UMM ADIYYAH CHAPTER 59 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 59 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

TJ dai ji yake yi kamar Juma’a ta yi nisa, yana shiga gida, ya tarar da Rahma da

Minaal sun sha kyau cikin kyakkyawar shiga. Da fara’arsa ya isa garesu, ya Cauki

baby Minaal ya fara mata wasa, ita kuwa tana ganin sa ta fara KyalKyala dariya.

“Za ka zarar min da yarinya Wallahi. Wannan dariyar ai ta fi Karfin jinjira.”

“Wannan ce jinjirar? Ki na ga yarinya da wayonta, tana hira tana gayu tana zama, ki

wani ce mata jinjira, ai an mana demotion, ko bayb princess?

“Kwa dai ji da shi ku kadai, kun ce mata baby, kun ce kuma ba jinjira ba.”
Minaal na kafaclarsa ya shige ciki, don ya kimtsa ya rage kayan jikin sa, zuwa
Kanana. Sai da suka shiga, ya juyo ya dubi Rahma.
“Meye?” Ta fada tana gimtse dariyar fuskarta.
“Kin fi ni sanin meye ne ai, wato ke za ki yi wayo ki zille, to ban manta ba.”
Hannu ya sa ya zagayeta cikin riKonsa, “A’a na sani ko ganin ‘yarka ya dauke maka hankali.?”


“Ke ma kin san ita ce first love dina ba yadda za ayi ki ture mata gwamnati.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ni ko na san da haka, tunda har yanzu ta like mana tana faman bibiyarmu.”
Kura mata ido ya yi, “Yi bayanin kalamanki, kin san ni Cin fa na ashirin na ke zuwa a makaranta, ba lallai bane na fahimci maganar da aka yi cikin dabaibayi.”
“Minaal. Ka zaci ban san sunan waye bane ko kuwa ban san cewa yanzu ta kashe aurenta bane, tana like da kai.” Kan TJ. Ne ya sara a lokaci guda, ya ji zufa a goshinsa ya tsattsafo, domin a iya saninsa, bai taba gwada mata wani abin da zai sa ta yi tunanin ko ya koma wurin Umm Adiyya ba.
“Me ya kawo wannan zancen kuma?” Ture shi ta dan yi kaclan, nan take ya san ta yi
fushi sosai, don ba ta cika nuna fushinta ba. Wata Kila wannan ya hana shi gane
cewa ta dau haske. Hannu ta sa ta karbi Minaal daga hannunsa. Haba Abba, wayar ka kullum na manne da kai, kamar Clan sandan ciki, motsi kadlan ka tafi Bauchi, ina sane da cewa ta kashe aurenta kuma ta koma gidan Yaya Isma’il
da zama. Bini-bini ka tafi wai ganin yaran yayanka. Ka manta da cewa kwanan nan ka dauko ni daga gidanmu, ko fuskar jerena ban canza ba, shi ne har idanunka sun fara yawo akan wata.
Hakan duk bai isa ba, na zo na fahimci cewa wa tsohuwar budurwarka ka yiwa ‘yata
mai suna, imagine me ka ke tunanin zan ji? Ka tsalleke uwata, ga Hajiya ita ma ka
tsallaketa, sai Ummu Adiiyya za ka saka. Me ya sa na sa mata inkiya? Tun a suna Www.bankinhausanovels.com.ng
aka fada min me asalin sunan, ni kuma ‘yata ba za ta amsa wannan sunan ba. Don
haka idan za ka daina nuna mana soyayyar bogi , ka tafi asalin wurin first love dinka ka nuna to, da zai fi mana.”

*************

BABI NA TALATIN DA TAKWAS

Wani numfashi ne ya kufce daga Rirjin TJ. Ya lumshe idanunsa, sannan ya Kara taku
Claya gareta. Kafaclunta ya riKe ya juyo da ita tana fuskantarsa.
“Rahma.” Ya facia idanunsa a lumshe kadan, “Kin san da cewa ina sonki ko?” Tabe baki ta yi, ta yi Kwafa hade da kau da kanta gefe. Hmm! Ka dai fadawa Minaal.” “To idan yau na mance ban fad ba, ina so ki sani ina sonki. Kuma sam ba na son
sabani da rashin fahimtar juna ya shigo cikin zamanmu. Zauna ki ji nayi miki bayani.” Bakin gadonsa ya zaunar da ita, ya zauna a gefenta hanunta Claya da baya rike da Minaal na cikin nasa, ya ce.
“Eh, sunan Ummu Adiyya na sakawa Minaal. Amma ban sa mata don cin fuska ba ko kuma don na Hata miki rai ba, sai don kawai kwadlayin ta yi kyawawan halin mai sunan.” Rahma dai bude idanu ta yi tana kallon ikon Allah. “Ko ba ke ba, ko ita ce a madadinki tsarina ne, na sakawa ‘yata ta farko wannan sunan, idan Allah ya azurtani da samun ‘ya mace. Saboda tarihin da ke tafe da sunan. Idan kin ji kamar na tozarta ki da yin hakan, ki gafarceni. Amma ina so ki sani, ke ma ki na da muhimmanci a wurina kuma da kaina na ganki, na je na nemi aurenki, akwai abinda ya fi wannan shaidar Kaunar da na ke miki?” Bai kai ai ka jirani na fito daga wani gidan ka Www.bankinhausanovels.com.ng
koma min ba, da alama.” Goshinsa ya tallafo, “Allah, kin koyi rigima Rahma, yes, na fara mata magana muna gaisawa, amma ban ce ina son na aureta ba, ban ma dade da sanin ta dawo gida ba.”
Hawaye kawai ya gani suna gangarowa daga idanun Rahama, tana gimtse labbanta, don kar ta fashe da kuka. Zare idanu ya yi ya shiga tambayarta ko lafiya. Shi a tunaninsa babu abinda mace ta Ki jini irin a Hoye mata, idan ana neman aure, shi ya sa shi ya fi so ya sanar da ita, idan abubuwa sun tafi yadda ya dace ai dole za ta sani a gaba, me zai sa to ya bari ta ji a bakin inda za a tada mata da hankali,
bayan alhakin kwantar mata da hankali na wuyansa?
Amma ai ka na shirin auren nata.” Ta fada cikin muryar kuka. Jawota ya yi jikin sa ya rungumeta, a tsanake hadle da Minaal din, “A halin yanzu babu wannan maganar, amma hakan na iya
faruwa gaba kadan, don haka na ke roKon ki jure, ba don halina ba, ki yi haKuri. Ban yi tsammanin hakan ba, amma ba mu muke tsarawa kanmu rayuwa ba. Idan hakan ta zo a cikin Kaddararmu, ki yi hakuri, kin ji?” Ita ba ta ko jin bayanansa, kuka take yi iyayin ranta, har aka fara kiraye kirayen sallah. TJ. Na kan rarrashi. Da ya yi sallah, ya shigo ne ya sameta a yadda ya bar ta. “Kawota na zauna da ita
Kan ki yi sallar.” Jikinta ba Kwari ta mida masa Www.bankinhausanovels.com.ng Minaal, sannan ta wuce, don ta Cauro alwala. Nan
take ya ji tausayinta ya kama shi. Hankalinsa dai bai kwanta ba, sai da ya tabbatar ta saki jikinta kadfan.
Shi kansa yana sane da sa’ar mace ta-gari da ya yi, domin iya zamansu ba a tafa jin kansu ba, sannan muddin ta kula ga abinda yake so, to ba ta fasa yi masa. To a Hangare Claya ga ta, a Dangare Claya ga soyay yar da yake yiwa Ummu Adiyya, wacce burinsa Claya, shi ne ya Bulle ya kai ga har abada tare, har a aljanna burinsa kenan.

****************

Tana shirya Safiyya ne da safe, wayarta ta shiga Kara, sama-sama ta dubi fuskar wayar. Bakuwar lamba ta gani, har kamar ba za ta Cauka ba, amma ta canza shawara ta Claga. “Assalamu-Alaikum.” “Wa’alaikumussalam’ warahmatulah.” “Ina kwana?”
Lafiya Kalau, an tashi lafiya?” “Alhamdulillah!” Ta facia tana KoKarin ta gano muryar, ta san mai muryar, amma da yake ba lamba, sai ta shiga duhun kai. “Salisu ne ke magana. Salisun Abuja.” Oh Yaya Salisu, yaya gida da su Aunty Mashkura?” “Alhamdulillah! Suna Kalau, uhm na shigo Bauchi ne jiya da dare, ban sani ba ko ki na gidan yar kin nan ne na (Airport Road)? Akwai maganar da na ke so na zo mu tattauna.” Ummu Adiyya ta yi shiru tana Www.bankinhausanovels.com.ng nazari, t
o ita kuma? Wace irin magana ce hakan
kenan? “Wani abu ne ya faru?” “A’a ba komai, idan dai ki na nan ko za ki ba ni lokaci sai na zo anjima?”
Eh ina nan.” “To shi kenan na gode. Allah ya kai mu.”
Ameen.” Ta fadla, sannan ta cire wayar a kunnenta cikin nazarin ko menene hakan? Surutun Safiyya ne ya dawo da ita daga guntun nazarin da take yi. Dakin Adda Zubaida ta shiga, ta samu ta idar da karatun Al-Kur’ani. “Adda ga ta,
bari na yi wanka, idan na bar ta a aki, aiki za tai min da turare ko jambaki.” “Ki rinKa dorawa a sama ai kawai, idan ba haka ba, haka za ku rinKa fama.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *