UMM ADIYYAH CHAPTER 46 BY AZIZA IDRIS GOMBE

 UMM ADIYYAH CHAPTER 46 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 



Daga wannan lokacin ta Kara debe darenta wurin bautawa Allah, dama tsayuwar
dare Cabi’arta ce, don haka Kaimi ta Kara akan na da. Ba inda take fita ta je, abinci
ma dai tana cinsa ne, don kar ta yi wa kanta illa.
A wata ranar Laraba ne ta bude Kofarta za ta sauka Kasa cikin doguwar rigarta mai
roba-roba, ta yi kicibis da shi a nan.
Idanunsa sun yi duhu, sun dan fada kwarminsu, amma har lokacin Kwarjininsa bai
bar shi ba, saukar da idanunta ta yi, saboda nauyin nasa idanun a kanta. “Lafiya ki Www.bankinhausanovels.com.ng
ke dai ko, ban ji ki ba jiya da yau?”
Kanta ta gyada masa. Kallon idanunta ya yi, yadda suke kumbure sun yi luhuluhu,
hannunsa ya daga zai shafa Kasan idanun, gaba daya ta canza kamar ba Umm
Adiyyarsa ba, mai murmushi da kawaici, da shiru-shiru, mai shiga rai da tsokana da
ban dariya da shagwaha da dirama.
Sai ya tuno alKawarin da ya yi mata, nan da nan ya maida hanunsa ya dunkule,
saboda wani matuKar buKatar riketa a jikin sa ya ji, ya ba ta hakuri, ya rarrasheta ya Www.bankinhausanovels.com.ng
zare mata ciwon da ya haddasa mata.
“Ehm! Ba kya zuwa aiki. Department sun yi korafi.”
“Oh! Na zaci kai ne shugaban wurin.” Ta facla a sanyaye, amma ya san ma’anar da
ke oye cikin kalamanta.

“Ahan, don haka ba shi zai sa ki yi sake da aikinki ba, abin da yake faruwa a gida
daban, da sha’ anin aiki, suna son su san kin bar aikin ne, ko ki na yi, za su tuhumeki
akan sakaci da aiki, idan ba ki koma ba. A tunanina sun fadi gaskiya.”
‘Hmm! Ka ce masu na bar aikin.”
Idanunta ya kalla, ya san ta facfa ne don ya ji haushi kawai. Haka nan babu wanda
ya yi masa magana, suna shakkar hakan, amma ai shi da ilimi yake aiki, ya san me


ya dace da wanda bai dace ba.
“Come on Adiyya, don’t be childish about this (kar ki mayar da batun nan shiriritar yara), wannan rayuwar aikinki ne daban da matsalolinmu, kar ki dorawa kanki wata damuwar ta daban.”
“Mr. Zaid Abdur-Rahman, I hereby resign from my position as the communications  Www.bankinhausanovels.com.ng
Engineer, at (AZ IT Consultants and Services). I hope this will serve as my official resignation. Ka fahimci yaren yanzu?” Langafe kai ya yi yana dubanta, hade da cije leben sa na Kasa kacfan, wani
gwauron numfashi ya sauke. “Ya-Allah! Adiyya, tun ba yau ba ki ke birkita min tunani da rayuwa. I love you so much, it hurts, ina so na ji na daina, in fact, na kwatanta mancewa da ke na cireki a raina, amma na gaza, kuma yanzu ba yadda na iya da ke, saboda ni na janyo komai. Ina tsammanin son da nake miki ne yayi yawa har hakan ya faru.” Nacfe hannayenta ta yi a Kirjinta, ta mayar da kanta baya kadfan had da daga habar ta cikin jajircewa. “Na ba ka amsata, ba na son aikin.” Ta fadla ba tare da ta kula da abinda ya facia mata ba. Put it in written, then. (Ki bayar a rubuce)” Ya mayar mata da amsa. Sannan ya juya
ya bar wurin. Don ba tantama saura kiris! Ya karya alkawarinsa. Lumshewan idanunta, tsumewarta, lobawar kumatunta, muryarta, daidai inda gashi yake kwance a goshinta, alamar yalwar gashin kanta mai laushi, wanda baya gajiya da shafawa…
Ya-Salaam! Komai game da Umm Adiyya yana hautsina masa Kwakwalwa da natsuwarsa ne. Www.bankinhausanovels.com.ng

*********

A falonsa ya tarar da ita ranar Alhamis, tana dan kada Kafafunta, da alama wani abu
take jira, kauda kansa ya yi zai Karasa ciki, sai ya ga ta ago ta dube shi. Gashin idanunta sun yi zara-zara, idanun sun yi fari tas! Da su, shaidar sun kwana biyu ba su ga gazal ba. Tashi ta yi ta nufo inda yake, “Yaya Zaid, ina so mu yi magana idan ka gama.” Jin hakan. Ya sa ya juyo yana fuskantarta. “Well, ga-ni nan ai, wani abu ne?” Murda yatsun hannunta ta shiga yi tana kallon Kasa, sannan ta dube shi kacfan, “Ehm, mu je dakinka?” Kai ya gyada mata, kansa a kulle, don bai san me take so da shi ba, bisa dukkan alamu koma menene wannan, ba zai so shi ba. Tana gaba, ya bi bayanta har suka hau sama. Tana zaune a Cakin nasa ya shiga ya yi wanka, ya samu ta cire masa kayan sawa.
Yanzu kam ya tabbatar akwai gagarumar matsala ba kadan ba. Umm Adiyya tana kula shi, tana nuna masa matsannanciyar kulawar da ba ta yi ba a cikin kusan
watanni biyar da suka shud. “Twinkle, ki bar kame-kame, ki fada min abinda ki ke so. Really zan ba ki. You don’t need to pretend (babu bukatar ki batar da kama).” Wani abu ta hadliya ta kawar da kanta gefe, hawaye kuwa suka ce salamu-alaikum.
“Kai ka bata komai. Sannan bayan wannan har ka na da Rarfin halin ja da ikon Allah. Ka nemi wasa da rayuwata, ba tare da shawarata ba. Idan kai ba ka son haihuwa ko zuri’a, ni na fadla maka nawa ra’ayin game da hakan, ba za ka fake da cewa don ni Www.bankinhausanovels.com.ng
ka ke yi ba. Idan don ni ne, ni clin na ce ba na so, ba shi kenan, sai ka bari ba.Ba ka san komai ba, ba ka san dubunnan mutanen da suke nema idanu a rufe ba,
kai ba ka ma san kai wace irin jarrabawa Allah zai ba ka ba, amma ni ka zahi da kcutar da ni. Na yi shiru ban ce komai ba, sannan upon all these, ka keta iyakar aure,kai min abinda ban taba tunanin makiyina ma zai min ba…” Kuka ne ya ci Karfinta,mai karya zuciya. Ya santa sarai, yanzu za ta birkice masa, wannan ya sa ya sauke ajiyar zuciya, ya matsa kusa da ita, “Adiyyah… Don Allah ki yi hakuri. Ina tabbatar miki da yanzu ba abinda na ke so irin kasancewarmu tare, amma abinda na yi, girmansa ya wuce komai. Ba ni da sukuni, duk lokacin da na aga idanu na ga ciwon da na haddasa miki a cikin Kwayar idanunki. Ban sani ba ko don abubuwan da nayi miki iya zamanmu. Allah Ya sa min wata jarabawa ta matsannancin Kaunarki da tunanin rasa ki kadfai
ya isa ya bar ni zaune ido biyu cikin dare.” Umm Adiyya kam Kwafa ta yi, ta share hawayen da yake biyo mata fuska. “Ka na nufin don kayi min wannan bayanin, shi zai daidaita abin da ka yi? Don haka
ka yi hakuri kawai, ina ga zan ci-gaba da cutar da kai ne, kai ma ka cutar da ni, so, ba zan iya zama ba. Ko yaushe na kalleka, rashin sonka ne yake neman kutsa kai cikin zuciyata. I can’t live with that, ban yi tsammanin zai kuma canzawa nan kusa ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Runtse idanu ya yi cikin tsantsar tashin hankali.
Twinkle na gane kuskurena, ba tun yau ba, a dalilin aurenmu, rayuwata ta daidaitu, na samu natsuwar da ban taba samu ba iya rayuwata, a kasancewa ta da ke. I mean.. Na sha yiwa Baffa abin alkhairi, amma ban taba ganin wannan alfaharin a idanunsa game da ni ba, har sai randa ya ga ina kareki, ina tare da ke, a dalilin Kaunarki, albarkar da na samu a rayuwata ba su da iyaka, ke alkhairi ce a gareni Adiyyatah…
Ki alhairi ce, kuma na ture wannan alhairin, a tunanina ina taimakonki ne, a tunanina ba na so na ganki cikin Kunci, sai ga shi a rashin sani na tura ki cikin Kuncin da kaina. A dalilin son kaina da ya min yawa. Ko don wannan ko yaushe zan ci-gaba da gode miki da kuma kimanta ki, domin darajarki ya Karu a idanuna fiye da zatonki.” Na san kamar yadda na ke fushi, haka ka ke fushi, amma akwai abu a raina, ba na son idan mutuwa zan yi na tafi da shi a raina. Zuciyata da nauyi sosai. Abinda ya faru… Ba ka kyauta ba. Amma ina son sanin, shin kai a ganinka aurenmu yana da
chance? Ni dai ban jin ci-gaba da…” Idanu ta cago, ta ga ya Kura mata nasa nagartattun idanun masu tsuma ruhi, su girgiza zuciya. “Abinda na ke nufi…”
Ajiyar zuciya ya yi, ransa ya Baci, baci kuwa ba na wasa ba. Wane irin wasa da hankali yarinyar nan take masa? Eh, ya san ya yi laifi babba, ba haka aka girmar da shi ba, ya tashi a cikin masu sanin hakKin ‘Dan-Adam, ya san darajar kowa da suke zagaye da shi. Amma wannan, bai hana shi munana mata ba. Amma abinda take masa, yana masa ciwo shi ma.
Duba nan, Umm Adiyya! Yaya ki ke so na yi? Na amince, idan har ina da laifi kan abinda ya faru, to ke kuma ke ki ka fi bada gudumawa.” ‘ago idanunta ta yi a zafafe ta kalle shi, cikin rashin yarda da kalamansa. “Eh, ke ki ka bada kaso mafi girma, kin san da cewa ranar me na kusa na aikata
akan halin da ki ka jefani? Don me? Ki na zaton halin da ki ka tsira, shi zai sa na yi miki yadda ki ke so? Wasu lokutan KaiKayi komawa yake yi kan masheRiya. Don haka ki yi yadda ki ke so. Na gaji. I won’t fight more on this(bazan yaki wannan al’amarin ba), idan har ki ka natsu, ki ka facdiawa kanki gaskiya. Lokacin sai muyi magana. Ni yanzu ba abinda zan iya ce miki kan tambayarki.” Yanzu so ka ke yi ka ce ni na janyo har kai min abinda kayi min ranar? Ka fada min
meye fa’idar ci-gaba da alaKar da ba ta da amfani? Kai ba ka sona, ba ka son hadla
zuri’a da ni, yaya zan yarda da kai kuwa? Ka je, ka yi abinda ka ga damar yi. Ka zo ka na ce min ni na jawo, bayan kai ka zo ka keta min haddi. ”
For Allah’s sake Adiiyya, you are my wife(ke matata ce)! Ina da damar na yi mu’amala da ke, idan kin hana ni, akan na bi na waje gwamma na dawo gareki,
koda a ace ya kama na Kwata ne a wurinki. So be it.” Take kuma ya yi da-na sanin furucinsa, domin yadda yake ta ba ta hakuri tamkar ya warware wannan furucin nasa ne, hakan na iya sawa ta yi tunanin ba da gaske ya yi nadama ba. “Ka sakeni to. Na gaji da zama matar taka, tunda ba a dole, sai ka sakeni kowa ma ya huta.” Ta fada cikin daga murya. Tun farkon rikicinsu yau ne rana ta farko da ta Www.bankinhausanovels.com.ng
aga murya sosai har tana Hari. Zaid ya yi shiru yana kallonta na tsawon lokaci, Kafafunsa ne ya ji sun sake kamar ba za su iya Caukar nauyinsa ba.
Dakin ya yi shiru kamar an dauke wutar (NEPA). Hawaye ya sulmiyo a idanunta, ta
sa bayan hannunta ta goge idanun.
“Fine! Ba na son mu rabu, amma a haka ki ba ni damar ganin Twinkle dina a karo na
Karshe kafin ki tafi. ”
Labhanta ta hada wuri daya da haKoranta, cikin KoKarin danne kukan da ke
barazanar kubce mata. Da gaske barinta zai yi ta tafi? Me ki ka aikata Umm Adiyya?
Hannunta ya riKe cikin nasa, ya Kare mata kallon tsab! Kamar wanda ya warke
ciwon makanta. Sannan ya ce, “Kin san wani abu? Son da ki ke min babu kamarsa,
domin kuwa a tsawon lokacin da na ke tare da ke, kin Kara kusantar da ni zuwa ga
Allah.
Akwai son da ya wuce wannan? Zan illatu ainun, idan na rasa ki Twinkle. Ban so ki
kayi min wannan furucin ba, bai dace da ke ba sam. Amma na gode. Sai da safe
Twinkle, ki kula da kanki.” Rie kanta ya yi cikin tafukan hannunsa, ya sumbaci
saman kanta, idanunsa a lumshe, sannan ya sake ta.
Fita ya yi daga Clakin ba tare da ta gama gane manufarsa ba. Hakan bai bar caure
mata kai ba, sai da ta samu saKonsa da safe.
“Ni Zaid Abdur-Rahman, na saki matata Umm Adiyya bukar saki daya, idan ta samu
miji, ta yi aure.”
Hayawe masu zafin gaske ne suka zubo daga idanunta, ta runtse idanun. “Yaya
Zaid son na’urarka ya fi son da ka ke min, sakin ma ta SMS za ka turo min? Ba za
ka ba ni damar ganin kyan rubutunka ba, a karo na Karshe?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Wuni ta yi Kasan claki, ba ta motsa ko ina ba.
Innayo ce ta ji shirun ya yi yawa,
hakan ya sa ta Karasa dakin Umm Adiyyan, don ta ga ko lafiya? Haka ta same ta a
zube a tsakar akin shame-shame kan Carpet, nan ko ta shiga tambayarta ko
lafiya?
Innayo dai ganin ba ta motsa ba, abin sai ya ba ta tsoro, ta kidime. Wayar Maami ta
nema, ba tare da Data lokaci ba.
“Eh, ina ga ba ta da lafiya ne, shi ma Yayan ya fita baya gida.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“To ki zauna tare da ita, zan taho yanzu.” of oie 2 2

*******

BABI NA TALATIN DA BIYU

Innayo dai sai gyaCla kai take yi kamar Kadangaruwa. Ita dai ta san koda rashin
lafiyar ma, akwai babbar matsala tsakanin uwayen gidan nata. Don cikin kwanakin
nan dukkansu babu mai walwala a gidan, kai an yi watanni ma ba walwala a gidan
nan, sabanin zuwanta a karo na farko yadda ta sansu.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *