UMM ADIYYAH CHAPTER 40 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Umm Adiyya
Tunda magariba ta kula da yadda Yaya Zaid yake kallonta, ta san magana ce a bakin sa. Amma dai bai ce komai ba, don haka ita ma ta basar, ta kula tun
dawowarta ran Litinin yake dari-dari da ita. Haka kawai ta tsargu, amma za ta jira,
sai ya fada mata koma menene, don kansa.
Gyara filonta ta yi ta bubbuga yadda za ta ji dadin kwanciya a kai. Sannan ta karkade kan gadon . “Dr. Zainab tana gaishe ki.”
Juyowa ta yi tana dubansa. “A ina ku ka hadu?” Littafin hannunsa ya ajiye ya kurbi
Kahwansa, sannan ya ajiye a kan durowar gefen gado, ya zauna a kan gadon.
“Dazu da yamma ina wurinta.”
Kallonsa ta yi wani iri, cikin tsuke idanunta, “Okay… Tun yaushe Doctor Zainab ta dawo Likitan maza kuma?” Dariya ya yi ya ce, “Ba ta dawo ba. Na je ganinta ne akan batunki.”
Lokacin ne Umm Adiyya ta zauna ta ba shi dukkan natsuwarta. “A kaina kuma?”
“Uhum! Na ga dai yanzu kin gama warwarewa.” Ba ta fahimci inda zancensa ya dosa ba, don haka ta Kara natsuwa da kyau. “Shi ne ka je ka tabbatar da hakan a
gun Likita ko kuwa me?”
“Shawara na je nema, kuma na samu. Ina ga zai dace yanzu kam ki dan huta haka
nan kafin ace mun shirya samun wani baby ko ba haka ba?”
Ganin irin sauyin da ya ziyarci fuskarta ne, ya sa ya Kara da, “Kuma da na kawo
batun ma ga Doctor. Ita ma ta yi na’am da hakan. Wannan ne ma ya sa na nemi
shawararta kan hanyar da ta fi dacewa mu dau mataki. Don haka ga wanda ta
rubuta miki. Ta ce duka instructions suna ciki.”
Ko dai Zaid bai kula da yadda fuskar Ummu Adiyya ta dagule ba, ko kuwa baya Www.bankinhausanovels.com.ng
kallonta yake maganar, domin yana kai aya, ta mike daga kan gadon. “T…I can’t believe this.”
“Ba ki tsaya kin saurareni ba Madam. Zauna, ai shawara ce ko?” Kallonsa ta yi wani iri, ta ma kasa yarda wai Yaya Zaid ke irin wannan maganar.
“Yaya ma za ayi ta zo kanka irin wannan shawarar, har ma ka je ka samu Doctor Zainab?”
“Abu ne mai sauki, duba da yanayin yadda kusancin wancan Harin naki da kuma wannan da ya faru, ina ga ya dace ace kin dan sarara haka nan, saboda wahalar da ki ke sha, a yayin faruwar barinki. Ba hurumina bane nayi miki bayanin komai dalla
dalla, amma ni dai kawai ina so ki san ba zan iya sake jure ganinki a cikin irin halin da na ganki ba a baya.
Kuma ke ma ko don lafiyarki, ina ga hakan zai dan taimaka, idan jikinki ya dan huta sai kuma mu sake jarabawa. Wannan ne kawai dalilina, ba wai wani abu bane, na ga kamar ki na so ki daga hankalinki ne akai.” “Dole za ka ce kawai mana, kai ai ba kai ka rasa abin nan ba, ni da yake jiki na ni Www.bankinhausanovels.com.ng
kadai na san me na ke ji. Gaskiya ni ina son yara, ba za kuma ka zo ka duddura min
magnunguna ba ka ce wai na huta, idan na zo komai na ya toshe na kasa samun haihuwa, kwana biyu ka ce kai aure za ka yi,
ka na son haihuwa. Gaskiya ka mayar
mata da magungunanta, ba zan yi amfani da su ba.”
Zaid kam shiru ya yi yana kallon Umm Adiyya har ta kai aya. Wani abu ya soke shi daga maganganunta.
“Kwarai mana na damu da abinda ki ke fuskanta, ni ma ina son samun yara kamar
ke, kamar kuma ko wane da namiji, amma akwai abinda idan har hatsarinsa ya shafi
rayuwa da mutuwa ko halin Kaka nika yi, a hakura a jinkirtan shi ya fi akan komai ko?”
Wurga filon ta yi kan gadon, sannan ta juya za ta bar akin.”Adiyya!” Ya sa baki ya kirata, amma ba ta ko saurare shi ba, da sauri ta fita tana share
hawayen da ta gaza rikewa.
***********
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
Shin ya ma san me mace take fuskanta a lokacin da ta rasa gudan jininta? Tun lokacin da za a ce mace ta samu labarin tana da juna biyu, a take a lokacin ta zamo uwa, bare ace ta ji motsin farko, ko kuma ta ji yunwa, yaro ya cure a cikinta, ko ta ci
mai Gumi yaro ya yi ta naushinta yana motsi.
Ba ta san me sauran mata suke fuskanta ba, amma tabbas ita kam iya inda ta fuskanta tun lokacin da ta fara barcin safe, ta san ita uwa ce, ta ji wani abinda bai taba kwatantuwa da komai ba, sannan yau ta tsaya fadan halin da ta shiga da ta Www.bankinhausanovels.com.ng
tsaya tana jin Yaya Zaid yana mata bayanin tsarin iyali, tun kan su ga Kwansu na
farko a duniya, bata san ma yadda za ta kwatanta yadda zuciyarta ta tarwatse ba kaca-kaca!
To daman ba da gaske yake son samun zuri’ar da ya sa take ta masu addu’a bane,
ko kuwa sonta ne ya daina? Ko dai meye ne, ita ba ta ga dai dalilin da zai sa ya kwaso masu wannan bala’i ba. Tana zaune a dakinta tana ta kuka, tana share hawaye, tana gunjinta, duk a zaman
jiran Zaid ya bi bayanta ya ba ta hakuri, amma tunda ta daga idanu ta ga karfe biyu
saura, ta san ba zai taba biyo ta ba, wannan ya nuna tsantsar kafiyarsa kan nasa dalilin.
Ita kuwa za ta nuna masa ba shi kadai ya iya kafiya ba. Domin da ta yi tsarin iyali
yanzu, gwamma ta Kaurace masa ma gabaki daya. Tunda haihuwar ce ai baya so. Ba ta san lokacin da barci ya kwasheta ba.
**********
Da safe da suka hadu a Kasa, ba ta ce masa komai ba, hakan kuwa ba Karamin damun Zaid ya yi ba, don ya fito da dan guntun fushinsa na jiya, yana magana, ta
tashi ta bar shi, ta ba banza ajiyarsa. Ba kuwa abinda ya tsana irin hakan, sannan yanzu ko gaisuwa ma ta Ki ta hada su. Daurewa ya yi ya danne nasa fushin, saboda ya san tana da dalilinta na fushin,
amma a hankali dai zai bi da ita har ta fahimci abinda yake nufi. Yaya jikinki?” Ya tambaya, abinda ya zo masa baki kawai kenan. Da sauki.” Ta amsa a ciki, murmushi ya yi na gefe, ya san duk ita nan nuna bacin ranta take yi. Mikewa ya yi ya isa wurin da take ya tada ita tsaye, hade da juyota da kafadunta. Haba me ya yi zafi Twinkle, za ta tsumewa Noorinta. Uhm?” Lumshe gashin idanunta ta yi, ta kau da kai gefe. “Oh, tawa ta sameni, yau ko dan murmushi ba za ai min ba, bare na samu gaisuwar safe na?” Juyowa ta yi ta bude masa idanu, hade da juya idanun. “Wannene kuma wannan?”
“Kin fi ni sani, idan ba dai tuna miki ki ke so na yi ba da wayo.” “Don Allah ka bar ni na wuce na yi latti, ina da aikin yi, idan kai hira ka ke jin yi, sai na dawo sai mu yi da yamma.” Ba kyau dai.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsayawa ta yi bayan ta fara barin wurin cin abincin. “Ka na son ka san meye ba kyau? Abinda ka yi jiya ba kyau, kuma ba zan taba yarda ba, don haka idan ka namin dadin baki ne ma, don na amince, zai fi kyautuwa ka daina, don ba zan sauka
daga kudiri na ba.” “Oh, da gaske?“ “Eh.”
“To shi kenan, idan haka ki ke so, mu ci-gaba, zan ga iya Karshen abin.” Ya fada a
tsaurare, ransa ya baci, ba don komai ba, sai don yadda ta fito Karara tana jayayya
da shi, bayan yana KoKarin ya lallabata. Ba zai tsaya yana ja in ja da ita ba akan
wannan. Ya riga ya dau alKawarin sai sun dau wani mataki koda na shekara guda ne, kafin su sake fara gwadawa. Don haka duk borinta za ta yi ta bari. Sai ya samu yadda yake so. Ba abinda ya yi masa zafi, irin cewa da ta yi ita kadai ta fuskanci ciwon rasa
yaransu, ba ta san me ya fuskanta ba, ba za ta sani ba ai, saboda a tunaninta shi bai
da kusanci da abinda ya faru, kamar yadda ta fada.
Rai ba dadii, dukansu biyu suka wuni. Koda ya dawo da dare ma bai shiga
sha’aninta ba bare su sake tattaunawa, haka dai suka ci-gaba da zama har kwanaki
biyu, ya kawo idanu ya zuba mata. Rana ta ukun ne ya sameta kai tsaye. Tana
kallonsa, ta shiga duba wani abinda babu shi a wardrobe dinta. Idanu ya sa mata, ta
yi sintiri daya, na biyu, a na ukun ne ya ce, “Umm Adiyya, zo ki zauna, magana za mu yi.”
Ajiyar zuciya ta yi, ta je ta samu kujerar kusa da gadonta ta zauna, ba tare da ta kalle shi ba, bare ta ce komai. “Na fahimci akwai abubuwa da dama da ba mu assasa ba a zamanmu ni da ke,
wata Kila ko don yadda aurenmu ya kasance cikin gaggawa ne, ko kuma ababen da
suka biyo daga baya, amma ina son ki san da cewa, ke matata ce, kuma ni mijinki
ne, akwai girmamawa a tsakaninmu. Idan za a samu hakan kuma dole sai da
fahimtar juna da kuma bawa kowa hakKinsa da ya dace. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kin yi wani abinda ba na so, kin kuma san ba na so, na daga miki Kafa, saboda ranki yana bace ne, amma ina so ki sani, ba zan lamunci sake faruwar hakan ba.Wannan kenan. Abu na biyu kuma, shi ne ina so ki fahimci inda maganar nan ta dosa. Kafin
na ce wani abu, za ki iya fadin meye matsalarki kan batun nan?”
Ganin ta yi shiru hae da kawar da kanta gefe, ya san ba ta yi niyyar cewa wani abu. Kin ga Umm Adiyyah, ba na so ki dauka a matsayar cewar alaKar da ke tsakaninmu tana faruwa ne don cimma burin samun zuri’a kadai, wannan na Allah ne idan ya so
ya azurtamu. Idan ya so ya hana mu.
Wannan alaka ibada ce, ita karan kanta, sannan dominmu ne, idan ki ka sa rai don
ki samu baby ne kawai, ki ka zo ba ki samu ba kuma fa? Kuma a tunanina ko ba don
lafiyarki ta zahiri ba, ko don lafiyar Kwakwalwarki ya cancanci ki samu hutu. Ba za ki
fahimta yanzu ba, saboda hankalinki ya kafe kan wani abu, amma ki yarda idan na
ce miki wannnan juyayin rashin yana taba ki a hankali, ta hanyoyin da ba kya tsammani.
Wannan ya sa na daukarwa kaina alKawarin ba zan bari ki sake fuskantar halin da ki
ka shiga a baya ba, idan har ina da halin da zan kwatanta hakan, duk da na san ba dabarar mu bace. Don haka ki dauki magungunan da na kawo ki yi amfani da su.” Kallonsa ta yi ta gefen idanu, sannan ta tabe baki, Ban taba sanin ba ka fahimci
ciwo na da abinda na ke fuskanta ba sai a yanzu. Mafarkina, babban burina duk duniya a farke ko a barci, shi ne na samu babies, sannan ka zo min da wannan magana da ta fi kama da alamara. Yaya ka ke tsammanin zan fahimceka bare na
amince da bidi’ar da ka zo min da ita? Yaya Zaid idan har ni ce zan sha wannan kafin ka zo inda na ke, to na yafeka har abada.” Adiyyah! Please ki fahimceni…” Mikewa ta yi ta fice daga dakin hade da bugo Kofar
Dakin, ji ka ke gam!
************
Kallo daya yayi mata da safe, ya fahimci kwana ta yi tana kuka, hakan ba Karamin karya masa zuciya ya yi ba. Sati guda suka dauka yana lallashinta kan ta amince su yi tsarin iyali, ya amince ko shi ne zai yi amfani da kariya, amma kamar me ingiza wuta a zuciyar Adiyya. Ta ma daina masa magana bare dariya. Haka suka kwashe tsawon kwanaki ana
wannan kwamacalar!WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Ranar da suka cika sati uku ne, ya shigo falon sama ya samu tana tsefe kanta. Gashinta ya bazu a bayanta da saman kafadunta a cike da shi baki wuluk! Sai sheki yake yi. Wariya kenan, shi ne ko a jirani na zo nayi tsifar ko?’ Sa hannu ta yi ta tufke gefe daya da babban abin daure gashi, sannan ta ce
“Taimakon da yake Kara kulle min kai, maimakon warwarewa ba.” Twinkle, Hajja Ku ma za ta sara miki yanzu kam a neman fad, daga tayin taimako?”
“Tunda ba ni na nema ba, ai da sauki, sai a barni.
Zama ya yi a kujerar da take, ya sa hannu ya karbi matajin gashin nata. Ya ajiye a gefe ya rikKe hannayenta. Me ya sa ki ke son ki tsiri abi’ar da ba ta ki ba? Ba kya tunanin hakKina ya kamaki
Adiyya? Rabona da ke watanni uku fa, tun kan na tafi Turkey. Yaya ki ke so na yi?”
Kawar da kanta ta yi gefe. KoKarin zame hannayenta take yi daga nasa. Shirun da na ke yi, da sararin da na ke ba ki, ba wai don ina jin tsoronki bane ko
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG