UMM ADIYYAH CHAPTER 62 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 62 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

hakkin dan Adam. Ba abinda ya burgeta da
shi, illa yadda bai boye mata darajar matarsa a
wurinsa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sabanin wasu mazan idan sun je neman karin
mace, sai su yi ta aibanta ta gida,
suna nunawa mace ita ce maganin matsalolin
da suke da su. Su kuma matan abin
takaici, sai su zaci haka abin yake, sai sun
shiga su gan shi da matarsa tif da taya.
Cak! Ta tsaya tana kallon takalman, kafin ta

dawo hayyacinta, ta shaki kamshin mai
su, dago kanta ta yi aiko idanunta take suka
fada cikin nasa, masu duhu da haske.
Ba shiri ta maida kanta kasa, ta hadiyi wani
abinda ba ta san girmansa ba, saboda
sai da ta ji wuyanta ya amsa.
Ta gefe ta matsa, ta yi niyyar gaishe shi, amma
ta san tana budan baki asirinta zai
tonu, domin kuwa muryarta a sargafe take.
Don haka ta shige cikin gidan ba tare da
ta tanka masa ba, ta saman kafadarsa ya bi ta
da kallo, har ta bacewa ganinsa.
Take hannayensa da suke ajiye a gefensa suka
dunkule, bai taba kwatanto wannan
ya zamo yadda haduwarsu za ta kasance ba.
Idan za a shake shi, bai san yaya yake so
haduwar tasu ta kasance ba, amma dai
bai taba kawowa kansa zai zo ya tarar tana
dariya har da mayar da kai baya,
idanunta suna kyalli, tana maida natsuwarta da
tunaninta akan waninsa ba.

Www.bankinhausanovels.com.ng
Lokacin da ya shigo gidan, ya san da mutane a
gidan, wannan ya sa kai tsaye ya
shigo falon, amma da zai shiga falon ya ji
muryoyi na tashi ne, kamar daga sama ya
tsinkayi zazzakar muryar Umm Adiyyah.
Yanzu ga shi sun hadu dukansu biyu sun gaza
cewa komai, bai taba jin ya rasa abin
fadi ba, iya tsawon rayuwarsa irin a wannan
lokacin.
Bai san zafin me daya ma yake ji ba, na gan-
inta da wani da ya yi ko kuwa na cewa
ta mance da shi, tana farin-ciki son ranta a
rayuwa, bayan shi kuma kullum da
tunaninta da taswirarta yake kwana ya tashi,
tsawon shekara guda? Ko kuma na
sakacin da ya yi har wani ya cusa kansa aa
rayuwar Adiyyarsa ne?
Tabbas idan bai yi nesa da wurin ba, zuciyarsa
za ta iya bugawa. Amma daya tashi
bawa kansa mamaki, maimakon ya fice daga
gidan, juyawa ya yi ya koma ciki. Yanaa
shirin kiranta a waya ne, ya ji motsi a kicin,
wannan ya sa ya shiga kai tsaye, hade
da yin sallama.
Bai ida shiga ba, ya hango bakin gyalenta, da
gudu ya isa inda take tsaye gaban
murhun gas, ya zare gyalen a jikinta, yana
kakkabe inda ya kama da wuta.
Da sauri Umm Adiyya ta matsa da baya hade
da dafe kirjinta cikin fargaba, kafin ta
kula da abinda ya ke faruwa.
Tunda ta wuce Yaya Zaid a bakin kofa, ta ji
gaba daya wani jiri yana neman ya
kwasheta. Abubuwa sun fi talatin take ji a wan-
nan lokacin, ji ta yi kamar ta yi kuka,
sannan kamar ta tsaya a wurin ta kare masa
kallo, ya canza gaba daya, tamkar an
kiba, ga
kwarjini, ya dan
gashin da ya bari ya kwanta a fuskarsa
kara masa
kara
hade da gashin bakin sa.
Ga kuma al’ajabin ganin sa a lokacin da ba ta
yi zato ba. Bugun da kirjinta ke yi
kuwa sam bai misaltuwa, ta danganta shi da
dimbin haushinsa da take ji, kodayake
me ya sa za ta ji haushinsa? Shi fa ya manta da
ita, har ma yana shirin daura aure,
wannan yana nufin ya kulle ma shafinta kenan
a rayuwarsa. Kodayake daman me ya
rage? Mutumin da tsantsar tsakaninta da shi a
waya, yaya za ayi ta yi tunanin tana
da wani sauran muhimmanci a wurinsa?
Kai abinda take ji a lokacin barkatai ne, ba ta
yi tsammanin su na da suna ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wannan ya sa ta ji ta shiga ta daura ruwan
shayi, ko za ta ji daidai. Ta yi zurfi a
tunannunkan da suka addabeta ne, kawai ta ji
an fizge mayafin da ta lullube jikinta
da shi. Wani mummunar faduwar gaba ne ya
dirar mata, ta juyo za ta yaki koma
waye ne, sai ta ga Yaya Zaid rike da gyalenta
mai ci da wuta, yana kakkabewa.
Yanzu ta fahimci dumin me take ji tuntuni a
jikinta.
Ina ki ke kallo haka, ki na aiki kayanki na ci
da wuta?” Abin da ya fara furta mata
kenan.
Ban kula bane…”
9
Ba ta Karasa ba ya katseta, “Yaya za ki yi aiki
da dogon mayafi a wurin wuta? Idan
wani abu ya sameki fa? Me ki ke tsammanin
zai faru?” Umm Adiyya kam baki ta
bude tana kallon ikon Allah, sai hucin num-
fashi yake yi, jijiyoyinsa sun bayyana.
Rabon da ta yi magana da mutum sama da
watanni takwas, haka kawai ya zo ya
hau masifeta, kamar dama abu ne na yau da
kullum da suka saba.
Me ya sa ka ke min fada? Ina ce ni ce zan ji
ciwon ba kai ba? Na gode da
taimakonka, amma Allah ne Ya takaita ai.”
Wani kallo ya sakar mata, sannan ya isa inda
take tsaye, ya mika mata mayafinta,
ya juya ya wuce ba tare da ya sake ce mata ko-
mai ba, yana fita, ya tada motarsa ya
bar harabar gidan.
Kai ka sani, ni ina ruwana, za ka zo ka na
tsume min, ka na min fada.”
Kashe wutar shayin ta yi, a take ta ji ba ta mu-
radin sha ma gabaki daya. Sai a
lokacin ta tuno wannan ne haduwarsu ta biyu,
tun bayan rabuwarta da shi. Ranar ba
ta san ya dawo ba a gidan Abba, tana sama ta
hango shi a Kasa ta farfajiyar saman
falon Maami dake kallon waje, sai kuma yau.
Ga shi suna haduwa, sun fara da
masifa.
Sai lokacin ta ji ta girgiza. Da gaske Yaya Zaid
ne ya zo yanzu ya tafi ko dai mafarki
na ke yi1?
***k *******
Tuki yake yi kawai, amma bai san ma inda zai je
ba, sai shiga tituna yake yi, yana
fita, daga karshe ya koma gida. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan ya canza kaya ne, ya wuce kicin, can ya
karaci zamansa, ya dauki gorar
ruwan sanyi a firij zai tsiyaya ne, idanunsa
suka kai kan wani guri daya dan duri
ruwa ya taso, damke hannun ya yi, ya kara
budewa, yana jin kunar da ya yi da
wutar jikin mayafin Ummu Adiyya ya fi sauki,
akan kunar da ke cikin kirjinsa a dalilin
ita kanta Ummu Adiyyar.
Amma daga abinda ya gani yau, bai ma sann
inda zai tsayar da bukatar zuciyarsa ba.
Hasken wayarsa da ke kan dan dandamalin (is-
land) kicin din ne ya dawo da shi
hayyacinsa, ya daga. Ganin daga ofis ne wa-
yar, ya sa ya kashe ya ajiye, domin
baya son duk wani abinda zai katse masa tu-
naninsa da lissafinsa.
Amma ba su dandara ba, sun sake kira,
kira,
Charles.” Ya amsa da murya kai tsaye, kai
ka ce ba a cikin damuwa yake ba.
“Yallaboi, an samu wani sabon ci-gaba game
da lamarin Mr. Akim.”
Me ya faru?
“Mun samu sunan kamfanin da suka dauke shi
aiki.”
“Charles jira ka ke yi, sai na tambaya kafin ka
ba ni ba
yani dalla-dalla?” Ya fada a
gajiye.
“Yana da kyau ka zo ofis tukuna, saboda mag-
anar ba ta waya bace.”
Yatsunsa ya sa a kwarmin idanunsa, ya
muntsini karan hancinsa, ya karewa kansa
kallo, yana sake da bakar T-shirt da wando mai
laushi na auduga ruwan toka
(sweatpants), sam bai yi shirin ya sake fita ba.
**************
Bayan mintuna talatin. Zaid na tsaye a cikin
ofishinsa, wanda wuta kadan aka kunna
don amfanin dare, ya dubi takaitaccen rahoton
da Charles ya mika masa.
“N-Bits? Ban taba jin sunan ba.”
Ni ma sai yau, kuma a bisa yadda suke da
karfi, ya kamata mu san da su.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Zaid ya yi shiru, yana kara nazarin rahoton.
“Hmm! A’a Charles, a bisa yadda suke
da karfi ne ya sa ba za mu san da su ba. Saboda
ba ayi kamfanin nan don komai
ba, sai don a tara muhimman bayanai, sannan a
watsar da kashinsa, a sake tada
sabon kamfani da zai taso, ya fi kowanne, sa-
boda sun bi kan kamfanoninmu sun san
sirrikan gudanar da wurarenmu.”
Charles ya gyada kansa, “Tabbas haka ne.”
Get Mr. Femi. Duk da dare ya yi, zan tashi
Engr Sufyaan da kaina, set upa
conference, we meet N-Bits tomorrow. Inshaa
Allah. Let’s give them a face. (Ka
hada taron gaggawa, gobe zamu hadu da N-
Bits, Bari mu fayyace ko su waye su.)
“Yallabai? Yaya za ayi su amince su karbi
gayyatar mu, ko mu je inda suke tunda ga
harkar da suke yi, wanda ya sauka a kan
ka’ida.”
“Su sun san aikin da suke yi, baya kan ka’ida,
amma ka dauka cewa da ni da kai ba
mu sani ba, kuma muna bukatar su zo su mana
wani aikin. Ka san da cewa ba mu
kadai suka yiwa barnar nan ba, tsawon
shekaru biyu kenan. Yaya za ayi haka kawai
sunansu ya bayyana a gano su? Dole sun
kuskure a wani wuri, kuma ana nemansu
yanzu dole za su nemi mafaka. (AZ IT Consul-
tants) za ta ba su wannan mafakar.”
Charles ya jinjina kai, cikin yabawa fasahar
Ogan nasa.
“Uhm! Yallabai na kira ASP na ji ko Mr..
Ehm Akim zai bada shaida kan sunan
kamfanin da suka dauke shi haya, sai ASP ke
fada min wai satinsa biyu kawai a
hannunsu, ku ka janye karar da ke kansa? Na
san ba hurumina bane wannan Www.bankinhausanovels.com.ng
tambayar, amma laifinsa, laifi ne mai tsauri.”
“Eh, tabbas laifi ne mai tsauri, zai iya yiwuwa
ya gaza danne kwadayinsa, zai iya
yiwuwa yana son ya balle ya gina nasa kam-
fanin ne. Har hakan ya janyo ya yi
abinda ya yi. Yana da iyali, matarsa kuma tana
kirana kaninta. So, ya biya tarar da
aka ci shi, ya dawo kuma da wasu daga cikin
kudaden da ya samu daga hannunsu.
Yanzu haka yana kirana duk karshen wata ya
fada min abinda yake ciki a sabon
wurin aikin sa.”
Yallabai gaskiya kun yi kokari, ba kowa ne
zai iya abinda ku ka yi ba. Allah ya saka
maku da alheri.”
Gefen labbansa ne suka motsa sama kadan,
alamar murmushi.
Suka ci-gaba da hada wayoyin da suka dace su
y.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *