne, ta dauki na’urar ta zille ganin Oga Akimu baya nan. Tana tafe tana tunanin me ya fitar da Yaya Zaid da sassafe ba sallama ne, ta dago kanta kamar wacce aka ce ta dago, take a lokacin murmushin fuskarta ya dauke
cak! Numfashinta ya tsaya a maKoshinta, yaya za ayi ta mance wannan fuskar? Ko dai ranar ba ta ganta bane, har ta gane ta, ko kuwa tsagerancinta ya kai ta wuce Umm Adiyya ba tare da ta tanka mata ba, alhali tana sane sarai da ko ita wace ce. A sanyaye ta tura Kofar shiga Karamin falon, ofishin Zaid, inda ta tarar da Stella tana kwashe wasu takardu daga Printer. Murmushi ta mata kawai ba ta ja gaisuwar ba, ta fada cikin Ofishin Zaid. Nan ta same shi dukufe kan komfuta. Da alama ya yi zurfi kan nazarin abinda yake dubawa, ko kuwa ya yi kamar bai san ta shigo ba. Ba tantama, don ya tattara bayanan da zai yi mata. “Assalamu-Alaikum.” Ta fadia cikin murmushi, dauriyarta na yau ba kama hannun
yaro, ba za ma ta bari ya san ta ganta ba, bare har ya samu ganin bacin ranta. “Wa alaikumul-Salam, Twinkle.”Aiki ya kawoni, don’t Twinkle me.” Ta fada tana murmushi, amma hakikanin gaskiya kallonsa kawai take yi. Dai-dai lokacin da ya juya kujerarsa mai taya, ta yi gaba kadan zuwa inda take tsaye, a gefen faffadar teburin ofishin nasa. Hannu ya
sa ya riKo hannayenta. Manyan idanunsa da suka fara lumshewa, ba tantama saboda rashin isasshen barci ko gajiya ko wani abin suka sauka a kanta tarr!
“Ko a wurin aiki ko a gida ko a dawa, you will always be my Twinkle, saboda haka kar ki nemi ma ki canza, ba zai yi aiki ba.” Zagayeta ya yi da hannayensa, ya Kara matso da ita kusa da shi. “Fada min, me ya faru?” Wani abu ta hadiya, a take ta fasa tambayarsa dalilin fitarsa ba sallama yau, sai
cewa ta yi, “In dai ka na son ka fahimci me na zo da shi ne, za ka buKaci ka koma daga gefe, ni ma kuma na zauna, kar na fadi ban isar da sakon ba… Game da sabon taswirar (design) nan ne.” Ta fada. Www.bankinhausanovels.com.ng
Goshinsa ne ya tattare cikin tunani, “Ina Akim?”
“Baya Ofis, kuma ina so na ci-gaba da aiki, ba na son yi ba daidai ba. Oga Musa kuma yau ya tafi Jigawa. Saboda haka ne na taho wurinka.” Kawai?” Ya fada idanunsa a lumshe, kansa ya kwantar a kan cikinta.
“Allah Yaya Zaid, this is so unethical. (Hakan bai dace ba).” To Sarkin aiki, zauna ki nuna min. Kar ki yi zaton kuma na manta.” Murmushi ya yi, sannan yayi mata nuni da ta zauna a kan kujerar zaman baKi, ba
don ya gaji da riKeta ba, ko kallonta. YaKe tayi masa, sannan da sauri ta matsa baya, don ba yadda za ayi ta nuna masa abinda yake yi, ya shafe ta, ba ta ji sukunin ba shi amsa, ba bare ta fada masa abinda ta ji ba. Kujera ta samu ta bude masa Komfutarta tana masa bayanin sabon (Network Layout) dun da suka yi. Kin yi kyau yau.” Ya fada a tsakiyar batunta, bayan ta dan tsaya domin numfasawa. Idanunta ta dago, ta dube shi, kumatunta ya loba lokacin da take KoKarin yin
murmushi. Jilbaab ne a jikinta, mai launin jinin kare, ya sake fiddo kyawun fatarta da haskenta sosai, ta hada shi da koren gyale mai duhun Kasan teku (Teal). “Na gode, ba ka ce komai ba, game da design din?
“Charles zai duba, sai ku saka sauran ababen da suka dace, idan Mr. Akim din ya dawo ki ce ina son yin magana da shi, ina son na san inda aka tsaya a batun (Farraz Groups) din nan, babban aiki ne yana da muhimmanci, ba na son a tsaya sanyi akai.”
“Shi kenan.” Ta mike za ta fita daga ofis din, ya dan ware idanu. Da gaske fita za ki yi? Yau ko gaisawa ba a bari na yi da baby ba.” Sai ka koma gida Sir, by the way, nice Perfume. Shi ne ko a kawo min nawa ko?” Ta fada hade da bude Kofar ofis din, ta bar Zaid zaune shiru cikin tunani. Me ya faru yanzu?

BABI NA ASHIRIN DA UKU

Tunda ta dawo tana kan Kafafunta, cikin hada kayan tafiyarsu. Ita da Maami za su wuce a safiyar washegari, wanda ta kama ranar Juma’a ce, jirgi za su bi saboda su samu abubuwan da za ayi a goben, da yake ba wani dogon lokaci za a dauka ba na
bikin Maryam din. Sannan wannan ne kawai hanyar da Yaya Zaid ya amince ta bi, idan har tana son zuwa bikin. A cewarsa kar a wahalar masa da baby.
Asabar za a daura aure, ayi budan kai a kuma watse a ranar lahadi kowa ya isa inda ya fito. Ta kammala hada komai, tana jan zif

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *