UMM ADIYYAH CHAPTER 36 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Ni kuma Yallabai?” Zaid ya dan leKa saman kafadarsa zuwa bakin Kofa, alamar neman wani mai
shigowa, “Ina da tabbacin kai kadai ka shigo cikin ofishin ko? Ka san ina da kyamarar tsaro a nan, ba kowa a falon waje.” Ya fada yana nuna dan Talabijin din komfuta da ke fuskantarsa, Kirar kamfanin (Apple). Waya ya daga, “Stella, kar wani ya dame mu.” Mr. Akim ya gyara zama, sannan ya muskuta cikin kujerar da yake. Zaid ya kafe shi da idanu hade da harde hannayensa cikin juna a saman teburin nasa. “Ina saurarenka, me ya shigo da kai?” Har yanzu idanunsa masu tsirga jiki da sa mutum ya shiga taitayinsa suna kan Mr. Akim. “Uhm, Yallabai dama na zo ne batun matsalar nan, ni ina ga hukuncin da aka yi wa
ZAMU TASHI
Hajiya ya yi tsauri, koda a ce za a dan sassauta mata. Ko Department ne a canja mata, idan ya so.”
“Hmm! Zaid ya fada cikin alamar sauraron Mr. Akim, idanunsa suka kai kan yatsunsa da suke karkadia dan makulli akan teburin. Laifinta yana da girma, ban yi tsammanin sassauci gareta ba, ta saci muhimman
takardun kamfanin nan, da sirrin taswirar aikinmu mafi girma, ciki har da wani aikin
da aka yi wa gwamnati da ma wasu ababen, ta sayar da su wa kamfannonin adawarmu, sannan ace mu bar ta? Mun bawa wani Kofar sake nanatawa kenan,
abinda ya dace shi ne a gwada misali a kanta, har sai wani ya yi tunani biyu kan ya
Www.bankinhausanovels.com.ng
fada wannan ta’asar. Ko ka na da wata hujja da za ta wanke ta?” “A’a kawai dai na ga yarinya ce mai hankali, kuma yanzu ta fara tashen aikinta, idan
an ba ta dama za ta amfani ma’aikatar nan sosai, akan a kore ta, bayan ta san sirrika da dama, ba Karamar barna za ta iya yi mana da abinda ta sani ba.” Wata gajeruwar dariya Zaid ya yi sannan ya ce, “Hmm! Na fahimta, sai dai a wannan matakin da ake ciki, ba abinda za ta iya yiwa kamfanin nan ya girgiza, saboda muna da goyon bayan Kasashe, muna kuma da manyan matakan tsaro. Ka yi haKuri kai ka
horas da ita, amma matakan da muka dauka a kanta, su ne daidai, dole ta fuskanci hukuma.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Jiki a sanyaye, Mr. Akim ya mike zai bar ofishin, har ya kusa isa bakin Kofa. Zaid yace “Mr. Akim kamar ka yi mantuwa.” Juyowa ya yi, Zaid ya hango gumin da ya tsatsafo a goshinsa duk da sanyin iyakwandishon din da ke ofishin. Idanunsa suka bude cikin razana, “Wannan? A ina ka same shi yallabai? Na dade
ina nemansa.” Zaid miKewa ya yi ya zagaya zuwa Kofar fita. Kwankwasa Kofar ya yi. “Wata Kila nan gaba idan za ka yi sata, za ka iya cire ababen cikin aljihunka gudun kar su fadi, a lokacin da ka zo guduwa daga wurin.” Take idanun Mr. Akim suka kada, “Sata kuma? Wace irin magana ka ke yi Yallabai?”
Dai-dai lokacin Kofar ta budu. Mr. Femi, ASP Sanusi da ma sauran mutane biyar da suka yi aiki a Karkashin Mr. Akim, suka shigo tare da Fayemi.
“Come on shut up.” Zaid ya fada cikin Kokarin danne Dacin ransa game da wannan mutumin mai rainin hankalin. “Yallabai, me yake faruwa ne?” Zaid ya runtse idanunsa, a lokacin idan akwai wanda yake da niyyar hallakawa a bayan Mr. Akim yake.
“Ka san abin da ban dariya, idan ka duba da kyau, duk taka-tsantsan! Dinka, na ganin ba a samu shaidar yatsunka a kan komfutar Adiyya ba, ba a samu a (Server Room) ba, ba a samu komai game da abinda ka aikata a boye ba, ka yi kuskure guda, sai ba ka boye abinda ba ka taba tsammanin zai kawo tonuwar asirinka ba.” Zaid ya sa hannu ya daga abinda ya ke riko a fuskar Mr. Akim “Nail cutter. Duk iliminka, da muguntarka, bai taba kawo maka cewa abu guda
kamar abun yankan farce bane, zai kawo Karshen Karyarka. Na san za ka yi mamakin yadda aka yi na gane naka ne, ko kuma kai ne? Umm Adiyya kai take bawa rahoto, idan Musa baya nan, kai ne shugaban Department dinsu, kai ka ba ta mabudin sirrinta a karo na farko. Tana da wayo don haka ta canja Www.bankinhausanovels.com.ng
shi, amma da yake ku na aiki tare, ka sha ganin tana amfani da shi har ka haddace shi. Ka san idan za ta fita cin abinci ko ba za ta dade ba, durowarta take budewa ta ajiye jakarta da na’urorinta, ka san yaushe take fita ta dade, ka san komai game da ita,
abu mafi muhimmanci, ka san idan na fahimci ita take satar asirin kamfani ba abinda zan iya aikatawa a kanta, saboda ita Kanwata ce, daidai lokacin da ka fahimci ita matata ce, wannan ya ba ka damar kai harinka a wannan lokacin. Abinda ba ka sani ba shi ne, ni ba haka na ke aiki ba, mai laifi, mai laifi ne.
Ka tura mata Virus ta Imel, ta kuma bude, ka dora mata laifi, amma mun san ba ita bace, saboda mai laifi baya bayyana kansa kai tsaye a bugu daya. Kuskurenka na farko kenan. Hasan surutunsa ya fi sawa a gaba, duk dadewarsa a ofishinku har yau bai taba bari kun fahimci bai iya aiki da komfuta ba, wannan ya sa ko yaushe yake cikinku tafiya
(Field Work). A tunaninsa babu wanda ya sani.” Tuni Hasan ya hadiyi busashen yawu, ya maida kallonsa Kasa hade da nade hannayensa ta bayansa. Jamila hankalinta ya fi raja’a akan (Games) dinta da kwalliyarta, da kuma wasu ababe da ba ta da lokacin yin irin wannan tunanin.
Musa, tsabtarsa da tsantseninsa sun yi yawa da har na yi tunanin shi ne da farko, saboda komai sai ya goge da Antiseptic, na zaci shaidarsa yake gogewa da farko, kafin na fahimci inda zai dora satar, ba zai dora a kan Adiyya ba, saboda yana sonta a lokacin.”
Oga Musa dai hannun tabarau dinsa ya gyara sannan, ya daidaita tsayuwarsa, ya kau da kai daga kallon Ogan nasa, Yaya aka yi ya gane? Oga Musa ya yi tunani a ransa. “Wannan ya bar mana Ayodele da kai. Ayo kirkinsa da kuma zagewarsa akan ko Www.bankinhausanovels.com.ng
wani aiki da jajircewansa ga kamfani cikin ruwa da rana, ba za su bari ya aikata abin da aka aikata ba Mutumin kusan a nan yake rayuwa. A bangare guda kuma, kai ne. Ba ka taba korafi don ba ayi maka yadda ka ke so ba, a Bangare guda kai ka ke yin tuhumar da tambayar, ba wanda zai maka a cikinsu,
bai cin na sama da kai. Kai Programmer ne da kamfanin nan take alfahari da iliminka. Kullum idan ba ka wani aikin, zama ka ke yi ka yanke farcenka sumul! Babu gargada. Wannan ya sa lokacin da na dauki komfutar Adiyya a cikin jakar da ka je
goge takun satarka a ciki, na tsinci wannan a gefen jakar. Na rasa inda na san shi, amma na san na taba ganin setin a wani wuri, saboda launinsa, ruwan bula, don haka na dage shi na sa a durowata, ban tabbatar da mai shi ba har sai da na ga ka na kada dan-uwansa, wato Karamin almakashin yankar farce, lokacin da muka kiraku dazu. Na san ba za ka iya ganin an mannawa wani laifinka ba, duk da hakan ne niyyarka da farko. Your guilt has caught up with you. Tambaya daya na ke so na yi maka. Is it all worth it? Ka kyautawa kanka?” Mr. Akim kansa na kasa, kawai suka ji gunjin kuka ya tashi, zabgegen mutumi da shi ya zage, sai rusan kuka yake yi, amma ba wanda ya tanka masa, saboda gaba daya
jikinsu ya mutu murus! Yallabai, don Allah, don Annabi ku yi hakuri, da gaske har gida suka je suka
sameni, ina buKatar kudin ne, sun ba ni miliyan talatin, abinda zan masu kenan, kuma na ga da wannan kudin, ni ma zan iya kafa nawa kamfanin a gefe, koda hakan ta kasance, an kamani, an koreni, shi ya sa na karba. Ku yi haKuri, ba zan iya biyan
su kudinsu ba, za su batar da ni ko su kasheni.”
Zaid Kura masa idanu ya yi, “Su waye suka sa ka?”
“Ni ma ban san su ba, kawai yaransu suka turo, na sayi filaye da kudaden na fara gini a garinmu, ba zan iya hada masu kudinsu ba. Kuma yarjejeniyar zan Karasa hada masu komai, bayan na kwashe Www.bankinhausanovels.com.ng Information a nan.” Shi duk wannan babatun da yake yi, hankalin Zaid baya kansa yana kan Umm Adiyya da ta kawar da kanta gefe, ba tantama kuka take yi, ba komai bane kuma ya sani, Sai tuna cewa Mr. Akim ne ya yi sanadiyyar shigarta tashin hankali har ta rasa
dan tayinsu, duk da Allah ne ya Kaddara ba za a same shi ba, amma Mr. Akim ne sila.
Da kansa ya nemi amincewarta akan ya nuna tamkar da gaske laifinta ne, saboda ta
hakan ne kawai mai laifin gasken zai sakankancewa ya ga kamar ya tsallake siradi ko kuwa rashin gaskiya ya dame shi, ya tona kansa. Koda yake cewa ya koreta, duk da ya san ta san da shirin, sai da abin ya yi masa ciwo, bai taba kawo da bakin sa zai iya Datawa Twinkle cinsa suna ba. “ASP, za ku iya zuwa da shi ya ba ku duk abubuwan da ku ke buKata, ya dawo da komai da ya dauka, idan zuri’arsa zai sayar ma, ya sayar. I don’t care. Take him apart.” Ya Karasa fada cikin dacin rai da idanu masu kada hanji. “Don kowa ya sani zan fadi wannan, Umm Adlyya ba ta da laifi, amfani aka yi da ita, aikinta yana nan, na yi hakan ne kawai don na zakulo asalin mai laifin. Mrs. Zubair ki yi haKuri da hakan da aka yi, duk da sai da izininki hakan ta faru. Mun gode.” Wani damka ya sha a hannun yaran ASP Sanusi, ba shiri ya boKare, yana kuka wiwi! Da hawaye. Suna daf da fita ne, ba tare da Zaid ya juyo ba ya ce, “Za ka so ka
canja Signature dinka na sata. Mr. Charles ya gano tsohon, (Puppet) koda watakila ka na da niyyar kara yi a gaba, bayan ka gama zaman kurkuku.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun yana sauraren surutai, na nuna ban mamaki daga bakin abokan aikin Akim, har ya fara ji suna watsewa da dai daya da dai daya, kansa ya daga sama yana Kokarin hadiye ciwon da zuciyarsa take masa, koda wasa bai taba kawo mutumin da ya yarda da shi irin Akim, zai iya masu haka ba, da shi suka bude kamfanin nan tare suka yi komai.
Ya san irin gwagwarmayar da suka sha, sannan dare daya ya bankadar da wannan, ya kuma tashi ya likKawa matarsa Umm Adiyyarsa sharri. Da bai Kare da yin hakan ba, da zai iya masa sassauci, amma banda yanzu da ya yi sanadiyyar Kwace masa duniyarsa. Hannaye ya ji sun sagalo shi, ta kasan hannunsa zuwa kafadarsa, duminta ne ya ratsa bayansa, a hankali ya runtse idanu, ba zai iya dubanta ba, amma dole ya ba ta baki.
Da sauri ya juyo ya riKota cikin wata irin runguma mai shiga zucci. Kuka take yi mai diri a cikin riKonsa. Shi ma bai san lokacin da ya ji nasa idanun sun kawo ruwa ba. Saman kanta ya sumbata, yana shafa mata bayanta a hankali. “Ya isa my Twinkle.” Dago kanta ya yi yana duban idanunta da suka yi ja, suka yi
luhu-luhu da hawaye, ya san ko ba komai, yau ta samu sa’idar cewa an warware
komai, zargi ya bar kanta, wanda duk da ta san ba ita ta aikata ba, amma sharri ba
abinda ya fi shi muni, da bacin suna, wanda har abada ba kowa bane zai fahimta, bare ace kowa ya zo ya yarda da gaskiyarka daga baya. “Uhm-uhm…” Gyarar murya suka ji daga bakin Kofa. Umm Adiyya ta yi saurin sake Zaid, ta shiga share hawayenta, sannan ta matsa bangaren kujerun zaman baki, (Couch) Ta zauna, yayin da Fayemi ya Karaso cikin ofishin.
Ya kula da kallon kissan da Zaid ya watso masa, amma ya matse ya Karaso. “Ehm… Ku yi haKuri da shigowata kai tsaye. Yallabai, ina buKatar sa hannunka a nan.” Karba ya yi, ya duba takardar sannan ya saka masa hannu. Ga shi.” “Saura nan.”
Zaid ya Kara karba ya saka, “Akwai wani wuri kuma?” Ya tambaya cikin nuna
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE