UMM ADIYYAH CHAPTER 31 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 31 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Tunda ta dawo tana kan Kafafunta, cikin hada kayan tafiyarsu. Ita da Maami za su wuce a safiyar washegari, wanda ta kama ranar Juma’a ce, jirgi za su bi saboda su samu abubuwan da za ayi a goben, da yake ba wani dogon lokaci za a dauka ba na
bikin Maryam din. Sannan wannan ne kawai hanyar da Yaya Zaid ya amince ta bi, idan har tana son zuwa bikin. A cewarsa kar a wahalar masa da baby.
Asabar za a daura aure, ayi budan kai a kuma watse a ranar lahadi kowa ya isa inda ya fito. Ta kammala hada komai, tana jan zif

ZAMU TASHI 

Cin akwatinta, ta ji wayarta na Kara. A Kaikaice ta duba lambar mai kiran. Takiyya ce.Haba Hajiya kuma tun daga bikin Yaya Saadik kawai sai a jiki shiru?”
Dariya Umm Adiiyya ta yi, “Ki dai duba (Call Logs) dinki, na kira, na ji isarku Damaturu. Yaya Oga Ahmad?” “Lafiya Alhamdulillah! Daman na kira na fada miki cikin satin da za mu shigar nan muna tafe Abuja, idan Allah ya yarda.” Ba shiri Umm Adiyya ta saki fara’a cikin murna ta ce, “Haba, Allah ya nuna mana lafiya, zan dai je Gombe, amma zan dawo zuwa Lahadi Inshaa-Allah, ina dawowa zan nemeki.” “Mu din ma sai Talata zuwan namu.” To Allah ya kai mu lafiya. Ki gaida Mai-gidan.” Tunda ta samu labarin zuwan aminyarta. Umm Adiyya ta ji ta warware. Tun daga lokacin kuma ba ta sake gwadawa Zaid wani abin ba, tunda ta samu ya

amince da batun tafiyarta Gomben. Bare ma me za ta ce masa? Ko ta dago Www.bankinhausanovels.com.ng zancen, ba ta da wata hujja, kawai hasashe take yi, duk da kuwa hasashe ne mai Karfi, ba ta son bawa abin muhimmanci, ta koyi yarda da shi, da Kyar, ba ta son bari wani gibi ya gitta a tsakaninsu, za ta ba shi
dama, ta ga iya gudun ruwansa. Domin ba ta yi tsammanin za ta iya jure samun karayar zuciya ba daga wurin Yaya Zaid a karo na biyu.

***********

Gidan Hajja Kubitto, suka taru a wannan ranar gaba daya jikokin Alhaji Muhammadu Nafada, saboda nan Amaryar ta yada zangonta. Tsohuwa mai ran Karfe, duk yawansu kuwa, kowa ta gani tana gane shi. Ba abinda ya fi mata dadi irin yadda take ganin zuri’arta da ta Modibbonta suka habbaka har ma za su iya tada Karamin Kauye.
Yaranta mata uku da nasu zauri’ar, Amina, Hauwa da Fatima Muhammad Nafada, ga kuma mazan ma su hudu da nasu. AbdurRahman Nafada, Abdullahi (Mai Kano) Nafada, Zubairu Nafada, da kuma autan mazan. Ridwaan Nafada, wanda yake
zama a Legas da iyalansa, da yawansu sun samu halartar bikin. Wannan ya sa aka hadu tamkar yadda suke yi ko wane Karshen shekara a tattauna matsaloli, a magance su a kuma yi zumunci. Toke kam, wannan bin jiki da ki ke yi, ina za ki yi Kwari, idan lokaci ya yi? Tashi za ki yi ki rinKa motsa jiki, idan ba haka ba, za ki samu matsala.” Hajja Ku, da gaske fada kawai ake yi, a yi ta sa mata tiKan aiki, hutu ake son mai juna biyu ta riKa samu.” Asma’ ta cafe.
“To sannu, ai ba da ke na ke yi ba, ki je ki yi ta kwanciya jagwab! Kamar yakuwa, zaki fadawa garinku, ni dai ba ruwana. Ummu tashi ki dan zagaya ki daina biyewa wannan.” Nafisan Goggo Amina ce take masu dariya, “Na ga alama ke muka biyo a aikin
asibitin Hajja Ku.” “Sai na ga iyayenku da suka daure maku mara, ku ke kirana da wannan sunan.” “Haba ‘yar gaye da ke ace, ana kiranki Kubitto, ai za ki Www.bankinhausanovels.com.ng bada babes.” Faruk ya fada lokacin da ya shigo cikin babban falon kakar tasu. “To ka ganshi shi kuma. Wai ba ka gama bokon naka bane? Su Aliyu duk sun kammala sun barka, na san Fa’izu kam fasaharsa ta kai inda ta kai, ya yi gaba ya barka a baya. Ka tsaya sai kalle-kallen yaran mutane, na ji wai har tambayar aure kaje ka yiwa kanka ko?” Faruk yana dariya, ya sosa Keyarsa. “Hajja Ku, da izini na je tambayar, mahaifinta ya ganni da kamala da natsuwa, a take ya ce ya ba ni ita. Musamman da ya ji na ambaci sunan Modibbo, ashe ma ya san shi, kin ji yadda aka yi kenan.” Oh, ni Ummu. Allah Ya shiryeka, can jariri da kai din ne za ka yi aure? Ka ce da ‘yar mutane me?” “Abinda ake cewa mana.” Falon gaba daya ya kaure da dariyarsu. “. (Fice ka ba ni wuri. Ka ji marar kunya.)” Hajja Kubitto ta fad cikin fulfulde. Fatima ce ta shigo ta ce, “Hajja Ku har yau dai ba ki ba mu wancan sirrin ba, yaya aka yi ku ka yi shekaru sittin da biyar da Modibbo, bai miki kishiya ba?” “Yo to na san masa, sai ki je ki tambaye shi ai
“Buzu ta baza masa kawai, ta takura dan taliki.” Nafisa ta fada. Kai ku wuce ku tafi gidan iyayenku, kun zo kun sani ciwon muKamuKi. Kun ga wadancan ‘yan rasa kunyar ma, uwar daki na suka shige. Allah kadai ya san me zaice mata, cikin jama’ar ma yana biye da ita. Ya bata min toke.” Lokacin ne aka kula
da ba Umm Adiyya a falon. Zaid ne ya leKo ya ce, “Zan turo miki Modibbo yana Kofar gida, na san ya dan matsa ne, shi ya sa ki ka samu sararin sakawa mutane idanu.” Malam Zaidu.” Ta sa baki ta kira Www.bankinhausanovels.com.ng sunansa. Gaba daya aka sa dariya, don kowa ya san yadda ya tsani a kira shi Zaidu, “Seerah ma da ya zo Zaid ya ce, ba Zaidu ba.” Hannun Umm Adiyya ya rike cikin nasa, “Zo mu je falon Modibbo, wadannan ba za
su bari mu yi magana cikin nutsuwa ba.” Da gaskiyar Hajja Ku, ka tafi anjima, za mu yi magana, yanzu za mu fara shirin fita wurin taro, ko mu yi waya.”
“Na ga alama ko wane dakika ma mancewa ki ke yi da ni.” Ya fada hade da turbune fuska, dariya ta yi masa. Ikon Allah, gani a gabanka fa yanzu, da gaske za ka sa idan na fita su sani a gaba.” Shut up, ni babyna na zo gani ba ke ba.” Ware idanu ta yi cikin mamaki, “Laalala. Cabdi! Na ji halin ‘yan duniya, sai ka kama hanya ka tafi ai, tunda babyn naka bai kai a iya ganinsa ba.” “Muna jinku daga nan.” Muryar Fatiman Baffa Mai-kano ne suka jiyo”. Tsaki ya ja, “Wai mutum ba za a bar shi ba na ‘yan sakanni, yau za ki bar gidan nan. “Ko kai ka tafi ba, ina cikin ‘yan-uwana ka tsamo ni, me ka ke son fada min?”
Ajiyar zuciya ya yi ya ce, “Dazu na samu wayar Femi.” Sai da gabanta ya fadii, jin ya ambaci abin ofis, wannan ya sa ta gyara zamanta a kujerar da suke zaune. “Me ya faru?” Akwai wani competitive firm da rahoto ya shigo dazu, su ma sun samu matsalar da taso, ta yi kamarceceniya da tamu.”
“Ya Salaam! Wannan yana nufin wani ne kawai kenan daga waje yake wanan aikin?”
Zai iya yiwuwa, amma tunda aka yi amfani da na’urar ki, yana nufin suna da mai masu aiki daga cikin wurinmu, sannan wani abin mamaki shi ne, ba su kai hari ga wasu wurare ba face kamfanonin da suke sayar da Services din tsaro. They are targeting the security vendors (masu sayar da tsaro suke hari).”
“Ka na ga za ku yi magana da wannan kamfanin? Idan ya kasance su suka yi wa kansu barna fa, don su samu hadin kanmu wurin samun tausayawarmu?”
“Ki na da point a nan. Zancen dai da na ke so ki sani, shi ne dole mu sake takatsantsan fiye da da. Abun ya wuce dukka tsammaninmu. Ya wuce tunaninmu. Ba mu
da garantin ba za su sake kai hari ba, koda ta wani bangare ne, mun dauki matakan da duk suka dace, Www.bankinhausanovels.com.ng gudun sake faruwar makamancin hakan, amma ya zamo lalle mu kula.” “Haka ne kam, anyi passing bulletin?” “An tura, ki duba.” Muryar Hajja Kubitto suka jiyo daga falo, “Kai Malam Zaidu ka bar yarinyar nan haka, ta ji da abinda take fama da shi.”
Kada kai ya yi suka sa dariya, shi da Umm Adiyya, Kasa-Kasa ya ce, “Wannan tsohuwar ba ta jira . Tashi mu je tunda an hana ni gaisawa da babyna.”
Bayan an ce ba ayi da ni? A nemo incubator a mayar da babyn, sai ku je can ku karata.” Jawota ya yi ta rabi jikin sa kadan har da lumshe idanunsa, “Na isa na yi rashin ruwa da ke, ai bayan ruwan ma har da tsaki na.” Kwace jikinta ta yi ta matsa gefe. “Na Ki wayon, Allah, sai anjima.” Ta wuce ta bar shi cikin dakin Hajja Kubitto. Ai ko suna fita, aka sa shewa, ana masu tsiya. Umm Adiyya dai aka bari da jin
kunya, don ta kasa ce masu komai. Shi kuwa Zaid ya wuce da su Aliyu can waje. Haka aka yi ta hidima, amma rabin hankalin Umm Adiyya ya tafi ga matsalar (AZ IT), me ya sa suka zabi su yi amfani da ita, za su iya amfani da koma waye a ofishin, me suke son cimmawa ne? Ajiyar zuciya ta yi, da ta ga ba ta bullo da wata amsa Kwakkwara ba. An hattama
biki, an kai amarya Maryam gidanta da ke (Shongo Estate), a nan cikin Gombe, komai an tsara mata shi cikin girma da fasali.

*********

Makullin motarta ta fitar daga jakarta, tana tafe zuwa inda ta adana motar, jikinta a
mace yake yau, kasancewar ba wani aiki sosai ta yi ba, ta dangana shi da gajiyar tafiya ne dai, don a dawowa sun rasa jirgi, sai tahowa suka yi a mota.
Manyan baki gareta, ta gama tsara duk ababen tarbar da za ta shirya masu harma ta bar wa Innayo sallahu, akan abinda za ta rage mata kan ta dawo. Cak! Ta tsaya lokacin da ta saka hannu a jikin Kofar motarta za ta bude. Take wani gumi ya yanko mata, ta ji idanunta sun rufe na dakika daya, duhu ya mamaye mata ganinta. Makullin motarta ne ya subuce daga hannunta ya fadii a Kasa, wanda ya yi
sanadiyar Kara razanata. Hannunta na rawa, ta sa shi a cikin jakarta ta fiddo wayarta, ta shafe kusan minti biyu, kafin ta iya samo lambar Zaid. Www.bankinhausanovels.com.ng
Fitsari ne ta ji ya matseta a lokaci guda, jin ta yi kira biyu bai daga ba, sai da ta sake
gwadawa a na ukun, sannan ya daga. “Twinkle mun shiga sallah ne…” “Ka Zo…” Na’am?’ Zaid ya maimata cikin sake son jin muryarta, domin sai ya ji kamar ba
Umm Adiyya bace ta yi magana. “Ina Kasa… A waje, ka zo ka gani.” Tana maganar muryarta na rawa, ba ta yi aune ba ta ga wani abu na diga, shafa fuskarta da za ta yi ne, ta fahimci hawayenta ne. Dai-dai lokacin ta jinginu da motar da bayanta, ta daga kanta sama tana Kokarin hadiye tsoronta da ma hawayenta. Umm Adiyya, me ya faru?”
Kamar daga sama ta ji muryarsa kusa da ita, sai lokacin ta fahimci a cikin riKonsa take. Matsawa ta yi daga jikin motar, zuwa lokacin Mai-gadin ya ga inda Mai-gidansu ya fito da hanzari, ya nufi motar, don ya san ba lafiya. Wani jijiya ne ya motsa gefen kan Zaid, ya cije haKoransa cikin tsananin tashin
hankali, amma bai furta komai ba. “Ruben, shiga ciki ka kira min Charles.” Mai-gadin ya damki hularsa ta uniform a hannu, da gudu ya shiga kiran shugaban
tsaro na kamfanin. Hannunsa ya sa ya zagaye Umm Adiyya, ya riKeta a jikinsa sosai. “Komai zai daidaita, it’s going to be alright. Mu je ciki ki zauna kafin a duba kin ji? Akwai abinda aka dauka?” Sai lokacin abin ma ya zo mata, da ta duba budadden motarta ko an cire wasu ababen.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *