UMM ADIYYAH CHAPTER 54 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 54 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

A hankali bayan aurensu ya shagaltar da ita da nasa salon soyayyar har ma ta saki jikinta da shi.
Wannan ya sa lokacin da ya zo mata bagatatan, ta razana har ma kwakwalwarta ta
koma ta kafe akan cutar da ita kawai zai yi, yana tariyo mata ranar da ta tsira da
Kyar a hannun Mijin Hajiya, a taKaice a take idanunta suka koma ganin mijin Hajiya,

maimakon Yaya Zaid.

********

Hannaye ta ji sun tallafo kafaclunta, ai ko nan da nan ta fadla cikin rikon Maami tana
kuka mai karya zuciya.
“Ba laifinki bane Ummu, ki daina kuka kin ji? It’s natural, ki ji abinda ki ke ji na tsoro da rashin sanin madafa, da rufewar kai. Amma fadan abinda yake damunki, shi ma yana taimakawa Kwarai. Ashe ba ki yarda da Maaminki ba Ummu?” Maami na yarda, Maami na yarda. Ba ma son hankalinku ya tashi ne, shi ya sa muka yi alKawarin babu wanda zai sani.”
Justice Khadija ta fahimci a guntun tunani irin na yaranta a wancan lokacin, ya nuna masu cewa yin shirun shi ya fi sauki. “Umm Adiyya, ban san me ki ke ciki ba, ba zan kuma taba sani ba, amma ki sani na


damu da ke sosai, damuwa mai zurfi, idan har ki na so ki yi magana kan abinda ya faru. Zan saurareki. Ina so ki saki jikinki, duk lokacin da ki ka shirya magana akai, Www.bankinhausanovels.com.ng
kawai ki fadla, kin ji? Muna sonki sosai, duk abinda zai faru da ke ba za mu taba
gudunki ba, don haka kar ki bar abu a cikin ranki, kin ji? Ki rinKa magana.”
Kai ta shiga gyadawa Maami, ita ma tana share hawaye yaran na sharewa.

***********

A daren Justice Khadija ta samu Mai-gidanta ta ce masa, “Akwai matsala fa.”
Juyowa ya yi ya dubeta, saboda iya tsawon shekarunsu matarsa ba ta taba fasa
masa Kwan labari ta wannan hanyar ba, haka nan ba ta taba samunsa kai tsaye ta
tuhume shi ba, bare ya yi tunanin abin da ke nan. “Matsala kuma?”
Nan ne ta zauna sosai a bakin gadonsa don tayi masa bayani, sai kuma ya ga tana
hawaye. To shi kenan, daga nan ya san lalle matsala ce gagaruma.
A hankali ta zayyane masa duk abinda ya faru. Abba kam tsantsar mamaki da
razana sun hana masa cewa komai. Maami ba ta jira ya ce Clin ba ta ce.
“Tana buKatar taimako. (She has been reaching out for help), tuntuni muna tunanin
taurin kanta ne da kafiya da rashin sanin ciwon kai. Amma taimako take buKata
gaskiya yanzu, domin abin nan ya taba Kwakwalwarta fiye da tunaninmu.”
“Amma kun ce… bai yi..”
“Abba, shi fyade ai, masu yinsa ba don su samu wani abu na gamsuwa suke yi ba, Www.bankinhausanovels.com.ng
wannan tsoron suke Kwata daga victims dfinsu. They feed on the fear, ta kuma rasa
shi. Sai mun tsaya mata sosai, don tana cikin wani irin hatsarin da ita kanta ba ta
sani ba, ta tara abin nan ta kulle a cikin kanta, na tsawon shekaru tara. Addu’o’i za
mu na yi mata, sannan dole ta fara ganin Likita.”
“Likita kuma har yanzu ba lafiyar ne?”
Maami ce ta dubi Abba, ta san ya fita razana, don tuntuni ya kasa yin KwakKwarar
magana ta natsuwa.
“Likitan Kwakwalwa na ke nufi Abba.” A lokacin idanunsu suka hadlu. Maami ta gyada masa kai a hankali.
Hawaye ne ya gangaro daga idanunta, hannu Abba ya sa ya riKota jikinsa, yana
shafa bayanta cikin lallashi, kafin ta ji ya yi ajiyar zuciya, sannan ta ji digan ruwa kan
fuskarta. Ya Allah!

*************

BABI NA TALATIN DA SHIDA.

“Da gaske ki daina dariya, it is not funny (Ba abun dariya bane).”
Maman Abul ta yi shiru, kamar yadda ta buKata na ‘yan sakanni, “Da gaske, har na hango ku.”
Muguwa, ta Allah ba ta ki ba. Allah, ki ga mutum gemai-gemai da shi ya yi sa’an
Abba, idan bai fi shi ba, ko kunya ma baya ji.” “Wai ke yaya ma aka yi ya sani ne?”
“Oho masa, tunda ba liKawa na yi a goshina ba
akan miji na ke nema, iya sanina
cikin wurin nan kaf, kowa a matar mutum yake yi min kallo.”
“Daman an san ke matar mutum ce mana, amma mutumin da babu shi ba. Da gaske
ki ba shi dama, kin ga ya hadfar da ke a course dinsa ko ba komai.”
“A mutu kar na haye.” Umm Adiyya, ta faca hacfe da juya idanunta. “Ni dai koda
wasa na zo na ce maku ina son Malam Yusuf, ba ni bace ku je ku min ruKiya aljani
ya turo min, don ba zan taba sonsa ba har abada.”
“Me ya yi zafi, ko kin ce ki na so za mu mareki, ki shiga taitayinki.”
Suna dariyar abin, suka iso daidai motar Maman Abul. “Sai da safe, ki gaida su Abul Www.bankinhausanovels.com.ng
khairi,” “Ba gida za ki yi bane? Sai mu je na ajiye ki.”
“A’a, ni kam kasuwa zan yi, daga nan, zan karBawa Adda Zubaida kayan cake dinta,
kin san yanzu fa ita babbar ‘yar kasuwa ce, order wannan na tafiya wannan ke shigowa.”
“Ai na ce ki fada mata ta bude wurin koyarwa lyawan ya kai inda ya kai, kin ji wanda
ki ka ba ni rannar ma Baban Abul cewa ya yi gaskiya zai bada a masa babba. Ki
shigo na sauke ki a gate.”
Umm Adiyya tana dariya ta bude marfin motar sannan ta ce “To sai kinzo, zan fada  mata tana da student, ni dai bar ni da kaiwa jama’‘a da kuma ci, ta dage sai na koya banda abin saman ba abinda na iya.”
“Ai kin yi mai wuyan.” Maman Abul ta fada lokacin da suka isa gate din, nan Umm
Adiyya ta sauka, inda ta tsaya domin ta dauki abin hawa, kasancewar motarta da ta
taho da ita daga Abuja tana wurin gyara, Adda Zubaida ce ta ajiye ta cikin
makarantar da azahar, sannan ta wuce gidansu Baban Walid inda ake biki. Yanzun
ma ga shiga kasuwa a gabanta, ga hadari da ta hango ya cika gajimare ta gabas.
Bata dade da tsayawa ba ta samu abin hawa kasancewar sun saba daukar dalibai
da ma ma’aikatan da suke fitowa daga jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchin.
Tana shiga Napep din ta fadi inda za ta je,
kuwwar wayarta ce ta ja hankalinta har ma ta bude jakarta ta dauki wayar.
“Ummu A, Allah sa baki manta sakona ba, ga ruwa nan ya iso. Kin hango gabas din nan kuwa?’
“Yanzu dai na ke hanyar kasuwar, zan yi sauri.”
“To shi kenan don Allah kar ki tsaya sanyi, gobe za su karba idan Allah ya kai mu.”
Tana dariyar Adda Zubaida ta kashe wayar.

***********

Abubuwa da dama sun faru a rayuwar Umm Adiyya a cikin watannin da suka shige,
abubuwan Karuwa da ci-gaba, da na jimami da na farin-ciki. Ciki kuwa har da Www.bankinhausanovels.com.ng
komawarta makaranta, domin kammala digirinta na biyu, bayan ta dawo gaban Adda
Zubaida da zama. Baban Walid da Adda Zubaidan suka ba ta shawarar yin hakan.
Sannan a wannan watannin ba ta taba jin kanta fayau ba tare da wani nauyi da ke
tattare da ita, ko boyayyen fushi ko kuma wani
Hatanci na zuciya ba, baya ga abinka
na yau da kullum da za ta ce su ake kira rayuwa.
Tunda Maami ta ji labarin abin da ya faru, ita da Abba suka Kara janta a jiki, suna
lailayarta kamar Kwan da za ta fashe. Har cikin ranta hakan ya mata dadii fiye da
komai. Musamman duba da halin da ta samu kanta a wannan gaba na rayuwarta.
Wannan ya sa Sati guda bayan faruwar hakan, ta shiga har dakin Maami ta sameta.
Kallonta take yi bayan ta fadii abin da ya kawo ta. “Maami na shirya.” Ta ce. Kin shirya me?”
Yatsun hannunta ta shiga murzawa da daya hannun, kanta a sadde a Kasa ta ce,
“Ranar kun ce duk lokacin da na shirya za mu je mu ga Likita. Na shirya.” Maami ta lumshe idanu, cikin jin dacli matuKa. Hannun Umm Adiyya ta riko ta zaunar da ita a gefenta.
“Ba komai Inshaa-Allah, nan da nan za ayi ya wuce. Hakan shawara ce mai kyau ki
ka yi. Allah ya kawo Karshen komai, ya Kara maku lafiya baki daya.” Ameen.” Ta amsa Kasa-Kasa.
Ba tare da Hata lokaci ba, suka wuce asibiti washegari, kasancewar sun gama duk binciken da ya dace, sun samu asibiti da ma Likita dai-dai matsalar Umm Adiyya. Dr.
Astha sunan Likitar da za ta rinKa ganinta, kasancewar ta Kware a bangaren warkar
da masu ire-iren matsalolinta. Mace ce mai yawan fara’a, ga ta a natse, don haka a sannu a hankali ta fara bi da Umm Adiyya, ta inda ta fara da tambayarta kai tsaye akan tana so ta ba ta labarinta. Umm Adiyya ta fara ba ta tarihin karatunta da garin da ta fito. Dr. Astha ta bar ta,
saida kai aya ta ce, “Labarinki na ke so. Ki facla min duk abinda ya faru randa aka
kai miki hari, daga farkon lokacin har zuwa lokacin da ki ka yi barci a ranar, ina son
na san komai, idan zai yiwu har kalan kayan da ki ka saka ranar ina so ki ba ni
Jabari.”
Umm Adiyya ta yi shiru tana kallon Likitan, ita da take cikin tashin hankali, yaushe za
ta wani tuna komai da ya faru ranar? “Ko ki na so na kira Mama ta shigo?”
Da sauri ta gyacla kanta, don ba ta yi tsammanin za ta iya ita kadai ba. Wannan ya
sa Likita da kanta ta koma ta kira Maami cikin ofishin, nan aka sake farawa.
Umm Adiyya kam ta dage ita ba za ta iya tuno komai ba, ta ba su labari sama-sama yadda Asma’ ta fadawa Maami. Likita ta yi murmushi, tayi masu godiya ta ce sai sun sake zuwa.
Suna fita ta ce, “Maami, wannan Likitan ta san me take yi kuwa? Tunda na zo fa ni
kacfai na ke ta Magana, banda kallo ba abinda take yi.” Maami ta yi murmushi ta ce, “Ba damuwa, next zuawanmu za mu ji ko za ta yi mana tambayoyin kuma.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani karon da suka sake komawa, hakan dai
aka kuma, Likita ta sake sawa ta ba ta labarin duk abinda ya faru.
Da aka yi na uku sak, ba canji. Umm Adiyya ta ce, “Maami baki na har ciwo yake yi,
matar nan, ina ga ba ta san me muke zo yi ba.”
“Me muka zo yi?” Mami ta mayar mata da tambayarta.
“Neman lafiya?” “To, waye kuma Likitar?” “Tta.”
“To kar ki damu, a sannu a hankali komai zai tafi daidai.” Yanzun da Maami ta zauna
ta ji komai da kunnenta, abin ya Kara kashe mata jiki, amma abin mamaki kullum Www.bankinhausanovels.com.ng
aka zo wannan zaman labarin. Adiiyya sai ta tuno wani abin sabo. Har ya zamana ba
ta Car-dlar idan ta zo ambaton sunan mijin Hajiya. Sai da aka shafe watanni suna zuwa wurin
Doctor Astha, tana sabunta masu
hanyoyi da dabaru, har ya zamana Umm Adiyya da kanta ta san cewa tana jin canji

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *