UMM ADIYYAH CHAPTER 44 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 44 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 


Iyayen nata kallonta suke yi kamar wacce ta zare, take kuma shirin kai hari. Abba ne ke da Karfin halin nanata abin da ta fada “Hauka dai!”
Maami kam cewa ta yi, “Iya shegen naki har haka ya kai ga haka? Tozarcin da za ki mana kenan? MaKaryaciyar banza, maKaryaciyar wofi…”
Tana shirin kunno wasu abin fadin ne. Abba ya dakatar da ita, “Khadija dakata, kar
ki zarge ta, tunda har ta yi tattaki ta fadi haka, hala tana da hujja ko ba haka ba?”
“Haba Abba, yaya ma za ka bada Kofar ka ce a saurareta, bayan muna ji, muna gani Karya ce tsuburu take shirya mana. Zaid din ke hauka, duk tsawon shekarun da muka san shi, ba mu gan shi da ita ba, sai ita ce mai idon ganin haukar? In ce dai ko
ke ce mahaukaciyar?” Umm Adiiyya ta taKarKare ta shiga muzurai har da jan majina, “Allah Abba ba sharri

na ke masa ba, da gaske na ke yi, kuma haukar da dare yake yinta, ya yi ta buge
buge. Shi ya sa ba wanda ya taba sani.”
Abba da Maami kam kallon juna suka koma yi, sai can Abba ya nisa ya ce, “Shi
kenan na ji batunki, zan neme shi, na tuntube shi da maganar ba, shi kenan ba? Ki shirya ki koma, gobe zan masa magana.”


Cikin kicdima da zaro idanu ta ce, “Abba yau ma fa da Kyar na sha. Allah ba inda zan koma, sai dai kawai su Faruk su je su kwaso min kayana…”
Hannu ta ji a bakinta. Maami ta kai mata bugu, “A kwaso miki kayan akai miki ina?” “Maami don dai kawai ba ku ga yadda yake yi bane. Allah ni kam yana ba ni tsoro.”
Maami kam har ga Allah a zuwa lokacin kallon Umm Adiyyar take yi a matsayin ita Www.bankinhausanovels.com.ng
ce ke da hauka, to banda sabon salo da fi’ili, yarinya da shegen tsatsibiri, wai Zaid ya haukace?
Har ta mike tana share Kwalla, uwar ba ta bar kallonta ba, daga baya ta maida
ganinta ga Mai-gidan, “Amma dai ba a gidan nan ka ke da shirin barinta ta kwana ba? Ai girma sai ya fad, haka kawai don ta zo ta gina mana labari, sai mu hau kai mu zauna? Ai ba daga sama ta fado ba. To gaskiya ni ban amince ba, don haka a daren nan, ba sai gobe ba, ni zan kira Zaid, ai shi din ba bakon mu bane.”
Har ta fiddo waya tana latsa lambar can nata. Abba ya ce, “Sai ki kira shi ki ce
matarsa ta zo gida, ta kira shi mahaukaci, ko me? Ai shi din da hankalinsa, kuma
tunda ya ji ta taho gida, hankali a tashe za ki gan shi yau din nan, ba sai gobe ba,
idan kuma ya kai goben ma, to zai fi, saboda kafin nan rayuka sun yi sanyi, sun
huce, sai ayi bayani a cikin kwanciyar hankali.”
“Hmmm! Amma dai kai ma da son zancen ka ke yi, yaya za ayi Ummu ta zauna ta Www.bankinhausanovels.com.ng
ce Zaid mahaukaci ne, ka biye mata, da dai a ce Zaid din wani ne daban to, haka kawai za ta kawo mana rashin hankali.” Ki dai bar maganar haka nan.”
“To yaya na iya, tunda ka ce.” Justice dai ta yi shiru, amma sai Kwafa take yi a ranta, ai sam baa kyautawa danta ba, haka kawai shari’a ba wanda ake tuhuma? Ai ko bata ida tunani ba, sai ga wayar Zaid, cikin sauri ta daga.
Daga dayan Dangaren ya amsa hankali a tashe, bayan sun gaisa ne ya ce, “Maami
don Allah kar ku yi mata fada, ku bar ta ta huce, koma meye sai ayi, ni ma ba zan shigo ba, sai goben.”
Cikin damuwa Maami ta ce, “Zaid yaya za ka ce kar ai mata fada? Shin ta fi Karfin
wani daga cikin mu ne? Ta dubi idon mu Fisabilillah ta kiraka mahaukaci. Gobe kuma me za ta yi?”
Wani irin faduwar gaba ne ya samu Zaid, yanzu duk fadin duniya Umm Adiyya ta rasa sharrin me za ta masa, sai na hauka? ‘Daya zuciyar ta ce, “To me ka ke so tace? Ka na neman matan da ba naka ba, ko kuwa shaye-shaye ka ke yi? Ko ka fi son
ta fadi gaskiyar komai?” Take ya ji gwamma dai sharrin haukar da ta dora masa ya fi dan dama-dama.
Amma a wannan lokacin, sai ya rasa amsar da zai bawa Maami, don haka ya shiga
ba ta haKuri. Tamkar Umm Adiyyar ce mai laifi yake kareta. Da kyar dai ta hakura akan sai goben, amma ranar dukkansu barcinsu ragagge ne.

**********

Ta dade zaune kan sallaya, bayan sallar Asuba tana wuridi, ba ta san lokacin da ta sulale jikin gado ba, har barci ya soma fizgarta, hucin numfashi kawai ta ji a saman fuskarta. Ba shiri ta ware idanu a hankali, don sam ita ba mai gigin barci bace. Www.bankinhausanovels.com.ng
Idanun da ta gani ne, suka sa sai da ‘ya’yan cikinta suka yi kuka. Maza ta yi KoKarin
gyara zamanta, amma nan da nan ya sa hannayensa karfafa ya hanata motsawa.
Take idanunta suka ciko da hawaye, ji ta yi kawai ta zunduma ihu ko za a kawo mata daukin gaggawa. Nan ma ya sa hannu ya toshe bakinta.
“Relax! Kar ki daga hankalinki, magana na zo mu yi Twinkle, idan ki ka yi ihu kuma
zan fita, ba tare da kowa ya sani ba, kin ga kuwa ke ce za ki zama mai haukar ba ni
ba.” Jin haka ya sa ta dan saki jiki kadan. Ya sa ya cire hannunsa daga bakinta.
Yana durkushe a gabanta yake dubanta ya ce. “Really? Umm Adiyya, hauka dai? Ni
ne na haukace? Har za ki dubi idon iyayenmu ki fada masu? Tsanarki har ta kai haka gareni ashe?
Na amince na yi kuskure babba, and I hate myself for it. Amma ki yi hakuri, ki min
sassauci, ba na cikin hayyacina ni kaina, bai dace na yi abinda na yi ba, in fact, ban
san zan iya aikata hakan ba. Ki yi hakuri, kar ki bari su sani, ki zo mu koma gida. Na
amince, duk yadda ki ke so, haka za ayi.”
“Don Allah ka tafi tun kafin nayi maka abinda ba za ka taba mantawa da shi ba.” Ta Www.bankinhausanovels.com.ng
fada muryarta cike da tsana, hawaye suna fita daga idanunta. Lumshe nagartattun idanunsa ya yi, ya shafo suman kansa, wanda take kwance a
kanannade tamkar na larabawa, suma dai na asalin fulani, har wani kyau ya Karawa
fuskarsa. Haushin kanta take ji, idan ta ji abu guda na Zaid ya burge ta.
“Please, ki natsu mu yi magana a tsanake, meye matsalarmu ne wai ke yanzu? Kar
ki bari mu sake fadawa cikin halin da muka shiga kwanaki, kar ki wahalar da mu, na
yi amanna da wuya za mu iya magance wannan matsalar ba tare da wani ya ji tsakaninmu ba. Me ki ke so mu yi yanzu?” Wani kallo tukun ta yi masa, wanda ita kanta ba ta san da shi ba, ba ta san yaushe wata dariyar takaici ta kubce mata ba. “Abin yi fa ka ke tambaya ta? Matsalolin,
wanne daya ka ke son mu magance? Na Kaurace min da ka yi? Oh! Na manta, ko wanda ka yi ta Kokarin dura min maganin hana haihuwa, ka na neman ka illata min mahaifa? Wane daya ka ke son ji? Oh right, lokacin da ka yi min fyade?” Da sauri ta mike ta bar jikin gadon hadle da bude Kofar dakin, “Ko kuwa har gaban
iyayena za ka biyoni, ka ida niyyarka, tunda burinka na Karasani bai cika baa gidanka?”
“Ya Subhaanallah! Umm Adiyya ki bar maganar nan, kar wani ya ji. Sau nawa zan ba ki hakuri ne?”
Hawaye kawai ta ji suna kwarara a idanunta, “Don Allah Malam ka fita, ai ni da
gidanka sai a wata rayuwar, idan har akwaita, amma wannan rayuwar kam na gama zaman wannan gidan.”
Yana kallon masifar da ke cikin idanunta, ya san za ta iya daukar ko wane irin
mataki, domin cimma hakan, don haka ya hakura. Ya san ko ba komai, su Abba za Www.bankinhausanovels.com.ng
su mayar da ita, idan ya biye mata kuma, to tabbas zai rasata. Shi ya sa ya yi yadda tace din, ya fice daga cfakin.

***********

Zaid ya yi sawu biyu zuwa gidan, amma kullum idan Umm Adiyya ta sauko, ba ta masa magana, haka zai Karaci magiyarsa ya yi gaba, ya yi ban hakurin har ya rasa me zai ce. Ga shi dai ta cewa su Maami ta hakura. Shi ya bar ta ta huta.
Ba damar ya ce ba haka bane. Amma da ya yi mata maganar komawa gidansa, sai
ta sa kuka, shi kuma tsoronsa Allah, tsoronsa abin da ya yi mata ya fito duniya. Gashi gaba daya baya samun walwala. Ko a wurin aiki, ya koma ya yi jagwab! Kamar ba shi ba. Wataran yana tafiya ma yana tunani, haka sha’anin dai ba dadin ji da gani.
Ranar da ta cika kwana takwas da komawa gida ne. Zaid ya ji gaba daya duniyarsa ta yi zafi, don haka daga wurin aiki, gidan Abba ya wuce, satin kaf, ba ta je aiki ba. Kai tsaye, ya wuce sama ya sameta.

******((

Tana nade Hijabanta, ta ji an murda Kofar dakinta na gidan Abban, daskarewa ta yi
da ta gan shi a bakin Kofar, a hankali ta ajiye hijabin da ke hannunta, za ta mike, amma cikin dogin takunsa biyu ya iso inda take. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba ta yi aune ba, ta gan shi kan gwiwowinsa ya rungumi Kafafunta yana cewa “Don
Allah Twinkle, ki yi hakuri, ban san kalaman da zan yi amfani da su ba. ki san cewa nayi nadama ki min afuwa.” “Yaya Zaid.” “Please… kar ki ce komai, kin fadi ma’ishi da shirunki. But it’s killing me… It’s just killing me.” “Yaya za ayi na yarda da kai, bayan kai ka kasance mai Konani da ababe masu
rikitarwa da zafin gaske? Sai yaushe zan ji dadin aurenmu har ma mu samu amintar
juna? Ban ma san me na ke ji ba a halin ” yanzu.
Kallonta yake yi kamar ta rikide ta zamo wata halitta. Daga bisani ya ce, “Lokacin da
na ke da tabbacin ba za ki gujeni ba, lokacin da na ke da tabbacin ba za ki fadawa su Maami, Zaid mahaukaci ne ba. Lokacin zan yarda na sakankance da ke Adiyya,
amma yanzu I really need you with me, Please.”
“Ba haka ake zaman tare ba Yaya Zaid, ba haka aure yake ba a duniyar gaske. Ni yanzu ba zan maka Karya ba, idan na ce maka komai ya Kare, na daina sonka. Bana sonka.”
A take ta ji riKon da ya yi mata ya saki, ya dago kansa daga Kafafunta, “No, no, no,
kar ki ce haka don Allah. Don alfarmar iyayenmu, ki KoKarta, ki daure ki yafe min mu
koma gida. Yau Maami har hawaye sai da ta kusa tayi min, tana roKon na yi hakuri da ke.
Ta zaci ke ki ka bata min, tunda ni na ki fadar komai, kunyar kaina da abinda na yi
ya hanani ce mata komai. Son kaina ya min yawa na sani, amma na yi wata Www.bankinhausanovels.com.ng
muguwar sabo da ke Umm Adiiyya, har ki ka zame min tamkar ke ce ruhina, ko
numfashina wahalar shaka yake min, dalilin
Bata miki da na yi… Amma na fada mata, ba laifinki bane, laifina ne.” Hannu ta sa ta share hawayenta. “Ka koma gida, zan dawo.”
Cak! Ya tsaya jin kalamanta, “Kin amince?”” Kai ta gyada masa, a hankali. Janyota
ya yi cikin jikinsa ya rungume tsantsam, idanunsa suna sheKin maiko suna nuna
tsantsar farin-cikin sa. Koda ya dago rike fuskarta ya yi a tafin hannunsa, ya hada
goshinsu wuri guda, yana zubar Kwalla, kamar ba shi Zaid Abdur-Rahman Nafada ba. “Na gode. Thank you so much.” Mikewa ta yi ta kauce masa, ta bar shi a durkushe a wurin yana bin ta da kallo.
Haka ya tashi jiki ba Kwari, ya san ta yi ne, ba don shi ba, sai don iyayensu.

************

Tana taya Maami hada abin karyawa ne washegari, amma gabaki daya ba ta cikin
hayyacinta. Tafiya take yi kamar wata mutummutumi. “”Ummu?” Ta ji muryar mahaifiyarta ta fito a tsanake. A hankali ta dago kanta tana
kallonta “Na’am Maami?” “Zo ki fada min menene yake damunki?”
“Maami…” Ta dan soma murmushi, sai kuma hawaye ya Dalle mata, jikin
mahaifiyarta kawai ta fada tana gunjin kuka, wannan ya tsinkawa Maami zuciya.
Sam ba ta son a kuma abinda ya faru a auren Zubaida na farko.
“It’s okay, babyna. Yi hakuri.” Hannunta ta ja zuwa falo suka zauna. “Menene?”
“Maami, yana yiwuwa mutumin da ka ke so, ka yarda da shi, ka ba shi komanka, ka zo ka daina sonsa?”
“Sai dai idan ba soyayyar ta gaske bace, dole akwai wani gurbi da ke rike da wannan a Kasan zuciyar mutum.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *