UMM ADIYYAH CHAPTER 57 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
Lafiyarsu Kalau, ta ce ta daina ganinka kwatakwata.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushi ya yi ya maida hankalinsa kan titi. “Na ji kin koma karatu, hakan yana da
kyau ai.”
“Ka yi aure.” Ta facla tana kallon titin da ke gabansu.
Murmushi ya yi, ya kawar da kansa kacfan, sannan ya juyo ya kalleta, “Yes, I am
married.”
“Har ma da ‘yarku, tana kama da kai, kyakkyawa da ita ‘yar dagwas. Na ga hotonta
a wayar Maman Walid.” Ta fada murmushi
makale a fuskarta.
“Kar ki sani tunanin, kina ganina a matsayin dan ddagwas.”
Harara ta dan masa a fakaice. “Haba Katoto da kai, ai sai ayi abin kunya.” Dukkansu
suka sa dariya, tana kallon gefen hanya suna tafiya. Bayan shiru ya gifta masu na
kusan tsawon minti biyu ne. Kamar daga sama TJ. Ya jefo mata tambayar.
“Har yanzu ki na son tsohon mijinki?”
Ba shiri Ummu Adiyya ta kusa ta Kware da yawunta, tari ya sarKe ta kaddan, sannan
Www.bankinhausanovels.com.ng
ta ce “Wannan tambayar ba ta huruminka, Uncle TJ. Kwanan nan ka yi aure, don
haka idan ma ka na tunanin wani abu ne, ka ma daina, ba lalle bane na sanar da kai
ko ina son tsohon mijina ko ba na sonsa.”
‘“Ummu Adiyya har yanzu ki na son tsohon mijinki?” Ya sake nanata tambayarsa ba
tare da ya damu da abinda ta fada ba. Juyawa ta yi ta dube shi baki a bude, ta ma
rasa me za ta ce. A fakaice ya kalleta ya bar ganin kan hanya.
Take kuwa suka yi gaba saboda birkin da ya taka a dalilin iso wata mota daf da ya
yi, bai san wuta ta tsayar da su ba.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ka ga abinda zai rinKa faruwa idan har muka hadu ko? Akwai hatsari duk lokutan
da muka hadu.”
“Har yanzu ba ki manta da kukar da ki kai min wanka da shi ba ko? Ga kek duka ni
kadai, idan da mai damuwa a cikin wannan lamarin, ina ga ni ne da ake ta min
kware-kware.”
Murmushi ta yi, “Ka mance komai ka ci-gaba da rayuwa, ina son abin ya tsaya a
haka. Ba na son mu wuce gona da iri.”
“Haka ki ka ce?” Ya fada hade da mata wani kallon da ya sa tsikar jikinta ya tashi.
Kau da kanta ta yi ta hadliyi wani busasshen yawu. Dai-dai lokacin suka tsaya a
Kofar gidan Adda Zubaida, ba wanda ya kai ta farin-ciki a wannan lokacin.
Tana sauka a motar ne, ta taba goshinta ta ji zufa. Me ke damuna ne wai yau? “Ummu Adciyya…” Ya facia a tausashe, tana juyowa ta ga wannan murmushin sa na
makale a fuskarsa, “Idan har kin canja shawara, kin san me ya kamata ki yi.”
Tsuke idanunta ta yi tana kallon shi cike da mamaki, “Me kake nufi? Mr. Ahmad
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tijjani Muhammad. Ba dai ka na tunanin na kiraka a waya ko na tura maka saKo ina
fayyace maka soyayyata marar yankewa bane ko?”
“A hakiKanin gaskiya, wannan zai iya fin komai dadfi da sanya ni farin-ciki. I’m looking forward to it (ina saurare).”
“Za ka dade ka na jira ashe.”
“Ina da dan guntun hope ai, tunda dadewa zan yi wurin jiran ba mutuwa ba.”
Murmushi kawai ta yi, ta kadla kanta, sannan ta sa hannu za ta bude Kofar falon. Sai
dai kan ta ida budlewa, an wangale Kofar. Adda Zubaida ce a tsaye a gabanta, ba ta
yi tsammanin tana farin-cikin ganinta ba a wannan lokacin, don haka kai tsaye ta
wuce Cakinta. Tana jin takunta a bayanta har ta
iso cikin Cakin. “Ummu A?”
“Ki kwantar da hankalinki. Adda Zubaida ba abinda zai faru.”
“Kin tabbata? Daga yadda na ke ganin al’amura komai ma ya faru, an gama. Me ki
ke so ne da rayuwarki? Ki na so ne ki zo ki shigewa mata gidanta da ba ta gama
gina shi ba ko kuwa me? Shekararsa dlaya da rabi da aure Adiiyya!”
“Adda Zubaida da dai kamar ke ki ka fi so na auri Uncle TJ. Ba wai ina nufin yanzun
auren shi na ke da shirin yi ba.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Da ki ka ce Ummu A. Da! Ba yanzu ba da yake da mata, matar da take girmamani
take jin kunyata, da ‘yarsu jaririyar wata bi
9°
yar.
“Na ji dadin jin cewa kin hutassheni da cigaba da samun sabuwar rayuwa.”
Ta fad tana kallon ‘yar-uwarta. Adda Zubaida kam bakin gado ta kama ta sulale ta
zauna.
“Yaa Salam, ki yi haKuri Adda ban yi niyyar fadan hakan ba. Ban san me yake
damuna ba kwanan nan. Ina jin kaina cikin kunci da takura . Kai na ya kulle, ina ji
kamar zan fashe, a saman wannan duka, ko wani mutum da dfan zafin kansa ya
kwaso hanya ya zo wai shi sona yake yi. Na yi masu kama da me neman soyayya
ne, ko na ce masu ni din araha na ke da shi, don kawai na taba aure?”
“Arha ki ke da shi Ummu Adiyya. Eh, suna da hanyar da suke nunawa mutum yana
da arha butu bulus, a ganinsu kin zubar da martabarki a lokacin da kalmar nan ta
zawarci ta haura kanki.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Me ya sa ki ke tunani maza suka fi bin kan zaurawa da sunan so? Saboda suna
tunanin you are just desperate, za ki iyayin komai, don ki samu rufin asirin komawa
rayuwar aure, wasu kam ma da ba su rike kansu ba gun zaurawan suke komawa
suna cashe rayuwarsu saboda a ganinsu sun riga sun saba da rayuwar aure, za su
iya bin koma waye don su samu natsuwarsu.
Ba na son hakan ta faru da ke Ummu Adiyya, ba ko ina ake samun irinsu Baban
Walid ba. Ya aureni yana saurayi, ina matsayin wacce ta taba aure, amma ban taba
ganin wanda duk duniya yake min kallo na girmamawa irinsa ba, bai taba ko gigin
rike hannuna ba lokacin da yake neman aurena.
Amma ba hakan bane ya hana shi iya zama nagartaccen miji, gawurtaccen masoyi
ba, ko kuma Uba na gani a fadfa ba. Ina so ki tattara tunaninki wuri guda, kar ki yi
gaggawa, ki yi zaben tumun dare.”
Ummu Adiyya ta share hawayenta, “Adda yanzu kin sa na ji ina son na kira TJ. Na
Www.bankinhausanovels.com.ng
ce ya ZO mu zanta, irin yadda mazan gidansu suka iya tarairayar macen nan haka?”
Adda Zubaida ta dankwaleta “Kaniyarki, ni sa’arki ce? Ki mance da batunsa, a
yanzu dai .”
“Na ji, tun asali ban sa shi a raina ba, duk da kuwa babu abinda ya rasa da na ke so
a mijin aure. A taKaice yanzu da muka yi maganar, Sai na ke ganin wautata da tun
farko me ya sa ban amincewa soyayyarsa ba, mutumin kirki ne na karshe.” Ganin
hararar da ‘yar-uwarta take mata ne, ya Sa ta tuntsure da dariya.
“Meye? Shi kenan kuma sai na hakura don ba kya so ayi wa ‘yar Cakinki kishiya?”
“Yaya Zaid, Ummu A…” Shiru ne ya ratsa kadan a dakin.
Nan da nan Idanun Ummu Adiyya ya kawo hawaye, “Shekara guda fa yanzu Adda,
ina ga zai fi kyautuwa ace kun cire ranku gaba Claya, ba za mu sake komawa ba.”
“Na ji labarin ya kusa zuwa fa.”
Idanunta ta kifta na tsawon dakikai biyar ba ta ce komai ba, kan ta ce “Oh, Allah ya
kawo shi Kalau.” A take ta ji makogwaronta yana toshewa. Gyara murya ta yi ta
hadiyi hawayen da suke son zubowa daga idanunta.
Ta dade da jingine shafin Zaid Abdur-Rahman a rayuwarta, ko kuma dai a iya yadda
tunaninta yake son tsayawa, ya zama kamar shudadden babi. Ba abinda ta sa a
gaba, sai karatunta da ‘yan yaranta, ita yanzu aure ma baya burgeta, ji take yi za ta
iya gama rayuwarta a haka.
Idan banda abu irin na yau ya kasance, wani ya kawo mata batun aure, tana ma
mancewa, face wasu lokuta Kalilan, wanda dole ne ta ji gibin wannan gurbin… Ya
tunaninta yake son tsayawa, ya zama kamar shudadden babi. Ba abinda ta sa a
gaba, sai karatunta da ‘yan yaranta, ita yanzu aure ma baya burgeta, ji take yi za ta
iya gama rayuwarta a haka.
Idan banda abu irin na yau ya kasance, wani ya kawo mata batun aure, tana ma
mancewa, face wasu lokuta Kalilan, wanda dole ne ta ji gibin wannan gurbin… Ya
Rahaman! Soyayyar Zaid Abdur-Rahman Nafadfa ta yi mata illa a rayuwarta.
26 26 2 2s fe 2s is 2 2 2k 2 og ok
“Eh na san za a samu ‘yar matsala ta wannan wurin, ban sani ba. Kawai ku je ko
Baffa Mai-Kano ku samu da Yaya Nazeef din zan yi KoKarin na shigo nan da sati
biyu Inshaa-Allah.”
“Amma Zaid ina so ka sake tunani kafin dai a yanke komai.” Salisu ya facia daga
Claya Bangaren.
“Haba, dan group, ya kamata ka sani, ba na wata tantama, kai ma ai ka ganta and
Rahaman! Soyayyar Zaid Abdur-Rahman Nafadfa ta yi mata illa a rayuwarta.
26 26 2 2s fe 2s is 2 2 2k 2 og ok
“Eh na san za a samu ‘yar matsala ta wannan wurin, ban sani ba. Kawai ku je ko
Baffa Mai-Kano ku samu da Yaya Nazeef din zan yi KoKarin na shigo nan da sati
biyu Inshaa-Allah.”
“Amma Zaid ina so ka sake tunani kafin dai a yanke komai.” Salisu ya facia daga
Claya Bangaren.
“Haba, dan group, ya kamata ka sani, ba na wata tantama, kai ma ai ka ganta and
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG