UMM ADIYYAH CHAPTER 33 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
yadda Zaid ya kasa, ya tsare, yana bin duk wani motsi na matar ta sa. Ba tantama kallo daya za kai masa ka san yadda ya damu Kwarai da ita. Hakan ya cika mata zuciya da dadii. “Zaid, ai da ka je gida kai ma ka samu hutu, sha biyu fa yanzu, ga aiki gobe, kar rashin hutun yai maka illa.” “Ba komai Aunty A’isha, bari na barku ku kwanta.” Ya san ya takura ta ne, idan banda haka ba, abinda zai matsarsa daga gangan Twinkle dinsa.
Sai da ya ga ta sha farfesu, sannan ya bar dakin hade da masu sai da safe. Koda ya je gidan ma, baccinsa kadan ne, don ana Asuba ya shirya ya Kara fitowa. Nan ya tarar da Abba ma a gate, shi ma ana sallar ya yiwo asibiti, sai dai sam ba yadda ya yi fatan samun Twinkle dinsa ya sameta ba. Tana cikin mawuyacin hali sosai. “Ai tun fitarka, a nan jiya kuma dai sai ta birkice, ciwo ya Ki ci ya Ki kicinyewa. Yanzu dai Likitan ya iso, ya ce za su Kara yin hoto, don a ga menene.” Aunty A’ isha ta shiga masa bayani. Salati kawai yake yi a zuciyarsa, shi dai fatansa daya kar wani abu ya samu Umm Adiyyarsa. Likita na zuwa ya hau gwaje-gwajensa, nan ne yake shaida masu cikin fa ya lalace, dole a cire mata shi muddin ana so ta samu lafiya, don ko an bar shi, sai
dai ta yi ta shan wahala.
ZAMU TASHI
Ba wani bata lokaci ya sa hannu, aka shige da ita wurin aikin. Ba shi ya bar asibitin ba har sai da aka fito da ita, ya ga dai da ranta, sannan ya sauke ajiyar zuciya. Takiyya ya kalla wacce take zaune a dakin asibitin. “Friend, sorry fa kin zo mana kuma mun janyo ki asibiti.” A’a haba dai ba komai Yaya Zaid, ga shi na ji dadin ganinta, ai ko ba komai hakan
ya fi, akan na ji ina daga nesa, yanzu ai sai na bada tawa gudumawar. Allah ya kawo masu zama, masu albarka. Ya kuma ba ta lafiya, wannan shi ne fatanmu.”Ameen! Ameen!! Mun gode. Allah Ya bar zumunci.” Kwananta daya a asibitin, bayan an burge cikin da suka gama Kwallafawa rai, kafin a Www.bankinhausanovels.com.ng sallamesu, kai tsaye gida suka wuce, suka tarar har Innayo ta gama shirya masu komai na abinci da ruwan wanka, gidan sai Kamshi yake yi kamar yadda ta san Umm Adiyya da son Kamshi, kullum gidan
baya rabuwa da turaren wuta dadada. Wunin ranar kaf! Sai sintirin zuwa gaisheta ake yi. Daga Kawayen Maami zuwa makwabta da ma nata Kawayen da kuma abokan aiki. Adda Asma’ ma har da nata KoKarin na biyo titi. Da yamma ko sai ga Mama da Anty ma sun iso. Umma aka bari a gida can Gombe. Tun bikin suke Www.bankinhausanovels.com.ng sa ranar zuwa, amma ba su zo ba, ga shi yanzu dalili ya kawo su. Kowa ya jajanta masu wannan Kaddarar kafin kuma su watse. Washegarin da aka mata aikin ne. TaKiyya da Ahmad ma suka koma Damaturunsu.
*************
“Hey, beautiful.” Zaid ya fada a hankali lokacin da ya zauna gefen gadonta a dakinta. “Yaya Zaid, ba zan karye ba dai.” Ta fada tana dariya, amma idanunta a cike suke da hawaye, wannan ne karo na farko da suka samu kebancewa tun dawowarta daga asibiti. “Hmm! Na sani, ba wanda ya kai ki Karfin hali ai da juriya, yaya jikin naki?” Lafiya, na samu sauki, na warke.” Ta fada tana kyafKyafta zara-zaran gashin
idanunta, cikin KoKarin mai da Kwallar ta. Princess dinmu ta tafi.” Ya fada yana wasa da yatsun hannunta. “Wa ya ce ma Princess ce? Ka sani ko Malam ne?” Murmushi ya yi, ya sauke ajiyar zuciya, gyarawa ya yi, ya jinginu da jikin allon gadon, sannan ya jawota jikin sa ya kwantar, yana shafa saman hannunta, “Ba komai Inshaa-Allah. Allah ya mana canji da wanda ya fi wannan, ya Kara mana
hakuri.” “Ameen.” Shiru ne ya ratsa tsakaninsu, abinda ya bata tabbacin cewa Yaya Zaid ya damu
Kwarai da abinda ya faru kenan, saboda da yanzu yana nan yana cikata da kalamai masu kwantar da hankali, da sanya natsuwa. “Last week ya fara motsi.” Ta fada kamar daga sama. Hannunsa ne ya tsaya cak! Daga shafa hannunta da yake yi. Wannan ya sa ta juyo da kanta ta dube shi. “Ba ka ce komai ba?” Girarsa ya Gaga, idanunsa suka waru kadan, zuciyarsa tana bugawa fiye da kima yace, ” To me zance?” Tashi ta yi ta zauna tana dubansa da kyau. Hura mata idanunta ya yi, hade da yi mata Www.bankinhausanovels.com.ng kasalallen murmushi. Abinda kawai na damu da shi, shi ne ke, kuma ina farin-cikin kasancewarki cikin Koshin lafiya, we can have many princesses, but only one Twinkle Star to shine her light upon them. Kin san muhimmancinki a gareni ko Adiyya? Don haka ki kwantar da hankalinki. Haka Allah ya so. Ba lokacinmu bane yanzu.” Haka ne, na gode da kulawarka a wannan lokacin.” “Always and forever. Inshaa-Allah.” Ta so tayi masa wata tambaya, sai kuma ta ji ba lokacin yinta ba kenan, yanzu kam abu guda suke nema, natsuwar zuKatansu kuma sun samu a cikin dumin juna, ba za ta katse wannan ba daga garesu Jin ana taba Kofa ne ya sa Zaid ya cire hannunsa da ya zagaye Umm Adlyya da shi.
“Kuma dan hirar ma ba za a bari mutum ya zo yi ba don Allah?” Ya fada fuska a yamutse, sannan ya sa takalmansa na cikin gida, ya isa bakin Kofar. Ya san ko wacece, yana budewa ya dan sosa kai ya yi waje, ba tare da ma ya jira me za ta ce masa ba. Adiyya kam ta gimtse dariyarta, ganin shigowar Anti. Ikon Allah, ke mai miji ko Ummu? Har kin fara barinsa yana shigowa ko? Kin san dai yanzu jego za ki yi, tunda da mai motsi ya fita a jikinki, ki tsaya biye masa dai.” Umm Adiyya kam banda sunne kai ba abinda aka bar ta da shi, me za ta cewa Anty to? Ko ta yi magana ma, ba lallai bane ta yarda hira kawai take yi da mijin nata ba, don haka ta yi shiru, ta gama kwasar hudubar da ake mata. Maamin ma dai da ta bari ki ka dawo nan. Tunda ko ku kadai ne a gidan nan sai ki kula da kanki sosai, ba sai na fada ba, ni dai gobe zan koma. Idan ki ka jiKowa kanki aiki kuma, to. Ita dai tana ganin ikon Allah. Ta sha guzurin kayan Kamshi kam, har ta gode Allah, banda su zuma da kayan yaji da aka ajiye mata kaya guda, kamar wanda Antin ta zo da wani shiri na musamman
don jego. Mama kam ta juya da direban Baffa Abdu. Antin ce dama ta rage tare da Yaaya Saadik za su koma. Ba ta tsaya a nan ba, har Zaid din sai da aka ja masa kunne a safiyar tafiyarsu. “To don Allah Malam, a sarara mata, ta samu lafiyarta haka nan. Ka san ‘yata dai ‘yar luwai-luwai ce kamar Kwai, lallaba take so da kulawa. Musamman yadda ta jikkatun nan, abinci masu kyau da Karin jini ya kamata ta yi ta ci, a kula da magungunanta Www.bankinhausanovels.com.ng
kuma. Allah Ya ba ta lafiya ya kawo masu zama.”
Duk tsiyar Zaid da fadinsa a yadda yake yau shiru ya yi, don ya ga abin na Anty ba wasa, da ta so ma tayi masa terere ne, wai za ta kira Maami. Umm Adiyya ta koma wurinta da zama, saboda za ta fi samun kula. Anty, to ai Maamin ma tana zuwa aiki, har gwamma a nan ma ga Innayo za ta kula da ita.”
Ai hannun Innayon zan damKa ta, na ga alama.” Shi dai yai tsit! Burinsa dai kar ace za a dauke masa matarsa. Hakan ko aka yi, sai gani ya yi ta kira Innayo tana mata jawabi. Har mota suka rakasu suka wuce.
**********
Yana tsakiyar aiki, wayar da yake amsawa daga Karamin falon karbar baKin sa, ta yi Kara. “Stella?”
“Mr. Charles ne…” Ya shigo.” Ya fada cikin wayar sannan ya cigaba da kammala abinda yake yi, cikin
dakikai Kalilan aka turo Kofar ofishin nasa. Hannun Charles da wani fayil, “Ina kwana Yallabai.” Ya danganta da me ka zo min da shi, mai kyau ko marar kyau? Murmushi mutumin ya yi, sannan ya tura masa fayil din.”Wannan rahoto ne bisa bincinken da muka yi akan komfutar Madam. A bisa shi na ke son na bada shawarar a tsayar da binciken akan ma’aikatan da suke cikin ofishinta, ko suka fi kusa da ita.
Domin abin mamaki, duk da komai an yi masa shigar siddabaru da Karfi ne hade da Www.bankinhausanovels.com.ng
KarKarfa. (Hacking), lokacin da aka shiga domin a goge signature na mai satar, an shiga ne da Password dinta, don haka koma waye, ya shiga ya dau komfutarta a mota, ya san Password diinta ne, na kusa da ita ne. Ta iya yiwuwa suna ganin lokutan da take budewa kullum.” Hmm! Na gode Mr. Charles, me ake ciki game da (Security Footages) din?’
“Ana kan recovering, sun lalata drive din ne, amma muna aiki akai.” “Ina son ku kammala zuwa Karshen satin nan, na ji a jikina mun kusa , na kuma shinshini inda wannan abin ya dosa, still ka bi a hankali, ka ci-gaba da aiki da mutum daya zuwa biyu a Team dinka da ka fi yarda da su, ba na son su fahimci lokacin da za a janye tabarmar kasansu. Za mu yi masu bazata ne.” Yes, Sir.”
************
A hankali dai komai ya fara komawa daidai. Bayan sati da barin Umm Adiyya. Duk wata kulawa da take buKata ta same shi daga Yaya Zaid har ma fiye da tunaninta, domin muddin yana gida, kusan komai shi yake mata. Wai ba ta gama warwarewa ba, tun Umm Adiyya tana masa dariya akan yadda
yake tarairayarta, tana cewa ya faye raki, har ta kula tsakaninsa da Allah ya masifar
tsorata da ganinta a halin da ya ganta ranar da za a cire mata baby ne. “Mutum ya haihu ma bare rashin lafiya?” “Hmm! Ba za ki gane bane, ba ki ganki bane lokacin da idanunki suke KakKafewa. Wallahil-Azeem, ba na fatan na sake ganinki a wannan yanayin da na ganki a ciki.” Ya fada mata, a lokacin sai da ta yi Kwalla. Ba ta san me za ta sakawa Yaya Zaid da shi ba, kan irin Kaunar da yake gwada mata. Idan ta auno nata son, ta san tana matuKar son shi, amma yadda yake nuna mata, sai take tunanin ko dunduniyar Kafarsa ba ta kamo ba a son da yake mata, shi ya sa a kullum garin Allah ya waye, to burinta shi ne ta kyautata masa, da iyayensa kamar yadda yake kyautata mata, ta kowace fuska.
Cikin hakan suke zaune har zuwa ranar da komai ya juya baibai. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da safe yana shiryawa zai wuce wurin aiki, kasancewar Umm Adiyya ba ta koma aiki ba tukun, ya sa ta tsaya, don ta taya shi shiryawa. Zan shigo latti yau. So, kar ki damu, idan kin ji shiru, akwai taron da za mu yi da baki daga Cincinnati, zan kiraki a tsakani.” Allah ya bada sa’a. Ya kare min kai kuma.” Ta fada tana murmushi, hade da matse masa Tie Cinsa. Allah ya kare ni daga ke dai da farko, ki ka cigaba da yin haka, ai sai ki Karasa ni.” Ya fada hade da janyota ya hadata da jikin sa. “Oho dai, ba ni bace mai yin latti.” Evil. Wicked. Cruel.”
“Na ji dai duka. Allah ya bada sa’a, a dawo lafiya.” Ta Karasa fada tana masa dariyar mugunta, ba ta yi aune ba, ta ji labbanta cikin nasa, ya dauki tsawon lokaci yana rikita mata lissafi, cikin wani salo mai narka gabobi da juya tunani. Sai da suka fara neman numfashi, sannan ya sake ta. Kamshinki ya iya tafiya da hankalin mutum, za mu zauna ayi min bayani. In fact! Bana buKatar bayanin ma, ki zauna kawai cikin shiri, anjima idan na dawo.” Yana fadan hakan ya kashe mata ido, ita kuwa nan take Karyarta ta Kare, tuni ta shiga wuki-wuki da idanu. Da sauri ta sake shi, “Ahaf! Shegen tsoron tsiya, da gaske yau kam sai dai idan gidan za ki bari, amma daga ke har Antin ba zan saurareku ba. Haka kawai…” Na ji sai ka dawo.” Tana Allah-Allah kar ya Kara yanko wani zance mai nauyin. “Wear something bright.
And flowy.” Ya fada daga bakin Kofa, sannan ya fita daga dakin, ita kuwa ta take masa baya, tana ji kamar tana yawo a gajimare. Yaya Zaid bai da dama. Idan ta biye masa wataran zuciyarta za ta tarwatse.
********
Ba ta yi kasa a gwiwa ba, duk wani shiri da ta san ya dace ta yi, shi ta yi har da kiran Adda Asma tayi ta Kara bata wasu shawarwarin da dabarun. Ta shirya tsab! Cikin
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG